Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban shigo dakinka ba, in na samu ganinka irin haka ya wadatar dani".


Dif wayar ta mutu sakamakon k'arewar credit dinta, da sauri Zaid ya duba wayarshi ya ga call ended, shi ya san bai kashe wayar ba, baya so ya katse wayar, ya na so su cigaba da magana, ya na jin dadin muryarta, so yayi ya sake kiranta, ya ma manta tana gabanshi, ta na lura dashi sosai, har ya dago kai ya kalleta, daria tayi ta mishi alama da katin wayar ne ya k'are, kunya yaji don gani yake ta dago damuwa a fuskarshi, tashi yayi ya shige daki.


Ita ko farinciki kamar an mata kyautan kujerar Makka, ta na cikin jin dadinta ne wayar Jay ya shigo, murmushi tayi ta dauka da Sallama. Da korafi ya fara.
"Labee nah, anya kin damu dani kuwa? Ba kya nemana, ba kya kirana, in na kiraki ba kya dauka, ko laifi na miki Labee?" Kamar yana gabanta ta girgiza kai tace "ko daya Jay, wallahi issues ne suke ta faruwa a gida, ruwan sama akayi kwana biyu, bangon Gidanmu ya fadi".
Jawad ya jajanta mata, yace "yau Saturday kuna gida" tace "eh wallahi" "ina zakije to?" A ranta tace dakin Masoyi amma a fili tace "babu fa, ina gida ba wurin zuwa".


Cike da shauk'i Jawad yace "ya kamata ace ina kallonki a halin yanzu, wallahi Labiba nayi missing dinki sosai, murmushi tayi tace nima nayi missing dinka". Jawad yace "ki saurareni nan da nextweek ko ta sama inshaAllah, zanzo naganki farincikina". Murmushi Labiba tayi tace to nagode.
Firan Soyayya sukayi kafin ya mata sallama, tashi tayi ta fada kitchen don daura Sanwar rana.


Kullum Sai Labiba taje dakin Zaid ta ganshi kafin ta tafi Makaranta, so da dama har ta gama surutan ta ta fito bai ce mata komai, ba ta kuma zuciya don banzan da yake da ita baya hanata dawowa gobe, in kuma ta dawo Makaranta zata tsaya a Bencin Eskaley ta ga in ya na nan, in ko bai nan da ta dawo Gida zata kwala mai kira a waya ya fito waje suna kallon juna daga inda suke suna waya.


Yau Talata sun fito daga Aji ita da Aisha, suna zaune a Caf suna cin Abinci sai ga Abu Sideeq, da murmushi ya k’arasa gunsu, su ma suka mayar mai da martannin Murmushin, kujera ya ja ya zauna yana jefan Labiba da kallon k’auna, tana cin Abinci ta waigi ta kalleshi tace “ba zaka bar kallona haka ba sai ka k’ara So na? Bayan na ce maka ka daina So na”.


Shafa dan gemunshi yayi yace “ba ni zan yanke hukuncin daina Son ki ba Labiba, ba yin kai na bane”.


Cokalin hannunta ta ajiye tace “Na sani, ba yin kan ka bane, So ne, ba kayi laifi ba, ba kai ka zabi ka so ni ba, zuciyarka ce, wanda baka da damar controlling dinta in har ta kamu da Soyyaya, za ta iya kamuwa da Son Fari, bak’i, mai kyau ko mara kyau, nakassashe ko mai lafia, mashayiya ko mazinaciya, So ba choice dinka bane, bakai ke zabar So ba, So din ne ke zabanka, amma ina kiranka da kayi So domin Allah”.


Abu Sideeq yace “Kinga wannan dalilin ne ya sa nake jin Zuciyata ba zata iya daina Sonki ba Wallahi bana son weekends ta yi saboda ba na samun ganinki, kin hanani kwatancen gidanku, ya zanyi?” Jinjina kai tayi tace “na san yanda kakeji trust me, wani lokacin zaka ji zuciyarka kamar ta dare a duk lokacin da baka tare dani ko? To So ne, shifa haka So yake, baida hakuri kamar Zawo, ina maka Uzuri, nima ka min uziri, Abokantaka kawai zan iya baka, wallahi kafin karfin wulakacin gu na, shiyasa na ke gaya ma iyakar gaskiana”..


Baya son maganar nan, mik’eewa yayi tare da kallon Aisha da ta cika da takaicin Labiba, yace “Sholy, barin je Class” da kyar Aisha ta murmusa tace “to Abu Sideeq bye”.


Ba tare da Labiba ta lura da Aisha ba ta cigaba da cin Abincinta, Aisha ta zundureta ta k’afa. Labiba tace “Yadai?” Aisha tace “wai ke Labiba me ke damunki?” Da mamakinta kalli Aisha tace “me ya faru?”.


A hasale Aisha tace “Why are you so Blunt? Me ya sa ba kya kauda Ido? Meyasa kike fadan abu kai tsaye? Mace fa kike fa, da kike ma Abu Sideeq magana haka wallahi ji nayi kamar na kashekinda mari don kunya da takaici, kin sake baki sai mishi bayani kike a kan Love, aa ke ga Dr din Soyyaya, kinsan me ke damunshi kaza da kaza, ki dinga sa wa bakinki linzami, dazun ma na ji su Hamza na gulmanki wai kince ma Yusuf kayan da ya saka ya mishi kyau, Labiba Ahmad ina ruwanki da kyaun da Yusuf yayi? Meye ruwanki da kayan da ya saka? na san you are a straightforward person, amma ba komai bane yazo bakinki zaki fada most especially Maza, ban san ya kukeyi a kudu ba amma mu a nan Arewa ba haka mukeyi ba, yanayin maganar mu da Namiji daban yake.


Ji fa daga randa Abu Sideeq ya zo gaya miki sirrin ranshi tun kafin ya fada kikace kin san yana sonki, haka fa kika ce mishi na son kana sona, gaba da gaba fa, haba Labiba, donAllah ki dinga Jan Aji, in namiji ya zo miki da wani bukatam So ki nuna ma baki san me yake nufi ba har sai ya furta da bakinshi, duk da Ya Jawad Yaya na ne, amma wallahi kin yi saurin ba da kai da yace yana sonki, baki bashi wahala ba, Mace ga kike, Labiba i am not criticising you, ba zan dauka ba in aka cigaba da yi da ke don kawai kina fadin raayinki ba wanda tsakaninki ne daAllah, but don Allah ki sai ma kanki mutunci, Mace da yanga, nuna isa da Aji aka santa, ba saurin ba da kai bori ya hau ba, a haka maza na Sonki ina ga kin fara jan Aji da yanga?”.


Labiba da take sauraron kawarta ta na jin abunda take cewa tace “Aisha Usman, Kina ta fadan Aji Aji, me kike nufi ne da Aji? Wai meye shi Ajin?”.


Aisha ta kalleta sosai, ta karanci har ranta bata san me take nufi ba, ta gyara zamanta tace “Labiba, You are a treasure and you are priceless, donot give anyone reason to look down on you, do not let anyone stomp on your Pride, its Ok to be straightforward, But Here in the North, a Girl’s Ego Comes first Okay?”.


Ta dade tana nazarin maganganun Aisha kafin tace “Aisha so a Arewa zubar da aji ne in ka fara approaching Guy, like kace kana son Namiji maybe don yana burgeka or something?” Da sauri Aisha tace “What? Ai da in tareka ince maka ina sonka, gwara Sonka ya kasheni tab, wannan ai zubar da Aji ne, ba girma”.


Murmushin Takaici tayi tace “To, dalilin kenan? Shiyasa in tace ma DanMakaho ta na sonshi ya keji kamar tace “zo mu yi zina ko zo mu kashe wani, Abun Mamaki ba zai taba k’arewa ba.


“Aisha yanzu in nace ma Namiji “Ina Sonka, ina kaunarka DonAllah ka So ni fa?” Aisha ta zare ido kamar Labiba tayi sabo tace “nace miki da kika gaya ma Namiji haka gwara kin koma gun mahallicinki da sonshi, ai zaki sha gori tunda ke ki kace kina sonshi, zai ta tutiya kan cewa ba shi yace yana sonki ba ke kika rok’eshi da ya soki, za kuma ki ga wulakanci kala kala indai Namiji ne”.


Labiba da tambayoyi kala kala a bakinta tace “Zai ta miki wulakanci yace baki da Aji ko?” Da sauri Aisha tace “Ehmana, zai ce ke dai baki da Aji, kin kawo min tallar kanki, ballagaza kawai”.


Da sauri Labiba tace “meye Ballagaza?” Aisha tace “Worthless person with no self respect” wani murmushin takaici ya subuce mata a hankali tace “WOW!!” nan ne kalaman shi suka dawo mata;


“KI SANI BA ZAN TABA SON MACE MARA AJI BA, BA ZAN SO BALLAGAZA IRINKI BA MAI TALLAN KANTA, MACEN DA ZAN SO KOBNAN GABA ZATA KASANCE MAI AJI, MAI KUNYA”.


A yanzu ne ta fahimci duk wata kalma da ta fito bakinshi, mai ya sa bata fahimci hakan ba? Ya Rabb, kallon da ya ke mata kenan?.


Tashi tayi ta saba jakkarta tace “Aisha Gida zanje” Aisha da mamaki tace “Gida? Lectures din 2-4 din fa? Labiba ta girgiza kai tace “ ba zan yi ba, gida dai nake son Zuwa”.


Nan da nan Aisha ta shiga damuwa tace “Labiba kinji haushin maganar da na miki ne? Kiyi hakuri donAllah” Labiba ta murmusa tace “ko kadan Aisha, baki bani haushi ba, illama taimaka minda kikayi kika firdo ni a duhu, sai dai in gode miki. Aisha zan ganki gobe inshaAllahu”.


Da sauri Labiba ta fita daga Cafteria ta bar Aisha, straight ta fita Makaranta ta ko ci saan samun abun hawa ba ta tsaya ko ina ba sai Gida.


Tun zuwanta Katsina Yau ne karo na farko da ta ji ranta ya baci, ita ya ke ma kallon Ballagaza mara Aji? Wacce bata da kamun kai? To Laifin me tayi? Son shi shine Laifi har ya ke danganta ta da ballagaza mara Aji? Saboda Son shi? Ya Allah, tayi mamaki, sakamakon da kake samu kenan in ka fada son wani? To indai haka so yake, Allah ya wadaran So, ba ta so kuma, ba ta so ta yi Soyayyar kuma.

Runtse idanunta tayi da ta tuna ya fa gaya mata bak’ak’en maganganu da yawa, tunanin wanda ta yi ya fi bata ranta fiye da ko wanne inda yake cewa
{“ba zan taba sonki ba, don baki da aji, bana son classless person, kina zuwa dakin Namiji, wa ya san ko dama haka kike? Wa ya san iya adadin mutanen da kika kai kanki wurinsu? Ohh, tunda kike nuna rashin tsoro a duk abunda nake yunkurin miki wayasan ko kin saba? Waya san ko ke yar hannu ce? Dallah ki fice min a daki, ki koyo kamun kai, ki zama mai Aji da har ni zan kawo kaina wurinki ba ke ki kawo kanki wurina ba kingane?}•.


Duk da Hausan da yake yi ya girme ma hausanta tayi amanna wannan ba abun Alheri ya fada ba, ba ta san me yake nufi ba, amma ita ta san zata koyi kamun kai kamar yanda ya bukata, zata yi Aji, za kuma ta daina kai kanta gun shi har sai ya kawo kanshi gunta, zata bi kalamun Aisha, sai dai Sonshi ya kasheta in yana kisa, amma zata sai ma Kanta mutunci.
***


Yau tun k’arfe 3 yake Gida don dazun da safe tace mishi 4 zata dawo, har 4 ta wuce, yana zaune bai ga Gitta wanta ba, har 5 yayi ta lek’e ya ga ta ina zata fito, shiru ba alamunta, ba Wayarta kuma, sai 6 saura ya ga ta fito daga Dakinta amma ko kallon Bangon Gidansu ba tayi ba, mamaki ya kashe Dan Makaho, hakan na nufin ta dawo Gida Kafin 4, amma bata nemeshi ba kamar yanda ta saba.


Ya dai share, ya fita, bayan maghrib yayi ta tsumayin wayarta, ba shi ba alamunshi, ya damu, meyasa yau bata nemeshi ba tun safe, ko bata da credit ne a waya? To meyasa bata zo gunshi ba, ko bata samu dama ba? Da tunaninta ya kwanta tare da k’agara safiyya tayi don ya san dole tazo ganinshi kafin ta tafi School.


Ita Ko Labiba tunda Uwata ta haifeta, ba ta taba kasa bacci ba irin daren ranar, zuciyarta har wani zugin zafi takeyi, Alwalarta na nan, kawai ta hau Sallaya ta fara Sallah don ta samu sauk’i.


Washegari da safe ta tashi ta yi ma yara wanka ta basu breakfast ta fita ba tare da ganin Zaid ba, karo na farko tun bayan rushewan bango, duk jinta takeyi wani iri.


Shi koyana zaman jiranta har 10 don zuwa ta gaya mishi zata tafi makaranta, amma shiru fa,har 11, wayarshi ya duba ya ga ba kira balle nessage, mamaki ya kasheshi, tashi yayi da sauri ya fita ganin 12 saura. Bencin Eskaley ya nufa, Eskaley kaga wucewar Yarinyar nan? Eskalay da neman magana yace “wace yarinya kenan?” Mur danMakaho ya sha yace “Beebs mana” Eskaley yace “yo ai ina bude shago naga wucewarta tun wurin 8 da minti 40”.


Hannu ya sa cikin sumar kanshi, tunanin goma da ishirin a kwanyarshi, da kyar ya koma Gida, don jiran dawowarta, still be ga dawowanta ba ba kuma kira, damuwa ya shiga fiye da zato ganin har suka kwana suka tashi Labiba ba ta kirashi ba, ba ta kuma nemeshi ba, hankalinshi ya tashi, to ko wani abu ya mata? Ko ta ji haushin maganganun da yake mata ne? Amma yaushe rabon da ya mata wata magana? Ai ko bayan nan tazo dakin ya fi so nawa, kuma shekaran jiya sun dade suna waya, me ya faru ne?.


Haka suka cigaba da Wasan Buya, har sai a kwana na ukun wanda shine Jumuat, ya fito ya zauna kan dakalin da suke waya tun bayan Sallahr Asuba yake zaune a wurin, yau sai ya ga fitar ta, a gaban idonshi ta ma Yara Shirin Makaranta, a gabn idonshi ta shiga da kalacinsu kasnacewar Kitchen da toilet duk a tsakar gida suke, yana zaune Yaya Muhammad ya fito rike da hannun yaran bayan Aunty aasiy ta rakosu suka fita.


A gaban idonshi Labiba ta fito daga dakinta sanye da Zani da Hijab da kwandon Wanka ta shiga Toilet, mamaki yake yanda ko ta gefen ido be ga ta kalla Bangon Gidansu ba, harkarta kawai takeyi, bata damu da ta kalli gefenshi ba balle ta san akwai hallitta a gurin. Nan Damuwa ya baiyyana fuskan Zaid, wanda yanzu ya tabbatar something is wrong somewhere.?”


Ya na ganin ta fito ta lek’a dakin Aunty Asee ta mata sallama yayi saurin tashi shima ya fita daga Gidansu sauri sauri gudu gudu don ya cin mata, tafiya take yi kawai, shi ko ya bi bayanta, ta ji kamar ana binta, ta juyo ta mishi kallo daya ta watsar, daidai nan zuwan wani mai Keke Napep, ta hau ba tare da tace ma mai KekeNapep din fga inda zata.


Turus Zaid yayi, menene hakan? Bata ganeshi bane? Ita ta gani ta watsar? Gabanshi ya dinga faduwa, zuwa yayi shagon Eskaley ya karbi World ya hau zuk’a sai da ya ji shi tatul. Gida yaje ya hau bacci bai tashi ba sai karfe 4 na rana, fatanshi ya ga missed call dinta amma babu, gabanshi ya tsananta faduwa, karo na farko a rayuwarshi ya samu kanshi da kiranta a waya amma sai dai me wayar har ta gama ringing baa dauka ba, ya na da tabbacin ta dawo saboda yau jummuaa, sake kira yayi no answer, kamar zaucacce ya cigaba da kiran layin baa dauka 27 missed calls ya mata, daga baya sai jin wayar yayi a kashe.


Sosai ya ga tashin hankali, messages ya tura mata yana son sanin me ke faruwa? Da me yasa ta bar nemanshi, meyasa ta bar kiranshi amma ba reply.


Haka yayi kwanan bakinciki da tararabi.
Weekends ya shigo DanMakaho ya fige ya kajame, kofar dakinshi ya zama wurin zamanshi, Aunty Asiyah ta sha ganinshi zaune a wurin sai dai ta murmusa mai daga inda take, amma bata son zamanshi wurin yana kalle musu gida, ya zamana dai kullum cikin Hijab take, su Sabit kuwa sai da ya musu alamu da suzo suka tsallaka, ya rike su yana musu hannunka mai sanda yana ina Mama? Amira tace tana Dakinta, Ina Baba? Sukace yana Kasuwa, ya danyi jim yace “Ina Bibs?” Sukace wa? Sai da ya sosa kai yace “Labiba” Amira tace “Aunty Labiba? Ta na daki”.


Zaid yace “Ok ku koma Gida” suka tsallaka suka wuce, wato shine bata son gani? Take kulla kanta a daki, yanzu inda take zama ta bari ko? To me yasa ta fara abunda ba zara iya jurewa ba? Wani yace ta shishige mai in ta san zata bari? Uban wa yace ma ta shigo rayuwarshi, danuwarta don ta ga ya damu shiyasa take azabtar dashi ko? To dole yau ya samu mafita, ba zai iya ba wallahi, ya gaji kuma.


Karfe 12:30am na dare ya tabbatar duk sunyi bacci, ba tare da tunani biyu ba ya tsallaka Gidan Mallam Muhammad, ba fargaba ko wani tsoro ya fada dakin Labiba, Dakin na warin mosquito coil, wayar shi ya haska yaga inda zai ganta, be ganta ba, sai Amira da Sabit da ya gani kan Gado, ta na ina? Ya tambayi kanshi yana waigawa ya ganta kanta a k’asa tana Sujjada, idonshi ya murza, ya kunna wutan dakin kasancewa da wuta, Labiba na cikin Sallah tayi zaton Aunty Asee ce, sai ba ta damu ba ta cigaba da sallahnta, don Aunty Asy kan shigo daukar wani abu a wardrobe dinsu.


Ta na Idarwa ta daga kai ta kalleshi, gabanta ya yanke ya fadi, zuciyarta ta karaya, da kyr tayi na maza ta mik’e tsaye ta linke dardumanta ta wuce shi ta kashe Hasken Wutar Lantarki, dama torchlight din wayarshi be mutu ba, dakin da dan haske, ganin ta na niyyar hawa gado ta kwanta, tana so ta gwada mishi cewa bata san da wani hallitta a wurin ba ya sashi kiran sunanta, muryarshi cike da yanayi madu wuyan Fassaruwa.


“Beebs”


Chak ta tsaya ba tara da ta juyo ba illa fasa hawa gadon da tayi.


“Beebs me na miki ne?”


Ba amsa


A tsorace yace “Ko kin dai na So nah neh?”.




#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO


Babi na Sha Biyu1⃣2⃣
(MANCY 🤱🏻)


Daga kai tayi ta kalli Farin Wata da ya haske tsakar Gidan, ta sa hannunta daidai saitin zuciyarta ta karanta: Allahumma La Sahla illa ma ja'altahu Sahla, wa anta taj alal hazna iza shi'ita Sahla.
Saboda wani radadin da taji zuciyarta na yi ba tare da wani dalili ba.


Da kyar ta isa dakin, ta bude k'ofar a hankali ta raba ta shiga, sai dai zama tayi dabas kan Katifar, zuciyarta ba komai ciki sai tunanin DanMakaho.


Muryarshi ya dawo kwakwalwarta inda yake cewa "tausayina kike ji ko Sona kikeyi? In tausayina kike yi, ki bari bana bukatar a ji tausayina, in kuma Sona kikeyi shima ki bari bana buk'atar a so ni".


Kamar yana gabanta tace "ni fa ba tausayinka nakeji ba, kai din ne nake So" ta idasa hawa kan Katifar don yin bacci. Sai dai me? Tunanin Dan Makaho na nan mak'ale a zuciyarta.


"Huh!!!"
Ya fada Cike da mamaki da takaici.
Ta ya tace haka? Ta yaya ta iya fada mishi haka? Wani irin guts ne da ita? Karfe sha biyun dare? Ta yaya ta iya kallonshi har cikin kwayar ido tace mishi tana sonshi? Wace irin Macece? A ina aka taba haka? Haka sukeyi a Kudu? Tambayoyi ya ta ma kanshi.


Daga bisani kuma Ranshi kuma ya soma baci, don me za tace mishi tana Sonshi? Don me zatace dagaske take sonshi? Ko zolayarshi takeyi? Was she mocking him?" Hannu ya sa a cikin tulin sumanshi ya zube kan Gado don yin bacci, sai dai me? Tunanin Labiba da kalamanta ba su bar zuciyarshi ba.
Asuba ta gari
ZaiLab
*****


Alhaji Abu Shamsu na Tuk'i cikin kwarewa da iyawa, a lokaci guda yana taya Mamanshi da kawarta fira, a wani bangaren kuma yana daga kai ya kalli madubi daidai saitin Maryama da ke ta kuka a hankali.
K'awar mamarshi ta juyo tace "Ki bar kuka Maryama, ki gode Allah wallahi da bata nakasa ki ba, kishiya ai bala'i ce, nima haka na sha wahalarsu, aure na 4 duka banji dadi kishiya ba, amma da nayi hakuri, wallahi gashi na ci ribar hakuri".


Hajiya tace "kiyi hakuri, na san tunanin yaranki ke damunki, inshaAllah ba wata damuwa, kin ba Allah ajiyarsu shi zai kula miki dasu, ki kwantar da hankalinki kije kiyi Iddah ki samu miji kiyi aure.


Mancy dai murmushi tayi ba tace musu komai ba, suka dinga tafia har suka isa Kano, Unguwar Yayanta ta fada, da kwatance suka isa har Gidan Yayan, an ci saa ya na nan ta shiga Gidan, suna ganinta duk suka tashi, Matarshi ta rik'ota.
Maryama Lafia? Mun ga motar kaya akace daga Gidan Alhaji Zaki, shin Lafiya?" Wani kuka ta fashe da shi wanda ya tada hankalin Yayanta Umar da Matarshi.


"Yaya Baban Zaid ya Sakeni, Saki uku ya min Yaya" a tare suka rafka salati "Maryama me kika mishi?" A gurguje ta basu labari, sosai suka jinjina ma lamarin, ran Yayanta ya baci, har yana ikirarin sai yaje Katsina ya ma abokinshi rashin mutunci.


Hakuri ta hau bashi tana gaya mishi ba yin kanshi bane, sannan ta tuna mutanen da ta bari a waje, da sauri ta mike tace ba ita kadai bane, Yayan ya fita ya isa gurinsu Alhaji Abu Shamsu, Maryama ta shigo da Hajia da kawarta, ta basu ruwa a buta suka kama ruwa sukayi Sallar Laasar.


Alhaji Abu Shamsu ya ba Yaya Umar baki, ya mishi nasiha, Yaya Umar ya ji dadin dattakon Alhaji Abu ya mishi Godia sosai, ya tambayeshi in shi dan Kano ne, Alhaji Abu yace "Abuja yake da Iyalinshi, sun zo bin Jirgine zuwa Abuja don Mamarshi ba zata iya zaman Mota ba daga Katsina har Abuja, sai kuma kawar mamarshi da zasu aje a Rijiyar Zaki, Yaya Umar ya jinjina kafin suka dan yi fira, sukayi musayar number kafin suka musu Sallama.


Bayan tafiansu ne tayi wanka ta yi sallah, ta kulle kanta a Daki ta cizga kukanta son ranta, Yaranta sune damuwanta, wani hali suke ciki? Bata ma son sani, ta fi so ta yarda da cewa suna nan lafiya lau, bata son ta karaya har ta kirasu su ma ta karya masu da zucia don tana da htabbacin in har dai ta kira daya daga cikin Dalo ko Zaid to shakka babu sai sun sa kuka, har ta biye musu ba za a samu mai lallashin wani ba daga cikinsu, nan ne ta dau alkawarin kashe wayarta har sai ta samu natsuwa a cikin ranta.


Bayan Wata 5


Har ta gama Iddah bata nemesu ba, duk da Yayanta yayi ta rokonta kan ta rok'esu amma ta k'i, ko Zaid ya kira ta wayan Yayan yace a ba Mancy kin k'arba takeyi.
Haka ta kasance a Gidan Yaya Umar, ta na k'okarin ganin cewa ba ta zauna cikin damuwa ba, yaran Yayanta na debe mata kewa, har tau bata kunna wayarta ba, yanzu so take ta fara ko da neman aiki ne dama da kwalinta na nursing, dama shi Alhaji Zakin ne yace be yarda da aiki ba shiyasa batayi ba, yanzu ko dole ta nemi aiki don ba za ta zauna haka ba.


Gabaki daya suke zaune a Parlon cikin Gida, wayar Yaya Umar yayi Ringing, cirowa yayi daga Aljihunshi ya ga mai kiran.
Alhaji Abu Shamsu ne.


Bayan sun gaisa ne yake sanar mishi da cewa ai yana kofar Gidanshi.
Zumbur Ya Umar yayi "Ah aha, ka ja zance da yawa, ga ni nan fitowa". Ya kallesu yace "Bak'o mukayi, Alhaji Abu Shamsu ne".
Mancy da Matar Yayanta suka kalli juna suna neman karin bayani, amma yayi gaba don shigo dashi.


Parlornshi ya kaishi, suka gaisa sosai sukayi firan bayan rabuwa. Yaya Umar ya tambayeshi yaya Mahaifiyarshi? Ya sanar dashi cewa ai har ta gama hutun a Abuja tana Katsina, yanzu ma daga Katsinan yake yaje gunta.
Yaya Umar yace "Allah sarki, Allah ya ja kwana". Alhaji Abu ya amsa da Ameen.


Shiru suka danyi kafin Alhaji Abu yace "Alhaji Umar ina Maryama?" Da murmushi yace "aff kaga na shafa'a ban kirasu kun gaisa ba".
Yace "bakomai, dakata dai kaji Alhaji Umar, tun tuni na so zuwa Gidan nan amma na dakata saboda Maryama na cikin Iddarta, na yanke hukuncin zuwa bayan Iddarta shiyasa na zo yau, hak'ikanin gaskia tun randa muka dawo da Maryama take cikin tunanina, na tausaya mata, kuma ina son Aurenta in har zata amince dani".


Yaya Umar da murna yace "me zai hana in har Maryama ta amince da kai, barin turo maka ita dai ku tautauna in har ta amince sai ayi wallahi" Alhaji Abu Shansu yaji dadin hakan ya gyara zamanshi shi kuma ya shiga ciki.


Maryama dauki ruwa kikai parlo, akwai bak'o na nan na jiranki. Da mamaki ta kalli Yayanta tace "Yaya Bak'o kuma? Daga Ina?". Murmushi yayi yace "Yi Maza

Please Login or Register in order to submit comment