Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fasassun Blocks ya tsallakesu, ya haska mata itama ta tsallake. Har tsakar Gidansu Labiba ya shiga.


Da taimakon Hasken Farin Wata suke kallon juna cikin Ido.
"So na kikeyi? Ko tausayina kikeyi?" Ya tambayeta kwayar idonshi kan nata.


"In tausayina kike ji, nagode, ki bari, ni bana bukatar tausayin kowa"
"In kuma sona kikeyi, shima ki bari, bana bukatar a So ni".


So biyu ta kyafta idanuwanta kafin ta tsaidasu a kanshi tace Dagaske Sonka Nikeyi.


Bata ganewa ya fada a ranshi, ya juya ya barta a tsaye, tafiyanshi yayi, ya sake tsallaka Fassassun blocks ya shige Gidansu, kan idonta ya bude kofar dakinshi ya shiga ya maida ya rufe.


Zubewa tayi a kan guiwowinta biyu a k'asa a hankali ta furta YA RABB.....


INTERMISSION.


Vote and comment line by line please..


#1love
#DM
#anatare
#SonSoFWA
#staytuned
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


Babi na Sha Uku
(SO❤)


Runtse ido tayi ba tare da ta ga mai yake shirin yi ba, ta tsorata matuk'a da yanayinshi, Idonta a runtse bakinta kawai ke motsi, girgiza kai yayi ya ciro Jallabiyarshi ta Gado ya zura, chan gefen Gado ya zauna yana shafa Mai.


Jikinta rawa kawai yake daga inda yake yaji adduar da takeyi "Allah ka tsareni da tsarewarka, Allah ka kubutar dani, Allah ka yafe mishi na san ba halinshi bane".


Wani murmushi ya subuce mishi mai kama da na takaici, ita ko ganin shirun yayi yawa ya sa ta dan bude ido, ba ta ganshi ba, ware idonta tayi ta duba gefe, abun mamaki zaune ta ganshi yana shafa Mai.


Murmushi tayi tare da gyara zamanta, tace "har raina na san ba zaka min komai ba".
Mur ya sha "Me kika zo yi?" Da murmushi a fuskarta tace "nazo ganinka ne" a tak'aice yace "Fita" tashi tayi ko a jikinta tace "to bari naje, dama ba dadewa zanyi ba, na ganka ai".


Kallon Mamaki ya bita da shi, wai ta yaya take a haka? Wulakanci ya mata fa, amma Dubeta ko a jikinta, tsakaninta da Allah babu abunda ya dameta.
Tashi yayi ya sha gabanta yace "Okay kina ji ba, duk randa kika sake zuwa min daki, sai na tari Yayanki na gaya mishi kullum sai kinzo min daki".
Kamar doll baby, haka ta kyafta idanuwanta tace "ashe kenan kullum zaka tare shi ka gaya mishi, don ni ba zan bar zuwa ganinka ba, sosai nake sonka Yayana".


Cike da takaici yace "Huh!! Wai ke bakya jin nauyin ce ma mutum kina sonshi? Ko haka kuke a Kudu? Ashe haka Matan kudu suke? Kenan a Kudu, Mata ba su da Aji? Mata ke tallan kansu? To ki saurareni da kyau, in wannan haukan da kikeyi ne kike kira da So, ki sani ni ba zan taba son Mace Mara Aji ba, ba zanso ballagaza irinki ba mai tallan kanta, Macen da zan so ko nan gaba zata kasance mai Aji, mai kunya".


Sake kyafta idonta tayi tace "Ka So ni donAllah".


Da takaici yace "Are you not listening? Maganar da na gama miki kenan, ba zan taba sonki ba, don baki da aji, bana son classless person, kina zuwa dakin Namiji, wa ya san ko dama haka kike? Wa ya san iya adadin mutanen da kika kai kanki wurinsu? Ohh, tunda kike nuna rashin tsoro a duk abunda nake yunkurin miki wayasan ko kin saba? Waya san ko ke yar hannu ce? Dallah ki fice min a daki, ki koyo kamun kai, ki zama mai Aji da har ni zan kawo kaina wurinki ba ke ki kawo kanki wurina ba kingane?".


Har ga Allah bata ma jinsa, hankalinta na gun yanayinsa, komai nashi abun burgewa ne, yanayinshi, yanayin maganarsa, yanayin fushinsa, ba abunda ya fi burgeta kamar yanda yake sa hannun damanshi yana murzan idon Hagunshi.


Murmushi cike da fuskarta tace "Har raina nake Sonka".


Takaici kamar ya kasheshi ya sa hannu ya tura mata kafadunta duka biyu yace "Dallah Mallama ki fitan min a daki" ya mata koran wulakanci, ita ko, ko a jikinta tayi murmushi ta wuce gida sadaf sadaf.


WasheGari ta sake fakar Idanun Aunty Asiya ta fada dakinshi, ba ya nan, bata ji dadi ba ko kadan, ta so ganinshi, da tunaninshi ta kwana jiya ta kuma tashi dashi jiya.
Da kallo ta bi dakin a hargitse, katifa ba gyara, duk lungu da sak'on dakin akwai karan sigarin da aka sha, ta bude toilet ta ga shima datti, ba ta son k'azanta.


Hijab dinta ta aje gefe ta hau gyaran dakin. Ta waiga ta waiga bata ga tsintsiyar shara ba, ta fita da sauri ta fada gidansu, kasancewar bango ya rushe ya sa suka daina zaman tsakar gida.
Labiba ta dauko tsintsiya da abun kwashen shara, da ledar Aerial, ta koma dakin, share dakin tayi tas, in har aka auna bolan dakin Mankas sai tayi tiya uku, kuma ba wani datti ke ciki ba illa ragowan sigari da kwali kwali, bak'ar leda ta samu ta juyesu tas ciki.


Toilet ta shiga ta wanke tas, ta bude Wardrobe din, Ghana Must Go ne, hannu ta sa ta bude zip din ta ga atamfa da laces sai shadda da yards na maza.
A ranta tace "ji kayayyakin da ba a dinka ba" a fili kuma ace "toh meyasa be dinkawa?" Wani tunani ya zo mata, ta tuna ya ce mata Babansu ya hanasu karban kayan Mancy, in ma ya gani k'onawa zaiyi, "Allah sarki, ba halin dinka kayan da Mancy ta turo muku, abun tausayi".
Kwashe su tsintsiyar tayi ta koma Gidansu.


BENCIN ESKALEY


Su 3 ke zaune a Bencin sai Eskaley da ke cikin shagonshi. Safiya ce amma ko wannensu na banka ma cikinshi hayak'i, ba su da wata damuwa, sigari kawai suke zuk'a.
Mankas daga gefe yake zuk'ar tabarshi, ganin Mota yayi ta ajiyeta a inda ta saba ajiyeta ya kalli su Tero yace "ga Jarabarban chan tazo". Baki daya suka bi gun da kallo. Mikewa Master yayi yace "wallahi warewa zanyi kafin ta iso"
Ya tashi yana niyyan guduwa yaji ta na cewa "Master gaban Babarka zan bika na lakada maka na jaki".


Chak ya tsaya tare da juyowa yana yak'en dole "Na matsu, Zan dan zagaya ne" mur ta sha tace "zagayawan uwarka, ban sigarin" kallonta ya tsayi yana kallon sigarin da yanzu ya kunnata, zaiyi asarar naira gomarshi da ita kadai ta rage mishi a dunia ya siya sigarin, muryarta yaji "za ka bani ko kuwa?" Tsaki yayi ya mik'a mata karar. Kafa ta sa ta murje shi tas, kafin ta matsa gun Haruna ta kwace nashi ta yar a kwata.


Na karshen Mankas ya zuk'a ya busa hayak'in, cikin fada yace "ka zuk'i uwarka, kuma ita ka busa ma hayak'i a fuska ba ni ba". Murmushi yayi ya tashi tsaye tare da furta sunanta "NeNe".
Iya k'arfinta ta sakar mishi Rank'washi a kai tace "Allah ya shiryeka Zaidu, nidai Wallahi—-" shiru tayi don Master, Haruna da Eskaley suka hada baki wurin k'arasa mata maganar da ta yi niyyanyi na "Zaidu Bawan Allah ba haka yake ba" kallo ta bi su dashi, so milliyan in zata ce haka, to so milliyan zasu karasa mata saboda maganar kenan "Zaidu bawan Allah" ba haka yake ba, kullum indai har ta zo to inshaAllahubsai ta fadi haka.


Mur ta sha tace "Uwarku kuke kwaikwaiya bani ba".
Gum sukayi suka ja bakinsu sukayi shiru, zama tayi kan bencin cike da isa don haka suke kullun.
Eskaley ne ya fara gaidata kafin sauran suka gaisheta har Mankas din, ta amsa tare da kallon Zaid tace "kai dai baka ji ko? Ka cigaba, kar ka fasa wannan bushe-bushen, kai ko kunya bakaji? Bakinka yayi bak'i dubeka donAllah".


Kai Zaid ya shafa yace "InshaAllah Zan bari Nene, ki tayani da addua, kai arr makaryaci, kullum haka kake cewa kuma baka bari, wallahi Zaid ka fita idona, randa zan tona maka Asiri wurin uwarka zaka sha mamakina, ka san dai ban tsoronka ko?".


Da sauri ya rude ya fara rantse ranste "wallahi Nenenmu na bari, ban k'arawa, dagaske bazan k'ara ba". Ko a jikinta don ta san k'arya ba yau ya fara shi ba, ta kuma san ba bari zaiyi ba, amam ba zata fasa mishi addua ba, harara ta galla mishi tace "ka je ka dauko Abincin cikin mota ko kuwa?".


Be tsaya tunanin yaushe tace yaje ya dauko abinci ba sai ma nufar motar da yayi da gudu.


Kallo ta bi Haruna, Master da Eskaley tace "Ce muku ku bar Shaye-shaye bata baki ne ko?".
Eskaley yace "Nenenmu zamu bari"
Kamar ta mareshi tace "dallah rufa min baki, ba kai ne dan iskan da ke saida musu ba".
Eskaley ya ja baki yayi gum.
Tsautsayi yasa Haruna cewa "ai daga yau mun bari, ba zaki taba kama mu da shan wani abu ba".


"ka min shiru ko sai na gwala kanka da bango? Kullum haka kuke cewa, banga laifinku ba, tsinuwa ke kanku, ta ya zaku bari uwayenku na tsinanku kullum".
Master zaiyi magana, daidai zuwan Mankas dauke da Basket ya girgiza mai kai alamun yayi shiru.


Ajiyewa yayi gabanta, kamshi ya bade wurin, waina ce da miya da taji naman miya tantakwashi, ta zuzzuba musu a plate kowa.
Cike da jin dadi suke ci.
Hannu ta nade a kirjinta tana binsu da kallon tausayi, ta san yanayi ne ya sasu halin da suke ciki yanzu, ta san takaici da bakinciki ya jefa da yawansu a halin da suke ciki yanzu, har ranta take son su kuma har ranta take tausayinsu.


Barin ma Zaid wanda tafi so da tausayinshi, hawayenta ba kusa suke ba, amma ranar da ta fara ganin Zaid a hali na shaye shaye sai da ta zubar mai da hawaye bayan ta saka an rufeshi a Cell.
A shekarun da suka shude, bayan Alhaji Zaki ya ma Alhaji Habib warning akan zuwa Nene Gidanshi, Zaid ya tafi da Nene Kaduna, Watanta Biyu ta saka daru dole a maidota Katsina. Zaid ya amince zai maidata amma ya bata sharadin ba zata sake zuwa Gidan Alhaji Ali Zaki ba, haka ta amince.


Bayan Zaidu Bawan Allah ya dawo da ita, washegari da safe ta fita, tayi Unguwar Tudun Matawalle kan Keke Napep, daga farkon Anguwan taga samari yan matasa na shaye-shaye, su kuma wadannan ba sa tausayin kansu ne suke shaye-shaye da farar safiya? Nene da shiga sharo ba shanu sai da ta tsaya wai zata musu nasiha.


Saukar daga Napep ke da wuya taga wani mai kama da Zaid na kokarin kai Sigari Biyu lokaci Guda Baki. Da gudu ta k'arasa wurin tana salati. Su 6 ne, dagowa sukayi suna kallonta cike da tsageranci.
DanMakaho ya hau network, be ma ganeta, World ya dan taba kafin yake bi da sigari biyu.


Da karaji tace "takwaran Zaidu bawan Allah, kai ne nan ke shan Sigari? Da kayan Maye?" Banza yayi da ita ya cigaba da suburbudar sigarinshi yana sake hawa network".


A fusace Nene tace "danuwarka ina kaduna Hankalina na gunka, na matsa aka dawo dani don kawai naga halin da kake ciki ashe kana nan ka zama dan duniya, kana cikin yan banza kana shan sigari, don bariki guda biyu kake hadawa lokaci guda kai tak'adari ko?".


Banza yayi ya kyaleta.
Terro yace "kai mankas dallah wacece wannan tazo tana mana haushin kare?" Cike da murya ta yan shaye shaye yace "yo wa ma ya santa? Ke dallah Mallama ware".
Ran Nene yayi mugun baci, bata san lokacin da k'walla ya cike mata ido ba, ranta ya baci ta wuce ta tsaida Keke Napep, ta yi gaba bata tsaya ko ina ba sai a Police Station, cewa tayi ta kawo k'aran Jikanta, shayeshaye suke suna taamali da kayan Maye, so take a rikeshi a ci ubanshi har sai ya tuno ko ita waye".


Mota Guda aka ba Nene, bayan ta shiga ta musu kwatance har gaban Bencin Eskaley, kafin su Mankas su farga, tuni anyi ram dasu, daga inda take take ta faman Mita "ni zaka ce baka sani ba? Officer ku ci man uwarshi donAllah" haka akayi gaba dasu tas aka rufe a cell.


Kwanansu Biyu kafin Nene ta koma, lokacin sun jigata sunyi laasar.
Zaid na ganinta ya mike tsaye "Nene kiyi hakuri donAllah, hankalin dalo na chan a tashe, ba ta san halin da nake ciki ba, kice su sake mu".
Hararshi tayi tace "sakarai, ka san da Dalo ka wofintar da rayuwanka, har kai dan mitsitsi da kai ka san shaye-shaye? To yau sai na gaya ma Dalo ko kai waye, ta daina girmamaka, don kai ba kowa bane face dan shayeshaye, gwara ta ganka a asalinka".


Hankalinshi ya tashi ya hau magiya yana mata alkawarin ba zai k'ara ba.
"Ka gaya musu ko ni wacece?" Da sauri ya gyada kai yace "wallahi na gaya musu, na gaya musu ke kakata ce" ta kallesu tace "to don uwarku sunana Nene, kar ku bar shaye-shayen, in na sake zuwa na ga kuna shaye-shaye, sai na sa an k'ara kamaku" da sauri suka fara rantsuwar sun daina basu k'arawa.
Haka ta saka a ka sake su.


Wani zuwan da ta sake yi ne ta iske suba gidan jiya, wato ba su bari ba, ta zagesu tas, ta ranrankwashi Mankas ta juya cikin Motar Gidan Lema.
Ya zamana duk zuwan da zatayi don ganin Zaid a nan Bencin Eskaley ta ke tarardashi, ranar ko ta zauna kan Bencin tace "don uwarku kuzo ku ban labarinku duka, ta yaya kuka fara shaye-shaye?"
Da Haruna ta fara, sai Terro, Master, Eskaley, Gayu, Bororo da Big loma.
Dukkansu sun bata tausayi, kowa da irin labarinshi, wanda kusan dukkansu suna da irin matsalar Zaid. Wato matsalar Matar Uba, yawancinsu Matar Uba ce Silan fara shaye-shayensu, Nene ta tausaya musu, ta musu nasiha ta nuna musu suma 'ya'yane, Alkawari suka mata sun bar shaye-shaye amma ina Sam. Ba alamun dainawa.


Nene bata kyamarsu, haka take jan su a jiki, ba kullum take zuwa ba, ta kan dade bata zo ba, amma in zata zo, da safe take zuwa kuma zata dafo Abincinta mai rai da lafia, ta zauna cikinsu, su ci ta kwashi kwanoninta ta tafiyarta Gida.
Duk zuwa sai tayi fada dasu amma hakan bai hanata sake zuwa inta samu dama.
Ba wanda bai son Nene a Bencin Eskaley gashi duk sun santa, indai kana zuwa Bencin Eskaley to ka san Nene, in ma yunwa ta koro su sai su zo Bencin Eskaley su zauna suyi ta adduan Allah shi kawo Nene da Abinci.
****


Santi Haruna keyi yace "Wai Nene, Siyo Wainar nan kikayi?" Mur ta sha tace "Uwar ka ke saidawa?" Haruna yace "daga tambaya?" Nene tace "daga amsa? Dan wulakanci tun Asuba nake aikin wainar nan, zaka ce siya nayi, aa ka manta".


Zaid yayi daria yace "Neneeee, mungode kwarai" kar ma ku gode "'yan tananiya, Allah ya shiryaka wallahi, ba haka Zaidu Bawan Allah yake ba" su Haruna suka karasa mata, sun san next statement din suka ce "uwarku kuke kwafa" duk suka kwashe da daria har Nene, wato kun daukeni Kaka, to ni ba kakarku bace ni uwarku da ubanku ce, don duniya baku da me sonku sama dani.


Baki suka hada suna "wallahi gaskia ne, Sai Nene, Allah ya kare mana ke, ya ja kwana, dariya tayi tace "Allah ya shirya ku" haka suka rakata bakin mota suna jiran ta basu wani abu duk da sun san da wuya ta basu".


Tace "kun dai san ko sisi ba zan baku ba ko? Ba zan baku kudina ku k'ona ba. sai Allah ya kuma min dawowa".
Haba Nene ai mun bari, ba ta tsaya amsa su ba ta shige Mota ta rufe, Zaid ya bude dayan wurin ya saka Basket suka daga mata hannu Driver ya ja suka wuce.


Zaid daga nan ya wuce Gida, straight cikin Gida ya nufa, dakin Dalo ya kwankwasa kafin ya shiga da Sallama, gaidashi tayi da Ina kwana Yaya? Da fara'a ya ansata yace "Yanzu Nene ta bar Unguwan nan" fara'ar Dalo ya fadada tace "haba? Shine ba ka kirani mun gaisa ba?".


Murmushi yayi yace "ta na gaidaki, kinsan dai kika fita Baba zai dakeki, rannan da nace ta shigo ku gaisa Baba ma ya manta da ita cewa tayi aa gwara ta tsaya waje, don in ta shigo baba ya mata wani magana bugun tsiya zata mishi, Dalo ta fashe da daria tace "yanzu sai ta bigi baba? Zaid yayi hanyar k'ofa yace "tab ko nima sai da aka rankwasheni yanzu". Daria sukayi ya fita dakin yayi Boysquaters.


Gabanshi ne ya fadi a lokacin da ya daura kafarshi cikin dakin, komai ya chanza, ba haka ya bar dakin ba, wa ya gyara? Da sauri ya fada toilet ba abunda ke tashi sai kamshi Aerial, wa ya gyara mishi daki? Wa ya wanke mishi toilet? Da sauri ya fita don koma wa cikin Gida.


Inda ya bar Dalo chan ya isketa, kallonshintayi da mamaki tace "yadai Yaya?"
Rasa abunda zai ce yayi. "Erhm Dalo, nace ke kika gyara min Daki bayan na fita?".
Sadiya ta girgiza kai tace "aa Yaya, me ya faru?".


Dan jim yayi yana dan tunani kafin yace "no karki damu" tare da fita.
Dakin ya koma yana tunani mai tsawo, wacece a gyara mai daki? Ko Yesmin ce don ita kadai ce ke mishi wannan karambanin, amma a iya saninshi Yesmin bata zo Gidan ba tun last 4months, waye zai mai haka? Who could have possibly done this?".


Idonshi ya kai ga Gidan Mallam Muhammad, da sauri ya girgiza kai yana fadin "Kai No, Aa gaskia, ba ma ita bace, ta ya ma zaayi in yi zargin itace? ba ita bace. Ba ya son yarda, ya tabbata ta zuciyya ga koran wulakanci da yayi mata jiya, ba ya tunanin zata taba dawowa har ma da farar safiya har ta mishi gyara haka,


Hannu ya sa yana murza idonshi.
Muryarta yaji tana cewa "Ya Zaid, har ka dawo?" Firgigita yayi kafin ya tsura mata ido yana mamakinta.


Fuska a daure yace "Ke ce kika shigo min daki?" Karasowa tayi ciki da fara'arta tace "eh wallahi, nazo ba ka nan, shine naga dakin yayi kacha kacha, shine na dan share" mur ya sha yace "wa ya saka ki?" Murmushi kan fuskarta ta dan kalleshi, nace "wa ya sa kaki sharan? Ni na sakaki gyaran daki? Don me zaki gyara min daki? Ni Mijinki ne? Kar ki sake shigo min daki, ke wai wata irin Mara Aji ce? Bayan tallar kanki da kikayi, har bauta kike yi ma samari? Lallai kam Ajinki ya zube, ko da yake ba Ajin balle ya zube".


Hannu ta sa a baki ta mishi alama da yayi shiru "shhh, menene abun tada jijiyoyin wuya? A kan me kake ihu? Saboda na maka shara? To kwantar da hankalinka Masoyi, ba zan kara ba, zan nema izinin ka kafin na maka shishigi, kai ba Mijina bane amma ina fatan wata rana zaka kasance Miji a gareni, lokacin zan share ko ina ba tare da na nema izininka ba".


Zaid yayi shiru don ta gama kasheshi da Mamaki, bata zuciya bata fushi, me zaiyi da zai sa ta rabu dashi ne? Tsaki yayi ya sa hannu a aljihun doguwar jallabiyarshi bak'a dake Hange, sigari ya dauko ya cinna mata wuta. Labiba bata ida bashi mamaki ba sai da ta tako kusa dashi ta zare Sigarin hannunshi ta girgiza mai kai.


"Ka ga dai ina da Athma, bana son hayak'i in na tafi sai ka sha abunka kaji Masoyi?" Kamar yayi ihu don haushi da takaici, wai me zai ma yarinyar nan ta rabu dashi ne? Ko Yayanta din zai samu ya gaya mishi yanda take bibiyarshi kila shi ya tsawatar mata, amma Aa ba zaiyi haka ba, ya san tarihin Gidansu, ya san dalilin da ya sa aka barta zuwa karatu Katsina, ba zai so zama silar batawar da Wanta ko Mahaifanta ba".


Guiwowinshi ya sa a k'asa tare sa hade hanayyenshi duk biyu yace "DonAllah Biebs, don Girman Allah, kar ki k'ara zuwa min daki, na hadaki da Allah, ina jiye miki abunda zai faru a duk ranar da aka ganki a dakina, wai ba kya tunanin wata rana a ganki a nan? Wallahi people will have other impression, ki cece mu duka".


Murmushi be kauce ma Fuskarta ba tace "wai ni ka durk'usa a gabana? Don na bar zuwan maka daki? Nima barin durk'usa mu dawo daidai, hakan tayi yanda yayi.


"tsaya kaji maganar Gaskia, wallahi Billahi har raina nake son ka, ina matuk'ar son ka, sosai nake sonka, wallahi a cikin zuciyata ina wahala in ban ganka ba, zugi zuciyata ke min in har ban ganka ba, Ban taba jin son wani abu ba a raina kamar yanda nake jin Sonka, zaka ga kamar na matsa maka, amma Wallahi So gaskiya ce, samun mai son ka Abun Alfahari ne, ina Sonka, ka min uzuri, ka min izini na cigaba da Sonka".


Sosai maganganunta suka kashe mishi jiki, zama yayi dirshan a k'asa, tare da lumsa idanunshi, wani irin yanayi yake tsintar kanshi a ciki, a hankali ya bude idonshi ya zuba mata su, sai faman murmushi takeyi yace "ki fa kyaleni, ni bana sonki I have a Girlfriend".


Irin zaman da yayi tayi da murmushi tace "to wa ya ce maka Ina son zama budurwarka? I dont want to be your girlfriend, i want to be your wife, ban damu da wanda suke sonka ba ko kai kake sonsu, abu daya na damu dashi, shine ni ina sonka, kuma zan cigaba da sonka ba tare da amincewarka ba, ka min uzurin wannan".


A duk lokacin da zata bude baki tayi magana, to inshaAllahu sai ta kwance mishi duk wani Noti na jiki, sai ta kashe mai jiki.


"Yaya Sunanta?"
Ya kalleta da mamaki tace "ita budurwar taka"


Ta na ganin tantanin makwalatonshi yayi sama da k'asa kafin yayi magana yace "Yesmin".


Tashi tayi tsaye kan kafafunta ta dauki wayarshi da ke kan Gado tayi dialing numberta, ya ko shiga ta duba numbern, ta ajiye mai wayar inda ta dauke shi duk yana aikin kallonta, ta kalleshi sosai.


"Ba ta kaini Sonka ba" ya dago sosai don kallonta, jinjina mai kai tayi tace "Yesmin bata kama kafata a Son Ka ba, ni ina sonka kuma ba zan daina son ka ba, ka rok'eni kan na bar shigo maka daki? Kayi hakuri ba zan iya ba, na dauka numberka, zan dinga kiranka a duk lokacin da nake buk'atar son jin muryarka, kuma dai ga numberta nan, zabinka ne kayi saving ko kar kayi, ni dai zan dinga kiranka, ka ji dadin ranar yau kaji Masoyi? ina maka Son So Fisabillilahi".


Juyawa tayi ta tafi abunta, ta barshi da mugun mamakinta, tambayar da shi kanshi zai so ya Amsa ma zuciyar yake ma kanshi, ta yaya ta ke haka? Why is she like this? She's too blunt Oh Allah, ita kamar makauniya, wai bata ga shi dan iska bane? Bata ga be chancaci soyayyarta ba? Ko kawai ita ta makance da son shi, shin bata hango ranshin dacewarsu bane? Ita bata san ya kamata bane? Bata san ya kamata tayi nisa da shi as far as she can? Wai harta ta ma fatan aurenshi? Tsaki yayi yace "tana ma hauka".
Sigarin da ta aje ya dauka ya cinna ma wuta ya fara banka ma cikinshi hayak'i.


Yana cikin banka ma cikinshi wuta wayarshi tayi ringing, dauka yayi ya kalli mai kiran, tsaki yayi gami da daura wayar a kunne.


Da muryarta mai dadin sauraro tace "Hello Masoyi?" Lumshe ido yayi ya bude yace "Waye?" Ya na jin sautin murmushinta tace "Sunana Labiba Ahmad, kuma ina Sonka".


Ji yayi kamar yayi ihu, da ta san yanayin da take sashi a duk lokacin da ta furta kalmar So a gareshi da ta rage Fada, ko kuma ta bar fada gabaki daya.


"Ka dan fito wajen dakinka" kamar yana kallonta yace "menene?" Cike da shagwaba tace "donAllah Masoyi ka fito Kofar dakinka, wani abu kawai zaka gani" kamar ba zai tashi ba ya tashi dai ya fita, yana fita ya ganta zaune kan dakalin tsakar gidan Yayanta, murmushi ta mishi tare da kashe mishi ido, bai san sanda ya zauna shima a bakin kofar dakin nashi ba ya na kallonta, taku 30 zai kaishi gareta, itama haka.


"Yauwa Masoyi, ka zauna a nan ina kallonka ina waya da kai". Mur ya sha yace "mai kike so ne?"
Da jin dadi tace "good question, kai nake so".


Tana ganin harararshi daga inda take, tayi dariya tace "komai kyau yake maka" yace "zan kashe wayata fa" " ka kashe amma ka tsaya na cigaba da kallonka". Ido cikin ido suke kallon juna, bai kuma kashe wayar ba, sun dau minti daya a hakan kafin yaji tace "ko

Please Login or Register in order to submit comment