Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi ka min Fira ko na je shagon Eskaley na zuk'i world".
Dariya ya fashe tare da mik'ewa yana fadin "Me zanyi in babu ke k'amshi?".


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN DA DAYA 2⃣1⃣
(KISHI🤨😏)


Labiba ta katse tsaye ta kasa zaune, girgiza k'afa kawai take, binibini sai ta lek'a window amma ba wani alamun sun fito, har yanzu suna ciki.
Zaid na cikin daki tare da wata Macen da ba ita ba, sosai zuciyarta ke mata zafi da zugi.
Da ita ce tayi yunkurin zuwa dakinshi da yace mata Mara Aji, to ita wannan me za a kirata dashi? Tunda har yunk'urin taba shi take. Tsaki ta buga mai k'arfi tare da cuno baki cikin k'unar rai chan kuma ta tashi ta sake lek'awa.
Kiraye kirayen sallah taji na maghrib, hamdala tayi a zuciyarta ta na me murnan dole su fito suyi Sallah.


Shiru shiru har ta fito tayi nata alwalan bata ga sun fito ba, yayyafi aka fara dama garin tun bayan laasar hadari ya hadu, da sauri ta shige daki tana fatan ya fito ya je Sallah.
Har dai ta idar da Sallah tana ayyanawa a ranta sun fito a yayin da take sallahnTa na idar da sallah tayi tasbihinta a kan dardumanta take har aka kira Isha'i, ta tashi tayi Ishai ta hada da Shafa'i da Wutr.
Ta na ji yayanta ya shigo tare da kullo Gidan alamun yau ya gama fita, tashi tayi ta shiga dakin Yayanta da Sallama.
Zama tayi kusa da Amira ta sake gaidasu kamar yanda takeyi duk bayan sallahr da tayi sai ta gaidasu.


Yayanta da Aunty Aseeyah suka amsa.Ameerah da sabit suka gaidata.
Mallam Muhammad yace “nikam Labiba wani abu naji a cikin anguwa wai ko hatsaniya ya shiga tsakaninki da DanMakaho da ‘yan bencin eskaley” dumm gabanta ya yanke ya fadi, mak’ogaronta ya bushe da k’yar tace “waye kuma danmakaho?” Yayan yace “wannan yaron da ke nan Gidan Alhaji Zaki wanda ya samu matsala da matar babanshi kwanaki”.


“Tabb yo ni ina na ganshi balle in samu hatsaniya dashi” ta shirgo karyan da ita kanta tayi mamakinta, yayan yace “wallahi kin dainji abunda ke yawo a Anguwa, yanzu bayan Masallaci Mallam Na’abba ke ce min ya ga kanwata na sa’in sa da dan makaho da yan bencin eskaley, ni dai na sha mamaki sosai har ina cewa me ya hada labiba da DanMakaho?”.


Aunty Aseey ta chafe tace “wai baban Amira yanzu baka san gulman yan unguwan nan ba? Ana ganinta ta na zuwa makaranta har sun fara kawi ma gulma da k’arerayi, tunda kayi tafiyar nan ba fa inda muke zuwa, da ta dawo daga makaranta muna gark’ame a daki, to wallahi in ma sonta sukeyi su fito su fada ba wai su dinga hado k’aryan da bai da wani amfani ba, in banda k’arya mai zai hada Labiba da ‘yan shaye shaye?”.


Mukut Labiba ta hadiye bak’in miyau, hankalinta na dagawa a duk lokacin da akace me zai hadata da dan shaye shaye? Amma a fuska yak’e takeyi.
Mallam Muhammad yace “in ma gulma ya je musu kan har yau baa gyara bangon chan ba to inshaAllah zan gyara da na hada yan kudaden nan, bulo tsada yake shiyasa, amma ni k’anwata ba ruwanta da yan bencin Eskaley.


Cike da rashin sanin yanda zaayi ta tashi tace barin shiga daki.


Zuciyar Labiba na tsinkewa har yanzu hankalinta na ga dakin Danmakaho, zuciyarta na ingizata da taje ta ga su nan ko ba sa nan ko don hankalimta ya kwanta amma ina ba zata iya ba, Yayanta na gida, ba zata bashi dalilin gasgata maganganun yan Anguwa ba.


Yesmin na fashin Sallah, ganin an fara yayyafi ya sa Zaid yin Maghrib da Isha’i a gida, nan suka cigaba da fira har karfe 10:30.


Anty Aseeyah ta shigo da Sabit da yayi bacci dakin babansu, ta koma ta dauko Ameerah har zata fita ta tsaidata ta hanyar cewa “Aunty Asee” Aunty Asiya ta dan tsaya tace “yadai Aunty Labs?”.


Labiba tayi murmushi tace “wai dama Jawad mukayi waya yanzu wai yace zaizo gobe” hak’ora Aunty Aseey ta yashe tace “ahh Mallam Jawad, aikam sai yazo Allah ya kawo shi lafia, zan gaya ma Yayan naki yanzu kuwa”.
Murmushi Labiban tayi tace “to Aunty, in yace wayeshi? Kice mai cousin din besty Aisha ce” “kar ki damu, ki ba danuwan Aisha bane ai yasan wata rana dole a zo wurinki” murmushi kawai ta mata tace “sai da safe” “Allah ya kaimu Ameen” Aunty Aseey ta fita ta wuce dakin Mijinta.


Labiba kashe datanta tayi ta mike ta rage kayan jikinta zuwa kayan bacci, ta fita don zuwa toilet.


“Ki tashi na rakaki gida Yas dare na sake yi” fuska ta danyi tace “Zaiddd” girgiza kai yayi yace “Yesminnn to 11 fa, get up” a shagwabe ta tashi ya mik’e shima yace “oya” ganin tana niyyan sake zama ya sa shi rik’o hannunta ya ja, ita ko ta cigaba da bubbuga k’afa kamar ‘yar shekara4.


“Zanyi Mafarkinka” yace “nikuma zanyi mafarkin kinyi mafarkina daria sukayi gabaki daya.


Fitowarta daga Toilet saitin idonta kan su biyu, da taimakon wutan lantarkin da ke tsakar gidan da kuma hasken farin wata ya hasko mata Zaid da Yesmin suna tsaka da tsinkar fure a ganinta.
K’irjinta ke barzanar fitowa, kenan tun kafin mangariba suke tare har yanzu? Me suke cewa? Hawaye masu dimi suka cigaba da gangaro mata, kasancewar garin akwai sanyi don yayyafin be dade da tsayawa ba atishawa yazo mata mai k’arfi.


Da Zaid da Yesmin sukayi saurin kallon inda sukaji sautin Atishawan.
Ganin ita suke kallo ya sata saurin shigewa daki har da dan tuntubenta.
“Beebs” ya fada cikin wata irin murya wanda yake chan k’asan mak’oshi.
Yesmin ta kalloshi tace “Wa?”.
Be san maganar da yayi ba ya fito
Yesmin tace “Ehen? Wacece?”.
Zaid ya dan murji kanennen idonshi yace “Mak’wabtan mune”
Yesmin tace “eh ai nagani, sai me kuma?”
Bangon Gidansu ya fadi saboda ruwan da akayi kwanaki, to so kusan uku ana gyarawa ana sake wani ruwan yana rushewa-” Zaid “ba wannan ba cewa nayi wacece?” Kafadunshi ya daga sama yace “a gidan take, k’anwar mai gidan ce” yayi gaba, juywa tayi ta kalli Gidan, ta rantse tana ganin alamun mutum a daidai window din wani daki alamun kallonsu ake, ba ta da zabin da ya wuce tabi bayan Zaid din.


Har bakin Parlorn cikin Gidan ya rakota inda Hudu ke zaune yana kallo, da mamaki ya bisu da kallo, ya kalli agogon dake sak’ale kan bango, duk zatonshi Yesmin na daki, ashe tana chan suna iskanci da DanMakaho.
Yi sukayi kamar basu ganshi ba
Yesmin tace “Zaid, kamar ya kamata na san ko wacece”.
K’ura mata ido yayi sosai kafin yace “sunanta Labiba Ahmad, tana karatu a HUK Polytechnic, kina buk’atar sanin yanda tayi yarintarta ko abunda take so ta zama in the future?”.


Duk da faduwan gaba ya Ziyarci Yesmin amma sai da ta murmusa tace “hakan ya isa, Goodnight Zaid” shima murmushin yayi yace “Goodnight Yas Yas” ta juya ta shige dakin dalo don nan take kwana, be shiga ba don ya san Dalo ta yi bacci ya juya shima ya fita ba tare da ya kalli Hudu ba.
Hudu ya bi bayanshi ta zaguna marasa dadi amma beyi da karfi ba don ya san Mankas yanzu zai tada duk wanda yayi bacci a gidan da Tashancinshi.


WASHEGARI


Tunda yara suka tafi Tahfiz bata zauna ba, aiki takeyi, a ranar sai da ta cire duk yanar dake a saman ceiling, aka zo aka share Gidan.
Mallam Muhammadu ya fito don tafiya kasuwa yace “Ahh su Aunty Labs yau fa ba zama saurayi zaizo” kunya ya bata ta sa hannu ta rufe fuska” Aunty Aseey tace “ai dai ka dawo ku gaisa ko?” Yace “eh to bari dai muga kasuwan” addua suka mishi a tare kafin suka rakashi har bakin k’ofa.


“Labiba, kije kiyi baccin safenki, Abuja ba nan kusa bane”
Labiba tace “wani bacci Aunty Asee? Yace fa ya taho” “ahh to ai dai koma meye sai dai Yayan naki ya aiko da cefanen ko?” Hakane “amma bari dai na dora sobon in yaso sai na hada na saka a fridge don yau da alama rana zaa k’wala”.
Aunty Aseey tace “nidai barin je na kwanta” “to shikenan Aunty”.
Labiba ta kasa tsaye ta kasa zaune ta je nan taje chan, ta goge nan ta goge chan.


“Ki fito wallahi muje kan dining muyi breakfast” ta fada ta na jan hannunta.
Dalo tace “Aunty Yas donAllah ki bari nayi kalacina a daki yanda na saba”
Yesmin ta harareta tace “ba nace miki bana son musu ba, just standup muje muyi breakfast”.
Dalo ta numfasa ta san gardama da Aunty Yasmin ba amfani ya sa ta tashi suka fita.


Suna kan Dining table gabaki daya har Alhaji Alin. Kan dalo a k’asa suka isa bakin table, tunda suka fito idon Hudu ke kansu, sosai Hudu ke ganin kyaun Yesmin amma yau sai ya ga Yesmin tayi muni, ya ga Kyaun Dalo sosai ganin Yesmin da Dalo ya sa ya hango munin Yesmin a lokaci daya, ta fiye tsawo kuka tsohuwa ce, dalo kuwa bata fiye gajarta ba amma yarinyace shakaf, cikin seconds da ba su wuce 30 ba ya ayyano dalo a zahirance yana ayyana wasu abubuwa a zuciyanshi.


Aunty Shafa ranta ya baci ganin Yesmin ta tunkaro table tare da Dalo.
Da ido Yesmin ta mata magana ta jawo kujera ta zauna tare da cewa “Ina kwana Baba?” Alhaji Ali ya kalli Shafa ta galla mai harara yayi saurin kawar da kai ba tare da ya amsa gaisuwan dalon ba”.
Dalo ba ta damu ba ta gaida Aunty Shafa tace “sannu ‘yar sarki jikan galadima, sai yanzu zaa tashi ba aikin fari bare na baki, anzo an zauna zaa cika k’undu”.
Dalo ta daga ido ta kalli Aunty Yesmin, kamshi ta murmusa ta girgiza mata kai.


Yesmin tace “Daddy ina kwana?” Da fara’a Alhaji Ali ya amsa, ta gaida Aunty shafa itama ta amsa, Annah tace “ina kwana Aunty Yas”.
Aunty Yesmin tace “Lafiya lau Annah, ke kikayi breakfast dinnan hala?” Annah ta kyabe baki tace “ni zanyi abinci chabda, mommy ce tayi”.
Yesmin tace “auu na zata ke kikayi, ashe ba banbanci ke da Dalon, duk ba aikin fari bare na baki sai dai a dafa kuzo ku cika k’undu ko Daddy?” Ta fada tana kallon Alhaji Ali, Alhaji Ali yak’e kawai yayi don baida ikon magana.
Aunty Shafa ta san cewa bak’a Kamshi ta gaya mata tace “ku ci abinci kin tsaya jan mutane da surutu sarkin magana”. Dariya k’amshi tayi tace “Ok lets all eat”.

Yesmin ta zuba ma Dalo Dankali da kwai da sauce din k’oda ta tsiyaya mata ruwan tea a cup, dalo duk a tsorace take bata ko son daga ido, godia ta mata kafin ta fara tsakurar abincin a hankali.
Ba ka jin k’aran komai sai k’aran cokula, ji tayi wani abu na bi mata k’afa, ba ta biye ba ta cigaba da cin Abincinta.
Amma sai ta ji abun na yawa har wurin guiwanta, gashi kuma bata sonyi kwakwaran motsi tayi laifi wurin babanta ko aunty Shafa. Sai ta share duk yanda take jin abun na damunta bata yi motsi ba, ashe wai Hudu ne ke shafar kafarta, kasa cigabawa tayi da cin Abinci, ta mik’e tsaye.


K’amshi tace “yadai? Ina zaki?” Dalo ta kalli Hudu da sauri ta kawar da kanta don wani irin daniskan daga gira ya bi ta dashi tace “na k’oshi ne” Yesmin tace “come on my friend zauna kici Abinci” Dalo ta marairaice kamar zatayi kuka tace “dagaske Aunty Yas na k’oshi” Aunty Shafa tace “kema dai Yesmin tunda ta k’oshi ki kyaleta mana” kafin yesmin tayi magana Dalo tuni ta isa daki.


Yesmin ta dauki plate and Cup din Dalo ta bi bayanta dashi ta shiga ta ganta zaune tace “ke wai ya?” Dalo tace “wallahi kawai i wasn’t comfortable” Yesmin ta harareta tace “in har bakya zama kusa da Mahaifinki ta ya kike so ku saba? Ansa ki cinye”. Da sauri ta amsa plate din Aunty Yesmin kuma ta fita ta cigaba da kalacinta, ta riga su gamawa ba tare da tace da kowa komai ba ta fita daga Parlorn, sun san BoysQuaters ta nufa.


Tafiyarta takeyi wa ta hango? Labiba ce ke kai kawo tsakanin kitchen da wajen diban ruwa, tsayawa tayi tana kare ma yarinyar kallo, yarinyace karama, ba zata wuce shekarun su dalo ba, kishinta ya turniketa, a hankali ta fara takawa har sai da tazo boarder tsakanin gidaje biyun Labiba na waigowa ta ga mata tsaye.
Bata karasa ciki ba ta murmusa mata, labiba ta kawar da kanta kamar bata ganta ba.


Yesmin da murmushi tace “Labiba, ki gaisheni” da sauri Labiba ta kalleta, ta san cewa wannan ta girmeta nesa ba kusa ba, a k’alla zata bata shekaru 7 ko 8 chan kasan murya tace “Ina kwana” K’amshi ta murmusa har ta samo answer tambayarta, tace “Lafiya lau, aiki kikeyi ne?” Uhm kawai tace, murmushi ta sake mata tace “oya ayi aiki da kyau kar mama tayi fada” bata jira me labiba zatace ba ta juya ta shigewanta dakin Zaid.


In ran Labiba yayi dubu ya baci, bata kin mutane, ranta sai yayi kuri yake baci, amma sosai Yesmin ta bata mata rai, haka kurum take jin haushinta, ta dade tsaye da roba a hannu, abunda yafi bata haushi shine ganin Yesmin ta shiga dakin Zaid, kamar ta janyota ta daba mata wuka takeji, zuciyarta Zafi Zafi zafi, kishi kishi kishi.


Yesmin na shiga dakin Zaid ta danne kirjinta, zuciyarta kamar ya fito, tabbas yarinyar nan na son Zaid, ta karanto son Zaid a idanunta, tambayar shine Shin Zaid na Sonta? Waigawa tayi ta kalli Zaid da ke sheme kan Gado, da alama ko asuba beyi ba, kuma duk ta k’are ya banki shegiyar wato World jiya da daddare ba ta san sadda ta daka mata duka a baya ba.


Kamar jira yake yayi firgigit ya tashi ganinta Yamutsutsuke idanunshi, hararshi tayi tace “bakayi sallah ba” yace “Uhm” ta sake galla mai uwar harara tace “ai sai ka tashi kaje kayi” sum sum ya wuce toilet ta samu wuri ta zauna zuciyarshi cike da tunanin Labiba, sai da yayo wanka kafin ya dauro alwala, ya shigo ya kalli gabas yayi asuba.
Ya kallota yafe “ina kwana yas yas kamshi”
Ba ta iya fushi dashi tace “ka kwana ladiya?” Yace “Alhamdulilah” tace “munyi breakfast na san ba zaka ci Abincin cikin gida ba shiyasa ban diba ma ba”.


Murmushi yayi yace “zan hada da kaina” tace “ni yanzu kankia zaka rakani”.
Yace “yadai?”
Tace “lafiya lau, kayana zan kwaso, wai yajin aiki ake”.
Yace “to daga yajin aiki sai a kwaso kaya?”
Tace “to zaman me zamuyi?”
Yace “ku kuma haka kuke?
Tayi daria tace “nidai mu tafi”.
Yace “Okay barin yi breakfast”
Tace “muje mu siya a crispy sai mu wuce”
Yace “Okay muje”
“Wai kai baka da kaya ne sai wannan jallabiyan”
Yace “Yesmmmin mu tafi”
Dariya tayi tayi gaba ya bi bayanta tare da rufo dakin.


A kan idonta suka fito suka tafi, hawaye masu dimi suka ziyarci idanunta.
Jin motsin Aunty Asee ya sa ta goge hawayenta da sauri.
“Baban Amirah be aiko ba?”
Labiba tace “eh wai be kai ga aikowa ba”.
Okay.
Ba da dadea ba sai ga yaro da cefane daga kasuwa
Labiba ta amsa ta gyara kayan miya ta yi blending.
Aunty Aseeyah ta taimaka ta.
Bayan Azahar sun gama tuwo miyan ogu da yaji stock fish da ganda ”
Aunty Aseey tace “maza ki shiga kiyi wanka”.


Labiba tayi wanka tayi alwala, bayan tayi sallah ta shirya cikin wani Swiss Lace black and red.
Ta na cikin shiri Jawad ya kirata yace ya shigo Katsina zai yi Sallah a Masallacin matafiya da ke dandagoro sai ya karaso.


Da kwatance Jawad ya iso Gidansu Labiba, be sha wahala ba don sun taba zuwa Tudun Matawalle da yayyinshi, har k’ofar gida Jawad yayi parking.
Ta fito don tarbanshi.
Sam be ganeta ba, wani irin kyau ta kara, hotunan da take turo mishi kwata kwata basuyi kama da ita a bayyane ba, sai gani yayi ganin da yayi mata a farko bata kai haka kyau ba, MashaAllah, tsarki ya tabbata ga sarkin da ya k’agi wannan hallitar.


Takowa tayi cike da murmushi tace “Assalam Alaikum Jay, barka da zuwa Katsina ta dikko dakin kara” kasa amsata yayi sai murmushin da yake cizga baki zuwa wuy, da hannun ta mishi Alama da Bismillah.


Tayi gaba, ya bita a baya kamar rak’umi da akala, har suka shiga gidan da Sallama, kasancewar ba wuta parlon akwai zafi ya sa ta shimfida musu babban darduma a waje.
Zama yayi suka gaisa sosai. Labiba ta shiga daki tace ma Aunty Asiya su fito su gaisa.
Hijab dinta ta saka suka fito tare, cike da girmamawa Jawad ya gaidata, ta tambayesu ya ya bar su Umma ya amsa da Alhamdulilah. Ciki ta shiga Labiba taje kitchen ta gabatar mai da Abinci a kan tray.


Serving dinshi tayi, Jawad baya cin tuwo, amma yau sai da ya bude ciki ya ci tuwon nan mulmula daya da rabi, zobo da ya fara sha sai da ya shane kofi ya kuma kara, anya baby ba Aunty Aseey tayi abincin nan ba?
Dariya tayi tace “ ta taimaka min da kwashe tuwo da tukawa, amma ni nayi miyana nayi sobona”.
Dariya yayi yace “amma abincin yayi dadi sosai, baby wallahi kin k’ara kyau”
Hannu ta sa ta rufe fuskarta.
Binta kawai yake da mayattaten kallo, be iya surutu ba, be da hayaniya, sai ya zamana ma in ta ga kallon yayi yawa sai ta tambayeshi ina kaza ko ya kaza?.


Jawad miskili ne, kallon kallo da murmushi yafi firan su yawa, suna zaune aka kira Laasar tace “muyi sallah ko?” Yace “eh k’asaru zanyi, amma yanzu zan tafi gidan Baban Usman sai naje na gaida Grannynmu sai naje masauki, anjima zan dawo na gaida Yaya”.
Murmushi tayi tace “to shikenan”
Aunty Asiya ta fito ya mata Sallama, Labiba ta rakashi har bakin Mota.
Tsayawa sukayi suna kallon juna suna murmushi.


Motarta ta danno layin, tun daga nesa ya hango ta tana yashe hak’ora kamar audaga, ita ko kamshi tukinta takeyi ba tare da ta san meke going ba, waigawan da zatayi taga jikin Zaid na kyarma a tsorace ta taka birki tace “Zaid are you Okay?” Kasa magana yayi amma jikinshi ba inda baya rawa, idonshi kan su, Yesmin ta maida idonta kan inda yake kallo.


Kallo daya ta masu ta gano Labiba ce, ta kalli Zaid da ke tafasa a ranta tace menene haka? Kishi kenan?.


Tuni Zaid ya fita daga motar ya nufesu, tafiya yake be san inda yake jefa kafanshi ba, wani abu Jay yace mata da ya sata daria sosai tana kallon gabas ta hango Zaid da ya tunkarosu kamar wani zaki, cikinta ya bada kululu, gabanta ya fadi, jawad ya juya mai baya be san me ke tunkaroshi ba, Labiba kam tsoro da fargaba sun mamayeta, bata san me zaiyi ba, nan take ta tuna karon Yan Bencin Eskaley da AbuSideeq basu kwashe da kyau ba, har yau bataji daga Abu Sideeq ba, tsoro ya sake mamayeta, tuni zufa ya keto mata, ganin yanayin Labiba ya sa Jawad saurin juyawa ga abunda take kallo.
Hango wani yayi ya tunkarosu kamar namijin zaki...
“Me ke shirin faruwa?”


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN DA BIYU 2⃣2⃣
(ZANCE 👫 )


"Me kake shirin yi? Meke kake tunani Zaid? Menene haka?" Tambayoyin da ke zuwa mai a kai kenan, daf da su ya tsaya chak, yana kallonsu daya bayan daya kafin ya dawo da kallonshi ga Yesmin da tayi saurin shan gabanshi tare da fadin "Sweetheart, saurin me kake haka?".
Bakinshi ya mai nauyi da k'yar yace "bakomai, dama so nake na rigaki shiga Gida".
Hannunta ta sagala ana shi ta jashi tace "nak'i wayon mu shiga a tare".
Yace "motar fa?"
Tace "na rufeta".


Wuce su sukayi suka shige Gida, da Jawad da Labiba suka bi bayansu da ido kafin suka juyo suna kallon juna. Jawad mamakin abunda ya faru yanzu yakeyi, zai iya rantsewa da Allah cewa wannan tunkarosu yayi, wurinsu ya nufo, to ya akayi ya chanza akalan abun? Menene haka? Ya kalli Labiba da sauri ta girgiza mai kai! Da yake wani miskili ne be tsawaita abun ba sai yace ta shiga gida zai dawo anjima.


Da yake a k'agare take da sauri ta juya ta shige Gida. Jawad ya kira wasu Almajirai biyu ya bude booth yace su kwashe kayan da ke ciki su kai cikin gidan chan, jiki na rawa suka kwaso kayyayakin cikin booth.
Ya basu 200 sabuwa dal, sai da ya ga shigan su kafin ya shige motarshi ya mata key zuwa Gidan k'anin Babanshi Baba Usman.


Isan Zaid da Yesmin BoysQuaters yayi daidai da shigowar yara dauke da kaya nik'inik'i suna shela "Sallam Alaikum wai ance gashi a ba Labiba".
Dakatawa Zaid yayi daka shiga daki ya ga Labiba tayi wuf ta fito ta nufa yaran tace "wai inji wa?" Hade baki sukayi sukace "wani ne a waje a mota".
Labiba ta bude baki tace "tohhhh" karban ledar tayi yaran su ka fita a guje tana waigawa ta hade ido da Zaid da Yesmin, wani mugun kallo ta karanta a Idanuwan Zaid.


Ganin tafasan da Zaid yakeyi ne ya sa Yesmin riko hannunshi ta jashi zuwa dakinshi, labiba tsaye tayi nan ta bisu da idon da ya cika fal da hawaye.
Muryan Aunty Asee taji ta na cewa "mai muka samu?" Da sauri ta mayar da hawayenta ta mik'a mata ledar tare da shigewa daki ta bar Auntyn tsaye a tsakar Gida, Auntyn bata dau komai ba ta biyota baya tare da zazage ledojin kan Gado.


Leda daya kayan Zak'i ne kama daga Chocolates ne kalakala da biscuits cookies irin wanda taga ana talla a MBC2, dayar ledar kuma kayan shafa ne da turaruka masu k'amshi kala kala sai atamfar da taga an rubuta Juilius Holland sai wani Leshi.


A tare suka kalli juna ganin kayan da ke zube kan Gado, Labiba ta budi baki tace "wannan irin kaya da yawa haka? Anya Aunty zan karba kuwa? Gaskia bari ya dawo Anjima zan mayar mai" Aunty tace "uhm uhm, kayan sunyi yawa ga tsada kuma, bari dai yayanki ya dawo a gwada mai, duk mai yace hakan zaayi".
Labiba ba tace komai ba, Aunty Asee ta dauki chocolate diary milk ta fita tare da barin Labiba a daki ita kadai.


Kallonshi kawai takeyi, yana zaune sai ajiyar zuciya yake sauke lokaci zuwa lokaci.
Sosai ta tsura mishi ido, sai da ya lura da kallon da take mishi ya dawo dubanta.
Yesmin tace "KISHI kenan?"
Zaid ya murje idonshi na hagu yace "bangane ba"
K'amshi tace "ba zaka gane ba, ni ai nagane"
"Son yarinyar chan kake"
Borin kunya ya fara "So? Wace yarinya? Ni bansan me kike magana akai ba".
Yesmin ta yi wani murmushi mai takaici tace "ni na san maganar da nikeyi ai, kana son yarinyar chan, ka ganta tsaye da wani, zuciyanka na maka zafi, ranka na baci, bakinka na rawa, kishinta kakeyi".
A hankali yace "I dont know what you are talking about Yas".
Mik'ewa tayi tsaye ba tare da ta kalleshi ba tace "Bari inje Gida" ta fita.
Kiran sunanta yayi "Yesmin"
Ba ta juyo ba, bata tsaya ba ta bace wa ganinsa, bai da k'arfin bin bayanta, bai da karfin dawowa da ita, in shi a matsayinshi na Namiji yaji haka, ita ya take ji? God, me zaiyi yaji dadi? World kawai ya dauko ya zuk'e k'ulli uku yayi shameshame kan Gado.


Tana a daki taji Sallaman Yayanta, shimfida matarshi ta mai a waje ta gabato mai da Abinci, yana ci yana santin dadi chan yace "ba dai bak'on Abuja ya tafi ba" Aunty Assy ta bashi amsa da "zai dawo bayan Isha'i" yace "ya dai ci tuwo ko?" Tayi daria tace "yaci kam".
Daga waje taji Aunty Aseey na cewa "Labiba firdo ma Yayanki tsaraban Jawad".


Sai da ta bata lokaci kafin ta fita jiki a sanyaye "Yaya sannu da zuwa" tsokanarta ya fara yi ta rufe fuska tana daria, bubbude mai kayan Aunty Aseey tayi tace "ka dai ga abun Arziki shine Labiba ke cewa sunyi yawa ko za ta mayar" yace "Aseeyah ba rokonshi akayi ba ai, ko rokonshi kikayi?" Da sauri ta girgiza kai yace "to kinga, abunda zaayi, in yazo anjima, zan yi magana dashi, zan tambayeshi in dagaske yakeyi aure ya kawoshi, tun wuri zan turashi chan gurin su Baba, kar ki manta Alkawarin da nama Baba cewa da kin samu Miji zakiyi aure, kema da amincewarki na da kin samu Miji zaki tsaida Karatu, to in dagaske yake tunda yazo har

Please Login or Register in order to submit comment