Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka rashin Sallah har gari ya waye”.
Idonshi na hagu ya sake murzawa kafin yace “barin shiga ciki”.
Labiba ya kalla wacce tayi saurin kauda idonta kafin ya juya ya shige dakinshi.
Mallam Muhammadu cike da tausayawa ya girgiza kai ya cigaba da sharanshi.
Aunty Aseey ta shige kitchen don cigaba da hada kalaci.
Ita kuma Labiba ta shige daki don shirya Sabit.


Ko da ya shiga Daki, toilet ya wuce direct yayi wanka kafin ya doro Alwala, yazo yayi Sallah rakaa biyu kafin ya zauna a kan kujera yana tunanin Labiba.
Ta tsaneshi har haka?
Har yace mata zai kwana a waje ta ki furta mishi kalma mai dadi?
Dagaske ta bar son shi?
To ko daman ba son shi din takeyi ba tausayinshi take?
“Ba tausayinka nake ba, sonka nake, sosai nake son ka”
Kalamanta ne suka dawo mishi kamar a lokacin take ambaton su a lokacin da yake tambayarta in tausayinshi take.
To ko dai ta sadak’as ne? Son da yake mata ba zai saka ta dole ba, ba zai tilasta mata wurin dawo da son shi a zuciyarta ba, tunani fiye da dubu a kanshi ya rasa abun yi.


Tunda ta shiga daki, take tunani, hankalinta baya wurin shafa man da take yi a jikin Sabit.
“A waje ya kwana?”
Don me zai kwana a waje? Baida hankali ne? Yanzu in malaria ta kamashi fa? Akan me zai kwana waje? Akan me? Ya burgeta ya kuntata ma kanshi a kan me? Oh Allah, ya zatayi? Dagaske ya fara sonta?”.


Muryar Amira taji inda ta ke cemata “Aunty Labs, kina lafta ma Sabit mai a jiki” da sauri hankalinta ya dawo jikin Sabit da aka kusa kwashe rabin roban Vaseline a jikinshi”
“Ya Rabb” kawai ta iya cewa.


A B U J A


Suna Zaune gabaki daya kan Dining Table suna breakfast Umma ke cema Babansu “Abba wai kasan Jawad Zance yaje Katsina ranar Asabar?”.
Jawad ya ma Umma wani kallon “haba Umma ya zakiyi irin maganar nan a gabana”.
Dariya tayi ta maida hankalinta gurin Abbansu
Abba ko yace “Lallai Autan Umma an girma, har ana zuwa Zance wani gari?”.
Murmushi Mancy tayi tace “ai Ya isa Aure, sai a mishi”.
Abdulmajeed yace “to wai kana nufin Overtaking dina zakayi ne?”
Mancy tace “ai gwara yayi tunda kai ka tsaya wasa”.
Abdulmajeed yayi dariya yace “kai Mancy”.
Abba yace “to ya sukace gidansu Yarinyan?”.
Jawad yace “Abba haka yayanta yace in tura manya na aje neman izinin chan Edo State”.


Abba ya aje kofin Shayinshi yace “Edo state kuma?”.
Da sauri Umma tace “Aiki ya kai babansu chan shine suke zama har yayi retire, yarinyar ma chan aka haifeta, amma yan arewa ne”.


Abba yace “kuma kana sonta?” Ba tare da ya kalleshi ba Jawad yace “Eh Abba”.
“Ya sunan Babanta?”
“Alhaji Ahmad Dakata”.
“Cikin garin Edo?”
Jawad yayi jim yace “bansani ba Abba, sai na tambayeta”.
Abba yace “Aa ba maganarta bane, kace ta hadaka da Yayanta, sai ka hadasu da Yayanku suyi magana, yayanku should report to me, ko ya kira Baba Usman dinku suyi magana”.
A ladabce yace “To Abba”
Mimi da ke wasa da dankali a baki tace “Abba nima ka min Aure”.
Dariya suka saka baki daya.


Yasmin ta fito sanye da doguwar riga mai kama da ‘yar kanti ta wuce dakin Zaid, daidai da fitowar Labiba rik’e da jakka da alamu Makaranta zata, Labiba tayi saurin dauke kai ta shiga dakin Aunty Asee don mata sallama, murmushi Yasmin tayi ta shige dakin Zaid.
Zaune ta ganshi cikin yanayi.


Da sauri ta karasa gunshi tana tambayarshi “Lafiya Zaid?”
Hanayenshi ya nuna mata ta bi hannun da kallo.
“Wani abu kamar cizon sauro”
Murmushin takaici yayi yace “ba kama bane, cizon sauron ne”.
Yasmin na bin duk ilahirin jikinshi da kallo tace “to me ya faru? Ji fa yanda suka cijeka har fuska, garin yaya? Bakayi fleeting bane? Ko maganin sauron nan da kake kunawa ya k’are ne? Ji fa kamar ka kwana a kwata, chabda har saman goshi”.
“Beebs ce, Labiba ce”.
“Meya sameta Zaid?”
Kamar zaiyi kuka ya kwashe komai ya gaya mata.
Yasmin ranta ya baci tace “saboda bata gaya maka magana mai dadi ba ka kwana a waje? Ji ciwon sauro a jikinka sunfi dari, ji yanda suka ma ja da fata, sun sha jininka, Zaid Malaria ta kamaka already, kuma kasan da wani abu yayi triggering ciwonka it will only worsen, Zaid what were you thinking? You had to prove that to her? Oh Allah, ba zan ga laifinka ba don So ne, So banzan abu ne, it makes us do stupid things, nikam tashi muje Asibiti, mu fara treating Malaria tun kafin ta mana mummunan Kamu”.


Ganin yanda ta tashi hankinta ne ya sa shi nadamar gaya mata dabara ta fado mai yace “Na sha Anti Malaria fa” tace “wanne?”yace “ACT” ina kwalin?” Yace “baki yarda dani bane?”.
Kafin tace wani abu ta hango Labiba ta window zata fita Gida.
Da sauri tace “Ina Zuwa”
Yace “Ina Zakije?”
Ta fara yafiya tace “ka jirani yanzu zan dawo”.
Da sauri ta koma cikin Gida ta dauko Wayarta da Key ta fita.
Sauri sauri gudu gudu ta karasa inda motarta take cewa “kai bude min gate”
Yau zaayi ta ta k’are ni da Labiba, makarantar zan kaita.
Bude gate akayi ta kunna motar ta fita da saurinta.
Labiba kuwa tafiya takeyi da sauri don bata so ta makara, yau 9 zatayi lectures gashi 8:30 ta yi, kafin taje School 9 tayi k’ila ta wuce, a zuciyarta take fatan akwai bus da taje zata tashi kar kuma ayi tsaye tsaye direct ta samu har batagarawa.
Bata kai ga isa shagon Eskaley ba Motar Yasmin ya sha gabanta.


Da mamaki ta kalleta.
Yasmin ta zage Window tace “Shigo”
Labiba tace “Makaranta Zanje fa”.
Yasmin tace “Hassan Usman Polytechnic Department of Animal Health and Production Technology, chan nayi nima”.
Labiba tayi jim, kaafin ta zagaya ta bude gaba ta zauna.
Wani irin sansanyan k’amshi taji ya bugi hancinta, k’amshin motar ya hade da k’amshin jikinta, zata iya bambance na motar da kuma na jikinta, don zata rantse ta ji kamshinta daga inda take dazu a gida da suka hadu, lallai kam wannan ‘yar kamshi ce, da Ita da Zuciyarta kawai suke wannan firar.


Yasmin ta gyara kan sitiyari ta fita daga Unguwan tana juya sitiyari cike da k’warewa.


Labiba ta fara shawara da zuciyarta chan ta yanke shawaran gaisheta tace “Ina kwana Aunty”.
Yasmin ta maida hankalinta ga Titi ba tare da ta kalleta ba tace “Lafiya lau”.
Ba wanda ya sake magana.
Yasmin shatata gudu takeyi cikin minti da bai wuce 10 ba tana gaban K’ofar Batagarawa, mai makon ta shiga School din sai tayi parking gaban Gate din.
Labiba ta kalleta da dan murmushi a fuskanta tace “Nagode” ta sa hannu zata bude k’ofar ta fita taji Yasmin ta danna Lock kofar ta datse ta ki buduwa.


Labiba ta kalleta da mamaki tana jiran bayani.
Yasmin fuska ba annuri tace “karfe nawa kike da lectures?”
Labiba tace “karfe 9”
Yasmin ta kai idonta ga agogon motarta tace “muna da sauran Minti 11, i will make it fast, Labiba, kin san cewa Zaid waje ya kwana Jiya?”.
Labiba ta dan kau da kai kafin tace “ni ban sani ba”.
Yasmin tace “Oh baki sani ba? To bari na gaya miki, Zaid waje ya kwana, a daren jiya ya furta miki Kalaman da na dade inaso na ji daga bakinshi, a daren jiya ya tona asirin zuciyanshi da na dau shekaru ina son ji daga bakinshi, a daren jiya ya furta miki abunda bai taba furta min ba, ya buk’aci ki ce mishi ko da ‘thank you’ ne amma kin faskara, ya rok’i ki gaya mishi magana mai dadi amma sai kika jefe kalamanshi da kalmar Yaudara”.


“Zaid bai cire rai ba, ya miki barazanar kwana waje in baki mishi magana mai dadi ba amma ko a jikinki, to ashe ba barazana bace ba, Kwanan yayi a waje, mosquitoes kuwa suka samu Abincin Dinner suka far mai, jikinshi yau ba ma tsaka tsinke duk cizon sauro ne wanda ina da tabbaci malaria ya kamashi lokaci kadan zai kwanta ciwo, ke ce sanadi kuma, kuma Wallahi wani abu ya samu Zaid, ba zan yafe miki ba”.


Labiba tace “kema son shi kike ai, to meyasa kike son ganin kin hadamu?”.
Yasmin tayi murmushi mai ciwo tace “ba ruwanki, na gaya miki kar kiyi Kishi dani, ni ba damuwanki bace, as long as kina zuciyarshi, to sai nayi yanda nayi ya sameki”.
“Zaid na Sonki sosai, yana matuk’ar kaunarki, in har kikayi amfani da son da yake miki wurin wahalar da zuciyarshi, baki yi wa SO adalci ba, ba ki chanchanci ki furta kalmar SO ba”.


Labiba ta turo baki tace “nifa ba sona yakeyi ba, haka kawai yake cewa yana sona, kema kin yarda dashi, haushi fa kawai yakeji don yana ganina da wasu”.


Cike da takaici Yasmin tayi tsaki, ji take kamar ta rufe labiba da duka.


Wayarta ta ciro ta danyi latse latse kafin ta daga wayar sama.
Labiba ta ji muryan Yasmin na fitowa daga jikin wayar da alama recording ne tayi playing inda taji muryan Zaid na cewa;


“Ki tambayeni Yas, tambayeni".
Taji muryan Yasmin din na cewa “Ina son sani, kana son Labiba ko ba ka sonta?".
"INA SONTA".


Labiba ta fara kaita bango a kausashe yace “ki bi a hankali Labiba, shawara nake baki yanzu, kuma dai lallabaki nakeyi, ina da halin maida Zaid nawa nikadai, amma ba zanyi ba saboda yana Sonki, bana so inyi Son kai, i dont want to be selfish, in har kika bari na sa Selfishness a cikin lamarin nan, Labiba in har ki ka bari na zabi kaina akan kowa, wallahi Zaid ba zai sake kallonki ba, Zaid ba zai sake bi ta kanki ba, ko iskar da ya deboki Zaid ba zai sake kallo ba, Zaid zai zama nawa, nikadai in har kika kaini bango Labiba, Fitar min a mota”.


A sukwane ta bude k’ofar ta fita, yanayin Yasmin ya bata tsoro, da sauri ta fara tafiya tana yi tana waigen Yasmin, Yasmin ta bude wuta ta yi wani irin reverse ta hau kan Titi, Labiba tsoro ya kamata, ganin yanda ta bude wuta a fili tace “Allah ya tsare” wani irin So Yasmin take ma Zaid da har zata sadaukar da kai haka ta nema mishi abunda yake so? Lallai in itace wallahi saidai ya mutu, in be sonta ba zata taba hadashi da wacce yake so ba.


Shiru tayi kafin Zuciyarta ya tambayeta tambayar da take son amsarta “Amma dagaske Zaid din na Sonta? Muryarshi ta tuna Radam ta wayar Yasmin inda yace “INA SONTA” zata rantse gaskia ya fada, ba zai ma wacce ta tambayeshi karya ba, ta aminta da kalamanshi, zuciyarta tayi naam dashi”.
Ta dafe saitin Zuciyar tace “Ina Sonka Zaid, Wallahi ina Sonka”.




#1love
#DM
%anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN DA BIYAR 2⃣5⃣
(SON SO ❤💖)


Tana shiga aji ta zauna, Besty bata kai ga zuwa ba, wayarta ta cire a jakka ta latso numbern Aishar, ringing biyu ta dauka "Hello Besty kina ina ne?" Daga bangaren Aishar tace "muna first gate gani nan karasowa.
Ta window Labiba ta hango Mallam na nufowa Ajinsu, daidai da rurin wayarta, ta duba ta ga Jay ne, ga kuma Mallam nan zuwa, ta san in bata dauka yanzu ba, ba zai damu da tana Lectures ba zai ta kwala mata kira, dauka tayi tare da sa kai kan desk.


"Hello Jay, Goodmorning".
Jawad daga bangarenshi yace "GoodMorning Baby, ya kike? Bacci kike halan?".
Labiba tace "Jay, yau Monday ka manta ne? Gani nan cikin Aji, ga ma Lecturer dinnan ya shigo, zan kiraka in na fito"
"Okay okay donAllah yi min sending Numbern Yaya Muhammadu, yanzu donAllah, kafin a fara lectures din".
Labiba bata son jan magana, ga Lecturer ya shigo ajin, ya fara cewa a shirya ya sa tace "Okay" tare da datse kiran.


Labiba ta tura ma Jawad numbern Baban Amira daidai da shigowar Aisha ta shigo class din da sauri ta ma kanta mazauni kusa da labs tare da tsunkulinta, gira Labiba ta daga mata tare da maida hankalinta gurin Lecturer da ke bayani.


A B U J A


Jawad kamar zazzabi tuni ya ma Office din yayanshi diran mikiya.
Bayan Secretary ya mishi Iso Jawad ya shiga farfajian offishin yayanshi suka gaisa.
Yaya Abdulhafiz yace "yadai autan Umma?"
Jawad yace "Yaya dazun ne Abba yace na baka numbern Yayan Labiba ka kirashi shine na amso numbernshi".
Yayan ya murmusa yace "Jawad, Abbanka ya kirani, ya min bayani".
Cike da jin dadi Jawad yace "Yauwa Yaya, ga numbern kirashi donAllah".
Yayan yace "tun yanzu Jawadb? Kamar jira ake"
Yace "Eh wallahi Jira akeyi, nidai call him now".


Yayar ya yi dialling Numbern Baban Amira Ringing daya aka dauka, Jawad ya ma yayanshi nuni da ya saka handsfree haka kuwa yaya Abdulhafiz yayi.
"Hello Assalam Alaikum"
Daga chan bangaren Mallam Muhammadu ya amsa da "Waalaikum Salam"
"Sunana Abdulhafiz Abu Shamsu, nine Babban wa a guri Jawad mai neman k'anwarka Labiba".
Baban Amira yace "to to, muna lafia?"
Suka sake sabon gaisuwa.


Yaya Abdulhafiz yace "Mahaifina ya Umurceni da na tuntubeka da Maganan Jawad".
Baban Amira yace "MashaAllah, kamar yanda na gaya ma Jawad, nace mai Inda gaske yake da Aure yazo, ya turo Manyanshi ga Manyanta, sai su nema mishi izinin zuwa zance kafin ayi na neman Aure".
Yaya Abdulhafiz yace "dama haka ya kamata, to yaushe zamu iya zuwa?"
"Ko yaushe kuka Shirya".
Yaya Abdulhafiz yace "shikenan zan tuntubi magabatarmu da maganan, kaima ka tuntubi naku, tunda ga waya sai mu ji yanda zaayi, amma for now muna son sanin Asalinku, Abbanmu ke tambaya".


Baban Amira yace "Mahaifanmu na cikin Garin Edo,a unguwar Uromi, Bari zan maka Text"
Yaya Abdulhafiz yace to shikenan mungode kwarai dagaske, ba, mu yan Anguwan Alk'ali ne, da ka tambayi Gidan Shamsu Abdulrahman Alo, zaa gwada maka gidan kakaninmu, sunan Mahaifin Alhaji Abu Shamsu, nima haka zan maka text gudun mantuwa".


Baban Amira yace "Ba laifi mungode kwarai".
Yaya Abdulhafiz yace "Sai kun jimu".
Sukayi Sallama.
Jawad baki uwa gonar audugu don burinshi na kan cika.


E D O


"Muhammadu kace akwai yaro mai neman Labibata?"
Daga bangaren Baban Amira yace "Eh Abba, suna ma maganar zuwa gunku neman Izini".
Alhaji Ahmad Dakata yace "MashAllahu, ya maganar mu?"
Duk da ya san maganar yace "Wacce Abba?"
Yace "Muhammadu Alkawarin da ka min na cewa da Labiba ta samu Miji zaka cireta daga Makaranta ka maido man Ita Gida na mata aure".


Baban Amira yace "ban manta ba Abba".
Abban yace "yauwa, auren shine rufin asirin duk wata diya mace, wanda tayi Allah ya sa mai Albarka, in Mijinta na da raayin karatu sai ya sakata in baidashi kuwa sai tayi yar sanaa tunda haka sauran yayyinta sukayi, amma Labiban ta amince ko?".
Baban Amira yace "Eh Abba, ita ta bashi numberta ya ba yayanshi ya kirani ai, kuma da yazo Gidana na gaya mata zan turo muku su, kaga ko tanayi tunda ta barshi yazo Gidana".
Baban yace "MashaAllah, wallahi naji dadi sosai, sai kaima ka fara naka binciken yanda suma zasuyi, in babu wata matsala sai a hade da bikin Yaruwarta Samira kafin Azumi".
Baban Amira yace "to InshaAllah Abba, a gaida su Mami da mutanen Gidan".
Sukayi Sallama.


K A T S I N A


Strike Din Likitoci bai dade ba, a hanyar Yasmin ta komawa Gidan Alhaji Zaki ta samu wayar sun dawo Yajin Aiki, ta garzayo Kankia she's on call, kuma akwai patients da yawa suna jiranta.
Gani tayi zata bata lokaci in taje Gidan Alhaji Zaki kuma ta tafi Gidansu ta kwashe kayanta, ya sa ta kira Zaid kamar jira yakeyi ya dauka nan da nan.
"Yasmin, ina kikaje you got me worried".
Murmushi tayi tace "Kankia zani, ana jirana a Asibiti, in aiki yayi yawa sai Weekends, in kuma ba aiki sosai zan dawo within the week, ka kula da kanka, kayi duk wani abun da ka san zai saka farinciki da jin dadi".
Zaid yace "InshaAllah"
Suka katse wayar.
A nan ne ya tashi ya shiga Cikin Gida don ganin Dalo kuma yayi Breakfast.


3:07 ta shigo Anguwar cikin Keke Napep, da 'yan Bencin Eskaley ta ci karo, ce ma mai napep din tayi ka tsaya nan. Ba ta fito ba sai da ta k'are musu kallo, ko wannen su da karan Sigari banda Mankas, ko ya gama shan na shi ne oho.
Fitowa tayi daga Keke Napep din ta k'arasa gun su, kanshi a k'asa, hayaniyar da suke mata ne yasa shi dago kai a hankali ya sauke a kanta.
Itama shi din take kallo.
Da sauri ya kauda kai, shi yanzu Labiba tsoro take bashi, kar ta mishi wani magana mara dadi, kar ta mai wulakanci gaban mutanen shi.
K'in kallonta yayi amma tana kallo yana dan satar kallonta, bata ce ma kowa komai ba.


Eskaley ne yace "Mankas wurin ka aka zo fa".
Kallonta ya danyi yaga tabbas shi din take kallo, to me ya faru? Me take so? Sai da ya dan bata lokaci kafin ya mik'e tsaye ya tako har gabanta.
Ido cikin Ido suke kallon Juna, 'yan Bencin Eskaley suka zuba musu ido.


Chan Labiba tace "Kai kace Kana Sona?".
Ido ya k'ura mata sosai kafin yace "Ni na ce ina Sonki.
"Har yanzu kana So na?"
Hannu ya sa ya dafe Zuciyarshi yace "Har gaban Abada zan So ki".
Idanuwanta ta lumshe ta budesu kafin tace "ina Sonka Fisabilillahi".
Murmushi yayi sosai har hak’oranshi suka bayyana tace “kaga Sauro ya cijeka, kar ka ya k’ara cizon man kai, bana so”.
Shewa 'yan Bencin Eskaley suka hau suna tafi, murna suke yi.
Terror yace "to wallahi Yayata ke gonarmu ce, duk wanda muka gani yazo gunki sai na sare mishi k'afaffu".


Murmushi tayi, ganin fuskokinsu da farinciki, its genuine, farincikin da ba kudi ya basu ba, farincikine na Solidarity da ta musu na son Danuwansu.
Ta gwada musu cewa Suma fa ‘yan Shaye Shayen mutane ne, suna da damar So, suna kuma da damar a So Su, Labiba kam ta tabbatar musu da hakan.


Zaid ya kallesu kafin ya dawo da kallon gareta yace “mu tafi Gida” murmushi ta mishi tace “mu tafi”.
Ba magana sukeyi ba, kallon juna sukeyi sai su dauke ido, sai su sake kallon junan, sai su kuma kawar da kai, sai suyi murmushi, sai suyi dariya, shine jin dadi da farincikin da suke ciki, duk wanda ya kallesu sai ya k’ara, kallo daya zaa musu a san cewa masoya ne cike da Soyayya da shaukin juna a lokacin.,basu damu da kallon da yan anguwa ke musu ba, don bama sa ganin kowa, junansu kawai suke gani, sauran mutanen dont matter, in dai zasu kasance tare, ba su da damuwa.


A bakin Gidansu Labiba suka toge suka tsaya.
Sama da k’asa ta kalleshi tace “Ka san kayi kyau Jiya?”
Daria ya subuce mai, be yi kokarin hana dariyar fitowa ba, bata taba ganin expression dinnan a tattare dashi ba, kawai sai ta jita cikin farinciki da walwala ganin ya sake da ita.
DanMakaho ya ga dai har nuna su ake ya lumshe ido ya budesu yace “Shiga Gida”.
Ta gyada mai kai alamun Amincewa.
Sai da ya ga shigewarta kafin shima ya shige Gidansu.


In har wani abun Farinciki ko na Bakinciki ya sameshi, world yake sha, amma yau kawai sai ya fadi kan guiwowinshi yayi Sujadda raka’a biyu don kam yaji dadi fiye da zato.


Ko da Yayanta ya dawo Gida suna zaune bakin daki akan tabarma suna cin Ayaban da ya kawo, Idonta kan Gidan Alhani Zaki so take taga ta inda zai bullo.
Baban Amira yace “dazu su Jawad sun kirani”.
Ita ina ruwanta? Ba ta shi take ba, ta Zaid take, bata damu da tambayan mai ya kira yi ba sai cewa tayi “dazun ne ya kirani wai na tura mishi numbernka”. Don ma kar ya ja wani magana ya sa ta mikewa ta shiga Dakinta.


Aunty Aseey tace “ke kuma da an fara magana sai ki fita? Baban Amira ya kuka kare?”
Baban Amira yace “eh yayanshi ya kira, na dai basu Sunan baba da Adireshin Gida kuma sun bada nasu, yanzu haka a kasuwa na tambayi wani abokina dan Anguwan Alkali a kasuwa, yace ya san Family din, kuma Alhamdulah naji bayani mai kyau, amma duk da haka ba zan tsaya nan ba, zuwa gobe InshaAllah zan shiga Anguwar Alkalin na tsananta Bincike kan Mahaifin yaro da shi kanshi Yaron duk da ba tashin nan bane, ba zai gaggara ba, da ka san wani wani ya san wani haka komai zaizo da sauk’i”.


Aunty Aseey tace “hakane, Allah ya sa a daidaita a yi damu”.
Amsawa yayi da Amin.
“Amma ka kira su Baba?”
Yace “eh munyi magana, ya bar min komai yace in fara bincike saboda su san wa zai zo neman diyarsu, in ma an daidaita so yake a hada da na Samira, kuma ya tuna min Alkawarim da na daukar mishi na da ta samu Miji za ta bar karatu, to muna Addua Allah ya sa shine Mijin”.


Guda Aunty Aseey ta sake tace “Ameen Wallahi, Karatun wa? Haba dai ai aure shi ne kan Gaba, ai wallahi Allah dai ya tabbatar”.


8:50pm


Ko da Jawad ya kirata sai taji yau duk haushinshi ma takeji, ko mai ya fada sam baya burgeta, a k’agare take ta katse wayar, da ya dauko magana a dokance sai ta sace mishi guiwa.
Ko da ya ce mata dazu Yaya ya kira Baban Amira.
Da sauri tace “Eh ya gaya min”.
Ita burinta ta katse wayar, shima ya lura kamar yau bata cikin yanayin, so sai bai matsa ba yace bari ya barta ta huta, haka suka aje waya”.
***
Ta na jin fitar Aunty Aseey daga dakinsu ta koma nasu dakin, tana ji ta saka sakata ta tashi ta dauko wayarta ta ma Zaid text.
Yana cikin shan sigarin shi yaga shigowar message dinta
“Kayi bacci ne?”
Daria Yayi kamar tana gabanshi ya ja sigari ya fesar cikin jin dadi yace “haba dai ko 11 batayi ba fa”
“Me kakeyi?”
“Zaune, missing dinki”
Tace “buri daya”
Yace “In kasance tare da ke daga yau har har abada”.
Batayi reply ba sai yayo zaton ko katinta ya k’are ya yanke hukuncin kiranta.
Ya zuk’i Sigarin karshe ya hangota ta window da sauri ya yarda ya murje be kai ga fesar da hayak’in bakinshi ba ta shigo dakin da murmushi a fuskarta.
Kallo daya ta mai ta san cewa baida gaskia sai tace “Yadai nawan?”. Kai ya gyada mata, tace “ka zama kurma ne?” Ya sake girgiza mata kai tace “fito da hayak’in zai maka illa”.
Cike da kunya ya juya mata baya ya fitar da hayak’in ba tare da ya bari taga yanda hayakin ya bar bakinshi ba”.


Zama tayi tace “its obvious, na san shan sigari kake, tun daga Tsakar Gidanmu na jiyo hayakin, kunya yaji sosai ya shafa k’eyarshi yace “Sorry”.
Ba ta damu ba tace “Well, burinka na son kasancewa tare dani daga yau har abada nazo ka ganni na yau din kafin kayi bacci”.
Sosai yake kallonta yana nazarinta ganin kallon yayi yawa tace “Yadai?”.
Yace “Ina tsoro”
“Tsoron me?”
Yace “ni dake bamu dace ba”
Tace “ah haba dai?”.


Ganin tana son maida abin wasa yace “dagaske nake, i am serious, bamu dace ba, wallahi gani nake kamar ma na kwareki, kamar cin mutunci ne nace ki Soni, kamar na zubar miki da kima nace ke nake so, ina jin kunya harga Allah”.
Tace “DonAllah ya isheni, ashe a goshi ake rubutawa ace wance da wane sun dace, ashe a goshi ake rubuta wane da wance basu dace ba, ashe baka yarda da Son So daga Allah bane, ashe baka yarda domin Allah nike sonka ba”.
Ya girgiza kai yace “ba haka nake nufi ba donAllah, wallahi bakiji kunyarki da na ji ba da kika kamani redhanded ina shan sigari, naji kunya, kuma ina tsoron abunda zai faru nan gaba in mutane suka son cewa soyayya mukeyi”


Tace “huh, yaushe ka fara damuwa da abunda mutane ke cewa game da kai?da zaka damu da abunda mutane ke cewa da ba ka taba fara shan sigari ba, da baka taba zama a bencin Eskaley ba, da baka yi abota da mutanen da sukayi kaurin suna ba, to kar ma ka sake kaji kunyata wai don kayi shayeshaye, in har ba zaka ji kunyan Allah ba, waceni Labiban Dakata?”


Kai ya sadda k’asa ta hango nadama da da nasani a cikinta sasauta murya tayi tace “ba a film ko novel bane balle na ce zan chanza ka kafin na soka, banda ikon chanzaka, kai kadai ke da ikon chanzaka, kai kadai zaka iya chanza kanka, Sigari, addiction ne ko? Fine ka saba, ba zaka iya daina sha ba, okay, regulate in kana shanta so dari a sati, ka shata so sha biyu a sati, in so 10 kake shanta a rana, ka shata rabi a rana, in so daya kake shanta a kwanaki 3, ashe zaka ma iya bari kwata kwata, na san da wahala, i know its hard, i know amma regulate, ba umurni nake baka

Please Login or Register in order to submit comment