Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba min ido kana kallona ka tashi ka bani magani nace."

'Dan 'bata fuska yayi yace." Ke! ni kikewa tsawa haka."? ganin yanda ya hasala ne yasa na shiga bashi hakuri ina hawaye.

Yace." Bani da magani a gida kuma tun jiya na fada miki cewa ba zan fita asibiti da wuri ba zan kwanta na huta a gida sai ki bari na tashi tukkuna."


Wani irin kallon takaici nake masa yaja bargo ya rufe jikinsa! fizgewa nayi ina kuka nace"Ashe dama munafurci ne."? ya kalleni nace" Wallahi kaji tsoron Allah akan abinda kake." mi'kewa zaune yayi rai a 'bace! yace'Tashi ki fita ki bani guri na huta." hannunsa na rike ina cigaba da zubar da hawaye nace"Dan Allah ka tausaya mana nida babyna."

Girgiza kansa yayi yace." Zan baki magani amma sai na gama bacci tukkuna." komawa yayi ya kwanta yana sake rufe jikinsa da bargo! a fusace! na fuzge bargon ai kafin na ankara ya kwada min mari!!! na dafe kuncinta ina kallonsa.......Cikin rashin mutumci yace." Wallahi zan tattakaki idan baki bani guri ba." mi'kewa nai a sanyaye na fita daga dakin, tsaki yaja mai karfi ya koma ya kwanta yana addua akan Allah yasa cikin ya zube ya huta.

Koda na fita falon kasa danne damuwata nayi kawai na zauna kan kujera ina kuka domin nasan shi kadai zanyi na samu sassauci a cikin zuciyata, abubuwan da mutumin yake min sunyi yawa akwai abunda nake dubawa shiyasa kwata-kwata bana so na shedawa mahaifiyarsa Mamma macace mai karamci da mutunci zaman da nayi da ita ya sa na fahimci nagartattun halayenta ta nuna min dukkanin kauna da kulawa wannan dalilin yasa kwata kwata bana so naje na tayar mata da hankali bayan haka kuma ina kokarin ganin na rufa asirin aurena sanin da nayi cewar fallasa sirrin aure bashi da amfani ga ma'aurata shiyasa nake hakuri da duk abubuwan da yake min amma yanzu ya zama dole na sheda mata irin halin da nake ciki domin na tsira da lafiya nida abinda ke ciki......hawaye na share na mike na shiga dakin na sameshi yana bacci cikin kwanciyar hankali, girgiza kaina nayi firji na bude na dauko goran ruwa da cup kadan na tsiyaya na zauna kan kujera Fala'ki da nasi kafa uku na tofa a cikin ruwan sannan na tofa ayatulkursiyu kafa daya bisimillah nayi nasha na rage kadan na shafe cikina dashi.....cup din na ajiye na kwanta kan kujera tare da tsirawa rufin dakin ido........cikin ikon Allah na samu sassaucin abinda nakeji Allah nagodewa na gyara kwanciyata bacci mai nauyi ya daukeni.



Sai wajejen uku na rana na tashi babu shi a dakin da alama bai jima da fita ba dan gabadaya dakin kamshin turaransa yake, wanka nayi na dauro alwala na fito nai sallah na shirya jikina na fita na sami abinci naci naji karfin jikina, su Mariya sukayi min rakiya can gurin mahaifana, alhamdulillahi naji dadin yanda naga jikin babana yayi sauki na zauna mukayi hira sosai sai daf da magariba na koma gurina.................. Sanin da nayi cewa ba a gurina yake ba yasa na rufe kofa dan ina tabbacin tinda mukayi haka dashi ba zai shigo yayi min bankwana ba, aikuwa har ya gama kwana biyunsa a gurin Lawisa bai shigo gurina ba kuma bai kira wayata ba, nima fushi nake sosai inaso na nuna masa cewar na gane abinda yake nufi dama ashe yaudarata yake yana nuna kamar ya hakura ashe domin ya samu biyan bukatarsa wannan dalilin yasa na dauki al'kawarin bijire masa tunda dai shi baya tsoron Allah.


Ko kunya daya dawo gurina ya dinga wani lalla'bani har tambayar jikina ya kawo wani magani wai na ciwon cikine duk sanda naji ciwo nasha zanji sassauci kar'ba kawai nayi na ajiye na bar masa dakin.


Falon ya fito wai na bashi abinci na hada masa komai na bar masa gurin, a falo na kwanta na kyaleshi a dakin, can dai da yaji shuru ban shiga dakin ba ya fito ya tsaya a kaina yana min magana! a fusace! na mike nace"Kai! na fa daina yarda da yaudararka na gane har yanzu kana kan bakanka baka kaunar cikina to Allah yana kaunarsa kuma insha Allahu sai na haifeshi lafiya."


"Sumayya ni kike d'agawa harshe?" nace"Ai kai ka janyo ni dai dan Allah ka matsa daga kaina bana bukatar dadin baki.''



"Okay naji kina iya tasowa kina bani hakkina ko kuwa."? wani banzan kallo nai masa nace" Ba kaji kunya ba!" shan kunu yayi yace."Kifa shiga hankalinki dani bani da sauki kin dai san halina ko."?

A fusace! nace"Ka jima ba kayi min mugun abuba dama ai ka saba nima na saba duk wani mugun sharrin da kuke bibiyata dashi zai koma kanku.'''


"Sumayya bayan ni ashe akwai masu binki da sharri.''? nace" Kwarai kuwa kaje kayi binkice." ajiyar zuciya ya sauke yace." Yanzu dai kiyi hakuri ki tashi muje." nace'' Kai komai abinka sai ka hakura ka kyaleni.''


Murmushi yayi yace."Kin san Allah bazan kyaleki ba ko kina so ko bakyaso sai na biya bukatata.'' kafin nayi yunkuri ya fara kokarin daukata, hannunsa na dinga bugewa ina matsawa, kawai sai ya turmusheni akan kujerar gabadaya ya sakar min nauyinsa! rashin karfi da kuzari yasa jikina ya mutu kyaleshi nayi ya biya bukatarsa saboda nasan idan nace zanyi buge buge ni zansha wuya amma ko kusa ban bashi had'in kai ba dan sandarewa nayi yayi kid'ansa yayi rawansa.


****
Abinda ya cigaba da faruwa kenan a tsakaninmu dik ranar da yake gurina da kokawa yake samun biyan bukatarsa ni a galabaice shi a galabaice gashi sabida tsabar fitina sai yayi sau biyu farkon dare da kuma asubahi.........

*Bayan wata biyu*
Cikina ya shiga wata na biyar sai jikina ya soma nauyi nayi wata irin qiba 'kuguna ya sake fad'i cikin gabadaya ya shanye gurin breast d'ina sai dai ya d'an fito tunda ya huda zani ana ganin tudunsa amma sai mai 'kurulla ne zai gane! bani da laulayi mai zafi sai dai nayi haske sosai mussaman kafafuna da hannuwana, 'Bangaran Magajin sarki kuwa kullum cikin 'kunci da takaici yake mutukar zai budi ido ya ganta da cikin sai yaji kamar ya sha'keta saboda haushi! shiyasa kullum cikin yi mata iskanci da wulakanci yake kuma idan dare yayi yazo ya mori albarkatun jikinta.


Ina zaune a falo tayi sallama ta shigo, cikin kwalliya, murmushi nai nace"Barka da zuwa." Mansura ta samu guri ta zauna nace" Ba kiyi zuciyaba." mirmushi tayi tace" Na dai kusa." nace"Kiyi hakuri insha Allahu ina nan zanzo musha hira.

Tace."Ai ke yanzu dole ayi miki uziri tunda kinyi nauyi.'' nace."Bangane nayi nauyi ba." dariya tayi tace" Ashe baki da hausa ina nufin d'an baba ya kusa zuwa." sai nasa dariya da fadin"Waye yace miki ina da ciki."? tace"Haba Sumayya gashinan har yayi kwari ai mu ba makafi bane."

Murmushi nayi ina girgiza kaina, ta mike da fadin"To ni zan koma amma kafin nan zan shiga gurin Lawisa itama mu gaisa da juna." nace"Gaskiya kin kyauta sosai kina da kokarin zumunci insha Allahu zamu zo." tace"Ai ita Lawisa zuwanta uku kece dai baki ta'ba zuwa ba." nace"Kada ki damu insha Allahu zanzo a kurkusa." tace" To shikkenan sai na ganki." har bakin kofa na rakata mukayi sallama cikin mutunci.



"Mansura kika ce Sumayya na dauke ciki."? Lawisa ce ke wannan maganar cikin tashin hankali!! Mansura ta girgiza kanta da fadin" Kwarai kuwa wallahi ciki ne da ita dan da alama ma ya kwana biyu tunda gashinan har ya fito.


Lawisa taji wasu zafafan hawaye na nema su kufce mata, murya na rawa tace"Mansura ya akayi haka ta faru? ya akayi Sumayya ta dauki ciki bayan Sai da ya tabbatar min da cewar itama yana bata kwayoyin hana haihuwa.''

Mansura tace"Lawisa bangane maganarki ba."? hawaye ta share ta shiga warware mata yanda sukayi, tun kafin a daura aura

Mansura tace"Amma gaskiya Lawisa kinyi ganganci waye ya fada miki ana haka? kawai sai ki dinga dibgar kwayoyi ba tare da kin tabbatar da cewar kina haihuwa ko bakya haihuwa ba, a gaskiya Lawisa na raina wayonki."


Hannu tasa ta goge hawaye tace"Wallahi Manusura na rasa yanda zanyi ne shiyasa na amince da bukatarsa sai gashi ya ha'ince ni." Mansura tace"Ai a zahiri ya fi sonta shiyasa yake so ya haihu da ita ke kuma yana baki kwayoyi idan zakiyi hankali kiyi idan ba hakaba to tabbas zai kaiki ya baro."


Cikin tsantsar tashin hankali da nadama tace"Mansura wallahi nima daga yau na daina shan kwayoyin sai dai duk abinda zaiyi yayi kuma idan baiyi wasa ba sai na samu Maimartaba na fada masa abinda yake aikatawa."



Mansura tace"A'a kada kiyi saurin yanke hukunci keda shi ku yankewa kanku hukunci a daki dole ya hakura kema ya barki haka tunda dai kishiyarki ta samu ciki kema sai kiyi kokarin samu amma kika fitar da maganar dake dashi dik sai kunji kunya."


Lawisa shuru tayi tana jajanta al'amarin, Mansura ta mike da niyyar tafiya, Lawisa har bakin kofa ta rakata tana mata godiya akan shawarwarin data bata .


Koda ya shiga gurinta ya ganta cikin rashin nutsuwa yasa ya tsaya yana tambayarta, kuka ta fashe dashi tace"ashe Sumayya ciki ne da ita shine ka munafurce ni kake ta bani kwayoyi ina sha ashe har kafi kaunar had'a jini da ita akaina."?


Jikinsa ne yayi sanyi yace."Ke waye ya fada miki tana da ciki." !? mikewa tayi tana kuka tace"Bana so ka raina min hankali ko ka 'karyata wanda ya fad'a min ba zaiyi min karya ba Matarka nada ciki dan har yayi kwari ma."


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Sai kiyi hakuri nima hakurin nake akan al'amarin ke kinsan bani da ra'ayin haihuwa a yanzu yanda kika ga cikin nima haka na ganshi.''' Tana kuka tace"Wannan wace irin magana ce kai kayi cikin amma kana cewa haka ka ganshi wato nice baka kauna ko babu komai ai zan samu Maimartaba na fada masa irin cutar da kayi min.

Da sauri yace."Duk wannan maganar bata taso ba tunda ciki kike so zaki samu zaki daina shan kwayoyi insha Allahu kuma zan baki maganin da zai kwanke miki mahaifarki ki samu ciki da wuri sannan inaso nayi miki albishir da cewa zamuje America tare akwai taron likitoci da za'ayi a asibitin da nayi aiki a can cikin satin da zamu shiga zamu tafi tare ki rakani."


Jin wannan magana yasa taji sanyi a cikin ranta taji dadi sosai daya za'beta domin yayi tafiya mai muhimanci da ita ko banza tasan tafi Sumayya a gurinsa, kwantar da hankalinta tayi ta bashi dukkanin kulawar da yake bukata.




*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne, idan kina so ki biya kudi ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
103
Sai ana Saura kwana biyu na samu labarin tafiyar tasu, shima ba daga bakinsa naji ba lokacin da naje gaishe da Mamma take min zancen a lokacin hankalina ne ya tashi sosai kishi ya taso min amma saboda kada ta fahimci wani abu yasa na nuna mata cewa nasan da tafiyar hakuri ta shiga bani da fadin"Tunda ni bani da koshin lafiya nai hakuri suje su dawo murmushi nayi na nuna mata cewa babu wani abu dake damuna akan tafiyar tasu tunda ya za'bi tafiya da Lawisa ai duk d'aya ne dani da ita, sallama nayi mata na koma gurina na kwanta abin duniya ya taru yayi min yawa, yini nayi cikin damuwa da 'bacin ran munafurcin da yake min dan zaiyi tafiya da Lawisa meye na 'boye min tunda ban isa na hanashi abinda yayi niyya ba wato daba dan na shiga gurin Mamma ta fada min ba da sai dai idan zasu tafi ya shigo yayi min sallama! girgiza kaina nayi na mike zaune jin alamun za'a shigo yasa na tsirawa kofar dakin ido, Mariya ce ta shigo tace"Ranki ya dade kina da bakuwa."
A sanyaye nace"Wacece."? dan jim tayi kafin tace"Wannan matar ce mai qiba wacce kika hanamu bude mata kofa."

Nace"Yanzu ma kada ku bude mata kofa ku rabu da ita idan ta gaji zata tafi." Mariya tace"To ranki ya dade." fita tayi ni kuma na mike tare da tsayawa bakin window ina mamakin abinda ya sake kawo Lauratu gurina na rasa abinda nayi mata take kokarin cutar dani na tabbata yanzu ma ba alkairi ne ya kawota ba.

Bud'e kofar dakin ce tasa nai saurin juyowa sai muka hada ido dashi ya shigo fuska a had'e! kallo na bishi dashi ina mamakin dawowarsa gida da wuri.

"Sannu da zuwa." nace ina kallon fuskarsa, yace."Sumayya yaushe kika koyi wulakanci da 'kin mutane ."? Nace"Ban fahimci maganarka ba." Yace." Aunty Lauratu tazo dubaki kin hanata shigowa hakane ko ba haka bane."? shuru nai na nemi guri na zauna! yace." Kada wani ko wata ya sake zuwa ki hana a bude masa kofa kin gane ko."?

Nace"Wai shin wace irin alaqa ce a tsakanin ka da matar da kazo kana tada jijiyar wuya akanta."


"Rashin kunya zakiyi min kenan."? sassautawa nayi nace" Kayi hakuri ba zan maka rashin kunya ba na tambayeka ne." Yace." Aunty Lauratu kanwar Hajiya Karima ce mahaifiyar Lawisa ina fata kin gane."


Nace"Nagane amma sai nake ganin ni bani da wata alaqa da ita sai ta musulunci dan haka banga dalilin da zai sanya ta dinga wanko kafa tana zuwa inda nake ba."


Cikin mamaki yace."Kina nufin tana zuwa kenan kina hanata shigowa."? nace"Kwarai kuwa bazan bari ta shigo ta cutar dani ba."

"Sumayya wai me yasa kike da zargi ne.? kallonsa nayi nace" bani da zargi dik abinda kaga nayi magana akai to naga zai cutar dani ne."

Yace."To na dai gaya miki kada ta sake zuwa ki hanata shigowa wulakanci bashi da dad'i." Kai tsaye! nace"Wallahi ba zan barta ta shigo ba." Ya tsira min ido yana kallona kafin yace." Akan wane dalili." ?

"Duba can gurin ka gani." ya waiwaya yana duba inda nake nuna masa, yace."Ke ni banga komai ba." ajiyar zuciya na sauke na mike tsaye na isa gurin! karasowa yayi gurin.

Nace"Sati uku da suka wuce ta shigo har dakin nan da niyyar ta watsa min asid ga sheda nan ka duba a ranar Allah ne kawai ya kare ni daga sharrin da ta shigo min dashi."


Cikin mamaki mai tsanani yake kallon gurin yayi duhu sosai lokaci guda ya gane asid ne kuma irin mai mugun karfin gaske.

"Sumayya ya akayi baki fada min ba." ? d'an ta'be baki nayi nace"Baka da lokacina ai tunda kaima neman lafiyata kake." hannu ya daga min rai a bace yace.'' ba'kar magana zaki fad'a min."?

Girgiza kaina nayi naja bakina nai masa shuru, yace."Saboda rashin hankali kina fuskantar irin wannan matsalar amma kija bakin ki kiyi shuru meye amfanin hakan.

Muryarta na rawa nace"Wai dan Allah har yaushe ka zauna dani ka bani kulawar da zan fada maka abinda yake faruwa! nafi kowa sanin halinka zaka iya cewa 'karya ne shiyasa nai maka shuru."


Murmushin takaici yayi yace.'' Ai sai ki cigaba da shuru kina cutar kanki duk ranar da suka samu galaba a kanki kada kiyi kuka da kowa." Nace"Insha Allahu dukkanin wanda yake nufi na da sharri sai ya koma masa."

Yasan har dashi a ciki shiyasa yaja bakinsa yai shuru ya nufi toilet yana mamakin abinda yake faruwa dole kafin ya tafi yasa matakan tsaro a sashen nata sabida gudun abinda ka iya zuwa ya dawo sosai al'amarin ya firgitashi.


Dakin na bar masa na koma falo na zauna, ya fito cikin jallabiya milk kallonsa nai na dauke kaina yace."Kiyi hakuri kizo ki bani abinda zanci." sanyi naji a zuciyata ganin yanda yake min magana, na mike na nufi dainng din ya biyo baya na kujera ya gyara ya zauna yana kallona ni kam na kasa sakin fuskata saboda 'bacin ran abinda yayi min......."Ya jikin naki ina fatan babyna ya wuni lafiya."? shareshi nai na tura masa plate din abincin gabansa, yace."Sumayya zauna zanyi magana dake, yanda yayi maganar cikin tsare gida yasa na zauna." Yace."Zanje america domin halartar taro irin namu inaso ki kula da kanki wannan abun da yake faruwa dake ya tsoratar dani mutuka kada ki sake yin shuru akan wani mummunan abu insha Allahu zan kawo matakan tsaro domin su saka ido a gurin sannan ita kuma Lauratu dole na dauki mataki akanta zata fada min dalilin da yasa take bibiyarki da mugun abu."


Nace"Dan Allah ka bar maganar nan ni wallahi bana san tashin hankali nasan ba komai ne yasa suke nufa ta da mugun abuba saboda abunda ya faru ne tunda dai kai kafi karfinsu to ni bari su huce akaina amma insha Allahu sharrinsu sai ya koma kansu."


Yace." Sumayya ba zan bar wannan al'amarin ba wallahi sai na dauki mataki akan dukkanin wanda yake kokarin ta'ba lafiyarki."

"Ni dai dan Allah ka bar maganar nan tunda dai nace Allah ai maganata ta kare wallahi bana so ta dalilina a sake samun wata matsalar kayi hakuri ka kyalesu da sharrinsu insha Allah zai koma kansu."


Cokalin dake hannunsa ya ajiye ya dauki wayarsa yana dubawa, nace"Ya kuma ka ajiye cokalin.''? girgixa kai yayi yace."Ba zan iya cin wani abu ba." .


Nace"Wannan dalilin ne yasa fa nayi shuru da bakina saboda nasan baka daukar abu da sauki gashi kana cin abinci ka ajiye............Kallona yayi yay murmushi wanda ya tsaya iyakacin l'ebanshi yace."Wannan al'amarin ne me sauki a gurin ki ko.''? kai na girgiza nace"Ba haka nake nufi ina nufin idan muka barwa Allah komai sai kaga yayi mana magani nasan suna so su dauki fansa ne akaina."

Yace.'" A kaina zasu dauki fansa bake da baki da laifi ba." nace"Ai kai kafi karfinsu dole su kyaleka su dauki hukunci akaina a ganinsu nice na janyo aka rataye Muddibo shiyasa suke so su dauki fansa akaina.


Tsaki yaja yace."Basu da hankali gabad'ayansu kin san Allah Sumayya dik wacce tayi miki lahani a cikinsu ba zan kyaleta ba koda kuwa harda hajiya Kariman a cikinsu sai na dauki mataki akansu."


Nace"Naji na kuma gode da kokarin ka amma dan Allah yanzu ka hakura ka bar maganar idan suka sake yunkurin wani akaina nima zan baka goyon baya ka dauki mataki amma dai yanzu kayi hakuri ka bar maganar.


Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki cokalin ya cigaba da cin abincin, lemo na tsiyaya masa a cup na mika masa ya kar'ba ya kur'ba ajiye cup din yayi ya cigaba da cin abincin nace"Amma ba zan 'boye maka cewar naji ciwon abinda kayi ba.


Kallona yayi yana tauna abincin dake bakinsa a tsanake yace."Me nai miki."? nace" Sabida ka shirya tafiya da Lawisa america sai ka 'boye min kasan dai ni ban isa na hanaka abinda kayi ra'ayi ba."


Tissue ya dauka ya goge bakinsa yana kallona yace."Lawisa ta samu labarin kina dauke da ciki hankalinta ya tashi wanda har hakan yasa take zargina akan nafi bukatar haihuwa dake shiyasa bana baki kwayoyi na nuna mata cewa nima karfina kikafi ta'ki aminta da maganata har tana ikirarin kai maganar gurin Maimartaba wannan dalilin yasa na yanke hukuncin tafiya da ita domin na rarrasheta acan."


Girgiza kaina nayi nace"To menene na 'boye min ni shine abinda yafi komai bani haushi sai dazu da naje gaishe da Mamma take fada min a lokacin nuna mata nayi kawai na san maganar dan Allah ka daina irin haka babu dadi."

Yace."To shikkenan tunda kin dauki hakan da wata manufa Allah ya baki hakuri." nace"Ai dole na zargi wani abu tunda naga kamar kana 'boye min.

Hannu ya daga min da fadin"Maganar ta isa haka kin san dai ke baki isa naji tsoronki ba ko? kallonsa nayi ya cigaba da cewa'' Bana munafurci kamar yanda kika zato kawai Allah ne bai nufe ni da na fada miki da wuri ba tunda yanzu kin samu labari magana sai ta wuce."


Mi'kewa nayi na bar masa gurin dan na lura da cewar ba zai fuskanci abinda nake nufi ba idan kuma nace dole sai na ganar dashi shaid'an zai shiga tsakaninmu.

Har nayi bacci bai shigo dakin ba......sai can naji motsinsa na bude idona ina kallonsa ya kashe fitila yazo ya kwanta kusa dani, jin shuru bai ta'bani ba yasa nasha jinin jikina ina tunanin ko yayi zuciya dan nasan halinsa da saurin fushi! ajiyar zuciya na sauke jin ya janyoni jikinsa ya rungumeni sai nasa hannuwana duka biyun na ratsa jikinsa kesses din fuskata ya shigayi kafin ya had'a bakina da nasa ya shiga tsotsar harshena da le'bena had'in kai na bashi sosai muka shiga biyawa junanmu bukata.


Washe gari cikin walwala muka tashi ni dashi sai abin arziki muke tamkar bamu ta'ba samun sa'bani ba, har bakin kofa na rakashi ya kar'bi wayoyinsa dake hannuna cikin kulawa ya rungumeni jikinsa yace."Ki kula da kanki da babyna." murmushi nai nace"Idan kana kiran babynka sai na dinga jin wani irin dadi a raina wallahi har so nake naga na haihu kana kula dashi."


Murmushi yayi yace."Ni kuma kullum da fargaba nake kwana nake tashi ina jin tsoron ranar da naquda zata kamaki ai ina jin kwanciya zanyi sai an k'ara min ruwa."

Dariya na dinga yi ina kallonsa, yace."Sumayya ina jin tausayin masu haihuwa wallahi shiyasa gabadaya bata burgeni." nace"Ka bar wannan maganar dan Allah dik abinda kaga Allah yayi to yana da manufa wuya bata kisa idan kuma na mutu gurin haihuwa aljanna zan shiga dan haka ka daina damuwa."


Yace"To na daina zan cigaba da yi miki addua." Cikin murmushi nace"Nagode rabin rayuwata." girgiza kansa yayi yana kallona tare da kannare idonsa " 'Dan sake maimaitawa naji sunana." yafada yana min wani irin kallo.......Hannunsa na rike tare da fadin"Rabin rayuwar Sumayya." yasa dariya tare da girgiza kai yace." Wani lokacin idan kina wani abu har mamaki kike bani! duk wannan soyayyar da kike nuna min anjima ba zata hanaki kiyi min rashin kunya ba.


Nace" Allah ya tsarani na raina ka kaifa mijina ne wallahi duk wani abu daka ga inayi maka a kan gaskiya ne, gashi dai mun dade a tare amma ka kasa gane halina."

Agogon hannunsa ya duba yace."Ni zan fadawa kowa halinki sumayya kina da kirki sosai amma baki yarda da zalinci ba kina da amana uwa uba addini bakya wasa da ibadah ke d'in 'yar baiwa ce ina kuma alfahari da samunki a matsayin matar aurena."

Sosai naji dadin yanda yake yabona rungumeshi nayi nace"nagode rabin raina naji dadi daka fahimci wacece ni ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a tsakaninmu Allah ya baka ikon adalci tsakanin matanka."

Ya amsa da ''ameen my love yau dai kinsa na makara dubi time." da sauri na duba agogon hannunsa takwas da rabi nace" Gaskiya nayi laifi nasan jama'a nacan na jiranka idan kaje kace su yafe min.'' yana kokarin fita yace." Gurin Lawisa zaki nemi afuwa dan kin cinye mata lokacinta a yanzu dai ba zan samu damar shiga gurinta ba sai na dawo." hannu na daga

Please Login or Register in order to submit comment