Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske ne Muddibo ne ya aikata ba sharri akeyi masa Kin saurari muryarsa a lokacin da yake shedawa hukuma gaskiyar lamari amma saboda san zuciya kina cewa sharri a kayi masa."


Lawisa na kuka tace"A gaskiya Yaya Wali ka bani mamaki wallahi wato kai ba zaka iya rufa asirin dan uwanka ba ko kenan yanzu ranar litinin din ba zakaje kuto ka bada sheda a kansa ba."

Dafe kansa yayi cikin tsantsar damuwa yace."Wace irin sheda zan bayar a kansa bayan da bakinsa ya fadi gaskiyar magana, dole zanje kuto domin jin irin hukuncin da sharia zata yanke a kansa."


Munniru yace."Ni wallahi na rasa ma abinda keyi min dadi a rayuwata nayi nadama nayi dana sani dana fito a cikin wannan masarauta gabad'aya bamu da power a masarautar nan komai mune a baya ai dole 'bacin rai yasa hawan jini ya kama babanmu.


Hajiya Karima ta share hawaye cikin takaici tace"Ai Munniru ba kuga komai ba a yanda babanku yake bani labarin yanda mahaifinsa yasha wuya a cikin masarautar nan sai kunyi mamaki mutuka! zuri'ar Abdullahi Adamu ta riga ta kwace sarauta ta kafa kanta ta hana kowa ya kar'ba daga hannunta ni wallahi har yanzu banga laifin Muddibo ba dan yayi yunk'urin kwatar hakkinsa, bari na fad'a muku abinda baku sani ba zuri'ar Abdullahi Adamu sune suka kashe kakanku da bakin ciki sai wayar gari akayi da gawarsa ya mutu da bakin ciki!


Munniru ya buga bango(garu) da hannunsa yana huci! yace."Tur! da zuria'r Abdullahi Adamu wallahi sun kasance azzalimai masu san kansu da yawa meye amfanin mu a masarautar nan da mu zauna muna ganin bacin rai a gwara mu tattara kayanmu mu fita daga cikinta..



Wali yace."Baka da hankali ko Munniru idan mun bar masarauta kana inda zakaje."? shuru yayi yana huci! Wali ya cigaba da cewa"Ka nutsu ka zauna kayi tunani malam komai kaga na faruwa to da yardar Allah idan Yayi nufin mulki ya cigaba da tabbata a hannun zuri'ar Abdullahi Adamu to babu yanda zamuyi idan kuma yayi niyyar k'wace mulkinsa ya kwace ya dawo dashi hannunmu kuma abunda nake so kuyi la'akari dashi anan shine Waziri da Galadima me yasa basa tayar da hankalinsu akan mu! kada ku manta suma fa suna da hakki amma sunyi shiru sun zubawa sarautar Allah ido ba wai dan basa sha'awar mulkin ba dukkaninsu suna so suna sha'awa sai dai babu yanda za suyi da abinda Allah ya hukunta saboda haka dan Allah kuma inaso ku hakura ku barwa Allah ikonsa kuma insha Allah idan baba ya samu sauki zan zauna na fahimtar dashi cewa shi mulki na Allah ne sai wanda ya za'ba yake bawa ba'a yiwa Allah dole akan ikonsa kowane irin hukunci ya zartar daidai ne."

Jikinsu ne yayi sanyi da nasihar da d'an uwan nasu, da alama dai duk cikinsu shine mai kyakkyawar zuciya tunda gashi nan ya zaunar dasu yana nuna musu abinda ya dace Ubangiji Allah yasa zasu dauki nasiharsa su hakura su barwa Allah ikon sa.




Bayan kwana biyu jikin Ciroma yayi sauki dan Magajin sarki ya tsaya a kansa sosai da sosai ya bashi dukkanin kulawar da ake bukata, alhamdullhi yanzu an samu yana iya sarrafa hannuwansa sai dai har yanzu idan yana magana ba'a fahimta sosai saboda yanda bakinsa ya karkace yana zubar da yawu....Ganin yanda hankali Maimartaba ya tashi akan hakan yasa ya zauna sosai ya kwantar masa da hankali yace."Insha Allah zai samu sauki ya dawo normal kamar yanda yake, jin haka yasa Maimartaba da 'yan uwansa hankalinsh ya kwanta, Suma su Lawisa suka kwantar da hankalinsu dan ganin yanda jikin mahaifin nasu yayi sauki sai dai har yayi kwana hudu a asibiti Hajiya Karima ba taje ba tana nan har yanzu da mugun nufi a cikin zuciyarta, cikin masarautar babu wanda bai je ya duba Ciroma ba amma ita da take a matsayin matarsa uwar 'ya'yansa ba taje ba tana zaune a gida tana sa'ka mugun abu a cikin zuciyarta.


*RANAR LITININ*
Kuto ta cika ma'kil da jama'a ana ta gabatar da shari'a yanda addinin musulunci ya tanada mai girma mai shari'a malam Umaru Musa ya d'auki takardar dake gabansa a nutse yake duba takardar yana girgiza kai! farin gilashin dake idonsa ya zare a nutse yace." Insha Allahu zamu kamanta adalci kuma zamu yankewa mai laifi hukuncin da addinin musulunci ya tanada muna rokon Allah yasa hakan ya zama izina ga masu hali irin na *Al'amin AbdulJabbar wanda akafi sani da Muddibo* Hukuncin da addinin musulunci ya tanadarwa dukkanin wani musulmin daya aikata kisa yana sane to shima akashe shi! Alhamdullahi wanda ake zargi da aikata laifin kashe masu rai guda uku ya amsa laifinsa ba tare daya wahalar da sharia ba saboda haka kuto tana bukatar ta saurari muryar wannan yaro a lokacin da yake wa hukuma bayanin yanda akayi yake aikata wannan 'barna kuto da jama'ar dake cikinta na bukatar su saurari jawabin da yayi domin kowa ya tabbatar da hukuncin da zamu yanke a kansa daidai yake da addinin musulunci."

Da sauri wani dan sanda dake tsaye a gefe ya dauko wayarsa a take ya kunna rocoding din da Acp yayi wa Muddibo a lokacin da yake jawabi a ofis dinsa......tun kafin rocoding din ya kare gurin ya kaure da haniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, Muddibo dake tsaye gurin tsayuwar masu laifi ya sunkuyar da kansa zufa sai keto masa take hakika bai ta'ba nadamar rayuwa ba sai yau, jama'a sai zaginsa suke suna ala wadai dashi.......Wali da Muniru sai girgiza kai sukeyi suma tamkar su fashe da kuka su kad'ai ne suka iya halartar kuto Hajiya Karima dasu Lawisa suna gida suna kuka saboda jikinsu ya riga yayi sanyi da jin irin kotu'n da'aka kai Muddibon kotun musulunci ce tsantsa kowa yasan Malam Umaru Musa tsayayyan al'kali ne wanda yake yanke hukunci akan doron gaskiya Kudi ko mulki na mutum basu isa susa shi ya kauce hanya ba komai muqamin mutum mutukar yayi laifi baya d'aga 'kafa sai zartar da hukuncin da addinin musulunci ya tanada

Maigirma mai shari'a ya bada umarnin akan cewa kotu ta samu nutsuwa, nan take kowa ya nutsu gurin yayi tsit! A nutse ya cigaba da cewa''Saboda haka kuto zata yankewa Al'amin Abduljabbar hukuncin kisa kamar yanda ya kashe shima za'a kashe shi!! ta hanyar rataya."!! yana gama maganarsa ya buga tevur din gabansa da wani d'an katako! hukunci ya tabbata da izinin Allah! mikewa yayi gabad'aya jama'a suka mi'ke suna kiran sunan Allah.
"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu! akbar!! 'Yan sanda kusan hudu suka kewaye Muddibo a rirrike a ka fito dashi yana kuka yana d'agawa su Wali hannu aka fita dashi y'an jarida da jamaa suka bi bayansu.......Wali da Munniru rungume juna sukayi suna kuka Wali yace." Munniru kaga irin rayuwar da nake gudu ko ka duba ka gani yanda Muddibo zaiyi mutuwar wulakanci jama'a sai tsine masa suke saboda mugun abunda suka aikata, dan Allah Munniru komai rintsi ka rike gaskiya kada kabi san zuciyarka irin na Muddibo." Munniru hawaye kawai yake sharewa yana girgiza kansa tabbas duniya abar tsoro ce shikkenan yanzu sunyi bankwana da dan uwansu.
*Allah kasa mufi karfin zuk'atan mu amin.*

Hajiya Karima faduwa tayi ta suma lokacin da ta samu labarin hukuncin da ya sauka akan d'anta koda ta farfado ma sambatun surutai ta dinga yi tamkar wata mara hankali sai alwashi take ci akan wallahi ba zata yarda ba sai ta dauki fansa! Wali ya rungumeta a jikinsa yana mata addua yana share hawaye.........A ranar Maimartaba kasa zaman fada yayi saboda tashin hankali yaje ya kwanta a sashen Fulani yana tunanin rayuwa......Magajin Sarki da Shatima yini sukayi cikin alhini da damuwa amma daga baya da suka zauna sukayi tunani sai suka ga hukuncin da mai shari'a ya zartar akan Muddibo shine daidai hausawa na cewa da kunyar lahira gwara ta duniya watakila hakan na iya janyowa Allah ya gafarta masa zunubansa, saboda haka sai dukkaninsu suka kwantar da hankalinsu su tsananta addua akan Allah yasa haka shine yafi alkairi a rayuwar d'an uwan nasu....




*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba! keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina bukatar biya ga yanda abin yake......Vip gruop#600 normal gruop#300 account number... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
90
Masarauta da jama'ar dake cikinta sun jima cikin alhini da damuwar abinda ya faru. mussaman 'bangarar Uwargida Huwaila ita da zuri'arta babu wanda ya kaisu shiga tashin hankali dan ganin irin hukuncin da ya sauka akan Muddibo duk sai suka tsorata kowacce ta shiga nutsuwarta dan saboda sun san koda sune suka aikata abu makamanci na Muddibo baza su tsira ba, sosai uwargida da iyalinta suke godiya ga Allah da bai nufi Muddibo ya kiran sunan d'aya daga cikinsu ba! wannan dalilin yasa kowacce ta nemi guri ta zauna a dakinta yanzu ba sosai ma suke zuwa masarautar ba saboda gudun kada asirinsu ya tonu..........Alhamdulillahi jikin Ciroma yayi sauki sosai dan yana iya komai da hannayensa sannan yana tafiya da kafafunsa sai dai rashin kuzari da bai dashi amma ya samu lafiya sosai Magajin sarki ya tabbatar musu da cewa zai warware idan an kwana biyu, Satin sa uku a asibiti ya dawo gida, duk irin kulawar da Magajin sarki keyi akan Ciroma baya burge Hajiya Karima kullum cikin zaginsa take tana kwashe masa albarka da fad'in "Yanda yayi sanadin mutuwar d'anta itama sai tayi sanadin mutuwarsa........duk sanda tayi wannan furucin sai Wali yayi mata nasiha harzuqa takeyi ta rufeshi da fad'a haka yake fita ya barta ransa a 'bace! bangaran Lawisa kuma ta dan samu sassauci kuma ta rage jin haushinsa tunda yayi sanadiyar samun lafiyar mahaifinta amma da itama ta k'ullaceshi a zuciyarta saboda yayi sanadin mutuwar dan uwanta! gabadaya idonsu ya rufe sam basa hango laifin Muddobo su dai suna nan akan bakansu na cewa sharri akayi masa, duk sanda zasuyi wannan furucin Wali hauka yake d'ora musu ya bar musu gurin dan takaici!! Ya lura Lawisa halinsu d'aya da mahaifiyarsu amma Munniru da Khalisat idan yayi musu magana suna ji kuma sun daina zagin Zuri'ar Maimartaba suna zaune lafiya da kowa a masarautar..............To Sati na uku a b'angaran Fulani gabad'aya na sanja fatar jikinta ta washe na 'kara qiba! su kansu sutturun da nake amfani dasu a jikina abin kallo da sha'awa ne duk wasu kayan kyale kyale da 'kawa na sarauta Mamma tasa an kawo min ina amfani dasu, kullum cikin ado da kwalliya nake na fito na zauna kusa da ita muyi ta hira Fulani wayayyiyar macace ta saki jikinta dani yanda na lura gabadaya bata suruktaka dani dan watarana ma idan nayi ado da irin kayan sarautar itace ke gyara min sai taga yayi daidai sannan hankalinta zai kwanta, a tsayin satikan da nayi a gurinta na koyi abubuwa da yawa na sarauta dana yau da gobe, sannan kuma sa'i da lokaci na kanje na gaisa da iyayena cikin walwala da farin ciki..............Cikin nutsuwa na fito daga daki na sameta a inda ta saba zama domin hutawa, kusa da ita na zaune a nutse nace"Mamma barka da hutawa." da murmushi a fuskarta tace"Barka kadai Sumayya yau kin wuni kina bacci baki fito da wuri." Murmushi nayi ina wasa da hannayena nace"Wallahi kuwa ni kaina nayi mamakin baccin da nayi sai da nayi tunanin ko maganin murar dana sha ne ya kashe min jiki."

Tace"Eh kwarai kuwa hakan zata iya kasancewa." Shuru nayi kaina a kasa kusan kullum idan inaso naje na duba mahaifana nakan ji kunyar fada mata, kwata-kwata bana so taga rashin kunyata.


Murmushi tayi tace"Sumayya kina so kije ku gaisa da iyayenki ko."? murmushi nayi tare dayin kasa da kaina. zamanta ta gyara tana murmushi tace"Ai duk sanda kike so kije gaishe da iyayenki ina ganewa na rasa me yasa kike jin kunyata Sumayya." 'Yar dariya nayi nace"Mamma kece Allah yayi miki kwarjini shiyasa nake kasa fada miki.'

Yar dariya tayi tace."Kwarjini har na kai ki sumayya."? da sauri na kalleta, ta daga min kanta tare da fadin"Gaskiya da rikon amanarki suna burgeki sumayya inaso ki sake dam'ke gaskiya hannu biyu duk rintsi kada ki kauce hanya ki tsaya akan gaskiyarki." Nace"Insha Allahu zan kula da maganarki.'


Tace."Babu damuwa kina iya zuwa ku gaisa amma kada ki tafi ke kadai kuje tare da mutum biyu." nace"To shikkenan." Ina kokarin mikewa ta shigo falon, kallo daya nayi mata naji gabana ya fadi, hajiya Karima ce! Mamma tace"Sannu da zuwa hajiya yau kece a gurina."

Cikin ya'ke tace"Fulani kenan ai kin san komai da dalili.'' guri ta nema ta zauna! na dan risina a nutse nace"Barka da yamma ranki ya dade." Wani banzan kallo tayi min kafin ta ta'be baki ciki-ciki ta amsa min. A sanyaye nace"Mamma sai na dawo." da sauri tace"To sumayya ki gaishe min dasu da kyau." Nace"Insha Allahu zasuji."
Hajiya Karima bin ta tayi da ido tana girgiza kanta, sauke ajiyar zuciya tayi bayan fitarta tace"Fulani gurinki nazo."


Mamma ta gyara zamanta sosai tana fuskantarta tace"Ai dama tunda na ganki nasan da akwai magana Hajiya Allah yasa alkairi ne yake tafe dake."


Hajiya Karima gyara yanayin fuskarta tayi tace"Magana ce akan Lawisa naga tunda ake maganar auran nan banji ana saka sunanta ba idan Ali ya fasa auranta ina bukatar karin bayani.

Cike da mamaki take kallonta kafin tace"Hajiya Karima wannan wace irin magana ce haka? a gaskiya banji dadi ba in banda abinki ya za'ayi Babana ya fasa auran 'Yar uwarsa."


Murmushin takaici tayi tace."Haba Fulani ai dole nayi zargin hakan saboda ganin gabadaya an daina zance Lawisa sai na wannan baiwar akeyi ai dole dukkaninmu muyi tunanin ko baiwa tafi 'yar sarauta."


Mamma ta girgiza kanta tana kallonta tace"Hajiya Karima dan Allah ki dinga gyara maganarki ya za'ayi kina babba ki dinga sakin maganganun da basu dace ba, wannan yarinyar Sumayya tuntuni ta 'yantu ta shigo cikinmu dan Allah ki daina irin wannan maganganun basu da dadi.

Tace"Sumayya ta 'yantu amma kuma bata gaji sarauta ba ko.''? Fulani ta kalleta takaici kamar ya kasheta, Hajiya Karima ta cigaba da cewa" Wannan yarinya Sumayya sam bata dace da Ali ba saboda gabanta da bayanta bayi ne mak'as'kanta, wallahi ni rasa wace jaraba Ali ya hango a jikinta ."


"Nagarta da kyawun hali babana ya hango a tare da ita shiyasa yayi sha'awar auranta, Kin san mazan da suke da wayo a yanzu sun daina duba so ko nasaba a aure nagarta da tarbiya suke dubawa kafin su auri mace wanda yanzu samun irin masu nagartar yarinyar nan zaiyi wahala sosai."


Tsaki taja tace"Duk da haka dai Masarauta nada al'ada a tarihin masarautar nan banta'ba jin wanda ya auri baiwarsa ba sai Ali ina ganin kamar zai barwa zuri'arsa abin magana."


Fulani tayi dariya tana kallonta tace"Babu wani abin magana da zai barwa iyalinsa, baiwa itama mutum ce kamar sauran mutane kuma idan Allah ya kaddara auran Babana da wannan yarinya rabo ya shiga tsakaninsu sai kiga ta haifi Sarki duk da take baiwa ma'kaskanciya babu ruwan ubangiji.

Da sauri hajiya Karima tace"Bana fatan nayi tsawan ran da zanga wannan rana dan lalacewa ace d'an baiwa shine zaiyi mulki tunda nake banta'ba ganin wannan kwamacalar ba."


Fulani ranta ya 'baci sosai ta rasa me yasa matar take da izgilanci rayuwar duniya a sannu ake bin ta na sama yana iya dawowa kasa na kasa ya hau sama, mutukar sarki ya auri baiwa ya 'yantata to idan ta haihu d'anta yana da gadon sarauta tunda dan sarki ne gabad'aya basu san mecece sarauta ba babu shakka koda mulki aka basu to ba zasu iya aikata komai ba sai shashanci!

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Hajiya Karima magana ta 'kare kije ki kwantar da hankali insha Allahu Babana zai auri Lawisa kamar yanda ya dauki alkawari tun farko."

Ta mike tana gyara lullu'binta tace"To yanzu naji kinyi magana mai kyau ni zan koma gurina." Fulani ta bita da kallo har ta fita daga falon, girgiza kanta tayi tana mamakin halin matar kwata kwata bata da dad'in sha'ani gashi duk maganar da tazo bakinta fad'a take bata taunawa.


Yau Yarima bai dawo gida da wuri ba hankalinmu duka ya tashi, Mamma ta kalleni a nutse tace"Ko zaki kira shi da wayarki ina ganin idan ya fad'a mana halin da yake ciki sai hankalinmu yafi kwanciya.'' Cikin nauyi nace"To shikkenan bari na dauko wayar a daki." a nutse na mike........Zama nayi gefan gado da wayar a hannuna number shi na kira sai da ta kusa katsewa tukkuna ya dauka, ajiyar zuciya na sauke a nutse nace"Ranka ya dade barka da dare." "Barka dai." ya amsa a takaice, nace"Muna nan hankalin mu duk ya tashi baka dawo da wuri ba ina fata lafiya."

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace."Sumayya ina da marasa lafiya ne mata biyu ne zasu haihu haihuwar tazo da tangard'a yanzu shirye-shiryen shiga dasu dakin teatar ake."

A sanyaye nace"Allah sarki wallahi har naji tausayinsu Ubangiji Allah ya sauke su lafiya." Ya amsa da "ameen ya rabbi ki bani Mammana mu gaisa." da sauri na mike da wayar a hannu na sameta zaune a inda take.
A sanyaye nace"Mamma gashi na sameshi a wayar." da sauri ta kar'ba tasa a kunnanta tana kiran sunansa.

Yace."Mamma Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya." ta amsa da "ameen babana yana jika wani iri Allah yasa kana lafiya." a sanyaye yace."Lafiya ba lau ba mamma yau na shiga rud'ani mutuka! da sauri tace"Subahanallahi me ya faru da kai."? ajiyar zuciya ya sauke yace."Wallahi Mamma wasu mata biyu ne zasu haihuwa sai wuya suke sha haihuwar ta'ki zuwa daga 'karshe ma sai al'amarin ya rikice suka dinga jijjiga duk sun fita daga hayyacinsu Mamma ashe haka kuke shan wuya gurin haihuwa."?


Cikin damuwa tace"Allah sarki! to Ubangiji Allah ya sauke su lafiya babana dan Allah duk wani taimako daka san suna bukata kayi musu Allah zai baka lada."


Yace."Insha Allahu zanyi iyakacin bakin kokarina akansu dan yanzu na bada umarnin shiga dasu dakin teatar ina ganin haka shine maslaha domin kuwa idan mun tsaya mun jinkirta to ana iya rasa rayukan su.'' A sanyaye tace"Babana Allah yasa ku shiga a sa'a Allah ya tashi kafad'unsu ya sauke su lafiya." Ya amsa da "ameeen ya Allah insha Allahu komai dare zan shigo gida idan naga aiki yayi kyau." Tace"To shikkenan ubana Allah ya bada nasara." sallama sukayi jikinsu duk a sanyaye.

Haka muka cigaba da zama a falon muna jajanta al'amarin dan ni kaina da ban ta'ba haihuwa ba ban kuma san yaya zafinta yake ba na tausayawa musu saboda wahalar da suke sha, har misalin goma da rabi na dare bai shigo ba, alamun bacci na gani a idonta a nutse nace"Mamma kije ki kwanta ki huta naga kamar kina jin bacci insha Allahu zai dawo lafiya." Tace"Wallahi kuwa bacci ne a idona Sumayya nafi so dai na zauna ya dawo naji lafiyar matan nan sun tsaya min a raina wallahi."

Nace"Nima haka Mamma addua zamuyi Allah ya rabasu lafiya insha Allah idan ya shigo komai dare zan tasheki amma yana da kyau kije ki kwanta tunda bacci kikeji kada yasa miki wani ciwon.'' Na fadi hakane domin na kwantar mata da hankali amma bana tsammanin idan ya shigo na tashe ta a bacci da safe sa gaisa......Yunkuri mikewa tayi na mike nima tare da gyara mata nad'in lifayar jikina, hannunta na rike muka shiga bedroom d'inta, gefan gado ta zauna nace"Bari na hada miki ruwan wanka.'' hannunta ta rike da fadin"Sumayya bana jin zanyi wankan nan dazu da yamma nayi kayan bacci zaki dauko min." da sauri nace"To tare da nufar wardrobe dinta, riga da wando masu taushi na dauko mata da hularsu da takalminsu na ajiye kusa da ita ta kalleni tace"Allah yayi miki albarka." kaina a kasa nace"ameeen Mamma." tace"Kina shan wannan maganin dana baki ko."? cikin jin kunya nace"Eh." tace"Idan sun 'kare koda kin tare a d'akinki ki fad'a min nasa a kawo miki wasu na fad'a miki ni ba surukarki bace kada kiji kunyata."
Ina wasa da hannuwana nace"To shikkenan Mamma." tace"Kije ki kwanta kema da safe ma gaisa dashi Allah ya dawo mana dashi lafiya."

Na amsa da ameeen tare da fadin"Sai da safe." Tace"Allah ya tashe mu lafiya." Koda na shiga dakina na jima a zaune ina tunanin rayuwa kafin nayi wanka na kimtsa jikina cikin kayan bacci riga mai hannun shima da wandonta iya gwiwa kayan masu tsantsine shiyasa suka kwanta a jikina, hula nasa a kaina har naja bargo sai kuma na cire sauke kafafuna nayi kasa a nutse na janyo drowar dake gefan gadon, magungunan na shiga fitowa dasu, tunda ta bani su tace na dinga sha kullum banta'ba shaba duk da nasan amfaninsu a tartare dani........Ajiyar zuciya na sauke a nutse na bud'e zumar itace tafi daukar hankalina bakin jarkar nasa a bakina nasha sosai na cire ina dan ya mutse fuskata gabadaya babu zaqi irin na zuma sai kadan bakina ya game da baurin magani, tsigar jikina ta dinga tashi, d'aya bayan d'aya na dinga daukar magungunan inasha ina rintse ido sai dana sha kowanne sannan na had'a maganin nasa a drowar na rufe, brush naje nayi na dawo na kwanta tare da rufe idanawana, waya ta na bari a kunne nasan mybe idan ya shigo ya kira ni sai na ajiyeta a kusa dani kawai......bacci ne yake nema ya dauke ni ina korarsa har dai ya samu nasarar sace ni 'na bingire bacci mai nauyi ya daukeni na dinga wani irin mafarkai marasa dadi........Can cikin baccina naji nauyi a kaina, a razane na bude ido ina kiran sunan Allah, da yake ban kashe hasken dakin ba yasa na gane wanene, da sauri nasa hannuwa na tureshi jikina sai 'bari yake! shima jikinsa na kyarma ya sake qamqame ni yana fitar da wani irin numfashi, a jigace nace"Wai meye haka ne."? muryarsa na dan rawa yace."Sumayya bana cikin nutsuwa ta ina cikin damuwa." jikina ya mutu nace"Ina fata ka samu nasara a gurin aikin ka."? matseni yayi sosai a jikinsa Yace."Na samu dukkaninsu anyi musu aiki lafiya lau amma d'aya yaron data haifa ya mutu." jikina yayi sanyi nace"Allah sarki Allah ya bata lafiya Ubangiji Allah ya bata wani." da sauri ya tashi daga kaina yana kallona, na mike zaune tare da kare jikina da bargo ido na zura masa naga duk ya rame! yace."Baki da hankali kike mata irin wannan fatan taci wuya irin wannan sai ta sake haihuwa." Cike da mamakin maganarsa nace"To meye a ciki ai ba'a kanta a kafara ba kuma ko wace haihuwa da irinta mybe gaba ba zata sha wuya ba."

Girgiza kansa yayi yace."Wannan ba tsari bane ace kullum rayuwar ki na cikin wahala tara 'ya'ya ba alfanu bane mutukar mace nashan wuya a gurin haihuwa sai ta 'kayyad'e ta."

Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa "Tara 'ya'ya shine bai da alfanu."?

Please Login or Register in order to submit comment