Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi da sauri na nufi dakin

Yana zaune a inda yake ganin shigowata yasa ya fara yunkurin sauka kasa. da sauri na janye kwandon abincin dake gaban gadon ya zuro kafafunsa a nutse ya mike tsaye bayansa nabi da kallo ganin ya nufi toilet yasa na sauke ajiyar zuciya.

Ina tsaye a gurin ya fito muka hada ido, kaina na sunkuyar kasa ina jin faduwar gaba kada'n kad'an, idan na kalli fuskarsa sai naji zuciyata na karyewa nima yanzu na tabbatar da cewa yana da makiya gaba da baya dalilin daya sa kenan naji zan iya sadaukar da rayuwata a kansa tausayi yake bani.

K'asan kafet ya zauna ba tare daya kalleni ba yace."Ki zuba min abinci nasha magani na kwanta bacci nakeji." Nace"to ranka ya dad'e." Kwandon abincin dake gabana na janyo na fara kokarin fito da fulas din dake ciki......Yace."Kada ki bude wannan dauko wancan na aunty Sakina shine nake bukata dan nayi mata al'kawarin cin abincinta."
A nutse na mayar da fulas din hannuna na janye kwandon gefe na dauko wanda ya bukata.

Cikin nutsuwa na fito da komai na kwandon na dauki plate mai dan zurfi na bude fulas din dake dauke da abincin. pride rice ce a ciki taji kayan lambu da nama amma kuma qamshin da take yasha bambam dana lafiyayyan abinci....Tsirawa cikin fulas din ido nayi ina duba abincin ciki. nan na hango taratsatsin magani a ciki dan wani gefan ma har ya rine da kalar maganin, kallonsa nayi gabana na fad'uwa yanzu ya za'ayi na fad'a masa abinda ke da akwai.

Kallona yayi yana yamutsa fuska yace."Zaman me kike ne ke nake jira fa." murya na rawa nace"Ranka ya dade abincin ya lalace." Wani irin kallo ya watsa min da fadin"Kamar yaya ya lalace."? Nace"Eh duba ka gani wallahi ya lalace gashinan kamshin sa ya sanja."

Tsaki yaja tare da fadin"Kinga bana son wata magana ki zuba min abinci naci koda tsutsa ke fita a cikinsa to tunda nayi alkawari sai na cika." shuru nayi ina sake sake a raina.

"Wai ba zakiyi aikin dana saki ba." Cikin tsawa yay maganar.......Cikin jin tsoro nace"Wallahi abincin bashi da kyau ba zaka ci ba." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta, a fusace! yasa hannu zai Dauki fulas din abincin nayi gaggawar daukewa. bayana nasa fulas din ina kallonsa kwallah ta cika kwarmin idona.

A murtuke yace."Ina wasa dake ko."? girgiza kaina nayi ina nufin aa. Yace."To zuba min abinci bani da lafiya bana son hayaniya." Hannu nasa na dauke kwallar data taru a idona nace"Sai dai na zuba maka wancan dan wannan da kake so kaci bashi da kyau." Yace."Wai cikin ki ko nawa ? ina ruwan ki idan naci lalataccan abinci cikina ne ba naki ba sannan nayi wa 'yar uwata al'kawari zanci abinda ta kawo min."

Nace"Kayi hakuri ba zan iya baka kaci abinda zai cutar da kai ba dan kai amana ne a hannuna." Kallona yayi yana mamakin maganata, yace." Wai Saboda me bakya son naci abincin aunty Sakina ne."? bakina ne ya su'buce da fad'in "Saboda akwai guba a ciki."
Gani nayi ya murtuke fuskarsa "me kike nufi? kina nufin anty Sakina zata cutar dani kome."? kai tsaye na daga kaina " Zata iya cutar da kai tun ba.......! kafin na karasa ya wanka min mari a kumatuna. cikin gigita nake kallonsa bakina na wani irin rawa so nake na fadi karshen maganar amma na kasa sakamakon marin daya waska min. kallon banzan da yake min yasa nayi gaggawar yin kasa da kaina.
*BINTA UMAR ABBALE*


*LAST FREE PEGE*
Kada ki sake ayi wannan tafiyar babu ke 'Yar uwa kada ki saka ganin kyashi a kan abinda kike so ki kauda kanki ki biya #300 ki karanta littafin nan hankali kwance........Vip gruop#600 Normal gruop#300 idan kati zaki turo #400 ne.



*PAID BOOK*
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
BABBAN YARO
MASHAHURI
SADAUKI OMAR
LADIDI KWADAGA
TSANTSAR BUTULCI
DA WATA A KASA
NIDA YAYA SADAM
YAR BANGAR SIYASA
MADADI

Kai tsaye zaki iya samun wa'innan littafan idan kin tuntu'bi wannan numbers
*08089965176*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
43&44
Yau dai nayi rantsuwar akan ba zan ta'ba jikinsa ba saboda na lura da gayya yake sani ina matsa masa sassan jikinsa da sunan tausa, na riga na gane ba manufarsa tausar ba burinsa kawai na dinga tatta'ba masa jiki yana sakin nishi da rungume fillo tun ina dau'ka abin nasa wasa har na tsargu da abunda yake a duk lokacin da nake masa tausar ya dinga juye juye a gadon yana matse fillo a kirjinsa idan yana ji da iskaci kuwa ya dinga danne min hannu kenan yana kwantowa jikina wannan dalilin yasa na gane ba tausar yake bu'kata ba.

Kafin goma na dare tayi zurga-zurgar jama'a yayi sauk'i, kamar koda yaushe muka shiga dakin domin yi masa bankwana yana zaune ragal dashi tamkar ba wanda yake jinya ba har wata qiba yayi ya kara haske hakan baya rasa nasaba da irin kulawar da yake samu a gurina , ni na tabbatar da cewa daba dan na tsaya a kansa ba da tuni makiya sun kaishi k'asa amma baya ganin hakan kullum cikin yi min masifa yake yana hantara ta mussaman idan yazo cin abinci nasa ido ko kuma na nuna ga wanda nake so yaci shi kuma sai yace ba zai ci ba, wanda bana so yaci shi zai ci, haka zamuyi ta jayayya da juna har sai Dr ya shigo ya raba gardamar dake tsakaninmu, haka yake hakuri yaci za'bin da nake so.

Su Haruna bayan sun masa sallama sun fita sai nima na kalleshi yana kokarin miqe kafa kan gadon nace"Nifa yau ba zan samu zaman tausar nan ba."?

Ya kalleni da fadin "Dalili."? Kai tsaye nace" Saboda ba itace manufarka ba." Shuru yay yana kallon wayarsa, Nace"Sai da safe." kai tsaye kofar fita na durfafa ina addua a cikin raina.

"Sumayya." Sunana naji ya kira tamkar a bakinsa aka rad'a sunan. tsayawa nayi ina kallonsa. gani nayi yana min sauk'akaken kallo cikin taushin murya yace."Zo muyi magana." Ganin alamar sassauci a tare dashi yasa na koma da baya

Gefansa ya nuna min a hankali yace."Zauna." banyi musu ba na zauna ina kallonsa. hannuwana ya rike a nashi yana min wani irin kallo wanda yasa tsigar jikina tashi, risinar da idona nayi dan ba zan iya jurar hada ido dashi ba.

"Kin same."? yafada a kasalance. Girgiza masa kai nayi nace" Sai ka fad'a." "Ina mutukar sha'awarki." Yafada yana bin ilahirin jikina da kallo.

Gabana ne ya dinga faduwa ina kallonsa ina mamakin maganarsa yana sha'awa ta wace irin sha'awa yake min.

Bakina na rawa nace"Ban gane maganar ka ba." Murmushi yay yasa hannu ya shafi gefan fuskarta da fad'in "Nasan dole zaki shiga mamaki da rud'ani in kikaji irin sha'awar da nake miki Sumayya komai na jikin ki yana burgeni yana k'yatar dani tun ranar dana d'ora ido a kanki na rasa gane kaina wallahi kinji rantsuwar musulmi kullum da sha'awarki nake kwana da ita nake tashi ki taimaka min ki bani kanki na mori albarkatun jikinki ni bance dole sai na shiga ramin ki ba wa'innan kawai nake so ki mallaka min." Yak'arashe maganar yana kokarin kai hannunsa kirjina........A zabure na bige hannusa na kalleshi ido cikin ido nace"Ina ce na fada maka ni ba 'yar iska bace ko."? Shuru yay yana kallona.
Cikin k'unar zuciya nace"Wato abinda zaka sakamin dashi kenan na kwana na yini a bautarka amma kake nema ka lalata min rayuwata to bari kaji ni ba 'yar iska bace jikina kuma na mijina ne wanda yake kaunata saboda Allah ya kuma biya sadaki aka daura mana aure da juna, kayi hakuri idan maganar da nayi ta b'ata maka rai kuma insha Allah ba zan fad'awa kowa ba." cikin rawar murya nake maganar ina mamakin al'amarin.


Kansa a kasa har na kare maganata ya kasa cewa uffan! haba ai dole yaji kunyar hada ido dani a ganina ban cancanci haka a gurinsa ba.......A sanyaye na zare hannuna dake cikin nashi na kama hanya na fita daga dakin,

a daran kafin nayi bacci na jima ina mamakin al'amarin dama jikina na bani sha'awata yake shiyasa kullum yake k'ureni da ido amma ban ta'ba tsammanin zai iya yin gaba da gaba dani ya fad'amin yana sha'awata na mallaka masa kaina, wato ashe dama a turai abinda yake aikatawa kenan.? humm! gashi dai fuskar salihai gareshi ashe shima shaid'anin kansa ne, to kuwa tunda haka ta kasance tilas nayi takatsantsan dashi domin kada ya samu nasarar cutar da rayuwata. da wannan tunanin bacci ya daukeni mara dadi da mafarka marasa kyawu.


Da safe tsaf muka sameshi kamar koda yaushe sai kamshin turare yake dakin ma haka, yana zaune a gefan gado suna magana da likita.

Muna shigowa likita yace."Yawwa gatanan ma ta shigo idan kayi breakfast din sai kasa maganin insha Allah anjima zan shigo a kwance daurin dake kanka.

"Okey." kawai yace ya dauke kansa, likita ya kalleni a nutse yace."Sumayya ga magungunan nan kan drowar ki bashi idan yayi break." Da sauri nace"Insha Allahu zan bashi.
Dr fita yay daga dakin, su Haruna suka shiga gaishe shi ya amsa a dakile yana kokarin kwanciya, fita sukayi daga dakin

A sanyaye nace"Yallabai barka da safiya ina fatan ka tashi lafiya." ? banza yayi min ya rufe idonsa, na dinga nazarin fuskarsa inaso nagano ainihin abinda yake damunsa, ba wani abu bane yake damunsa illah rashin samun had'in kanki dalilin da yasa kenan yake wannan fizge fizgen, zuciyata ce take min wannan maganar nace"Aikuwa idan hakane zai dad'e cikin kunci dan nayi rantsuwa da Allah babu wani namiji da zan mallakawa jikina sai mijina na sinna......."Ranka ya dade ka tashi kayi bre......."Fita a dakin nan."! Cikin tsawa ya fadi maganar har yana mikewa zaune." Dakewa nayi nace"Kayi hakuri dan Allah kayi break kasha magani kaji dai abinda dr yace ko."? da sauri ya sauko kwalayen maganin ya watso min a jikina. "Ki fita tun kafin na taso."

Rai a 'bace! nace"Saboda ina kula lafiyarka kake min tsawa maganin nan fa kanka zaka shawa kake watsi dashi." Dirgowa yayi daga bed din ya durfafo ni yana huci! da sauri na bude kofar dakin na fita ina jin wani irin faduwar gaba, shin wai me yayi zafi ne? me mutumin yake so ya mayar dani! daga taimako sai sharri ya biyo baya.

Jikin kofar na jingina ina mayar da numfashin fargaba gabadaya gwiwata tayi sanyi nayi masifar tsorata da al'amarin, sai da na samu nutsuwa tukkuna na samu guri na zauna tare da rafka ta gumi.


Na kai minti talati a zaune kafin na yake shawarar sake shiga dakin...mikewa nayi a sanyaye da niyyar shiga dakin, Ya shigo gurin. sunkuyar da kaina nayi a nutse nace"Ranka ya dade barka da asubah."

"Barka dai." kawai yace yasa hannu a jikin kofar ya bude ya shiga tare da mayar da kofar ya rufe.

Shuru nayi ina tunanin waye a cikinsu sam bana gane su Shatima ne ko Muddibo kusan dai suna yanayin kama da junansu harshi Yarima tunda dukkaninsu farare ne masu tsayi.

Komawa nayi na zauna ina jiransa ya fito daga dakin na shiga, ko minti uku banyi da zama ba ya fito yana duba agogon dake daure a hannunsa, ganin ya fito yasa na mike da sauri "Ranka ya dade ka sauka lafiya." Tsayawa yay yana min wani kallo kafin yace."Meye ma sunanki."? Nace"Sunana Sumayya Lawi."
Yace."Okey na shiga na sameshi yana bacci idan ya tashi ki sheda masa zuwana akwai tufa (Apple) dana kawo masa inaso idan ya tashi a bacci ki bashi yaci kinji ko."

Da sauri nace"Insha Allahu zan bashi." Hanyar fita ya kama ba tare da ya sake magana ba, dakin na shiga da sauri. yana kwance ruf da ciki ya matse fillo a kirjinsa, girgixa kaina nayi cikin zuciyata nace aikin kenan rungume fillo gaskiya yana da tsananin bukata daga ganinsa, yana da kyau ya gaggauta aure domin shine mafita a gareshi.

A hankali na karasa shiga dakin,nasa hannu na dauki ledar tufar(apple) din kan kujera na zauna na shiga fito da ita guda shida ce manya manya ido na tsira mata ina nazari, gani nayi kaman huda a jikinta dan a yanda nasan apple bata da huje huje sumul take, a take na tsargu da ita nayi saurin mayar da ita ledarta na daure bakinta tamau! toilet na shiga na wanko hannuna na fito, maganin dake tarwatse a kasan dakin na kwashe tsaf na ajiyesu kan drowar dan tsayawa nayi ina kallonsa bacci yake sosai kuma daka gani yana jin dadinsa, ajiyar zuciya na sauke na dauki ledar apple din na bud'e dakin na fita.


Can inda aka tanada domin zubar da shara na nufa, na samu wata sanda mai tsayi na tona sharar ledar apple din nasa a ciki na mayar da sharar na rufe, gurin na bari da sauri.

Daf da zan shiga reception din na hango su Haruna gurin masu gadin asibitin suna hira cikin zuciyata nace"Wato dama nan suke zuwa su zauna girgiza kaina nayi na bar gurin

Ina shiga Dr na fitowa daga wani daki, murmushi naga yayi min wanda ya ban mamaki yace."Sumayya ina fatan Yarima yasha maganin nasa."? shuru nayi ina tunanin abinda zance masa." "Yake kyakkyawa Ina magana kinyi mun shuru ki bani amsa mana."

Maganarsa tasa na tsira masa ido ina mamaki! tunda nake babu wanda ta'ba kirana da kyakkyawa kowa muni na yake gani amma saboda cin mutunci na likita yake kirana da sunan mai kyau.........Dago kai nayi na kalleshi naga yana sakar min wani lafiyayyan murmushi, shan kunu nayi nace"Be sha maganin ba bacci mai nauyi ya dauke shi.

"Ayya keda nace kiyi kokari ki bashi kafin ya kwanta alright bari na shiga yanzu na tashe shi yasa magananin." Dakin ya nufa da sauri nima na rifa masa baya.


A zaune muka sameshi da waya a hannunsa, kallo guda yay mana ya watsar damu Dr na ya'ke ya karasa kusa dashi da fadin"Ranka ya dade garin ya yau ka kwanta ba kasha maganinka ba."

A dan ya tsine yace."Bacci ne yaci karfina amma ina ganin babu damuwa yanzu idan naci abincin zansha." Dr kallona yake cikin tuhuma yace."Haba baby me yasa kike wasa da aikin ne? wannan fa shi muke sa rai ya zama Sarkinmu amma kina wasa da lafiyarsa." Nace"Dr ba laifina bane shine yace sai yay bacci ya tashi zaici wani abu."

"Okey to tunda ya tashi yanzu dan Allah ki tsaya sosai ki tabbatar yaci ya koshi kin gane ko.''? da sauri nace" Eh na gane" Juyawa yay yana kallonsa yace."Yallabai ni zanje na duba marasa lafiya dan Allah ka daure kaci abinci sosai kasha magani."
Yace."Okey kada ka damu." Dr fita yay daga dakin shi kuma ya mi'ke tsaye. had'a ido mukayi nayi gaggawar yin kasa da nawa.
Yace."Wai baby sunan bai dace dake ba yarinya kinfi dacewa da *Gwamma* dubeta dan Allah da ba'ki kamar wani guri."!
Cikin tsantsar takaici da bakin ciki na kalleshi ya watsa min harara mai zafi! hanyar toilet ya nufa yana jan tsaki! bin bayansa nayi da kallo zuciyata nayi min wani irin zafi.....
*BINTA UMAR ABBALE*



*Littafin na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta whasap da wannan number
*07084653262*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
41&42
Cikin wani irin yanayi wanda yake nuna tsantsan 'bacin ransa yace."Kina nufi auntyna zata sa min guba a abinci dan ta cutar dani, ashe har kin kai matsayin da zaki kalli tsabar idona ki fada min wannan maganar."!!! Hawaye ne ya wanke min fuska bakina na rawa nace"Kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ban yarda da nagartar abincin ba shiyasa nayi wannan maganar amma ni bana zargin auntynka da wani mugun abu, dukkanin abinda kaga nayi a kanka ina kokarin ganin na rike amanar da mahaifiyarka ta bani.

A lalace yace."Wato ke har kin kai matsayin da za'a dauki amana ta a baki me kika sani a rayuwa." ? Ido cikin ido nace"Ni nasan abinda baka sani na ranka ya dade dan Allah ka bani goyon baya akan dukkanin abinda za kaga nayi a kanka wallahi ba zan cutar da kai ba." "Rufe min baki." Yafada yana watsa min harara, ya cigaba da cewa'' Daga yau sai yau kada wani dan uwana ya kawo min abu ki dora zargi a kansa bani da kamar su a duniya banyi imanin da cewa zasu cutar dani ba saboda haka babu abinda ya shafe ki da tsakanina dasu." Sunkuyar da kaina kasa nayi tsabar takaici ya hanani cewa komai...."Kina ji ko bakya ji."? Ba tare dana dago ba nace "To." "Zuba min abincin naci." Yafad'a yana tsatstsare ni da idonsa.
'Kin zuba masa nayi na sake 'boye fulas din a bayana gabana sai faduwa yake ina jin tsoron ya turmushe ni ya dauki abincin yaci.......Gani nayi ya dafe kansa yana girgizawa da sauri nayi yunkurin tashi da fulas din a hannuna ya wani finciko ni na fad'a kansa fulas din abincin yay nasa guri duk rabi ya zube a gurin. da sauri na mike daga jikinsa gabana na bugawa, ya dinga hararata murya na rawa " nace kaga ka zubar ko." Tsaki yaja mai karfi ya mi'ke gani nayi ya nufi inda d'aya kwandon abincin yake ya dauko guri ya samu ya zauna yana kokarin zuba abincin. Nufarsa nayi dan na zuba masa "Idan kika zo nan sai ranki ya 'baci ki fita ki bani guri bana bukatar ganin ki.'' A sanyaye na tsaya ina kallonsa yana kokarin bude fulas din. juyawa nayi na fita raina a bace na dauko tsintsiya da abin kwashe shara gyara gurun daya 'baci nayi na goge gurin tsaf, ina kokarin fita Dr ya shigo, a nutse na gaishe shi nasa kai na fita daga dakin zuciyata gabadaya babu dadi.

Muna zaune a reception likita ya fito daga dakin cikinmu babu wanda yay gangancin shiga muna dai kallon yanda 'yan uwa da abokansu suke zuwa su shiga dakin domin dubashi.....goma da rabi jama'a sun tsagaita, Haruna ya kallemu da fadin" Yana da kyau muje mu dubashi idan akwai abinda yake bukata sai muyi masa muje mu kwanta."

Gabad'ayan mu muka miqe muka nufi dakin....Yana kwance kan bed da waya a hannunsa muka gaishe bai tare daya kallemu ba ya amsa, Haruna yace."Ranka ya dade akwai abunda kake bukata muyi maka.''? Girgiza kansa yay yace."Bana bukatar komai kuje ku kwanta sai da safe." Godiya muka mike muka juya da niyyar fita.
Nice ta karshen fita naji ya kira sunana. juyowa nayi ina kallonsa. "Zonan." yafada idonsa a kan wayarsa, a sanyaye na saki kofar ta rufe na koma na tsaya tare da sunkuyar da kaina, na kai minti goma a tsaye a kansa kafin yace."Ki matsa min kafafuna." Kallonsa nayi inaso nayi magana naga yasha kunu.
Kasa motsi nayi gabana na faduwa ni kam na rasa wane irin mutum ne wannan abinda Allah ya haramta sai yace sai nayi masa.

"Ko ba zakiyi bane."? Nace" Bai dace ba na ta'ba jikinka ba dan Allah kayi hakuri na kira maka Haruna yayi maka." Mikewa zaune yayi yana kallona yace."Kafafuna nace ki matsa min ba Al'aurata nace ki matsa ba." da sauri na kalleshi ina mamakin maganarsa, Al'aura lallai mutumin baida kunya. Ya cigaba da cewa! ni bazan ji wani feelings ba ballanatana kiyi tunanin wani abu zai faru a tsakaninmu dan kin matsa min kafafu babu abinda zai faru ki kwantar da hankalin ki."

Wannan maganar da yayi tasa naji kwarin gwiwa a jikina dama ina tsoron faruwar wani al'amarin ne. Ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye wayar kan drowar ya koma ya kwanta yana kallon rufin dakin.

A d'arare na zaune a gefansa nasa hannuna a kafafunsa na soma dannawa, rintse idonsa naga yayi yana sauke ajiyar zuciya, dauke kaina nayi daga kan fuskarsa na cigaba da daddana masa kafafunsa ina neman tsari a cikin raina......Gani nayi yayi ruf da ciki ya dauki hannuna ya dora kan cinyarsa 'kasa-'kasa yace."Ki danna min nan." Hannuna ne ya shiga karkarwa nayi sauri na janye ina danna inda be sani ba! shuru dakin yay na kusan minti ashirin na gaji na cire hannuwana ina dan kallonsa shuru naji kafin naji saukar numfashinsa, a hankali na mike ina leka fuskarsa naga idanunsa a rufe ina tunanin bacci ya daukeshi, kamar na tasheshi ya gyara kwanciyarsa sai dai na rabu dashi sabida ina tsoran kada na tashe shi ya bijiro da wata fitinar, fita nayi daga dakin tare da ja masa kofa.........

Kasancewar asibitin babbane yana dauke da ma'aikatan jiyya yasa
Washe gari da safe da muka shiga gaishe shi muka sameshi yayi wanka ya shirya jikinsa cikin k'ananun kaya sai kamshin turare mai dadi yake.
Gaisawa mukayi dashi kafin su Haruna su fita su barni dashi, a dakin, Jikina ne ya bani kallona yake na dago kaina babu walwala a tare dani nace"Ranka ya dade ana iya had'a maka breakfast yanzu."
Kansa kawai ya daga min still idanunsa na kafe a kaina, tsaki naja a raina na tsani wannan d'abi'a tashi idan ya dinga kallon mutum kamar ba zai bari ba........"Ki had'a min tea kada kisa sugar da yawa.'' nace"To ina kokarin dauko kwandon dake dauke da kayan tea din.
Sukayi sallama suka shigo dakin. Uwar gida Huwaila ce da yaranta guda biyu su uku kenan....cikin isa da taqama suka karasa shigowa dakin., sunkuyar da kaina kasa nayi Nace"Barkanku da zuwa." Babu wacce ta amsa min a cikinsu nace"Ina fatan kun tashi lafiya."Nan ma basu ce min komai ba, jikina a sanyaye na bude fulas din tea ina tsiyayawa a cup.gefe guda kuma ina jinsu suna gaisawa dashi suna tambayarsa jikinsa.

Cikin kulawa yake amsa musu har yana tambayar antis dinsa yaransu, mikewa nayi a nutse na isa gurinsa na mika masa tea din na kallashi nace"Ina iya tafiya."? Daga min kansa yay ya cigaba da magana da 'yar uwarsa, da zan fita sai da nayi musu fatan fitowa lafiya cikinsu babu wacce ta amsa min.


Harabar asibitin na fita na samu wani guri na zauna ina kallon masu shige da fice tunani nake inasu Haruna suka shiga kuma dan tun fitowa ta gurin banga gilmawarsu ba......Motocin dake dauke da tambarin masarauta ne suke shigo cikin asibitin, da sauri na mike na nufi inda motocin ke parking Maimartaba ne dashi da Amaryarsa Fulani suka fito daga mota guda, d'aya motar kuma su Waziri ne a ciki, sunkuyar da kaina kasa nayi cikin ladabi na gaishe su, cikin kulawa suka amsa min, gaba nayi da sauri domin na jagorance su dakin da yake........Jama'ar dake kai kawo a asibitin ganin Sarki dashi da muqarrabansa yasa suka dunga zubewa suna kwasar gaisuwa, kofar dakin na bude tunkafin su karaso, sai da suka gama shiga dakin tukkuna na mayar da kofar na rufe na samu guri na zauna ina sauke ajiyar numfashi

Maimartaba da Amaryasa sunji dadin ganin yaronsu ya samu lafiya a tsakankanin kwanaki bakwai da faruwar al'amarin ya samu lafiya ya warware sosai kumburin da fuskarsa tayi ya sa'be sai tabbanin dake saman goshinsa likita ya tabbatar dacewa a yanzu babu abinda ya rage a tare dashi sai jiran cikowar naman goshinsa inda ya bugu da dutse kasancewar gurin yayi rami sosai yasa ba'a kwance masa bandejin ba, abinda ya rage kenan a jikinsa.

Ba iyayensa ba kadai sukayi murna da farin ciki ba har damu masoyansa munji dadi sosai da result mai kyau ya fito, ganin yanda ya bugu a kansa ne yasa iyayansa hankalinsu ya tashi suna ta fargaba kada ya samu matsala a kwakwalwarsa sai gashi likita ya tabbatar musu da cewar lafiyarsa lau abinda ya rage a tare dashi shine jiran tofowar naman goshinsa da yayi rami shima kuma da yardar Allah baza a dauki dogon lokaci ba......Cike da farin ciki Maimartaba da amaryarsa suka bar asibitin wanda kafin tafiyarsu sai da ta sake jaddada min cewa na kula sosai da shige da ficen jama'a a dakinsa sannan na kula da abinda zai ci

Please Login or Register in order to submit comment