Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kara dukan"!!

Muddibo shuru yayi kansa na kallon kasa sai zare ido yake, Acp ya kalli su Soloman dake tsaye suna jiran umarni yace."Ku cigaba da aikinku ina ganin dukan be isheshi ba.!


Muddibo ya razana a firgice! ya daga hannuwa sama jikinsa na rawa yace.'' Kada ku dake ni zanyi bayani." Acp ya kalleshi tare da fadin "ka tabbata."? kansa ya daga hawayen nadama na zubo masa

Mikewa yayi ya kallesu cikin bada umarni yace." Ku kawo shi ofis." yana gama maganarsa ya fice.


A rirrike aka shiga dashi ofis din dan gabad'aya jikinsa ya saki bashi da karfi da kuzari ko kwabo tsabar duka da tashin hankali yasa duk kammaninsa suka sauya......Ali da Shatima suka dinga kallonsa ganin yanda duk kammaninsa ya sauya.


Acp zama yayi a kujerar dake fuskantarsa, sai da ya tabbatar da cewa ya dan samu nutsuwa tukkuna yace."Muddibo kai muke saurare." Ofis din ya dauki shuru na 'yan mintina kafin Muddibo ya fara magana cikin rawar murya yake musu bayanin abinda ya dinga faruwa a masarautar shine mussababi dan dukkanin mace-macen da akayi shine sanadi duk yana aikata hakane dan bukatarsa ta biya akan d'an uwan nasa.

Magajin sarki idanunsa sukayi jajawur! ya zubawa Muddibo ido yana mamakin al'amarin! shi kuwa Shatima sam bai damu ba saboda dama shi can yasan shine silar faruwar dukkaanin abinda yake faruwa.

Acp kansa na kasa yana rubutu a kan wata doguwar takarda, ya kai minti goma yana rubuce rubuce a takardar kafin ya dago kansa, yace."Muddibo da kuma ka musanta zargin da ake maka ko zaka iya fada mana dalili."?


Cikin nadama yace."Dole na musanta domin na kare kaina amma yanzu dana fahimci cewa asirina ya tonu ai gashi nan nayi maka bayani yanda ya kamata." Acp murmushi yayi ya cigaba da rubutunsa, bayan ya gama rubutun sai yayi magana da karfi tare da kiran Soloman, da sauri suka shigo. yace."Ku mayar dashi.'' da sauri suka nufeshi, suka mikar dashi tsaye, rirrikeshi sukayi zasu fita ya juyo yana kallon 'yan uwansa hawaye ne suka gangaro masa shikkenan kuma yasan tasa ta k'are a duniya yazo a banza zai koma a wofi!


Acp ya nannad'e takardar hannunsa cikin nutsuwa yace."Ranka ya dad'e mu nan mun gama aikinmu insha Allahu ranar litinin mai zuwa zamu tura shi kuto domin al'kali ya yanke masa hukunci muna rokon Allah ya
kiyaye gaba Allah ya tsare gabanka da bayanka dukkanin wani mai nufin ka da sharri muna rokon ubangiji Allah ya mayar dashi a kansa."


Magajin sarki ya sauke ajiyar zuciya tare da bashi a hannu cikin mutunci yace." Acp nagode kwarai da gaske kaima ina rokon Allah ya daukaka akan aikinka Allah kuma ya kareka da dukkanin abin'ki." Acp na murmushi ya amsa da ameeen." Ya mikawa Shatima hannu sukayi sallama da juna, har bakin mota ya kai su bai kuma bar gurin ba sai da ya tabbatar da cewa motocinsu sun fita daga station din cikin k'oshin lafiya........



*Na kudi ne..!*
Kada ki karanta min littafi idan baki biya baa, keda kika futa da book din keda Allah, idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip group #600 normal gruop#300....account... 0542382124...Binta umar gtbank... idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
88
Yini nayi a kwance ina baccin gajiya sai daf da la'asar daya shigo Mamma ke sheda masa cewa tun bayan fitarsa nake bacci ban tashi ba kai tsaye dakin ya shiga, ya sameta kudindine a cikin bargo tana bacci ya jima a tsaye a kanta yana kallonta tausayinta na ratsa masa jiki, a hankali ya zauna gefan gadon yasa hannu ya janye bargon data rufa dashi, tafin kafarta ya shiga shafawa yana kiran sunanta a hankali, cikin bacci naji tsigar jikina na tashi yayin da kafata ta dama keyi min kaikayi janye kafar nayi ina sake jan bargon, ya janyo ni da sauri yana kirana, da sauri na bude idona, nan na ganshi dab dani a zaune! da sauri na mike zaune ina gyara bargon jikina cikin dubara na gyara zanina daya tattare daga ciki.........Kallona yayi cikin sassauci yace."My lov ashe tunda na fita bacci kike baki tashi ba bare kici abinci kisha magani." Kaina na daga masa ba tare da nace masa komai ba, yace."Okey to yanzu ya kike jin yanayin jikin naki."? A hankali nace "Da sauki kaina ne kawai yake min ciwo.'' yace." Shima zai daina insha Allahu, kije maza kiyi brush sai kizo kici abinci ko."?
A hankali na mi'ke ya rike hannuna da fad'in"Ko na taimaka miki ne? girgiza kaina nayi tare da kwace hannuna nayi gaba da sauri, to har na fito daga toilet din yana zaune a dakin, kai tsaye hijabi na duba cikin kayan dazu nasa a jikina na tsaya a kan dadduma domin gabatar da sallah, mikewa yayi ya fita daga dakin, ganin uku da rabi tayi yasa kawai na gabatar da sallahr la'asar na jima kan daddumar ina addua kafin na shafa a fuskata na mike a nutse da hijabin a jikina na fita daga dakin

Babu kowa a katon falon sai jakadiya tana 'yan gyare-gyare gaisawa mukayi tace"Ranki ya dade ai yau kinsha bacci sosai da sosai." cikin mamaki nake kallonta jin irin sunan data kira ni dashi, mirmushi tayi tace"Ga abinci can a shirye idan kina bukata sai na kawo miki inda kike."

Girgiza kaina kawai nayi ina kallonta nace"Ina Mamma."? da sauri tace"Ta shiga ciki domin tayi sallah."

Shuru nayi ina kallon kasan gurin lallai zama da mad'aukin kanwa guy nan ya koya min sara bini bini sai kawai na kurawa kasa ido sai kace me neman wani abu nazari da tunani ne idan Sukayi wa mutum yawa yake sanyawa ma kayi abu baka san kanayi ba shi dai al'amarin ya zame masa jiki magana daya biyu zai yi k'asa da kansa ya jima yana nisawa.


Muryarta naji ta doki kunnena."Ranki ya dade a tashi lafiya." da sauri nace"Jakadiya ki daina kirana da wannan suna yayi nauyi da yawa."

Murmushi tayi tace."Beyi nauyi ba ranki ya dade ya dace dake domin kin cancanta lokaci kadan zaki zama matar Yarima mai jiran gado kinga kuwa ai sunan daya dace a kira ki dashi kenan."

Shiru kawai nayi ina binta da kallo, tayi murmushi a nutse ta juya naga ta shige wani daki dake can k'urya nafi tunanin dakinta ne dan ganin yanda take shige da fice a dakin.


Falon na shiga bi da kallo ko ina tsaf tsaf dashi sai kamshi yake iri-iri gabadaya ma na kasa bambamce kamshin da falon yake komai ya tsaru kayan al'ada iri iri a falon ban ta'ba tsammanin akwai ranar da zata zo na zauna a kan kujerar falon ba sai gashi cikin ikon Allah yau nice a hakimce a kan kujera cikin shigar suttura irin ta sarauta har da alkawarin aure a tsakanina da dan sarki! a gaskiya babu abinda yafi gaskiya da rikon amana dadi a duniya gaskiyata da rikon amanata sun janyo min alkairi na zama abin kallo abin mutuntawa da ganin daraja na tashi daga baiwa na dawo mai 'yanci! hummm! rayuwa kenan idan Allah ya kaddara aurena da Yarima a matsayina na baiwa yar gidan Lawi mai hidima da dawakai watarana ina iya haifar sarki! kadan daga cikin ikon Allah kenan! ajiyar zuciya na sauke mai zafin gaske nasa hannu ina share hawaye dake zubowa a kumatuna.......shigowarsa yasa nayi gaggawar sunkuyar da kaina kasa ina dubarar goge fuskata, kusa dani ya zauna yana nani'kata kujerar kuma mai cin mutun daya ce dik ya takure ni.


Kasa dago kaina nayi na kalleshi saboda damuwa, idan da sabo yaci ace na saba da halayyarsa.


Hannu yasa ya dago fuskata ya tsira min ido lokaci guda ya karancin yanayin da take ciki.....cikin tausasawa yace." Me akayi miku kike kuka?
Kallonsa nayi ina kokarin bagarar da maganarsa nace"Wane irin kuka kuma yanayin bacci ne kawai a idona."


"Kada ki raina min hankali mana na shigo na sameki kina goge hawaye amma ki karyata maganata bana so kiyi zaman takura idan nan beyi miki ba zaki iya komawa sashena ki zauna mutukar hankalin ki zai kwanta."


Cike da mamaki nake kallonsa kafin nace"Na koma sashen ka na zauna akan wane dalili? wai kan dan Allah me yasa watarana baka tunani ne."?


'Bata rai yayi yace."Ni ne mara tunani."? girgiza kaina nayi nace"Allah ya baka hakuri ban fad'a maka maganar dan kaji haushi ba abinda ya dace nake so na nusasheka yanzu kawai ba'a daura mana aure ba sai na tare a sashenka me kake tunanin zai faru."?


Shuru yayi yana kallona, na dauke kaina tare da matsawa daga jikinsa, sake matsowa yayi ya matseni a jikin kujera, murya na rawa nace"Dan darajar Allah kayi hakuri ka matsa kada Mamma ta fito ta same mu a haka."

Ya matsa tare da fadin"Tunda kince Allah na matsa shikkenan ko .''? shuru nayi masa, yace."Kinci abincin dai."? kai na girgiza alamun aa. Yace."To tashi muje muci ko."
Mikewa nayi ya mike tare da kokarin rike kuguna da sauri na kauce na bashi guri, mirmushi yayi kawai yayi gaba nabi bayansa ina mamakin shu'umancinsa.

Muna zama gurin cin abincin ta fito daga dakinta jikinta nannad'e da lifaya da carbi madaidaici a hannunta, gani nayi ta saki fuskarta cikin wasa da dariya tace"Ango da amarya ne za suci abinci a tare." da sauri na sunkuyar da kaina kunya duk ta dabaibayeni.......tana kokarin zama gurin zamanta yace."Mamma na shigo na sameta ita kadai a zaune a falo tana share hawaye shine nake tambayarta dalili tace babu komai ni kuma na k'aryata tabbas nasan akwai abinda ke damunta take kuka.


Cikin kulawa tace"Sumayya menene."? kasa cewa komai nayi gabadaya kunyarta nake ji, tace"Ki gama cin abincin kizo ki sheda min abinda ke damunki ni ba surukar ki bace mahaifiyarki ce." Nace"Mamma babu komai wallahi kin san na yini ina bacci shine dalilin da yasa fuskata ta sauya.

Da sauri yace."Karya kike yi." shuru nayi tare da sunkuyar da kaina dan gabadaya bana san jayayya dashi.


Tace."Ki gama cin abincin Jakadiya ta rakaki gurun iyayenki ku gaisa." wani irin sanyi ne naji ya ratsa zuciyata, yace."Mamma ni zan rakata." Tace"To hakan ma yafi ma'ana sai ku gaisa sosai ka k'ara sheda musu abinda keda akwai duk da nasan maimartaba ya shedawa mahaifinta abinda yake faruwa a tsakaninku."


Yace."Babu damuwa insha Allahu zanyi musu bayani sosai wanda zai gamsar dasu nasan kuma zasuyi farin cikin da faruwar al'amarin."


Cikin farin ciki nake cin abincin na saki jikina sosai muna hira dashi, Mamma dake can falo tana jinmu idan ya kama tasa baki a hirar tamu tasa bakinta ayi da ita, cikin fahintar juna muka kammala cin abincin yace."To maza dauko maganinki a daki." da sauri na mike naje na dauko maganin, kar'ba yayi ya fito dasu ya dinga bani daya bayan daya, sai da ya tabbatar nasha kowanne sannan ya umarce ni dana mayar da ledar maganin daki, ina ajiyewa na fito na sameshi a tsaye suna magana da mahaifiyarsa magana ce dai akan abinda ya faru yana fada mata cewa Muddibon ya fadi gaskiyar lamari yayi rocoding din komai so yake Maimartaba ya shigo da daddare sai ya kunna musu su saurara."

Kaina a kasa nazo na wuce bakin kofa na nufa, ya biyo bayana, Mamma naji na fadin"Sumayya ki gaishe min da iyayen naki."

Da sauri na juyo cikin ladabi nace"Insha Allahu zasuji." Nice na fara fita kafinsa, gabad'aya naga ana bani girma yanda ake gaisheshi cikin mutunci da daraja nima hake ake gaisheni, na dinga takure jikina cikin hijabi ina mamakin ikon Allah!

Har muka isa gurinmu a takure nake saboda ganin yanda jamaa ke bin mu da kallo gami da girmamani!

Hayaniyar mata na dinga ji a cikin gidan namu. kallonsa nayi shima ya kalleni, nace"Ko zaka tsaya na shiga na sheda masu zuwanka."? yace."Duk yanda kika ce haka za'ayi ranki ya dade.''

Cike da mamaki nake kallonsa jin irin sunan daya kira ni dashi.

Yace."Meye kike kallona."? girgiza kaina nayi da mirmushi a fuskata na wuce cikin gidan, Tawagar mata na gani gurfane gaban Tambaya sai fadanci suke mata saboda abun al'karin daya sameta.....ina shiga Uwani ta mi'ke da sauri ta rangwad'a bud'a! da fad'in "Ga amaryar nan ma tazo." Gabad'ayansu suka mike tsaye Tambaya sai mirmushi take tana kallona! nima da murmushin a fuskata na shiga gaisawa dasu, suka dinga amsawa suna yi min fatan alkairi." Nace"Ku nutsu tare muke da Yarima yana waje a tsaye hayaniyar ku tasa ya tsaya." Gabad'ayansu suka shiga nutsuwarsu kowacce tasa takalminta domin tafiya.....Tambaya tace"Sumayya maza jeki shigo dashi, kin barshi a tsaye." nace"To." Tawagar matan dake gidan suka biyo bayana, ganinsa a tsaye yasa suka zube kowacce gwiwa a kasa take gaisheshi, na dinga mamakin yanda yake amsa musu a sake yace."Gabad'ayansu su tashi su tafi. da sauri suka mike suka wuce, sai da gurin ya samu nutsuwa tukkuna na kalleshi a sanyaye nace"Ka shigo amma Babana baya nan sai Tambaya kad'ai zanje na kira shi yanzu."


Girgiza kansa yayi yace."Ki bari kawai idan na gaisa da mamanki sai munje can gurin aikin baban mu gaisa." nace"Ka bari dai na kira maka shi." Dan 'bata fuska yayi yace."Haka zaki tafi babu sucurity kina so makiya su ritsa ki ko."?

'Babu abinda zai same ni sai ikon Allah." girgiza kansa yayi yace."Ban yarda ba tare zamuje kome zai faru ya same mu a tare.'' wani irin kallo nake masa shima yana yi min nasa da yake mutukar kassara ni. a sanyaye nace"To muje ku gaisa da Tambayan." da hannu ya nuna min hanya ma'ana nayi gaba, bayana ya biyo muka shiga.


Sosai nayi mamakin yanda ya zube gaban mahaifiyata yana gaisheta ita kanta Tambaya sai da abun ya bata mamaki ta dinga jin kunya da nauyi tana kauda kanta da barin kallonsa, addua kawai take mana tare da fatan alkairi a rayuwar auran da zamuyi, ya dinga amsawa cikin kulawa yana sake yi mata karin bayani akan al'amarin, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa ina mamakin sauyawarsa a kaina, lokaci guda na dinga jin wani irin masifaffan sonsa na ratsa ni yanda yake mutunta iyayena yafi komai dadi a gurina.



Lawi yana tsaka da hidima da dawakai muka shiga gurin, da sauri ya cire hular malafar dake kansa sabida girmamawa, yana kokarin zubewa a kasa kawai yaga Yariman ya zube masa, jiki a sanye yace."Ranka ya dade tashi dan Allah bancanci wannan gaisuwar ba."

Mirmushi yayi ya kalleshi da kulawa yace."Ka cancanci irinta tunda har ka haifa min matar rufin asiri." Lawi yaji hawaye na nema ya kufce masa! hannuwansa ya had'e guri guda yace "Godiya nake ranka ya dade."


Cikin kulawa yace."Baba babu kalmar godiya a tsakanina daku dan haka ku daina akan Sumayya babu irin abinda ba zanyi ba, wannan yarinya jigoce a rayuwata nagode kwarai da irin tarbiyar da kuka bata"

Lawi cikin farin ciki da alfahari ya d'ora hannunsa a saman kaina "Ubangiji Allah yayi miki albarka yarinyar arziki hakika haihuwarki babbar nasara ce a tare damu." hannuna na dora a kan nasa nace"Baba nima ina alfahari daku da kasantuwar ku a matsayin iyayena ko wane mataki na kai rayuwata kune sanadi kun kula dani kun tarbiyantar dani kun d'ora ni akan tur'ba mai kyau kun d'ora ni a kan hanya madaidaiciya babu abinda yake tsakanina daku a yanzu sai kyakkyawar addua ina rokon Allah yaja da ranku ya kuma kara muku lafiya mai amfani."


Ya amsa da ameeen suma ameeen Yarinyar arziki Allah yasa albarka a rayuwarki da rayuwar auranki." ya kalli Yarima dake tsaye yana kallonmu yace."Ranka ya dade naji dadi kuma nayi alfahari dacewar zaka auri jinina a gaskiya nayi farin ciki kuma nayi addua sosai ina rokon ubangiji Allah ya sanya muku alkairi a zamantakewar auranku Allah ya kade fitina yasa anyi kenan ya kareku ga dukkanin sharrin abin'ki."

Yarima cikin jin dadi ya dinga amsawa da ameeen ya Allah baba muna godiya sosai da sosai............Zuciyata tayi wasai! na dinga jin nutsuwa na ratsa jikina hakika yanzu na amince da cewa Yarima na sona tsakani da Allah yanda yake karrama iyayena yake mutuntasu yasa naji duk duniya bani da masoyi kamarsa ina mutukar kaunar iyayena shiyasa duk wanda ke mutuntasu nake ganin darajarsa Yanzu Yarima Ali ya samu kyakkyawan matsayi a cikin zuciyata Allah ne kad'ai yasan irin kaunar da nake masa.


A dakin taro kowa ya hallara iyaye da 'ya'ya da jikokin masarautar kowa yana gurin, Magajin sarki ya fito da wayarsa a nitse ya kunna rocoding din muryar Muddibo ta fito rad'au!! vollom ya karo yanda kowa zaiji da kyau!! kowa ya shiru yana sauraran Muddibo yana jawabi akan abubuwan da ya dinga shiryawa a masarautar........Famliy din Ciroma suka cika gurin da kuka Hajiya Karima kasa tsayawa tayi ta gama saurara tana kuka na tashin hankali ta bar gurin, da daya bayan daya 'ya'yanta suka bi bayanta, Ciroma yana zaune a gurin bai tashi ba har sai da recoding din ya 'kare! Magajin sarki ya kashe wayarsa ya ajiye kusa dashi, a nitse ya sheda musu cewa"Ranar litinin za'a shiga kuto dashi domin al'kali ya yanke masa hukuncin daya dace dashi dan haka dik wanda yaga yana da ra'ayin zuwa sai ya shirya yaje." babu wanda ya nuna sha'awar zuwa a cikinsu Iyalin Uwar gida Huwaila irinsu aunty Safiyya suka dinga zare ido a gurin gaskiya sunji dadi sosai da Muddibo ya rufa musu asiri suma sunyi nasu sai dai kuma bai ka nasa muni ba!! Maimartaba yace kowa ya tafi gurinsa tunda gaskiya tayi halinta sai a jira hukuncin da al'kali zai yanke a kansa, jiki a sanyaye kowa ya fita daga gurin taron..........Ciroma na daf da shiga sashen sa ya yanke jiki ya fad'i!! Hadiman dake aikace aikace a gurin suka rufu a kansa suna ihu!!!! kafin kice kwabo tawagar 'ya'yansa dake cikin gidan sun fito, mazan ne suka daukeshi suka shiga dashi ciki dakinsa suka shiga dashi su kwantar dashi a gado sun kewaye shi suna yi masa firfita! Ciroma bakinsa ya murgud'e sai zubar da yawu yake! magana yake so yayi amma ya kasa, Hankalin iyalinsa ya tashi, Wali shine me bin Muddibo da sauri yace."Bari naje na kira Magajin sarki yazo ya dubashi." Hajiya Karima cikin tsawa! Tace."Wali ka sake ka kira Magajin sarki ya shigo sashen nan sai na d'aga maka nono wallahi sai na tsine maka albarka."!!! Khalisat tace."To Yanzu hajiya muna ji muna gani zamu barshi ya mutu i duba da ki ga yanda yake haki! jininsa ne ya hau da karfi."
Cikin karaji!! Lawisa tace"Khalisat ba za'a kira Yarima ba ai bashi kad'ai ne likita a duniya ba! saboda haka kawai kai Wali ku daukeshi kusa a mota mu nufi babban asibiti a dubashi." Wali yace." me zai hana a kira Dr Sa'adu ya dubashi a gida."?
Hajiya karima tace"Aa shawarar Lawisa zamu dauka ku daukeshi kusa a mota muje babban asibiti." Manniru yayi saurin fita domin bada umarnin fito da mota...





*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya! keda kika futa da book din keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300....account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKAWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
89
Sai bayan fitarsu daga gidan tukkuna Maimartaba ya samu labarin abinda ke faruwa ransa ya 'baci sosai da abinda iyalin d'an uwansa suka zartar ba tare da saninsa ba, ace akwai babban likita a gida amma su daukeshi su kaishi wani asibiti domin su nunawa duniya halin da suke ciki, sosai ya dinga jajanta al'amarin a cikin zuciyarsa, Waziri ganin yanda ya damu da a'lamarin yasa ya dinga tausar sa da kalamai masu sanyi Sarki ya dan samu sassauci a zuciyarsa sakamakon rarrashinsa da 'yan uwansa ke masa amma dai duk da haka zuciyarsa na can tunanin halin da Ciroma yake ciki dalilin da yasa kenan gari na waye wa suka shirya zuwa asibitin domin duba jikin nasa.

Yanda suka tarar dashi cikin halin ciwo ya firgitasu dan gabadaya komai na jikin Ciroma ya daina aiki yana kwance sai dai ayi masa komai, Likitan dake tsaye a kansa ya sheda musu ciwar jininsa ne ya hau sosai sanadiyar tashin hankalin daya shiga amma insha Allah zai cigaba da kwanciya a asibiti su kuma zasu cigaba da kula dashi har ya samu lafiya."

Maimartaba girgiza kansa kawai yayi yana mamakin kudirar ubangiji Tabbas ya yarda da cewa d'an adam ba'a bakin komai yake ba duba dai lafiya lau suka yini da Ciroma amma lokaci guda Allah ya sauya masa hallita, babu shakka idan suka rasa dan uwansu ta sanadiyar bacin ran Muddibo ba zasu yafe masa ba........Umartar Wali yayi akan ya kira Magajin sarki a waya ya sheda masa cewa ya turo motar asibitinsa tazo ta dauki Ciroman yana ganin kamar haka yafi mutunci.


Hajiya Karima ita da zuriar ta babu yanda suka iya suna ji suna gani Magajin sarki ya turo da mota a kasa Mara lafiyan a ciki a ka tafi dashi asibitin, Tsabar bacin rai yasa hajiya Karima buge zaninta ta koma gida tare da fadin"Ba zata zauna zaman jinya ba mutukar ba sanja wa mijinta asibiti ba.

Maimartaba yace kowa ya kyaleta! dama asibitin basa bukatar 'yan jinya akwai ma'aikatan da suka san aikinsu sai kawai ya basu umarnin tafiya gida bayan ya kwantar musu da hankali akan rashin lafiyar mahaifin nasu............Koda suka koma cikin tsananin damuwa suka samu mahaifiyar tasu sai zubar da hawaye take, Lawisa da khalisat suka zauna suna taya ta kukan. abun duniya ya taru yayi musu yawa Muddibo ya jefa su a cikin tsaka mai wuya ga rayuwar mahaifinsu na tangal tangal.....Hajiya karima hawayenta ta share ta kalli 'ya'yanta cikin rawar murya tace"Yanzu haka zaku zauna ku zuba min ido ina kuka kuna kuka ba zamu zauna mu nemawa kanmu mafita ba."


Wali yace."Hajiya wace irin mafita kike so mu nemawa kanmu? duk fa abinda kika ga ya faru to da sanin Allah saboda haka dan ki kada kice zaki dauki fansa saboda nasan halinki da ri'ko! Muddibo shine ya janyowa kansa masifa muma gashinan ya jefa mu a cikinta a yau da kwanan mahaifinmu ya kare da tuni sai dai labari."


A harkuqe! tace"Dallah malami rufe min baki mai matacciyar zuciya! ayiwa dan uwanka sharri amma ka dinga cewa shine ya janyowa kansa wato kana nufin kaima ka yarda da sharrin da'aka liqa masa."

Cike da mamaki! yake kallonta kafin yace."Hajiya dan Allah ki nutsu ki shiga hankali ki daina wannan abinda kikeyi mutane zasu dauka kin samu ta'bin hankali! wannan fa al'amarin da

Please Login or Register in order to submit comment