Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsiro da fitina dan tunda naga kwayoyin idanunsa sun sauya nasha jinin jikina......"Wane irin awo kuma bayan wanda Dr Sadiya tayi min jiya." a kasalance yace "Nawa awon na mussaman ne." A dan tsorace! nace"Aikuwa bana bukata." kokarin sauka nake ya hawo gadon nace"Dan Allah ka sauka kaje falo gani nan." Girgiza kansa yayi yace."Kada ki bari aji kanmu dake kawai ki barni nayi abinda ya shigo dani domin kin san duk abinda zakiyi ba zan janye ba gwara ki hakura ki bani hadin kai."


Jikina ne ya mutu na dinga kallonsa, ina jin tsoron abinda zai faru......kwantar dani yayi a hankali yayi dubarar cire min rigar jikina, tunda ya fara sarrafa ni gabad'aya jikina ya rikice sha'awar dana tara ta tashi jikina na sakar masa muka shiga biyawa kanmu bukata...




*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan AllahโœŠ๐Ÿ?)

109&110
Koda na fito daga toilet din tsaf na samu dakin jakadiya sai goge goge take ita kuma Mamma na zaune a gefan gado ta dauki yaran duka ta rike a hannayenta kallo guda za kayi mata ka hango tsantsar farin ciki a tare da ita, Jakadiya da sauri tazo ta rike ni tana fadin"Sannu Sumayya." kaina kawai na daga mata muka karasa bakin gadon ta rike dani, Zama nayi a hankali nace"Mamma sannu." cike da kulawa tace"Sumayya aike za'ayi sannu." sunkuyar da kaina nayi ina murmushi......Tace "Amma nayi mamaki da wannan haihuwar taki sumayya me yasa kina jin ciwo tun yamma baki fada ba.

Kaina a kasa nace" Mamma wallahi ban tashi da wani ciwo mai tsanani ba kawai dai Allah ne ya kawo min haihuwar da sauki."

Girgiza kanta tayi tace"To Alhamdulillahi ina rokon ubangiji Allah yasa ki d'ore da haka ina fatan kuma babu inda yake miki ciwo."? nace"Babu Mamma sai dai ciwon mara kadan kadan.'' tace"Sannu insha Allah shima da ankwana biyu zaki daina ji." Ta kalli jakadiya da fadin" Ki duba mata kaya masu kauri tasa a jikinta sai ta kwanta ta huta." Jakadiya da sauri ta bude wardrobe tana dubawa


Riga da zani na atamfa ta dauki min ta taimaka min nasa a jikina, rigar sanyi nace ta dauki min nasa a jikina, ina kokarin kwanciya Mamma tace"Ki daure kici abinci sumayya." nace"To Mamma. Jakadiya ta fita da sauri minti biyar ta shigo hannunta da plate din abinci.

Kar'ba nayi a nutse nayi bisimillah na fara ci muna hira Jakadiya ta kunna turaran wuta a dakin ta nufi bandaki ruwan wanka ta hada ta fito dashi a madaidaicin baho, Mamma tace"A wanke musu jikinsu sai a goga musu zaitun.'' jakadiya ta mika hannu domin kar'bar babyn Mamma ta mika mata hassan din da fadin" shi zaki fara wanke wa dan na lura kamar bashi da hakuri sai tsotsar hannunsa yake da alama acici ne." Jakadiya na dariya ta kar'beshi Tace."Kinga shi kuwa wannan bacci yake tunda ya bude idonsa sau daya bai sake ba yana ta bacci." Dan murmushi nayi bance komai ba, Tace."Ai da safe su Tambaya zasuji labari mai dadi sumayya kin iya haihuwar a tsanake babu fargaba da tashin hankali."

Nace"Mamma kullum dama ina rokon Allah ya sassauta min idan nazo haihuwa Allah maji rokon bayinsa ya amsa min adduata."


Mamma tace"Aikuwa dai sumayya dukkanin wanda zai rike addua yana tare da nasara a rayuwarsa...........Tare suka shigo dakin shida Lawisa, Mamma tace"Yanzu ashe sai da kaje ka taso ta da tsohon daran nan." Yana kokarin magana Lawisa tace"Wallahi Mamma gwara da yaje ya tasoni nazo naga irin kyautar da Allah yayi mana." zama tayi a kusa dani fuska a sake tace"Sumayya sannu." Nace"Yauwa sannu ranki ya dade.'' tace"Ina fata dai baki manta dani ba a lokacin da kike nakuda." Dariya nai ina kallonta nace"Haba yaushe zan manta dake nayi miki addua sosai kuma insha Allahu ta kar'bu." Mamma tace"Aikuwa Lawisa ki kwantar da hankali adduar mace mai naquda bata da hijabi insha Allahu kafin tagwaye su girma kema kin samu rabonki." Tace."Ameeen ya Allah Mamma."


A nutse ya karaso kusa damu ya tsaya, Mamma ta kalleshi taga duk yayi wujiga wujiga tace."Babana wai tare da kai akayi nakudar ne."? girgiza kansa yayi yace."Ko daya Mamma ni a lokacin ma data haihu ina toilet wallahi sai fitowa nayi naji kukan baby.''

Tace."Ai abun da mamaki sai dai ba'a mamaki da ikon Allah!! naga kayi firgai firgai ne shiyasa nayi zaton ko ka taimaka mata."

Dariya yasa yace."Mamma ina ni ina wannan ya'kin ai sai ku na dai sha matsa a gurinta kafin Husaini ya fito." Mamma ta kalli yaron tana murmushi tace."Allah sarki ai daka ganinsa zai yi hakuri." Murmushi yayi yana leqa fuskar yaron.


Koda Jakadiya ta gama wanke Hassan din Lawisa ce ta kar'beshi ta shiryashi tsaf tasa shi a towel yace na kar'beshi na gwada bashi nono. kunya ta hanani na fito da nonon kawai sai yazo yana kokarin daga min riga a nufinsa ya fito da nonon.....a fakaice na buge hannunsa, na fito da nonon ina kokarin sawa yaron a baki, ko kunyar mahaifiyarsa baya ji ya tsuguna yana nuna min yanda zanyi, ni dai gabadaya kunya ce ta rufe ni itama Mamma basarwa tayi sabida ta riga tasan halin rashin kunyar yaron nata.


Cikin ikon Allah yaron ya janyo ruwan nonon cikin dubara irinta 'ya'yan zamani ya shiga zu'kar nononsa gabadaya muka dinga mamakin wayon yaron, Mamma tace"Dama yaran yanzu da wayonsu ake haifarsu, sai dana tabbatar da cewa nonon ya isheshi na cire masa sai na mikawa Lawisa shi ta karbeshi tana goge masa baki, Hussainin na karba na fara kokarin sa masa nonon a baki, yaron kasa kamawa yayi sai ya fara kuka, Mamma tace" Allah sarki shi bashi da wayon dan uwanshi ki kama masa nonon a hankali zai iya." Cikin dubara na kama kan nonon nasa masa a baki yana mamula a hankali kafin ya kama sosai ya shiga tsotsa, ajiyar zuciya na sauke ina godewa Allah a bisa ni'imar da yayi min.

Washe gari da safe kowa ya samu labarin haihuwar aikuwa sasheh cika yayi da jama'a wasu na fita wasu na shigowa kaina ya dinga ciwo saboda hayaniya, aikuwa Lawisa na sheda masa cewa kaina na ciwo yace a rufe sashen kada a sake bari kowa ya shigo kana ya umarceta data bani wayar yana so muyi magana.

Kar'ba nayi tare da sawa a kunnena yace."My lov kada ki janyowa kanki lalura garin san gwanintarki kin son jama'a suna ta damunki da hayaniya please dan Allah ki kwanta ki huta nace kowaye yazo kada a bude masa kofa, sannan kuma kada kisawa jikinki ruwan zafi sosai ki sirka kafin kiyi wankan."

Nace"Kayi hakuri ni kaina wallahi so nake na kwanta abin ya gagara gabadaya mutane sun hana duk wanda yazo burinsa na saurareshi wannan dalilin yasa nake tsayawa muna gaisawa.'' Yace."Ni dai na fada miki ko auntis d'ina ne suka zo ban bada damar a bude musu kofa ba." " Yar dariya nayi nace Babbar magana kenan." Yace."Kwarai kuwa keda kin dauka abin wasa ne my lov lafiyarki ita kadai nake bukata kin haihu lafiya bana so hayaniyar mutane tasa miki ciwon kai."

Nace"Ka kwantar da hankalinka babu abinda zai sameni insha Allah jama'a kuma dole kayi hakuri dasu." Yace." To shikkenan zanzo na kasa na tsare a sashen duk wanda yaga ina gurin sai ya juya ya tafi " Dariya nasa ina mamakin rashin kawaicinsa, yace."Wato kin mayar dani sakarai ko."? da sauri nace"Aa ranka ya dade kayi hakuri sai kadawo ko." ajiyar zuciya ya sauke yace."Ki bawa Lawisa wayar zamuyi magana." Sai da yay maganarta wallahi na tuna tana dakin, cikin jin nauyi na mika mata wayar ta karba a sanyaye sukai magana.



To haka kwanakin haihuwata suka cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da kulawa ta kowanne bangare Mamma na iya bakin kokarinta a kaina haka nan itama Tambaya nayin nata kokarin akaina da 'yan tagwayena da suka amsa sunansu Hassan da Hussaini Maimartaba kullum sai ya aiko da safe an daukesu an kai masa yayi musu addua sukan jima a gurinsa kafin a dawo min dasu..........Uwargida Huwaila ita ke shigowa kullum da Yamma ta gasa min jikina tayiwa yara wanka, ita kuma jakadiya itake kula damu da safe su aunty Safiyya kuwa shatara ta arziki suka had'o mana nida tagwayena kowanne da akwatinsa saqe da kaya, na samu kyautuka muhimmai ranar suna kowa kokarinsa ya faranta min nida 'ya'yana taro akayi sosai kuma aka tashi daga taron cikin koshin lafiya



*Bayan wata hud'u*
Yara sunyi wayo sosai dan har an fara koya musu zama......a lokacin ne kuma Allah ya azurta Lawisa da nata rabon ranar da suka tabbatar da cikin ita da mijin nata suka dinga murna da farin ciki......Ina zaune a kan kujera da Hussain a hannuna yana min rigima Ya shigo tunda na ganshi cikin walwala nasan akwai magana.

Zama yayi kusa dani tare da kar'bar yaron yana jijjigashi yace."Wai kukan me yake."? nace"Watakila yunwa yake ji wallahi kaga hassan duk ya shanye ruwan nonon." Hannu yasa kan nonon yana latsawa, na ture hannunsa da fadin"Kai kam kafiye wasa." Yace."Sumayya ban yarda ba kodai mitsininsa kikayi nasan Hussani da hakuri fa.".

'Yar dariya nayi nace"Sai dai idan kaine ka mintsineshi." shiru yayi min yasa yaron a kafada yana jijiigashi! Mariya ce ta fito daga kicin hannunta rike da fida cike da madara....har kasa ta durkusa ta gaishe da sauri ta miko min fidar ta bar gurin, nace"Kawoshi na gwada bashi madarar ko zai sha. miko min shi yayi na kar'beshi sai harbe harbe yake ina sa masa fidar a baki ya kama yana tsotsa

Ajiyar zuciya muka sauke a tare dashi, dan tsokana yasa hannu yana jan kafar Hassan dake kwance a gefena,

Murya na rawa nace"Dan Allah kada ka tsokaneshi kasan rigimarsa tafi ta Hussani." yace.""Ai so nake suyi ta baki wahala idan kikayi zuciya sai kiyi musu kani ko kanwa."


Wani irin kallo na watsa masa." dariya yasa tare da lakuce min hanci.....nace"Haba kai yanzu idan na samu ciki sai kayi murna ka duba fa kaga irin wuyar da nake sha da yaran nan."


Yana mirmushi yace."Meye a ciki sumayya a wuya bata kisa ko yanzu kika samu ciki ina farin ciki wallahi nasan ke 'yar baiwa ce Allah zai rangwanta miki."


A sanyaye nace"Hakane amma dai ni inaso yaran suyi kwari tukkuna idan kuma Allah ya kawo sai nagode masa." Yace." Yawwa 'yar albarka kinsan Lawisa ma Allah ya bata nata ko.'' na kalleshi cike da farin ciki nace"Ya za'ayi na sani tunda ba fada min kayi ba.".


Yace."Yau muka tabbatar da cikin tana can sai murna take." Nace"Kai kuwa ai dole tayi murna wallahi nima na tayata farin ciki Ubangiji Allah ya rabasu lafiya."

Ya amsa da ameeen yana min kallon kasa-kasa.....walwalar fuskata na rage nace"zaka fara ko."? Yana munafikin murmushi yace."Ki kira wa'innan yaran su dauki babys d'in nan muje daki."


Zum'bura baki nayi nace"Ni babu wani daki da zanje." Matsoni yayi yana sumbatar wuyana yace."Idan kuwa hakane lallai za'ayi abun kunya dan zan iya danneki a falon nan babu abinda ya dameni da hadimanki."

A sanyaye na kalleshi, girarsa ya daga min daso ya tabbatar min da maganarsa


Mariya na kwalawa kira da sauri tazo nace Ki goya Hassan kuje can gurin Mamma." da sauri tace"To ranki ya dade." Mikewa yayi ya shiga daki......ban bi bayansa ba sai da na tabbatar da cewa Mariya ta tafi da yaran sannan na bishi dakin.



*BAYAN SHEKARU GOMA*
Alhamdulillahi abubuwa masu kyau da marasa kyau sun faru a cikin wannan shekarun da suka wuce a cikin abubuwa masu dadi da suka faru a cikin shekarun da suka gabata Allah mai kowa da komai ya azurta Doctor Aliyu da da zuria maza da mata guda goma Sumayya nada shida hudu maza biyu mata yayinda Lawisa keda hudu mata biyu maza biyu, bayan wannan baiwar da Allah yayi masa sai ya daukaka darajarsa ta bangaran aikinsa na likitanci gwamnati ta d'orashi a kan babban matsayi saboda irin gudumawar ya dinga bayarwa a zamanin daya wuce Doctor Aliyu Abdul-aziz babban likita ne da duniya tasan da zamansa..............Abubuwa na rashin dadi da suka faru a masarautar kuwa shine rashin Jajirtattun mutane da akayi wato Baba Waziri da Lawi mahaifin Sumayya, mutuwar wad'annan bayin Allah ta girgiza jama'a Maimartaba Sarki Abdul-aziz yasha kewa da alhini kafin ya barwa Allah sabida yasan shi kansa idan lokacinsa yayi tafiya zaiyi inda sukaje, sai ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da gudanar da mulkinsa cikin tsari gami da bin dokokin ubangiji gefe guda kuma yana nunawa 'Ya'yansa Ali da Shatima yanda ake gudanar da mulki akan bigire na gaskiya da adalci! Aliyu da Shatima yanzu suna a matakin shekaru ar'bain da biyar a duniya kowanne ya mallaki hankalin kansa a cikinsu Allah ne kad'ai yasan wanda zai gaji mulkin masarautar...........
*Daga karshe nake cewa Ubangiji Allah ya za'ba abinda yafi alkairi a tsakaninsu".*







*'KWARYA TABI 'KWARYA*
*END๐Ÿ”š*

*ALHAMDULILLAHI*


_Jama'a nan na kawo 'karshen wannan littafi mai suna 'KWARYA TABI 'KWARYA Ina rokon Ubangiji Allah ya yafe min kusakuraina ladan dake cikin littafin Allah ya sadamu dashi bakid'aya masha Allah ina mi'ko sa'kon godiyata gareku masoyana wanda na sani da wanda ban sani ba ina godiya kwarai da gaske ina kuma alfahari daku mutuka ina rokon Allah ya bani ikon da zan cigaba da nishad'antar daku da kuma fad'akar daku..........Taku akoda yaushe take muku fatan alkairi๐Ÿ™‹๐Ÿผโ€โ™€๏ธ_



*_DAN DARAJAR ALLAH DA MANZON ALLAH KADA KI/KA HAD'A MIN DOCUMENT NA LITTAFIN NAN BAKU SAN YANDA NAYI NA RUBUTA ABUNA BA KADA KU HAD'A MIN DOCOMENT KUYI MIN SHARING A GRUOPS BAYAN KUN SAN NA KUDI NE KU BAR MIN LITTAFINA NA IYA HADA DOCOMENT DIN๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป KAJI TSORON HAKKIN DA BA NAKA BA_*




*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake........Completed #600 ne sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*


*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment