Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




"Bayani suka ma Baba da su Mama kan cewa ba wani abu, jini ya taru sakamakon wani abu da ya shiga, amma sun diga magani, a hankali zai washe" Godia Baba ya musu tare da zama, be kalli Minyama ba da ke kuka ballantana Mama da ranta ke cike da Fargaba, tsoro, dana sani, suna nan zaune har Minti 30 suka dawo don bude idon, a lokacin nima na farka daga dan baccin da na samu bayan kukan da na sha".


"Warware Bandage din Likita yayi tare da cewa Zaid Bude idonka, sai labari ya sha bambam, da nayi yunkurin budewa sai nayi sauri na rufe, na yi hakan fiye a k'irga amma na kasa budewa, ba wai don idon ya manne ba, sai don tsoro, tsoro ya hanani budewa, Likita yayi, yayi amma na k'i budewa, fita Likita yayi don ya kira su Baba, kila in Baban ya min magana zan bude, nan su Baba suka shigo har da Minyama da Mama."


"Rungumeni Baba yayi, kamar jira nake na fashe da kuka idona na mai radadi fiye da zato, Baba shima kukan yakeyi, rik'e dani sosai ya ke magana a hankali "Zaid ka bude idonka, ka ganni Baba ne, Girgiza kai kawai nakeyi, hawaye na zuba daga idona, Baba ba zan iya ba".


"Baba yana kuka Sosai yace Zaid kar kace ba zaka iya ba, ba ka so mu cigaba da zuwa Filin Polo kallon Wasan Polo? Zaid in baka bude idonka ba, ta ya zaka ga na sa riga a bai-bai? Wa zai ce Baba ka zubar da miya a rigarka? Wa zaice baba-- Baba be k'arasa ba ya fashe da wani irin Kuka, duk mai rauni sai da ya tayasu".


"Jarumina, ka bude idonka kaji? A hankalina na fara bude idon ko second 3 beyi ba nayi sauri na rufe don ji nake kamar ana barbada min barkono a ciki".


Hannu Baba ya daura a kai kamar dan yaro yace
"ta nakasa min shi, shikenan yaro na ya zama Makaho".


Likitoci dai sukayi bakin k'okarinsu don ganin na bude Ido amma na kasa, sun sake bincika idon sun tabbatar ba komai a ciki, tsoro ne kawai, sai suka yanke shawaran bari na na dan kwana biyu, k'ila kafin lokacin tsoron ya fita a raina.


"Ba inda Baba yaje a Asibiti yake kwana, ba ya cin Abinci, dangi sai tururuwan zuwa gani na suke duk da an hanasu shiga, Mama duk ta fita hayyacinta, tana tsoron abunda zai faru, har yanzu Baba bai ce mata komai ba, duk da itama da ita ake zaman Asibitin, rashin mata magana na damunta matuk'a".


Har a kwana biyun ba wani Cigaba, haka suka sallamoni, sukace da Baba a hankali zan bude Idon, Baba ya ji haushi sosai har ya kusa dukan daya daga cikin likitocin, be koma dani Gida ba, sai wucewa dani Abuja da yayi, ba wanda ya san inda muka nufa, hankalin kowa tashe yake.


Lokacin Duniya a kwance take, ya mana processing zuwa k'asar Italy don zuwa Asibiti, ba a jima ba mu ka tafi Italy daga ni sai Baba, ba wanda ya san inda muke a Gida, Minyama Kuka, Mama Kuka.


Satinmu 2 a k'asar Italy, wanda suma kamar a kasar mu Najeriya, ba su ga komai a idon ba, illa tsoron da suka gani a tattare da ni, pediatric vision therapist shine ya duk'ufa wurin ganin na bude idon ta hanyar exercising idon kuma Alhamdulilah tsoron ya ragu sosai don yanzu ina dan bude Idon hagun amma ba completely ba. sai ya zama ina kanne idon kamar wanda ke tsoron wani abu zai shiga.


Ba yanda zasuyi dani don hakan ya zame mini Habit (Dabi'a) sallamarmu sukayi muka dawo Nigeria Abuja muka dan huta. Daga kallon Baba ka san cewa bai ji dadin sakamakon da muka samu a K'asar italy ba to amma ya zaiyi? hakan yafi da ace danshi ya makance gabaki daya, da ya kalleni sai yace "Zaiduna kayi hakuri, an nakasa min kai" ni sai dai na kalleshi.


Haka muka dawo Katsina, kowa yayi farincikin ganinmu, barinma Minyama da ta kasa kawaicin sai da ta rungumeni tana hawaye, Mama kuwa tsoro ya hanata magana har yau bata san Matsayinta ba, nima ban saki jiki a gabanta ba. Baba ya rik'eni yayi dakinshi dani, mukulli ya a ma dakin, don bai yarda da kowa ba, toilet ya fada, don yin wank, su Minyama kuwa suka shiga kitchen tareda Mama don yin abincin bak'i. Minyama ta lura da dari-dari da Mama keyi, ita fa har yau bata san me ya faru da ni ba.


Dangi sai zuwa mana Barka suke, a lokacin da Baba ya fito daga wanka, ina nan zaune yace muje na ma wanka, tubeni yayi ya min wanka kafin ya shafa min mai, ina da kaya a dakinshi, ya ciro min riga da wando tazarce irin nashi, anko mukayi, sai da yayi rubutu a 'yar takarda kafin ya rik'o hanuna ya jani zuwa babban Parlo inda yake cike Mak'il da 'yanuwa da abokan arziki, harta hajiyansu Baba su Mama Asabe sun rik'ota sun kawota.


Sai da Baba ya je gabanta ya gaisheta kafin ya fara amsa gaisuwan mutane, har yanzu yana rik'e da hanuna idona daya bude daya a kanne.


Baba Sani yace "wai yaya Ali me ya samu Zaid a ido, daga asibiti ba mu kara ganinku ba?" Baba yayi murmushi mai zafi yace "Zaidu ka gaya musu meya sameka a ido ranar nan da na dawo daga lagos" idanuwa suka dawo gurina na dan sa hanuna na murza idon, na kalli Minyama da ta yi kasak'e don son jin me ya samu idon, nayi imani kuma gaban mama na ta faduwa ganin yanda tayi firifiri.


"ba Mama bace ta wurgo min cokali me yatsu a ido don wai naci abincin da ta ma Baba"
Daki ya kaure da Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, Minyama ta bude baki cike da mamaki, ko da wasa Mama bata taba gaya mata abunda ya faru ba.


Ita ko Mama kamar kasa ta bude ta shige ciki, ta rasa mai zata yi, dangi sun samu abunda suke so, nan kowa ya samu abunda yake fada.


Gyara murya Baba yayi, yace "In Zaid yace Mama to kuwa kun san Shafa'atu yake nufi, auren Soyayya mukayi da Shafa'atu, na aureta ne saboda ta na So na, nima ina Sonta, amma meye amfanin Zamanmu in har bata son abunda na haifa?".


Wasu sukace ba amfani.
Baba yace "ba na tauye mata hak'k'inta, ina biya mata buk'atunta, laifina, na ba Zaid abincin da ta girka min, wai Abinci, ta kan abinci ta nakasa min shi.


Da kunne na na ji Shafa'atu na ce ma Zaid ta tsaneshi, da kunnena wallahi naji tace da ta san hbaka zai zame mata da ta markade cikinshi tun kafin ya zama gudan jini, wai yaro kamar Zaid ake ma wadannan maganganun".


Magana daya ce, ba zan iya zama da wacce bata son Gudan jini na ba, ba zan iya zama da wanda ta tsani farincikina ba, kin nakasa mishi ido nan gaba ban san me zaki nakasa mai ba, Shafa'atu na tsaneki kamar yanda kika tsani Zaid, a yanzu kuwa na Sakeki SAKI UKU ga takardarki.


Jikin kowa sai da yayi sanyi, Minyama na can rakube sai da gabanta ya fadi, ita ko Mama jikinta sai rawa, idanuwanta na ta ambaliyar hawaye, kana iya karanta tashin hankali daga fuskarta, bakinta har wani rawa yakeyi hak'oranta na bugun junansu da karfi, durkusawa tayi a gabanshi, tace "Alhaji, donAllah kayi hakuri, kar ka sakeni, kayi hakuri, wallahi ina son Zaid, dama sharrin shaidan ne ya sa nayi abinda nayi, kuma wallahi tsautsayi ne, ba ma da niyya nayi ba, amma tun lokacin Alhaji banda wani kwanciyar hankali, donAllah ka yarda dani, muje ciki na maka bayani, nidai kawai ka janye, ba zan iya rayuwa ba kai ba".


Mik'ewa Baba yayi yace "kin taba ganin inda aka janye Saki 3? To in baki sani ba, ba aure tsakaninmu, Aurenki ya gama a kaina.
Baba ya ja Hannuna ya yi ciki dani ya bar kowa zaune
Banda Mama da ta ke burgima a k'asa tana wasu surutai mai kama da Sambatu.


Ni Ali zaka wulakanta? Ni ke tare da kai tun kafin ka san kanka, yau ta kan yaronka ka wulakantani gaban matsiyatan k'anenka, ni Ali? Bayan son da nuna maka? Sai chan ta fashe da wani irin kuka mai karfi, da yawa sun tausaya mata, haka suka fara fita daya bayan daya.


Da k'yar Minyama da ke daskare wuri guda ta taso don lallasanta, amma cikin zafin nama Mama ta tureta wanda hakan yayi sanadin faduwar Minyama akan wani table dake kusa da kujera, Minyama ta sak'i yar k'ara, su Asabe da suka rage a parlon suka yo kanta.


Dukan Shafa'atu suka fara yi don har ga Allah ba sa sonta, Ladidi ce tayi dakin Yaya Ali don sanar dashi Minyama na fitar da jini ta goshi.


A sittin muka fito, Baba ya kamata ya rik'e don zuwa Asibiti, bayan ya kira Securities dinshi suka fitar mai da Shafa'atu daga gidan a wulakance.


A Asibiti a ka ma Minyama Dressing muka dawo Gida, ta birkice ma Baba tana kuka tace "Alhaji, ba ka kyauta ba, irin sakin da Manzo baya so, shi kayi haba Alhaji" ranshi bace "wai ke wace iri ce? Ba kiji abubuwan da tayi ta kuma ce game da Zaid ba? Kurma ce ke? Kika san tun yaushe take mai mugunta yanzu da Asirinta ya tonu ba sai ki gode ma Allah ba da a nan abun ya tsaya, Allah kadai ya san abunda take mishi, kwanaki da yake cewa tana rankwashinshi yar barikin ba karyatawa tayi ba harda kukan munafunci? Nifa da ba ke kika haifeshi ba da na ce ba kya sanshi.


Tace Alhaji wallahi Kishi ne, duk macen da zaka aura dole tayi kishi da Zaid ba laifinta bane yace Shiyasa ba zan sake Auren ba, ke kadai kin isheni, ta dan sausauto da murya tace "ko in ta sake aure zaka Maidota?" ke Hajia Maryama ki fita Idona, ke Hajia Maryama ki kiyayyeni, zan mugun bata maki rai, a duk randa kika sake min maganar Shafa'atu, na dai saketa ko? Na kuma wuce gurin, ke kuma in da Dan Cikinki zakiyi Kishi zaki sha Mamaki, zan manta da Usmanu abokina ne na miki Rashin Mutunci, haka Baba yake yi in har yana fada a kaina idonshi rufewa yakeyi, Son da Baba ke min ya wuce tunaninki Labiba, ba zaki iya gane adadin Son da yake min ba.


Minyama jikinta yayi sanyi, kar fa garin neman gira ta rasa ido, garin gyara auren wata ta bata nata, tun daga ranar bata sake maganar Mama ba,
Mu dai ba mu san ya take ba, ko ta zo Gidan ba ma sani don Already Baba ya sa matakan tsaro na kar ta sake zuwan mai Gida. Haka muka shafe Mama a rayuwanmu.


YanUnguwa, Abokanan wasana, Manya da yara suka koma ce min DANMAKAHO, don da Ido daya nake amfani, abun har ya zame min jiki, don ko da yaushe ido daya a bude daya a rufe, Baba ba ya son sunan amma ya ya iya? Niko yarinta a lokacin har kidi a ke min ana min Wakan Zaidu DanMakaho me rijiyan naira niko inta rawa na ba tare da wata damuwa ba.


Duk wanda ya kirani da DANMAKAHO amsawa nake bai dameni ba, da yawa kan ce ina da wautar 'yan fari, amma fa sosai nake da farinjini, in dai na fito, to ko ina na shiga zakiji ana DanMakaho, DanMakaho manya da yara.


Wai kin san abun mamaki?bayan sakin Mama da shekara 2 Minyama ta samu ciki har ta haifeshi bayan wata 9?
Labiba ta jinjina kai tace "ikonAllah your Sister?" kai Zaid ya daga mata yace "lokacin aka haifi Halimattu Saadiya taci sunan Hajiyar Baba, tsakanina da ita Shekaru 11, kuma wani ikonAllah daga nan Minyama bata sake ko da batan wata ba.


Darling kamar yanda Baba ke ce ma Sadiya, ta fini haske, ta na kuma da shiga rai kinsan yanda mu ke sonta kuwa?" Sosai ta samu Soyayyar mu 3, ni Baba, Minyama sai kuma dangi, wallahi ta tashi cikin So da K'aunar kowa.


Ta yi Girma da Wayau, ta shiga Makaranta lokacin nikuma nagama na shiga Secondary.
Zaid ya dan murza idonshi tare da yin wani guntun murmushin da ya burge Labiba da alama wani abu ya tuna, ta nutsu tana kallonshi ta ji muryarshi ya cigaba da cewa "wai kinsan In Baba yace mata Darling ita mai tsiwa sai tace ba Darling ba Dalo, nikuma sai ince Dalo wai kuma sai tayi ta kuka" Labiba ta murmusa itama, murmushin ya sake yace


"Ni dan Boko wai sai na ke cema Minyama Momcy"Dalo bata iya cewa Momcy ba amma da tsamin bakinta sai da ta sa mata sunan da har gobe ya bita, kinsan me take ce mata?" da sauri Labiba ta girgiza kanta tace "Momso?" dariya ta ba Zaid wanda yana yi yana murzan idonshi kuma hakoranshi sun bayyana".


Tace "Atoh, ai naji ance mata Darling tace Darlo, Mumcy kuma sai Momso ko?"


Kayyatacen murmushi yayi yace "Mancy, Mancy ta ke ce mata".


Sunan da Darlo ta sanya ma Momcy kenan, ni Mancy, Baba ma Mancy, kowa ma Mancy, rayuwarmu gwanin ban shaawa, muna da Gata, kudi, kwanciyar hankali, muna kyautata ma Makwafta da danginmu, muna taimakawa duk wanda yazo mana da kukanshi, muna sharewa ma wanda ya tunkare mu da matsalarsu hawayensu, kuma ko wani Gida a Anguwar na da kwanon Abinci rana da dare.


Labiba wallahi ba mu san akwai wani abu wai shi damuwa ba, Baba da Mancy na biya mana ko wace irin bukata.
Motoci na sunfi 3 wanda duk baba ya mallaka minsu, kudi a account dina kuwa sai na rasa me zanyi dashi.


Bamu san komai ba sai Jin Dadi, Farinciki Annashuwa.


Da lokaci yaja Baba ya sake fantamawa cikin Siyasa, Mancy ta zama Sister a General Hospital, ni kuma na tafi karatun Degree a London bayan an sha fama da Baba wanda da k'yar ya yarda na tafi karatun, amma kinsan duk hutu ina dawowa Gida, in ban zo ba su zasuje, duk a lokacin duniya na kwance.


Wani dawowa hutu da nayi na san Yayanki, Baba ya aikeni da dubu 10 Gidanku, yace ka shiga gidan da ke jikin gidan nan, ka kaima Muhammadu kace gashi ya siya Rago yayi hidimar Suna inji ni, da na tambayi Mancy waye shi sai ta ce min wani Matashi ne mai sanin ya kamata, Ba su dade da dawowa garin ba, matarshi ce ta haihu, nace "ayyah Allah sarki, barin kai mishi sakon Baba" Lokacin aka haifi Ameera diyarki.


Na koma Makaranta na hada Degree dina, mai makon na dawo gida kawai sai na Jona Masters dina bangaren abunda na karanta wato Engineering.


"Ke nagaji"


Ya fada ya na me fito da kwalin Sigari a gefen Wandonshi, kallon mamaki ta bishi dashi, a ranta tace "ba dai Sigari zai sha a gabanta ba, aa ba shi bane, ya zai sha Sigari a daki?" a sannan hancinta ya jiyo mata warin sigarin da ya dade a dakin wanda sai yanzu ta ankare da warin meye.


Ba ta lura ba sai ganin hayak'i tayi na tashi, zabura tayi ta kalleshi, ashe tuni ya kyasta sigarin nan yana bankama cikin shi hayak'i.


Baki sake Labiba ke kallonshi, DanMakaho ya wuce tunaninta, kasa daurewa tayi sai da ta tanka tace "yanzu a daki ka ke shan Taba?" banza yayi da ita, sai ma kara kunna wata da yayi.


Ba ta yi shiru ba tace "ina laifin ka fita daga waje, ni gashi hayak'i ya isheni, kasan ina da athma" tarin k'arya ta fara yi.


A tak'aice yace "Fita"


Da sauri ta tsaida tarin k'aryanta, ta na son jin karashen labarinshi, akwai tambayoyin da take son ya amsa mata tace "ai bance zan fita ba, gani nayi bai kamata ace kana shan Taba ba a daki ba".


"Dakinki ko nawa?" ya soko mata tambaya da sauri tace "aa nakane, Allah ya baka hakuri".


"Kinga bansan wannan san iyawan da kike min ko?" Murmushi tayi tace "kayi hakuri".


Jikinshi yayi sanyi "Ok, kina ji ba? Komai ya chanza ne a ranar da na dawo Naija, wani hutu mukayi na dawo Gida".


Ranar da ba zan taba Mantawa ba, muna zaune a Bukkar waje Ni,Mancy da Dalo muna shan Fruits, dama Daddy yayi tafiya kwananshi 8 ba ya gida yaje Abuja wani aiki.


Sai ko ga Motocin Daddy sun shigo harabar Gidan, gabaki daya muka tashi don murna, mu uku muka hau rigerigen karasawa ga Daddy.


Sai ya fito kanshi a dage, maimakon ya kula mu da muka zak'u da ganinshi, sai dauke kai yayi ya zagaya ta dayan side din motar, a lokacin muka fahimci cewa bayan Odilenshi akwai mutum a Motar.


Wata Mata muka ga ta fito daga bangaren da Daddy ya bude k'ofa, ta fito ta na mana kallon kaskanci, gabana ya fadi na kalli Mancy wanda itama na rantse gabanta ya fadi, duk tsawon shekarun nan, duk rashin wayau na a wannan lokacin fuskar nan bata taba gushe min ba".


A kagauce Labiba tace "Wacece?" Zaid yace "Wacce tayi sanadiyar da ake ce min DanMakaho" Labiba ta zaro Ido tace "Aunty Shafa'atu?" Zaid yace "Exactly" labiba tace "Ya akayi? How comes? Wai itace dama Aunty Shafa ta yanzu? Ba saki uku Babanku ya mata ba?".


Sigari Zaid yaja Sosai ya furzar cikin bacin rai ya cigaba da cewa
"Ni da Mancy muka tsaya kallon kallon, Dalo bata santa ba, da gudu ta karasa gun Daddy don ta rungumeshi, yanda kika san wanda Kashi ya taba, haka Daddy ya zabura da da Dalo ta nufoshi, Dalo bata fahimci yanayin Daddy, ta kara kusantoshi, da wani Zafin nama Daddy ya ture Dalo ta fadi k'asa"


Mamaki ya rufe mu, da sauri na k'arasa gun Dalo na dagata don ta fara kuka, da murmushi a fuskana mai dauke da mamaki nace "Daddy sannu da zuwa" wani irin muguwar hararar da ban taba ganin Irinta ba Daddy ya wurgeni dashi, gabana yayi mugun faduwa a lokacin da na hango tsana a idon Daddy, lokaci daya wallahi Allah na fita hayyacina".


Mancy na tsaye fa, mamaki ya gama kare mata, da k'yar ta iya daga k'afa ta karaso tace "Sannunku da zuwa, Hajia Shafa, Baban Zaid,Sannunku da zuwa".


Kamar jiranta Baba yake "Baban Zaid? Kar ki sake kirana da wannan sunan, ke ki ma fitar min a Gida Na Sakeki Saki Uku Maryama bana sonki bana son ganinki".


Wani tsalle nayi na rik'o Mancy da ke niuar zubewa,Hankalina a tashe, Mancy kuwa kasa motsi ta yi, Dalo kuwa ta fashe da kuka ta karasa gun Daddy tana jijjiga shi "Daddy me kake cewa? Me ya faru? Daddy wacece wannan?".


Turetan Daddy ya sake yi, yace "muje Hajia Shafata" Hamshakiyar sai yanzu tayi magana tace "yi gaba Alhajina gani nan zuwa" kamar jiran umurni yake yayi gaba, takowa tayi kusa da mu tana murmushi mai kama da na mugunta.


Idonta a kaina tace "Zaid, ko ince DanMakaho, ina fatan baka manta ni ba? In ka manta ni zan tuna maka, ba zan so ka manceni ba, yanda ban taba mantaka ba, kaima ba zaka taba mance ni ba, yanda na tozarta a sanadiyarka sai ka wulakanta a sanadiyata, sai ka zama abun kwatance a garin Katsina"


Ta kalli Mancy tace "Alkawari nayi, duk randa na shigo cikin gidan nan ke kuma zaki fita"


Ta kalli Sadiya tace "Dalo ko? Ba a taba baki labarina ba? Nice Aunty Shafa dinki,Matar daddy dinku, shekarunki sha biyar? Shekaruna 16 rabona da gidan nan, na kuma dawo ba fita".


Ta na kaiwa nan ta wuce ta barmu tsaye, kowannenmu hankali tashe yake, bamu da wani sauran farinciki daga ranar, galihun mu ya bace, komai ya watse mana, duniyarmu ta koma k'ankanuwa".


Labiba ta fashe da kuka tace "ni fa ban gane ba, Ina Mancy? Me ya faru bayan nan? Ni har yanzu banji me nake son ji ba, donAllah ka gaya min". Kuka take sosai.


Zaid ya tashi tsaye yace "kinsan Allah nagaji, yunwa nikeji, ya dade da nayi magana mai tsawon haka, kar ki damu wata rana zan idasa gaya miki labarin, kawai dai a gurguje Mancy na aure a Abuja ta na da diya daya".


Kina son sanin meyasa na tsinci kaina a yanayin nan? Its obvious amma na miki alkawarin ida baki labarin, but a takaice zan iya shan kwalin cigari biyar a rana shisa 'yan bencin Eskaley suke ce min MANKAS.


Hello Bibilicious fans, afuwan, komai ya daidaita nagode da adduoinku da fatan alherinku gareni.


#Ilove
#DM
#SonSoFWA
#anatare
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Tara (ABUNDA YA FARU)


Labiba na ta girgiza kai tace "donAllah ka gaya min mai ya maidaka haka?".


Dan kallonta yayi lafij yace "are you not listening? Ba ki fahimci duk abunda na fada miki ba yanzu? Isnt it obvious? Matar Uba ta maidani haka, ke ko komai sai an gaya miki kafin ki fahimta?".


Sausauta murya Labiba tayi tace "naji, ina son sanin Meyasa ka fara shaye-shaye? Wacce rana ka fara shan Sigari? Meye dalilinka na shan Sigari?"


Kallonta kawai DanMakaho yayi, mai take so ya sanar da ita baya ga abunda ya gaya mata yanzu? Ya lura ta na da naci sosai, tsaki yayi ya yayi hanyar k'ofa yace;


"Nagaya miki yunwa nakeji, ina da buk'atar cin abinci".


Gunguni tayi tace "da kana jin yunwa da ba ka banka ma cikinka wuta da sassafe ba".


Waigowa yayi yace "me kikace?"


Baki ta zumburo tace "fa banyi magana ba".


Kai ya girgiza sosai yace "kina wasa dani Labiba, zan miki hankali"


Ya sa kai ya fice, da sauri ta mik'e tsaye ta figi jakkarta ta bi bayanshi.


"Tsaya, ya zaka barni a nan?" Be juyo ba yace "dama ni na kawo ki?" "To wai ta ina zan fita?" Bai fasa tafiyar ba yace "ta inda kika shigo".


"Seriously?" Bai amsata ba yayi gaba abunshi, ba ta da zabin da ya wuce ta tsallaka fasassun bulo ta ketara zuwa Gidansu.


**__**_**_**_**_**_**_


Wannan Sakin da Alhaji Ali ya mata, ya girgiza duk wani gabban jikinta, ta san dole ya dau hukunci, ta san shirun da ya mata yana neman hukuncin da ya dace da ita, amma Saki? Saki har uku? Ba ta tunanin ta canchanci Saki Uku, ita da ta soshi tsakaninta da Allah, tun bai kai haka ba, ta zauna dashi da dadi ba dadi, ta shanye bakincikin da danginshi suka ta k'unsa mata, wai ita ya saka saboda danshi? yanzu ya zata yi? Ita fa ba ta so ta yarda, don tunanin na barazanar fasa mata kwanyar kai.


Yunk'uri tayi daga inda take durk'ushe a tsakiyar unguwa ta nufa Gidan da niyar shiga, sai dai kash akwai masu tsaron Gidan, suka sa mata fullstop daga bakin gate, tayi magiyar ta yi haukan amma a banza, wani ma daga cikin securities din ya shaida mata in ta sake zuwa zai ya daureta.


Kuka Shafa'atu keyi sosai, kallo daya zakayi mata ka san tana cikin tashin hankali, da ta ga ba sarki sai Allah, sai ta ja kafarta ta nufa Unguwarsu Aminiyarta Er Rabi.


Hankali tashe ta isa Gidan, jikin kawarta ta fada ta fashe da kuka mai ban tausayi, hankalin Er Rabi ya tashi, ta shiga lallashinta da kyar ta samu ta bata labarin duk abunda ya faru.


Kirji Er Rabi ta dafe, Saki uku? Yau an shiga uku, a kan wani dalili zai sakeki? Shi be san tsautsayi ba? Hmm Shafa'atu, wallahi banga laifin kowa ba sai laifinki, tun yaushe nake binki kan ki barar da cikin Maryama? Tun yaushe nake ce miki a batar da Zaid, saboda ni wallahi na san yaron nan shi zaiyi Sillar barin gidan ashe Hassashe na ya tabbata, yau mun shiga uku, sai da Alh Ali ya fara mahaukacin Azziki zai sakeki?"


Kuka Shafa ta fashe dashi tace " nidai ki taimaka min in koma, magiya ta fara yi mata, Er Rabi ta lura kawarta na son zarewa, dawowa kusa da ita tayi, ta tariyota jikinta tana lallashinta tace "kinsan dai a yanzu ba aure tsakaninki da Ali, sai kin sake wani

Please Login or Register in order to submit comment