Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa ke tura yaronshi police station?" Haka tayi ta fadi har ta shiga cikin Gidan Lema, Mami ta mata sannu da zuwa, Nene tace "ke yau ni naga k'awar Saude".
Sai da Mami ta dafe k'irji tace "a ina Nene?".


"Wannan Kishiyar Maryaman"
"Nene dagaske an Saki Hajia Maryam?"
"Ke ina baki kina k'in karba, Makira ce Matar nan, wai ke in gaya miki Yaro na samu bakin gate ya bani labarin duk abunda aka ma Maryama, ke fa da naje samu nayi sun ma Takwaran Zaidu Bawan Allah Rubdugu, aiko na shigar mai, na tsokale wa Uban Ido, ita kuma na lallasata".


Mami tace "yanzu Nene fitanki har kinyi Dambe?" Nene tace "aa fa ni fa ba dambe nayi ba, bugun tsiya na mata, ke dallah ina kaiki.
Ke shaida ce irin So din da Alhaji Zaki yake ma Matarshi Maryama da Yaranshi, kina zuwa Gidan Kema, kinga kyakyawar Alak'a tsakaninsu, ke kawai sai rana daya, ya auri tsohuwar Matarshi, ya zabure ya ma Matarshi duka gaban 'yan anguwa, ya cika mata saki 3 ya sa aka kwashe mata kaya, ya zo ya tsani yaranshi, ya shigo da Agola su biyu, ya fifita su fiye da yaran cikinshi, me zakice? Me kike ganin ya faru?"


Mami ta danyi jim kafin tace "ta na iya yiwuwa Chanji ne kawai, ko dokin sabon auren da yayi ne".


Hannu Nene ta sa a kai dauke da takaici tace "ke wai bakiji me nace ba, don yana dokin aure sainya juya ma Yaran cikinsa ba? Ya kike magana ne kamar ba ki san aikin asiri ba, ke da Saude ta rafka muku asiri ke da Mijinki aka rabaku tsawon shekaru?.


Mami tace "kawai banson zargin Asirin ne, tunda bamu da hujjah".


Nene tace "wai ya kike magana? In ba asiri ba meye? Hujja ya wuce wanda na karanto maki, ke wai don uwar yaron nan da ni zai sa a kulle a pirisin?".


Mami ta zaro Ido, tace ya akayi? "Aa wai mun bugar mishi Mata, ya kira YanSanda wai su tafi dani da Zaidu Bawan Allah, nace mishi ya kira min Habibu, da yaga uwar bari, sai cewa yayi a barni amma a tafi da Dan, yanzu dan na chan kulle, ki latso min Mijinki".


Sai ko gasu shigo tare da Uncle Zaid.
Nene ko ta tarbesu "Oyoyo Sannu da zuwanku" Uncle Zaid ya murmusa yace "Nenemu ni da Seebi".


Jawo hannunshi tayi ta zaunar dashi tace "wai Zaidu Bawan Allah, ina kawata Hajia Maryama da ke Tudun Matawalle wanda ka taba kaini Gidanta?" Cikin fahimtarta yace "Matar Speaker Ali Zaki?".


Tafi tayi cikin jin dadi tace "itafa"
Uncle Zaid da neman k'arin bayani yace "me ya sameta?".


Nene tace "to asiri kishiyarta ta ma Mijinta ya saketa saki 3 bayan ya lakada mata na jaki, ya kuma juya ma yaran Baya, kai wai jiya suka kori su Raliya masu abincin da na kai ma Maryama, aiko Raliya tazo ta gaya min duk abunda ke faruwa, ni ko na wanke kafa na sa Sabitu ya kaini Gidan.
Kai wai daga isa na naga sun saka takwaranka Zaidu a tsakiya suba ta jibgarshi, ni ko naci dammarata nayi kansu".
Kai wai sai ga 'yan Sanda sunzo wai tafiya da mu, wai zasu samu bayan Karta, wai mun bigi Matarshi, niko nace wallahi bai isa ba, sai dai a tafi da danshi ba dai ni ba, kuma nace a latso min Habibu ai ba su kadai bane Manya".


Daddyn Rafeeq ya jinjina kai yace "Gaskia da Ali Zaki yayi Babban kuskusre da yayi gigin Kulleki" Nene ta yi darian jin dadi tace "yo shiyasa na bashi tsoro wallahi, shegen ya tsorata, ai gaba da gabanta".


Uncle Zaid ya girgiza kai yace "wai Nenenmu ni da Seebi yanzu dambe kikayi? wai ba ma na hanaki Shiga abunda bai shafeki ba?".


Gimtsa baki tayi tace "yi hakuri Mamman".


Mami tayi daria tace "yau Zaidu Bawan Allahn zaa watse?".


"Yo ai naga Zaidu Bawan Allah ko meye nama Hajia Maryama ban fadi ba, matar da ta soni kamar Uwarta, ke Aisha da muke Makka wani ciwo da nayi, wallahi ita ke hidima dani, duk nisan Samanmu sai ta sauki ta siya min abinci da magani, ta rirrikeni in zan fadi, ni ko gani da raki da fada, yanda kika san diyata haka nake watseta , duk tsarabar da na maku ita ke zabar maku kuma so dayawa ita ke biyan kudin, karamcin Maryama mara misaltuwa ne, to yanzu don na taimaka ma yaranta sai ace nayi shiga sharo ba shanu?".


Duk suka jinjina kai, tace "Alhaji Habibu DonAllah kayi man taimako, kaje polis station ka sa a firdo Takwaran Zaidu Bawan Allah, kuje kuyi belinshi, wallahi dan gata ne, be saba irin rayuwar nan ba".


Daddyn Feeq yace "InshaAllah Nene, bari inyi waya inji yana a wani Police Station ne".
Ba jimawa yace "yana Police Station din Tudun Matawalle, barin je inji". Nene tayi wuf tace "muje". Gardama da ita bata lokacine, fits sukayi su Uku, Nene da Alhaji Habibu da kuma Zaid BawanAllah.


Ko da suka isa Police Station din tuni DPO ya fito ya tarbesu, ba bata Lokaci Alhaji Habib ya buk'aci a saki dan Gidan Alhaji Ali Zaki da aka kawo dazun". Jim DPO yayi kafin yace "anya kuwa Alhaji? Alhaji Zaki yace mu rik'eshi kar mu sake mu ba kowa Bail dinshi, kayi hakuri Sir yaron kangararre ne, Mahaifinshi ke da rights akan shi kuma yace a hukuntashi".


Nan Nene ta fara surfa musu ruwan Bala'i wanda Su Haruna da ke bayan Karta sun ji banda Zaid da ya dade a duniyar da World ta kaishi. Da k'yar Uncle Zaid ya firda Nene daga police station din don da har ta fara maganar dukan DPO.


Daga Station basu wuce ko ina ba sai Gidan Alhaji Zaki, iso aka musu har parlo, tare da hamshak'iyar suka fito, suna ganin Nene Shafaatu ta sha mur, riko hannunta Alhaji Zaki yayi suka karasa cikinParlon, hannu ya ba Zaid da Daddyn Feeq sukayi Musabaha".


Alhaji Habibu yace "Alhaji Ali, Nene ta zo mana da wata magana wai ka sanya an kulle Zaid, munje muyi bailing dinshi sunje ba bail, Alhaji komai yayi zafi maganinshi Allah, kayi hakuri ka firdoshi".


Kallon Hajia Shafa yayi ta banka mishi harara, lokaci daya ya fara bala'i "Haba Alhaji Lema, wai ni ina ruwanku dani da iyalina? Shin Zaid din ba yaro na bane? Ina ruwanku ko yanka shi zanyi? DonAllah ina ganin Girmanka, ka tsaya a nan, ba zan dauki shiga sharo ba shanu ba".


Nene ta katseshi ta hanyar cewa "Kai dallah sakarai rufa ma wa mutane baki, ka na zaune sai juya ka ake kamar Masa, kai Asirin ma sai fa sakarai take ma tasiri, shiyasa da ta kamaka tayi maka mugun kamu, to wallahi ka natsu kayi wa kanka kanka fada".


Ta matsa kusa da Shafa'atu ta sake mata wani zazzafan Rankwashi wanda ya sanyata ihu, a tare Alhaji Zaki da Zaid Lema suka tashi, Zaid yayi kan Nene, Zaid ya janyeta yana "Haba Nene".


"Ni Zaidu wallahi ban san harka da Stupid, nidai a Sako min Amanar da Allah ya bani".


Shafa'atu wanda rankwashin ya shigeta ta fara kuka "wallahi Alhajina sai ka sakeni, ba zan iya ba, ace har Gidana wata tsohuwa zata dinga bina tana duka na? Kamar yar yarinya? Ni wallahi ba zan iya ba".


Hankalin Ali Zaki ya tashi da sauri yace "Alhaji Habib Lema, ba gaya ma ina mugun jin kunyarka, ku fitar min daga Gida, ku fita daga harkan Gidana, wallahi in Mamarka ta sake taba Matata wallahi ba zamu kwashe da kyau ba".


Aiko ya tunsura Nene tace "Allah ya tsine maka in har ka bari muka kwashe da kyau, Shege, mara hankali".


Zaid ya ja hannunta tayi ta fizgewa, da k'yar ya iya fitar da Nene daga Parlon, ga Nene da karfi.


"Alhaji Habib Lema, ka ja mata kunne, ta fita daga harkan Gidana, ko kuma hukuma ta shiga tsakaninmu, ai mata Iyaka da Gidana".


Daddyn Feeq be iya magana ba sai dai fitan da yayi a zucciye.


A Mota yace "Don Girman Allah Nene ki fita daga harkan Gidan Zaki, Nene ta ya zan iya dauka in wani ya miki rashin kunya, Nene ki sa mishi ido, duk daren dadewa gaskia zata bayyana, Dan shi ne, chan cikin ranshi akwai sonshi a cikin shi, donAllah kar ki sake zuwa Gidan".


Zaid ma ya shiga lallashinta da tausassun lafazi, yana cewa ta bisu da addua, Allah ne zai kare ma Maryama Yaranta.


Takaici ya hana Nene cewa komai sai Girgiza k'afar da takeyi tana tunanin yanda zata shigo Gidan Alhaji Zaki karfe ukun dare ta ci ubansu daga shi har Matar.
***


Kwana na 2 a Cell, banda wata damuwa, saboda me? Saboda World, sosai yake batar min da duk wata damuwata. Baba bai zo ba, bai kuma ce a sakeni ba, so ba ranar fita daga wannan wurin.


A kwana na ukun ne Ina zaune kawai naga wani kurtu ya lek'o yace "kai Dan Gidan Zaki fito" mamaki ya cikani, to Baba ya hakura kenan, ya sa an firdoni, tashi nayi na fita sai ganin Dogarawa fiye da uku tsaye da dorinarsu.


Dogarawan nan suka tisa k'eyata bayan sun sanar dani cewa mai Martaba Sarkin Katsina ke nema na. Motar Emirates muka Shiga Har Fadar Sarki dake K'ofar Soro, wani dogaribya fara shiga bayan Mintuna Goma sai gashi ya dawo yace mu shiga.


Ina Shiga Fadar gabana ya fadi, ganin Dalo durk'use gaban Fada, daga gefe kuma Baba ne da Aunty Shafa, sai Hudu da Annah, sai wata da ke Durk'ushe tana ta bayani ta bawa Fada baya".


Muryarta kawai ya ankarar dani ko wacece.


"Nene ce".


Kwakwalwata ta fahimci cewa Nene ce dai ta kawo Baba k'ara.
****


Tun bayan dawowar su Nene daga Gidan Zaki ta rasa sukuni, bata da wani madafa ga shi Zaidu kamar yayi kuka wurin rokonta a kan kar ta sake zuwa Gidan Alhaji Zaki. Bata san ya zatayi ba har kwana 2 suka shide bata da wani dabara, duk tayi sukuku, bari ta kira Seebinta ko zataji sanyi.


Zuwa yanzu Nene ta iya kiran Mutanen London a waya da taimakon hotunan su wanda Zaidu Bawan Allah ya sa a jikin ko wani Contact, Hoton Seebi ta lalubo cikin contacts din ta danna kira don tana da kudi fiye da Dubu 10 cikin wayar duk don kiran Mutanen London wanda Zaidu BawanAllah ne ke sawa".


"Hellooo Neh-Neh" taji muryarshi
Da sauri tace "Dunkum. Kai na kira?" Ta na mai dauke wayan daga kunnenta tana sake duba screen din don ganin wa ta kira kuma dai hoton Nasibar ne.


Mur ta sha kamar yana gabanta tace "kai dallah ba mai wayar wayarta". Dan daria yayi yace "Neh-Neh kinyi missing dina ne? Baki nemeni kwana biyu ba".


Yau bata da lokacinshi cewa tayi "kai Arr, ina Nasibar?" Dan daria ya sakeyi yace "Sunje wani Birthday Party ita da Yarona".


Tsaki Nene tayi tace "Wani yace ba yaronka bane? Rasa kunya beran kitchen, kace ta kirani in ta dawo".


"Wai ya Neh-Neh yau sai gwasuleni akeyi? Wai ba mun shirya ba? Ai mun bar fada ko? Ko yau kin tuna kanki a Airport ne wurin masu Red din Kunne" ya karashe yana daria.


"Wallahi Dunkum ubanka zanci"


Guntun tsaki yayi yace "kinga Matsalarki ko Zagi? Wai ba Uncle Zaidu ya hanaki Zagi ba? Barin kirashi in gaya mai".


Da sauri ta katseshi "kai dallah tsaya kaji, ka tuna Hajia Maryama Mamarsu Takwaran Zaidu BawanAllah da Dalo?".
Rafeeq yace "Eh na tuna kawarki da kike bamu labarinta, me miki Wanki a Makka".


Cike da jin dadi tace "Good, good Dunkum, to wallahi Mijinta ya mata Saki Uku, ya mata dukkan tsiya gaban Mutane" nan ta shiga bashi labari kamar a gabanta akayi, har zuwa zuwanta na farko da dukan da ta ma shafa, da kulle Danmakaho da akayi da zuwan su karban bailing dinshi".


Ran Rafeeq ya baci, wai yaushe mutane zasu bar zama Victim din Matar Uba? Karon shi da Saude ya tuno, abubuwan da tayi da yanda ta shiga tsakaninshi da Mahaifiyarshi ya tuno, guntun tsaki yayi yace
"Neh-neh Wai are Women Selfish?".


Nene tace "Uwar me? Hausa zakai man dallah".


Tsaki yayi yace "Neh-neh tunda Baban bai dubi Girman Daddy ba ya ci muku mutunci, ai yana da magabata, in ya fi karfin Magabata ai bai fi karfin Hukuma ba, in ko yafi karfinsu bai isa ya fi Karfin Baban Kowa na Katsina ba".


Nene tace "Sarkin Katsina".
Rafeeq yace "Shine Magana kawai, Neh-neh ba tare Kukaje Makka da Amaryar Sarki ba?".


Nene cikin Jin dadi tace "ehmana dakin mu daya da matar sarki da Maryama".


Rafeeq yace "ki samu ganinta ta miki hanya kawai".


Allah Dunkum? Yace "wallahi kuwa"
Tace "Zaidu Bawan Allah ya rokeni kan na fita daga harkarsu wallahi".
Rafeeq yace "Nene sharesu wallahi, ki taimaka musu, ni na san sharrin Matar Uba, DonAllah kar ki karaya".


Cikin Samun Karfin Guiwa tace "tankiyu Dunkum, i lobiyu, i miss you Dunkum".
Yace "Yeah Right i miss you too My Amazing Granny".
Ji yayi tace "Uwarka ka zaga"
Tsaki yayi yace "kina da damuwa wallahi, ke fa kika fara turancin, kuma in an miki sai ya zama laifi?"
"Oho dai kace ma Matarka in ta ga dama ta kirani" dif ta kashe wayar.


Ta yanke Hukunci, Washegari karfe 8 na safe tafita, bata gaya ma kowa ba balle a hanata, ko driver bata bi ta kanshi ba ta samu A daidaita Sahu ta hau sai Gidan Sarki, Part din Gimbiya, aka ma Nene iso, bayan wasu mintuna Gimbiya ta fito, aiko ta rungumo Nene, suka gaisa cike da mutunta Juna.


Nene tace "mai Martaba na nan? Shi nazo gani? Ko yana da bak'i?" Gimbiya tace "ko da bak'i ai zai ga Nenenmu ina fatan Lafiya?"
Nene tace "k'aran Sakaran Mijin Maryama na kawo".


Gimbiya tace "wani abun ya sakeyi? Ko sati biyu baayi ba da Maryama ta zo nan maganar rik'on yaya wai don ya saketa sai dai su bita".


Nene tace "kinji Gilu ko? Ashe kun ma san da maganar, to shekaran jiya wacchan naje Gidan, naga matar da kanenta da uban sun mishi taron dangi sai bugunsh suke wai bayan nan kuma ya kulleshi a Police station, ke cin kashi kala kala ake musu a gidan nan, nace aiko suna da Gata, shine na garzayo don Ganin Mai Martaba". Gimbiya ta mik'e tace barinje in mai bayani.


Bayan Sarki ya saurari Nene ya aika a Kira Mishi Alhaji Ali Zaki da Iyalanshi Gabaki daya, sannan ya tura Police Station a sako Zaid.
Wannan Kenan
*****
"Aa Allah ya kara ma Imani, Matata suka tarar mawa, Nene kuwa harni ta tsokale wa ido" Nene tayi karaf tace "ba gaskia bane, kaine dai kuka taran mashi, ni ina ni ina dambe? Ina neman shekara Saba'in da dori? Ta ya tsohuwa kamata zata iya Dambe da kai da wanchan matashin da kuma Matarka? DonAllah Mai Martaba duk wanda yaji wannan ai ya san karya ne".


Duk da ina cikin tashin hankali sai da na murmusa da jin zanttutukan Nene. Bayan Sarki ya ji bayanan Nene da kuma na Baba da na Shafa'atu, aka min tambayoyi aka ma Dalo tambayoyi Sarki ya yanke hukunci.


"Alhaji Ali Zaki, wannan ya zama karo na karshe da zamuyi zama kanka da yaranka, na saurari komai, na fahimci komai, ba ruwan Matarka da Yaranka, ba ruwanta da su, ke shafaatu ba ruwanki da duk abunda zai ma yaranshi, ba ruwanki da hanashi, ba ruwanki da sa shi, na miki iyaka da su, yauwa ba kuma da k'ayyade musu abincin cinsu, gidan ubansu ne, yana iya sakin ki, amma bai iya sakinsu, kina jina?".


Shiru tayi bata amsa ba, bata ankara ba sai jin Dorina tayi a bayanta, wani irin bank'arewa tayi tare da sakin ihu, haka wannan dogarin ya sake shada mata a baya yace "kinji ko ba kiji ba?" Da sauri tace "naji wallahi, wallahi naji".


Hankalin Alhaji Ali ya tashi amma ba abunda zai iyayi da ya wuce sanya ido, Sarki ya ja ma Baba kunne sosai, kafin ya tambaye in akwai mai magana.


Nace ina da magana "Masters nakeyi, saura kwanakin da ba su wuce 3 na fara jarabawa, Baba yayi freezing accounts dina, ya kwace duk wani abun da ya bani, ya hanani komawa don kammala karatuna".


Sarki yace "Alhaji Zaki hakane?" Baba ya fara in ina yace "Wallahi Mai martaba, ba kudi ne, amma inshaAllah da komai ya daidaita zan maidashi".


Sarki yace "to madallah, duk da zaiyi wuya ace kai baka da halin maidashi karatu ba damuwa bane wannan, indai be rasa ci da sha ba to komai mai sauki ne, wannan tsakaninku ne, ku tashi ku tafi, ku kuma in akwai wani abu kuna iya zuwa Fada ku sanar dani, akwai mai magana?".


Baba yace "eh ni, mai Martaba, donAllah ace ma wanchan Tsohuwar kar ta sake zuwa man gida, tayi nesa da iyalina donAllah, ayi mata iyaka da Gidana". Nene ta murmusa tace "indai Gidanka ne ba zan kara zuwa ba".


Murmushin da takeyi ne ya fadar ma Baba da Aunty Saude Gaba, ba su yarda ba, wannan tsohuwa akwai bariki".


Sarki yace "to Madallah"


A haka ya sallame mu, ko ba komai Nene ta kwatar mana yanci ta siya mana mutunci, ta nuna mana muna da sauran gata.


Nene ta rik'e hannuna da na Dalo ta ja mu waje tace "ku je Gida, da kunga abunda bai muku ba ku kirani, ka kula da kanwarka" sosai hankalinmu ya kwanta.Nene ta tsaida abun hawa tayi tafiyarta Gida abunta.


Mu kuma da Motar Emirate a ka maidamu Gida, ba wanda yace ma kowa komai sai ni da Dalo da ke fira jefi jefi.


A ranar Baba yaje Gidan Alhaji Lema don kara ja mishi kunne kan Uwarshi, lokacin sun fito daga Masallaci shi da Abbii(baban Nasiba) a nan ne ma ya san Mamarshi na wani Case, shi kuma Alhaji Lema a nan ne ya san cewa Nene taje Gidan Sarki, hakuri Abbi ya ba Baba. Nan suka shiga tattaunawa tsakaninsu.
Abbi yace "wallahi ko me zaa ma Nene ba zata fita daga harkansu ba, oh Allah Nene ita bata damuwa taje ta siya fada da kudinta".
Alhaji Habib yace "kawai Zaidu gobe ya wuce da ita Kaduna kawai, ta dan kwana biyu chan".


Abii yace "anya zata yarda ta bishi?
Alhaji Habib yace "wannan kuma aikin Zaidu bawan Allah ne". Dariya sukayi baki daya.


Da kissa da kissina zasu bar Gidan ba tare da sun sake waiwayan gidan sarki ba, ki kulla makirci da duk wani sharrin da zaki iya musu, fadan ba naki bane, ya zama na Uba da yaranshi, ke kawai ki zama 'yar kallo. Hudubar yar rabi kenan da tazo Gidanta, haka kawai zatayi dole tayi taka tsantsan bata son duk abunda zai sake hadata da gidan Sarki don ta ji Dorunar nan, ta san me zatayi. Da kansu zasu bar Gidan baki alekum.


SAI DAI ME?


Rayuwa ta cigaba mana, ba dadi, ba mu taba waya da Mancy ba tunda ta bar katsina, tunda na dawo ni ke shiga kitchen in dafa Abincina, ban yarda na ci abincinsu ba, wani community school Baba ya maido Dalo wai be da kudin biyan makarantar da take a da, amma kin san me? Chan ya maida Annah, ga hudu da ke fantamawa cikin Motocin Gida ni ko nawa kallo.


In naji Bakinciki kamar ya kasheni, na kanje dakin Haruna na shak'a World, a hankali na dinga taba Sigari har ya zame min jiki, a rana sai in sha kara fiye da biyar, komai ya cigana da wakana Babanmu na fiffita Bare kanmu, kashi ya fimu daraja, banda Abinci da wurin kwana ba komai na Babanmu a wurinmu, ke sai yazo ma na daina damuwa da komai, na daina shakkun Baba, na fetsare, na koma abota da su haruna na zama wani dan jagaliya, na koma Taraiyya da yan Bencin Eskaley. World din na batar min da duk wata damuwa, sai likafa ta cigaba sai in zuqi World na bi da kwalin Sigari guda, to fa Sigar Zuk'i daya nake mishi ya kare na cillar na kunna wata, shiyasa suke ce min Mankasssss...


Ke kwatsam wata rana ina daki Dalo ta shigo dakina Hankalinta tashe, tana kuka wai ance mata ina shaye-shaye, ni abokinsu Eskaley ne. Hankalina ya tashi bana so ta taba ganin wannan side din nawa, nima kukan na sa nace mata "wallahi zan bari, ba zan karaba". Da kyar na samu tayi shiru na lallasheta. Rakata nayi har dakinta a cikin Gida, tausayinta ke kamani, duk ta fige ta lallace ta kuma yi duhun bak'i".


Nazo wucewa daidai dakina na da na ji muryar Hudu na cewa "eh na saka mai a karkashin katifar shi" sai na ji Aunty Shafa tace "Yauwa kawai ai shi ya dauke su" sai kuma suka sa darian shewa.


Kafadu na na daga, ba su dameni ba, na wuce dakina da ke baya, na dauko ragowar World na zuk'e, na zauna ina recieving current din da World ke bani a lokaci daya ina busar sigari, ina jina a gajimare naji an banko kofar Daki.
Baba, da Anty Shafa ne, a dage na kallesu na watsar na cigaba da bankan Abuna".


Cike da hargowa Baba yace "Kai DanMakaho, ina Sarka da yan kunnen Zinarin Matata da ka shiga ka sace a dakinta?" Duk da Maganar ta buga zuciyana ban dago na kallesu ba na cigaba da busar Sigarina".
Aunty Shafa ta fara kukan munahinci tace "wallahi da idona naga ya fito dashi daga dakina, na mishi magana kan ya bani abuna ya min zagi ta uwa ta uba, shime nace ni ba zanyi komai ba balle ace ban kyauta ba, bari kai ka dawo tunda kai ka haifeshi sai ya baka".


Wani murmushin bakinciki nayi wanda ya sa na zuk'e ragowar Sigarin, ido na ya kada yayi jazir, amma dai tak bance musu ba.


Cin kwalar rigata Baba yayi "Danubanka yana ina? Hudu duba min dakin nan".
Don rainin Wayau Hudu ya daga Katifata kawai sai ga sarka da yan kunne? Kutumar.
Wai sai suka shiga rafka Salati.


"Wallahi kai ba dana bane ba, ni ban haifi Barawo ba, Maryama ta dade tana haintata, cikin shege tayi ta lakafa min Da, ashe Barawo ne, Allah ya isa tsakanina da Maryama, ta sa na raini Barawo, shege dan shegia, Allah ya isa na, Allah ya tsine ma Maryama".


Da sauri na kwace kaina nayi hanyar Fita.


Muryar Makirar naji tana cewa "dama Alhaji baka san DanMakaho Shege bane? Be da Uba, kai a ka dauka sakarai a ka lakafa maka shi, kai kuma ka raineshi tsakaninka da Allah".


Wani kukan Kura nayi na finciko hannun Baba na tillashi waje, kafin su ankara na sa mukulli na kulle Dakin, kafin ta farga da me nake niyyan yi na ciro Charger Laptop dina na dinga laftarta ta da shi, ihu takeyi na sa k'afa na tande kafafuwan ta, shi ko Baba daga waje Hankalinshi a tashe yana ta kokarin budewa, ya rasa yanda zaiyi.


Sai da nagaji da kaina na kyaleta, duk tayi laasar, fuskarta tayi suntum, wannan shine ba a rabu da bukar ba, ita zaman shekara 15 din da tayi ba wai don ta zo dan Miji na dukanta bane, ita bata ma ga wani chanji ba, bata ga ribar shekarun da ta dauka ba, zuwa zatayi ta samu Er Rabi dole a sake sabon Zama.


Ni ko na kyasta Sigarina na hau busawa, bude k'ofa nayi na bi ta inda Baba ke tsaye cike da tashin hankali, ya na ko ganina ya hau la'anta ta.


"Allah ya tsine maka DanMakaho, Allah ya watse maka Karama, Allah ya kwashe maka Albarka, Allah ya laance ka" ya dinga tsina na.
•••••


Kalar kukan da Labiba keyi ne ya sa shi tsaida labarin, murmushi mai cike da tarin takaici da bakinciki yake yace "Kefa kika dameni da na baki labarina, kuma da na fara sai kuka?".


"INA SONKA"


Ta tsaida duk wata na'urar da ke jikinshi daga aiki.
Da kyar ya iya lallubo kalmar "Sha biyu Saura, dare yayi sosai, tashi muje na rakaki Gida".


"DAGASKE, Ina Sonka".


Cikin ido ya kalleta ya hango tsantsar Gaskiarta tsakani da Allah, wannan wace iri ce? Wace kala ce cikin Mata? Ya san ba da dabi'ar 'yan arewa, don babu wata 'yar arewa da zatayi abubuwan da Labiba keyi, ba 'yar arewa mai ajin da zata kalli Namiji gatsau haka ta gaya mishi kalmomi masu tsada, dauke kanshi yayi sakamakon binshi da wani kallo da takeyi.


Ba tare da ya kalleta ba yace "Its Late, ki tashi na rakaki Gida".


Hawayenta ta goge ta mik'e tsaye yayi gaba ta bishi a baya, da hasken Torchlight ya haska

Please Login or Register in order to submit comment