Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma kar ki sake zubar min da hawayenki".


Da sauri ta tureshi ta tashi da zafin nama ta ruga dakinta tare da saka sakata ta rufe, jikinta rawa yakeyi, wannan wani sabon hali ne Uncle Hudu ya tsuro dashi, bata saba da wannan dabia tashi ba, ta fi sabawa da dabiar kyara da hantarar da yake mata, bata son yanda yake son fara shige mata, bata so ko kadan.


Shi ko jinta a jikinshi ya kashe mai nasa jikin, kasa yunkurin binta yayi, kawai ya ayyana ma ranshi sai ya samu yarinyar nan ko ta halin k'aka amma dagaske yake sha'awarta don wannan ba wani abu bane illa sha'awa kuma sai ya ja ta a jikinshi ta sake dashi kafin ya cimma burinshi, ya lura tsoron shi kawai takeyi, amma ya san yanda zai bullo wa lamarin.


Inda ta barshi nan ta iske shi, yana ganin Motar ya karasa gunta da sassarfa, gani yayi ta hade gabas da yamma ta murtuke fuska, bude gaban motar yayi ya zauna tare da cewa "Yas Yunwa nikeji".


Bata kulashi ba ta ja motar ta bar Anguwan.
Royale Restaurant ta nufa dasu, su ka shiga ciki suka siya abinci suna ci.
Zaid yace "wai fushin me akeyi da ni?"
Banza tayi ta kyaleshi.
Yace "Okay Okay inaji, zan amsa miki duk wata tambayar da zaki min, ina jinki Yas".
Girgiza kanta tayi alamun aa tace
"Aa, ni ai ban kai na san gaskia ba, Nayi zaton na chancanci na son abubuwan da ke boye a ranka, ashe baka daukeni a bakin komai ba, ashe baka ma yarda dani ba".
Da sauri ya girgiza kai yace "Yass, i dont want to hurt you"
Da sauri tace "hurt me with the truth"
Numfashi ya ja yace "Ki tambayeni Yas, tambayeni".
Da sauri tace
"Ina son sani, kana son Labiba ko ba ka sonta".


"INA SONTA".


Numfashinta ne ya dan tsaya kafin ya dawo ta boye damuwarta da murmushi tace "Meyasa ka kasa ce mata komai dazun? Mai yasa ka kasa kare kanka, meyasa kaki gaya mata kaima kana sonta?".


Hannu ya sa ya murji idonshi na hagu yace "saboda yin maganar bai da amfani, kare kaina baida wani amfani, haka nan fada mata kalmar so ba zai amfaneta da komai ba".


"Inji wa? Wa yace maka haka? Ka san tun yaushe nake son jin kalmar So a bakinka? Ka gwada gaya mata, ita ta san amfanin da zai mata, fada mata sauke nauyi ne kai zaka ji sak'at, itama hakan, i think kaje ka gaya mata, zaku kasance cikin farinciki ku duka".


Kallonta yakeyi sosai kafin yace "Yas, wani irin abu kikeyi haka? Ba kya jin haushina? Na kasa biyanki kwatankwacin abunda kika min? Ba ki tsaneni ba kan ina son wata ba ke ba? Ba ki ji na fita ranki ba ina kallonki ina gaya kiki ina son watanki, Yesmin ya zanyi da ke? Kina turani wurin wata bayan ke mai so na ce, ba kya kishi na? Ba kya jin zafin turani ga wata?".


Murmushi mai ban tausayi tayi tace "Sosai nake sonka, ina kuma kishinka fiye da zatonka, burina shine samunka, na rikeka ni kadai, amma a dayan bangaren farincikinka shine nawa, in har Labiba ce farincikinka, ina maraba da sadaka da ita, in So daya tak Labiba kake ma ita, zanyi yanda nayi ka sameta, don dai ka kasance cikin farinciki, irin son da nake maka kenan, haka ne adadin son da nake maka, in har kana son ganin farincikina to ka kasance cikin farinciki".


Ji yayi idonshi ya ciko da ruwa, zuciyarshi na zugi.
"Yasmin how could you love me this much?"
Murmushi tayi tace "wallahi fa, nima ina tambayan kaina wannan."
Yace "dagaske ba abun daria bane, Yas kina sa ina jin haushin kaina, na kasa baki abunda kike so, amma wallahi ki sani ina sonki kamar yanda nake son Dalo, kina da Girma da daraja a idona, k'imarki kullum karuwa yake a zuciyana, bana son k'untata miki, yin soyyaya dake wallahi kunci zai jawo miki, kuma ina sonki da ba zanso wani kunci ya kusanceki ba, bana son bata miki rai, bana kuma son abunda zai bata ranki ko menene, bana son saba miki, shiyasa dazun na kasa cewa komai, ana barin halas don kunya, Haka ne zan biyaki hallacin da kika dau shekaru kina min, zan ga kin auri wanda zai so ki fiye da tunaninki, wanda zai kula min dake, wanda zaku kasance tare har k'arshen rayuwarku".


Sosai take son fashewa da kuka, amma ta dake tace "Awwn so touching, to in ka gama maganganun ban tausayi ka tashi muje ka ba Labiba hakuri, ka kuma gaya mata kana sonta fiye da zatonta, kuma zaka shiga layin manema aurenta".


Zaid be san lokacin da ya fashe da wani irin dariyan takaici ba.
"Aure? Aure fa kikace Yas"
"Wa zaiyi aure? Ni? Ni Mankas zanyi aure? Hahah funny".
Yasmin da mamaki tace "what is funny kuma?"
Ya dan tsagaita darian marasa lafian da yakeyi yace "ai na jiki da wani magana ne kamar almara, wai zan shiga layin manema aurenta".
Yasmin da mamaki tace "Yes, what is wrong with that?".


Zaid ya gyara Zama yace "Okay let me make this Straight".
"Kinsan ina iya amincewa da Soyayyarki ko da ba kece Yasmin k'amshi ba? Ina iya ganin wata ince ina so, wata na iya ganina tace ta na so, na amince na kuma bata mata lokaci don wallahi zan bata lokacin duk wanda maganar So ya shiga tsakaninmu yanzu, Amma But No ba zan fara wani abu mai suna Soyayya ba, ban amince miki mun fara Soyayya tun farki saboda kin fi karfin na ci amanarki kin fi karfin na hainceki, kin fi karfin wulakanci a guna, duk yanda da zuciyata ke ingiza ni kan mu fara soyayya na ki saboda na san ba hanya mai bullewa bace, ba zan taba bata lokacinki ki ba shiyasa Yesmin ban taba jin wani abu da ya wuce na Yanuwantaka game da ke ba, saboda bata miki lokaci kawai zanyi, na hanaki samari, kuma ni ba zaki sameni ba, bana cikin jerin samarin da suke soyyaya da biyu, bana cikin samarin da ke bata lokacin Yanmata kuma sun san ba aurensu zasuyi ba".


Duk yanda zuciyar ta ta karaya bata fada murmusawa ba ta gyada kai tace "na sani, na san da haka, amma Labiba fa? Abunda kakeji game da ita daban ne dana Yasmin K'amshi, ita me ke hanaka? Meyasa?".


Ajiyar zuciya ya saki yace "Yasmin kina sa ina ta maimaita magana daya".
Yasmin tace "Labiba fa?"
Yace "Labibaa, Labiba, to ita Labiba yanzu kinga ai tana da tsayyaye, da idonki jiya kinga wanda yazo gurinta"
Tace "kaima zaka fara zuwa gunta".
Yace "Yasmin so kike na bata mata lokaci itama, shi wanchan da Aure yazo mata, nikuma bata lokacinta kawai zanyi, to meye amfanin zuwa in the first place?".
Yasmin tace "inji wa? Kaima da Auren zakaje mata".
Yace "wai wani irin aure? Wanda ke da lafiya, kamala da tsawon rayuwa fa shi yake planning jin dadin rayuwa har ya sa Aure ciki".
Galala ta kalleshi tace "kai kuma baka da tsawon rai ko?"
Ya gyada kai yace "Kin fi kowa sani ai".


Tace "kul, kar ka sake ka ce min na sani, ban sani ba, na san kai Namiji ne kamar kowa, na san kana da rights to love and to be loved".


Ya katseta "Yasmin, kar ki maida mu baya, kin fi kowa sanin i am sick, kin fi kowa sanin how sick i am, meye amfanin zuwa in the first place, meye amfani fara abun da nasan it wont last, meye amfanin fara abunda zai taba zuciyar yarinya, what if we started all that sai nazo na mutu, kinsan damage din da hakan zaiyi mata? Kinsan illar da zai mata? Kinsan yanayi da hakin da zata shiga sanadiyar rashina? Son da nake mata ba wai yanzu bane, har gaba da zata shiga wani hali bayan ba ni a doron kasa, kinga ko na zalunceta na sa ta saba dani bayan ni ba rayyaye bane".


Cikin zafi tace "to sai aka ce ka kusa mutuwa? Sai a ka ce kar ka ji dadin rayuwanka kamar mutane? Sai akace kar kayi planning future dinka? Kai Allah musuru ne? Ka san ranar mutuwanka? Ko ance maka cuta na kisa? Wa ya san gawan farin? Mutane nawa suke da ciwo more worse than you and are living happily? Mutane nawa ne suke fit and sound ba tare da ciwo ba mutuwa ke zuwa musu farat daya, eh yes Your liver is infected, your lungs are damaging, and you are not taking your medications sai ka ga dama, kai baka da plans saboda you believe you are dying, ba ka da wani hope, kai kana zaune kana jiran mutuwan ka, haushin da kake bani da kake irin surutan nan, ban dade a Islamiya ba, ban da sani sosai a addini amma tun ina karama na san cewa ba a so bawa na yankewa daga rahamar Allah, Zaid wake up, you deserve to be happy".


Shiru yayi yana nazarin duk maganganunta.
Maganganunta sun ratsa shi.
Yace "Yas ta ya zaayi a barta ta soni? Ta ya zasu yarda da dan Shaye Shaye? Dan zaman kashe wando? Ta ya zaayi ta aure wanda bai da aikin fari bare na bak'i sai zaman bakin hanya?".
Yasmin tace "ka tashi tsaye, ka gyara, ka chanza, ka kimtsa kanka, and komai zai zama tarihi, ba decision din danginta bane, decision din zuciyarta ne, kar ka manta kafin ka sota ta soka, ta san ko kai waye, amma ta zabi da ta soka a matsayinka na wanda ta san dan shaye shaye ne, i think shes ready for what to come, ina dai so ka ma kanka karatun ta nutsu, since you are planning to love, i think you need to work on how to live".


Kallonta kawai yakeyi yana neman karin bayani tace "ehmana, Maganin da kayi watsi da su su zaka dawo ka sha in har kana son kasancewa tare da ita, you strive to survive, or tunda baka son hurting dinta, zan sameta na gaya mata matsalarka kila in ta saka shan magani dole ka sha tunda ita ake so".


Da sauri ya girgiza kai yace "dont be like this, kar kice haka mana, ki sani Son da nake miki yafi karfin Soyayyan maaurata, so ne na jini fa".
Kafadunta ta daga tace "i am not complaining ai ina dai fada ne, duk da haka zan mata bayanin ciwon ka, na gaya mata ka bar shan magana saboda ka cire rai da rayuwa yanzu haka mutuwarka kawai kake jira".


Da sauri yace "aa donAllah, kiyi hakuri, na bari wallahi, muje ma ki siya min magani yau zan fara sabon medication".
Da mamaki da jin dadi tace "Ahh Lover Boy Allah ya baka hakuri, yanzu dai ka jira monday a sake ma tests a ga me zaa ma prescribing".
Dokinshi ya kasa boyuwa yace "Nagode Yasmin, Allah ya biyaki da Aljannah , Allah ya saka miki da Alheri. Allah ya faranta miki yanda kike faranta min".


Yasmin tace “Ohhh you are so sweet, dallah mallam tashi mu tafi you are making me emotional, kafin ka sani kuka”.
Daria yayi yace “Okay okay muje”.
Ganin jin dadinshi ya sa Yasmin jin dadi itama har suka tafi Gida.


Gab da Maghrib Jawad ya isa Gida, isowarshi kenan don ya tsaya a Kaduna, Babban Parlorn Gidan ya shiga, daga Mancy sai Mimi,da sallama ya shiga Mimi ta karasa da gudu tayi hugging dinshi, murmushi kawai ya mata tace “Ya Jawad ina kaje?” A takaice yace “Katsina naje” Mancy ta fadada murmushinta tace “Ashe KT kaje Jawad” ba yabo ba fallasa yace “Eh” tace “lafiya dai ko?” yace “Uhm, naje ganin wasu ne” Ayyah Allah sarki, ai bansani kayi tafiya ba” a kagauce yace “Umma kadai ta sani, ai ba dadewa zanyi ba shiyasa ma ban fada ma ko Abba ba” tace “uhm hakane, Allah ya huta gajia dan Umma”.


Wucewa yayi cikin Gida don sanar ma Ummanshi dawowanshi.
Tun dazun take kiran wayar Zaid ba ta shiga, sai tace bari ta kira wayar Dalo kila tana kusa.
Ringing daya ta dauka, amma yanda ta ji muryarta ta san cewa akwai wani abu.
“Sadiya me ya sameki?”
Dalo tace “bakomai Mancy, ya gida”.
Mancy tace “uhm uhm sadiya, muryarki cike take da tsoro, wani abu suka miki?”
Dalo ta fashe da kuka, hankalin Mancy ya tashi, ta hau tambayarta abunda ya faru.
Dalo cikin kuka tace “nidai Mancy don Girman Allah ki zo ki tafi dani, i dont like it here, mancy kinga Uncle Hudu dazun” sai tayi shiru kuma.
Hankalin Mancy ya tashi tace “me ya miki? Gaya min Sadiya, me ya miki?”.
Ba ta san me za tace mata ba, nauyin maganar taji, duk da be mata komai ba, tattabatan da yakeyi ne bata so, amma ta ya zata ma Uwarta bayani? Ba tayi wannan sabon da ita da zata iya gaya mata komai ba, ganin Mancy zata isheta da tambaya kuma ita bata san me zata ce mata ba ya sa ta kashe wayan.


Mancy ta shiga tashin hankali, ta sake kiran wayan ta ji switched off, nan da nan cikinta ya duri ruwa, ta nemo numbern Zaid wanda suke daf da Gidansu Labiba.
“Assalam Alaikum Mancy”
“Waalaikum Salam Zaid, Ina Dalo?”
Yace “Mancy tana Gida”
“Yanzu muke waya da ita tana kuka, wai ko Uncle Hudu ya mata wani abu? Ta dai k’i magana yanzu kuma na sake kira naji wayarta kashe”.
Mai makon Gidan su Labiba sai ya wuce Gida a guje Yasmin ta bi bayanshi tana son jin mai ya faru.
Dakin ya nufa a guje yana kwankwasawa Dalo fito nine da sauri kuwa ta bude kofar ta fada jikinshi tana kuka.


Alhaji Abu Shamsu ne ya fito daga Dakinshi zai tafi masallaci ya ga Mancy tsaye yace “wani abu ya samu Sadiya Maryama?” Kai ta shafa tace “aa wayarta ne a kashe, shine danuwan ya dubota” girgiza kai kawai Alhaji Abu yayi be san irin wannan zurfin cikin irin na Mancy ba, wato ba ta daukeshi a matsayin Uba yaranta ba, shikenan ido kawai zai sa mata” ya sa kai ya fita don zuwa Masallaci.


Yasmin tace “gaya min Dalo, me Hudu ya miki?” Zaid ya fara huci yace “Wallahi sai na kashe Hudu” da sauri Dalo tace “me yayi? Be fa yi komai ba, dazun ne fa na fita naga bakowa shine naji tsoro, shine fa nayi waya da Mancy taji ina kuka nace mata ina tsoro sai ga Uncle Hudu ya shigo sai naga ashe akwai mutane fa, tsoro kawai nakeji in nikadai ce”.


Zaid da Yasmin suka fara lallashinta tare da cewa ba zasu sake barinta ita kadai ba, Zaid ya kira Mancy ya mata bayani, yace da Yasmin bari yayi Sallah.
Dalo kam ajiyar zuciya kawai takeyi wani na bin wani.
Yasmin tace “yau mutanen Gidan dare akayi a waje kenan”
Dalo tace “uhm gashi kam har yanzu ba su dawo ba”
Yasmin tace “muyi Sallah mu dafa abinci”
Dalo tace “to Aunty Yas”.


Suna kan Table suna cin Doya da sauce Hudu ya fito daga daki ya yo kan table din yace “abun solo ne? Mu fa?” Jikin Dalo ya fara bari, Zaid ko kallonshi beyi ba, Yasmin tace “Ayyah abincin mutum 3 ne”.
Hudu da bariki ya sa hannu cikin plate din Dalo yace “bari na ci na diyata” haba tuni jikinta ya hau bari jin hanayensu sun gogu. Wani mugun Kallo Zaid ya watsa ma Hudu amma Hudu ya dauke kai irin be ma san kallon da Zaid ke mai ba, sai ma Kashe ma Dalo jiki yake da kallonshi.


Haka suka gama Dinner, su Hajia Shafa sun dawo Zaid da Yasmin sun tafi baya ita kuma dalo ta shige daki ta sa key.


Yesmin tace “yanzu ka zo muje Gidansu Labiba ayi magana once and for all”
Yace “aa Yas, its late, 9 ta wuce, bro dinta ya dawo, kuma ni i am already nervous, ni tsoro ma take bani”.
Yasmin tayi daria tace “ji fa, nawa labin take? Ko ta girmi dalo befi ta bata 1year ba, yanzu ita ke kada maka gaba? Haba jarumina kar ka bani kunya mana”.


Yace “oho dai nidai wallahi wani iri nakeji”
Tace “yanzu dai meye abunyi, ba zamu je ba ?”
Yace “dare dai yayi, akwai gobe”
Tace “Allah shi kaimu, nima dai yau bacci zanyi da wuri, barin je na kwanta, goodnight”.
Har tayi gaba ya tsaidata ta hanyar kiran sunanta “Yasmin”.
Ta tsaya tare da waigowa
Yace “Thank You, Thank you for Everything”.
Har ta dan karaya don idonta ya ciko tayi saurin mayar da hawayenta tare da jefanshi da murmushi tace “Goodnight Zaid”.
Tayi saurin tafiya har ta hada da gudu gudu.


Zama yayi kan dakali yana tunanin abubuwan da suka faru tun daga safiyar yau zuwa yanzu, “Yasmin, Yasmin ta chanchanci Farinciki, yasmin ta chanchanci ta ji dadi, baya mata irin Son Soyayya, bai so kuma ya so ta saboda tausayi zai zalunceta in yace yana sonta, amma InshaAllah zaiyi duk abunda zai sata farinciki zai kuma tsaya mata gwargwadon ikon shi”.


Sai kuma Chanji, ya san shan World da sigari a jikinshi ne dolen dole ya bari in har yana son kasancewa tare da Labiba, dole ya watsar da duk wani mummunar dabiar da ta zameshi Jiki, amma tambayar shine ta ina zai fara?.


Ya dade yana sakawa da warwara, ya ga fitowarta daga Daki rike da wayarta wanda take amfani da fitilar jikin wayar wato torch light.
Kallonta kawai yayi ya sake murmushi, a ranshi yace “Biebbs kenan, akwai wuta fa ko me zatayi da torchlight?”.


Kitchen ya ga ta shiga kuma chan ta fito, yana ganinta ta shiga toilet ta fito, ta tsaya kamar tana neman abu sai taji wayarta yayi ringing.


Tana ganin waye tayi saurin kallon Sashen Da yake, a zuciyarta tace “tun yaushe yake zaune a nan? Ban lura dashi ba”.


Zuciyarta ta kwadaitu da ta dau wayar, dauka tayi tana zabga mai harara daga inda take.
Cikin wata irin murya yace “Bibbs”.
Cike da Masifa tace “What? Meye?”
Yace “INA SONKI”.
Dif ta dauke wuta, duk wani na’ura na jikinta suka tsaya chak suka kasa motsi, k’irjinta kamar ya fito, wani yanayi ta shiga da bata san ko wani iri ne ba, jikinta murus ya mutu jin muryarshi tayi chan k’asa da k’yar ta saita kanta don jin abunda yake cewa.


Da dukkan numfashin da na ja, da dukkan numfashin da na sake kina cikinta, rufe idona da budewarshi kina cikinshi, kullum kina tsungunne a cikin zuciyata, bansan me zanyi kuma ba, bansan ko ina da damar jin haka game dake ba, bansan ko matsayina ya kai na ji haka game dake ba, ba laifina bane, ba yin kaina bane, haka na tsinci kaina, tun daga ranar da na sanyaki a idona nake jin haka game dake, ban san ko daidai bane jin haka game dake amma ina so na yarda da cewa banyi laifin jin haka game dake ba, ina so ma yarda ba laifi bane Sonki, sonki ba sa6o bane da zaa hukuntani a kai, INA SONKI SOSAI , Ina sonki Labiba Ahmad Dakata”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN HUDU 2⃣4⃣
(SAURO🐝)




Dif ta dauke wuta, duk wani na'ura na jikinta suka tsaya chak suka kasa motsi, k'irjinta kamar ya fito, wani yanayi ta shiga da bata san ko wani iri ne ba, da k'yar ta iya furta "YA ALLAH".
K'yafta idanunta tayi sau biyu tana juya kalamanshi, bata san mai ya kamata ta ji ba, dadi? Ko akasin haka.


Ba zata taba bari kalaman yaudara irin ta maza suyi tasiri a wurinta ba, da k'yar ta iya ce mai "ka bar yaudaran kanka, ba so na kakeyi ba, bakincikinka Ka ganni da waninka, wanda yanzu kam ba yanda zakayi, tunda dai ina da wanda nake so, dole kam yazo guna, kuma in har muna makwaftaka musamman da wannan rufzazen bangon to dole ka ganmu, amma zan sake gaya ma, ba ruwanka da duk wanda zaka ganni tare dashi, ba zai yiwu ka dinga kora min samarina ba, so ina rok'onka da ka fita daga rayuwata yanda ka buk'aci na fita daga rayuwarka".


Cikin wani murya mai kama da hankali tashe yace "Biebbs, me kike so kice? Me kike so? Ba kya so na kuma?"
Da sauri tace "Eh, haka nake so nace, bamu da wata alak'a da ta wuce na Makwaftaka, ni da kai bamu dace ba".


Gani tayi ya tashi tsaye daga zaunen da yake, ya tako har gaban fasassun blocks amma be ida shigowa gidansu ba yace "Aa kar ki ce haka donAllah, biebbs ya kike so nayi? Sonki ya shiga jikina, ya zagaye tsoka da bargona, ya kike so na cireki a zuciyata? Wai manSai da kikayi nasarar chusa ma zuciyana sonki zaki ce baki sona kuma? Wani irin abu ne wannan? In fushi kike dani kiyi hak'uri donAllah".


Ji yayi ta tsinke wayar, da sauri yayi yunk'urin karasowa gareta tayi saurin shigewa daki tana haki, dirshan ta zauna a k'asa, zuciyarta na barazanar fitowa, a halin yanzu bata san me ya kamata tayi ba, ta dade tana son jin kalaman nan a bakinshi, ta dade tana so ya furta mata kalmar so, yau ya furta mata, meyasa bata gaya mishi yanda take sonshi ba itama? Message ya shigo wayarta da sauri ta bude ta ga Zaid ne.
"Akwai Sauro, zan kwana a nan in har baki fada min wani abu mai dadi ba".


Tashi tayi da sauri ta lek’a ta window ta ganshi a takure, A fili tace “ina abunda ya dameni? Ka kwana nan mtss, kalaman yaudaranka ba zasu yi tasiri a kaina ba”. Hayewa tayi Gado tayi adduar Bacci kafin baccin yayi awon gaba da ita.


Sauron Katsina marasa kunya a gaban idonka ma sai su cijeka balle bayan idonka, haka Saurayen Tudun Matawalle sukayi dinner da DanMakaho, tun yana sosawa, yana kashesu da hannu, yana tsaki gashi bai da abun rufa, taurin kai da ya sa ma ranshi, shi ya hanashi shiga daki ko da ya dauko abun rufa ne, haka dan MAKAHO ya kwana a waje wanda bacci rabi a bude ya yishi, sai gaba da Asuba bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi.


Alarm dinta ya tadata, bude dakin tayi ta fito, idonta tsaye yayi chan sashen, wani murmushin takaici tayi tare da mamaki, wai dagaske kwanan yayi a nan? Sai taji zafi kuma, bata ji dadi ba, kamar ta karasa gunshi ta k’yaleshi ta shiga Toilet ta wanko bakinta tare da dauro Alwala, ta shiga kitchen ta dauko babban tukunya ta cikashi taf da ruwa sannan ta janyo risho (stove) ta kunna ta daura tukunyan kafin ta fito daga kitchen din sai da ta sake kallonshi kafinta shige daki k’irjinta na mata nauyi.


Rakaatanil Fajr tayi kafin tayi Asuba tayi zikrorinta na safe kafin ta tashi don tada yara ta musu Wanka yau Monday.
Ta fito rik’e da hannun Ameera, yana nan bai motsa ba.
Itama ta rasa abunyi, yau ko Asuba be yi ba, yana nan yana baccin asara a waje. Baban Amira ne ya turo k’ofar Gidan hannu shi dauke da Bak’in Leda wanda shakka babu Breadi ne da madara da lipton da milo na sachet, wanda duk rannan da zasu sha tea baya dawowa daga Sallahr Asuba sai gari ya waye ya tsaya siyansu.


Ganinshi ya sa Labiba dawowa daga tunaninta kar yace DanMakahon take kallo, tace “Yaya Ina Kwana” ya amsa da “Lafiya lau Aunty Labs” Amira tace “Baba ina kwana” yace “Lafia Amirori wanka zaayi ko?” Tace “uhm” Labiba tayi saurin shigewa Kewaye da Amira ta dauki bokiti ta shiga kitchen ta diba ruwan zafi ta k’ara a na tukunyan ta sirka kafin ta shiga yi ma Amira Wanka.


Kamar dai kullum in yana Gida, Baban Amira ya dauko tsintsiya don Share tsakar Gidan, Aunty Aseey na Kitchen tana hada Tea a dogon Jug, Labiba ta shiga da Amira ta fito da Sabit dan mishi wanka taji muryan Yayanta yana “SubhanAllah, DanMakaho ne chan?”.
Da sauri ta kallesu taga Yayan na k’okarin k’etara Gidan Alh Zaki.
Ta naji Aunty Aseey na cewa “yanzun haka shaye shaye yayi ta kai mai karo shiyasa yayi Mankas a waje”.
Labiba tayi saurin dafe kai.


Mallam Muhammad ya fara bubbuga shi tare da cewa “DanMakaho, tashi gari ya waye fa” firgigit ya tashi a dan tsorace tare da murzan idonshi na hagu.
“Dan Makaho ba dai anan ka kwana ba? Ji cizon sauro ko ina a jikinka”.
Zaid ya bi jikinshi da kallo, ya ga cizon sauro runtuma runtuma.
“Kayi Sallahr Asuba kuwa?” Ya ji Mallam Muhammad na tambayanshi
“Aa” ya girgiza kai.
“Haba DanMakaho, ka san k’arfe nawa yanzu? Bakwai ta yi fa, me ya ja

Please Login or Register in order to submit comment