Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaifin nasu ya auro Fulani Hawwa suka tashi a tsaye dasu da mahaifiyarsu suka dinga jifanta da asiri iri iri wanda ya janyo mata matsala dik lokacin data samu ciki daga zarar yayi kwari sai ya zube hankalinta ya tashi sosai ta dage da azkar gami da rokon Allah ya kareta dan tayi imani cewar al'janu ne ke ra'bar jikinta tunda wani lokacin idan ta kwanta bacci suna zuwa suyi ta tsorata ta.......tunda ta samu cikin Aliyu ta dage da adduar har Allah yasa yayi k'wari gashi cikin ikon Allah ta haifeshi lafiya dalilin daya sa kenan tana haihuwarsa ta daura masa wannan laya mai dauke da ayatulkursiyu saboda tasan tilas ita da yaron su fuskaci kalubale mai girma a masarauta...........Yarima Ali ya taso cikin kauna da so da kulawar iyayensa duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan yana kaunarsa, Ita kanta mai babban daki ganin kamar maimartaba naso ya gane manufarta akan yaron yasa ta zauna da 'ya'yanta ta umarce su akan kada su sake su nunawa yaron 'kiyayyarsu a fili komai za'ayi ta karkashin kasa za'ayi masa, wannan dalilin yasa suke danne hassadarsu a kansa suke nuna masa kauna ammfa Allah ne kadai yasan abinda ke zuciyoyinsu..........'Bangaran 'yan uwan mahaifinsa kuwa babu wanda ke nuna masa kauna da kulawa sama da Waziri shike jansa a jikinsa sosai yana nuna masa so hakan yana yiwa maimartaba dadi a cikin ransa yana kuma yiwa dan uwan sa addua akan Allah shima ya azurtashi da 'ya'ya masu albarka, Waziri Abdul-raham matansa uku amma duk cikinsu babu wacce ta ta'ba haihuwa sai da ya auri matarsa ta uku da yake bazawarace tana da 'ya'ya a wani a gidan sannan aka gane cewa rashin haihuwa daga gurinsa ne shiyasa yake masifar kaunar 'ya'yan 'yan uwansa.......wannan dalilin yasa Ciroma da Galadima suke jin haushinsa dan ganin kamar yana fifita Yarima Ali akan 'ya'yansu Galadima shine mahaifin Shatima shi kuma Ciroma shine mahafin Moddibbo wanda yaci sunan mahaifinsa shine suke kiransa da suna Moddibo, Ciroma Abdul-Jabbar nada 'ya'ya goma dan duk yafi 'yan uwansa yawan 'ya'ya shiyasa har kullum yake fatan sarauta ta dawo hannunsa, mata shida maza hud'u, cikin 'ya'yanshi akwai mai izzah da taqama tamkar ubanta ne a sarki a cikin masarautar haka take rashin mutunci tare da cin mutuncin duk wanda tayi ra'ayi, Gimbiya Lawisa kyakkyawa ce ta karshe sai dai ko kusa ko alama bata da kyawun hali tana da d'abiar izigilanci da wulakanta mutane mutum komai girmansa bai wuce cin mutunci a gurinta ba........Gimbiya Lawisa tun kafin tayi wayo tayi hankali Allah ya d'ora mata masifar son Yarima Ali a cikin ranta duk da tana yarinya k'ank'anuwa ya tafi karatu hakan besa ta mance kammanin sa ba. shiyasa yanzu take ta murna da farin cikin dawowarsa masarauta sai shirye shiryen walima takeyi domin nuna masa farin cikin dawowarsa lafiya........Da kanta ta shirya tsaf cikin shiga ta alfarma tare da bayin dake take mata baya ta nufi 'bangaransa domin sheda masa abinda ta shirya masa na taya murna..........
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊?*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_




*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah)
13&14
Aunty Safiyya a nutse take kallonsa kafin tace"Kai kuwa Magajin sarki meye laifin Lawisa dan Allah kada kaje ka dauko mana ta waje gwanda ka duba a cikin gida ina ganin kamar haka zaifi alkairi." Shuru yayi mata tare da sunkuyar da kansa. Tace"Idan ka auri 'yar uwarka a ganina sai kafi samun cikakkiyar kulawa kuma tabbas hakan zai faranta ran iyayenmu dan Allah ka duba maganata da kyau kaji ko."! har yanzu kansa na sunkuye a kasa ya'ki kallonta ballantana ya bata amsa. mirmushi tayi tare da mikewa da fadin"Miskili kenan to kai dan Allah da irin wannan halin naka wacece zata iya zama da kai idan ba 'yar uwarka ba? babu macan da zata juri wannan wulakancin naka."
'Dago kansa yay yana kallonta cikin rashin walwala yace."Aunt Safiyya mai yasa kuke yi min irin wannan kallon ne? wallahi ban san ya ake wulakanci ba a rayuwa ku lura da kyau da'bia tace rashin son doguwar magana shiyasa nayi shuru na kyale ki amma duk irin maganganun da kikeyi ina jinki."

Murmushi tayi tana kallonsa tace"Eh ni zan fadawa kowa hakan d'abi'ar kace shiyasa ma ai nace bama so ka auri bare gwara ka auri ta gida domin sai tafi jurar zama da halayen ka." murmushi yay wanda ya tsaya iya lab'bansa yace."Aunt Safiyya ki bar wannan maganar dan Allah.'' Jin abinda yace yasa Lawisa saurin kallonsa gabanta na faduwa lallai wallahi tasa rai ganin aunty Safiyya ta shiga maganar yasa take jin tamkar ma ta aure shi ta gama.

Aunty Safiyya ta kalleta tare da fad'in "Lawisa kina sonsa ko."? babu kunya tace" Eh aunty. " murmushi tayi tare da kama hanyar fita tana fadin"Ba zan tafi gida ba har sai na bari an tashi daga fada na fadawa maimartaba halin da ake ciki.
Da sauri ya dago kansa yana kallon bayanta cike da mamakin jin abinda ta fad'a......Fuska a kirne ya kalleta da fad'in "Tashi ki fitar min a daki wato dama abinda ya shigo dake kenan? waye ya fad'a miki ina sha'awar auran zumunci dake."?

Lawisa gabanta ya dinga faduwa tana so tayi magana amma ta kasa saboda tsabar kwarjin da yayi mata gashi ya tsareta da idanunsa masu girman da furgita mara gaskiya.

A sanyaye ta miqe tana gyara alkyabbarta hanyar fita ta kama ranta sai tafarfasa yake yi lallai wai duk wannan kyawun nata da kyawun surar jikinta bata burgeshi ba hakika taji takaicin tsawar da yayi mata meye laifinta da zaice baya sha'awar auran zumunci da ita.......masu take mata baya ganin ta fito fusace yasa suka shiga hankalinsu da sauri suka rufa mata baya suna sunkuyar da kansu 'kasa.............

****
Cikin saurin na fito daga gurin mu domin zuwa duba dawakan da babana ke hidimarsu tun safe dana zuba musu abinci ban sake zuwa duba su ba saboda yini mukayi wankin kayanmu nida mahaifiyata wannan dalilin ne yasa ban je gurin da wuri ba............Ina daf da shiga kofar dawakan na hangeta ita da masu take mata baya, sanin halinta naso a girmamata yasa na sunkuyar da kaina qasa har suka karaso gurin nace" Barka da yamma ranki shi dad'e." banza tayi min bata amsa ba sai hararata take ni kam ban san me yasa ta tsaneni ba tsakanina da ita harara ne da kallon banza. Ganin taki amsawa yasa da sauri nayi nufin shiga kofar......Naji ta daka min tsawa da fad'in "Ke! mahaukaciya dawo ki tsaya a inda kike ko nace ki tafi ne."? Cike da mamaki nake kallonta kafin nace" Ranki ya dad'e na gaishe ki kin'ki amsawa me kike so nayi miki a yanzu ina da uziri zan zubawa dawakai abinci."
Kallona naga tanayi tana girgiza kanta, ni kaina sai da na gama maganar nazo ina nadama sabida nasan na tarowa kaina jaraba, ni haka nake bana barin magana a cikina idan mutum ya gaya min biyar sai na fada masa goma gashi bani da tsoro ko kad'an cikin dubbanin mutane aka ajiye ni zan iya kwatar kaina saboda ina da baki.

Inda nake tazo ta tsaya tana yi min wani irin kallon raini! kafin na ankara naji yawun bakinta a fuskata, da sauri na dago kaina ina kallonta........Tana wani irin huci! tace"Yanzu Sumayya a matsayinki na makaskanciyar baiwa a gidan nan har kina da damar tsallake umarnina nace miki ga abinda nake bukata kice kina da uziri."?

Hannu nasa na goge yawun data tofa min nace"Ranki ya dade ki gafarce iya bakin kokarina nayi miki na baki girmanki na risina na gaishe shin to dan Allah dan annabi me kike so nayi miki ."
Mari! ta kwad'a min a kumatuna kafin na dawo daidai ta sake waska min wani a d'aya gefan! Ido jawur nake kallonta ina jin tamkar nima na fitar da hannu na rama! marin......hannu ta daga kawai tana nuna ni tsabar b'acin ran dana kuntunka mata ya hanata magana, a rayuwar Gimbiya Lawisa tun tasowarta a gidan sarautar babu wanda ya ta'ba yi mata gardama akan umarninta sai Sumayya......Juyawa nayi zan shiga kofar dawakai ta janyo faffad'an wuyan rigata aikuwa a take rigar ta yage da yake rigar ta yadi ce mai dogon hannu zanin kuma na shadda kamfala shine uniform din mu a cikin gidan mata zani maza wando amma dai duk ranar jumaa muna sanya tufafi masu kyau domin girmama ranar haka ma ranar sallar 'karama da babba sarki nayi mana d'inkuna na atamfofi muyi ado domin murna da zuwan ranar.........Hannu nasa da sauri na dafe wuyan rigar ganin yana kokarin sab'ulewa. Tsira mata ido nayi rai a 'bace! nace tsirara zakiyi min ne? kada fa ki manta kema macace idan kinyi min tsirara a idanun jama'a kamar kin tonawa kanki asiri ne."
Wani marin ta sake bani tana huci! ni kuma mirmushin takaici nayi hannuna dafe da kuncina ina kallon ikon Allah........Jama'a ne suka taru a gurin sai bata hakuri suke harda masu durkusa mata, Buba ta kalla dake riqe da shar'be'biyar bulala tace"Bani bulalar nan." Da sauri ya mika mata yana fadin "Tuba take ranki ya d'ad'e."........Ganin ta d'aga bulalar zata shaud'a min yasa nayi saurin fizgewa na nannad'eta a hannuna sai kawai muka tsirawa juna ido nida ita jama'ar dake gurin da ita kanta mamakin karfin halina suke.........Ta girgiza kanta tana kallon Buba tace" Inaso ka samo igiya mai kauri ka daure mata hannuwa da kafafu yau nayi al'kawarin sai naga karshen taurin kanki."..............Kallonta kawai nake tsabar takaici da bakin ciki yasa nake jin kamar na zazzabga mata bulalar dake hannuna, ina kallon Buba ya tawo da murtukekiyar igiya gabana ya yanke ya fad'i ganin ya nufo inda nake....................yasa na juya baya ina neman mafaka babu dan duk ko ina mutane ne sun kewaye mu, tsugunawa nayi a kusurwa hawaye ya kwace min, Buba babu tausayi yazo ya shiga kici kicin daure min hannuwa da kafafuna sai tirje tirje nake ina haurinsa amma sai da ya samu nasarar daure ni tamau! gwiwowina a kasa kaina a sunkuye na soma jin saukar bulala a gadon bayana.......tsabar taurin kaina yasa na kasa motsi ina dai jin radad'in bulalar na ratsa min jiki amma saboda na nuna mata a banza takeyi yasa na daure.........Gimbiya Lawisa sai da jikinta yay sanyi ganin ko gezau na 'kiyi ballanatana na nuna mata ina jin zafin bulalar, tunani tayi ko itace ba ta iya bulalar ba rai a 'bace tace"Buba zo kayi mata ka tabbatar da cewa ta ratsa jikinta shegiya basamudiya yanda take da wannan gansameman jikin dama ai duka ba zai ratsa ta ba." Gefe ta koma tana haki! dan ba karamin galabaita tayi ba.'' Buba cike da bin umarni ya daga bulalar zai shaud'a mata, muryarsa ta katse masa hanzari.....Kafatanin jama'ar dake gurin suka juya suna kallonsa ganin ya nufo gurin ne yasa kowa yayi k'asa da kansa har ita Lawisan sunkuyar da kanta tayi......Cikin nutsuwa ya 'karaso gurin aka bud'a masa hanya ya shiga har inda nake durkushe! ta 'kasan idona nake kallonsa yana tsaye hannuwansa duk biyun a baya sai kalle kalle yake a gurin kafin naga ya kalleta babu fara'a a tare dashi yace."Yace."Meke faruwa ina zaune Haruna ke sheda min ga jama'a sun taru kuma kina gurin saboda haka inaso nasan abinda ke faruwa."
*BINTA UMAR ABBALE*

Shearing👏🏻
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊?*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)



17&18
Tana kishingid'e a killace a guri guda da cazbaha a hannunta tana lazimi yau ita kadai ce a zaune a falon babu hadimai a kusa da ita ta bukaci zama ita kad'ai ne domin ta kad'aita kanta da mahallicinta shine da dalilin da yasa ta sallami bayin dake kusa da ita.

Tunda ya shigo take sakin murmushi idanunta a kansa har ya k'asara kan kilishin da take kishingide zaman raquma yay a gabanta tare da sunkuyar da kansa cikin tsantsar ladabi yace."Mamma barka da yamma." hannunta guda ta dora a saman kanshi tana shafawa gyaran murya tayi tana nuna masa cewar akwai abunda takeyi....Kansa ya dago yana kallonta sai ta nuna masa carbin dake hannunta tana murmushi had'e dayi masa nuni dacewar ya jira ta kammala.

Murmushi yay a nutse yasa hannu kan tire din dake gabanta wanda ke cike da kayan marmari.. tufa(apple) ya d'auka yasa a bakinsa ya gutsira yana sake gyara zamansa a gurin.

Kallonsa take tana murmushi mai ma'ana wanda kai kana ganin yanayin fuskarta zaka gane cewar tana cikin farin ciki kuma akwai soyayya da shaquwa mai yawa a tsakaninta da yaron nata.


Magajin sarki sai da ya cinye tufa(apple) uku tukkuna ta kammala lazimin a nutse tace"Babana barka da yamma." Ya dago kansa da sauri yace."Mammah barka dai ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya." Yafadi maganar a sanda yake kokarin riko hannuwanta.

Tace."Lafiya lau na wuni ina fatan baka da matsala dan tun safe nake jiran shigowarka yau ba kayi shigowar safe ba ina fatan lafiya."

Zamansa ya gyara har yanzu kuma hannuwansa na rike da nata yace."Wallahi Mammah yau bacci na yini ina yi sai gefin la'asar na tashi nayi wanka wannan shine dalilin da yasa ban shigo mun gaisa ba."


Ajiyar zuciya ta sauke tace"To alhamdulillahi tunda lafiyarka lau dama akwai muhimiyyar maganar da nake so mu tattauna da kai."

Ya sake gyara zamansa cikin kulawa yace."Ina sauraran maganar Mammah." Da farin ciki ta tare da ita tace"Ashe bayan dawowarka gida kun shirya tsakaninku kai da Lawisa 'yar gurin Kawun ka Ciroma d'azu da safe maimartaba yake sheda min yanda al'amura suka kasance hakika naji dadi sosai daka za'bi matar aure acikin dangi ina ganin hakan sai yafi mana kwanciyar hankali da kai baki daya."


Shiru yayi kansa a kasa ya rasa abinda zaice. ashe sai da aunt Safiyya taje ta fad'i maganar wallahi shi ya dauka da wasa takeyi! tunda yake bai ta'ba sha'awar auran zumunci ba saboda gudun lalacewarsa yafi so ya fita waje yaje can ya auro saboda baya so ya auri 'yar dangi zumunci ya sake lalacewa dama a lalace yake shiyasa kwata-kwata baiyi na'am da maganar ba ashe sai da taje ta fadi maganar.

Fulani ganin yayi shuru tace."Babana ko akwai matsala ne? naga kayi shuru kana tunani kayi min bayani dan ba naso ayi al'amarin nan rayuka su 'baci idan ba kai ke son al'amarin ba to tun kafin tafiya tayi nisa a warwareshi."


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yana kokarin 'boye damuwar dake fuskarsa yace."Mammah ba wani abu bane yasa kika nayi shuru ina tunanin abinda aunty Safiyya ta aikata bayan nayi mata bayani cewar babu wata alaqa ta soyayya a tsakanina da Lawisa kawai tazo ta ganta ne a ranar dana dawo tazo tana sheda min cewa ta shirya walima domin murnar dawowata gida lafiya to ita kuma aunt Safiyyan shine take tunanin soyayya ce a tsakanina da ita.

Fulani shuru tayi tana mamakin al'amarin ta kalleshi a nutse tace"To yanzu wace shawara ka yanke dan gaskiya al'amarin yayiwa Maimartaba dadi bashi kadai ba har sauran 'yan uwansa sunyi farin ciki nima kuma naji dadin hakan idan kace ka janye maganar baza suji dadi ba.

Murmushi yay wanda ya tsaya iya le'bansa yace."Mammah bana fatan ranar da zata zo na 'bata muku rai dake da maimartaba tunda dai maganar nan ta fita har iyaye sunji to ina ganin babu damuwa zan auri yarinyar amma a gaba dole na 'kara aure mutukar Allah ya had'ani da wacce nake so."


Fulani murmushi tayi tana girgiza kanta cike da tsantsar farin ciki a maganarta tace"Ubana ina alfahari dakai mutuka ina jin dadin yanda kake kula dani da gudun 'bacin raina ina rokon Allah ya azurtaka da zuria masu albarka kamar yanda kake mana ladabi da biyayya kai ma ubangiji Allah yasa 'ya'yanka suyi maka.

Cikin sakin fuska ya amsa da ameen Mammana.! dama nace ina bukatar masu hidima a sashena domin wani sa'in hidima nayi wa Haruna yawa."

Cikin kulawa tace"Ayya ai wannan mai sauki ne ubana dama saboda nasan baka san hayaniya yasa na tura maka Haruna saboda nasan yana da nutsuwa amma insha Allahu zan sake turo maka mutum uku sun isa ko."? Yace."Yace mutum biyu ma sun isa sai su zauna su uku ina ganin hakan yafi" Tace."To shikkenan Ubana kada ka damu insha za'a turo masu hankali da nutsuwa.


***
Washe garin ranar bayan mun fito daga gurin karatu ni da Lahira muna tafe muna magana, Haruna yasha gabanmu yace."Sumayya Lahira kuje can b'angaran Fulani ana bukatar'ku.''

Kallonsa nayi nace"Haruna ina fata dai lafiya ba wani laifin mukayi ba." Yace."Babu komai ku kwantar da hankalinku sannan ba ku kad'ai aka nema ba har da sauran 'yan uwa.'' Ajiyar zuciya na sauke nace"Haruna dan Allah zan duba jikin babana kuje kawai na biyo bayanku daga baya."

Da sauri yace."Wai sumayya mai yasa kike gardama da umarnin masarauta akwai 'ya'ya da yawa da iyayensu suke halin rashin lafiya amma basa irin abinda kikeyi.

Hannu na d'aga masa nace"Haruna abinda yasa kaji nace haka sabida nike bashi magani yanzu haka Tambaya mahafiyata suna d'akin dahuwa(dakin girka abinci) suna aiki girka abinci kuma nasan idan naje bai zama dole a sallame mu da wuri ba shiyasa nace zan fara dubashi na bashi magani tukkuna.

Haruna yace."Ba za'a wani dad'e ba insha Allah kedai kawai ki shige muje." Girgiza kaina nayi na kalli Lahira dake rungume da jaka nace"Muje." Haruna gaba yayi da sauri muka rufa masa ba zuwa b'angaran Fulani.
A jere muka samu 'yan uwanmu bayi maza da mata sunja layi a bakin k'ofa kai tsaye 'bangaran mata muka nufa nida Lahira muka tsaya shi kuma Haruna da sauri ya bude kofar falon ya shiga ciku.....Surutai ne suka shiga tashi a gurin bayan shigar haruna falon dukkanin mu muna mamakin tara mu da Mammah fulani tayi sabida mun san da cewar ita din macace mai mutunci da karamci bata fiye tara mu taci mana mutunci ba kamar sauran 'bangarorin dake gidan, dukkanin mu dai addua mukeyi akan Allah yasa alkairi ne.

Haruna na fitowa muka bishi da kallo ya kalli 'bangaran maza da sauri yace."Ku shigo a nutse." Suka dinga shiga falon a nutse har suka qare, kusan mintina goma sha biyar da shigarsu suka fito kowa ya kama gabansa banda mutum biyu da suka ja gefe suka tsaya.

Haruna ya kallemu da fadin"Ku shigo a nutse." Da sauri muka tu'be takalman mu muka fara shiga daya bayan daya.

Zubewa mukayi a gabanta muna gaisheta.....Amsawa ta dinga yi cikin walwala tana kallonmu fuska a sake babu nuna 'kyama

A nutse ta dinga tambayar sunayenmu muna fad'a mata, ta d'ora idanunta a kaina fuskarta a sake tace"Sumayya ina tsammanin zaki fi 'yan uwanki kuzari da kazar kazar saboda haka ke kad'ai zan dauka a cikin ku zaki kasance daya daga cikin hadiman Magajin Sarki zaki dinga kulawa dashi da duk abunda yake bukata keda sauran 'yan uwanki amma su din maza ne Haruna da Isa da Hamza ke kad'ai ce mace a cikinsu."

Tunda take maganar gabana ke fad'uwa sam banyi farin ciki dajin wannan al'amarin ba ba dan komai ba sai dan sanin da nayi cewar bani da lokacin kaina na farko ina d'awaniyya da mahaifina na biyu ina kula da aikinsa dake cikin gidan ina nufin d'awainiya da dawakai, na uku kuma karatun dana k'wallafawa raina a kansa wanda ba kowane yake da ra'ayin yinsa a cikin masarautar ba, dama Maimartaba ya bude sashen karatu a gidan sabida mu, wanda yake da ra'ayi yaje ya dauki darasi na boko dana arabic wanda kuma baya da ra'ayi yayi zamansa to nida iyayena muna da ra'ayin karatu shiyasa suka goya min baya domun na samu ilimi yanzu haka mun kai izifi talatin a cikin al'kur'ani maigirma, sauran littafan addini kuwa nan ma mun sauke wasu 'bangaran boko ma ina fahinta sosai dan ina jin turanci amma ba sosai ba wannan dalilin ya sanya naji gabad'aya banji dadin a'lamarin ba


Cikin kokarin danne damuwata na kaskantar da kaina cike da ladabi nace"Godiya nake ranki ya dade hakika naji dadi mutuka da kika za'be ni a matsayin wacce zata kula da sashen Yarima ina rokon ubangiji Allah ya bani ikon daukar amanar da kika bani."

Cikin farin ciki Fulani tace."Babu damuwa Sumayya kuna iya tashi ku tafiya Haruna zai jagorance ku zuwa sashen nasa sai ku gabatar masa da kanku a matsayin wanda na turo ku.

A nutse muka mike mukayi mata sallama cike da ladabi muka fita daga falon, Haruna dasu Isa suna tsaye suna magana na kallesu fuskata babu walwala nace"Ku muje ko."? Haruna yace."Ke aka za'ba."? Daga masa kaina nayi na kalli Lahira nace"Dan Allah kafin ki shiga gurin ku ki duba babana ki bashi magani idan kuma Tambaya ta dawo shikkenan." Lahira tace"Kada ki damu insha Allah zan dubashi sai kin shigo.


Lokacin da muka isa b'angaran nasa a kishingid'e muka same shi cikin furanni yana sanye da 'kananun kaya gabansa kayan marmari ne cikin tire wayarsa yake dubawa fuskar nan a had'e! cikin zuciyata nace "Naga sanda zan ga dariyar guy nan kullum fuska babu rahama Allah dai ya kyauta."

Gabansa muka zube gwiwoyinmu a k'asa had'a baki mukayi gurin fad'in "Barka da hutawa Magajin sarki muna fatan mun same ka lafiya."! K'asa mukayi da kanmu bayan mun gama maganar.....

Shuru yayi mana kamar bai san damu a gurin ba, raina ya 'baci sosai aqallah mun kai minti goma a gurfane a gabansa kamar wasu masu neman gafara wannan wace irin rayuwa ce.

Kallonsa nayi a lokacin da yake kokarin gyara zama karaf! muka had'a ido kwarjini yayi min wanda yasa na ma'kale maganar dake raina nayi kasa da kaina gabana na fad'uwa guy ya tara duk abubuwan da ake bukata yana da kyau sosai gashi dogo abinda yafi birgeni a tare dashi manyan idanunsa wanda suke a lumshe k'wayoyin idanunsa basu cika fari ba sun d'an sirka da ja banta'ba ganin kwayar idanunsa tayi haske ba.
muryarsa ce ta katse min nazarin da nake.....
*BINTA UMAR ABBALE*

Shearing 👏🏻
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊?*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_




*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA''ATU S YARI*
(Kainuwa dasha Allah✊?)
15&16
Ganin yanda ya tsira mata idanunsa gami da sake tamke fuskarsa ya sanya jikinta yay sanyi tana jin tsoron ya tozarta a gaban wa'inda suke ganin kima da mutuncinta.........Cikin kokarin aro jarumta tace"Tunda nake a cikin gidan nan babu wanda ya ta'ba yi min musu akan umarnin da zan bashi sai wannan ba'kar yarinyar mai fuska irinta ba'kar akuya ta raina ni sosai sai kace ni din abokiyar adawarta ce, gabad'aya mutane suna gaisheni suna bani girma da mutuncina amma ita kokarin ratse ni take ta wuce ina ganin ko wane irin hukunci nasa ayi mata ya dace da ita sabida ta kasa mutunta ni."

Wani irin kallo yake min tamkar yana kallon abu mai muni! koda yake ban sani ba ko shima ya hango munin nawa da mutane suke fad'arsa wannan dalilin yasa da sauri na sunkuyar da kaina kasa zuciyata tana wani irin zafi! ta k'asan idona nake kallonsa sai ya mutsa fuska yake yana kare min kallo.

A dan sace na dago kaina muka had'a ido dashi! da sauri na

Please Login or Register in order to submit comment