Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ciki ya fara bayyana a jikin Maryam, tara miyau a baki, da amai in taji tashin zuciya, daga Shafa'atun har Alin ba su dago cikin bane don ba sani sukayi ba.
Ita dai Maryam ta san ciki ne da ita, in ta fara kwarara Amai kamar ta amayo hanjin cikinta.


Wata Rana Hajia Er Rabi, k'awar Hajia Shafa'atu tazo gidan, Maryam ta fito don gaisheta, kallo daya ta mata ta san cewa tana da shigar ciki, da ta shiga ciki, tace "kawata, ashe mutuniyar har ta dau ciki" Shafa'atu ta mata kallon rashin fahimta. Er Rabi tace "kar ki ce baki san tana da ciki ba?" ta dan zamo daga kujera tace "kar ki ce man ciki gareta, wallahi ban sani ba, shima Alin bai sani ba" Er Rabi tace "lallai kam, ban yi mamaki ba don ko bari baki ta ba yi ba, ba ki san yanda ake gane ciki ba, to Kishiyarki Ciki ne da ita".


Dam gabanta ya fadi "yanzu Maryam ciki ne da ita? Bata gaya mani ba?" Er Rabi tace "ke ya ma fi haka, kinga yanzu da kika sani, sai mu 6arar da cikin ba tare da kowa ya sani ba, balle mu shiga zargi" ido ta zaro tace "a barar da shi fa kika ce?" ta girgiza kai da sauri, tana da kishi sosai amma rashin imaninta bai kai nan ba, ta san Mijinta ya dade yana neman haihuwa, kuma amfanin Maryaman kenan ta haihu, bata ji dadin cewa ba ita zata haifa ma Ali 'ya'ya masu kama dashi ba, amma ba za ta taba halaka dan Cikin Maryama ba.


Ta kalli k'awarta tace "ba wannan maganar, duk da bana so ta haihu, ba abunda zan mata gaskia, Cikin Mijina ne, farincikinshi nake so, don gaskia be rageni da komai ba" baki sake take kallon Shafa'atu tace "lallai Shafa'atu, kina tafka wauta, wayace miki Dan Miji Da ne? Kinga zaki tafka kuskure, a duk ranar da Maryama ta haihu musamman Namiji ti kashin ki ya bushe, ba mai kara kallonki da daraja, ke ce Uwargida, amma gida zai koma nata. Dangin Mijinki kuwa dama sun tsaneki da ta haihu sunanki abar tausayi".


Hajiya Shafa'atu tace "nidai gaskia a bar maganar zubda cikin" Er Rabi tace "an bari, amma zakiyi kuka da kanki, ni kinga tafiyata" ta mik'e ranta a bace "haba kawata ina zaki?" tace "yo zaman me zanyi? Ana gwada maki annabi kina runtse ido".


Hajiya Er Rabi ta fita, Shafa'atu ta bi bayanta tana magiyar ta tsaya amma tak'i.


Da daddare wurin cin Abinci, suna zaune su uku kamar yanda suka saba, Shafa'atu tace "Alhaji, Albishir ne dani me zan samu" ya tsaya da cin tuwo ya kalleta yace "Shafata duk abunda kike so zan baki, gaya min" Maryama ta zuba mata ido, tana tunanin abunda Shafa'atu ke tafe dashi, murmushi tayi tace "Maryama Ciki gareta, akwai danka a Mahaifarta" mamakin ya sa Maryama kallonta, shi ko Gogan wani Yammm yaji a kunnenshi, ba zai iya fasalta abunda yakeji a tattare da shi ba a cikin wannan lokacin, duk suka zuba ido don ganin halin da zai shiga.


Mamaki ya basu duka, da k'yar yayi murmushi yace "Allah Sarki, to Allah ya raba lafiya" ya mik'e tare da cewa bari ya wanko hannunshi, Shafa'atu ta bishi da ido, a matsayinshi na wanda baa taba mishi irin wannan Albishir din ba, tayi mamakin yanda ya karbi zancen, to ko baya son Haihuwan ne shiyasa bai taba mata k'orafi kan rashin Haihuwar ta ba, tunaninka da yawa suka darsu a zuciyarta.


Ita ko Maryam ba ta ji dadin yanda Mijinta ya karbi Zancan ba, ko da ace ya saba haihuwa aka ce tana da ciki ya kamata a nuna farincikinshi, ita da take da burin haihuwa duk shekara don ta cika mishi Gida da 'ya'ya, amma ba komai, ta tashi ta kwashi kwanonin ta kai kitchen ta dauraye kafin ta koma daki.


Alh Ali Zaki na shiga dakinshi ya fada kan Kujera tare da fashewa da wani irin kuka, kuka ne mai dauke da ma'anoni da dama, shi ne Zai haihu? Shi Allah ya azurta matarshi da ciki? Shekara fiye da bakwai da aure? Yau shi matarshi ke da ciki? Farincikinshi ba mai fassaruwa bane. Alwala yayi ya jera nafilfili don nuna farinciki ga Allah SWT.


Watanni sun shude


Tun Safe ta ke jin nak'uda, amma sai ta daure, ganin ciwon na k'aruwa yana sake yawa ya sa ta fitowa ta kwankwasa dakin Shafa'atu tana cije baki.


"Yaya Cikina kamar zai balle, mutuwa zanyi" da sauri Shafa'atu ta kamota tace "gashi Alhajin be nan, ko zaki sake daurewa har ya dawo?". Maryam ta riko hannunta tace "ki taimakeni, wallahi mutuwa zanyi, nidai ki kira Unguwanzoma".


Kamar daga sama sukaji Sallamarsu Ladidi da Asabe, Shafa'atu ta manta rashin jituwarsu ta karasa gunsu tace "yauwa ina jin Maryama nak'uda takeyi" Ladidi tace "to da me zaki mata? Ke zaki karbi haihuwar ki danna kan yaro ya koma?" ran Shafaatu ya baci "ai da banson a haihun da tun lokacin da take da ciki na barar da shi" Ladidi tace "ai ko ba ki fada ba na san bakincikin cikin nan kikeyi, to ta Allah ba taki ba, sai an haifeshi munci moriyar Magajin Yaya Ali da yardan Allah". Asabe tace "kinga muje mu taimaka mata, tana cikin mawuyacin hali".


A daddafe suka kaita dakinta, haihuwar ce dama, bayan yan mintuna ta santalo danta jazur dashi, bayan Ladidi ta gyara Da da Uwan ta aiki Asabe zuwa chan GidanGandunsu taje ta fadi haihuwar.


Shafa'atu na nan tsaye gefe tana jin kukan jariri tsoro ya mamayeta, kasa shiga dakin tayi sai ta wuce dakinta ta fashe da wani kukan da bata san ko na meye ba, fargaba ne fal ranta.


Kamar daga Sama sai ga Alhaji Ali da Kanenshi, yana Gidansu Asabe ta je ta fado haihuwar, Shafa'atu na jin muryan Mijinta ta fito waje,
"Alhaji sannu da dawowa" be ko kalleta ba ya wuce ya barta tsaye, gabanta ya fadi, me kenan? Ta tambayi zuciyarta, bayanshi ta bi da ido, kafin ta rufa mai baya.


Yana shiga ya amsa Jaririn daga hannun Ladidi ya rungumeshi tsam a k'irjinshi, tsigar jikinshi suka mimike, wani yanayin da be taba shiga irinshi ba ya shiga, hawaye suka soma kwaranyowa daga idanuwanshi, hamdala yake yi yana godewa Allah, addua ya ma yaronshi, kafin ya karasa gun Maryama yana ta jero mata sannu yana sanya mata Albarka.


Duk a kan Idon Shafa'atu, hawayen bakinciki ta fara ta fita daga dakin da sauri.
Labarin Haihuwa ya Zagaye Gari, sai zuwa barka akeyi, ana taya Alhaji Ali murna, kullum Gidan ceike yake da Danginshi da yan barka.
Shafa'atu ta zama kamar bakuwa, don da ta zo wuri ake mata habaici, ita Maryama bata da ta cewa sai yanda dangin Miji sukayi da ita don ma suna sonta, kowa so yake ya burgeta, daga masu dafa mata abinci, sai masu ina zaa saka da ita.


Alhaji Usman da Iyalanshi da Dangin Maryama sunzo barka, da yawa sun tsaya Suna.


An san Alhaji Ali da kyauta, amma tunda akayi haihuwar nan, ya Soma kyauta kamar baya son kudadenshi, kyautata ma Makwaftanshi yake.
Ranar Suna aka radawa yaro Suna ZAID ALI ZAKI.


Zaid ya sha kyaututuka daga manyan 'yan siyasa.
Anyi babban liyafan Sunan da baa taba yin irinshi ba a Anguwar.


Wani sabon kulawa Alh Ali ke ba Zaid da Mahaifiyarshi, dan kawaicin da yake ma Shafa'atu a da yanzu babu shi, gabanta yake nuna tsantsar soyayarshi ga danshi, in yana tare da Zaid ba ya da lokacin kowa da komai, Abujan da yake yawan zuwa yanzu ya bari, in ko Zaid na kuka da kanshi yake zaro Nono daga Jikin Maryama ya ba Zaid ko gaban waye.


Ba ya kawaici ko shariya wai don Zaid ne dan fari, mutane na mai uzuri ganin be taba haihuwa ba.
Shafa'atu ta fara jin ba daidai ba, Alhaji Ali ya rage damuwa da ita, kacokam hankalinshi ya koma kan Zaid, tun tana daurewa har ta tare shi wata rana da maganar a parlo.


Yana rike da Zaid a k'irjinshi "Alhaji, magana nake so muyi" ya dan kallota amma be fasa ma Zaid wasa ba, hakan da yayi ya nuna mata yana sauraronta tace "Alhaji, wai kai baka da lokacin kowa da komai sai na Zaid? Kai ko dan kawaicin Dan fari bakayi? Alhaji, ba ka gudun bakin mutane? Komai Zaid komai Zaid?" baki sake yake kallonta yace "Shafa'atu wace irin magana ce wannan kike? To in banyi lokacin Zaid ba lokacin wa zanyi? Don mutane kar suce banda kunya, ko kuma kar suce banda kawaici sai na k'i nuna ma yarona So, Kauna da kulawa? To mutane sun dade ba suyi magana ba, aj dade baa zageni ba, banda kamar Zaid wallahi, kuma zan iya rabuwa da kowa ta kan Zaid ko da Mahaifiyarshi ce balle ke".


A tsorace ta kalleshi, mamakinshi take, tace "Alhaji Ni? Sai ka rabu dani ta kan Zaid? Me na mishi?" yace "Yo sai na rabu da ke nana Shafa'atu, haka kurum kinzo min da wani soki burutsu, ni da Dana? Duk mai son ganin bacin raina to ya kawo kushe ga Zaid, kika cire Mahaifiyata, Wallahi na fi sonshi fiye da kowa a Duniyar Yanzu, to ki bi a hankali".


Hankalinta ya tashi sosai, sum sum ta tashi ta shige dakinta tana fashewa da kuka Sosai.
Haka ta kwanta zuciyarta na k'una, tunaninka kalakala, washegari ta ma Gidan Hajia Er Rabi diran Mikiya,
Matsalarta ta karanto mata.


Er Rabi tayi dariya, "ba ke dadi Miji ba? Ba yanda banyi dake kan a barar da cikin nan ba ki ka ki, gashi ya zame miki ciwon Ido, mai makon ace kinyi Kishi da Kishiyarki, kin kare da kishi da Dan Mijinki, ai wallahi kuka yanzu kika far yinshi, ba zaki san tsakanin Mahaifa da Gudan jininsu ba tunda ba haihuwa kika taba yi ba".


Bata rai tayi tace "abun 'yar gori ce?" tace "aa, ina dai gaya miki ne, kashin ki zai k'ara bushewa a duk lokacin da Maryama ta sake haihuwa, in ko ta cika mishi Gida da yara to wallahi zaki zama Almajira a cikin gidan aurenki, kar ki yarda ta sake haihuwa, ki tashi tsaye Shafa'atu, ki kwatar ma kanki 'yanci".


Jin saukar maganganun Er Rabi take kamar Darma mai zafi, dole ta tashi tsaye, da ta bisu ta arziki ba abunda ya kare ta dashi, zata bisu ta tsiya, duk sai ta ci uwarsu, nan Hajia Er Rabi tayi ta zugata tana gaya mata abubuwan da ya kamata tayi.


Tun daga ranar Hajia Shafa'atu ta chanza ma Maryama, a gaban Mijinsu kamar ta goya su ita da Zaid, amma a bayan idonshi Kashi ya fisu daraja.


Zaid na da Wata 5 Maryama ta sake daukan Ciki, hankalin Shafa'atu ya tashi ya a ka k'are da Zaid balle an yi mishi kanwa, kila Alhaji Ali ba zai samu lokacin yi mata magana ba.
Samun Er Rabi tayi, ta gaya mata ai Maryama na da ciki, wani magani ta bata tace ta zuba mata a cikin Abinci.


Ta ko ci saa cikin ya zube, bayan Maryama ta sha bak'ar wahala. Tun daga lokacin nan, ciki ya bar Zama a jikin Maryama, da tayi da cikin ya zube, kusan bari 9 tayi a shekara 4.


A cikin Shekarun nan Hudu da suka shude, Alhaji Ali yayi wani irin kudi mai ban tsoro, ya koma Sabon Gidanshi da ke Tudun Matawalle, Gidan Sama ne, a Sama akwai Dakuna 3 daya na Maryama daya na Alhaji Ali, daya na Shafa'atu, sai a k'asa Akwai K'aton Parlo da dakuna biyu, sai k'aton Kitchen din da duk mai sanwa take shiga.
Sai kuma ya na da masu dafa Abinci a baya inda Boysquaters suke, Gidajen da ke kusa dashi kullum suna da kwanon Abinci a Gidanshi, tunda ya dawo Anguwar kullum yana da 'yan maula masu jiranshi a k'ofar Gida, bai taba gajia ko kosawa da su ba, yana musu ihsani.


Kullum hannunshi rik'e da na Zaid, duk inda ya sa k'afa to Zaid na biye dashi, mutane kuwa sai su dinga wasa Zaid da kirari ko don ya musu Alheri, Zaid na da matuk'ar wayau, baya da k'uiwa, duk yan Unguwa na sanshi, yana da son mutane kamar Mahaifinshi, yana da shekara 4 yayi wani irin wayau.


Shafa'atu tsanar ta ga Maryama da yaronya karuwa yake.ta yi ruwa tayi tsaki dai gun hanata sake haihuwa, duniya ba abunda ta k'i jini irin Zaid, abunda ke bak'anta ranta, sai ta dage tayi abinci domin Mijinta, sai Alh Ali ya kira Zaid wai tare zasuci, ko kuma ya kwashe mishi namomin yace "maza cinye Zaiduna" abun nan na ci mata tuwo a kwarya, ji take ta na iya harbeshu da bindiga.


In ko ranar Girkin Maryama ne sai tayi sanadin bata mata sanwa, ko ta k'ara mata gishiri, ko yaji, don dai suyi fada da Alhaji, amma bata taba jin kansu ba.
Yaran Yayan Maryama na zuwa mata hutu sosai, in har Alhaji Ali baya nan, to Abinci a cikin Samira take ba Maryama wai da ita da bak'inta, ta kuma kulle kitchen din CIkin Gida don kar Maryama ta dafa komai a cewarta ai ana abincin gandu, zai zama albazaranci ayi ta dafuwa kalakala. Maryam bata taba kaima Mijinsu k'orafi ba.


Da ta hadu da Zaid to sai fa ta hada shi da wani Rankwashi, ko tsunguli, in ko yana bacci har razor ta ke sawa ta fasa mishi jiki dan k'eta.


Ran da ya ba kowa mamaki, randa suke zaune gabaki daya su hudu suna cin Abinci, Zaid na kan cinyan Babanshi yana sa mishi doya a baki kamar an tsunguleshi yace "Yauwa Baba, kaga kullum mama sai ta tsunguleni ta min haka akai" ya Rankwashi baban a kanshi a hankali yace "amma ni mai zafi takeyi min, me na mata baba?".


Mama kamar yanda yake ce ma Shafa'atu, kowa ya san ita kadai ce Mama don Maryama Minyama ya ke ce mata.
Alhaji Ali ya kalli Shafa'atu, Maryama kuwa kau da kanta tayi, yace "Shafa'atu? Ke kin Rankwashi shi da tsungulinshi? A kan mene?" Shafa'atu da tayi zaune kamar gawa ta kasa motsi, mamaki ta hanata motsawa.


Sai da ya daka mata tsawa kafin ta fara borin kunya, haba Alhaji, kai ka san yanda na dauki Zaidu kamar dan cikina, don me yaro dan shekara hudu zai ma magana ka hau kai? In tsunguleshi inji me? Daga jin maganar nan an san kitsa mai a kayi, kuma ban yafe ba, Zaid ni na san ba kayi wayon hada maganganun nan ba, na san gaya maka akayi, ba wani abu, don ban taba haihuwa ba shine ake ta min abubuwa a gidan nan".


Jikin Alhaji Ali yayi sanyi, shi ya san Yaronshi beyi wayon yin karya ba, amma kuma maganganun da Shafa'atu tayi sun shiga ranshi. Sai dai ya share ya cigaba da cin Abincinshi, amma ya kudurta a ranshi duk wanda ya matsa ma Zaid shima zai matsa mishi.


Wannan kenan


Vote and Comment line by line pls


#1love
#DM
#anatare
#SonSoFWA
#nagode..


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Takwas (WANENE SHI?)


Bibilicious freaking fans, Vote before reading please, thank you.


Ya kalli Labiba yace "A zaman Gidan Kishiyoyi, ko a auro Amarya tazo ta takura ma Uwargida, ko kuma Uwargida ta takura ma Amarya, a gidanmu ba haka bane, Matar Ubana , ni ta takura mawa, da yaron Gidan take kishi, ni ta sanya wa Ido".
Idan har ta bude idonta ta ganni, ji takeyi kamar ta kasheni.


Ba zan manta ba wata rana Baba ya tafi Lagos wani Taro, a lokacin ina da shekara 5, na shiga Makarantar Boko, ranar da Baba zai dawo Mama ke Kitchen, ta dade tana hada Abincicika kala 2 masu dadi, da farko tuwo miya taushe, sai na biyu Shinkafa da ya ji kaza ko ta ina, kuma don rowa sai tayi don cikinshi kadai.


Kamshin Abincin ya cika Gidan gabaki daya, har na kasa hakuri na bita har kitchen nace "Mama zanci Abinci" kora na tayi har da dan biyoni da gudu.


Fadawa nayi daki kan Minyama, ta kasance ta na jina da Mama a kitchen, rik'oni tayi tace "Zaid, ba fa yunwa kakeji ba" nace "Ni Abincin Mama nake son ci, kuma ta hanani, bakomai, ai da Baba ya dawo tare zamuci"


Minyama ta kalleni sosai kafin ta rik'o hannayena duka tace "Zaid, kana ja min matsala, DonAllah in Babanka ya dawo kar kaje wurin ci Abincinshi, zan maka irinshi ranar Girkina kaji DanAlbarka?" sai da Minyama ta dade tana lallashina kafin na amince ba zanje gun Babana ba in yana cin Abinci.


Da Baba ya dawo, kamar ko da yaushe da tsarabata ya shigo, ya dauke ni ya tillani sama ya chafe "Farincikina" kamar yanda ya saba ce min, ni ko na mak'alk'aleshi ina dariya, yace "Kayi Kewana?" nace "Sosai ma".


Ina kallon Mama ta galla min harara, da yake ita ce ta biyoshi daki, tuni na shiga taitayina na dan zame na bar musu dakin.
Nan suka sake gaisawa, sai da yayi wanka kafin suka fito Parlo tare, ta gabatar mishi da shagalin da tayi dominshi, ta zuzzuba mishi a Plate.


Baba ya lumshe ido yace "wai kin san yanda nayi kewan Girkinki Shafata?" Murmushi tayi tace "ai gaka ga shi, sai kaci ka k'oshi, nayi dominka kai kadai" Baba yayi murmushi yace "nagode k'warai".


Da Bismillah ya fara cin Abinci, Shafa'atu ta zuba mishi ido cike da so da kauna, tana ganin yanda ya lumshe ido ta san cewa yaji dadin Abincin ta fadada murmushinta.


Loman da Baba zai k'ara ya dan dakata, bude baki yayi yace "Ina Zaid?"
Da sauri tace "yana gurin Minyamanshi ko, yi sauri ka ci kar ya huce Alhaji"
Kamar zai mik'e tsaye yace "Kira min shi yazo muci Abinci".


Ranta a bace tace "be fa jin yunwa, na bashi, bari na k'ara mai wani, akwai saura a kitchen kai dai ci"
Fuska ya dan bata yace "kinsan dai bana iya cin Abinci ni kadai in ba da shi ba" ya mike tsaye ya nufo dakin Minyama.


Ina daga chan rakube ina zaune, ban saba zama haka ba in Babana na Gida, a ko da yaushe ina jikinshi in dai aka ce yana Gida.


Yana shigowa ya ganni zaune daga gefe, yace "yana ganka a nan? Bayan ga Abincinmu chan"


Na dan kalli Minyama ta min ido nace "na k'oshi" be tsaya wata-wata ba ya cicciboni.


Minyama ta dan ci gabanshu tace "Alhaji, da dai ka barshi, ba ya jin yunwa" Baba ya harareta yace "sai ki gaya min yaushe na fara cin Abinci a KT ba tare da Zaid ba, kai Matan Gidan nan ku fita idona fa" ya fita tare dani a jikinshi ya koma Parlo inda Mama ke zaune ranta a Jagule.


"Shafata kinga ga Zaid din, ashe Maryama ce ta hanashi fitowa, zauna kaji Farincikina mu ci Abinci" ko kallon mu Mama ba ta yi ba, illa hucin da take yi, shi ko Baba be lura ba, ni kuma abunki da kwadayyaye, na zauna da na sa a cokali daya a baki sai naji kamar ban taba cin Abinci mai dadin wannan ba, sai kuma na ga kamar Abincin ya min kadan.


"Baba In cinye?" da sauri Baba yace "Cinye tas Zaiduna".


A hasale Mama tace "Haba Alhaji, ba fa ka ci komai ba".


"Zaid ya nuna ya na so, a kawo min na Gandu in ci" ran Mama yayi kololuwa gun baci. Sanwan da ta dauki Awowi ta na yi, wanda tayi domin shi be ci ba, sai dan loma dayan da yayi, fuuu ta tashi ta bar wurin kamar zata tashi sama.


Shi ko Baba hankalinshi ya maido guna cewa yake "Yi Sauri ka cinye Zaiduna" ni ko na zage na cinye Shagalin nan tas.


Dan Makaho ya tsagaita yana dariyan takaici kafin ya dan sha mur tare da murza kanannen Idonshi. Labiba kuwa zuba mishi ido tayi tana sauraronshi tana son taji k'arshen Labarin, ta k'agu taji amsoshin tambayoyinta.


Ya cigaba da cewa "Shi fa Baba har ga Allah bai san Mama ta ji haushi ba, in Baba na tare da ni kowa yake mantawa, ba ya karantar damuwa a fuskan Mutum, haka ya rik'o hannuna muka shiga Dakin Mama, inda muka ganta zaune, da alama Kuka ta sha, ko bi ta kanta Baba beyi b ya fada toilet din Dakin, ya barni zaune tare da Mama.


"Ni ko na matsa gunta "Mama me ya faru kike kuka? Baba ya miki fada ne? Zance ya daina miki fada" tureni tayi daga jikinta, na sake tashi na nufota "Mama wai" kafin na gama maganar da zanyi, Zuciya ta ci Mama ta riko min kunne ta fitar dani daga dakinta ta wurgar dani a Parlo."


"Da yatsa ta nuna ni "Zaid ka fita idona, ina tausayinka duk ranar da na kama ka, dan Ubanka Abincin kai na dafa mawa? Da zaka zauna ka cinye? Maye ne kai da duk k'oshin da kayi in na dafa ma Babanka abinci sai kaci, kai baka k'oshi ne? Wallahi duk randa na sake dafa mai Abinci kaci sai na ci ubanka, shege Maye, na tsaneka Zaid, da na sani da na barar da cikinka tun kafin a haifeka" ta juya fuu tayi hanyar dakinta."


"Kalamanta kenan a gareni, ba zasu taba gushewa a k'walwata ba, ban manta su ba tsawon Shekarun nan, kinsan me nace mata?" da sauri Labiba ta gyada kai alamun "aa" ya dan murmusa yace "yarinta ma dai to, ce mata nayi nima ban sonta kuma zan sa Babana ya koreta".


"A hasale ta juyo, ta san zan aika, ji take kamar ta shak'eni na mutu, a gefenta ta wawuro wani Cokali mai yatsu, fork, daga inda take ta saito ni ta wurgo min cokalin nan cikin bacin rai tare da cewa "in ka fasa ka ci Ubanka, shegen yaro ka zame min alak'aik'ai, wallahi sai nayi maganinka".


"Cokalin nan be tsaya ko ina ba sai a cikin Idona na hagu, wani gigitacen k'ara na saki wanda ya tsorata Mama,


"Allah Sarki Babana ashe duk abunda ke faruwa yana kallonmu, a guje ya k'araso gareni inda na ke zube a k'asa, ya tariyo ni jikinshi yana jijjigani, ni ko ihu nake ina ambaton idona".


"Minyama ta fito a rude, ita kanta Mama ta mugun rudewa, Baba ya ciccibeni, yayi waje dani, Mama a rude ta bi bayanshi, Minyama ma binmu tayi a baya".


Baba be tsaya jiran Direba ba ya figi mukuli ya fada mota, itama Mama da Minyama Mota daya suka shiga, hankali a tashe suka bi bayanmu da mu kayi General Hospital.


"A Emergency a ka karbeni, a lokacin Jini ya taru a cikin Idon, likitoci suka karbeni. Suka hau aiki, Alhamdulilahi ba wani ciwo a can cikin Idon, dama kin san ido baya son bak'on abu nan dai suka diga min magani a idon, suka rufe da bandage bayan Minti Talatin zasu dawo na bude in na bude ba wani abu InshaAllahu".

Please Login or Register in order to submit comment