Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "eh shi".


"Okay Zaid Ali Zaki Friend dina ne tun yana London, yana Cambridge ina Oxford so we know eachother for long, and relationship that i have with you ba zai hanani cigaba da abotana da shi ba, so incase kin ganni a gidanki to wurinshi na zo ba wurinki ba".
Duk da ran Hajia Shafa'atu bace yake ta kwantar da kai tace "yi hakuri diyata, ai gidana gidanku ne, kina iya zuwa duk lokacin da kike so kinji diyata?"


Bata amsata ba ta tashi ta shige ciki.
Hajia Er Rabi tace "lallabata zaayi har ta rabu dashi, ban son matsi kin gane?"
Da sauri ta amsa da eh ranta a bace.


Washegari kuwa Yesmin ta dira gaban gate din Gidan Alhaji Zaki. Wayar Zaid ta kira tace tana k'ofar gida
Dama ya shirya yana fitowa suka wuce Asibiti bayan ta shaida ma Ali zuwansu yace yana Consulting room din da suka hadu jiya.


Jiki a sanyaye ya amsa sallamar su, zama sukayi suna kallon juna.
Da kyar suka gaisa.
Dr Aliyu yace “anyi compiling results din duka gasu nan”
Zaid da karfin hali yace “gaya min me ke samun danka baba?”
Yesmin ta mike zata fita Zaid ya rik’o hannunta yace “haba madam, ki kawo ni Asibiti kuma ki tafi ki kyaleni sam”
“Zaid please”
Dr Ali yace “K’amshi gashi ki duba kigani”
Ta girgiza kai
Zaid yace “come on, take it, duba kigani mana”
Hannu ta sa jikinta na dan rawa
Ta duba paper na farko
Ta duba na biyu
Ta duba paper na ukku
Ta duba Xray din
Sai ta fashe da wani irin kuka.
Murmushin takaici Zaid yayi yace “Nifa na sani, i know”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DANMAKAHO 😉


BABI NA SHA TARA 1⃣9⃣
(ILLAR SIGARI 🚬)


Dr Ali yace “haba k’amshi, kar ki tsoaratar da Patient, soon fa zaki fara HouseManship, haka zaki dinga sanar musu da results? K’amshi, ina so ki kama kanki yanzu, ki kwantar da hankalinki donAllah”.


Zaid yace “Huh, to meye? Ni ai na san ciwona, na san matsalata, ba sai kun sakaya komai ba”.
Dr Ali yace “Zaid, you are sick”
Zaid yace “i know”
Dr Ali yace “Busan hayaki na illata kusan ko wani gaba na jikin mutum kamar ciwon Huhu, ciwon Zuciya, cutar Mak’ogaro wato Bronchitis, cutar jijiyoyin jini, hak’ark’ari ko awaza, ido, baki, gabar haihuwa, k’ashi, mara da sauransu”.
Numfashi ya aje yace “Zaid, munyi investigating jikinka, sakamakon busan hayakin da kakeyi wanda ba sigari kadai bane har da wiwi, Daya daga cikin jijiyoyin dake bada jini ta samu matsala, gab take da ballewa, a yanzu baka da Athma amma rashin daina shan sigari na iya janyo maka Athma, Alhamdulilah lafiyar Huhunka kalau, amma rashin daina shan sigari na iya taba maka Huhunka wanda wallahi Zaid akwai mugun damuwa in ba ka daina shan Sigari ba. Zaid akwai Tuberculosis a tattare da kai, duk da dai minor ne, possibility of it becoming major da yawa ne, tunda you are on the verge of coughing out blood, kuma abinci bai dameka ba, so TB din can be cured tun kafin yayi worsening”.


Yesmin k’amshi hawaye ke kwaranyowa daga idanunta, shi ko Zaid cewa yayi “nifa nasan banda lafia, but bansan haka abun yake ba”.
Dr Ali yace “kaje Asibiti? Ko mene?” Zaid yayi murmushi mai ciwo yace “banzo Asibiti ba, kawai tuna watannin da suka wuce nasan jikina ya chanza, in nayi tari k’irji na na ciwo, to nasan wallahi banda lafia, kuma its obvious Sigari ne, tunda ina mishi Shan fitan hankali”.
Dr ya fara mai fada “haba Zaid, da tun a lokacin kazo Asibiti ai da an rage wani abun, da komai ba yi worsening ba, ciwo ba a mishi zurfin ciki, da anga slight change, kamata yayi a garzayo Asibiti”.


Zaid yace “nifa Its Fine”
Cikin muryan kuka Yesmin tace “dallah, its not fine, Ali donAllah ka rubuta mishi magani, and advice him as a Doctor and as a friend”.


Rubutu yayi sosai a Wani takarda kafin ya dago ya kallesu, mik’a ma Yesmin takardan yayi yace “gashi magungunan ne, a siya ya fara Medication ASAP”.
Yesmin tace “InshaAllah kam, yanzu zaa siya”.
Tashi tayi tace barinje na siyo kafin ku gama magana”.
Tashi tayi ba wanda yace mata komai.


Gyara Zama Doctor yayi yace “Chronic obstructive pulmonary disease (COPD) is a chronic inflammatory lung disease that causes obstructed airflow from the lungs.
Wannan shine yake kama duk wani rik’ak’e a shan Sigari, wanda in ya kamashi, in Allah be sauwake ba sai dai mutuwar mutum.
Alamominshi sune; Karancin Numfashi musamman wurin yin ayyukan yau da kullum kamar tafiya, Atishawa, k’ank’ancewar k’irji, kaikayin mak’ogaro da farin safiya, chronic tari da mura da zai haifar da majna da tasono wanda zaa ganshi yellow, fari ko green k’arara, baki zai zamu blue yatsu ma haka, yawan gajia da kasala, rama, kumburin kafa, guiwa da duk wani gaba na jiki”.


“Kafin yazo ga haka Zaid, donAllah ka yi ma kanka fada ka datsar da wannan dabia ta shan sigari a busawa jiki hayak’i, Zaid, nasan its hard, you are addicted to smoking, it would be hard for you to stop now, amma zakayi duk yanda zakayi ka rabu da Sigari rabuwa na har abada, medication dinka donAllah ka dinga yi, kar ka aje magungunan nan, you have to be strong for your Sister Okay?”.
Zaid yace “InshaAllah zan bari”.
“Allah ya baka iko” ya amsa da “Ameen”
Haka yayi ta mishi nasiha da k’ara karanto mai illolin hayak’i har Yesmin ta dawo dauke da Ledoji.
Dr Ali ta ba, nan ya ware duka magungunan ya masu bayani da yanda zaiyi amfani da su, godia suka mishi, Zaid ya kwashi ledojin suka fita.


A cikin Mota ya ga duk ta wani damu yace “Yesmin” da sauri ta katseshi tace “donAllah kar ka ce min komai in har ba zaka ce min kayi quitting Sigari ba”.
Numfashi ya ja ya sake yace “Yazz banson miki k’arya, amma its not easy, i am addicted fa”.
Hannu ta sa a bakinshi tace “shhh, kar ma ka saka a ranka wai ba zaka iya ba, wallahi zaka iya, let me help you please”.


Hannu ya sa ya murza kannanen idonshi yace “Okay” kafin ya maida kanshi kan kujera ya kinshingida, ganin haka ya sata saka seatbelt tare da yi ma Motan Key.
Sai da ta tsaya Yusrah’s Kitchen ta musu Take away din Abinci kafin suka wuce Gida, straight dakinshi suka nufa, sai da suka ci Abinci kafin ta ballo mishi magungunan kamar yanda Dr ya musu bayani, ba gardama ya karba ya afa duka kusan guda Goma a baki ya sha.


“Yesmin kije Gida ki huta donAllah” kallonshi tayi cike da so da kauna tace “aa zan tsaya tare da kai”.
Yace “aa donAllah, ki tafi, na ji sauk’i, dama chan ba abunda ke min ciwo, kawai kece da over reacting” harararshi tayi cike da k’auna tace “naji din”.
Yace “dagaske kije Gida, in tsoro kike, na miki Alkawarin ba zan sha sigari ba”.
Murmushi tayi tare da mik’ewa ta dau jakkarta gami da cewa “I trust You, zan kiraka every minute of every hour”.
Murmushi yayi yace “kar kuma a dameni, zan sha magani a lokaci”.
Murmushi sukayi a tare bata san lokacin da tace “I Love You” ba.


Sosai ya k’ame k’am yana kallonta yana san karantar fuskarta, ita kam dan daburcewa tayi ta rasa gaba zatayi ko baya.
Murmushi yayi yace “ki kula da kanki K’amshi, kiyi tuk’i a hankali, kar ki damu da yawa a kan Zaid, Zaid ba zai sha Sigari ba”.
Wani farinciki ke ratsa zuciyarta tace “Madallah da Zaid, zan zo na ganshi Gobe, Sai Allah ya kaimu”.
Yace “Allah ya kaimu”
Sallamar kenan ta tafi ba tare da ta shiga Gidan Anty Shafa’atu ba.


Zaid kam kamar yayi hauka, burinshi ya sha Sigari, ji yake ko wani gaba na jikinshi na kira mishi Sigari, safa da marwa yayi tayi, kwashe Sigarin yayi duka na dakin ya fita dasu zuwa Bencin Eskaley.
Ganinshi ya sa su Tero ihu da murna, mik’a musu yayi yayi saurin juyawa don kar su fara sha gabanshi ya ji shima yana son Tabawa.
Ranar a dakin Dalo ya yini don kar ya kadaice har zuciyarshi ta fi karfinshi ya sha Sigari.


Haka ma washegari, har akayi kwana uku Zaid be sha Sigari ba, amma da ka ganshi kasan bai lafia, duk ya tsomare, kullum sai Yesmin tzo duba shi, kuma tana jin dadin yanda yake responding to treatment.
A rana ta hudun ne Alhaji Ali yace an mishi Sata naira dubu dari 5, nan take Shafa’atu tace “ai Zaid ne, ta ganshi ya fito daga Dakin”.
Ba Bincike Alhaji Ali ya Bi Zaid daki ya hau dukanshi ko ta ina, yana laantarshi yana tsine mishi ba tare da ya damu da yanayin da Zaid din ke ciki ba.


Nan take ya kira Police Station aka zo aka tafi da Zaid, rannan Dalo ta yi kuka kamar zata mutu.
Alhaji Ali yace da DPO ku nakasa min Shi har sai ya fito man da kudina, ana kai Zaid bayan karta aka rufe shi da duka ko ta ina, ga rashin Lafia shi kam Zaid be san dukan me ake mishi ba, kuma ya k’i furta kalman Bani bane.


Yesmin tayi ta kiran wayarshi be dauka, hankalinta ya tashi, ta k’araso Gidan, dakinshi ta wuce straight bashi ba alamunshi.
Sai wayarshi da ta gani kan gado,a sukwane ta shiga cikin Gida dakin Dalo ta isketa durkushe tana kuka, da sauri ta taryota jikinta tana tambayarta baasi.


Dalo ta kwashe komai ta gaya mata, hankalinta ya tashi, ta fita da sauri, ta shiga Motarta ta wuce Police Station don amsan bailing Zaid, amma fir aka k’i bada bailing shi.
Tunda case din gidane wai sai wanda ya sa aka kulleshi yake da daman firdoshi.
Rasa abunyi Yesmin tayi.
Taci kuka ta gode Allah
Sauro bata so ya tabashi balle wani abu babba da sunan duka.
Ya zatayi? Taya zata fitar da masoyinta daga cikin wannan k’angin?.


Riii daga Police Station ta wuce Gidan ALHAJI Ali. A cikin gida daga inda ake parking Mota ta iske Dalo ta hade kai da bango.
Ta na ganinta ta rugo ta rungumeta tana kuka.
“Aunty Yesmin donAllah bani wayarki na kira Nene taje ta firdo min da Yayana, Nene kadai ce zata iya fito dashi, bamu da kowa sai ita”.
Yesmin ta kalleta tace “Dalo ina so ki yarda dani kingane? Yanzu ba Nene kadai ne da ku ba, ina nan tare da ku, i want you to trust me”.


Hannunta ta ja zuwa cikin Gidan inda Hudu da Hajia Shafa’atu suke zaune, suna ganinta da yanayinta suka mik’e tsaye.
Kallon Dalo tayi tace “je ki daki ina zuwa”.
Da sauri ta wuce daki tana haki.


Kallon Hudu tayi a kyamace kafin ta waiga ta kalli Anty Shafa’atu tace “kina jina, ina so ki ba Mijinki Umurni ya firdo min Zaid”
Aunty Shafa tace “Yesmin, ki yi hankali dani, ni ba tsararki bace, kar ki dinga ganin ina lallabaki kice zaki kawo kin raini, ba ruwanki da duk abunda ya faru a gidana”.


Yesmin ta kankance idonta tace “kece zakiyi hankali dani, ina da sirrinki a tafin hannuna, sosai na san komanki, shekarunki 15 zaune kina zaman jiran Alhaji Ali, ke harta mahaifin Annah wanda kuka...” da sauri ta toshe mata baki ta na huci don sirri ne daga ita sai Er Rabi suka sani, bata san Er Rabi sakara bace tana tatauna sirrinta da diyarta, ya zata yi mata haka? Meyasa zata mata haka? Wannan maganar ko Hudu bata so ya sani.


A dakile tace “Yesmin, me kike so ayi yanzu?”.
Ture hannunta tayi daga bakinta tace “ki sa Mijinki ya firdo Zaid daga Cell”.
Wayarta ta ciro a charge ta lates wayar Alhaji Ali, cike da umurni tace.
“Alhajina, ka sa su sake Zaid”
“Aa kar ka damu, ya dawo gida kawai bakomai”.
Ta kalleta tace “Angama”
Yesmin tayi murmushi tace “barkanki”
Ta juya ta fita daga Parlorn
Hudu da mamaki yace “Aunty, maganar me takeyi?”
Banza Shafa tayi dashi ta wuce daki tana hucin tana so ta san ta yanda zatayi maganin Yesmin.


Yesmin ta jira a Dakin Zaid kusan hour daya, sai ko gashi ya shigo rai a bace, dauke da kwalayen sigari kusan 5, jikinshi ko ina bari yake, wai shi zaace ya saci kudin babanshi? Shi Zaid zaa lakafa ma Sata?”.
Yesmin ta zo rik’eshi ya daka mata wani irin tsawa wanda ya kada mata yan hanji, janta yayi ya fitar da ita waje tare da rufe kofar yana jin magiyarta na ya bude k’ofa amma fir ya k’i.
“Don Girma da Darajan Allah kar ka sha Sigarin nan, Zaid akwai hanyoyin da zaka mance damuwanka ba tare da kasha komai ba,donAllah Zaid” be ma san tana yi ba.


Kamar mayuwanci ya kunna sigari ya fara Zuk’anta irin an dade baa hadun nan ba, ya shanye kwali daya.
Ya kwance kullin world ya hadeta ya fara zuk’anta ba sassautawa sai da ta kai mai karo sannan yayi Mankass kan gadonshi.


Baccin Awa Hudu yayi, kafin ya tashi jikinshi duk a mace, amma kafin ya bar kan Gadon sai da ya kunna ma wata sigarin wuta, sai ya tashi ya bude k’ofa da niyyar fita, Yesmin ce zaune kan dakali tana waya da sauri ya murje sigarin da k’afa yana fadin “Ohh Yesmin”.


Taci kuka harta gode Allah.
Riko hannunta yazoyi ta ja da baya
Ya sake yunk’urin rikota tace “ka k’yaleni”
Chan kasan mak’ogaro yace “Yesminnn”
Tace “ni ka barni”
Hannunta ya ja suka koma daki.
“Yesmin i am sorry”
Yesmin tace “Zaid donAllah ka rayu, live healthy, if your life is meaningless to you ni it means the world to me, don Girman Allah live well”.


Zaid ya murmusa ya rik’o hanayenta duka yace “Yesmin kinga irin life din da nake living? Babana Mahaifina ya lak’a min Sata, ya kaini Police station, aka min dukan mutuwa, babana mahaifi fa, tsinuwa, laanta suna kaina,to wani jin dadi ya rage min? Gaya min, meyasa ba zan sha abinda ya fi sigari ba?”


Kuka Yesmin take sosai, harda Majina, ya girgiza mata kai yace “Aa, Yesmin, ki tayani addua, dont stress yourself, na san kina min k’okari, nasani kina kan yi min kokari, amma donAllah kar ki ba kanki wahala, ba zan iya daina shan sigari ba, cikin kwanaki ukun nan i felt like i am dying, na san ba zan wuce yau ban sha world ba, Yesmin i cant thank you enough, amma wallahi in lokacina yayi ko da shan sigari ko ba da shi ba, zan mutu, everything is formality, in lokacinka yayi ba makawa sai ka tafi, donAllah just pray for me Okay?”.
Kuka takeyi ta kasa magana, da kyar ya lallabata tayi shiru.


Tun daga ranan Yesmin sai tazo Gidan tare suke yini, sunyi mugun sabo da Dalo, har ta sai mata waya.
Zaid da Dalo na son Yesmin sosai, tun Aunty Shafa na ma hajia Er Rabi mita har ta hakura, ba yanda zata yi da ita, hajia Er Rabi kuwa tace duk ranar da ta bata ma wa yesmin rai karshen alakarsu yazo. Yesmin ta zame mata ciwon ido.


Zaid ya kan ji nauyin Yesmin sanin cewa ta na sonshi amma shi baya jin komai game da ita, tana da wuri mai girma a zuciyarshi da yafi karfin soyayya, yana sonta kamar yanda yake son Sadiya Dalo.
Bata taba nuna mishi wai tana so ya sota ba, a cewarta ganinshi cikin farin ciki ya fiye mata komai, ta kalleshi ta ga murmushinshi ya isheta rayuwa.


Yesmin Kamshi ta zamo wani jigo a gun Zaid da k’anwarshi Sadiya. Ta fara HouseManship dinta a General hospital for 10months kafin aka turata Ondo Akure tayi Service kafin ta dawo Katsina a Matsayin Dr Yesmin Hamis.


C I G A B A N L A B A R I


LABIBAAAA.......




#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa


[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN2⃣0⃣
(KALLON KALLO👀)


Yesmin K'amshi ta fito sanye da wata doguwar jallabiya mai kyaun tsiya, daga bacci ta tashi a dakin Aunty Shafa, k'amshinta ya cika gurin.
Hudu ne kadai a Parlo, Auntyg Shafa'atu sun fita da Annah.
Hudu na ganinta ya ji wani abu ya fizgeshi, da murmushi ya taryeta har ta zauna ta daura k'afa daya kan daya.


Bude hak'oranshi yayi yace "Yas Yas, Allah ua miki kyau wallahi kamar ke kikayi kanki".
Guntun murmushi tayi tace "aa ba ni nayi kaina ba, Allah ne yayi ni"
Yak'e Hudu yayi, ya san Yesmin da datso magana dole sai yayi taka tsantsan.
Yace "wai Dr Yas nayi ta kiranki baki dauka, ba kuma kya calling back, kuma na san kina ganin Missed call".


Bata tanka shi ba, ta ciro wayarta tace "wai har yanzu baka gama ba? To ina jiranka a ciki please". Ta saka wayar cikin jakka tace "Uncle Hud, wallahi ina ganin missed calls dinka, attimes ma akan idona kake kira, but attimes kawai am not in the mood to pick your call kagane? Don na san usual surutanka zaka min, kuma ni banda energy din jinsu over and again kagane?".


Kafin Hudu yace wani abu, ya shigo, babu wani abu sabo a jikinshi amma sosai ya ma K'amshi kyau.
Tuni ta mik'e tsaye har ya tako har gabanta, kallon kallo suke wa juna, Hudu na zaune ya gama k'ullewa ya kalli wannan ya kalli wannan.
Gira Zaid ya daga mata yace "Ya Da Kallon?".


Murmushi ta sakar mai tace "Sosai kayi Kyau Zaiduna".
Kafin Zaid yayi magana Hudu ya fincike Zaid ya mayar dashi gefe ya sha gaban K'amshi yana huci yace;
"Yanzu ke Yesmin ta kan wannan Dan Makahon mara gata kike min wulakanci? Ta kanshi kike k'in saurarana?".


Zaid yace "kai so kake na maka mugun bugu ko? Ka manta bugun tsiyan da na maka ko".
Hannu K'amshi ta daga mai tace "kash Zaid, rabu dashi, ba girmanka bane magana da Agola, akwai rashin gata da ya wuce agolanci? Yana kasan kafar yayarshi yana fadanci kamar wani marok'i sai abunda ta dauka ta bashi, kamarshi yazo yayi katokato, cima zaune, ba cis ba as, duk randa babanka ya rabu da yayrshi ba baida sauran gata, bai da amfanin komai, kar ka sake ranka ya baci ta kan wannan cima zaune, barin kira Dalo, don Outing dinnan da ita zamu".


Wuce su tayi duka, shi ko Zaid kashe ma Hudu ido yayi tare da rufa ma K'amshi baya.
Wani Ihun bakinciki Hudu ya sake ba wanda ya kallo inda yake suka shige dakin Dalo a tare.
K'amshi tace "Hajiya Sadiya tashi muje Yau outing zamuje"
Ido ta zaro tace "ina zaku?"
K'amshi ta dagota daga kwancen da take tace "dake zamu ko ma ina zamuje".
Dalo ta sake ware idonta tace "ni ina zanje? Baba ya hanani fita fa".
K'amshi tace "come on my friend get up and dress up".
Dalo tace "Aunty Yasmin ki rufa min Asiri donAllah, wallahi Baba yace kar na sake na taba fita, ya Zaid gaya mata donAllah".
Zaid ya murza idonshi da murmushi a fuskarshi yace "Ai fa Dalo Yesmin ba zata ji ji ba, tunda tace da ke zaaje da ke zaaje din, sai ta san yanda zatayi da baba in ya kama mu, ki tashi dai kafin ya dawo muje mu dawo".
Dalo tace "in suka gaya mishi fa?"
K'amshi tace "i know how to shut them up, trust me".


Numfashi Dalo ta ja ta sake a hankali kafin ta bude Wardrobe ta ciro wani doguwar rigar da Mancy ta aiko mata dashi, gudun magana ne ya sa bata taba sakawa ba, Zaid yace "zan jiraku a waje" ya fita.
Sai da ta shirya suka fita tare gaban Hudu wanda yana ganin fitowar Dalo ya dauko waya don shaida ma yayarshi.


Zaid a gaba Dalo a baya Yesmin a seat din driver suka fita daga Gidan.
Wayar Dalo ke ringing ko da ta duba Aunty shafa ce, sai da hanjin cikinta suka kada, ba kasafai Aunty shafa ke kiranta ba, in har ta kirata to ita Aunty shafa ta fita kuka tana so Dalo ta mata wani abu sai ta kirata.
A daddare tace "donAllah ku maidani Gida bana son problem, ga Aunty shafa na kirana".
Yesmin ta cigaba da tuk'inta tace "answer and put the phone on speaker".
Bin umurnin Yesmin tayi ta kawo mata wayar daidai gemunta.


Muryan Aunty Shafa ya karade Motar "Ke Sadiya Gidan Uban wa kika tafi harda sa sabbin kaya, karuwancin da kika saba zaki ko?".
K'amshi tace "Wai ya Aunty Shafa? Dalo na tare dani, ko akwai matsala ne?"
Da sauri ta sauta murya tace "kingane Yesmin Babanta ne be so tana fita a gidan".
Yesmin tace "to muna tare ba wani wuri zataje ba".
Yesmin ta ma Dalo alamu da ta katse kiran.
Zaid na gaban Mota bece musu komai ba, ya san akwai wani abu da Yesmin ta sani wanda Shafa take tsoron a sani shiysa take daga mata tana kuma bari tana takata amma ko so daya be taba son sanin ko meye ba, abu daya ya sani shine ya yarda da Yesmin dari bida dari.


Chimex Shawarma ta nufa dasu, su ka bada order aka gasa musu guda biyar duk chicken and sausage ta biya kafin suka je Havillah Ice Cream.
Anan suka ci Shawarman bayan ta siya musu icecream.
Fira sukayi su uku cike da kaunar Juna, sukayi pictures kafin suka koma mota, yawo kawai sukai tayi a Garin Katsina, Girman Yesmin ya k'aru a idon Zaid, don ya dade be ga Dalo cikin farinciki irin na yau ba, sai da ta tsaya a Dadin Kowa ta siya ma Dalo Chocolates kafin suka koma Gida gab da Maghrib.


A kusan tare suka isa Gidan da Baba. Ganin Sadiya da Zaid a tare ya sa zuciyarshi nauyi, Yesmin tace "Ina wuni Daddy" ya amsa da murmushi "lafiya lau Yesmin yaushe aka zo?"
Tace "dazun da safe na zo, na zo muku weekends" yace "ayyah mungode sosai ina sukayi posting dinki bayan service?" Tace "General hospital na Kankia" "Allah ya taimaka" yana kallon Zaid da ya dauke kai ita kuma Dalo ta na jiran saukan fada ko duka a daddare, be ce musu komai ba, gaba yayi zuciyarshi na mai nauyi, yaranshi.. ya Allah".


Yesmin ta kallesu duka tace "muje ko?".
Tayi gaba suka bi bayanta.
Suna hanyar parlo sukaji muryan shafa'atu na cewa "Alhaji kaga Sadiya tun dazun ta fita, har yanzu ba ta dawo ba".
Nan da nan fuskar baba ya chanza " Ina Sadiyar, ba zata huta ba sai ta jawo min magana cikin Gidan nan ko? To kafin ta kasheni ni sai na kasheta".
Tuni Dalo ta koma bayan Yayanta a tsorace, shima Zaid ya tsorata da sudden change din baban, yanzu fa ya gansu, ya san tare suke, amma be ce komai ba, amma matarshi tayi magana duk ya koma wani zararre, matar nan ta maida masu mahaifi kamar wani toy.


Yesmin ta kallesu tace "Relax, ba abunda zai faru" parlorn ta k'arasa shiga ta wurga ma Aunty Shafa'atubwani mugun harara mai ma'anoni da yawa. Hajia Shafa ta dan tsorata tace "Laah kaga Alhaji na manta, ashe Sadiya da Yesmin suka fita, na ma manta, kar ka damu". Kamar wani pagal ya washe hak'ora yace "au haba dai? To to to ashe suna tare da Yesmin, ai ba damuwa, barin shiga daki" yayi haba Hajia shafa tayi saurin rufa mai baya don bata shirya haduwa da Yesmin ba.


Sai da suka kai Dalo har daki kafin suka fito a tare.
Hudu da Annah suna tsaye a Parlo.
Don Zaid ya k'ular da Hudu don ya san yana son Yesmin yace "Yesmin ayi rigegen zuwa dakina" da daria tayi saurin fita ya rikota ta fizge hannun ta arta a guje shima ya bita a gujen, bakinciki kamar ya kashe Hudu.


Yanzu shi ke gaba tana biye dashi a baya sukayi BQ.
Ita kuma ta fito daga dakinsu da Plates a hannu ta ga wata na bin Zaid suna gudu suna daria.
Zuciar Labiba ya halba.
Chak Zaid ya tsaya yana kallonta yanda itama take kallonshi, hakan yasa Yesmin chogewa itama don kallon abunda yake kallon.


Budurwa ce ta gani tsaye daga chan bangaren tana kallonsu, daga inda take ta hango fushi a idon yarinyar da bata wuce 18 ba, kallon Zaid tayi ta ga hankalinshi kacokam na gun yarinyar da wani expression a fuskarshi da ta kasa gane ko menene.
Yarinyar ta ga ta share wani abu a idonta kamar hawaye, ta wuce kitchen sauri sauri gudu gudu, a kan idonsu ta sake dawowa a guje ta fada daki.


Wani jijiya Yesmin ta hango a kan Zaid duk ya damu.
Jiki a sanyaye tace "Zaid who is She?"
Murya chan k'asa yace "Noone".
Kafin tace wani abu tuni yayi gaba ya wuce dakinshi tare da barinta tsaye.
Gidansu Labiba Yesmin ta kalla kafin ta tsaya wani nazari kafin ta shiga dakin Zaid ta ganshi kwance rigingine duk yanayinshi ya chanza.
Murmushi tayi tace "Yau ko ka

Please Login or Register in order to submit comment