Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abinda zai sha.
Sake zage damtse nayi akansa sai ya zamana kullum tsakanina dashi sai munyi fad'a yayi ta yi min tsawa yana marina ina daurewa duk rintsi bana barinsa yaci ko yasha abinda bai gamsar dani ba.......
*BINTA UMAR ABBALE*



*Na kudi ne*
Idan kina bukatar biya #300 ne 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 kiyi min mgn ta wsp da wannan number 07084653262 ga me bukatar ViP gruop #600
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
45&46
Cikin tsabar takaici da b'acin rai ya fito daga toilet din ya same ni a tsaye. kasa kallonsa nayi saboda ina gudun na fad'a masa maganar da zata dunguzuma masa zuciya, a yanda nake jin raina a bace kowace irin magana ina iya fad'a masa dalilin da yasa kenan na sunkuyar da kaina kasa ina cigaba da sha'kar takaici da 'bakin ciki.
"Munyi waya da Muddibo yanzu ya sheda min cewa yazo ina bacci ya kawo min apple so kizo ki bani ita kad'ai nake muradi a yanzu.''

Kallonsa nayi gabana na fad'uwa yana zaune a gefan gado yake wannan maganar gashi ya kafe ni da manyan idanunsa......kasa cewa komai nayi domin nasan sai mun haura dashi akan hakan dalilin da yasa kenan nayi shuru ina tunanin abunda zan fad'a masa.


" Ko bakya ji ne.''!? yafada a d'an hasale! a jajurce nace "Lokacin dana duba apple d'in sai naga ta lalace shine na zubar da ita." Gani nayi ya kura min ido ransa a 'bace yace."Wato ke ba zaki daina yi min katsalandan acikin al'amurana ba ko? shin ina ruwan ki da abinda d'an uwana ya kawo min, yau ko tsutsa apple din ke fitarwa baki da hurumin da zaki zubar min har sai na tashi a bacci na gani to saboda haka kije ki d'auko a duk inda kikaje kika zubar ko kuma wallahi na 'bata miki ranki.''


"Ranka ya dad'e kada fa ka manta kai amana ne a gurina ya za'ayi na barka kaci abinda zai cutar da kai wallahi apple din bata da kyau shiyasa na zubar kuma meye amfanin na bar abinda zai tayar maka da hankali idan ka ganshi ka gafarce ni ranka ya dad'e."


Mi'kewa naga yayi ya durfafoni fuskar nan a murtuke! da har na tsorata sai kuma wata zuciyarta tace''Ki dake ki daina yawan tsoronsa sai ya raina ki. tsayawa nayi ina kallonsa har ya karaso inda nake tsaye, kawai yasa kirjinsa yayi baya dani saura kiris na fadi k'asa bayana ya jingina da bango(garu) sai muka shiga kallon kallo dashi, kasa jimirin kallonsa nayi na lura akwai wani sirri a cikin kwayar idanunsa gabad'aya jikina ne yake naman mutuwa jin kirjinsa ya danne nawa.

"Zaki d'auko min apple dina ko sai nayi miki Zigidir a d'akin nan wallahi bani da mutunci zan iya tu'be miki kaya na tozartaki." Gabana ya dinga bugawa na kalleshi inaso nayi magana, amma na rasa abinda zance jajayen idanunsa da ya zuba min sun kassara ga'bban kijina.

Mun jima a haka yana danne da kirjina ina fitar da numfashi da kyar kafin wani karfi yazo min na tunkud'eshi da karfi hanyar futa na nufa da sauri ya ri'ko hannuna na riqe kofar dakin da karfin gaske! da karfi ya jani sai gani a jikinsa, fad'uwa mukayi tsakiyar dakin na ganni kwance a saman kirjinsa, a zafafe na mike tsaye na sake nufar hanyar fita, kafarsa yasa min na fadi a gurin... kafin nayi wani yunkuri ya danne ni kauda kaina na dinga yi jin hucin numfashinsa na dukan fuskata

Cikin rawar murya nace"Ka d'aga ni kada wani ya shigo ya same mu a haka." Banza yay min ya cigaba da bin fuskata da kallo. rai a bace nace"Ranka ya dade ka tashi a kaina kada zuciyata ta tunzurani nayi maka abinda bai dace ba.

A sar'ke naji yace''Duk abinda kike ganin zakiyi kiyi." Hanci na sha'ka! rai a mugun 'bace na dunga tureshi ina kici kici zame jikina, Sake matse ni yake yana danne ni! hawayen bakin ciki suka zubo min yawun bakina na tattaro na fesa masa a fuska. ina kuka nace"Allah ya isa mugu azzalimi."

Babu walwala a tare dashi yace."Ni kika tofawa kazamin yawun ki? ni kike wa Allah ya isa."? Kauda kaina nayi ina jan tsaki tare da dukan kirjinsa.

Fuskata naga yana bi da kallo duk inda nayi da ita sai ya bini da tashi fuskar, kokarin had'a bakina yake dana shi ina kaucewa amma sai da ya samu nasara yasa bakinsa a nawa duk turje turjen da nake ina gumtse bakina sai da ya samu nasara ya dinga tsotsar min le'buna yana cizona.
Hawaye nake ina dirka masa duka a bayansa ko gezau beyi ba sai da yasha bakina iya son ranshi ya zare bakinsa, ido jawur yake kallona, kunya da tsanarsa suka sa na kasa hada ido dashi.
Sauka yay daga kaina na mike zaune ina gyara rigata.

"Wallahi Allah sai ya saka min abinda kayi min kuma daga yau na daina kula da kai zan samu wacce ta turo ni na sheda mata cewa farautata kake yi kaga daga nan shikkenan ma'kiyanka sai su samu nasara a kanka."

Ina gama maganata na miqe da niyar barin gurin, hannuna ya riqe na kalleshi ina goge fuska, yace."Mutukar kika fadawa mahaifiyata ina farautarki to wallahi daga ke har iyayenki kun daina shan ruwa a masarautar nan sai kun fuskanci hukunci mai tsauri daga gurina, kawai ki bani jikinki na mora shine kikewa bakin ciki da ganin k'yashi waye zai gani waye zai san abunda ke faruwa a tsakanina dake 'yar kauye irinki na nuna ina sha'awarki ki tsaya kina min yanga okey kiyi gangancin fad'awa iyayena wannan maganar kiga irin hukuncin da zai biyo baya."


Jikina ne yayi sanyi jin furucinsa sai na tuno da nasihar mahaifina kullum sai ya umarce ni akan bin umarnin masarauta Yarima Ali ya nuna min cewa shi d'an sharri ne zai iya shirya min wani sharrin reshe ya juye da mujiya ni da iyayena mu muzanta a masarauta wannan tunanin da nayi yasa gabadaya naji gwiwata tayi sanyi da hukuncin da nayi aniyar dauka a kansa.

"Muje inda kika zubar min da apple ki dauko min kayata. maganarsa ce ta dawo dani tunanina, cikin rashin mafita nayi hanyar fita ya biyo bayana.


Sai dana isa gurin da kamar minti biyar ya karaso kwata-kwata yanayin tafiya ta da tashi ba daya bane ni ina da zafin nama yanayin girman jikina bai hanani kazar-kazar ba dalilin da yasa kenan da nasa hannu a aiki nake saurin gamawa

Karasowa yayi yana bin gurin da wani irin kallon k'yank'yami! sandar dana tona sharar dazu yanzu ma ita na dauka na fara yunkurin tona sharar domin dauka masa tsiyarsa......Hannu yasa ya kar'be sandar ya jefar da ita can nesa, babu fara'a a tare dashi yace." Hannu zaki sa ki dauko.'' Na dinga kallonsa ina jin takaicin abinda yake min.

kasa sa hannuna nayi dan nima k'yank'yami ne dani sai kawai na sunkuyar da kaina zuciyata kamar ta tsage saboda bakin ciki......"Ke! kin barni a tsaye rana na dukana ga kud'aje na bin jikina, kisa hannu ki dauko min apple dina ko kuma naci mutuncin ki anan gurin.

Cikin takaici nace"Ai da zan sa apple din ba hannuna nasa na tona sharar ba sanda nasa kuma ka jefar da ita." Babu ruwana da sanda kika sa yanzu hannu zaki sa ki dauki min." yafada yana kusantoni. ganin kada mu aikata abu irin na dazu yasa nayi shahadar sa hannuwana a cikin sharar ina tonawa, can na dauko ledar apple din har ta soma jikewa da ruwan k'azanta.....Mika masa nayi da fadin"Gashi.'' Ya kai minti biyu yana kallon ledar apple din ya tsine fuskarsa yayi kafin ya tsartar da yawu ya juya da sauri ya bar gurin.....kasa'ke nayi da ledar a hannuna ina tunanin abinda yake nufi da hakan da yayi.

Hawayen takaici da bakin ciki ne suka shararo min! nasa hannuna ina gogewa wasu na sake zubowa. gaskiya duk inda ake neman mara mutumci guy nan ya kai, ashe dan ya tozartani ya wulakanta ni yasa yace lallai sai nasa hannuna a cikin shara! kuka nake sosai abubuwa sun taro sunyi min yawa gabad'aya ni yanzu tsoro ma yake bani wallahi tunda ya nuna yana sha'awata nake jin fargaba da tsoron abinda zai biyo baya a tsakanimu, yanzu ta wace hanya zan kare kaina daga sharrinsa, shuru nayi ina tunanin karbar shawarar da zuciyata ke bani, zan shiga d'aure masa fuska daidai da 'kwayar zarra ya daina ganin sassauci a tare dani, duk sanda kuma ya sake yunk'urin kai hannunsa jikina to zanyi iyakacin kok'arina na 'kwaci kaina, da wannan tunanin na bar gurin, ina sake karfafawa kaina hukuncin dana yanke.


***
Tsakankanin kwana ki biyu aka kwance masa bandejin dake nannad'e a kansa alhamdullhi aiki yayi kyau dan goshin sa bai nuna wani mummunan tabo ba gurin da yayi rami ya ciko sosai sai abinda ba'a rasa ba, a ranar asibitin cika yay da 'yan uwansa suka kewaye shi kowa na nuna murna da farin cikinsa dangane da samun lafiyarsa, Lawisa na kusa dashi sai kula take dashi tana bashi abubuwan ci da suka kawo masa, gabadaya kasa nutsuwa nayi dan ina jin tsoro kada yaje yaci abinda zai cutar dashi, mikewa nayi a sanyaye na nufi d'akin, har nasa hannuna a jikin kofar sai kuma na cire tsoro nake ji na shiga dakin wani yaci min mutunci, a sanyaye na juya da niyyar komawa na zauna aka bud'e dakin da sauri na juya baya gabana na faduwa, Muddibo ne ya fito daga dakin fuskarsa babu walwala yace.......
*BINTA UMAR ABBALE*



*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account 0542382124..Binta umar gtbank...idan katin zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
49&50
Cikin nutsuwa na 'karasa na sameta inda take zaune, zama nayi kaina a kasa nace"Barka da wannan lokaci ranki ya dade jakadiya tace kina nema na."

A nutse ta gyara zamanta tana kallona cikin kulawa da kwantaccan murmushi a fuskarta tace"Barka kadai Sumayya ina fatan kun dawo gida lafiya." A nutse nace'Lafiya lau ranki ya dade." zamanta ta sake gyara tana kallonta tace." a gaskiya naji dad'in n ganin babana lafiya lau yayi ki'ba ya k'ara kwarjini idan ba'idona ne ke min gizo ba sai nake ganin kamar har haske ya k'ara, gaskiya Sumayya kin iya kiwo kin kula min da babana yanda nake so." Cikin farin ciki da jin dadin kalamanta kalleta nace"Godiya nake ranki ya dade.'' Tace"Ai ke zanyi wa godiya Sumayya dalilin da yasa ma kenan na kira ki domin na nuna miki jin dad'ina akan abinda kikayi min sannan na baki kyautar dana tanadar miki."

Murmushi nayi cikin nuna farin cikina da yabawar dana samu daga gurinta nace"Ranki ya dade sabida Allah nake kula da Yarima badan kyauta ko yawancin wani abu ba duk abinda nake masa saboda Allah nakeyi bayan nan kuma ai ya cancanta a kula dashi a hidimta masa.

Tana murmushi tace"Duk da haka dai Sumayya baki ji bahaushe yana cewa "yaba kyauta tukwici ba." Yar dariya nayi ina kara sunkuyar da kaina kasa....Tace"To kingani dole in nuna miki farin cikina a zahiri sannan nayi miki ihsani dan kiji dadi."

Nace"To godiya nake "Ranki ya dade." Wata madaidaiciyar akwati dake gefanta ta janyo tace"Ki dauki akwatin nan Sumayya duk abinda ke ciki naki ne na baki kiyi ado dashi a ranakun juma'a da sauran muhiman ranaku."

cike da murna da farin ciki na dubi akwatin sai kyalli take tana daukar ido nace"Kai masha Allah ranki ya dade hakika naji dadin wannan kyauta da kikayi min ina rokan Allah ya kare ki daga sharrin masu sharri ranki ya dade Allah yaja zamanin ki ya kara miki lafiya da nisan kwana." Da murmushi a fuskarta ta amsa da ameeen kafin ta d'ora da fadin" Kina iya zuwa ki aje akwatin a gurin ku kije sashen babana ki duba idan yayyunsa sun bar sashen ki fito da dukkanin abinda suka kai masa mutukar naci ne kada ki bar komai ki fito dashi a fitar dashi can waje a zubar."

Da sauri nace"Insha Allah yanzu zan cika umarninki ranki ya dade." Mikewa nayi da akwatin a hannuna nayi mata sallama.....sauri sauri nake tafiya da akwatin a hannuna har na isa sashen mu, ko zama banyi ba na aje akwatin Tambaya tace"Wannan akwatin fa ? kin shigo kina gaggawa ina fata dai lafiya."

Ina kokarin fita nace"Lafiya lau zanje sashen Yarima na dawo sai nazo mu bude akwatin dana ajiye." Ban jirayi amsar ta ba na fita da saurin gaske, gabadaya hankalina ya tashi da jin cewa tun dazu yayyunsa na sashensa, sai na dunga zargin mybe ma sun samu nasara a kansa watakila na shiga na tarar da gawar sa ko kuma na tarar dashi cikin mawuyacin hali, idanuwa na ne suka taru da ruwan hawaye nace"Insha Allah babu abunda ya sameshi." ........koda na shiga falon su Haruna na samu suna aikace aikace! ajiyar zuciya na sauke ina rarraba idanuna a falon, can na hango tarin warmas da kuloli a shirye akan kilishin da yake zama dan hutawa, ba tare da shawarar kowa ba na nufi gurin, ban yarda na zauna masa a kilishi ba gefe na tsuguna na soma binkicen abincin......Motsin saukowar sa yasa nayi gaggawar kallon benan gabana ya yanke ya fadi ganin yanda yasha kunu yana min kallon tuhuma, da sauri na mike daga gurun can gefe na matsa kaina a sunkuye nace barka da fitowa.

ko kallona beyi ba ya zauna a gurin, su Haruna suka karaso suka gaisheshi suka fita, kallona yayi a watse yace."Me kika tsuguna zakiyi min akan abinci ko zaki zuba min guba ne."

Idona na zuba masa ina mamakin maganarsa....Yace."kin tsareni da ido ko nayi 'karya ne."? girgiza kaina nayi ina danne 'bacin raina nace." "Zan duba ne domin na tabbatar da ingancin su." Ya 'kalle ni yana girgixa kai yace."Wato ke ba zaki daina saka kanki a kan abinda be shafeki ba ko."

Kaina a kasa nace"A gafarce ni ranka ya dade." tsaki yaja da fad'in" Ki bud'e ko wanne abinci ki zuba min cokali daya a plate yanda nayiwa kowacce al'kawarin cin abincinta to ba zan sa'ba ba."

Cikin bin umarninsa na tsuguna a nutse na fara budewa kular farko fatan doya ne wanda yaji kifi da da curry sai kamshi yake yi ido na tsira a cikin fatan sai naga kamar curry yay yawa da alama an zuba magani a ciki dan ban yarda dashi ba, kular na matsar gefe......tsawa! ya buga min da fadin"Meye haka zaki bude kuma ki matsar ko ba cewa nayi ki zuba min ba." Yanda ya tsattsare ni da ido yasa da sauri na de'bo fatan cikin cokali nasa a plate din.....Daya kular na bude.......Miyar hanta ce da taji kayan lambu itama sai kamshi take amma kuma ba tayi kyau a ido ba tayi b'aki kamar ba'a sa kayan miya a ciki ba.
Girgiza kaina nayi nace"Ranka ya dade kada ka hada abinci kala kala kaci cikin ka ya b'aci ina ganin kaci guda daya ya isa."

"Ina ruwanki ? cikin ki ko nawa."? abinda ya fada kenan yana tsatstsare ni da ido, cike da takaici na bude kular shinkafar na zuba a plata kana na zuba miyar hantar a gefe.
Kula ta uku na bude farfesun dankalin turawa ne da kifi a ciki sai daya kular dake dauke da supargetti (Taliya) plate na dauka na zuba a nutse na jere su a gabansa." kallonsa nayi ya wani hard'e kafafu nace"Na gama had'awa."
Warmars din ya duba da fadin"Kin bude wannan ne."?
Nace."Ka gama cin wa'innan." bece min komai ba ya gyara zamansa, barin gurun nayi ina jin faduwar gaba tsintar kaina nayi dayi masa adduar kariya daga Allah.

Bisimillah yayi ya fara da plate din fatan doya, ya cinye wanda na zuba masa ya janyo na gabanshi shinkafa ba ta dameshi ba shiyasa ko cokali daya beci ba miyar k'awai ya d"an sha ya ture plate din, na ukun ya janyo yana jin k'arnin kifin dake tashi a miyar zuciyarsa ta tashi, da sauri ya ture plate din, yana kallon gefan da nake, saurin sunkuyar da kaina nayi dan bana son ya gane kallonsa nake....."Zo ki janye kayan nan na gama." Da sauri na mike naje na kwashe plates din dake gabansa.

"Bude min warmars din." Ba tare da nace komai ba na tsuguna na shiga bud'e masa snacks ne duk a ciki suna ta kamshi...."Zuba min a plate." Ya umarce ni, zuba masa nayi na mika masa kusa dashi, gyara zama a nutse yasa hannu ya dauki cake guda daya yasa a bakinsa, yana taunawa yaji radad'i a bakinsa furzar dashi yay a gurin, da sauri nida shi muka bi gurin da kallo, babu komai a cikin cake d'in , na kalleshi da sauri sai naga alamun jini a bakinsa, cikin fad'uwar gaba nace"Ranka ya dad'e meye a bakin ka." ? Hannu yasa da sauri ya shafo jinin yana dubawa! kuka nasa ina kallonsa ina hawaye nace"Kaga abinda nake gudar maka ko.? ni dama nasan sai kaci baragurbin abu.....mikewa yay da sauri ya hau samansa, ina kuka ina dudduba cake din babu alamun komai a cikinsa shar dashi sai kamshi yake, na mike tsaye hankalina duk ya tashi! addua nake yi Allah yasa cake din be shiga cikinsa, dan daka gani guba mai karfi akasa a ciki.
Shawara na yanke a kan nabi bayansa domin ganin halin da yake ciki......Kofar dakin a bude na sameta ba tare da tunanin komai ba na shiga, kakarinsa naji a toilet a guje na shiga toilet din, na ganshi ya rike kirji yana ta kakari babu abinda ke fita, k'asan gurin na kalla naga jini d'is-d'is yana diga.

Hawayen nadama suka wanke min fuska Yanzu da wane ido zan kalli mahaifiyarsa data gama yabo na, me zan fad'a mata? bayan ta bani umarnin fitar da kayan abincin daga sashensa gashi na barshi yaci abinda ya cutar dashi, bani da bakin magana! dana sani da nadama suka baibaye ni, dana sani na bar shi ya dake ni ya mare ni nabi umarnin mahaifiyarsa na hana shi cin abincin......Sheshshakar kukanta ne ya ishe shi ido jawur ya dago yana kallonta sai yaga ta d'ora hannuwanta duk biyu a kanta tana zubar da hawaye.

Tausayi ta bashi! ya dafa bango(Garu) ya mike tsaye. da sauri na kalleshi nace"Sannu ina fatan babu inda ke maka ciwo ? bai kalle ni ba yazo zai wuce hanya na bashi ya fita nabi bayansa, samunsa nayi kasan kafet yana maida numfashi.

Gabansa na tsuguna ina kallonsa idanuwansa sunyi jaja wuyar, a sanyaye na sake yi masa sannu ina tambayarsa abinda ke damunsa.''' Kallona yay yace."Babu abinda ke damuna ki daina damunki kanki." Nace" To Alhamdullhi dama haka nake so naji dan Allah ranka ya dade ka dinga yarda da maganata dik abinda kaga inayi a kanka da umarnin mahaifiyarka nake yi ina fatan yanzu zaka gane gaskiyar maganata."
Hannu ya daga min da fad'in "Kije kawai bana san dogon surutu." A sanyaye na mike na kama hanyar fita daga dakin banji dadin gwasale ni da yayi ba..

Bayan fitar ta daga dakin mamaki sosai ya shiga yi akan abinda ya faru! to me hakan ke nufi? ashe dai duk tsayayyar da yarinyar nan takeyi da gaskiyarta 'Yan uwansa na jini zasu kasheshi!? wai shin ma snacks din da yaci na wacece a cikinsu.? bashi da mai bashi amsa, ajiyar zuciya ya sauke ya jingina bayanshi jikin gado har yanzu yana jin zafi a mak'ogwaron sa, yana jin kamar an tsatstsaga masa da reza, pridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi wai ko ya samu sa'ida yana sa ruwan a bakinsa yaji radadi da zugi a mak'ogwaronsa da kyar ya iya had'iye ruwan ya ajiye goran ruwan a kusa dashi yana mamakin al'amarin.


Cikin sauri na fitar da kayan abincin na lodasu a cikin wani buhu mai zurfi dan har kulolin na hada ina ganin suma barinsu had'ari ne d'aure bakin buhun nayi na umarci Hamza da ya dauka ya fita buhun, oma nasa sosai na wanke hannuna kana na koma ciki.

Samunsa nayi tsakiyar falon yana safa da marwa, nace"Kana bukatar wani abune." ? "Kije ki kira min Haruna." yafada yayin da yake kokarin zama kan kujera da sauri nace to na juya na fita.

Tare muka shigo da Haruna yace."Ranka ya dade gani." Da kyar naga yayi maganar." Ungo jeka pharmacy (gurin seda magani) ka kar'bo min wannan maganin." Haruna ya 'karasa kusa dashi da sauri ya kar'bi takardar hannunsa da kudi.

Fita yay da sauri! nima na juya da niyyar fita......"Ke! juyawa nayi ina kallonsa, "Kada ki kuskura naji maganar nan a bakin kowa mahaifiyata ma ban amince ki fad'awa ba kinji ko."?

Da mamaki a tare dani nace" Ranka ya dade mai yasa baka so mahaifiyarka tasan abinda ke faruwa? wannan al'amarin fa bai kamata a 'boye ba, ya kamata ta sani domin ayiwa tufkar hanci da wuri."

"Ke baza a ta'ba fada miki magana kice to ba sai kin kawo hojjojin ki ko."? A sanyaye nace" Ranka ya dade ba haka bane duk abinda kaga na'ki aminta dashi kai tsaye to na duba naga ba mai kyau bane dan Allah ka bari a shedawa mahaifiyarka a'lamarin nan."

"Ke ki kula fa ni babu me shiga tsakanina da 'yan uwana kinji na fad'a miki ban yarda wani abu na cutarwa naci ba saboda haka na fada miki ki iya bakinki ban amince ki fadawa kowa wannan maganar ba.

Na dinga kallonsa ina jin wani irin takaici a cikin raina 'kiri-'kiri yana ganin gaskiya yana takewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya amma wai fadi yake bai yarda yan uwansa zasu cutar dashi ba, girgixa kai nayi nace" To shikkenan tunda baka so kowa ya sani insha Allahu babu wanda zan fad'awa."

Kauda kansa yay daga kaina ya tsirawa kasan gurin ido." Nace"Ina iya tafiya."? hannu ya daga mun alamar na tafi, na juya da sauri na bude kofa na fice raina a 'bace! na isa sashen mu...




Na kudi ne..!
Koda zaki ganshi a gruopa na sata ne idan kina bukatar biyan kudi ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300...account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turu #400 ne kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
47&48
"Ke ranar dana zo na kawo Apple din nan kin bashi yaci ko kuwa."? Cike da tuhuma yake min maganar sannan ya wani tsatstareni da idanunsa, cikin zuciyata nace"Ni dai na shiga uku kowa so yake yay amfani dani gurin cimma munufarsa, cikin ladabi nace" Ranka ya dade na bashi sai dai ban sani ba ko yaci ko kuma beci ba dan umartata yayi dana fita daga dakin.
Ajiyar zuciya naga ya sauke a fusace! ya bar gurin, zama nayi a sanyaye ina bin hanyar da yabi kallo nace "Insha Allahu Allah ba zai baku nasarar cutarsa ba." shuru nayi ina mamakin abinda sukeyi gabad'aya sunbi sun tayar da hankalinsu akan sa kowa so yake yaga bayansa sabida suna ba'kin cikin kada ya gaji mulki a hannun mahaifinsa, a gaskiya idan haka sha'anin sarauta yake da bita da k'ulli gami da ma'karkashiya to babu shakka akwai matsala da damuwa acikin al'amarin sha'anin sarautar dai ya zama sai gyaran Allah dan gabad'aya kowa babu Allah a cikin zuciyarsa.

Sai bayan la'asar Jama'a suka tsaigata, koda muka shiga dakin ragal muka sameshi a zaune yana ta abinda ya saba, latse latse a waya, a jiyar zuciya na sauke naji dadi sosai ganinsa lafiya lau, Haruna da

Please Login or Register in order to submit comment