Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine k'arshen shigowa yace “Jawad, je kira man Sadiya”.
Mik’ewa yayi ya tafi dakin Mancy.


Tana zaune ta tana Waya da Yasmin ya shigo da Sallama.
“Aunty Yas, ina zuwa”.
Ta kashe wayar ta amsa Sallamarshi.
Zama yayi kan kujera yana kallonta.
Yace “me kika ci da zakice bakiji Yunwa”.
Murmushi tayi tace “dagaske bana jin Yunwa”.
“Oya tashi muje dining table ke kadai muke jira”
Bambarak’wai taji abun, bata saba ba, ita yau ake jira a dining? Tafi sabawa da zaman Daki.


Muryarshi taji “Sadyyy”.
“Tashi mu tafi, stand up”
Kallonshi kawai tayi, ya tisa k’eyarta suka fita.
Gabaki daya ‘yan table din suka juyo suna kallonsu, sai da ta zauna Abba yace “to Bismillahnmu, Sadiya, kiyi serving dinmu”.
Ta tashi a tsanake ta shiga zuzzuba ma kowa abinci.


K A T S I N A


Abun ya tsaya mishi a rai shiyasa ya kasa bacci.
Karfe 11:30 ya ji ana bude kofar dayan dakin. Tashi yayi ya leka, yaga Labiba ta fito tana Sanda kamar me shirin shiga sata.
Mamaki abun ya bashi.
Ya bita da ido yaga ta nufa Hanyar Gidan Ali Zaki, wurin Langa Langan, ido ya zuba mata yaga gudun ruwanta, ta ina zata bi?.
Gani yayi ta fara girgiza langa langa tana daddako kusoshi da suka danneshi.
Baki Baban Amira ya bude.
Aunty Aseey ta tashi tace “lafia?”
Bai bata amsa ba, ta tashi tazo bakin Window, baki ta bude da mamaki.
“Labiba?”.
Baban Amira yace “Shhh, tsaya muga mai take shirin yi”.
A hankali suka bude kofa suka bi bayanta a hankali, ta langa langa suke kallonta tana gaban dakin Zaid tana magiyar ya bude mata.


“DonAllah Soulmate ka bude min, zuciyana zafi, hankalina ya kasa kwancia, donAllah ka taimaka ka bude min na maka bayani”.
Kusan minti 20 tana mai magiya, sauri duk sun bi kafafunta.
Dabara tazo mata ta leka wurin ramin jikin kofar ta hangoshi sheme kan gado yayi baje baje.


Ta dan yi daria tace “au ashe bacci yakeyi, zan dawo gobe i love you”.
Baban Amira ya kalli Asiya suka jinjina kai, a hankali suka koma daki, suna kallonta ta shigo, ta gyara langa langan, harda daukan dutse ta bubbuga wurin kusa, ko tsoro batayi, ta lallaba ta shige daki.


Ai mamaki kashe su yayi, Aunty Aseey dai ta kwanta ta barshi zaune.
Jikinshi sanyi Yayi, Labiba tayi nisa haka bata jin kira, ya santa, kafiya gareta, in ba rabata yayi da garin ba, ba zasu rabu da junansu ba, yanke hukunci maidata Gida zaiyi Gobe InshaAllah.


Da Asuba ya gaya ma matarshi shawarar da ya yanke, bata ji dadi ba amma wannan ce hanya mai bullewa
Baban Amira ya sameta kan dardumarta a dakinta, ta gaishe shi, yace “Labiba, tashi ki hada kaya, Edo zamu tafi”.
Tace “Yaya Lafiya? Wani abun ya faru?”.
Yace “Eh to ina jin wani abu ya faru, amma sun ki gaya min, kuma na san in na ce musu zamuzo Abba zai hana, gwara muje kawai mu gani”.
Gabanta ya fadi tace “Mami ce ko Yaya?”
Ya girgiza kai yace “aa ba ita bace”.
Wayarta ta wawuro, ya fizge ya jefata Aljihu yace “na gaya miki banso su san zamuzo, in ba zaki tafi ba in yi tafiya ta”.


Da sauri ta tashi tace “Yaya wallahi ba zan iya zama ba, hankalina yayi Gida kuma muje”.
Yace “kiyi sauri kiyi wanka”.
Tace “Aa Yaya, mu tafi kawai, ka siya min Bread a Tasha”.
Baya son ta chanza raayinta, yace hado kayanki, tace “Akwatin a shirye yake, jiya na shiryashi”.
Yace “to mu tafi”
Yara na Bacci, Aunty Aseey tana ta hawaye, hawayen rabuwa da Labiba, sosai take son Labiba, bata so rabuwa da ita ta wannan hanyar ba.
Ganin Aunty Aseey na kuka, ya sa jikin Labiba yin sanyi sosai, ta rungumeta itama tana hawayen tace “Aunty Aseey inshaAllah bakomai, ki bar kuka, Yaya mu tafi da ita”.
Yace “Labiba ga yara, ba kudi sosai hannuna, kudin dawowa ma sai Abba ya bamu”.
Ta share mata hawaye tace “Ba zamu dade ba kinji Aunty Aseey?”.
Har bakin Kofa ta rakasu, suna fita bakin Titi suka samu Express guda biya. Ya tsaida su ka tafi Tashar KTSA don hawa motar Suleja, kasancewar babau Motar Edo daga Katsina, daga Suleja zasu hau Motar Edo.
Allah ya tsare Hanya.
*
Wurin karfe 1 na rana ErRabi ta kira kawarta tace mata ta dawo da Asuba, ance mata tazo.
Tace “gata nan zuwa yanzu yanzu akwai matsala”.
Aiko suna gama wayar ta ciri gyale ta fita ko Annah bata gaya ma fitarta ba.
*
Garin Kankia yayi dadi sosai sakamakon yayyafin da ake ta yayyafawa mai dan k’arfi, a gajiye ta dawo Call Room ta zauna, ta cire wannan takalma irin ta likitoci tana matsa k’afarta da wuyanta, wani doctor da suke cema Chief ya na mata daria “You look tired doc?”.
Tayi daria tace “Chief i am so exhausted Allah, i want to go home today but i cant drive, but first thing in the morning tomorrow InshaAllah”.
Ba ta ji mai Chief yace ba saboda wayarta da ta shiga ruri.


Ta dauka taga Sam ne.
Sam mai aikinsu ne kuma amintaccen Mummynta ne don cikin gidan ba inda bay shiga, shi Er Rabi ke aika yana kaima mabiyanta magani.

Dan tsaki tayi, kiran me yake mata? Ta dauka da “Hello Sam, what is it?”.
Yace “Ehn small madam, na you talk say make i holla you anytime wey Aunty Shafa show ba?(Eh Hajia karama kece kika ce na gaya miki duk ranar da Aunty Shafaatu tazo ba?”.
Da sauri ta gyara zama tace “Ehen..”
“She don come house, and she dey vex, i greetam sef she no answer me(Ta zo gida, tana cikin bacin rai, har gaidata nayi ma bata amsa ba”.
Yasmin tace “Sam, where them they?(Sam suna ina?”)
Yace “them dey Madam’s room”.
Tace “Abeg Sam, hurry enter the room on that switch wey i give you the other day, puttam for their front, send your account number nownownow” (danAllah Sam ka shiga Dakin nan, wannan abunda na baka kwanaki ka kunna minshi, ka ajeshi gabansu, ka turo min Account number dinka yanzu yanzun nan”.
Daria yayi yace “no wahala madam”.


Sai da yayi Knocking ya shiga da tray din karfe a hannu ruwa ne da juice, a jikin tray din ya manna recorder din, kamar magnet take ‘yar karama, in baka san da ita ba ba za ka gane zamarta ba, ya aje a gaban Aunty Shafa’atu ya fita.


K’amshi ta ciro wani abu kamar Mp3 a jakka ta sa earpiece. Ta dauki Jakkarta ta rataya tana tafiya zata tafi dakinta a Doctors quaters tana sauraran maganganunsu wanda duk hargowa ce ta zuwan Mancy da chanzawarta da jin zafinsu, sunfi minti 30 suna magana daya, har k’amshi ta isa dakinta ta zauna tana jinsu.


Ta na jin Muryar Mummynta na cewa “Yanzu Shafa’atu ki fadi abunda kike so, da bakinki kawai zaki ce ga abunda kike so”.
Ta ji Aunty Shafa’atu tace “Wallahi na tsani Maryama da duk wani abu da ya danganceta, kinga kallon kaskancin da ta min? Nidai ta mutu, a kashe min ita, ke Dalon ma ta mutu, Dan Makaho yayi hauka ya mutu shima”.
ErRabi ta bata fuska tace “Ke ban san iskanci, ba Yasmin ke son shi ba?”
Shafa’atu tace “ke Wallahi baya sonta, dazun nake gaya miki aka kama shi da budurwarshi ko karuwarshi a daki, da na mishi maganar Yasmin cewa yayi kar na sake mishi maganarta, ya tsaneta ba abunda zaiyi da ita”.


Er Rabi Ta lula wata Ashar, tace sai ko yaci Ubanshi, diyata zai yaudara? Bayan son da take mishi? Aiko yanzu zan aiki aljani ya shakeshi har sai ya mutu, anjima zanyi na Maryama”.


Tuni Jikinta ya fara rawa, wani fitsari taji a jikinta na gangarowa, kanta ya sara, ta rasa me zatayi, fita tayi daga dakin, sauri sauri bata san lokacin da ta arta a guje ba, bata damu da kallonta da mutane keyiba, ta na gudu tana neman layin Mummynta, wayarta bata shiga, Aunty Shafa’atu ta nema. Itama haka wayar tata.
Sai a kira Sam.
“Sam where you dey, take your phone to Mummy now”.
“Ahh small madam i don commot”.
Cikin Ihu tace “Sam, go home now, call me ASAP”.


Dafe kai yasmin tayi cikin rashin sanin abunda zatayi.
Sama ta kalla taga ruwan sama akeyi yafi k’arfin yayyafi.
Da gudu ta shiga ruwan nan, ta sa hannu a Aljihu ta ciro key ta wuce inda tayi parking Motarta.
Ta shiga ta cigaba da kiranta not reachable, ta sake kiran Sam yace ya kusa.
Tura ma Mummy messages tayi kala kusan Biyar, saboda rashin sanin abunyi harda voicenote ta mata na kuka a whatsapp.
Ganin kamar tana bata lokacinta yasa ta bar Asibitin a guje.
Wadanda suka ganta sun nemi layinta.
Bata iya daukar wayar kowa ba, asali ma rejecting takeyi tana neman numbern Mummynta hankali a tashe.


Abu na Allah, Cikin Garin Kankia Ruwa akeyi sosai, baka ganin Motoci na tafia, da yawa sunyi Parking Motocinsu a gefe sai ruwa ya tsagaita, amma ita cikin ruwan nan take tafia, kuka takeyi sosai da karfi kuma, driving takeyi Kacokam, speeding takeyi kuma, burinta daya ta ganta a garin katsina, cikin gidansu kafin a ma Zaid komai.


Wayarta ta yi ringing Sam ne. Da sauri ta dauka, mai makon ta tsaya tayi parking ta amsa wayar, sai ta cigaba da tukinta ko gudu bata rage ba.
“Hello Sam”
Muryar Mummy ta ji “Yas”
Kamar jira take ta fashe da kuka


“Mummmmy, dont do it, Mummy kar ki kashe min Zaid, wallahi Allah Ina son shi, Zaid shine farincikina, in kina son Farincikina kar kiyi komai da zai taba shi ko wani nashi”.
Yasmin DanMakaho be sanki wata yarinya yake so, me zakiyi da wanda bai san mutuncinki ba, upon all the sacrifices you made for him? Wallahi he must pay with his life”.
Kamar a gabanta tayi ta girgiza kai kamar kadangaruwa hawaye na kwaranyowa a kumatunta.
“Wallahi Mummy ki kayi wani abu da zai sa na rasa Zaid ko farincikinsa, ba zan taba yafe miki ba” kamar zautatta chan kuma ta koma lallashi “MUMMY, donAllah ki bari, mummy ki dauka wannan rokon da nake miki roko na karshe da zaki min abinda nikeso, ko meye kar ki min amma ki min wannan, this is all i ask, ki rabu da Zaid, ki zare hannunki daga lamarinsu, mummy for me please”.


Bata ga Katon dutsen Checkpoint din da ke gabanta ba, Sai ji tayi kawai ta bigeshi. Motar walwalwal tayi ta sake fadi, sai Wuta, duk da Ruwan Saman da akeyi, bai hana Motar Yasmin ci da wuta ba.


Er Rabi taji Gbam kamar an bugi wani abu.
Sai taji Yasmin ta bar magana sai faman “Hello Hello take cewa ba amsa”. Amma wannan bugun da taji ya bata tsoro, sai chan kuma taji dif. Trying Wayar Yasmin ta shiga yi amma ya k’i shiga, nan hankalinta ya k’i kwanciya.


Mutanen gari suka firfito, babu wanda ya iya zuwa wurin, ga Ruwan Sama ana yi, amma Mota na ci da wuta, to wani taimako zasuyi? Amma duk da haka yan kwana kwanan Kankia sunzo da motarsu, don kashe wutan nan, Ikon Allah ya tsahirta wutan nan, ruwa ya dauke.
Sai hayak’i, duk da sun san cewa ba lallai bane akwai rai, haka jamian suka daga motar suka kifar, aka bude ga mutum zaune, amma sun kasa gane Mace ce ko Namiji saboda k’onewar da gawar tayi”.


“Inalillahi wa ina ilaihir rajiun” kalmar da duk wanda ke wurin ke fada kenan.
Wani tsoho yace “Ba rai, wannan bawa ya amsa kiran Mahalicci, Allah ka karbi shahadar wannan Mammaci, wutan duniya ta ci bawan nan, InshaAllah ya kubuta daga ta Lahira, Allah ka sa muyi mutuwar Shahada” yan wurin suka amsa da “Amin”.




#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA ASHIRIN DA TARA 2⃣9⃣
(ZAN RAYU DA KAI ❤ ZAN MUTU DA KAI 😭 )


A tasha tayi Sallahr Asuba, Motar Suleja ta hau, tunda ta shiga Motar suka fara tafia gabanta yake faduwa, fargaba da tsoro suka cika mata zuciya, kar suyi Accident fa, ji take kamar ta sauka, amma zuciyarta ta riga ta kitsa mata, bacci takeji amma bata ga ta bacci ba haka tayi zaune tana sak'e a ranta.
Allah ya kaisu Suleja Lafia, daga nan ta hau Motar Katsina.


A B U J A


Mancy na dakin Abba, Dalo ita kadai ke zaune a Dakin Mancy ta na neman wayar Zaid ta kasa samunshi, a duk lokacin da ta tuna Yasmin da Alherinta sai ta zubda hawaye, sallama yake tayi, bata ji ba, har yazo gabanta ya zauna.
Hannu ya tafa, ta dan firgita.
"Ina kwana?" Ta gaisheshi kanta a duk'e.
Bai amsa ba yace "tunanin me kikeyi?".
Murmushi ta dan kirkiro tace "bakomai".
Yace "Ba nace a daina kukan nan haka ba?".
Marairaicewa tayi tace "fa ba kuka nakeyi ba?".
Irin muryarta yayi yace "to me kikeyi?
Da sauri ta kalleshi jin yanda yayi magana kamar wani dan auta, au danauta ne ashe, dauke ido tayi saboda kallon da yake binta dashi.
Yace "Kin gaya min matsayin Yasmin a wurinku, zan sake gaya miki kamar yanda na gaya miki jiya, shi mamaci addua yake so fiye da komai, kuka baya kara musu komai sai nauyi, ki roka mata rahama, balle ita da muke sa ran inshaAllah tayi mutuwar Shahada, ki bar mata kuka please".


Duk jikinta ya mutu da yanayin maganarshi, shi haka yake? Haka yake magana? Muryarshi sanyi? Wannan in ta cigaba da sauraran muryarshi sai ya sa ta shiga wani yanayi".
Yace "dama Abba yace muje na miki register Catering School kafin a samo miki Admission a Nile University".
Cikin jin dadi tace "Dagaske?".
Ya langwabar da kai yace "eh dagaske".
Ta sa hannu ta rufe fuskanta, ta lura Ya Jawad na san zolayarta.
Ya mik'e tsaye yace "ina jiranki a waje".
Ya fita, ta bi bayanshi da Ido.


FIKRA Catering School ya mata register, maimakon su wuce Gida, sai ya shiga Yawon nuna mata gari, don ya san in suka koma Gida daki zata shige tayi ta kuka, shi kuma har ga Allah baya son Kukan nan.
Sai da ya ga tayi daria kafin ya daina k'okarin sanyata daria.
Akwai wani abu da yake ji a game da ita, yana ganin kamar Tausayi ne, amma cikin zuciyanshi ya san ba haka bane.
Na wani dan lokaci Dalo ta manta da damuwarta, yanda Jawad ke ji da ita ya sa take jin wani abu game dashi, ta san shi ba tsaranta bane Hmm, a dai bar maganar.


K A T S I N A


Tarin da Dr Ali ya ji Zaid nayi jiya ya tsaya mishi a rai, yana tsoron kar stage din TBC dinshi ya kai ga Liver Transplant, wayarshi ya dauka ya latso Zaid amma wayarshi is switched off, sak'e sak'e yayi tayi daga k'arshe ya yanke hukuncin zuwa ganin Zaid, daga nan ma ya zo ya mishi tests a ga yaua matsayin ciwonshi yake yanzu.


Maigadi ya tabbatar da cewa Zaid na cikin gida, ba tare da jiran komai ba Dr Ali ya nufi Boysquaters, yana shiga dakin ya ga Zaid kwance murus k'asa, da sauri ya karasa gunshi yana jijiga shi, da alamun ba yanzu yayi collapsing ba.
Da yake Dr Ali Giant ne, haka ya saba Zaid a baya ya fita don kaishi Asibiti, a kagauce yace da Maigadi "donAllah je ka fada cikin gida Zaid baya da Lafia, na tafi dashi General Hospital"
Bai jira cewar maigadi ba ya bude motar ya tura Zaid shi kuma ya shige motarr.
Maigadi yayi cikin da gudu don sanar da su.
Hannah kadai aka samu, Shafaa na chan gun Er Rabi.
Da aka gaya ma Hannah tabe baki kawai tayi yo su ina ruwansu da wani rashin lafian Zaid? Allah sa ma ya mutu.


A Asibiti tuni an kaishi Emergency Room Likitoci suka dukufa kanshi, abunda Dr Ali ke gudu shi ya faru, Kusan rabi da kwatar Hantar Zaid ta lallace, kuma in har baa mishi dashin Hantar ba, to Hantarshi zata fashe, ga Hak'ark'arinshi duk sunyi bak'i saboda hayak'i dake bi ta wurin.
Dr's suka yanke shawaran yi mishi aiki cikin gaggawa saboda kar lallacewan Hantar ya tabo Huhunshi.
Wani daki a ka kai Zaid don a kara mishi ruwa da jini saboda he is very weak.


Har ya farfado Dr Ali na dakin yana kallonshi cike da tausayawa.
Muryar Zaid baya fita, amma sai da yayi karfin halin cewa “Na kusa mutuwa ko?” Sai da ya kasa kunne kafin yaji abunda yake cewa.
Dr Ali yace “Zaid ba wanda ya san gawan Fari, zaka samu lafia”.


Zaid yace “kar ka boye min, ka gaya min”.
Dr Ali yace “Zaid, liver dinka is damaged, you will need a transplant”.
Zaid ya lumshe jajayen idanuwanshi yace “tawa ta kare kuma, zani bi Yasmin”.
“Aa donAllah, kar kace haka, zanje gidanku na samu babanku, an san wanda zai baka hantar a diba, da anyi transplant din shikenan inshaAllah, duk da your ribs are infected once you quit smoking, you will be fine by God”.


Zaid ya murmusa yace “ina kace zaka? Gidanmu? Waste of time, kar kaje, nikam da drip dinnan ya kare zan koma Gida”.
Duk da ya san abu ne mai wahala, but zai koma gida ne kawai ya jira ajalinshi


*****
E D O


Har Bayan Azahar Mami bata ga Labiba ba.
Abun ya k'ular da Maminta, don Ubanta fushi take don an mata fada? Shiyasa bata fito ta gaishesu ba? Bata tunani ko Sallah ma tayi, tashi tayi a fusace, ta kama Labiba sai ta mareta, bude labulen dakinsu Labiba tayi, sai gani tayi wayam ba kowa.


Mamaki ya kamata, tun dazun take Prlo, yaushe labeen ta fita? Haka kawai ta tsinci kanta da lek'a kasan gadon.
Da sauri ta bar dakin ta shiga dakinsu Samira, suna nan zaune duka.
"Samira ina Labiba?"
Samira tace "tab, yo ai ni duk yau banga Labee ba".
Mami tace "tashi duba man Gidansu Jamilu ko ta shiga".
Kuiwa garesu, sai da ta dan bata lokaci tana zumbura baki kafib ta fita.
Jim kadan ta dawo tace "mamarsu jamilu tace ba ma su san Labee ta dawo ba".
Mami tace "Ikon Allah".
Mamarsu Samira tace "fushi tayi fa, kila tana Gidan Zainaba, sai kunyi biko zata dawo."
Maminta tace "Aiko Zata ci Ubanta"
Ta koma dakinta ta dauki wayarta takira diyarta Zainaba.
Ko amsa gaisuwarta batayi ba tace "Maza kice Labee ta hau A daidaita sahu ta dawo Gida yanzu ina jiranta".
Zainaba tace "Mami wace Labeen? Labee ta dawo ne?".
Mami tace "bata Gidanki?".


Zainaba tace "ai ban ma san ta dawo ba".
Kit Mami ta kashe, kiran Mai bi ma Baban Amira tayi Hamza, tace "Hamza labee na gidanka?"
Hamza yace "Aa Mami, sai dai in gidan Zainaba".
Ruwa idon Mami ya kawo tace "Hamza Labee ba ta gida, bata gidan Zainaba, in ba gidan Zainaba ba, gidanka, in ba ta nan ban kuma san inda take zuwa ba".


Hamza yace "Kar ki daga Hankalinki Mami, kinsan Labee dai, ba zata wuce Gidajen Yayyinta ba, barin kira su Hashim, sai naci Ubanta in tana fita bata gaya miki ba".
Mami tace yauwa Kirasu.
Daya bayan daya Hamza ya kira Yayyinshi da Kannenshi masu aure, daga wanda ba su ma san Labeen ta dawo Edo ba, sai wanda suke ceea aa bata zo ba".
To shima fa nan Yaya Hamza ya kasa Zama, ya hau dan babur dinshi ya burko zuwa Gida, da niyyar in ya kama Labee, wallahi babu abunda zai hana shi zane ta da Belt din Jikinshi.


Abu kamar wasa Duk inda aka san Labiba zata iya zuwa sai da aka bincika amma ba alamun wani ya ganta, an kira wayarta a kashe.
Hayaniya ya firdo da Yaya Muhammadu da Abbansu
"Mai ya faru?" Suke ta tambaya
Maman Samira tace "kunga tun dazun ne muke neman Labiba ba mu ganta ba, ba inda ba mu dibata ba, duk gidan da muka san Labiba na zuwa munje bata ba alamunta, wayarta a kashe kuma".
Abba ya saka salati, ya ma rasa me zaiyi, baban Amira kam kwallah ya fara yana tunanin tana ina.
Ba mai zama, kowa aka barbazu neman Labiba, babu wanda ya kawo ta koma katsina.
A bayyane Abba yace "kina ina Labiba?Allah ka tsare min Labiba a duk inda take".


K A T S I N A


Farfadowa tayi ta bi masu zaune a dakin da ido.
Ganin ta bude ido ya sa su mikewa tare da matsowa bakin gadonta suna mata sannu, barin ma Shafa'atu da ta fi kowaccen su zak'ewa.
Er Rabi bata iya ce musu komai ba, ta cigaba da binsu da ido daya bayana daya kafin tayi yunkurin tashi, zasu riketa ta daga musu hannu.
Da kanta ta tashi ta zauna kan Gadon ta kalli ta gefenta tace "yau wace rana?".
Alhamis aka ce mata.
Murmushi tayi tace "yau kwanan Yasmin Uku da rasuwa? Ina nan kwance kamar gawa? Meyasa baku tadani ba?".
Ba wanda yace mata komai, sauka tayi da kan Gadon ta sa Slippers ta fita daga Dakin.
'Yan kwarakonta suka bi bayanta da gudu suna mata magana bata tsaya amsa kowa ba.
Sam na ganinta ya bude mata K'ofar Mota ta shiga ya Ja Motar zuwa Gida.
****


Dr Ali bai ji cewar Zaid ba ya nufi Gidansu, zuwa gidan ke da wuya ya ga Shafaatu da Iyalanta zaune a bukkan gidan, ya gaidata ta amsashi tana son jin ko waye.
Yace “Alhaji Ali na nan?”
Tace “aa baya nan, wake nemanshi?”.
Dr Ali yace “ni ne”
Tace “lafia?”
Yace “dama Zaidu ne baya da lafia sosai, yana chan kwance, emergency surgery zaa mishi inda zaa chanza mishi Hanta, shine ake son relative ya zamana shi zai bada hantarshi”
Galala take kallonshi kafin tace “oh ashe baida lafia, yo ai bamu sani ba, mu kwana runfa daya ace har yana Asibiti ace bamu sani ba? To ba ruwanmu, kar wanda ya sake zuwa mana gida batun Zaid”.
Dr Ali yace “ni babanshi na zo gani, in baya nan ku bani number dinshi in nemeshi”.
“Shafa ta harareshi tace ai bayyi nisa ba, Annah je ki kira min Daddynki”.
Annah ta tashi tana harare harare ta tafi cikin gida jim kadan sai gashi sun dawo tare.
Dr Ali dai na ganin ikon Allah.
Yana zuwa yace “ina wuni?”
Kafin ya amsa Shafaatu ta fara bambami


“Wai Zaid zaa ma dashin Hanta shine aka zo tafiya da kai a bude cikinka a farka ka a cire naka a saka mai kai kuma sai mutuwa”.
Dr Ali yace “Aa wallahi ba haka bane, Baba, Lafiyayyen Hanta kamar bishiya ne, in aka dibeshi bayan wani lokaci da kansji zai tsiro ya dawo normal form dinshi, ba duka ake cirewa ba, diba zaayi”.
Baba yace “me ya samu Zaid din ne?”.
Jin haka Shafaatu tace “Ya kashe hantar shi da Hayaki, ya lallace shine za a zo wurinka ka bada wani Hanta, kar ka sake ka yarda”.


Kamar wanda aka sa ma battery ya fara bambamin fada.
“Ni dan Iska ne? Ni zan bada Hanta na? Kar Allah ya sa ya warke in ni yake jira”.
Dr Ali kamar yayi Ihu yace “Baba Danka Ne fa”.
Baba yace “donUbanka ka fitar min A gida”.
Dr Ali ya kasa motsi, da gudu ya dauko wani gatarin da ake saran flowers ya bishi da gudu Dr Ali ya fita.
Nan Shafaatu ta samu fagen Aibata Zaid.
%%%%%


Er Rabi na zuwa ta ga Gidan kamar ba ayi zaman gaisuwa ba, ba kowa a gidan, ta shiga ta bada umurnin "kar wanda ya shigo mata Gida, tana son kasancewa ita kadai a wannan gabar".


Dakin Yasmin ta shiga, ta na shiga ta saka jam lock tare da sulalewa k'asa, kuka kawai takeyi, kuka mai taba zuciya, ashe Baban Yasmin na nan zaune kan Gadonta, ganin Er Rabi ta shigo ya sashi yin Lamo.


Sai da ta dau lokaci mai tsawo tana kuka kafin ta share hawayenta.
Wayarta ta shiga tana scrolling Messages din Yasmin.
Inda duka rok'o takeyi kar ta taba mata Zaid dinta.
Hajia Er Rabi ta yi mamakin irin wannan So da Yasmin ke ma Zaid, yanzu ta mutu kenan tana son cetar Zaid ko? Amma dai wannan ba.


Sumbatu take "wai ta yaya zata mutu? Ta yaya zata tafi ta barta? Bata san ta na sonta ba? Bata san tana sonta fiye da rayuwa da kanta ba? Ya take so ta rayu bayan ba ta a duniya? lallai duniya abun tsoro, ko daren rasuwarta sai da sukayi Chatting fa.
Kila ma ta bar mata message yau da safe, bata bude ma, data ta kunna,messages suna ta shigowa.
Karanta last chat dinsu take kafin taga Voice note kusan 7.


Na farkon ta bude.
"MUMMY, kinsan Zaid ne farincikina ko? Mummy ki rabu da Zaid, in kika mishi wani abu wallahi ba zan taba yafe miki ba, ".
Kuka Er Rabi ta sake tare da playing Voice note na biyu inda tace
"Mummy, Ina son Zaid fiye da rayuwa da kanta, ki ka kashe Zaid, daidai yake da kin rasani".
Duk sai da tayi playing Voicenotes dinnan tas, tana jin muryar diyarta tana kuka tana nadama.


Messages din ta cigaba da bi inda wani

Please Login or Register in order to submit comment