Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin firansu mai dadi ne wayar AbdulMajeed yayi ringing,
Ya kallesu baki daya da murmushi a fuskancshi yace "Daddy Usman ne"
Jawad yace "kace sirikinka ne"
Ya jefeshi da harara.
Mancy tace "kai wani irin Gudu Daddy Usman keyi haka? Har ya isa kenan".
Jin tashin hankali sukayi a muryan Abdulmajeed.
"Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, mai ya sameshi? Yanzu yana ina?".


Kowa na cikin parlorn ya fara tambaya mai ya sami Uncle
Usman.
Kasa magana yayi sai da Abban yace "Kai Abdulmajeed, ka gaya mana mai ya samu Daddyn naku?".
Abdulmajeed kamar yayi kuka yace "Abba hadari Daddy Usman yayi a Charanci, ya bige wani mutjmi har mutumin ya mutu amma shi Daddyn yana Asibiti ba abunda ya sameshi sai dai wai ya bugu a kai".


Tunda ya fara magana suke Salallami da Salati.
Abba cike da kidima ya ciro wayarshi ya kira chan Katsina gidan Iyayenshi ya sanar dasu, da su je Charanchi yanzu yana nan tahowa gobe InshaAllah.
Ya Kalli Iyalanshi da sukayi saye cirko cirko yace musu "ku shirya, gobe inshaAllah zamuje Katsina".
Amsa mishi sukayi duk jikinsu a sanyayye


K A T S I N A


Ai yayewa akayi a Unguwar Alkali harta Hajiarsu Alhajin suka kwasa suka nufa Charanci har su Aishan.
Kafin su je an gano Gidansu Mamacin, suka shiga akayi magana, Allah ya sa Saurayi ne, baida Iyali, Mahaifiyarshi kam taci kuka sosai amma ta yafe Wanda ya bamkeshi yayi kaffara, aka rufo mamacin.
Basu kwana a Charanci ba suka wuto Katsina.
Asibiti zaayi dashi yace shi dai donAllah a kaishi Gidanshi don ya tsorata sosai da abunda ya faru.
Tunda suka dawo Gida ake zuwa yi musu jaje ko wani lungu da sak'o, gidanshi ma bude ya kwana saboda masu shiga da fita, wasu sun kasa hakura safiya tayi su zo, abunku da 'yan dangi.
*


'Yan Abuja tun safe wurin 8 suka fito, Mota biyu sukayi, AbdulMajeed ke jan Abba da Matanshi Umma da Mancy, sai Abdulhafiz ke jan Matarshi Ummita da Jawad da Mimi, a tare suke taafiya ba'a gudu da Abba, shiyasa suke dadewa akan hanya, sai da suka tsaya a Zaria suka ci Abinci a Shagalinku kafin suka sake daukan hanya.


Sun iso Charanci wurin Karfe2, tambaya sukayi gidan da aka banke wani Jiya, har kofar Gidan aka kaisu, suka shiga, sai kallonsu ake tayi aka dai gaigaisa.
Abba yace "ina Mahaifan yaro?"
Aka gwada musu Uwarshi.
Yace "Uba fa?"
Akace ya dade da rasuwa.
Abba ya gabatar da kanshi a matsayin Yayan wanda ya banke mata da, ya roke su gafara, mahaifiyar yaro tace "wallahi Alhaji, lokacin Saminu ne yayi, K'anenka ne sila, amma lokaci yayi ba wata dabara da zai tsaida tafia".
Matar ta burgesu, nan aka musu karamci aka kawo musu ruwa fiya wota (pure water) da damammen fura.
Ba wanda bai sha furan nan ba sai mimi da bata shan fura, suka sha suka sake musu gaisuwan mutuwa kafin Abba ya cika Mahaifiyar yaro da Alheri.
Godia ta hau yi ta na kuka tace "Saminu ya tafi, amma sanadiyar shi sai samun Alheri nakeyi, Dazun ma Maidakin Mutumin tazo da tawagarta, wallah sun cika mu da abun Alheri, mungode mungode, Allah ya ji kanka Saminu".
Da kyar suka bata baki ta bar kuka, suka musu rakiya har bakin Mota kafin suka dau Hanyar Katsina kuma.


A Garin Katsina.


Zaune ta isketa a babban Parlo tana kallon dadin Kowa sabon Salo na karfe 3.
"Nene Jaje zanje Unguwan Alk'ali kafin yara su dawo Islamiya" Nene da ke tamnar cingam tace "Jaje na me? Me ya auku?".
Hajia Aisha tace "wallahi Mijin k'awata ne yayi hadari, yayi banka a hanyar charanci, har wanda ya banke ya Rasu".
Nene tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Allah sarki, kije dani nima nayi musu jajen".
Hajia Aisha Lema tace "Eh sai muje Nene, abun ba dadi wallahi ".
***


Welcome to Katsina ta gani a tollgate, gabanta ya yanke ya fadi, Katsina...bayan ta auri Babansu Jawad tazo katsina so uku zuwa hudu, bata san meyasa wannan karan ta ji faduwar gaba ba, jikinta ya soma rawa, haka kurum ta ke jin faduwar gaba a zuciyarta, Zaid, Sadiya, ya kamata ta gansu, amma ina bata shirya ganinsu ba, ba yanzu ba, shiyasa kamar zuwanta na baya har taje ta dawo bama zasu san ta zo ba.
Straight Gidan Daddy Usman suka nufa.
Aisha ta rugo da gudu ta rungume Umma kafin ta rungumi Mancy.
Ta gaida Abba da yayyinta ba tare da ta kalli AbdulMajeed ba.
Suka karasa har Parlon Daddy Usman, Parlorn cike yake da mutane, aka gaigaisa aka ma Juna Jaje, Alhamdulilah jikin da sauki sai ciwon kai, akayi wa juna barka ba abunda ya samu Daddy Usman, Antisco tace "Abinci na Parlo na, ku muje kuci kun kwaso hanya".
Abba yace "ai mun tsaya Charanci gaisuwa sun bamu fura munsha".
Antisco tace "ai abun bai yi dadi ba, nima dazun da safe mukaje muka sake musu gaisuwa, duk da lokacinshi ne yayi harda sila dai".


Suka sake jajantawa juna kafin suka dunguma baki daya Parlon Antisco, Mancy ta shiga toilet din Parlorn.
Sai Ga Hajia Aisha da Hajia Nene sun shigo Parlon Antisco, Antisco ta musu maraba, suka tarbi juna suka zauna don yi ma juna Jaje da Barka, Alhaji Abu Shamsu ya gaida Nene ta mishi Jaje, Suka gagaisa duka harda Umman su Jawad, Antisco ta rakasu chan Parlon Daddy suka mishi Allah kyauta, suka koma Parlornta don parlon Daddy cike yake da 'yan anguwan alkali.
Jawad da yayyinshi suka zuba Abinci suka fita waje wai Mota zasu.


Fitowar Mancy daga Toilet ta hada ido da Nene, tare suka zare ido suna mamakin ganin junansu, Mancy tace "Nene?".
Nene ko ta buga muguwar tsaki ta tashi ta fita daga Parlorn. Duk suka bi tsohuwar da ido Umma na ma Alhaju Abu magana da ido ya mata alamun baisan ko wacece ba.
Mancy da Hajia Aisha Lema suka bi bayan Nene.


Nene na daga kofar parlo a hakimce tana jiran Mamyn Rafeeq ta fito su wuce amma a zuciarta mamakin chanzawan Mancy take, da alamu duk inda take tana jin dadin Aurenta.
"Hajia Aisha Ina wuni? Ya yara? Ya wurin su Rafeeq da matarshi?" Mami ta amsa mata da fara'a, "lafiya lau Hajia Maryam ya bayan rabuwa?" Mancy tace "Alhamdulilahi".
Kallon Gogiyar tayi, gogarku sai tamnar cingam ake kachalkachal ana kallon gefe irin bata san akwai mutum a gurin ba.
Murmushi Mancy tayi tace "Haba Hajia Neneta" Nene bata amsata ba, tace "Hajajju Nene mutanen Makka, Allah ya sake hadani dake a Makka na goyaki bayana" yanzun ma ko kallonta bata yi ba, hannu Mancy ta sa ta na taba cinyar Nene ta na kiran sunanta.


"Nene, Nene, Nene, haba Nene" Nene ta mik'e cike da masifa tace "haba Mallama, ya zaki ta sani gaba kina min Noiiiiise? Is Stupid? Ke tsaya ma is no me ne? Nace is no me?".


Mancy ta murmusa tare da rik'o hannayenta biyu tace "I know you very well Nene" hannu Nene ta fizge ta bugar ma Mancy baki tace "Ni kike ma turanci? Dan iskancin kin sa k'afa kin bar Katsina, ba waya ba komai, kika maidani wata mara amfani ashe yanda na daukeki ba haka kika daukeni ba, kin take duk wani abunda ke tsakaninmu da k'afa, bayan shekara kusan 4 kinzo kina cika min kunne da surutu, har da karfin halin turanci, Allah ya tsine miki kika sake furta man kalmar turanci".


Mamin Rafeeq tace "kiyi hakuri Nene, kina daga Murya, kar 'yan Parlo suji" Nene ta sake bude murya tace "Su ji, nace Su Ji, ai gwara su ji".


Mancy ta murmusa ta sake rik'o hannun Nenen tace "kiyi hakuri donAllah, ban kyauta ba, nasani ni mai laifi ce wallahi, Nene banda zabi ne, abubuwa sun fara da sauri ne, wallahi a lokacin ban san me nayi ba, kuma ni wallah kunya ma nikeji, ki yi man hakuri donAllah, fushinki na sosa min rai donAllah Nene".


Nene ta dan sha mur tace "kinsan na gaji Yafiya wurin Mahaifina, na yafe miki, amma banji dadi yanda kika watsar dani ba, kika nuna ma duniya baki da gata a Katsina, ni yanda aka ci maki mutunci a garin Katsina da kin gaya man sai na sai miki mutunci kuma in ci uban mutum ko uban wa ya tsayar mai daga nan har gaban ko wani dan shegia amma kika tsallakeni, ke kika sani".


Mancy tayi ta kallon Nene da mamaki, ta san Nene bata da hakuri bata da ragowa amma yanzu ta ga Nene ta koma kamar wata 'yar Tasha.
Nene tace "yana ga kina kallona? Ko zagin uwata zakiyi?".
Mancy ta hau Girgiza kai tace "Nene ki rufa min Asiri, wai ba ma kince kin hakura ba?".
Murmushi tayi tace "oyoyo Maryama, nayi missing dinki".
Mancy tace "Hajia Aisha kinga Nene ko? Turanci tamin, nikuma in na mata a zageni".
Mamyn Rafeeq tace "ina ji dazu har tsine miki akayi".
Daria sukayi tare.


Nene tace "sai aje a ga su takwaran Zaidu bawan Allah ko?".
Mancy ta dan rage annashuwa tace "Aa Nene".
Nene ta sha mur nan da nan tace "bangane Aa ba? Ba zakije ki ga yaranki ba? Ke wai wace irin stupid ce? Me ke damunki? Baki da zucia? Wace irin uwa ce ke? Wallahi ki guji haduwarki da Ubangijinki, Allah yace dukkanku Makiyayya ne, kuma sai Allah ya tambayeki yanda kikayi da naki Kiwon, ya kikayi da kiwonsu? Daya ya zama dealan Wall kobo biyar ba zaki saye shi ba, ta macen Allah ya tsare miki ita, wallahi jiya naji a radio wata ta kashe kanta saboda bakinciki, ke kiyi hankali, ke kin ma ci uwarki in kikaje ganinsu, ke Aisha wuce mu tafi".


Alhaji Abu Shamsu da Matarshi suka fito bakin Parlon da alama sun gama jin duk wani abunda suke tattaunawa.
Mancy tuni ta sha jinin jikinta
Alhaji Abu Shamsu yace "wallahi Mama, tun kafin na auri Hajia Maryama na nuna mata ina son rikon yayanta amma ta hanani, ta nuna min gwara ta barsu Gidan ubansu, na ce mata ko zata bar Namijin ta dauko Macen don Tarbiyar diya mace in ba Uwa to akwai Matsala".


Nene tace " kai k'yale sakarar, ai maryama da kake ganinta muguwar sakara ce"


Umman Jawad tace "ke ko Maryama har yau baki huce ba? Ai ba zaka dauki laifin uba ka shafa ma yaranka ba, wake fushi da 'ya'yan cikinshi, ke ko kije ki gansu ko so daya ne".


Nene tace "sai wani aiken da take musu duk wata na banza, ce miki sukayi suna Son abun hannunki? Sunfi bukatar ki, yaro na nan ya zabge ya tsure, a lokaci guda sai ya shanye kwalin sigari daya,ga tabar wiwi yana zukarta kamar ba gobe har wani suna yan jagaliya ke ce mishi wai Mankasss".


Mancy cike da kidima tace "ba dai Zaid ba".


"Aa Ubana" Nene ta fada cike da fada.
Mamyn Rafeeq tace "haba Nene kiyi shiru".
Ita ko Nene kira take "ban yin shiru, laifin wa? Wallahi lafinki ne, da kyar in baida ciwon k'ofa dan wallahi fari yke fayau, in ya mutu Kurani ke kika kashe danki".


Tuni Mancy kafa ya fara rawa, fitsari ya cika marar ta taf kamar ba yanzu tayi fitsari ba.


"Alhaji, donAllah ka min izinin zuwa ganinsu, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, na shiga uku na, Zaidda shaye shaye?"
Alhaji Abu yace "Maryama kinsan dai tun yaushe nake binki muje ki gansu ko? Kin san ba zan hana ba, ko yanzu kika ce su dawo Gidana ina maraba dasu".


Ba ta tsaya jinshi ba ta shiga ciki ta dauko gyalenta tace da Mimi je ki wurin Yaya Aisha, yarinya ta mak'e kafada, Mancy bata da lokacin yi gardama ta fito a hargitse.


Alhaji Abu yace "nima zanje" Umma tace "itama zata" haka Mancy ta shiga Motar Hajia Aisha Lema, su Alhaji Abu suna biye da motarsu a baya.
Dama Abdulmajeed ya zagaya zance wurin Aisha, Abdulhafiz ya gaji yace zai dan kwanta so ba tare da sanin inda zasu ba Jawad yace bari ya kaisu, Abba yace ka bi bayan motar nan yabi Umurni yana tuk'i.
"Abba ina zamu?"
Abba yace "just drive".
Bin bayan motar Mamyn Rafeeq yake, har ya ga Anguwar su Sanyin idaniyanshi ne, da niyyar in ya saukesu zaije ya ga Babynshi dama Allah Allah yake neman chance ya fito wayarta tun jiya kashe, duk ya damu.


Sun zo Daidai Bencin Eskaley Nene tace "dan tsaya nan, kinga Bencin chan, chan suke zaman kashe wando, barin lek'a inga Zaid din na nan, ta lek'a tace "Kai Takwaran Zaidu bawan Allah na nan?"
Master ya fara ganinta yace "Sai Nene".
Aiko hankalinsu tero yayo kan Motoci Biyun nan.
"Nene da me kika zo mana yau?" "da uwarku" nazo ta koma tace "baya nan, yana gida Muje Aisha" ita kam Mancy kallo daya ta ma Bencin Eskaley gabanta ya tarwatse wai Zaidunta ne ke rayuwa irin ta Mashaya, ta kasa yarda.


Master yace "Wallahi Nene Solo zata mana yau, gata chan ta tafi ta kai ma Mankas, shegen ba bamu zai yi ba, ku mu bita".
Nan fa Eskaley ya kulle shago suka biyan Motar Nene su hudu.
**
Gabanta ya tsananta faduwa da ta hango gidan Alhaji Ali Zaki, duk abunda ya faru a shekarun baya suka dinga dawo mata kamar a lokacin abun ke faruwa.
***


Yau Saturday, Mutanen Gidan sun tafi Daura Biki, Baba ma ya kaisu da kanshi, daga ita sai Uncle Hudu a gidan, Ya Zaid bata san ko yana daki ba, ta kira wayarshi bata shiga, Wani irin k'ishi takeji, amma bata son fita daga dakin, ta zabi tayi zamanta a daki hankalinta zaifi kwancia don har ga Allah bata son duk wani abu da zai hadata da Uncle Hudu.


Ya fara wuce gona da iri, ita tsoronta kar ya mata wani mugun abun, kar ya dakusar mata da rayuwa, ya goga mata Fenti da ba zai taba goguwa ba.
Saidai k'ishi takeji ba na wasa ba, har ta na ta shak'uwa, yanke hukunci tayi na tafia daukowa a kitchen ko ta diba a dispenser da ke parlo.


Kamar barauniya haka tayi Sando har parlo tayi amfani da Cup din wurin diban ruwa.
Ji tayi an mata wani irin chakulkuli a gefen cikinta wanda ya sakata sakin Ihu da k'arfi.
Da sauri ya sa hannunshi a bakinta tare da rik'o k'ugunta.


"Matsoraciya, meye abun Ihu"
Gani irin rik'on da ya mata ya sa ta fashewa da kuka tana fadin "ka sakeni donAllah, bani so fa Uncle Hudu, donAllah sakeni" tana k'okarin kwace kanta shikuma yana sake rik'ota tare da tariyota jikinshi.
**
Ya fito daga Dakinshi zai shiga ya ga Dalo kafin ya fita waje, ya ci karo da Nene da wasu mutanen da bai shaida ba, sai ‘yan Bencin Eskaley da mamaki yake binsu da kallo.
Yace “Nene ta ya kika shigo da su Master? Meye kuka cika mana Gida”.
Nene da bakinta ya dade a Bude tace “Takwaran Zaidu Bawan Allah, wannan wankan fa? Ina jallabiyar? Wa ya baka jamfa ka saka?”.
Zaidu ya kalli Jikinshi yana murmusawa kafin yace wani abu master yace “yo ai Nene mun zata kece kika mishi kika mana solo, kwana uku kenan yana sa kayan nan”.


Nene tace “Aifa kayan nan sun shiga uku, har sai sun fita hayyacinsu za a bar saka su”.
Hajia Aisha Lema ta girgiza kai, ita Nene wai ta manta mai ya kawo su ne? Zata biye musu suna wasu maganganu.


Jawad ya gane Zaid, Tsaf ya ganeshi, kallon kyama yake mishi.
Mancy da ta gama karantar danta tsaf, duk ya fita hayyacinshi, ba yaron da ta bari bane shekaru 4 da suka wuce, mai makon yayi K’iba, sai ya rame yayi duhu, a k’azance.
Baki ta cire ta kira sunanshi.
“ZAID”.
Inda ya ji kiran ya kalla, kallo daya ya mata ya shaidata.
Baki na rawa yace “MANCYYY”..
****
Kasa kama kansa yayi, ya fara kokarin kai mata kiss a baki ta dinga kwacewa amma rikon da ya mata ba na wasa bane, ganin kiss din zai bata mai lokaci ga dama ya samu, kokari yake kawai ya cire mata zani, ya ko ci nasarar cire mata Zanin, tana kiciniyar guduwa ya daga hannu ya kamtseta da mari, ya sake marinta a gefe dayan, tuni ta sheme a kan kujera, ya sa guiwan shi ya danne ta, yahau kiciniyar cire belt dinshi, dogon wandon shi ya fadi, ta ga daga shi sai Boxers ya rage, hankalinta ya tashi matuka, duk wani k'arfin dake gareta ta tattara ta hado Kalmar "YaaaaYaaaaa".


Duk wanda ya ji Ihun nan ya san ba na lafia bane,a sittin suka shige Parlorn har 'yan Bencin Eskaley, gani sukayi Hudu na niyyar haye Dalo da.


Wani Tsalle Zaid yayi ya dira gaban Hudu.
Mancy ta zube K'asa saboda gani take tata ta zo k'arshe.
Umman Jawad tayi saurin zuwa gun Dalo ta rufeta, kwata kwata bata motsi da alamun ta suma.
Zaid ya kai ma Hudu naushi yafi kala 10a baki lokaci guda.
Nene kam ta shiga tsakaninsu tace kuje ku kai ta Asibiti ta juyo ga Hudu da yayi wik'i wik'i da ido charaf ta rik'e gaban Hudu tace "k'aikayi yake maka? Wallahi kaciya zan sake maka yanzu, gundule ka zanyi wallahi"
Master cike da tasha yace "ga Aska Nene,danuwarka Kanwarmu ka danne?"
Terro yace "yau sai ka bi uwarka Lahira".
Nene cikin Muryar 'yan Daba tace "ku zo ku danne min shi".
Kafin kace kobo yan bencin Eskaley sun yo kan Hudu.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa.
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI 2⃣7⃣
(HADARI)


Ganin dai dagaske Nene ta sa an shimfide mata Hudu a k'asa zata yanke shi ya sa Alhaji Abu Ya tsawatar yace "ku bari donAllah" ya kalli Nene yace "Mama donAllah kiyi hakuri".
Nene tace "bashi kwarto ba? Ai barin irinsu da mafitsara bala'i ne, irinsu ne masu fyade 'yan shekara 3, ka bari kawai na gilleshi".


Alhaji Abu yace "aa mama kar ku yanke hukunci da kanku, ku bari Hukuma ta yi aiki".
Nene tace "naci uwar Hukuma"
Master cike da tasha yace "yo Baba ina mu ake kira da 'yan zaman banza Bata Gari? Marasa gata, mune mutanen banza, mune masu halin Akuyanci, to wallahi Baba ga mu nan dai, duk cikin mu ba shegen da aka taba kamawa wai ya danne wata, iskancin mu bai kai nan ba, mu dai barmu da shan Siga da World"
Ya nuna Hudu da Hannu yace "amma don Uwarka kai da kake kallan mu a mak'askanta, in ka bi ta gaban mu ka 6ude mu da kasa da k'ura, kullum kanai mana kallon k'yama, ashe kaine dan akuya dan shegia".


Terro ya dura mai wani irin zagin da kowa da ke gun sai da ya ji nauyin zagin "dan kaza kazanka k'anwarmu zaka danne?".
Ya kaimai nushi a baki, kamar jira 'yan Bencin Eskaley suke suka rubduga mai suka dinga dukkan Hudu ko ta ina, jini ta baki ta hanci.


Nene ta hau tafi, tace "ku ci Ubanshi wallahi, ku ci kutumar ubanshi".
Alhaji Abu ya dinga ce ma su Terro su bari, suka k'i, ya je wurin Mankas da ke tsaye kamar gunki ya dafa shi yace "Zaid, donAllah ka musu magana, kar su kar shi".
Zaid baya motsi.
Jawad idonshi yayi ja alamun tashin hankali, yana tsugunne kusa da Mancy da Mamarshi da kan Dalo ke kanta, Mancy sai jijjigata take,Hajia Aisha Lema kuma tana ta mata firfita.


Alhaji Abu Shamsu ya rasa abunyi, ya dafe kai ya dake juyawa ya tako gaban Nene yace "donAllah ki sa su bari, Mama in rai ya baci, hankali bai gushewa, in rai ya baci, hankali ke nemoshi, kiyi hakuri, yanzu in sun kashe shi, me kike tunanin zanyi faru? Sun kashe rai, ke da ke musu gata zaki iya cetansu baki daya a gidan yari?".


Wani dan tunani Nene tayi kafin tace "kai ku kyaleshi".
Ba su ji ta ba sai da tace "danuwarku ba ku jina? Nace ku cika shi ko?".
K'yaleshi sukayi suna huci, Alhaji Abu yace "ku fesa mata ruwa".
Jawad da dan sauri ya k'arasa gun dispenser ya bude ya dibo ruwa ya ba Mamar Rafeeq.
Fesa ma Dalo tayi.
A firgice ta farfafo, tana bude ido ta sauke su kan Mancy, a sittin ta zabura ta shige Jikin Zaid da ke chan gefen ta ruk'unkumeshi.


Zaid ya rungumeta yana shafan bayanta, firgice Dalo take, jikinta be bar kakkarwa ba.
"Yaya, Uncle Hudu ne".
Zaid yace "Its Okay, he wont hurt you".
"Yaya wata mai kama da Mancy".
Zaid ya kalli Mancy ya kau da kai ga cigaba da lallashin Dalo.
Nene ce ta rik'o hannun Dalo da Zaid ta tura cikin dakin Dalo, ta rik'o na Mancy ta turata itama dakin ta ja k'ofa ta rufe.


Ta kalli Hudu da 'Yan Bencin Eskaley suka zagaye kamar a cage, ta kalli Alhaji Abu tace "sai ka kira police ko wallahi na barshi da su Eskaley".
*
Daidai da isowar Alhaji Ali Zaki kenan da Hajia Shafa da kuma Annah.
'Yan Parlorn suka bi da kallon Mamaki, basu gane kowa ba sai 'yan Bencin Eskaley, da mamaki suka kalli juna shi da matarshi.
Idon Hajia Shafa ya sauka kan Nene da ta fara chakal chakal da baki kamar mai cin Cingam, haka take in balai da masifa na cinta, sai ta fara cin Imaginary chew gum.


Hajia Shafa'atu bata kai ga magana ba ta ga wani sheme a k'asa kamar matattace yana fitar da jini ta baki ta hanci, ga ido ya kumbura, numfashi da k'yar yake fitarwa, kallonshi tayi sosai, hajinta ya kada, baki na rawa tace "Hudu?".


Hudu da jin muryar yayarshi ya na son tattaro karfinshi ya tashi ya ji an take mishi hannu ya koma lakwaf.
Hajia Shafa'atu ta k'araso gun shi da gudu tace "Hudu, me ya sameka? Uban wa ya tabaka?".
Nene tace "Ubanki ne".
Hajia Shafaatu ta fashe da kuka tace "Alhajina ba zan iya ba nidai ka sakeni, wannan matar bata bar bibiyanmu ba ko? Yanzu ta zo ta sa 'yan iska sun duka Hudu, wallahi ba zan yarda ba ka kira Police wallahi yanzu ya kwashe su duka".


Nene ta daga hannu ta mareta tace "Barikin Sojoji zaa kaimu, nace a kaimu barikin sojoji, in baki bar kallona ba sai na tsokale miki ido, hatsabibiyar Mata, kai kuma sakarai hotiho soko, har yau asirin be bar kan ka ba? To kaji da kunnenka, wannan dan akuyan da ya gaji Akuyanci wurin Iyayenshi, shi muka kama dumudumu zai ma diyarka Sadiya Fyade, akan wanchan kujeran muka kamashi yana niyyan afka mata, da Alhaji ya kyaleni ai wallahi Kaciya zan sake mai".
*
Dalo da Zaid kallon Mancy sukeyi cikin Ido, ita kam Mancy ta kasa hada ido dasu, kanta a k'asa, ba ta san ta inda zata fara ba, lallai ita mai laifi ce.
Zaid ne ya fara magana inda yake cewa "Kin gani ko Mancy? Kin ga abunda kika ja mana ko? Seconds 10 zamu k'ara rayuwar Dalo zata ruguje, wallahi da mun k'ara 10seconds da shikenan Hudu ya lalata ma Dalo Rayuwa, Mancy ba zan gaya miki abubuwan da suka faru ba a iya shekarun nan, amma Mancy baki kyauta ba da kika barmu a nan, musamman Dalo, da kin tafi da ita gabanki, Mancy 10secs fa zamu k'ara•" muryarshi ta karye.


Mancy da Dalo suka sake fashewa da kuka.
Mancy ta zube kan guiwowinta tana kuka tace "ku gafarceni 'ya'yana, hak'ik'a ni din mai laifi ce, na muku laifi gagarumi wanda ni a gani na Gata ne na muku, wallahi ba zanso kuyi Agolanci ba, a ganina duk bacin gidan Mahaifinku baku da inda ya fishi, balle ku ba yara bane, bansan na jefa rayuwarku a wani hali ba, ku yafe min don Girman Allah".
Tsakanin Da da Mahaifi sai Allah, zuciyoyinsu ya tabu.


Ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Dalo ta rungume Mancy kamar zata shige cikin cikinta tace "Mancy nayi Kewarki Sosai wallahi, i have missed you so much".
Mancy itama ta rungumeta tana kuka tana "Ki yafe min Sadiya, ki yafe ma Mancy, a ganina ina yin abunda nake ganin shine daidai".
Dalo tace "Mancy, wallahi bakiyi min komai ba, kewanki kawai nayi sosai, Mancy ki tafi dani".


Gyada kai tayi tace "ba zan sake nisa da ku ba, aure da mutuwa kawai zai rabani da ku, wallahi daidai nake da Babanku yanzu, bai isa ya rabani da ku ba, bai isa ba wallahi, kafata kafarku".
Zaid ya fashe da wani irin dariya mai hade da takaici da bak'inciki.
A tare suka kalleshi.
Mancy tace "Eh Zaid, k'afata, k'afarku".
Zaid yace "k'afarki k'afar Sadiya, zan tabbatar da hakan, ko Baba bai isa ya hana ba, matarshi kuma ko da bak'ar Jaba take tsafi ba ta isa ta hana ba, zan tabbatar da hakan".
Mancy ta kalli Zaid tace "Kai fa?".
Yace "Ina zakije da Baligi kamar ni? Gidan Aurenki?".
Mancy ta girgiza kai sai taji Zaid kamar Magana yake gaya mata tace "Aa Zaid, kuskure nayi a baya, zubar da ku shine babban kuskuren da na tafka, amma yanzu

Please Login or Register in order to submit comment