Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Allah yayi masa, cikin ikon Allah Haruna da Hamza suka farfado Isa kuwa ta Allah ta kasance a kansa ya mutu, Haruna da Hamza suka dinga kuka suna kallon gawar dan uwansu, Magajin sarki duk dauriyarsa sai da ya zubar da hawaye hakika mutuwar Isa ta ta'ba shi, ma'aikata ya umarta dasu had'a gawar Isa su daureta.

Lokacin da Maimartaba ya samu labarin mutuwar daya daga cikin mutum ukun da tsautsayin ya ritsa dasu, hankalinsa ya tashi ainu! ya dinga mamakin al'amarin yana tunanin da tuni fa d'ansa ne zai mutu idan da Allah ya nufe shi dacin doyar, lallai babu shakka dole ya tsautsara binkice akan wa'inda keda hannu gurin faruwar wannan al'amari.

Magajin Sarki bai bari ya fito daga asibitin ba sai da ya tsananta binkicensa akan sanin wace irin guba akayi amafani da ita domin a cutar dashi, ragowar doyar dasu Haruna suka rage ita yasa aka dauko masa yayi ta binkice a kanta har sai da ya gano yanda al'amarin yake, anyi amfani da gubar ne a cikin man da'aka soya doyar ya dinga girgiza kansa tabbas wanda ya aikata wannan aikin bashi da imani kuma baya k'aunarsa da gasken gaske, dole ne shima ya tsananta binkicensa akan faruwar al'amarin......hannuwansa ya wanke tas ya dauki rigarsa ta likitoci yasa yasa farin gilashinsa, kana ya kwashi wayoyinsa da duk abinda yake bukata ya fita daga ofis din nasa,

Direban sa ne ya bude kasa kofar mota ya shiga ya zauna, da sauri ya zagaya gurin zamansa ya kunna motar suka fita daga asibitin........a rikice ya tarar da gidan sarautar mutane sunyi cirko cirko kowa yana alhini akan abinda ya faru, umartar direban yayi daya yatsar da motar, ya zuge glass wani bawa ya kira da sauri yaje ya runkufa yana gaisheshi ba tare daya amsa ba yace."Kowa ya koma gurinsa tsayuwar bata da amfani wanda ya mutu ya riga ya mutu addua zakuyi masa." Da sauri bawan yace."Ranka ya dade a gafarce mu bari nayi sauri na isar musu da sakon ka."

Gilashin motar ya rufe ya bawa direba umarin tafiya.


Ciroma na zaune a dakinsa yana jijjiga kafarsa ya kalli Muddibo rai a bace yace."Gabadaya al'amarin beyi min dadi ba naso ace Shi wanda akayi aikin dominsa shine ya mutu ba bawan sa ba, amma babu komai insha Allahu hak'an mu sai ya cimma ruwa a kansa."

Muddibo cikin rashin jin dadi yace."Nima wallahi gabadaya al'amarin beyi min dadi ba amma ina ganin dole ne mu d'auki shawarar mu ta biyu akansa amma ba zamu gabatar da komai ba yanzu sai 'kura ta lafa tukkuna."

Ciroma shuru yayi yana kumbura fuska, hannu ya mika ya dauki tufa yasa a bakinsa yana taunawa yana girgiza kansa yaso ace Yarima ne ya sheqa barzahu da yafi jin dadin hakan amma babu damuwa shima ba zai tsallake tarkonsu ba.


Kai tsaye bangaran mahaifiyarsa ya nufa, koda ya shiga samun iyayen nasa yayi sunyi jugum! kana ganinsu kasan suna cikin alhini da damuwa, zama yayi kansa a kasa ya gaishe su, suka amsa suna binsa da kallon tausayi da jin kai irin na iyaye da tuni ma'kiya sun samu galaba a kansa,

A nutse yace." Ranka ya dade ya mukaji da wannan mummunan al'amari daya faru.'' maimartaba ya sauke ajiyar zuciya yace."Sai godiyar Allah kuma muna nan muna addua akan Allah ya bayyana mana wa'inda suke da hannu a cikin wannan al'amarin shi kuma wannan yaro daya riga mu gidan gaskiya muna rokon Allah ya jikansa da gafara.""

A nutse ya amsa da ameen kafin yace.'' Ranka ya dad'e kafin na fito daga asibiti nayi binkice sosai akan abincin da ya janyo faruwar al'amarin sosai nayi binkice na gane matsalar daga cikin man da akayi amfani dashi ne ina tunanin ya samu matsala ma'ana yayi expire shine dalilin daya janyo yayi musu lahani a ciki

Cike da mamaki suke kallonsa, Fulani tace"Yanzu kana nufin man suya shi ka dai zai iya janyo a rasa rai suma fa sauran Allah ne yayi da sauran kwanansu a gaba da da tsautsayi da tuni sai da labarinsu gaskiya ban yarda da maganarka ba."


Maimartaba yace."Anya kuwa Yarima kayi binkice yanda ya kamata nima ina ganin man suya shi kadai ba zai janyo hakan ba

Murmushi yayi yana kokarin danne damuwarsa yace."Ranka ya dade ku yarda da maganata gaskiya ce dan kafin na yanke hukunci sai da nayi binkice sosai akan abinda ya janyo faruwar al'amarin nan man suya zai iya kisa mutukar ya tashi daga aiki ma'ana lokacin sa ya wuce ranka ta dade ka tuna kayan abincin dake bangare na a store suke a rufe shi kansa man a gwangwani yake a rufe kuma ya dauki lokaci mai tsayi a ajiye yarinyar nan da tayi aikin abincin bata da ilmin da zata duba ta ga lalacewar abu ta dauka tayi amfani dashi bayan ya gur'bata wannan dalilin yasa na yanke shawara kan cewa gobe idan Allah ya kaimu duk zan sa a fito da kayan abincin dake cikin store d'ina a fita dasu can wani guri a zubar sabida gudun afkuwar wata matsalar." Maimartaba shuru yayi duk jikinsa yayi sanyi tabbas hakan na iya kasancewa

"Babana nifa ban yarda da wannan maganar taka ba, har yaushe ka dawo garin da kayan abincin ka zasu lalace kuma me yasa lokacin da wannan yarinyar Sumayya take maka girki ba'a samu matsala makamanciyar wannan ba, nidai ina zargin wannan yarinya Suwaiba da Safiyya ta kawo maka."

Girgiza kansa yayi yana kokarin kawar da damuwarsa yace."Mamma dan Allah ki daina zargin kowa akan faruwar wannan al'amari na fad'a miki ga dalili ki yarda a haka ke dai kawai ki cigaba dayi min addua akan Allah ya kare ni daga kowane abin qi."

Jikinta ne yayi sanyi tace"To shikkenan babana Allah ya kare ka da kariyarsa." Maimartaba yace."Da har nasa an rufe yaran guda biyu to tunda gaskiyar lamari ta bayyana idan ka fita sai kasa a bud'e su." Yace."To godiya suke ranka ya dad'e." Sarki jijjiga kansa yayi yana kallon yaron nasa tare dayi masa addua a cikin zuciyarsa, mikewa yayi a nutse yace."Ni zan shiga gurina na huta a tashi lafiya." Fulani tace"To babu damuwa yanzu zan aiko maka da abinci nasan dai kana bukatarsa." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Mamma tsabar fargaba da tension ya sanya cikina ya cushe amma babu damuwa ki aiko zanci insha Allah.'' maimartaba yace."Ka daure kaci abinci kada ka zauna da yunwa komai yayi tsanani maganinsa Allah.'' Yace."Insha Allah." Sallama yayi musu suka bishi da kyakkyawar addua.



*Na kudi ne..*!
Kada ki karanta min littafi sai kin biya, keda ki ka fita da book din keda Allah....idan kina so ki biya ga yanda abin yake...vip group #600 normal #300 accont..0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(kainuwa dashan Allah✊?)
67&68
kame-kame ya fara yana so ya tuna tsayin kwanakin da yarinyar ta dauka bata zuwa aiki, ganin yana kwane-kwane yasa ta 'bata fuskarta a kaurare tace"Babana baka da gaskiya duk yanda akayi kaine ka kore ta da 'bakin halinka."
Da sauri yace."Haba mamma kada kiyi min wannan shedar mana wallahi ni banyi mata komai ba kawai wayar gari nayi naga bata zuwa aiki shiyasa ai nace ki aika a kirata a gabana idan nayi mata wani abu sai ta fada."
Fulani jikinta ne yayi sanyi tace"Yanzu duk tsayin wannan lokacin a'ina kake samun abinci ni dai baka ta'ba zuwa ka nemi abinci a gurina ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Mamma ki kwantar da hankalinki na gane abinda kike gudu insha Allah babu abinda zasuyi ya same ni." Tace"Insha Allah ka dai fada min inda kake samun abinci."
takarashe maganar idonta a tsaye a kansa

"Mamma Lawisa ce take kawo min daga 'bangaransu." Fulani shuru tayi tana kallonsa tana girgiza kanta shikkenan tasan sun wanke sun bashi yasha sai dai kawai ta dage da addua a kansa ba tun yau ba tasan wacece Hajiya Karima macece mai biye biyen malamai duk ta d'ora 'ya'yanta a turba mara kyau shiyasa gabadaya bata kaunar auransa da Lawisa saboda tasan zasuyi tayi wa yaron ta surkulle......."Mamma akwai matsala ne naga kinyi shuru kina girgiza kai."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Bani da abinda zance sai dai addua akan lamarin Lawisa ita zaka aura dan ta baka abinci kaci ba laifi bane amma kafin kaci duk abinda zata kawo maka naci ko nasha ka dinga addua tukkuna."

A sanyaye yace."Insha Allah zan kiyaye." Wayarta dake kusa da ita dauka ta kira Jakadiyarta, taba umarnin kiran Sumayya.


Ina zaune tsakar gidanmu ina bitar karatun al'kur'ani Jakadiya ta shigo, ganinta ya sanya min faduwar gaba, al'kur'anin na rufe a nutse muka gaisa da juna tace"Fulani ce tace kizo tana neman ki." Kafin nayi magana Tambaya tace Allah yasa dai lafiya." jakadiya tace."Lafiya lau babu wani abu insha Allah." Ganin yanda Tambaya ta razana yasa nayi saurin daidaita kaina nace"To shikkenan kice mata ganin zuwa." Jakadiya ta amsa da to ta tafi. mikewa nayi ina yar dariya na kalleta nace"Wai mai yasa duk sanda aka aiko kirana daga cikin gida kika tsorata."
Cike da kulawa tace"Dole na tsorara Sumayya bana son wani abu ya same ki na sharri na fahimci mutane nayi mana hassada saboda kawai kina kula da Yarima Lami da sauransu duk sun daina amsa gaisuwata ko haduwa mukayi a gurin rabon abinci basa kulani wani lokacin ina ji suna gulmar mu shiyasa nake jin tsoro kada a shirya miki wani sharrin."

Murmushi nayi nace"Kada ki damu insha Allahu babu abinda zai faru sai al'kairi maganar su Lami kuma ki ajiye ta a gefe kiyi abinda ke gabanki Hassada sukeyi idan sun gaji zasu bari."

Tace."To shikkenan Sumayya amma ki 'kara kula kinji ko." Nace"Insha Allah zan kiyaye." Takalmana nasa nayi mata sallama na tafi.


Cikin nutsuwa nayi sallama na shiga falon, 'kamshin turaransa ya tabbatar min da cewa yana gurin, kaina na sunkuyar kasa na cigaba da tafiya a nutse har na karasa inda suke na zube a gabanta cikin ladabi nace"Barka da dare ranki ya dad'e."

Cikin kulawa kamar koda yaushe ta amsa da "barka dai Sumayya ina fatan kuna lafiya.?
" Lafiya lau ranki ya dade Jakadiya ta sanar dani kina nema na.'' a nutse na fadi maganar ina kara yin kasa da kaina ban yarda na kalli gefan da yake zaune ba ta gefan idona nake ganin irin kallon da yake min cikin zuciyata nace "Kallo sai kace sabon makaho."

Falon ne yayi shuru na minti biyu kafin naji muryarta a nutse ta kira sunana.
Amsawa nayi ba tare dana dago ba, Tace."Inaso ki fada min dalilin da yasa kika daina zuwa aikin sashen Yarima ashe kin watsar da amanar dana baki ban sani ba."

A sanyaye nace"Ranki ya dade ki gafarce ni ba daina zuwa aiki nayi ba wallahi kwana biyu ne nake ta rashin lafiya shine dalilin da yasa na daina zuwa."

A yanda ta fadi maganar tana rawar murya yasa ta gane karya take, Tace"Haba Sumayya mai cuta ai ya fita daban ki dube ki fa a dan tsayin kwanakin da nayi banganki ba kin 'kara girma ban yarda baki da lafiya ba kina 'boye min wani abune ki fad'i min gaskiyar magana shin me babana yayi miki kika daina zuwa ki kula dashi."

Shuru nayi dan gabadaya ta daureni da jijiyoyin jikina, tace"Kina jin tsoron ki fada min kada yayi miki wani abu ko."? Da sauri nace"ba haka bane Mamma ki yarda da maganata ta farko bani da lafiya ne amma ni Yarima beyi min komai ba kuma insha Allahu gobe zan cigaba da zuwa aikina."

Murmushi tayi tana girgiza kanta tace"Shikkenan tunda kin 'boye kin kasa fada min gaskiya ni zan baki hakuri akan laifin da yayi miki dan Allah ki daure ki cigaba da kula dashi har lokacin da Allah zai kawo lokacin auransa insha Allah kin kusa hutawa tunda an tsayar da rana wata uku masu zuwa idan matarsa nada ra'ayin zamanki domin ki cigaba da yi musu hidima to sai ki cigaba da zama idan kuma bata da ra'ayi sai ta kawo sabbi su cigaba da gabatar da aikin da kika bari ina fata kin fahimce ni kuma kin huce fushin ki."

Murmushi nayi nace"Ranki ya dade ki daina hadani da Allah akan wannan al'amarin, wallahi kinfi karfin komai a gurina shiyasa duk sanda wani abu ya taso naga kina bani hakuri nake mamaki! kada ki damu insha Allah nayi miki al'kawarin cigaba da kula da amanarki har zuwa lokacin da kika fada ina rokon Allah ya bani ikon rike amanarki.

Murmushi jin dadi tayi tace"Sumayya dole nayi miki godiya domin kin cancanta ayi miki komai kina da hankali da nutsuwa gaki da iya lafazi kyawawan halayenki sune suka sanya naji kin kwanta min a raina har na yarda dake a matsayin mai kula da gudan jinina dan haka dan nayi miki godiya ba abin damuwa bane."

Murmushi nayi ina jin kaunar matar a cikin raina, hakika da Yarima ya gaji halinta da karamcinta da baiyi wasu abubuwan ba na rashin kyautawa cikin nuna farin ciki da yabawar da tayi min nace."Ranki ya dade nagode sosai da samun yabo daga gurunki."
Kaina ta dafa a nutse tace"Allah yayi miki albarka." na amsa da ameen ina mirmushi. tace"Kina iya tafiya gobe idan Allah ya kaimu sai ki cigaba da aikin ki." Risinar da kaina nayi nace"To shikkenan ranki ya dade a tashi lafiya." A nutse ta amsa tana murmushi, gefan da yake zaune na kalla nace"Ranka ya dade a tashi lafiya." Ciki ciki ya amsa min. na mi'ke a nutse na fita daga falon

Koda na koma gurinmu samun Iyayena nayi a zaune a tsakar gida suna magana shigowa ta yasa sukayi shuru dukkaninsu suka bini da kallo, murmushi nayi na zauna kusa da babana a nutse nace"Baba ina fatan baka ci abincin ba." Cike da kulawa yace."Ai ban jima da shigowa ba mahaifiyarki ke sheda min inda kike." Ganin yanayin damuwa a tare dasu yasa nace"Eh hakane dan Allah ku kwantar da hankalin ku ba wani abun bane aiki tasa ni shiyasa kuka ga na dad'e."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."To Alhamdulillah maza jeki dauko mana abincin muci." Da sauri na mike na nufi kicin domin dauko abincin...Tambaya daki ta shiga ta shiga gyara mana gurin kwanciya, nida mahaifina abinci muke ci a nutse muna hira cikin fahimtar juna shakuwar dake tsakanina da babana ba takai wacce take tsakanina da Tambaya ba, babana mutum ne mai sauki hali yana da barkwanci kullum cikin wasa da dariya yake kuma dukkanin abinda za'ayi masa na 'ba tanci ba zaka ta'ba ganin bacin ransa ba mutum ne wanda duniya da dukkanin abinda ke cikinta be dameshi ba.


Washe gari da wurwuri na tashi domin ina so naje nayi duk aikin da zanyi na gama a kan lokaci na samu damar zama gurin karatu, tare muka fita da babana ya nufi b'angaran dawakai ni kuma kai tsaye sashen Yarima na nufa, duk wannan sammakon dana buga samunsa nayi a shirye cikin k'ananun kaya da cup a hannunsa ya shirya tsaf da alama daf yake da fita gurin aiki. jikina ne yayi sanyi na kalli agogon bango nan naga karfe bakwai da rabi, shaf na manta ya fara fita aiki dana sani ina idar da sallar asubahi na shigo nayi ayyukana na huta.

Babu walwala a tare dani nace"Ranka ya dade barka da safiya ina fata ka tashi lafiya."?
Cup din tea din ya ajiye kan tevur din dake gabansa babu yabo babu fallasa yace."Barka kadai." Kicin na nufa ba tare da na sake magana ba. Suwaiba na samu tana soya doya da kwai gaisawa mukayi na tsaya ina tunanin abunyi....kamshin turaransa ne ya tabbatar mana da shigowarsa kicin,
Kasa nayi da kaina dan har yanzu ina ganin bakinsa, a nutse yace."Ke Ki ajiye wannan aikin da kikeyi me shi ta dawo kije kawai na sallame ki kada ki kara zuwa kiyi min hidima." Suwaiba ta ajiye abin hannunta a nutse tace"Godiya nake ranka ya dad'e."
Hanya ya nuna mata da hannunsa alamar ta futa, kai a kasa ta fita daga kicin din.
Shiru na minti biyu kafin naji gyaran muryarsa, dago kaina nayi babu walwala a tare dani, yace."Me yasa baki zo akan kari ba? ko kin manta na fara fita aiki.'' Nace"Wallahi na manta amma ka gafarce ni naga Suwaiba ta gama hada komai bari kawai na fito maka dashi.....girgiza kansa yayi alamun baya bukata.
Juya yayi zai fita yace."Idan na dawo daga asibiti ina da muhimmiyar magana dake."
Bayansa nabi da kallo ina mamakin wace magana zamuyi, har ya fice daga kicin din ban dauke kaina daga hanyar daya bi ba, na jima sosai a kicin din ina tunani akan maganarsa, ajiyar Zuciya na sauke ina addua akan Allah yasa al'kairi ne ke tafe dashi, kicin din na gyara tsaf na juye soyayyar doyar da Suwaiba ta soya a cikin kula na dauka na fita da ita, can gurin su Haruna na nufa na dire musu kular a gabansu, Haruna yana murmushi yace."Ranki ya dade me muka samu ne."? Cikin kulawa nace"Soyayyar doya ce na kawo muku Suwaiba ta soyawa Yarima tayi mishi yawa shine na yanke shawarar kawo muku." Cike da farin ciki ya kalli su Isa da fadin "Ku taso ga abin arziki Sumayya ta kawo mana." Gurin suka iso suna min godiya na dinga mamakin godiyar da sukeyi min. nace"Haruna ni zan tafi gurin karatu sai yamma zan shigo." Yace."To babu damuwa Sumayya." gurin na bari da sauri naje na dauko jakar litattafaina na wuce gurin karatu.....ko zaman minti ashirin banyi ba hayaniya ta tashi wani malami ya shigo ajinmu da fadin"Ke Sumayya fito." gabana ya fadi jin ya kira sunana! fitowa nayi daga cikin 'yan uwana ya tasa ni a gaba tun kafin mu karasa gurin na hango Haruna da Isa ri'ke da kirji sai kakarin amai suke, a gigice na k'arasa inda suke ina tambayar abinda ke faruwa Usuman ne yace."Ki rufe mana baki anan gurin ba kece silar faruwar komai ba."
Murya na rawa nace"Usuman ban fahimce ka ba dan Allah kayi min bayani." Tsaki yaja kafin yace."Tun bayan da sukaci doya da 'kwai din da kika basu cikinsu ya hautsine sai amai suke suna zawo ko ba kiga yanda kudaje ke bin gurin ba.''
Da sauri na shiga binsu da kallo naga yanda kudaje ke binsu suna tashi sai kakari suke suna yunkuri idanunsu yayi jajawur! kuka na fashe dashi nace"Wallahi tallahi bani bace." Buba ya kawo min mari a fusace yace idan baki rufe bakin ki ba yanzu zaki sha duka anan gurin." Gum! nayi ina zazzare ido hade da kallonsu Haruna dake durkushe a gurun.......Jakadan maimartana ne ya iso gurin shida wasu fadawa suka saka su Haruna a mota suka nufi asibiti, hankalina ya tashi sosai na juya domin shiga gurinmu, Jakada yace."Kece Sumayya ko."? da sauri na daga kaina. Yace."Muje Maimartaba nasan ganinki." gabad'aya gwiwata tayi sanyi jin abinda yace bani da yanda zanyi dole nabi bayansa zuwa fadar Maimartaba nasan dai zai tuhume ni ne akan abinda ya faru dasu Haruna........


*Na kudi ne!*
Allah ya isa idan kika karanta! idan kina so ki biya ga yanda abin yake vip group #600 normal group #300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaku turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
73&74
Da 'kyar na iya cin abinci na mik'e domin wanko hannuna dakin na dawo na same su suna magana shigowata yasa suka tsira min ido, a nutse nace"Zanje sashen Yarima koda abinda yake bukata nayi masa, cike da tausayi da kulawa sukace "To sai kin dawo." Fitowa nayi daga dakin nasa takalma na fita.

Koda na shiga falon shuru babu kowa da alama yana sama ko kuma be shigo ba, juyawa nayi da niyyar shiga kicin naji motsinsa, a hankali na juyo ina kallonsa yana sakkowa, kaina na sunkuyar har ya sauko ya zauna kan kujera gaishe shi nayi hade da fadin"Ko kana da bukatar wani abu.'' Kai ya girgiza kafin yace.''Bana bukatar komai kije ki huta." Tsira masa ido nayi......ganin inaso nayi magana yasa yay saurin katse ni da fadin"Sarkin zargi da rashin yarda nace kije ki huta naci abinci a gurin Mamma.


Sarkin zargi da rashin yarda maganar nayi ta nanatawa a cikin raina wato duk abinda nake nunawa a kansa bai dameshi ba tunga gashinan yayi min wata fassarar tunda nake kula dashi dayi masa hidima bai ta'ba yi min godiya ba ko kuma ya nuna min jin dadinsa kullum cikin fada min bakar magana yake, kaina na girgiza ba tare dana sake magana ba na juya da niyar fita daga dakin.


"Sumayya." a kasalance naji ya kira sunana, juyowa nayi muka hada ido dashi, yace."Idan hankali ya kwanta inaso muyi magana dake." ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa ido da ido nace"Ko wace irin magana ce take bakin ka zaka iya fada min a yanzu ina sauraronka."

Girgiza kansa yayi yana lumshe ido yace.''Sai kin samu nutsuwa tukkuna dan na fahimci yanzu bakya cikin hayyacinki." Kaina na girgiza tare da fadin"Babu damuwa Allah yasa naji alkairi." Murmushi yay had'e da shafa sajensa yace ."Alkairi ne insha Allah.'' Ganin yana munafikin murmushi yasa na tsargu babu shakka har yanzu akwai mugun abu a cikin zuciyarsa, sallama nayi masa na kama hanya na fita ina mamakin al'amarin


Cikin kwanaki bakwai da rasuwar Isa al'amura sun d'anyi sauk'i masarautar ta samu nutsuwa kowa ya fawwalawa Allah ya cigaba da harkokinsa 'bangaran basawan masarautar kuwa kullum cikin shirya kitumurmura da ma'kar'kashiya sukeyi har yanzu sunqi saduda burinsa bai wuce ace sunga bayan Yarima Ali ba inda shi kuma nashi bangaran kullum zuciyarsa fes take a kansu baya ta'ba yarda da cewa sharrinsu da makircinsu zaiyi tasiri a kansa tunda ya riga ya kad'aita Allah yayi ya'kini da cewar babu abunda zai sameshi sai abinda Ya hukunta, ko a fuska bai ta'ba nunawa kowa ba duk bayan kwana biyu sai ya shiga kowane sashe na gidan sun gaisa inda su kuma suke nuna masa kauna a fili a bad'ini kuwa su kadai suka san irin 'kiyayyar da suke masa

Magajin Sarki ya turke Suwaiba ita dashi ya tsoratar da ita mutuka Suwaiba na kuka gami da nadamar abinda tayi ta sheda masa yanda al'amarin ya faru, wato Muddibo ne ya tursasata kan lallai sai tabi umarninsa tayi amfani da wani igur'bataccan ruwa mai wari daya kawo mata cikin wata jarka yace lallai tayi dahuwar abinci da ruwan kuma ta tabbatar Abinda ta dafa Yarima yaci, babu yanda ta iya haka ta dinga mu'ku-mu'ku da ruwan guban har dai ta yanke shawarar dafa doya dashi, bayan ta tsame doyar ne tana tsaka da soyawa a ranar da al'amarin zai faru ya shigo kicin din ya sallameta daga aiki ita kuma Sumayya ta dauka ta kaiwa su Haruna suka ciki.

Magajin Sarki beyi mamaki ba dan yaji ta ambaci sunan Muddibo dama tuntuni yake zargin akwai sa hannunsa a cikin faruwar al'marin, nasiha mai ratsa jiki yayi mata ya tsoratar da ita sannan ya nuna mata illar abinda ta aikata wato ta amince an hada baki da ita anyi kisan kai. Suwaiba kuka kawai take tana neman gafararsa, yace."Bani zaki nema gafara ba Allahn daya hallice ki shi zaki nema gafara ki tuba ki nemi gafararsa sai ya yafe miki."
Tace."Insha Allah na tuba nabi Allah da manzon Allah ba zan sake yarda wani ya tursasani ga aikata sa'bon Allah ba.'' Magajin sarki yaji dadi sosai da tuban ta, sallamarta yayi ta tafi tana addua akan Allah yasa kada ya fad'awa mahaifinsa harda saka hannunta a cikin faruwar al'amarin, bangaran Yarima kuwa baya tsammanin zai fad'awa kowa maganar domin fitar da ita yana nufin abubuwa da yawa barin ta shine yafi kwanciyar hankali.


******

Yau asabar duk ranakun weakened baya fita da wuri

Please Login or Register in order to submit comment