Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, shawara ce, ba don Labiba ba, don Lafiyarka, na san kana shayeshaye amma na furta maka kalmar so, which means ban damu ba”.


“Allah ne ya dora min sonka, to ya zanyi? Cizgeka zanyi a raina bayan Allah ne ya dasa min Sonka a raina? Ba fa zabina bane, in zabi na ne Makka zanje na So Sudaiz, so ina so ka san its Natural, Ina sonka saboda Allah, fissbilillahi wallahi, kafin na furta maka kalmar So, na san akwai k’alubale da yawa, da complications kala kala da zasuzo, akwai abubuwa da dama wanda na san Sonka zai ja min, i damned the consequences and chose to love you, so ka min adalci ka bar cewa bamu dace ba, ni da kai mun dace fa, ban cire rai zaka daina shan sigari ba, ka ceci unborn kids dinmu kar a dinga jefansu da maganganu marasa dadi saboda haka, so you need to change for good”.


“Labiba zaki iya aurena?”
“Toh zancen kake so, wai kai baka da android phone? Da kana dashi da video call zamuyi whenever you miss me, ba sai na sha wuyar zuwa ba kamar wata baraniya”.
Murmushi ya mata yace “tashi na raka ki Gida”.
Ba musu ta fito ya rakota tare da jaddada mai tana sonshi din, ya gasgata din,ya dawo zuciyarshi wasai tare da k’uddirtawa zai rage shan Sigari kuma ya bar shan world”.


Washegari Zaid ya tattara kudin Account dinshi Tas ya siyo Android phone ba don komai ba don ya dinga Chatting da Bibbs dinshi.
Aikam cikin kwana dayan nan sukayi wata irin Shak’uwa, son junansu suke sosai, har ya jirata ta dawo daga makaranta, ta tsaya Shagon Eskaley, suna faman yin selfie da wayarshi, ya na ganinta ya nufota yau ma shigar Yard akayi Ash wanda K’amshi ta dinka mishi
Labiba tace “wai hotuna akeyi da sabuwar waya? Inye, kayi kyau sosai wallahi naji dadi da na ganka haka”.
Yayi murmushi yace “naji dadi da kika ji dadi, nima zan dinga saka irin kayan nan don in miki kyau kiji dadi”
Tafi tayi cike da jin dadi
Yace “na san kin gaji ko? Muje Gida ki huta”.
Sallam sukayi da su Eskaley suka fara strolling, ba su damu da masu binsu da kallo ba, kawai son junansu suke ba su damu da kowa ba”.
***


Yana son kiranta amma bai da kudi, sabuwar waya na gun Tero da ya koma an so wayar ba ya nan, baya so kuma ya matsa mata kar ta ga kamar so yake tazo gunshi irin na jiya, shiga yayi cikin Gida ya bata lokaci wurin Dalo kafin ya dawo Daki. Yasmin ta kirashi wurin k’arfe 10:30 waya suka hau yi tana bashi labarin gajiar da tayi, sai wurin 11 suka aje wayan.
Mai ya kamata yayi? Baya jin bacci, fitowa yayi wajen daki, ya zauna kan dakalin gaban daki yana tunanin karon su da Labiba dazu kalar farinciki da ta sakashi, kai ya daga sama yana kallon kyawawan taurari.


“Fitsari ta fito? Ruwa ta fito Sha? Allahu Aalam, shidai kawai yaga Labiba ta tako har Gidansu ta zauna a kan Dakalin da yake zaune a kai tare da daga kai sama suna kallon sararin samaniya a tare.
“Suna da kyau” tace mishi cikin wani murya.
Yace “taurari? Suna da kyau sosai kam”
Wani irin dadi ke ratsasu yana shiga kowani sassa na jikinsu.
Idonshi ya murza ta girgiza kai tace “ka daina, ka daina murza idon nan” kallonta kawai yakeyi, kamar ya hadiyeta don So yace “Ina Sonki Bibbs”.


Cike da shagwaba tace “wannan Auntyn fa?” Zaid ya murmusa yace “ta koma Aiki”
Ta dan maido hankakinta gareshi ta “Son ka takeyi ko?”.
Dan jim yayi kafin yace “Yas ba matsala bace”.
Labiba ta turo baki tace “wace iri ce ita? Tana Sonka kuma take son ganin ta hadamu?”.
Murzan ido ya sakeyi yace “yin maganarta dake, ban mata adalci ba”.


Labiba ranta ya dan sosu ganin Antyn na da mahimmamci a rayuwanshi tace “Fine, ni son iyawanta ne bana so, tana acting kamar ta fi kowa Sonka a dunia, ga feleke da iyayi, shekaran jiyan nan da tace ta rakoka zance wurina kamar na mutu wallahi saboda da takiaci, kai ma ka fi ban takaici duk ka ban haushi da ka biyota wani zololo kai an rakoka zance, dont you have legs?”.


Ji yayi ta burgeshi Ainun yanda take magana cike da sanyi amma ita a ganinta ranta bace yake.
Zaid yace “Kishi kenan?”.
Baki ta turo tace “oho, nidai kar ta sake wani cewa ta rakoka Zance”.
Dariya yayi yace “Yes Ma”.


Kema wannan da yazo gunki rannan Sonki yakeyi, kuma har daria kike mishi, you look happy, harda murguda baki..
Daria tayi tace “Jayy dina kenan”
Hararta yayi yace “meye kuma Jay”.
Tayi daria tace “J for Jawad”.
Baki ya tabe “meye wani J? Aa H ne, you are so Unromantic”
Tayi daria tace “why are you like this?”.
Yace “point is i dont like him, kuma dagaske kar ya sake zuwa wurinki, kin dai ji ai mai su Terror suka ce miki jiya? Wallahi they will hurt him suka ganki dashi, and I cannot stop them, don ba ji zasuyi ba, so in ba so kike su karya mai k’afa ba, he should never come back again” ya fada yana dage kafada.


Harara ta zabga mai tace “kaga kai da mak’arabanka su fita daga hanyan mutane na? Poor Abu Sadeek tun ranar bai sake bari mun hadu ba, ina ta so mu hadu na bashi hakuri baya bari, kuma yayi blocking din chance din haduwar mu, bai ma zuwa School din sosai, ko yana zuwa wallahi nidai ban ganinshi”.
Dadi Zaid yaji ya tafa yace “weldone yaro yaji warning, so same thing will happen to that spoilt brat, dagaske kar ya sake zuwa”.


Dadi maganganun shi ke mata, ashe yana kishinta haka tace “nifa ka daina kora min samari”.
Ya hayyak’o yace “Labiba Ahmad i am dead serious, kar wanda ya sake zuwa wurinki, ke tawa ce nikadai”.
Kamar ta narke don jin dadi ta lumshe idanuwanta ta bude tace “I am dead serious Zaid Ali Zaki, ni taka ce, kai nake so har cikin raina”.
Cikin wani yanayi ya kalleta yace “har ranki?”..
Ta murmusa tace “Ehh, har chan cikin raina nike sonka”.
Yace “Ina Sonki Wallahi, ina Sonki nima”.
Tace “to dai Jawad kam ba matsala bane, abunda ya faru Cousin din Bestyta ce, kuma ni dama wallahi Girmanshi nake gani, and other days da muka samu sabanii, ji nayi zaman Katsina ya isheni, ni kawai i was desperate na yakiceka shiyasa nayi tunanin maybe i could give him a chance, and still babu wani abu da ya chanza game dashi, ina girmamashi, ina kuma ganin mutuncinsa, kuma dama ina da niyar gobe inshaAllah na gaya mishi ni kai nake so, yayi hakuri kar na bata mishi lokaci ya nemi wata yayi hakuri kam, so Mr Zaid kai kadai nake so, kuma ni na amince Ni taka ce”.


Zaid ya ji ta gama burgeshi matuk’a, wani girmanta ya sake girma a idonshi, she’s so matured ya Allah, wato ba ta iya cewa ranakun da ya mata wulakanci ba sai dai ta ce rannakun da suka samu sabani, gaskiarta na burgeshi, ya san tunda tace zata tsaida Jawad, zai ranste zata tsaida shi din don ya lura she is so honest and straight, ya san zata dakatar da Jawad din, ganin zata saka shi kuka saboda murna yace “Mallam kika sake kika min saving sunan as wani Z or kikace min Z sai na cijeki, wai J aa F”
Daria tayi sosai harta na rufewa don ta na tsoron kar ta yi harta ta tado masu bacci”
Tace “amma fa duk daya ne, sounds the same Z or Zaid duk daya ne”.
Yace “ke ni fa ba ABCD nace ki min ba”.
Tayi daria ta latso contact dinshi ta nuna mishi tace “daga ranar da nayi saving number dinka, har yau this is what it has been”.
‘SOULMATE’ ya gani barobaro a jikin Screen din wayar.


Lumshe idonshi yayi, ya dau seconds yana jin wannan yanayin kafin ya bude ido, k’aunarta na sake kunnuwa a zuciyarshi yace “Zaki kasheni da dadi, its late, tashi muje na rakaki, ki tafi daki, ga sauro duk ya cije mana kafafu?”.
Daria tayi tace “naji dadi da yau ba kai kadai ya ciza ba, gwara da suka hada dani, we are in this together”.
Daria yayi yace “Sannu Lover Girl, zaki gaya min wa ya koya miki Soyayya, wannan H dinne ko?”.
Daria tayi tace “heyy, ya kake bata ma saurayina suna, jay ne fa”.
Yace “Allah zan rankwasheki kika sake ce mai saurayinki, ni kadai ne saurayinki”.
Tace “heyy, you havent even asked me out yet”.
“Haha oh Oh, Labiba Ahmad Dakata will you be my Girlfriend?”.
Tace “Uhmmm sai nayi tunani”.
Ya hararega cike da kauna yace “Shutup and get up, muje ki shige daki”.
Batace komai ba ta mike, suna tafia cikin sando kar a ji su kamar barayi na shirin shiga sata
Sai kuma Zaid ya dan tsaya chak duk ya jin rashin dadin yanayinsu, juyowa tayi cikin muryar rada tace “yadai?”.


Shima cikin muryan radan yace “Ba sai kin sake zuwa Gidanmu ba daga yau, ni ne namijin, daga yau ni zan dinga biyoki Gidanku, but we are going to do it Legal, zan zo miki kamar ta yanda duk wani Namiji ke zuwa wurin abar sonshi, i will come through the gates not the walls, lets do it legally ko?”.
Kamar ta maidashi ciki don So tace “Lets do it legally”.
“I love you”
“I love you so much babe shiga ciki”.
Bata juyo ba ta shige daki, shima sai da ya ga ta shige daki ya koma nashi dakin yaga 1am har ta kusa yace “lallai lokaci na gudu in kana tare da masoyi”. Kan katifarshi ya haye yana tunanin Labibarsa.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa




[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA ASHIRIN DA SHIDDA 2⃣6⃣
(BAIKO 💍)


Da yake duk sun sa ma kansu abun, cikin kwanaki biyu su ka binciki Juna, akwai wani Mutum a Benin City, shi Abban Jawad ya tura ma Details kan Alhaji Ahmad Dakata yayi mishi background check kan family dinnan kuma ya samu gamsasshiyar Amsa.
Yace mishi Mutumin babban mutum ne datijo kuma bai da matsala, gidan shi Gidan Mutumci ne.


Haka nan Baban Amira ya binciko Asalin su Jawad a Unguwan Alkali, kasancewar Family dinsu ba boyayye bane, babu wani abun Assha da ya ji game da Family din, ya kira Mahaifinshi ya sanar dashi, baban yace "to Alhamdulilah, kace su turo".
To kafin ma Baban Amira ya kira Yayan Jawad yace mai su turo sai ko ga dan Halak din ya kira ya sanar dashi cewa "Akwai wani Uncle dinsu da yazo Abuja, zai koma ran Friday, to sauk'i suke so ba sai an tado kowa daga Katsina ba a tura su chan Edo neman Izini why not su tafi gobe Alhamis? Ba tare da an wahalar da mutanen katsina ba? Amma fa sai in ba matsala a wurinku be san ko its a short notice ba?".


"Bakomai" Yaya Muhammadu yace, zan gaya musu suyi shirin tarban ku Gobe in Allah ya kaimu, suka rabu a mutunce don yin shirin tafiar su kuma da tarban bakin.


Yaya Abdulhafiz ya gaya ma Abbansu yanda sukayi da Yayan Labiba, shi kuma Abban ya kira k'aninshi ya gaya mishi, k'anen yace bakomsi suna iya tafia gobe su dawo goben Friday sai ya dawo Katsinan.
Abba yace "akwai stress, bari na aiki Abdulmajeed naga ko zamu iya samun tickets to Edo"
A hakan suka rabu.


Yaya Muhammadu ya kira Gida ya musu bayani cewa gobe zasu zo saboda wasu dalilai, Babansu Labiba yace "haba bakomai su zo, ita kuma ka saka ranar kawo min ita Gida, tunda dai ga Miji, a bar karatun haka nan".
Mallam Muhammadu yace "InshaAllah baba, bari dai suzo muga yanda zaayi ba zai gagara ba InshaAllah". A hakan suka rabu.


WASHEGARI EDO STATE


Kamar yanda Abba ya tsara su 5 suka ya tafiar zuwa Edo Benin City, Abba, Daddy Usman, Yaya Abdulhafiz, Yaya Abdulmajeed da shi kanshi Jawad din, a cewar Abba gwara su ga wanda zasu ba diyarsu tun yanzu.
Tafiya ce mai nisa, sun iso Edo after 12, kamar yanda aka umurcesu, Dan Achaba suka tsayar su ka bashi adireshin gidan yayi gaba suka bishi a baya har kofar Gidan Alhaji Ahmad Dakata.


Yana a bakin Gate din Gidanshi tare da Manyan Yaranshi su 4, suka tarbesu cikin mutunci,
Sukayi ma juna Musabaha cike da farinciki kafin Alhaji Dakata ya ja hannun Alhaji Abu Shamsu har cikin Parlo suka zauna.
Bayan 'yan gaishe gaishe, aka ci abinci don sosai Alhaji Dakata ya sa aka musu Abinci har kala 3, sunci sun gyaste.
Alhaji Abu Shamsu ya gabatar da Daddy Usman a matsayin kaninshi kuma waliyi madaurin auren 'yayanshi.
Ya gaya mishi yana da mata biyu da yara 4 Abdulhafiz shine babban danshi sai mai bi mishi Abdulmajeed sai auta a mazamai neman diyarshi kuma Jawad, sai miemee yar shekara 3.


Alhaji Dakata yace "MashaAllahu, Allah ya raya mana zuria, nima dai Matana 2, ko waccen su na da 'yaya takwas, ni mai tarin zuria ne, Babban yaro na shi ne Labiba ke gunshi a Katsina, wannan sunanshi Hamza, sai wannan sunanshi Faruk, ga Aliyu wannan kuma mai sunan babana ne Lawal.
Da faraa suka sake gaisawa.
Daddy Usman Abba yace yayi magana.
"Alhamdulilah kamar yanda ka sani munzo ne don muga tushen Yarinya kuma mu nemi a ba dan wurinmu Izini ya dinga zuwa gunta su fahimci juna".


Alhaji Dakata ya murmusa yace "Mallam Jawad, kai ne ke son Diyata Labiba? Fada min naji daga bakinka".
Jawad ya dago kai ya sauke da sauri irin kwarjinin da mutumin ya mishi.
"Eh nine".
Alhaji dakata yace "ka shirya aure?".
Jawad ya kalli Babanshi kafin yace "eh na shirya".


Alhaji Dakata yace "to MashaAllah, abu yayi kyau, Itama nayi magana da Yayanta yace tana sonka tunda ta barka kazo gida wannan alamace ta yarinya na sonka din, nikuma gaskia a tsarin gidana, ban yarda ayi ta zuwa zancen nan ba, in aka ce yaro na son diyata, in na bincike yaro na binciki halinshi da asalinshi, sai in kirasu a daura aure, bana son bacin lokaci, amma naji dadi yanda ka kwaso min Iyalinka na gani, naji dadi wannan ya nuna halin girma, na amince da ku dari bisa dari, na ba danku Labiba, kuzo duk lokacin da kuka shirya ayi auren".


Alhaji Abu Shamsu ya murmusa yace "Alhamdulilah mun ji dadi sosai da karamci, amma so muke ka gaya mana cewa ga ranar da kake so muzo ayi maganar Aure, diya taka ce, magana ma takace".


Alhaji Dakata yace "wallahi bakomai, ni da kuka nuna kuna son nawa? Ko yaushe kuke so sai ayi, ku dai da kun shirya kuzo".


Alhaji Abu yace "dagaske Alhaji kafada, mu fa a shirye muke, ko yaushe ne, Mu ko yanzu kace a daura ai sai a daura".
Daria sukayi gabaki daya.


Alhaji Dakata yace "to shikenan, faduwa tazo daidai da zama, akwai yaruwar Labiba wato Samira, an saka ranarta, auren nata nan da kwana 45, in babu matsala, ina so in hadesu su biyu na aurars".


Alhaji Abu ya fadada fara'arshi yace "ba wani abu InshaAllah, mu da aka ma gata? hakan ma yayi, ba amfanin raba biki biyu a shekara, gwara kawai a hadesu".
Dadi kamar ya faso zuciyan Jawad jin shi zai yi niyyar aure nan da kasa da wata 2.


Daddy Usman yace "aikam bari in bada kudin neman Aure"
Ya ciro naira dubu dari a Aljihu ya kawo ma Alhaji Dakata har gabanshi.
Ya sa hannu ya karba, yace "naira dubu dari? Ai tayi yawa Alhaji Usman".
Daddy Usman yace "aa bata yi ba, bikin Autan Umma ne fa".
Alhaji dakata yace "aa gaskia tayi yawa, nifa aladar nan wai ta bada kudin neman aure da ina da yanda zani yi dana hanata"


Daddy Usman yace "haha, to tunda dai anayi, shikenan muma munyi".
Alhaji Dakata yace "wallahi sunyi yawa, amma abunda zanyi, na dauki dubu hamsin na neman auren, dubu hamsin na sadakinta".
Alhaju Abu Shamsu yace "shikenan an raba gardama".
Duk sukayi daria suna masu ganin mutuncin juna.


Da zasu tafi aka cika musu booth da Doya da Makani da jarkan Manja, suka rabu suna sambarka da junansu.
Bayan tafiyansu ya kira Mallam Muhammadu ya sanar dashi duk yanda sukayi. Baban Amira yace "hakan yayi Abbanmu, ina kasuwa sai anjima zan koma gida na sanar dasu yanda akayi, MashaAllah abu yayi kyau".


Gidansu ya kachame da Abbansu ya sa bikin Labiba rana daya dana Samira, 'yan uba kam ba su ji dadi ba, balle da labarin yazo muso cewa gidansu mai son auren Labiba mai kudi ke, duk surukan gidan babu mai kudinsu mijin Labiban, a da suna ta jin dadi Samira zatayi aure Labiba batayi ba, yanzu ko ransu ya baci jin ta samu Miji dan Babban gida kuma.
Mamin Labiba kam godia take ma Allah da zai nuna mata bikin Labibarta.


K A T S I N A


A Masallacin Anguwar yayi Sallahr La'asar, Mallam shehu ya tareshi a hanya yana tambayarshi.
"Wai ni Mallam Muhammadu wannan k'anwa taka ya ma sunanta?".
Baban Amira ya murmusa yace "Labiba Sunanta".
Mallam Shehu yace "ita fa, ni ina mamaki, meye hadinta da wannan yaro dan gidan Alhaji Zaki"
Baban Amira bai gane zancen ba yace "wai wa?
Yace "wannan yaro mana DanMakaho"
Da mamaki yace "DanMakaho kuma? Ita fa ko saninshi batayi ba, me ko zai hadssu?".
Mallam Shehu yace "ya zakace ko saninshi batayi ba bayan kullum sai na gansu tare, jiya da tsaye na gansu a shagon Eskaley kuma suka ketaro Anguwa tare, duk wands ya gansu ya san masoya ne, kuma sai da suka tsaya kofar Gidanka sukayi zance kafin ta shige gida".


Mamaki duk ya bayyana a fuskarshi yace "Anya dai? Ba dai Labiba ba".
Mallam Shehu yace "hmm, baka yarda ba ko? Ka dai bincika ka gani, dama nace in gaya ma ne don ka san yanda zakayi ka datse Alakara su tunda dai kowa ya san DanMakaho dan Shaye shayene kafin ta zubar maka da mutunci gwara ka katse ma hanzarinsu gudu".
Baban Amira ya ma rasa abunyi don shifa bai yarda ba, haka ya k'ama hanyar gida jiki a sanyaye.
****


Fitowar ta kenan daga Gida, ta ganshi tsaye ya rungume hannu a kirji kafarsa daya kan bangon gidansu.
Suna hada idanuwa suka murmusa ma Juna, kusan a tare suka ce “Kinyi kyau, kayi kyau”.
Sukayi daria a tare yace “ai ban kai ki ba”.
Tace “ka fini mana”
Yace “ya makaranta? Are you stressed out?”
Tace “i was, amma ganinka ya sa gajiar duk ta tafi”.
Ya dago kai da murmushinshi kafin yace wani abu ya Hango Mallam Muhammad na nufosu.
Ya dan tsorata yace “Shiga Gida Biebbs” da mamaki ta kalleshi tace “meyasa?” Murya k’asa k’asa yace “ga Yayanki nan”.
Ta dan waiga ta ga shi dinne, ko a jikinta don ma murmushi take mishi da ya zo gabansu ya kallesu daya bayan daya.
Labiba tace “Yaya sannu da zuwa”
Baban Amira yace “DanMakaho mai kakeyi a kofar gida na?”.
Zaid ya dan fara in ina yace “bakomai, dama wucewa zanyi”.


Labiba tayi karaf tace “Yaya wurina yazo”
Mallam Muhammadu ya kalleta da mamaki yace “wato maganganun da ake fada game da ke a anguwa”.
“Gaskia ne” Ba tare da ta san me yake nufi ba ta amsa shi.
Mallam Muhammadu yace “Labiba shiga Gida”.
Tace “To Yaya”
Ta kalli Zaid tace “Barin shiga ciki, sai munyi waya”.
Zaid sadda kanshi k’asa kawai yayi, wai ya ta ke haka? Ta ya take iya fadan abunda ke ranta ba tare da ta sakayawa ba? Ai a irin yanayin nan k’arya ya kamata tayi, ansan bata k’arya, amma dai yanda bata ji nauyin yayanta ba ya sa shi jin wani iri.
Yana jira yaji Yayanta yace wani abu amma bai ce ba illa ce mishi sai anjima da yayi.


Ya shiga Gida ya ga Labiba tsaye, kwala ma matarshi kira yayi.
“Asiya, Asiya”.
Sai ko gata ta fito da sauri jin kiran Mijin nata
“Wai dama kinsan Yaron nan DanMakaho na zuwa gurin Labiba?” Ido ta bude tace “wallahi ban sani ba, DanMakaho kuma? Wani irin dan Makaho? Tare ka gansu?”. Ta tambaya tana kallon Labiba.
Labiba tace “Yaya fa bata sani ba”.
Yace “yi min shiru”.
Aunty Aseey tace “dagaske ne? Ke ko me zakiyi dashi?”.
Baban Amira yace “bude kunnenki kiji, kar na sake ganinki da Yaronnan, kuma an sanya ranar aurenki da Jawad, sadakinki dubu hamsin na gun Baba, dazun sukaje neman aure Baba kuma ya amince musu, tunda ya ansa sadakinki”.


Labiba jin abun take kamar Almara tace “Yaya chabda, lallai kam”.
Yace “kin dauka wasa nike?” Kallonshi ta tsaya yi tana karantarshi, iyakar gaskia ta karanto a idanunshi.
“Yaya ta ya akayi bansan shiryshiryen nan ba?”
Yace “kinyi waya da Jawad jiya zuwa yau?”
Tunawa tayi rabon da suyi waya tun ran Tuesday, kuma messages dinshi a whatsapp suna chan tayi hanging.


Tace “Huh, Yaya har kai baka min maganar ba”.
Yace “tunda kika kawo minshi Gida magana ta k’are”.
Ko a jikinta tace “nikam ba a daura ba ai? To ku mayar mai da sadakinshi, nikam DanMakaho nike so, kuma ni shi zan aura”.
Ta shige ciki ta barsu da mamaki, barin ma Baban Amira, Labiba bata taba mishi rashin kunya ba, shekara 26 ya bata, amma yanzu ita take mishi rashin kunya akan Namiji? Namijin ma DanMakaho?.


Zuwa yayi yana kwankwansa mata amma ta ki bude dakin, ran baban Amira ya baci, ya shige daki.
Itama Labiba ranta a jagule ta kira Mamarta ringing daya ta dauka tace “Mami, dagaske an kawo sadakina? Dagaske bikina rana daya dana samira?”.
Mami tace “Eh Labiba, aikam mutanen Kirki”.
Labiba tace “Mami nifa ba zan aureshi ba, so daya yazo nan gidan, kawai suka zagaya suka ma Yaya Muhammadu magana shine ya turasu chan gun Baba”.


Mami tace “Labiba mai kike son cewa? DonAllah nidai ki rufa min Asiri, bakiji me ake ta cewa a cikin Gida ba”.
“Mami su fada abunda suke so, nikam ba zan auri Jawad ba, ina da wanda nake so”.
Mami tace “Labiba kiyi hakuri donAllah, kinsan babanki kaifi daya ne, ya amince musu, ki rufa min asiri”.
Labiba ta lura Maminta ba zata gane ba yanzu tace “Mami zan kiraki, ina zuwa” ta kashe wayarta.


Sukuku ta karashe ranar Alhamis, ba wandata ma magana har yaran yayanta, da daddare ta sha zancenta da Zaid a waya ba tare da ta damu da komai ba, don ba mai mata auren dole so wannan ba matsala bace, ta cigaba da harkan gabanta.


F R I D A Y.


Daddy Usman yazo musu Sallama, Doya da makani damanja Galan Biyu da suka samo jiya a Edo AbdulMajid ya saka mai a booth, yayi breakfast, sukayi dan fira da Yaran Yayanshi kafin yayan ya fito, sannan yayi sallama yace "bari ya tafi".
Gabaki daya Iyalan Alhaji Abu Shamsu suka rakoshi har bakin Mota suka mishi fatan Allah ya sa a isa lafia suna mai mai fatan Alheri.
Daddy Usman ya kama hanyar ta dikko dakin Kara.
***
Tsautsayi ne ya faru da Alhaji Usman a hanyarshi ta komawa Katsina, yana daf da shiga Katsina a Charanci yayi hadari inda Shanu suka gitta mai garin kauce musu ya bige wani Mutumi tare da fadawa wani kwalbatin da ya sa shi buguwa a kai.
Mutanen Anguwa suka kawo dauki, da aka duba sai aka wanda Alhaji Usman din ya bige ya cika don ko shurawa beyi ba.


Da yawa kan idonsu abun ya faru sun san cewa ba laifin Alhaji Usman bane, nan da nan yan garin suka taimaka suka kai Alhaji Usman Asibiti mafi kusa.
Wayarshi wani ya ciri ya cire sim din ya saka a wayarshi don wayar Alhaji Usman din akwai Pattern.


Duba contact list yayi yaga dai ba wani suna Mama ko Baba, sai yaga Contact din My Son.
Da sauri mutumin ya latso numbern.


A B U J A


Abdulmajeed cike da shagwaba yace "Yanzu kai shikenan Abba ka yarda Jawad ya rigani Aure?"
Mancy tace "to tunda baka da niya ba gwara ya yi overtaking dinka ba?".
Abdulmajeed yace "fa Mancy ba laifina bane, ko dazun sai da nace ma Ya Abdulhafiz yama Daddy Usman magana a hada bikin da nawa da na Jawad Abba ya hana, wai ba ya so ya shiga hakkin Daddy, kuma wai karatu takeyi sai ta gama ND1, afterall wallahi cireta ma zanyi daga Poly, Haba Polyn lafia".


Abban ya harareshi yayi saurin sadda kai, Umma tace "gaskia Abbansu da ka bari an hadasu, ai ba shiga Hakkin Aisha diyarka ce kaine waliiyyinta, in ka yanke hukunci kanta ba mai ce maka don me?".


Shiru Abban yayi kafin yace "shikenan, bari Usmanun ya isa zamuyi waya, sai mu ji in zaa iya hadesu".
Abdulmajeed ya gallawa Zaid harara yace "mallam sai ka bar mi gwalo hakan nan, inshaAllah ba zaka rigani aure ba".
Jawad yace "hahah aiko zaka sha madaran mamaki".
Sukayi daria baki daya.


Suna

Please Login or Register in order to submit comment