Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan mu bashi sak'on be dauka ba" "Oh Allah, sorry na wahalar daku, ko ku barshi" Majeed yace "haba Mancy, har muzo gari kuma mu juyo da sak'o? Ba wani abu bari na sake kira InshaAllah zamu sameshi".


"Nagode sosai, bari nima in kira k'anwarshi in ba ya nan sai ta amsa" nan suka katse wayar.
Tudun Matawallen suka nufa kamar yanda Mancy ta gaya musu.


Majeed be fasa trying numbern shi ba, Jawad har ya k'ulu, shi fa be son bacin lokaci, tsaki ya sake yi, shi ba Fan din Mancy bane, be kuma k'inta, kawai dai bata cikin 'yan kayanshi kamar yanda yayyunshi biyu ke yinta.


Sun fi minti 10 a cikin Tudun Matawalle basu san inda zasu ba, sake kiran Mancy Majeed yayi tace "kuyi hakuri, wallahi wayar k'anwar tashi kashe take, na kuma ta kiranshi be dauka ba wallahi, kuyi tafiarku kawai Majeed".


"To Mancy ya sunan Maigidan sai muyi sallama mu bada a ajiye musu" dan jim tayi na wasu sakwanni kafin tace "kawai Majeed ku dawo ba wani abu" ba ya so ya matsa sai cewa yayi "to Mancy, amma banji dadi ba" ya kashe wayar ya ce masu "tace a bari kawai, amma banji dadi ba wallahi".


A k'ufule Jawad yace " to ya zamuyi, nan zamu lallace? Ya Hafiz mu tafi please" ta Mirror Hafiz ya kalli k'aninshi da harara yace "Jawad!!!" kawar da kai yayi, Hafiz yace "Majeed sake kira" Majeed yace "for the 14th time, Allah ka sa ya dauka".


Bencin Eskaley


World DanMakaho ya zuk'a, sarauta ta sa mai, k'afa daya kan daya ya daura, yana kallon kowa a dage, me tsautsayi kawai zai shiga harkanshi yau, yanda yake jin kanshi tsaf zai kakarya mutum.


Master da su Haruna ke buga Whot, suna yi suna busar sigari, yau ma basu da arzikin siyan World,sunyi ma Eskaley Magiya amma fir ya k'i basu".


"Wai Mankas ba wayarka ke k'ara ba tun dazun, kusan so 10?" Haruna yace "yo ina zai iya dauka, World fa ya ta6a" Master yace "yo in baka dauka ka kashe shegia mana, ni nan ta cikan kunne"


Tsaki Eskaley ya buga ya mik'e ya nufa Mankas hannu ya sa a Aljihun gaba inda Wayar ke k'ara, dauka yayi kafin ya amsa da "Hello?".


"Eh Hello, Zaid?" daga bangaren Eskaley yace "Eh to ba Zaid din bane" daga dayan bangaren a ka ce "DonAllah gamu a Tudun Matawalle, sak'o aka bamu daga Abuja mu kawo ma Zaid, don Allah ina zamu sameshi?" Eskaley yace "kuna ta ina?" "mun dan shiga cikin Anguwar" "Ayya, ku dawo farkon Anguwar, akwai wani kiosk nan Yellow".


Eskaley ya kalli su Master yace "Daga Abuja aka aiko wasu gun Mankas, gashi Mankas na birnin Sin ya zaayi?" Master yace "to ya fa? Uban kowa ya san Mankas na eh ya ne".
Horn sukaji na wani mota bak'a k'irar 507, duk suka tashi don yau kakarsu ta yanke sak'a.


Wayar Mankas ta sake ringingin Eskaleh ya dauka " Hello? Kaine a bakar Mota? Eh nan ne, barin zo" Eskaley yayi gaba, su Master na binshi a baya.


Ta Window suke kallon masu tunakaro su, "'Yan Shaye-Shaye ne" cewar Jawad "Mai ya hada yaron Mancy da Shaye-Shaye?" inji Hafiz, ba su da wannan amsar illa fitowa da sukayi gabaki dayansu.


Musabaha sukayi da dukkansu harda Jawad da ya mik'a musu hannu a kyamace, su ko 'yan bencin Eskaley kamar su musu Sujjada don biyayya, Hafiz ya kallesu daya bayan daya, ya lura duk ba na kirki cikinsu, duk warin Sigari suke, daurewa dai yayi magana yace "Ina Zaid?" Master da Haruna suka kalli juna suna tunanin waye Zaid? Shaf sun manta da wani Zaid".


Kafin Master yace "au Mankas? Gashi chan baya, in sak'o ne ku kawo a bashi" Majeed yace "Aa, hannu da hannu zamu bashi" Haruna yace "Ai Mankas ya hau network, ba zai gane bayanin da zaku mishi ba, mune Aminnanshi".


" DanUwarku Mahaukaci ne ni da ba zan gane bayani ba?" gabaki dayansu suka juya, Mankas ne ke tunkaro su, tuni Master da Haruna suka matsa mai ya k'araso yana k'are musu kallo duk a dage, ya tsaya kan Jawad mai kallonshi a k'yamace, Mankas ya wurga mishi mugun kallo shima kafin ya kalli su Master yace Duk ku ware?".


Hafiz ya mik'a mishi hannu, k'in amsa yayi, ran Jawad ya mugun baci, Majeed yace "Zaid, Mancy ce ta bamu sak'o mu baka".


Runtse ido yayi da k'arfi ya bude, tuni ya dawo hayyacinsa, Hafiz ya nufa da sauri ya dan durkusa " DonAllaj kayi hak'uri babban Yaya kuyi hakuri, wallahi akasi aka samu" daga yanda yake magana sun san a buge yake, yana dai k'okari ya dawo hayyacinsa ne.


Hafiz ya girgiza kai yace "Zaid, Mancy Mutuniyar kirki ce, donAllah ka bar Shaye-Shaye" da sauri Zaid yace "Wallahi na bari, ba zan k'ara dama yau na fara" sun san ba gaskia ya fada ba amma dai suka share" Majeed ya bude Booth ya dauko Ghana MustGo dan k'arami ya mik'a mishi.


Karba yayi, yace "nagode, Allah tsareku, ko uban wa ya tabaku ku gayan naci uwar mutum, duk garin Katsina, ko da kuwa Sarkin Katsina ne".


Takaici ya sa Jawad saurin fadawa Mota, Majeed ya girgiza kai yana mai fatan shiriya, shiko Hafiz da yake Ustazu ne sai da ya sake masu Mankas da abokanshi nasiha kan su bar Shaye-Shaye.


Nan suka fara mishi rantsuwar kaffara kan sun daina ba za su sake ba. Master har yana k'arawa da cewa dama don rashin abun yi ne ya sa suke Shaye-Shaye. Hafiz kudi ya ciro kusan 10k ya basu.
Master yayi wuf ya amshe tare da zuba Godia kamar zasu goyasu. Addua suka dinga zuba musu har Hafiz ya shige Mota ya ja suna mishi byebye.


Mankas be tsaya bin ta kudin da aka basu ba ya dauki ghanar nan ya danna a guje yayi Gida kamar wani zararre.


Su ko su Master yau take Sallah, World suka siya kowa qulli biyar biyar.


Washegari
5/05/2013


Tashi sukayi yau ba ruwa a Gidan, Drums dinsu empty, dama da k'yar suka samu Ruwan Alwala da Asuba, ko ruwan da zasu dafa suyi kalaci basu dashi.


"Oh ni Labiba ya zamuyi? Gashi Baban Amira bacci yake yi balle yaje nemo mai ruwa, bansan tadashi wallahi" Labiba tace "to Aunty Aseeyah ko in fita inga in zan samu mai Ruwan?" dan shiru tayi tace "Oh, ko zaki dan lek'a Gidan Alhaji Zaki ki samo mana a Kettle? Naga su borehole garesu".


Ba tare da wani tunani ba tace "eh wallahi barin shiga, ina zuwa" da sauri ta fita.


Aunty Asee mamakin Labiba take kawai ta ga fuskarta da walwalwa daga cewa taje Gidan Alhaji Zaki debo ruwa.
Maimakon Kettle wani Plastic Bucket na fenti taga ta dauko.


"Aa Labiba, ina zaki iya daukan wannan Bokitin, ki dibo a Kettle din zai isa kafin Yayanki ya tashi, ya nemo mai ruwa". Da murmushi tace "Anty Aseeyah kar ki damu, zan debo daidai ni" bata tsaya jin me zatace ba, tafita da sauri tana jin wani annashuwa a tattare da ita burinta daya, Allah ya sa ta Hadu da DanMakaho.
**


Tun jiya da ya kwanta bayan Maghrib be farka ba sai yanzu, fitowa yayi don ruwa be zuwa a toilet dinshi, Alwala zaiyi ya hade sallah tun Maghrib din jiya zuwa Asubar yau.
Fitowa yayi zuwa Babban Tankin Gida.


"Hajia masu Gidan bacci suke, nikuma banda hurumin barin ki diban ruwa, aikina Gadi kawai".


"Yauwa ga DanMakaho nan" karasowa yayi gunshi yace ya akayi ne Manu?" yauwa wannan yarinyar Gidan Baban Amira take, ruwa suke so a tsammasu" juyawa yayi ga Labiba da ta shagala tana kallonshi, da kannennen idonshi ya kallota yace "ki shigo ki diba, Manu barta ta diba".


Kamar sakara ta bi bayan dan Makaho har bakin Tank din gidan, karban Bucket din Labiba yayi ya tara a Fampo ya bude fampon, hankalin Labiba na gun karantarshi,
fari ne, amma wahalar rayuwa ta maida Fuskarshi bak'i, bayan hannunshi da dan haske amma tafin hannun da duhu, bakinshi ma yayi duhu, ganin kallon k'urillan da Labiba ke mishi ya sashi cewa " Chanjinki na nan, in na chanza zan kawo miki".


Wani irin kallon da be san na meye ba take binshi dashi, ji yayu ta fara magana tace "Meyasa?" dan kallonta yayi da kannenen ido me kama da bacci yace "Meyasa sai nayi chanji zan baki chanjinki?".


Da sauri ta girgiza kai tace "Meyasa baka iya kare kanka? Meyasa kake tsayawa ana daura maka laifin da ba naka ba? Meyasa kake daukan laifin wasu? Duk a zatona DanMakaho nakasasshene da ba zai iya tabuka ma kanshi komai ba, a zatona Dan Makaho bai da karfi da ikon kare kanshi, ashe ba haka bane, ashe kawai Dan Makaho Matsoraci ne, ashe dan Makaho ba zai iya tsayawa garkuwa ma k'anwarshi ba" baki bude yake kallonta cike da dumbin mamaki.


"Yanzu ba lokacin bude baki bane ka kalleni kamar Photo, ina jinka jiya da aka ce ka dauka naira dubu dayan da na baka, ba sai ka min k'arya ba, na san baka da ko sisi, ina kuma ji ranar da akace kana iskanci da k'anwarka, ina son sanin dalilin da ya sa baka iya kare kanka".


Da k'yar yace "Wacece ke?"
••••••


Yay!!! Late night post


Afuwan


Dont forget to vote and comment line by line


#1love
#DM
#anatare
#FWA
#SonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Biyar (RUWAN SAMA)


Barka da Sallah Bibilicious freaking fans, da fatan anyi Sallah Lafia? Allahu ya maimaita mana na badin badada.


Okay, please, before you start reading Vote first, number of Votes na decreasing, ku bani barka da Sallah ta hanyar voting kafin karatu Nagode.


"Dan Makaho ba tambayar da zaka min ba kenan, ka gaya min mene dalilin da ya sa ba ka iya kare kanka?" shiru yayi be da niyyar amsata.


"ba fa shiru zaka min ba, amsa nake so ka bani, meyasa kake daukar laifin da ba naka ba?"


Hannu ya sa ya shafi sumar kanshi "first of all ki daina min magana kamar wata uwata, secondly ba zaki ta6a ganewa ba, everything is beyond your expectations (komai ya zarce zatonki)" wani kallon mamaki take bin shi da shi, turancinshi mai kyau ne kalar na turawa.


Mamaki ya gani a fuskarta "Oh wow! kallon jakki, dak'ik'i kike min. I'm a Graduate Miss, thank you very much for asking, in kinaso zo in daura miki ruwan a kai, in ba kya so kuma sauri nake Sallah zanyi".


Bata gama mamakin da yace shi Graduate ba ne kuma taji wai Sallah zaiyi da mamaki tace "Asuba?" ba tare da jin komai ba yace "da Maghrib da Isha'i ba".


"Auzubillahi, haba Dan Makaho, me kake yi haka da ya hanaka Sallah? Me kakeyi da ka tara Sallah haka? Kai banji dadi ba wallahi, ka bari bana so" fada ta fara mishi sosai.


Cike da Mamaki ya dubeta kafin yace "To Hajia Maryam, zaa bari". Kallonshi ta danyi tace "wacece Hajia Maryam? Ni sunana Labiba?".


"To ai naga kin tasani gaba kina ta min fada, in ba uwata ba, ba uwar da ta isa ta tasani gaba tana min fada, kuma ni bandamu da sanin sunanki ba, kuma ki daina labe kina jin gulma, duk randa kika sake tsareni kika titsitseyeni da tambaya sai naci Uwarki".


Ya dauki Bokitinshi yayi gaba ya barta tsaye cike da mamakinshi, dan bude murya tayi yanda zai jiyota tace "ai dai ban tsoronka, zamu sake haduwa kuma" ba tare da ya juyo ba yace "aiko zakici Uwarki".


Da sanyayyar guiwanta ta dauki handle din bokitinta ta fita guiwa a sage.
Tana shiga Gida ta diba ruwan a tukunya ta kunna Risho.
Aunty Asee na lura da ita, yanayinta ya chanza, ba kamar da ta fita ba "Labiba? Wulakanci suka miki halan?" da k'yar ta girgiza kanta, tace "kai na ke dan ciwo" "ki shiga ki dan kwanta zai bari" kamar jira take ta fada daki, ta zube kan Gado kafin ta mik'e zumbur ta zauna.


K'wak'walwarta ta shiga tana sak'a da warwara.


Gidan Alhaji Ali Zaki Babban Gida ne, duk Anguwar ba Gidan da ya kai Gidanshi Girma da kyau.
Zaid na da k'anwa Sadiya? To ina Mamarsu? Ko ta rabu da Alhaji Ali ko kuma ta rasu.


Tabbas Hajia Shafa Matar Ubansu ce? Sauran muryoyin da take ji kuma na yaranta ne, ta san 'yan uba da matar uba, don ta na dasu, Gidansu gidan yawa ne, amma tsakani ga Allah ba sa irin zaman Gidan Alh Zaki.


To shi DanMakaho tunda Iliminshi meyasa ba zai nemi aiki ba? Meyasa yake shaye-shaye? Meyasa ya bata rayuwarshi haka?.


A baiyane tace "Ya Rabb! Ina son sani, nasan ba hurumina bane, amma ina son sani" Wayarta ne ya katse mata tunanin da takeyi.


Jawad ne, murmushi ya dan su6uce mata kafin ta dauka da Sallama.
"Labee nah, ina son ganinki kafin na koma Abuja" abunda ya fara ce mata kenan.
Murmushi ta saki mai laushi kamar tana gabanshi, kafin tace "Ina kwana? Ka tashi lafiya?".
Da sauri ya katseta "Wallahi ba Lafia ba, ina ta tunaninki, let me see you please".
Sausauta murya tayi tace "kayi hakuri, ni bansan me zance ma Baban Ameerah ba, amma nan gaba zan mishi maganarka, sai kazo Gida ko?".
Jim ya danyi kafin yace "Alright, Zamu biya ta Gidansu k'awarki kafin mu dau hanya, i will call you later, Ina Sonki Labiba".


Bata taba sanin ana shiga irin wannan yanayin ba, ba ta taba saurayi ba, da yawa nace mata suna Sonta, ba ta taba samun kalaman da sukayi tasiri a zuciyarta ba kamar na Jawad, Ina Sonki Labiba.


Maganar ta sake dawo mata katseta yayi "kinyi Shiru" tace "to me zan ce?" "kice kema kina So na" murmushi tayi tace "ka cika shagwaba, kai dan Auta ne?" yace "Ehmana, ashe ana ganewa, OK gotta go, zan kiraki in na isa Abuja".
"Allah ya tsare ya kaiku lafiya" ya amsa mata da Ameen.
Gab da zasu katse wayar.
Yace "Labiba, a hankali zan koya miki So na, I love you".


Kaste wayar sukayi, Ruf da ciki ta kwanta, wani irin yanayi ta shiga, wannan ne yanayin da ma'abota soyayya ke shiga? Wannan ne yanayin da ke ta6a zuciya. Pillow ta janyo ta rungume a k'irjinta tare da lumshe ido,
Mantawa tayi da duk wani abu, ta manta da komai, har DanMakaho, ba abunda zuciyarta ke aiyana mata sai JAWAD.
Shin Son so ne?.


Jawad da Yayyinsa sai da suka biya Gidan Kakarsu, kafin sukaje Gidan k'anin Babansu suka musu sallama. Jawad ya sake jadadda ma Aisha son da yake ma Labiba don ta kafa mishi Fada a wurin kawarta, yayi alk'awarin dawowa ba da dadewa ba, daga Gidansu Aisha ba su tsaya ko ina ba sai a Shagalinku Restaurant dake Zaria sukaci Abinci sukayi Sallah kafin suka sake daukan hanyar Abuja.


ABUJA


Da Marece suka iso Garin Abuja, Gidansu da ke Garki suka nufa, a tare suka fito daga Motar, Autarsu Mimi ta hangosu, da gudu ta kwasa ta na musu Oyoyo, AbdulMajeed ya dagata sama yana chafewa, Jawad shafa kanta yayi kawai ya shige ciki ya barsu, yarinya ce 'yar shekara uku, amma akwai surutu da shiga rai, cikin muryarta tace "Yaya Ina kukaje? Mancy tace kunje Katsina, ni meyasa bakuje dani ba?" Abdulhafiz yace "Sorry Mimi, da mu ka fita bacci kikeyi next time OK?" gyada kai kawai tayi.


A jikin AbdulMajeed suka k'arasa cikin gidan. A main Parlor duka zube, sai ga Jawad ya fito daga wani Daki, Mahaifiyarsu na biye dasu, bakinta har kunne saboda murmushi. "Sannunku da zuwa Boys" a tare suka gaisheta da "mun same ku lafiya Hajia? Ya gidan" da murmushi ta amsa musu da "Lafiya lau, ya mutanen KT?" suka amsa mata, tayin abinci ta musu.


AbdulHafiz ya mik'e yace "bari dai na k'arasa Gida Hajiya, Ummita ta min Waina" Hajia tace "to ba matsala ka gaidasu, muje na rakaka ma" ta k'arasa gunshi tana dan turashi kamar mai gudun kar yaga wani abu ko kuma kar ya tsaya yin wani abu, ranta ne ya dan sosu da taji yace "bari na Gaisheda Mancy" AbdulMajeed ma yace "Mimi sauka muje mu gaida Mancy" yarinya ta k'i sauka, haka ya dauketa a jikinshi, ya bi bayan yayanshi suka wuce Hajiyarsu da Jawad da je tsaye suka nufa hanyar dakin Mancy.


Abunda bata so kenan, abunda take gudu kenan, bata so yaranta suna ba Kishiyarta muhimmanci, suna nan tsaye sai ganin fitowarsu sukayi su duka har bakunansu na motsi da alamu wani abun ta basu, ranta ya baci, don me suka maida zuwa gaishe da kishiyarta Wajibi, itace Uwarsu ba Mancy ba, amma don me zasu dinga raba musu matsayi? Har suna cin abun hannunta?.


Muryan Mancy sukaji "Jawad, ashe an dawo, ya hanyan?" ba yabo ba fallasa yace "lafiya lau" tace 'Abdulhafiz, Allah ya huta gajia, a gaida Ummita, ke kuma zo nan ki bar Yaya Majeed yaje ya huta" Mimi ta mak'e kafada. Abdulhafiz ya musu sallama ya fita don tafiya Gidanshi, AbdulMajeed ya ba Mancy Mimi da k'yar shima ya wuce daki, Jawad ya ja Hajiyarshi suka shige daki, ita kuma Mancy ta ja hannun diyarta suka wuce daki.


Jawad ya zauna kusa da cinyar Mamanshi, ya na mai bata labarin Labiba, da irin son da yake mata, da kuma gaskia shi aurenta yake sonyi, Hajia Luba tayi mamaki matuk'a, ita ta san yaronta Miskili ne a wani fanni, ta san halinshi da kyale mutane, so da yawa kawayenta ke so su hadashi da 'yaransu amma fir yake nuna ba ya da raayi, tayi mamakin yanda ya furta da bakinshi kan cewa ya samu Mata.


Hajiya tace "to zan kira Antisco din na tambayi hallayar yarinyar" Jawad yace "to Hajia, bari ma na kira miki ita ku gaisa" Hajia tayi murmushi ganin zumudin Jawad.


KATSINA


Labiba ta lek'a dakin Yayanta inda matarshi ke kishingide tace "Aunty Asee barin je in siyo kati, duk yau bamuyi waya da su Mami ba" mik'ewa tayi "tace yauwa nima siyo min na dari" Labiba tace "to" fita tayi tana gyara zaman mayafinta.
Daidai da fitowarshi daga Gida, karaf suka hada idanuwa, dauke kai ya fara yi, ya fara tafiya, da sauri ta bi bayanshi tana fadin "DanMakaho Chanjina, zanyi amfani dasu" chak ya tsaya ya dan juyo, kafin yace "wai ba kince kin san Kudin be wurina ba? Ban dasu yanzu ban da dalilin samun su, na san inda kike, da na samu zan kawo miki har Gida"


Yana kai wa nan ya juya ya cigaba da tafiyarshi, dan jim tayi kafin tayi saurin binshi tana cewa "Dan Makaho, tsaya tsaya DonAllah" dan dakatawa yayi "ka rakani wurin siyan Kati, kaga dai shagon Oga kulle yake, dole sai chan Bencin Eskaley, kuma 'yan shayeshaye ke wurin, nikuma ban san zuwa, ka sansu ban so su ci mutunci na, ko su min magana bana son magana da su wallahi, ni tsoron su ma nakeji, donAllah ka rakani" ta k'arashe kamar me niyyan kuka.


Ya harzuk'a yace "wai ke don Uwarki me kika daukeni? Zan fa ci uwarki, zan babbala ki, ki fita harkana" fuskarta ya dan chanza amma murmushin be gushe da ga kan fuskarta ba tace "dazun da safe ka zagi Uwata so biyu, yanzu ka sake Zaginta, shin me ta maka? Ba ma fa ta sanka ba? Amma kake ta zaginta, don nace ka raka ni?".


jikinshi yayi dan sanyi, shafa kai yayi da hannu kafin yace "to ai duk cikin 'yan bencin Eskaley na fisu shaye-shayen don me zakice na rakaki, ba kya tunanin na miki wani mugun abun yanda kike shishige min haka?". Kallonshi tayi ta ga yanda yake kallonta da kannennen idonshi tace "I'm safe with you, na sani, in zaka rakani muje". Gaba tayi da sauri ya cin mata suna tafiya kafada-kafada ba mai ce ma wani komai har suka iso shagon Eskaley.


Tuni su Master da Haruna suka fara shewa "Shege Mankas, wo kai Mankas" Master yace "Yayar mu ina wuni, ya kwana biyu? A dan dari biyu inci abinci donAllah" Tero yace "amma wallahi kin hadu fa, kina da kyau, Labiba ta kawar da kanta kawai tana mai da na sanin zuwa shagon nan, ina ma yaro ta samu ta aikoshi nan, kamar tayi kuka, jin irin maganganun da suke mata.


"Zan ci uwarku ku ka sake mata magana, danuwarku kalarku ce? To danuwarku waninku ya sake cewa wani abu game da ita, zai kwana Asibiti billahilazi" Tero yace "Kai ji Mankas, yo kai ka shiga wurin sai ka hanamu shiga, indai ba kalarmu bace kaima ba kalarka bace, ai tunda muka ganta tare da kai, ai mun san 'yar hannu ce, Eskaley bata World, dan na san shi tazo saye, ba sai an tsaya mana wani kwane kwane ba, mun san kina Eh-Yaneh Malama".


Kafin Labiba ta gama gano inda Zancen Tero ya nufa, tuni DanMakaho ya kai Tero k'asa ya na kai mai nushi ko ta ina, ba wanda yayi yunk'urin rabasu don sun san halin Mankas, Labiba da tashin hankalin yayi yawa sai ta rasa me zatayi, tana waigawa inda zata ga jama'a don a samu mai rabasu, kowa harkan gabanshi yake , sai da Mankas ya ma Terro Ha6o kafin ya barshi, ya tashi ya nuna su da yatsa yace "duk daniskan da ya sake mata magana sai na ci uwarshi" fizge kudin hannun Labiba yayi yace "Eskaley bamu Kati" Tero ya mik'e a wahalce yace "Wallahi Mankas sai na rama, ko ba yau ba" Mankas yace "zo rama dan uwarka" ya nufoshi da gudu Tero ya bar gurin.


Be ko kalleta ba ya amshi Katin daga wurin Eskaley, gaba yayi ganin haka ya sa ta bishi a baya, sai da suka zo har k'ifar Gidajensu kafin ya mik'a mata katin, amsa tayi tace "Nagode, meyasa kayi Fada?" kallonta yayi ya kawar da kai, tace "Fada be kamace ka ba, be maka kyau ba, komai be maka kyau, ka bari donAllah " a fusace tace "Danuwarki bana ce ki bar shiga harkata ba" shiru tayi ta sadda kanta kasa, sai daga baya yayi laakari da zaginta da ya sakeyi.


Hannu ya sa ya murza idonshi na hagu, yace "kinga ke ke sa ina zaginki, kiyi hakuri, ki kyaleni, ki fita harkata" kallonshi take sosai kafin ta daura hannunta saitin k'irjinta tace "bansan menene ba, Zuciyana daidai nan, na min Zafi, bansan meyasa nake son saninka ba, ba son meyasa na damu da lamuranka ba, dagaske banson meyasa ba, amma dagaske Zuciyana na min Zafi, yana azazzala min, yana tafasa, zakayi mamakin don me ko? Nima mamakin nake, don me, so ka taimakeni, ka gaya min, ko zan samu sausauci".


Kafin yayi maganar Wayarta ta fara ruri, dubawa tayi taga Jawad ne, har ya katse bata dauka ba, ya sake kira DanMakaho yace "ki dau ka wayanki, zan sake ganinki, za kuma ki san ko Ni Waye, ban taba maganar nan da kowa ba, amma zanyi dake, ki shiga ciki, zamu sake Haduwa".
Da duk wata kalmar da ta fito bakinshi suka samu zama a Zuciyarta, samun kanta tayi da bun umurninshi, ba tare da ta ce mishi komai ba ta shige Gida tare da amsar Wayar Jawad.


"Haba Labee nah, ina kika aje waya ina ta kira?" dan guntun murmushi tayi "sorry na fita siyo Kati ne" "God, laifina ne, by the way, Hajiyata zaki gaisar" Dakinta ta fada, tace "Haba Jay, is too early" wani darian farinciki taji yayi, yace "Zamuyi maganan sunan da kika bani Anjima, amma ga Hajiar" kafin tace wani abu ya sadata da Hajiarshi.


Da Sallama ta amsa "Hello Assalam Alaikum" Labiba ta saki

Please Login or Register in order to submit comment