Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida to yaje chan Asalinki ya nemi aurenki ba mu son dogon soyayyan zamani".


Tunda ya fara magana ta sadda kanta k'asa ta ji zuciyarta na wani irin zugi, Aure? Aure? Da wani ba Zaid ba? Ya Illahi. Sai da ta tabbatar yayan ya gama magana ba tare da tace komai ba ta tashi ta shigewarta daki, Aunty Asee ta k'ara da cewa kasan amincewar Yanmata masu kunya shine tashi ba tare da sunce komai ba".
Yayan ya murmusa yace "MashaAllahu, bari dai yazo muji".


Jawad kam yana barin Gidansu Labiba ya wuce Gidan Uncle Usman gidan 'kanin babanshi, Aisha tace "Ya Jawad fa tun dazun ka iso sai yanzu muke ganinka?" Antisco tace "sai da yaje ya ci girkin diyata" Jawad yayi murmushi yace "kyaleta Antisco, so take na fara ganinta kafin naje na ga matata?" Aisha tayi shewa tace "Allah ya baku hakuri yaya, shegia Besty an samu Miji a sama" harara ya zabga mata yace "wallahi ki kayi wasa sai na ma Yaya Majeed budurwa" hararar ta rama tace "shi kuma makaho baya iya budurwa da kanshi sai ka mashi?" Antisco dai tayi ta daria, sai da ya huta kafin yaje gidan Kakansu ya gaidasu kafin ya tafi masauki, yayi sallahr Maghrib ya jira Isha'i kafin ya kira Labiba yace gashi nan zuwa.


Tunda ta bar Gidan Alhaji Ali Zaki ta koma gida ta kulle knta a daki take ta riskar kuka, ranta a jagule, ta isa gida cike da tashin hankali, yanayin da ta gani a tare da Zaid dazu, yanayin da ta dade take buri ta ganinshi a ciki amma a dalilinta, ta dade tana mafarkin Zaid na Kishinta, Zaid na shiga yanayi a dalilinta, Sai gashi yau a gaban idonta Zaid ya shiga yanayi ta kan ‘yar karamar yarinya da take aji 1, yau Zaid dinta ke kishin wata ba ita, Allah ka kawo mata sauk’i, Allah ya yaye mata wannan damuwa nata, Allah ya iyakance mata Son maso wanin da takeyi, rannan taci kuka har ta gaji.
Er Rabi ta sameta tana kuka sosai hankalinta a tashe take tambayarta waye ya sa ta kuka, wani mai gangancin ne ke sanya tilon diyarta kuka.
Tarayota gabaki daya tayi jikinta tace “Baby me ya sameki? Me aka miki? Waya tabaki?”.


Da kyar ta samu tayi magana, “Mummy Zaid ba ya sona, ba ya sona Mummy, duk son da nake mishi be sona sai wata yarinya wanda da kyar ta kai shekara 17 a duniya, mummy ni Zaid zai ma haka? Bayan duk abunda na mishi?”.
Tuni Er Rabi ta shiga huci kamar Zaki tace “donuwar Dan Makaho ke zai ma haka? Don har yanzu na barshi yana jan numfashi a doron kasa, saboda kene fa baby, saboda ke, amma har yana iya yaudararki? Ya zabi watan ki? Lallai Dan Makaho, wannan shine babbar kuskuren da ka tafka a rayuwa, sa yesmin kuka shine ajalinka”.


Wani tsalle Yesmin tayi ta duro gaban Mamarta tana haki tace “Mummy, wallahi aa, kar ki sake, kar ki taba yin wani abun da zai taba min Zaid, kar ki sake wallahi, wallahi ki ka taba Zaid wallahi daidai yake da rasani, Mummy kikayi ma Zaid wani abu ba zan taba yafe miki ba kuma sai na kashe kaina”.


Da sauri Er Rabi ta girgiza kai tace “aa baby, ba ma zai kai ga haka ba, ina kokarin kare matabanki da cin mutuncin da ya miki, ba zan dauka ba, ba zan iya dauka naga ana saki kuka ba Yesmin”.
“Mummy ina mugun son zaid fiye da kaina, rayuwana na cikin garari in har Zaid ya mutu ko ya bace, ba zan iya rayuwa babu shi ba, shine farincikina, Mummy ina sonshi fiye da rayuwa da kanta”.


Kalaman Yesmin sun fara ba Er Rabi tsoro, tana tsoron irin mutuwar son da diyarta ke ma mak’iyin aminiyarta, wannan lokacine da zata zabi farincikin diyarta ko kuma na aminiyarta.
Lallashin Yesmin ta fara yi, da k’yar ta samu tayi shiru, tace “zan baki wani kwalli, ki shafa in zakije gidan Shafaatu, da kin hada ido da shi, zai ji duk duniya bai da abunda yake so sama dake, zai so ki fiye da uwar da ta haifeshi”.


Yesmin tayi murmushi tace “Mummy, bana bukatar irin wannan Son daga gun Zaid, ba na son kazamar soyayya irin wanna, bana son kyamataccen so irin wannan, bana so Zaid ya so ni ta hanyar nan, ina So Zaid ya so ni daga zuciyarshi, da niyyarshi da yardanshi, Mummy Zaid ne farincikina, farincikina shine farincikinshi, in kuma kina son ki ganni cikin farinciki kar ki sake yi ma Aunty Shafaa aiki a kanshi, shi kuma farincikinshi itace Labiba? To bari a samo mishi farincikinshi” magana Yesmin kawai takeyi kamar baa hayyacinta ba.


Er Rabi kallon diyarta kawai takeyi cike da tsoro, fargaba da mamaki, ya zaayi diyarta ta ma wani mahaluki irin wannan Son? Ta yaya? Kuka yazo mata da sauri ta fita daga dakin Yesmin ta rufe tana fargaban rasa diyarta.


Lokacin da Jawad ya iso Gidan Mallam Muhammad ba wuta a Gidan, kuma basu da Generator, amma gidan babu duhu saboda hasken Gidan Alhaji Zaki ya shigo tsakar Gidan, ga kuma farin wata, ga kuma rechargeable lantern.
Yaya Muhammad ya tarbe Jawad don Labiba na cikin daki Aunty Aseey ta tsareta kan sai ta chanza wanka da kwalliya, to tayi wankan shafa takeyi.


Zaune suke a kan Carpet daya, Yaya Muhammad yace “Mallam Jawad ka ga Gidan sai duhu, sai hakuri” kan Jawad dai a k’asa shi bai ma san me zaice ba, yo shi ina ruwanshi da gidansu tunda yarinya yake so?.
Baban Amira yace “Yaya sunanka? Kuma kai dan ina ne?”
Jawad ya hadiya kafin yace “Sunana Jawad Abu Shamsu, ni ne na uku a gidanmu, ina da yayyi biyu da k’anwa daya, iyayena ‘yan Unguwar Alkali ne a nan garin amma muna Abuja zaune, ina aiki a wani Company kuma ina bussiness”.


Baban Amira ya jinjina kai yace “Mallam Jawad naji tak’aiceccen tarihinka, to an dai san wata alakar mace da namiji wanda ba muharamai ba bai wuce aure ba, amma duk da haka ina son ji daga bakinka, mai ke tafe da kai? Meye k’udurinka a kan kanwata Labiba?”.


Jawad yace “Ni Sonta nakeyi da aure, kuma na ma gaya ma Mamana”. Baban Amira ya murmusa daga jin shi ya san akwai shagwaba a tattare da shi Auta ne, yace “Yaron Mama, Mama za ta maka aure yanzu?” Murmushi yayi don yaji alamun zolaya a tare dashi.
Niyyar tashi baban amira yayi yace “to dai duk yanda kayi da manyanka ka gayama Labiba, sai ta gaya min sai kuje chan gida Edo, don uwayenmu na chan”.


Jawad yace “InshaAllahu, nagode kwarai Yaya”
Baban Amira yace “Mu ke da Godia munga dawainiya”
Jawad ya sadda kai k’asa yace “bakomai”
Daki ya koma ya kira Labiba.
Labiba ta fito rike da Amira da Sabit suka iso gaban Jawad, gaishe shi sukayi, jawad ya dauki sabit yace “dazun nazo kuna hadda”.
Sabit ya gyada kai yace “Eh, kuma munada Chakulats da yawa”.
Ameera tace “Sabit ummi tace mu gaisheshi mu koma daki, tashi mu tafi”.
Mak’e kafada yayi alamun ba zaije ba.
Labiba tace “yi tafiyanki amirori barshi”
Amira ta ruga ciki da gudu.


Jawad ya maida hankalinshi dungurgum wurin Labiba da ya lura da chanjinta, ya lura da yak’en da takeyi, amma tayi iya k’okarinta na ganin bai fahimci akwai wata damuwa ba.
Fira suka danyi ba yabo ba fallasa yace “gobe so yake yazo da safe kafin ya tafi”
Allah shi kaimu kadai ta ce.
Har Sabit yayi bacci ta dauke shi ta kaishi daki saboda sauro ta dawo, su ka dan zauna na wani lokaci.


Hamman k’arya ta fara yi yace “bacci ko baby?”
Ta gyada kai tace “eh wallahi Jay, ga kuma sauro”
Shima ya gaji don sauron sun cijeshi.
Yace “to barin in tafi InshaAllah zan zo muyi Sallama k’arfe 10 gobe”.
Tare suka mik’e tsaye, wanda yayi daidai da fitowar Zaid wanda yanzu ya tashi daga baccin asaran da ya sha ba mangariba balle ishai, fitowarshi yayi daidai da dawowan wutar lantarkin da ya karade Gidan da haske.


Idon Zaid kansu, idonsu kan Zaid wanda yake sanye da dogon riga kawai, babu riga har ana ganin saman boxers dinshi.
Da sauri Labiba ta kauda kai, shi ko Zaid zuciyarshi ke ingizashi kan ya je ya nakada musu duka dukansu biyun.
Tafiya ya fara yi yana doso su, nan da nan cikinta ya duri ruwa, me Zaid zai shigo gidansu yi? Mai zai ma Jawad, me zata ce ma Yayanta meye hadinsu da shi? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun.


Zaid ya k’etaro Gidan Mallam Muhammadu bai tsaya a ko ina ba sai a gaban makunnin hasken lantarkin Gidan dake daidai k’ofar dakin Labibar, hannun shi ya sa ya KASHE FITILAr.
Ya sake wuce su ya koma gidansu ba tare da yace da kowa komai ba.


Kallo suka bishi dashi Jawad dai ya ga abu yayi yawa ya daure yace “Baby waye wannan?”
Shiru tayi
Ya sake cewa “baby waye wannan wai?”.
Tace “Zaid ne”
Yace “Zaid”
Tace “ka tafi barin shiga akwai sauro”.
Jawad bai ja magana ba yace “Good night Baby”
Tace “Good night Jay”.
Ya juya ya bar Gidan a kan idon Zaid, ya juya ya shige dakinshi, ganin Dalon da ya so yi ya fasa.


Ita kuma Ranta bace ta kunna Fitilar Gidan ta shiga dakinsu Yaya tace ya tafi.
Yaya yace kinji kinji yanda mukayi.
Sadda kai kasa kawai tayi kafin ta tashi ta koma dakinta.


Wai meyasa Zaid ke mata haka ne? Wai meyasa yake kada mata gaba haka, wai meyasa yake nuna kamar yana kishinta, donAllah ya bari, wannan dabiar da yake yi, hakan da yakeyi yana sa ta na ji kamar tana da damar samunshi, nuna irin wannan kishin zai sa ta kasa kwantar da hankalinta ta rungumi Jawad a matsayin Mijin Aure, ta na tsoro, kar ta sa ma ranta dogon burin samunshi amma ta rasashi ta wahala daga karshe, kai bata yiwuwa, yau dole ta sama ma kanta mafita dolen dole.


Jawad kam suffar Zaid yake ta tunanowa, shine wanda Mancy ta taba aikosu wurinshi, dan Mancy ne, tabbas shine, dama baida hankali, yana shaye shaye, banza ne ba zai bari ya dameshi ba balle yayi tasiri a kanshi, nan da nan ya kawar da tunaninshi.


Karfe 11:30 Labiba ta tashi ta zura doguwar abayarta ta tabbatar kowa yayi bacci, tayi sando zuwa gidan Alhaji Ali.
Tura k’ofar dakin Zaid tayi ta sameshi a bude, yana zaune yana zuk’ar sigari.
Yana ganinta yayi saurin mik’ewa tare da kashe karan sigarin.
Kallon juna sukeyi suna k’okarin karantar juna, ganin kallon da yake jifatar dashi na neman tasiri a zuciyarta ya sata daure fuska tace
“Wai me kake nufi ne dani? Menene haka kake min, baka tashi yin wulakancinka sai ka ganni da wani? Me hakan ke nufi? Ba kai kace na fita daga harkanka ba? To na fita daga harkan ka meyasa kake son shiga nawa? Ina abunda ya kwalaka da k’asa da duk wanda na tsaya da shi sai ka so bani kunya, haka kai da abokanka kuka tozarta Abu Sideeq, kuma Zaka zo kana wasu abubuwa gaban Jay, to wallahi ka fita harkata, ba ruwanka da duk wanda zaizo wurina balle ka sani jin kunya, kar ka sake nuna fuskar ka a inda nake ka gane?”.


Ta na gama magana ta fita daga dakin bata tsaya ko ina ba sai dakinta ta rufe ta sa sakata tare da zubewa kan gado tana mamakin jarumtarta, lallai tayi kokari, ba ta fushi bata fada bata masifa amma yau Zaid ya sa tayi, numfashi take mayar wa a hankali, har ta dawo daidai, haka bacci yayi awon gaba da ita.
Shi kuma Zaid idanuwanshi na nan k’yam ba alamun bacci, world din ma kasa sha yayi ya tsaya yana nazarin kalamanta yana juyasu, sigari kadai ya iya sha har gab da Asuba inda naunauyar bacci yayi awon gaba dashi.


K’arfe 10 Jawad yazo Gidan sukayi Sallama ya kama Hanyar Abuja.
Kafin 12 rana sai ga Yasmin ta dura a Gidan Alhaji Ali Zaki.
Sai da ta shiga cikin Gida inda ta iske Amna da Anty Shafa’atu a Parlo.
Anty Shafa tace “Ke ‘yar hutu haka akeyi? Sai kawai naga wayar mamarki wai ‘yar hutuna ta koma gida, haka ake hutun?”.
Murmushi tayi din ta san bariki ne kawai don tasan Hajia Shafa’atu kwatakwata bata son zamanta a gidan don ta hana ta rawan gaban hantsi.


“Wallahi Aunty jiya na shiga wani rububi amma ai gani na dawo” yak’e kawai Shafan tayi tace “dama Kasuwa zamu, ko zaki bi mu” Yesmin tace “sai dai kun dawo, a siyo min Agwaluma” sukayi gaba tare da fadin “Allah sa mu gani”.


Dakin Dalo ta shiga suka gaisa tace “ashe Aunty Yesmin ba nan kika kwana ba” tace “eh wallahi Dalo, barin dubo yayanki ko ya tashi”.
Tace “eh ya tashi , ya ma shigo”.


Yasmin ta fita ta nufi BoysQuaters.
Sai da ta k’are ma Gidan su Labiba kallo kafin ta shiga dakin da sallama.


Yana ganinta ya mik’e tsaye tare da fadin “Yasminn”
Murmushi ta mishi tare da daga mai gira
“Yadai nawan?”
Ya mike tsaye ya matso kusa da ita yace “I am soo sorry Yas”.
Giran ta sake dagawa “forr?”
Shiru yayi
Tace “kayi wanka?”
Yace “Eh”
Tace “beyi kama da kayi wankan ba, ni fa wannan Jalabiyar sai na k’onata”.
Yayi daria ta bude wardrobe dinshi ta ga ba komai ciki sai wata Ghan Must go
Ta sa hannu ta bude ta ga duk kayyaki ne wanda baa dinka ba.
Tace “na wa ye?”
Yace “nawa ne da na Dalo”
Wani tunani tayi ta ciro wani Yard mai kyaun gaske navy blue da skye blue tace “zo muje”
Yace Ina?
Tace “bansan tambayoyi”
Hannun shi ta ja ba su tsaya ko ina ba sai cikin Mota
Horn tayi Mai gadi ya bude Gidan suka fita
MeelaMeerna Stitches ta tsaya suka shiga, ta bada Yards dinnan biyu tace “Ku auna shi yanzu ku dinke su duka”.


Zaid zaiyi magana ta harareshi tace “bana Son gardama”
Haka ya tsaya aka auna shi suna zaune kusan Awa Biyu aka dinke mishi kaya kala biyu a ka goge, ta tsaya ta sai mai Hula k’ube, da wasu turaruka, yana zaune a mota.


Ta shigo da kaya ta ja yace “Yasmin”
Ta katseshi ta hanyar cewa banson surutu
Shiru yayi har suka isa Gida ta turashi toilet tace kayi wanka wannan kayan zaka saka zan dawo nan da 30 mins.


Ta fita ta koma cikin Gida wurin dalo, baayi minti 15 ba sai ga Zaid ya shigo cikin Gida
Console din Parlon ne ya hasko mai kanshi a jikin madubu, sai da gabanshi ya fadi, mantuwa ta mance ranar da yayi shiga ta kamala irin yau, mantuwa ta mance randa ya ga yayi kyau kamar haka, madallah da Yesmin, madallah da ta tuna mishi wannan part din na nan.
Dakin Dalo ya shiga
Da Yesmin din da Dalon duk suka bude baki suna kallonshi
Yayi kyau sosai
A tare suka ce “wallahi kayi kyua”
Daria yayi yace “Dalo It was all Anty Yas dinki”
Tayi murmushi tace “na sani, thank you Anty Yesmin Allah ya biya miki bukatunki na Alheri”.


Basarwa tayi kawai tace “Muje ko?”
Da Zaid da Dalo suka hada baki suka ce “Ina?” tace “Zance Zamu”
Dalo tace “Zance? Ahh a dawo lafia”.
Daria tayi ta ja hannun Zaid suka fita daga cikin Gidan tace “kasan zai fi sauk’i in muka ketara ta nan?” Ta na mai nuna gidan su Labiba”.


Zaid bai fahimceta ba yace “meye?”
Tace “well never mind, ba zamuyi scaling ba, its illegal, bari mu bi ta gaban Gida”.
Janshi tayi, shi kuma binta yakeyi kamar wani soko.
Yaga sun wuce parking lot yace “motar fa?”
Tace “inda zamuje zance ba sai mun shiga mota ba”
Zaid mamakinta yake kawai, bata gama bashi mamaki ba sai da ya ga sun toge a kofar Gidan Mallam Muhammadu gidansu Labiba”.


Cike da mamaki yace “Yesmin me mukeyi a nan?”
Murmushi tayi tace “Zance mu ka zo”
“Zance wani irin Zance?”
Ba ta amsashi ba, sai kiran wani Almajiri tayi tace shiga gidan nan kace ana sallama da Labiba a waje.


Tana Kallo ita da Aunty Aseey yara na makaranta suka ji ance “wai ance ana sallama da Labiba a waje” Labiba tace wai “inji wa?” Yaron yace “ni bansani ba su biyu ne dai” Labiba da mamaki tace “ko wanene?” Aunty Aseey tace “sai ki tashi kije ki duba”.


Zaid ya juya da sauri zai koma Gida ta yi saurin shan gabanshi tace “Rai na ya baci jiya, amma zai fi baci yau in ka tafi ka barni tsaye ni kadai anan”.
Zaid ya juyo gareta cike da tausayawa yace “Yasminnn, yasmin you are hurting yourself”
Tace “ban san surutu, bansan gardama, ban kuma son tambaya” ta ko rik’e hanunshi gam.


Daidai da fitowar Labiba ta choge ta tsaya ganin wani mai kama da Zaidu amma wannan Babba ne don sanye yake da manyan kaya, kuma wannan ya fi Dan Makaho kyau, kallon kallo sukeyi ba ma ta lura da wata a gun ba, hannu ta ga ya sa ya murji idonshi na hagu.
Zuciyarta ta kawo mata kuwa a kwakwalwarta
“Shine, wallahi Shine, Dan Makaho ne”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN DA UKU 2⃣3⃣
(INA SONKI❤)


Tare yake da wata zuciyarta ta ankarar da ita, ido ta kai wurin Yesmin da ke tsaye tana zabga murmushi, fukarta ba yabo ba fallasa.
"Labiba"
Labiba ta kalleta ba tare da ta ce komai ba.
K'amshi tace "Zance fa muka zo, haka zaki tarbemu?".
Labiba ta rausayar da kai kafin tace "Zance kuka zo? Wurin wa? Ko kuma zance kuka zo yi a gidanmu? Chan be isheku ba har sai kunzo gidanmu?".


Yesmin tayi murmushi tace "zance muka zo dai wurinki,ciki zamu shiga? Ko nan zamu tsaya?".


Tsayuwa Labiba ta gyara tare da hade hanayenta guda biyu bisa k'irjinta tace "ban gane ba? Zance kuka zo wurina? Wani irin zance kum?".
K'amshi tace "Zance irin wanda saurayi ke zuwa yi Wurin budurwa, zancen soyayya, ni 'yar rakiya ce".


Labiba da mamaki Ta juya ga Zaid tace "Kai gaya mata kayi so na kakeyi ko meye?".
Ta kalli k'amshi tace "Wanda ake so, ake zuwa zance gurinshi, nikam ba so na yakeyi ba, you got it all wrong".


Yesmin tace "ba sai ya gaya min ba ai, i got it right, sonki yakeyi sosai wanda zuciyarshi na zugi in ya ganki tare da wani, jiya munji haushi sosai da muka ganki da wani, shiyasa yau mukazo don kar mu tsaya kallon ruwa kwado ya mana k'afa".


Labiba tace "ke ba budurwarshi bace?".
Yasmin tace "kar kiyi kishi dani".
Labiba tace "aa ba zanyi kishi da ke ba, naki ne ki rikeshi kinji? Ku bar zuwa mana gida kuna mana sallama, Zan shiga gida" ta juya da sauri zata koma.


Yasmin ta yi saurin rikota tace "dagaske kar kiyi kishi dani, ni ba damuwarki bace ba, damuwata shine ki bamu dama, mu shiga cikin masu nemanki mu fafata, don ba zamu yarda wasu su dinga zuwa gunki ba, jiya saura kadan zuciyarmu ta fashe da ta ganki da wani tsaye".


Labiba tayi dariyan takaici tace "wai waya ce miki so na DanMakaho keyi?".
Yasmin tace "Sonki Zaid keyi".
Labiba tace "ba so na yakeyi ba, yana kishin ganina da waninsa ne kawai"
Yasmin tace "ashe ma yana sonki sosai, don sai abun da kake so kake yima kishi, ba ki sani ba ke yarinya ce".


Cike da zafi Labiba tace "gaskia ne, a yarintar na tareshi da k'okon barata a kan ya soni, da yarintar fa na kamu da son shi, kinsan da Allah da Annabi nake rokonshi ya soni?kinsan me yace? Cewa yayi banda Aji, ni ballagaza ce, ba zai taba son yarinya mai tallar kanta ga da namiji ba, ni yar kudu ce banda kamun kai, ni kaza ce, ni kaza ce, be san so ba, bai ma so adalci ba, in har wai don mace ta ce tana son namiji shine rashin kamun kai, to bai chanchanci furta kalmar So ba".


Yasmin ta dafe gefen kirjinta tace "kiyi hakuri, bamu kyauta ba, mun gane kuskurenmu".
Bakinciki ya turnuk'e Labiba da ta kalki Danmakahon da ke tsaye kamar ya tsohon soja ba motsi sai binsu da kallo da yakeyi daya bayan daya.
Tace "kurma ya koma? Be iya magana? Kinga hakan na nufin zuwanku nan ma was all your idea, ke kika tilastashi yazo, wannan zuwan naki ne, so donAllah ina ganin girmanki Aunty, kar ki sake zuwa min da irin maganar nan, ni dai DanMakaho na dade da yakice shi a zuciyana, babu wani abu tsakaninmu da ya wuce makwaftaka".


Kafin Yasmin tayi magana, tuni Labiba ta shige Gida da sauri ta maida k'ofa ta rufe.
Yasmin ta Zabga ma Zaid harara tace "wai kai wani iri ne? Kaga abunda ka ja ko? Kai da zaka lallasheta a wuce wurin amma ka tasamu gaba kana ta kallo kamar wanda ya samu Tv? Haba?".


Tausayinta ya mamayeshi, ba komai ya sashi kasa magana gaban Yesmin ba sai jim nauyinta da yake da kuma girma da darajan da take dashi a idonshi ya kasa ce ma Labiba komai, ai ana barin halas don kunya.
Yace "Yass, ba sai kinyi haka ba donAllah, kina ba kanki wuya, nifa wannan yarinyan ba abunda kilke tunani bane, 'yar karama da ita me zanyi, kawai kinsa yarinya ta gama mana rashin kunya".


Yasmin tayi wani guntun murmushi tace "kamar na chanchanci sanin gaskiar lamarin nan, na tafi Gidanmu".
Gaba tayi yayi saurin binta a baya yana kiranta amma tayi banza ta kyaleshi, har ta bude mota tayi shigewarta ta tafi Gidansu ranta na k'una da zafin jarumta irin na abunda tayi don neman farincikin abunda takeso, tuk'i takeyi har ta isa Gida.


Labiba na shiga gida ta rufe k'ofa tare da jingina jikin k'ofa tana mayar da numfashi, ba namijin kokari tayi ba wurin gaya musu magana, duk da bata tsoron magana gaban ko waye amma Zaid daban ne, shine weakness dinta.


Ta na jin Yasmin na mishi fadan ya zo yay tsaye ya kasa magana, ta na jin ansar da ya bata ma cewa ita yarinya ce ba abunda zaiyi da ita, k'wallah ta matse da ta ji muryan Aunty Asee na tambayarta waye ke sallama da ita "wani dan ajinmu ne" tayi k'arya, ba ta san meyasa ba in dai kan Dan Makaho ne, to ta zama expert wurin k'arya, jiki a sanyayye ta shige daki.


Maimakon ya shiga Gida, sai ya wuce center, shiganshi Gida ya san World kawai zai taba, duniyar ta juya mai, yana dauke da damuwa, zafi biyu, yana so ya yi clearing kwakwalwarshi, tafiya kawai yakeyi zuciar shi na ga Yasmin don ba ta Labiba yake ba.
Ba ya son yanda take k'untata ma kanta kawai don ta burgeshi ko don ya samu farinciki, kwatakwata baya son yanda take zaban farincikinshi kan nata, hakan ba adalci bane.


Wayarshi ya dauka a aljihu ya kira Yasmin din kamar ba zata dauka ba ta dai dauka tare da fadin "Yadai?"
Yace "donAllah ki dawo"
Tace "me zan maka Zaid? Baka yarda da ni ba, ban san komai game da zuciyanka ba, to wani irin zama kake so muyi? Baka yarda dani ba, ta yaya kake so na taimaka maka".
Numfashi ya ja yace "na san baki isa gida ba, DonAllah ki dawo, ina son miki magana, zan jiraki bakin gate".
Dif ya kashe wayarshi.
***


Da ta ji Gidan Shiru ta san cewa ba kowa, mutanen gidan sun fita, Fitowa tayi don ta gaji da zaman Daki, sanye take da riga da skirt na material, ba ta daura dankwali ba saidai ta yafa shi a kanta.
Parlo ta shigo tare da kunna TV ta kamo tashar ZeeWorld.
Daga Daki ya fito, ba aikin fari bare na bak'i, bacci ya tashi, idanunshi suka sauka kanta, ya san ba kowa a Gidan, zuciyarshi ta raya mai wani abu, ba ta san da fitowarshi ba, takowa yayi har gabanta tare da zama kusa da ita ji tayi kamar an jingina da ita, da sauri ta waigo ta kalleshi, zumbur tayi zata mik'e yayi saurin mayar da ita ta zauna, tuni jikinta ya duri ruwa, tuni jikinta ya fara rawar mazari.


Da wani murmushi mai sa kuka ya kira sunanta "Dalo".
Kasan motsi tayi sai rawan da Jikinta keyi.
Sake yunkurin tashi tayi a karo na biyu ya sa hannu ya janyota tare da zuba hanayenshi kan cinyoyinta biyu.
Murmushi yake mata "Dalo, wai meyasa kike dari dari da ni? Ni ba uncle dinki bane, ki saki jikinki dani, zan zame miki gata a gidan nan, i will do anything you want" Murmushin da yakeyi ne ya na daga nata gira ya sata fashewa da wani kukan bak'inciki.
Da sauri ya tariyota jikinshi yana fadin "Oh No Dalo, kar kiyi kuka? Uncle Hudu ne ya saki kuka? To zan hukunta shi kinji?

Please Login or Register in order to submit comment