Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"yo ita 'yar aiki ce da zaa dinga daukarta tana tayin aiki? Nidai barinje in daukota gaskia".
Mancy tace "kayi hakuri Jawad gobe zai dawo da ita".
Jawad yayi dan guntun tsaki ya latso wayar baban yayanshi yace "Hello Yaya, ga Abba nan na ta fada wai ka dauke mishi diya, yace gobe da sassafe ka maido mishi diyarshi kar ya bata maka rai".
Jin muryan Abba sukayi a baya yace "karya ake mun, ni da bansan ma anyi ba?".
Umma tace "Wai Jawad, Wai Abbanku zai maida Dalo Katsina gun Babanta".
Gaban Jawad ya fadi ya zaro ido yace "Abba wai dagaske? Meyasa? DonAllah kayi hakuri, ba Babanta yace ya bar maka ita aure ya rabaku?".
Abba shima ya biye yace "ai Auren zan mata a Katsina".
Ya zaro ido sosai, sai chan yaga suna dariya, sai ya gane ashe zolayarshi suke
Jawad ya bubbuga k'afa cike da shagwaba
Su Mancy suka sa daria baki daya.
Abdulmajeed yace "ana so ana kaiwa kasuwa"
Ya murguda baki yace "ina ruwanka?".
Abdulmajeed yace "ko kayi making move, ko ma hadeta da Aisha nayi Mata biyu rana daya".
Jawad yayi hanyar kofa yace "in ka fasa".
Dariarshi sukeyi sosai Abdulmajeed yace "Mancy Your Boy is In love".
Mancy tace "ai na lura da kanwar taka itama ta na yinshi"
Alhaji Abu ya kalli Iyalanshi cikin dadi yace "Alhamdulilah"..


Washegari Yaya Abdulhafeez ya dawo da Dalo da safe don daga gidansu zai wuce aiki.
Suna kan table suna breakfast.
Sukayi Sallama tare da gaisar dasu.
Abba yace "Yadai? Wannan sammako haka? Kamar ana tsiranku".
Abdulhafiz yace "Abba ance kana ta fada, shiyasa nace in zan wuce aiki zan maidota".
Jawad ya dinga ma Abba Signal da yace eh don in ya gane karya ne zai bata mai rai.
Abba yace "yo eh, sai a dauke man 'Yar yainyata haka akeyi?".
Dalo dai tayi ta daria.
Umma tace "kuzo kuyi breakfast".
Dalo tace "wallahi a koshe muke".
Mancy tace "zo ki kwashe wanda aka ci".
Tace to Ta zo tana hada plates din da aka bata iya daukanta ta nufa kitchen.
Kamar an tsunkureshi ya mik'e yana hada cups yace "dama kitchen din zanje".
Ba wanda yace komai Illah murmushin da suke ta zabgawa.


A Kitchen ya isketa tazo wucewa ya rufe mata hanya.
"Sadyy kikaje gidan Yaya kikayi zamanki ko, kin sa zuciana wahala, yana ta missing dinki".
Bude idanuwanta tayi alamun hakuri tace "i am sorry, zuciyar ta daina Zafi, maganin tazo".
Yace "ni dai kar ki yarda ki sake nisa dani, jiya su Ya Majeed har da zolayana suke".
Shagwaba yake ta zuba mata shi ala dole dan auta.
"Ina ruwansu da kai da zasu zolayeka? Ka rabu da su, zanyi maganinsu".
Yace "Ina Sonki kinji?".
Murmushi tayi ta sadda kai k'asa tana daria.
Yace "wallahi sai kin fada yau, kullun in ta fada ba kya fada?"
Hannu ta sa duka biyu ta kulle fuskanta.
Ya sa cokalin hannunshi ya k'wankwashe mata hannu budewanta yayi daidai da futar "Ina Sonka nima".
Lumshe ido yayi yace "Princess"
Lumshe ido tayi tace "Prince".
"Umma, Mancyy wallahi ga su nan suna soyewa a Kitchen".
Umma tace "Me suke soyawa kuma?".
Mancy dai daria take kasa kasa
Dalo kamar ta shige k'asa saboda kunya.


Alhaji Abu yace "to abu yayi kyau, barin gaya ma Alhaji Ali, in zaa iya hade bikinsu Zaid wallah duk aurar da ku nake in huta"
Da gudu Dalo ta shige Daki.


Alhaji Abu ya kira Alhaji Ali, a handsfree aka saka wayar bayan sun gaisa Alhaji Abu yace "wai wasu sabbin tsuntsayen soyayya muka samo, nace ko dai mu aurar dasu mu bige aiki?".
Daria Alhaji Ali yayi yace "Wa da wa?".
Alhaji Abu yace "Diyata da Jawad"
Cike da jin dadi Alhaji Ali yace "Sosaiii ma, ai kawai a buge aiki".
To sai ka gaya ma su Labaran cewa Su uncle Usman dinsu zasu zo neman aure da saka ranar ran jumaa"
Alhaji Ali yace an gama.


Haka ko akayi, a karshen satin aka kai kudin neman aure, da sa rana Family house dinsu Alhaji Ali zaki.
Shirin Biki ake tayi gadan gadan.
Kullum sai Umma da Mancy sun shiga kitchen.
Alhaji Ali ya turo 2mil wai a ma Dalo kayan daki.
Alhaji Abu ya kirashi yana fada "diyarka ce da zaka turo kudin kayan daki?".
Alhaji Ali yace "Allah Nagode, diyarka ce, wai da gudummuwa ce na turo, amma in ba a so a maido min abuna".
Alhaji Abu yace "baka isa ba, wanda yace ka turo".
Sukayi daria.


A Gidan Yaya Abdulhafeez, Flat ne Uku 3 bedrooms each, Abba ya gina ma 'yaranshi gida tun kafin Abdulhafiz din yayi aure, nan zasu zauna duka.
Sai ya kira Zaid a waya yace "to Ni dai bansan inda kake son zama ba, zaka zauna a Abuja in samo maka aiki ka hadu da yanuwanka?".
Zaid yace "Abba, nidai Katsina nake so, nan nake son Zama, aiki kuma akwai abunda nike jira".
Abba yace "to ba laifi, ka nemo gidan da ya maka, ni zan siya".
Zaid yace "Abba Baba ya bani Gida a Goruba road".
Abba yace "shifa Baban naku karambani, wa ya aikeshi baka Gida? To dama abunda na yi ma su Jawad nike son yi maka, to amma tunda an rigani, zan siya maka Mota kai da Matarka, sannan na samaka chanji a account".
Cike da jin dadi Zaid yayi ta zuba godia.


Alhaji Ahmad Dakata ya ma Labiba da Samira kayan daki, duk abunda aka siya ma Samira an siya ma Labiba, komai iri daya ne.
Zaid yace "ba sai sunyi komai ba, Baba ya gyara gidan".
Tace "ai da bakuyi wahala ba, nan ma anyi komai".
Yace "kuma sai anyi wahalar daukosu daga Edo?ai kawai a barsu"
Hayyakoewa tayi Labiba tace "a yi yaya dasu? wallahi, sai an sa min kayan da Abbana ya min".
Ganin rigima take neman tada mishi yace "to Baby, ba abun fada bane, sauki nake nema".
Tace "to angode amma sai an kawo".
Yace "Allah ya kawo lafia".
Ita fa zuciyarta a wuya yake, kowa ya tashi zai ce "wallahi ki rage son Zaid, wata rana zai miki wulakanci, namiji butulu ne, da ka nuna mishi So, wulakanci ke biyo baya"
Da sun fara maganar nan tashi takeyi ta barsu sai suce ba ta son gaskia..


Yan Bencin Eskaley suka hado mishi gudumuwar naira Dubu dari 25k suka hada each.
Da farko yace "ba zai ansa ba".
Master yace "kai yaro ka amsa wallah mun fika kudi don business mukeyi kai ko mai baka saidawa".
Daria Zaid yayi yace "Yan dunia, ku zo musha World don murna".
Master yace "uwar World zami sha, kana so Baba ya anshe tallafi ne ne"
Daria yayi ya musu godia.
Suka ce ka kaimu Gidan Nene.
Yace "wallahi Nene damuwa ce".
Suka mishi magiya ya rakasu.
Ashe leda sukayo mata.
Sai da sukayi drama a gidan Nene tace wallahi ka bar ganin zakayi aure, sai na saka daki karfe ukun dare na ci ubanka dariya suka saka.


B I K I B U D U R I


Katsina Duk suka gangado.
Ba tare da yin wata bidiah ba
Ran Asabar din Satin aka daura Auren AbdulMajeed Abu Shamsu da Amaryarsa Aisha Usman
Da kuma Jawad Abu Shamsu da Amarayarsa Halimatu Aliyu Zaki a sadaki naira dubu hamsin.
Da Aishar da Sadiyar duk Abuja a ka kaisu gidajensu.
Sati na sama suka garzaya Edo don daurin Auren Labiba.
Duk da ance ma dangi yan katsina an hutarshe da su ba sai sunje ba duk wahala ce amma Edo ta kwashi mutanen Katsina da yawa.
Bayan an daura auren Aminu Shehu da amaryarsa Samira Ahmad Dakata aka daura auren Zaid Ali Zaki da Amaryarsa Labiba Ahmad Dakata da Sadaki naira dubu hamsin.
Text ya mata _Burina ya Cika, Alkawarin Allah ya cika, ina tayaki murna Mrs Zaid Zaki, ina tayaki murnan zama matata_".
Murmushi kawai tayi kafin ta yi sujudul shukur, wai yau itace ta amsa sunar Matar Zaid? Allah mai iko.
A ranar Hajia Bilki ta kirata tana neman afuwa bata zo bikinta ba. Labiba tace "haba Anty ai ba komai, babu ma abunda akayi sai Wedding Fatiha".
Tace "to Albishirinki, consider this as my Wedding Gift, Anyi recruitment, Zaid ya samu One Star 🌟".
"Allahu Akbar Allahu Akbar, nagode Aunty Allah ya biyaki da Aljannah".
Tace "Ameen, Allah ya bada saa, in kun gama Amarcinku nan da 3months zaije training".
Dadi kamar ya kashe Labiba, kasa hakuri tayi sai da ta kirashi ta bashi good news.
Duk da mutane sun mishi yawa sai da ya matsa gefe ya nuna murnarshi yace "wai ke ina kika samu hanyar CD?".
Tace "wallahi wata baiwar Allah ce take sonmu take son taimaka mana".
Yace "Alhamdulilah, Allah ya biya baiwar Allahn nan da Aljannah".
Ta amsa da amin
Yace "zan kiraki, muna pictures da mutane, ina sonki kuma".
Kit ya kashe wayar".


A ranar aka dauki Samira aka kaita gidanta da ke Birnin Edo, washegari kuma aka tafi da Labiba zuwa Abuja daga Abuja aka dauketa a Jirgi zuwa Kano, daga Kano suka iso Katsina duk a gajiye ba a tsaya da ita ba ko ina sai gidanta.


S O Y A Y Y A R U W A N Z U M A


Tana zaune a bakin gado, shi kuma yana daga ƙasa akan rug mai laushin gaske.
Hannunsa na kan cinyarta. Wani karamin kurji ya fito masa wajen gemunsa, a hankali take kokarin fasa mashi kurjin, ba abunda yakeyi sai shagwaba da lalaci a dole zafi yake ji.


"Wasshhh" ya sake fadi a karo na kusan goma. Amma wannan karan harda tura baki sosai tareda jan kansa baya. Kallonsa tayi tareda sakin masa murmushinta wanda ke kawatar mata da fuska.


"Haba Mijin, ka tsaya na gani mana, Haba Masoyi." Ta karasa maganar tareda tallabo mashi fuska.


"Ni gaskiya banaso"


"Just this once, I promise." saita daga hannu daya sama alamar ta rantse. Langwabe kai yayi ya tsaya.. kafin ya kafeta da kannannen idanuwanshi,
Wai yau gashi ga Labiba a matsayin ma'aurata.
Kallonshi tayi ta ga yana kallonta.


"MIJIN" tace cikin muryan da bai wuce raÉ—a ba. Bai amsa ba saboda hankalinsa baya kanta. "BABE" ta sake kiranshi, amma bai motsa ba, bakinta ta hura mashi iska kadan a wajen fukansa wanda yayi zumbur ya dawo hayacinsa.


"A penny for your thought," tace tana murmushi. Riko hannunta biyu yayi ya daura kan fuskarshi, ya shafa kumatunshi da hannunta sannan ya sumbacesu su biyu. Idan da sabo yaci ace ta saba da irin kallon da Zaid ke mata, kokuma wani abin dayake mata na nuna so da kauna. Amma kullum kamar sabon shafi ake budewa.


Kullum sanshi yana daɗa ƙaruwa daga ɓargonta har duka ilahirin jikinta. Kowane Sonsa na gaɓoɓinta yana amsa irin soyayyar da Zaid yakeyi mata.


Janyonta yayi ƙasa zuwa inda yake zaune, ya tallabo fuskarta Ya hada idanuwansu. Baice komai ba bayan kallon kallon da sukeyi. Duk jikinta yayi sanyi, Zaid yanada wani kwarjini wanda bata taba ganiba. A murya ƙasa ƙasa yayi magana.


"Ki daga fuskan ki." bata kula ba illa murmushi. Wai yau itace take kunyansa sosai. Tama rasa ganewa da gaske ta kasa kallonsa ne ko tsabaragen iya shege ne. Ta tuna irin liver dinta lokacin datake zuwa dakinsa, amma yau gashi a matsayin mijinta amma tayi bala'in laushi.


"Ki daga please, badan halina ba sai dan soyayyar danake maki."


Bin umurninsa tayi ta kalleshi.


"What are you doing to me beebsss?" yaja sunar sosai chan cikin makoshinsa. Kai zaka zata shiya rada mata shi. Ita kanta a lokacin tasan cewa tunda tazo duniya babu wanda ya taba kiran sunan haka, Yafi zama akan bakinsa kamar danshi aka halicce ta.
_Dan shi mana aka halicce ta, she's surviving for him. Rashin sa zai zame mata barazana a rayuwarta_ ta tuna.


Magrib aka soma kira, ba ita kadai ba harshi yana bukatar hutu sun sha jigilar hanya, a gajiye suke, ba abunda zasu iya yi, yau hutu kawai zasuyi.
Labiba ta zame mashi tamkar world wanda he is addicted to a da. Duk yanda yake muradin shan World ko wani Sigari duk yanda yake san sha ko kadan, input dinta duk yafi mashi zugi. Har tsoro yake ji saboda soyayyar ta yayi mashi babban kamu.
Idan yaje sallan magrib zama yakeyi a masjid yana tilawa har a kira isha. Text ya tura mata kafin ya dawo.


We were once on separate paths
We knew nothing of each others existence
I agonise by the thought of that
Indeed they were my darkest time
Fast forward to the present
You have become part of me
Like my very own DNA....


Bata karasa karantawa ba ta lumshe ido sai murmushi takeyi. Kalaman Zaid yana dama mata lissafi sosai. Tana kan sallaya sanda ya dawo. Dakin yana kamshin turaren wuta wanda ke ci daga burner a chan kurya gefen socket. Sannan ga AC an kunna madaicin. Dole duk fushinka da gajiya idan ka shiga zakiji ka soma sauka. Gata itama fuskanta yana glowing, yasan ba komai bane illa yawan alwala daya haskaka mata shi. Idon ta a rufe yake, amma zakaga karamin murmushi yana tashi daga kasan leɓanta. Shima kwanciya yayi gefenta ya sakalo mata hannu yayi wrapping dinta sosai.
Sunfi minti kusan biyar a haka. Saiya juya da ita ya kwantar da kansa akan kirjinta, bata hana shi ba illa matse ido tana murmushi. Shima rufe idon yayi numafshin sa yana hawa da sauka. Hannunta ya saka hannunsa saiya harde biyu.


A zuciyarshi yana son Labiba.
Labiba Alheri ce, itace Alherinshi, Cikin ransa baya komai illa gode mata yanda take sonshi, yanda ta tsaya tareda shi a lokacin da yake ba kowa ba, a lokacin da bai da wani gata ko galihu, yanda ko sau daya batayi judging din mugayen É—abi'unsa ba. Yanda koda yayi mata wani abin take tausasa zuciyar ta ta kuma yafe mashi.
Lokacin da yake dizgata amma bata hakura ba, yanda ta take maganar kowa don ta kasance tare dashi, bata guje shi ba.


Yasan ba zai taba biyanta ba, Babu wani abin duniya dazai fanshe abinda tayi, saidai zaiyi amfani da karfinsa yayi kokarin ya kawo mata duk wani jin dadin rayuwa..
Ta mashi halarci sosai, ba zai taba taking dinta for granted, shi ba butulu bane, zai gwada mata Namiji dan Goyo ne.
Duk da ba zai biyata ba, amma alkawari ne, tana cikin adduarshi a kowacce sujaddarshi .Addu'a ya ke binta dashi da fatan zata gama da duniya lafiya.


"I love you Babe," ya fada a bayanne.


"I love you more Sugar," ta fada itama.


"Ina Sonki Matar".


"Ina Sonka Mijin".


"Ina Sonki Sosai".
Tayi daria tace "Sosai nake Sonka".
"I love you baby" tun tana amsawa har ya ji ta shiru.
Haka yayita nanatawa wanda saida dukan ilahirin jikinsa ya gasgata abinda ke fita daga bakinsa. Komai na jikinsa ya aminta da soyayyar ta. Daga kansa yayi ya kalleta yanda take barci cikin natsuwa, wai har tayi bacci, gajiya ce ba komai ba.
Wani hawaye ya ziraro masa daga idanu.
Bai share ba ya barshi yana zuba.
Tausayinta ya kamashi.
Allah kar ka bashi ikon zaluntarta, Allah ka bashi ikon biyan Soyayyarta da k'auna.


He needs her now more than ever, itace battery din rayuwar sa. Kamar yadda waya ba zatayi aiki idan babu battery ba, shima haka yake ji da ita. A hankali ya tashi ya sumbaci goshinta, daga nan sai kumatun ta, sannan ya daura akan bakinta. Bayan nan ya daga ido ya kare mata kallo saiya daura kansa kuma akan kirjinta.


Bazai taba gajiya da sauraran yanda Zuciyarta ke bugu ba. Bugun bana komai ba illa bugun sunanshi watau ZAID.
***^^^


Yau Babbar Bak'uwa garesu
Hajia Aminene Mamman zata zo, Tun Safe ta rasa me zatayi don ta burge Nene.
Bata sanwa, amma don ta burge Nene sai da ta sa Zaid ya jona mata Gas.
Yace "really? 3days after your Wedding zaki fara abinci?"
Gira ta daga mai alamun Eh.
Yace "Dagaske Beebbs ki daina matsa ma kanki, wannan Tsohuwar baki iya mata, wallahi gwasule ki zatayi".
Tace "nidai ka barni, sai na mata, ka kira min Balele na aikeshi kasuwa".
Yace "to Allah ya bada Saa".
Ta murguda mai baki tace "Ameen".


Parlo ya koma bayan ya aiki Balelle kasuwa ya fara kallo.
Balele yaje ya dawo ya kawo mata duk abunda ta aikeshi.
A sannu sannu ya dinga jin kamshin abinci na shigo mishi.
Sai da tayi kusan 3 hours a kitchen kafin ta fito tayi setting table.
Zaid yace "Whats Cooking? Ya bubbude coolers, yaga cooler daya pepper chicken, daya Fried rice, daya tuwon semo da egusi da ya ji kayan miya da k'amshi.


Yace "Lallai Beebs, baa ma Mijin abinci ba, shine aka ma Nene?".
Ta langwabe tace "kar ka damu, zaka ga shagalin da zan maka kai kadai".
"Okay oo I hope she will be impressed though".
"Nikam kana kada min gaba, ka kyaleni".
Yace "okay oo, sai muje muyi wanka, kafin ta karaso".


Drivern Gidan Lema ya shigo gidan Zaid da misalain karfe 2:30 na rana.
Nene ta fito rik'e da Basket din Abinci a hannu.
Ta shiga Gidan da Sallama.
Tsaytsaye sukayi suna jiran shigowarta.
Idon Labiba ya kai kan Basket din hannun tsohuwar da ta shigo.
Sannu da zuwa ga Nene ga Nene.
Zaid ya karbi Basket din, Nene ta rungume Labiba.
"Yau ga ni ga Matar takwaran Zaidu bawan Allah".
Labiba ta durkusa ta gaidata.
Nene ta amsa cike da kulawa.
Har kan kujera ta jata suka zauna suka sake sabon gaisuwa.
Nene tace "Wallahi kina min kama da jikata Nasiba, don dai Seebi ta fiki dogon hanci".
Labiba ta murmusa tace "Allah Sarki".
Zaid yace "in ma so kike kice Seebinki tafi Matata kyau ba yarda zan ba, matata tafi kowa kyau".
Tace "Kai dai ka sani dan nema,".
Labiba tace "Nene muje kan table muci Abinci".
Nene tace "wallahi yunwa kau nikeji, da na gama Abincin ko ci banyi ba nayi wanka na taho".
Ta mik'e tsaye tace "takwaran zaidu bawan Allah dauko Baskyat din".
Kan dining suka nufa gaba ki daya.
Zaid yace "wannan Coolers din fa Nene, me ke ciki?".
Ta amsa daga hannunshi tace "Abinci na dafa mana muci mana, me ake zubawa dama a cikin cooller".
Da sauri ya kalli Labiba yace "ai ta miki abinci, kala kala ma, gasu nan kan table".
Nene tace "Too, daga kawoki shekaran jiya har kin fara sanwa? Wace amarya ke abinci a wannan lokaci".
Yace "sai da nagaya mata fa, tace sai tayi na tarban Nene".
Nene ta murmusa tace "Allah sarki, kuma gashi nima nayi Abinci, nace ma Aisha bari na dafa ma Matar takwaran Zaidu bawan Allah abinci, amma tunda kin dafa, ai sai ku aje ku dinga dumamawa kuna ci".


Da sauri Zaid yace "Aa mu dai ci yanzu dake".
Harara ta zabga mishi tace "wannan fa da na dafa, ya kake so nayi dashi?".


Yace "Amma kya ci abincin Amarya ko?"
Tace "ba zanci ba, nace ba zan ci ba".
Ta bubbude coolern ta dauki cokali ta dibo miyan kubewanta danye ta riko hannun Labee ta lasa mata tace "lasa kiji".
Labiba ta sa a baki.
Nene tace "tsakaninki da Allah abincinki ya kai nawa dadi?".
Labiba tayi daria tace "ina ma zaa hada? Ai ban taba jin miya mai dadin wannan ba".
Cikin dadi Nene ta tafa hannu tace "yauwa 'yar gari, shi mijinki da baa mishi gwaninta har ya fara yan surutai, nifa ba kowa nake ma abinci baa, amma ina ji dake shiyasa na dafa miki".
Labiba tace "aiko nagode sosai".


Labiba ta sauke Abincinta na kan table, ta daura na Nene, ta kai mata kitchen.
Zaid ya bi bayanta, yana cewa "kin gani ko? Na gaya miki, matar nan ba a iya mata, kinga ta wahalar min da ke".
Labiba ta harareshi tace "meye wahala? Chabda, nikam burgeni tayi, ba ta da bakunta".
Zaid yace "kyab, nenen zata miki bakunta? Shes full of wonders".
Tace "oya muje tana jira".
Suna fitowa suka ga har ta zuzuba musu a plate.
Tuwo ne miyan kubewa danye da yaji tantakwashi ga man shaniu na tashi.


Zaid yace "ni fa ba zan ci tuwo ba, abincin Matata zanci"
Nene tace "Alkuran ba zaka ci ba, ni na dafa maku abinci kace ba zakaci ba? Uban kutura yayi kadan".
Yace "wai ya Nene zakizo Gidana ki min iko".
Tace "a gaban Matarka zan lakada maka shegen duka, ka zauna ka ci tuwon nan, ko na danne ka na maka dure".
Baki ya bude, ya san zata iya, ya san zata aika, ya zumburo baki ya zauna.
Labiba ta dinga Daria.


Nan fa suka kwashi mulmula bibbiyu.
Nene tace "ahap sai gashi an cinye ana tande hannu, waya ce ma borno gabas take?".
Zaid yace "aidai an fi karfinmu ne".
Tace "kai Arr, bangaya ma ba sai ga 'yayan albarka Tero, haruna Eskaley da su Master sun kawo min abubuwan arziki, turmin Atamfa jiya da leshi da turarruka, da takalmi da mai da sabulun wanka da na wanki, wai na sanya a Albarka a sanaarsu".


Yace "kin manta ni na ka wo su? Kuma atamfa ne ba leshi, kuma ba kwanan na bane an kusa wata daya da yi, amma kina magana kamar jiya suka kawo".
Harara ta zabga mishi tace "ai dai sun fi wani da ko hakin ashana bai taba siyo man ba".
Yace "ba zai taba siya ba in jiranshi ake".
Tace "kai dai ka sani mak'on na mak'ok'o masu cin katako".
Yace "eh din naji".
Labiba ba abunda takeyi sai daria, ai kawai taji tana son Nene kuma ko kadan bata 6ata mata rai ba


Nene tace "Kinsan haka mijin Jikata Seebi yake da shegen feleken tsiya, don dai shi dunkum ne, be magana".
Labiba tace "Allah sarki, Katsina suke aure?".
Nene tace "Katsina? Haba, jikata na Landan, Ingila take aure, nima ai na taba zuwa".
Zaid ya ma Labiba ido alamun tsaya kiga ni.
Yace "mu fa an ishemu da wata Seebi, wai seebi na aure a London"
Nene tace "wallahi tana Landan, tambayi mamarka kaji,chan take aure".
Zaid yace "Mu dai ba mu yarda ba, yanzu haka tana Kano zaa raina mu ace tana London".
Nene tace "Wallahi aa London suke, tsaya ma ka ga hotonmu da naje muka dauka".
Ta mike ta koma parlorn don daukar wayarta.
Daria yake kasa kasa yace "so nake na k'uleta fa".
Labiba tayi daria chan k'asa tace ai na ga alama, na dagoka.


Nene ta dawo, har ta dauko wayar Ta nemo hotunan don ba inda bata shiga da Android Phone dinta. Ta nemo pictures din da suka dauka a chan zata nuna musu kenan.
Zaid yace "ai rana bata karya, a nuna mana mu ga Zahiri".
Nene ta tsaya, tana kallon Zaid, ya ma rainata, ita kuma harda biye mishi.
Zaid yace "In dagaske ne a nuna mana mana mu ga Seebi a London".
Nene tace "karya nake danuwarka".
Ya fashe da daria Labiba dai ta dan sha mur.
Nene tace "zanci ubanka takwaran Zaidu bawan Allah, zan gurza maka rashin mutunci".
Yace "Haba Neneta".
Ta harareshi tace "Gidanmu zani".
Labiba ta riketa tana kyaleshi Nene ai ba wurinshi kika zo ba.
Nene ta harareshi tace "Uziless (useless) muje daki mu barshi, mai tsamin jallabiya, Allah ya sa baka taho dashi ba dai nan".
Daria Zaid yayi yace "Naji, ya san ta k'ule, yau haka zaa karashe ranan da mitan Nene.


Har bayan Magrib Nene na gidan.
Sai chan aka zo daukarta.
Labiba ta je yi mata take away din gara.


Akayi akayi Nene ta tafi da Abincin da akayi dominta tace "sam ba zata dauka ba, kawai sai a ga na koma gida nikiniki da abinci, ba zan dauka ba to".
Zaid yace "haba Nene ta bata lokaci ta miki abinci ba ki ci ba, kika hanamu ci kuma sai kice ba zaki tafi dashi ba? Haka akeyi?".
Tace "wani ya sata? Iyayi, wace amarya ke abinci? Ba zan dauka ba wallahi".
Zaid yace "to wallahi nan gaba kika sake zuwa ko ruwa ba zamu baki ba".
Tace "naci ubanku kuwa daga kai har ita din".
Yace "haba Nene, kar ta jiki mana".
Tace "yo sai na kirata na fada a gabanta".
Yayi saurin cewa "yi hakuri, kina iyaawa.


Labiba ta shigo dauke da ledoji gara cincin da dubulan da alkaki cike da ledoji.
Nene tace "Thank you Thank you".
Ita Labiba taga Nene 'yar gayu tace bari ta burgeta irin da turancin nan tace "Nene mungode, we appreciate your visit, May God Bless you".


Nene tace "Keeee, ni zakiyi wa turanci? Baka gaya mata baa turanci a gabana ba? Ko zagar min uwa kikayi?".
Labiba tayi saurin girgizai kai a daburce tace "wallahi Aa, ba zaginki nayi ba".
Ganin hankalinta ya tashi ya sa Nene daria tace "ja'ira har ta tsure, to nasan ba zaki zageni ba, turancin ne banso, wanda ya man turanci gani nake kamar ya zagar min uwa".
Labibs ta murmusa tare da sakin ajiyar zucia.
Nene tace "To Thank You, Sorry, Byebye".
Ba ta jira cewarsu ba ta fada mota Driver ya jata.


Zaid ya rungumo Labiba yace "Yau dai kin ga Nene".
Naunauyar Ajiyar zuciya tayi tace "Yau naga Nene".
Yace "Haka fa take, ai Nene damuwa ce, yanzu zata kwance maka zani a kasuwa, kuma ta manta ma ta gurza ma".
Tace

Please Login or Register in order to submit comment