Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga yi ba, sai ga DAN MAKAHO kamar an jefo shi, bai ganeta ba daga nesa, sai da ya zo kusa ya ganeta, daga nesa yake hango dariyarta, kamar gudugudu ya karaso garesu kamar zai bugeta, da sauri tayi baya.


Abu Sideeq yace “Mallam Yadai?” Labiba tace “kar ka kulashi, kyaleshi Abu Sideeq, dan shaye shaye ne” DanMakaho bai damu da maganganun da ke fita daga bakin Labiba yace “Beebs, waye wannan?” Maimakon ta amsashi sai cewa tayi “Yanzu Abu Sideeq saura kwana nawa a fara Exams?”.


Abu Sideeq yace “less than 2 months fa” tace “wow ashe bamu da time sosai”. Su ka cigaba da firansu ba tare da kula DanMakaho ba, yanda Labiba ke daria ya fi k’ona ran Dan Makaho.


Yace “Beebs kice mai ya tafi please” Labiba ta ki cewa komai, Dan Makaho ya juya ga Abu Sideeq yce Mallam ka bar nan Unguwan nan yanzu” Abu Sideeq yace “Meyasa? Unguwar Babanku ne?” Labiba tace “Haba, nace kar ka kulashi kaima”.


Dan MAKAHO yace “Eh, kalli chan, ka ga sign an saka Ali Zaki Street ko? To Ali Zakin Babana ne, so ka bar Unguwar nan”. Abu Sideeq yce “kinga Labeey ki rabu da irin yan shaye shayen nan, haka zasuyi ta uttering nonesense in ana shiru ana kyalesu”.
Yace “to ka fitar dani in kana iyawa” Zaid yace “my Pleasure” Gefe ya matsa ya ciro wayarshi, suna kallon yana waya ba su tanka mai ba, ba su san da wa yayi waya ba, sai kawai su ka cigaba da firansu.


Cikin Mintunan da ba su kai 5 ba sai ga Yn Bencin Eskaley kusan su 9 a guje, kowanensu da makamin shi a hannu, masu Gora, sanduna, Wukkake, Zarto da wasu Makamai irin na ‘yan sara suka, ganinsu ya sa yan Unguwa rugawa, ganin wurinsu suka nufo Abu Sideeq da Labiba suka hada baki wurin Fadin “Inalillahi wa ina ilaihir rajiun”.




#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA SHA SHIDA1⃣6⃣
(Zumunci🤝)


Hannuwanta ta daura a kan k'ugunta cike da masifa tace "wai menene haka? Meyasa kake min haka DanMakaho? Dazun ka tozarta bak'o na, yanzu har kana da guts din threatening dina? Zaka sha Giya? Really DanMakaho? Zaka sha Giya? To ka sha mana, ai naga ba a cikin Littafina zaa rubuta maka zunubi ba ko? Sai abu na k'arshe, kar ka sake gigin shigo mana daki".


Sosai ya ke kallonta, ya sasauta murya yace "why are you doing this? Meyasa kike yin haka?".


Cikin dan daga murya tace "meyasa nake mene? Me na keyi?".


"Da bakinki ki ka ce kina So na, da bakinki kika ce ba tausayina kike ba, me ya faru? What happened?".


"Huh, da bakinka kace in Sonka nake na bari, baka bukatar a So ka".


Da sauri yace "amma ai ko da nace haka baki bar So na ba. Ko da na ce haka ai ba kiyi paying mind to it ba, baki damu da abunda nace ba, kawai kin cigaba da sona baki fasa abunda kike ba why now?".


Cikin Zafi tace "nagaji, na daina, ba zan iya ba kuma".


Shima cikin zafin yace "Uban wa yace ki fara dama? Ban sanki ba, kika nema na sanki, ki ka shiga rayuwata, ki ka kutsa sai da kika san labarina, ki ka sa na fara sabawa dake, kika min sabo dake, sai yanzu na saba da ke, zaki ce min wani kin gaji? Meyasa kika fara abunda kika san ba zaki jure ba? Uban wa yace ki shishige min, uban wa yace ki ce kina sona ba tausayina kike ba? Uwar wa yace ki min sabo da kanki in kin san akwai ranar da zaki toshe ni?".


Chan kuma yayi dan jim, kafin ya ja numfashi ya karya harshe cikin sanyi k’wayar idon shi a nata “look, i’m sorry i lost it, kin saka na daga miki murya, please, in ma wani abu na miki, kiyi hak’uri, we can sort it out, kinji”.


So biyu ta kyafta idanunta kafin tace “Haqqun, So Gaskia ne, bani na daura ma kaina Sonka ba fa? Allah ne, kuma shi zai yaye min, yana kan yaye min ma” ta juya da sauri ya sha gabanta yace “DonAllah kar ki bari, kar ki bar So na”.


Cike da fada tace “nikuma in Allah yayi dunia don Manzo”.
Da sauri ya sa hannu ya rufe mata baki yace “ba zaki bar so na ba, zaki cigaba da So na, zan ji dadi in kika cigaba da So na kinji,?”.


Takaici kamar ya kasheta, ba abun da ta ke son ji ba kenan, ba ta fito don ya ce mata kar ta bar sonshi ba, ina laifin ya bata hakuri yace “yana sonta shima, ko bai ce haka ba ina laifi yace “zan koya son ki? Ya dai nuna mata tana da mahimmanci a rayuwarshi, ko bata da shi ya nuna mata nan gaba zata iya zama mai mahimmanci a wurinshi, ba wai ya kalleta yace kar ta daina sonshi ba, ko kuma ta cigaba da sonshi, wato bata da wani amfani, ta cigaba da bibiyanshi yana jin dadi yana ya6a mata maganganu, abunda yayi kewa kenan, ko kadan be yi kewanta ba, bak’ak’en maganganun da yake gaya mata ita kuma bata zuciya yake missing.


Taku biyu tayi da baya da baya kafin ta juya, hannunta ya rik’o, tana juyowa ta kamtse shi da mari, kafin ta juya da sauri don komawa Gidansu, bai damu da Marinshi da tayi ba, sunanta ya fara kira.


“Biee, bieebs beeebs tsaya mana kiji”.
amma bata tsaya ba sai da ta shige dakinsu ta datso da karfi kafin ta sa hannu biyu ta rufe bakinta saboda wani kuka mai k’arfi da ya zo mata.
Cikin Bacci Aunty Aseey tace “Labs, kece?”.


Labiba ta saita kanta tace “Uhm,toilet naje”
Aunty Aseey bata tanka ba ta koma bacci, ita ko Labiba kuka take a hankali, zuciyarta na mata zafi, bata taba jin kwatankwacin abunda Dan Makaho ya sa ta ji ba, ba komai.


Mankas fa? Zaune yake kan dakali yana kallon hasken farin wata, me yace? Me yayi zafi? Me ya mata ne ta tsaneshi kwana biyu? Bibbs dinshi, to shi fa be san me yayi ba, and she’s not even talking balle ya san me yayi so wrong” da kyar ya samu ya shiga daki ya banki world dinshi kafin ya kwanta bacci.


Washegari
Da Misalin k’arfe 10 na safiyar ranar Litini, Wanka Zaid yayi kafin ya shiga Gida ya hada breakfast dinshi ya shiga dakin Dalo ya tambayeta in akwai wani damuwa, babu ta ce mishi, yace “ni yau ziyara zanje” dariys tayi tace “da ina da ina zaa?” Yace “yau ai sai inda mai ya k’are”.


Daga Dakin Dalo ya fita daga Gidan, daidai da fitowar Labiba daga na su gidan don yau Lectures din rana gareta. Ido cikin ido suka kalli juna, ita ta fara dauke ido kafin shima ya cire nashi, gaba tayi kafin ya rufa mata baya har ya cin mata ba tare da daya daga cikinsu ya ma danuwansa magana ba, kuma duk bakin titi suka nufa, ba su kula junansu ba, daga nesa zakayi tunanin jerawa sukayi amma wai nan fushi sukeyi da junansu. A bakin titi suka rabu inda Labiba ta hau Keke Napep, shi kuma ya tsaida Okada ya hau.


Tunda ta shiga Department take baza ido neman Abu Sideeq, wayarshi bata shiga, a daddafe tayi lectures, suka fito Aisha tace “ke wai ya? Duk baki da sukuni,Lafia?”.
“Hmm, Wallahi Besty jiya Abu Sideeq yazo Anguwarmu, kinsan ‘yan shaye shaye, suka tareshi suka mishi barazana, wai kar ya sake zuwa Anguwar, to tun jiya nake ta kiranshi na bashi hakuri sam wayar tashi bata shiga”.


Aisha tace “Ahh, lallai kila yayi zuciya” labiba tace “muje donAllah ki rakani Ajinsu”.
Suka fita tare.
Abu Sideeq bai zo ba, hankalin Labiba ya tashi, ko dai Mankas karya ya mata, sai da suka ma Abu Sideeq wani abu, aiko ranta ya baci, ga fargaba kuma.
A daddafe ta koma Gida.


Family House din Alhaji Zaki ya nufa, Gida ne da duk k’annen Alhaji Ali ke zaune saboda part part ne a gidan wanda Alhaji Alin ya gina ya mallaka ma k’anenshi.
Da sallama ya shiga Gidan Gidan Baba Sani ya fara Shiga, immediate din Babanshi, da yake baya aiki ya iskeshi, sosai ya gaida kawunshi, ya tambaya ‘yanuwanshi akace sun tafi makaranta. Baba Usman ya shigo yace “Ahh lale, mallam Zaidu ne a gidan namu” da faraa Zaidu ya gaida Baba Usman, Ya amsa, kusa da yayanshi ya zauna.

Baba Sani yace “Zaid ina Sadiya? Yaya take rayuwa a cikin Gidan nan?” Murmushi Zaid yayi, yace “Kawu ta nan lafiya, ya dai hanata fita,jiya na mishi maganar ya barta ta fara zuwa koyon sana’a ya k’iya”.


Kawu Usman ya girgiza kai yace “Allah ya isa tsakaninmu da Makirar Mace irin Hajia Shafa’atu, wannan mata ta cuce mu ta zalunce mu”.
Kawu Sani ya murmusa yace “Shi Allah fa baya bacci, wallahi koman nisan Jifa, k’asa zai duro, a dade anayi sai gaskia, ku dai muje zuwa”
Kawu Usman yace “kullum ina k’ara godewa Allah da ya sa Inna ba ta rayu ta shaida wannan kayan bak’in cikin ba, sai bayan ranta abubuwan nan ke faruwa, Yayanmu Gatanmu rana daya aka shiga tsakaninmu” ya karashe kamar zaiyi kuka.


Kawu Sani yace “wai Yaya Ali ace bai da mak’iya sama damu? Mu shak’ikanshi? Ace mune baya son gani, mune ya hana zuwa inda yake, bama Gidanshi ba, anguwan da yake ya mana iyaka? Hmmm”.


Charaf Baba Usman yace “ka tuna min lokacin da ya sa aka kullemu a police station wai don munje Gidanshi, Matarshi ta sa ya datse duk wata alak’a damu, babu zumunci, ‘ya’yanmu ba sa zumunci da ku, wannan Matar Allah ya tsine mata yanda ta shiga tsakaninku, ni tsorona kar Dalo tayi tunanin Dangin Ubanta sun yadasu”.


Zaid yace “Kuyi hakuri Kawu, ba wani abu ai Dalo ba yarinya bace, ta san an fi karfinku ne, ta san komai tunda ko nan da kofar gate din Gida an mata iyaka, kuma maganar zumunci ni zan dinga zuwa InshaAllahu ina sada zumunci da ku da ‘yanuwa na, mun san cewa baku yada mu ba”.


“Haka ne, Allah ya isar mana” kawu Usman ya amsa da Ameen.
Kawu Sani yace “Ya Hajia Maryam?” Zaid yayi murmushi yace “tana Abuja”. Yace madallah in kunyi waya ka gaisheta donAllah” Zaid yace “zataji”.
Hannu ya saka a Aljihu ya zaro kudi naira dubu biyu ya ajiye gaban Baba Sani yace “Kawu kwayi Cefane”.


Da sauri kawun ya ture kudin yana “Allah ya sauwak’e, Allah ya sauwak’e mu karbi kudinka Zaidu, muna k’annen mahaifinka bamu baka ba, bamu taimaka muku ba shine kai zaka bamu kudi?Aa sam, ko alama”.


Kawu Usman ya chafe yace “wallahi Zaid bamu da shi ne shiyasa bamu taimaka muku, to dama Yayan ne gatanmu shine k’arfinmu, to Shedaniya ta shiga tsakaninmu ta rabamu dashi, buga buga muke, da k’yar muke samo ma iyali Abincin da zasuci, wallahi shiyasa bamu tsinana ku da komai alhalin kune abun tausayi, donAllah kar ku ga kamar mun yardaku”.


Zaid ya gyara Zama yace “Ko Daya Kawu, ku ji da kanku, mu wallahi a wadatace muke, duk wata sai Mancy ta turo mana kudi, wallahi ba komai, haba kawu, mu duka victims ne, akwai ranar da Baba zaiyi kuka da idanunshi, zai durukusa gabanku ya rok’e Ku gafara kan abunda ya maku, yanda ya wulakanta zumunci Allah...” bai samu ya k’arasa ba sakamakon rufe mishi baki da Kawu Sani yayi.


“Kul Zaid,kul kar ka furta mugun Alkaba’i kan mahaifinka, wlh ba yin kanshi bane”


“Allah ka tsine mata, ka kwashe mata Albarka, kai dama bata da wani Albarka, Allah ka watsar da ita”. Cewar Kawu Usman.


Zaid dai ya juya kanshi karin ya mik’e tsaye yace “barin shiga gidansu Kawu Labaran”.
Karan Sigari Kawu ya hango a Aljihun gabanshi.


“Yanzu Zaidu baka bar Shan Sigarin ba? Har wannan tabar ta wiwi ba ka bar sha ba ko? Anya Zaidu” Shafa kai yayi cike da kunya yace “Na bari ban k’arawa” Kawu yace “karya kake, haka kace kwanaki da kazo” Zaid yace “InshaAllah zan bari, donAllah ku min Addua”. Cike da tausayi kawu Sani yace “Allah ya sa ka bari, Wallahi hayak’i mugun abu ne, na san illarta tunda nima gashi nan ina fama da ita, in na fara Tari kamar zan taro hak’ark’arina, kai ko da kuruciyarka, Allah ya shirya ka Zaid”.
Ameen ya amsa tare da fita da sauri.
Albarka suka sa mishi tare da daukan kudin da ya bari.


Haka Zaid ya zagaya duka gidajen K’annen Babanshi, suna sa musu Albarka shi da kanwanshi, kuma duk Gidan da ya Shiga sai an kwashe ma Shafa Albarka an tsine mata, da Alama kullum sai an tsine mata a gidan nan.
Sallama yayi dasu duka kafin ya kama hanyar Gidan Goggonshi Asabe daga nan zaije Gidan Goggo Ladidi.


Da Murna Goggo Asabe ta taryeshi, ta rasa mai zata bashi, kame kame kawai take, ita mijinta ba mai k’arfi bane, dama duk Alh Ali ne gatansu, tunda ya zame hannu kan lamarinsu duk suka tagayare, ina Shafa zata da duk hakk’in wadannan mutanen?.

“Kai Allah ka tsine ma Shafa’atu, dan Uwar Matar nan da Girman Ubangiji Allah sai ta wulakanta tun duniya kafin ta je Lahira, Matar nan bata tsoron Allah, k’iri k’iri ta juya mana kan Wanmu mai k’aunarmu? Ta rabamu da ku? Ba mu da halin zuwa ko da Anguwarku balle Gidanku? Allah ka isar mana” shidai Zaid yak’e kawai yakeyi, yau ya san baida labarin da zaiji da ya wuce tsinewa Aunty Shafa’atu” haka suka danyi fira ya bata naira dubu itama kafin ya hau Achaba zuwa Gidan Goggo Ladidi.


Sosai ta ji dadin Ganinshi, da ban hakuri ta fara na rashin kiransu a waya ta ji ya suke, kafin ta la’anci shafaatu.
“Hmm Zaidu, da Inna na nan da kila da bakincikin Mahaifinka zata koma ga Mahallicinta, duk da ba yin kanshi bane Allah ka ma Matar nan abunda ta mana, wai ni zanje gurin Yaya neman taimako kan ya ma Hajara Gado da Kujera lokacin da zatayi aure? Matar nan ta sa Yaya ya min Wulakanci, ya sa aka firdani kamar kayan wanki, tare da bige min warning kar na sake zuwa Anguwar? Aka sake gani nan sai na kwana police station? Ni Ladidi ciki uwa daya uba daya? Rannan na kwana kukan bak’inciki”.
Zaid ya bata hakuri, suka jajanta wa juna kafin ya mata ihsani yayi sallama.


Haka kurum yake jin dadi, ya sada zumunci, ya samu Albarkan Magabata.
“Uhhh, yau kunanshi ya dade yana jin tsinuwa da la’anta kalakala, its time for nishadi”. Ya murmusa tare da tsaida Okada yace “ka kaini Layout Gidan Habibu Lema”.


Wayarta ya kira, sai da ya matsa da wayar gefen kunenshi saboda hargowarta wurin kiran “Helllo” idonshi ya juya yace “Nene, ina k’ofar Gidanku” “to to gani nan fitowa”.


Ba jimawa sai gata kuwa “Takwaran Zaidu bawan Allah” ya gaisheta ta amsa, tace “uban me ya sami idonka naga sun kara k’ank’ancewa?” Murza na hagun yayi ta sa hannu ta daka mai duka.
“Wai ba nace bana so kana taba idon nan ba?”
“Nene wai sai yaushe zaki bar dukana?”.
“Sai randa ka bar shan wall yake ko uban wa?”.
Yace “World”.
“Oho, ina ruwana da shi tunda ba sha nike ba? Meyasa me ka ne? Kayi bacci kau jiya? Ko baka lafia? Ka kara bak’i ka sake kazancewa”
“Kai Nene banson Wulakanci”.


Dan shiru yayi kafin ya gyara tsayuwanshi yace “Nene, akwai wata makwabciyarmu”
Charaf tayi tace “Son ta kake?”
Da sauri ya girgiza kai yace “AA ita ke Sona fa, ita fa ta furta min So, gatsau fa tace min Sonka nake, dagaske nake sonka, can you imagine”
Nene ta bishi da wani kallo raini ta na mai bura hanci tace “to sai me? Nace sai me? So nawa akayi? Allah ya ji k’an Mamman, da bakina nace mishi yana burgeni, kuma na gaya ma Mahaifina, Babana ya samu Babanshi yace ya ba Mamman ni, har ya mutu yana gode ma Babana”.


Zaid da mamaki yace “Nene kece kika kai kanki wurin Namiji?”
Tace “kai Arr yi man shiru, in son Labarin kake ka zo na baka, amma yanzu gaya man kana sonta?”
Yace “kawai na damu da ita ne, haushi na takeji, banson ko ta bar so na ba”.
Nene tace “to me zai dameka in ta bar sonka? Ai ba sonta kake ba ko?”.
Da sauri yace “aa ai na saba da ita ne”.
Nene ta buga tsoki tace “kai Gele, sonta kake, ko ka furta mata So, ko ka rasata gabaki daya, kai ni nagaji da tsayuwa, sai munyi waya tunda baka shigowa”.


Shigewa zatayi ta barshi tsaye baki a bude, “Nene wai meye haka? Ke da nazo wurinki muyi fira?” “Nagaji nace,gashi warin sigari kake, amai nikeji” ta shige ciki yace “lallai tsohuwarnan ta ci uwar rainin wayau” daga ciki ta bude murya yanda zaiji tace “Uwarka”.


Tsaki yayi ya banka ma Gate din harara kamar ita yake harara, hakan bai sa yayi nadamar zuwa gurin Nenen ba, don sosai yake son tsohuwar.
Bakin titi ya tsaya don samun abun hawan da zai maidashi gida Laasar ta kusa.


Ta fito da buta kenan ta tsugunna don yin Alwalar Sallahr Laasar. Ta ganshi tsaye yana waya, so daya ta kalleshi ta cigaba da alwalarta.
Shima wayarshi ya cigaba yana mai kallon Gidan Mallam Muhammad.
Ji yayi an rufe mishi ido ta baya.
Hannu ya sa ya daura kan hannun da aka rufe mai fuska.
Laushin hannun tabbas mace ce K’amshin turarenta ya ziyarci hancinshi, k’wak’walarshi tuni ta gaya mishi ko wacece, shakka babu itace, ita kadai ya sani wacce zata iya mishi wannan abun.


Labiba na dagowa ta ga abunda ya sa ta sake butan hannunta, jikinta rawa yake kamar mazari, wata ce ta sa hannayenta ta rufe ma Zaidunta Ido, haushi ya bata da beyi yunkurin janye jikinshi ba, to ko ya zata Dalo ce? Ranta ne ya sosu ganin wani murmushin da bata taba gani ba gurin Zaid, bude hanayensu yayi tare da juyawa ga yarinyar.


Lumshe idanuwanshi yayi ya bude, sosai suke sakar ma junansu murmushi mai k’ayatarwa.
A hankali ya furta sunanta “YESMIN”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


Babi na Sha Biyar1⃣5⃣
(KE TAWA CE😍)


Kafin su idasa k'arasowa gunsu tuni ta sha gaban Abu Sideeq, ta kare shi da hanayenta, tuni su Master suka zagaye su.


Mankas da isa da tak'ama yace "ki shiga Ciki, ko in sa suyi gunduwa gunduwa da namanshi".


Hankalinta a tashe ta kalli su Master tace " donAllah kar ku mishi komai".


Tsawa Zaid ya daka mata yace "ki shiga Gida ki rufe k'ofar kar ki tsaya ko ina sai daki".


Tsoro sosai Zaid ya bata, ba ta san wannan Zaidun ba, wannan ba shine Zaid din da fara So ba, wannan ba Dan Makahonta ban, wannan wani ne daban, wannan shine MANKAS.


Da sauri ta juya ta shige cikin Gidan gudun ta tsaya gardama su ma Abu Sideeq wani abu, ba za ta iya dauka ba in har wani abu ya samu Abu Sideeq ba, bata san mai zatayi ba.


Abu Sideeq ido ya raina fata, jikinshi sai rawa yake, Zaid ya kalleshi cike da tasha yace "yan shaye-shaye ko? Uwar meke faruwa in ba a kula su ba? Kace me?" Shi dai Abu Sideeq ba bakin magana.
Zaid ya matso kusa dashi ya sausauta murya.
"Beebs Yarinyata ce, Beebs Tawa ce, kar ka sake zuwa inda take, wallahi ka sake zuwa Unguwar nan, hmmm, zan gwada maka Tudun Matawalle na Mankass ne".


Wuce su yayi tare da ma Master inkiya da su rabu dashi, Gidansu ya wuce ba tare da damuwan mutanen da ke kallonsu ba, afin kace wani abu Haruna ya finciko Abu Sideeq ya bashi mari kala Uku, ya gwada shi da hannunshi "kar ka sake taka k'afarka cikin Unguwar nan kanaji?" Abu Sideeq ya gyada kai da sauri.


Hannu Haruna ya sa cikin Aljihun Abu Sideeq ya zaro ya ciro kudin da ke cikin Aljihun dubu-dubu guda 7, Haruna da jajjayen hak'oranshi yace "mu raba? In dau 3 in baka 4?" Kafin Abu Sideeq yayi magana Master yace "dan uwarka mu fa?" Haruna yace "to kai Ware" da sauri Abu Sideeq ya hau Abun hawanshi ya burka ya bar unguwar a sittin.


Terror ya kalli Unguwar, cike tap kamar kallonsu suke kamar ana shooting film, yace "duk ku ware, ko in sareku magulmata" da sauri kowa ya dare suka bar wurin. Su ko suka wuce bencin Eskaley da murnan sun samu kudin siyan World.


Hannunta rawa yake tayi, safa da marwa take tayi, Aunty Aseey na toilet, hankalinta ya gaza kwanciya sai da ta lek'a ta k'ofa ta ga ba kowa wurin sai tsiraran mutane, ba su Mankas, gabanta ya tsananta bugu.


Chan sai gashi ta hango shigowarshi BQ, wurin ta tsura ma ido hawaye na neman kufce mata, shima tsayawa yayi yana kallonta idonshi cike da wasu abubuwa, wani abu yake ji game da ita da yake fizgarshi, dagaske yakeyi da yace "ita tashi ce, bai san ta yaya zata zama tashi ba, amma tabbas ita tashi ce shi kadai, dama kwanaki kadan ya rage mishi a duniya, zai kasance tare da ita kafin ranar rabuwarsu tazo, kafin tazo, in dai yana lumfashi, babu mamijin da ya isa ya zo kusa da Labs, ko tana so ko ba ta so, zai iya saran duk wani namijin da zai rab'i Beebs dinshi.


Wayarshi ya zaro ya tura mata text, tana kallonshi, yana kallonta ta bude message din.
"Saurayinki is fine, ya tafi Unharmed, ki gaya mishi, kar ya sake zuwa Inda kike, ke TAWA ce Beebs, You Are Mine alone, kin fahimta?".


Ba ta san wani sanyi na ratsata ba, sai da taji wani yanayi na neman rufeta, ba za ta so ya ga reaction dinta ba, kallonshi tayi ta galla mishi harara tare da buga wani tsaki ta shige daki.
Tana shiga ta fara latsar wayar Abu Sideeq amma wayar a kashe, duk ta damu, amma hankalinta ya dan kwanta da Mankas yace mata ya koma Gida ba tare da sun mishi komai ba.


Tsaye yayi ya bi bayanta da kallo tare da murzan idonshi ya wuce Cikin Gida.


"Kai Dan Makaho, mai nake ji ne a cikin Unguwa? Fada kayi da wani a kan Mace?" Mankas ya kalli Babanshi da ya shigo yana huci, be kula shi ba ya shiga kitchen don dafa indomie, sai kuma ya fasa, ya bude k'ofar dakin Dalo, ya ganta zaune jigum, murmushi ya mata tare da kashe mata ido daya, murmushi ta mishi, ya rufe mata k'ofa.


Baba da Aunty Shafa’atu na tsaye inda ya barsu, yazo zai wuce “Baba yace Don uwarka ba magana nake maka ba? Wallahi Zaid in ka nemo magana kar a sake a tunkareni a matsayina na Ubanka, duk wanda ya kawo min kararka zance kai ba dana bane a tafi da kai chan Police Station, shege har ka san yanda ake fada kan Mace”.


Wucewa yayi yaji Shafa’atu na cewa “ni tsorona Alhaji kar yayi ma Diyar Mutane Ciki, ka san halinshi” daga waje inda yake ya bude murya don ya tabbatar zata ji yace “Uwarki Zan Ma Ciki”.


Ihu Shafa ta sake, Alhaji ya bi bayan Zaid wai zai bigeshi yana tsinanshi amma ko a jikin Zaid ya buda daki ya shige ya rufe k’ofar a fuskar Alhaji Zaki.
Nan kamar an kunna shi ya hau bambamin Fada “Allah ya tsine maka Zaid, Allah ya k’untata maka yanda kake k’untata min da matata”.


A sukwane Labiba da Aunty Asee suka fito daga Daki, tsinuwar da yake mishi ba dadin ji, Aunty Aseey bata ankara ba, sai ganin Labiba tayi harta k’etara Gidansu Zaid”.


Da k’arfi Aunty Aseey tace “Uhm uhm Labiba”. Amma Labiba tuni tana gaban Baban Zaid da tunda ya ga Aunty Aseey ya ji wani irin mugun Kunya.


“Ina Wuni?” Alhaji Ali ya amsa mata da “lafiya lau” tace “Baba, sunana Labiba, ba ka san Bakin Iyaye halaka ne ga yaransu ba? Ka san tsinuwan Mahaifi ga yaro ba zai taba sa yaro ya dace a rayuwa ba? Shin baka san mugun alkaba’i na janyo halaka ga mutum balle dan da ka haifa? Shin baka son Yara amanar Allah ne a wurin Uwayensu ba? kuma tabbas Allah zai tambaye ka yaya ka yi kiwonsu, in rai ya baci hankali ke nemoshi. Magana mai dadi sadaka ce, in yau Zaid ya maka ba daidai ba, ka zaunar dashi kace “Zaidu Eh, ka min ka za kamin kaza ban so, don Allah ka bari” wallahi zai

Please Login or Register in order to submit comment