Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin hakan baya hana haihuwa idan rabo ya rantse komai tsantsenin mutum sai ciki ya shiga....Sannan kuma ta wani 'bangaran hakan na ragewa ma'aurata jin dadinsu misali idan namiji yazo zaiyi release dole zai fita daga cikin ramin hakan zai rage masa jin dadin ta 'bangaran mace kuwa idan baki da saurin kawowa namiji na samun satisfied zai barki da wahala wani namijin idan ya kawo sau daya shikkenan ya gama duk abinda zakiyi masa ba zai sake tashi ba, kamar dai Yarima yana da kar'fin sha'awa amma kuma baya dogon zango yake gamsuwa kuma idan yayi sau d'aya baya 'karawa! ita kuma Sumayya tana da nisa sosai tana bukatar dogon zango kafin ta gamsu gashi an samu matsala ta 'bagaransa a lokacin da take kan ganiyar jin dadinta a lokacin shi kuma yake gamsuwa kuma saboda gudun haihuwa ya cire jikinsa ya barta da wahala, duk da bata san kan al'amarin sosai ba ta tabbatar da cewa akwai cutuwa a ciki dole ne ta nemawa kanta mafita tun kafin tafiya tai nisa.................Ta jima tana tunane-tunane kafin ta mike jiki a sanyaye ta fita falo ba tare data cire hijabin jikinta ba.


To koda ya dawo da daddare ma sabgar gabansa yayi ya fita ba tare da ya tanka mata ba ta lura yaji haushin abinda tayi masa d'azu shine dalilin da yasa yayi watsi da ita da al'amarinta......Sai da tayi bacci ya shigo dan yana can tare da Shatima suna hira, wanka yayi yasa kananun kaya na bacci ya kwanta kusa da ita.


Kwanciyarsa a kusa dani yasa na bud'e idona jikina na janye ina addua akan Allah yasa kada ya nemi wani abu, kafin ma na gama tunani naji shi a jikina yana shafa wuyana shiru nai masa ina ji yana kesses din baya yana sake matseni a jikinsa, na dinga jin wani irin yanayi a jikina, janyewa nayi, ya mike zaune rai a b'ace! yace."Wai meye hakane? kina abu sai kace 'Yar kauye."


Shuru nayi yace."Kin san duk fushin da kike ba zai hanani biyan bukatata ba me nayi miki tun safe kike fushi na tambayeki dalili kince babu komai."


Uffan bance masa ba, ya koma ya kwanta tare da birkitoni kansa, ringume ni yayi tsam! yana kokarin sa bakinsa a nawa, yanda yake min yasa gabadaya sha'awata ta tashi, jikina ya mutu na kyaleshi yana ta juya ni yanda ransa keso.


Banji zafi sosai ba kasancewar ina da bukatar al'amarin yasa na sakar masa jikina gabad'aya muka fita cikin hayyacinmu yauma kamar jiya yana jin zaiyi release yayi yunkurin cirewa hanashi nai na rikeshi jikina sai rawa yake ni kadai nasan irin halin da nake ciki! da karfi ya fizge jikinsa kan cinyata ya zubar da sperm din. Ya wani kwanta a kaina yana sakin nishi! takaici yasa wasu zafafan hawaye suka kwaranyo min, hannu nasa da sauri na goge na shiga turesa daga jikina.


Ba tare da wata damuwa ba ya mike ya nufi toilet, mikewa zaune nai ina duba jikina da duk ya 'bata min wannan wace irin rayuwa ce sai kace wanda yake auratayya da karuwa! karuwai ne ba'a san haihuwa dasu ake zuba musu sperm a jiki amma matar sinna a dinga yin wata irin mu'amula da ita irin ta yahudawa." Kuka ne yake kokarin kufce mata tana kokarin danneshi...........Yana fitowa daga toilet din ya kimtsa jikinsa yazo yana kokarin kwanciya bedshirt din yake turewa dan a tunaninsa shima ya 'baci! Mikewa nai na bar masa gurin, wanka nayi na fito na kimtsa jikina kujera na nema na kwanta zuciyata na wani irin zafi!


"Sumayya."! naji ya kira sunana murya a sama! shuru nai masa.

Yace." Wane irin abune wannan kika tsiro dashi zaki bar gado kije kujera ki kwanta.'' ? kamar da dutse yake magana, A fusace! ya mike zaune tare da kunna bedlamp yana kallon inda take kwance.

"Bakya ji ne ina miki magana."? murya a cunkushe nace" Ina ji.'' yace."Okey to ki dawo ki kwanta kusa dani." da sauri nace"Dan Allah ka rabu dani nai kwanciyata anan dan banga amfanin kwanciya a kusa da kai ba.''


Shuru yayi na mintu biyu kafin ya d'aga kafad'a alamun rashin damuwa bedlamp din ya kashe ya koma ya kwanta tare da rufe jikinsa da bargo, bacci mai nauyi ne ya daukeshi ni kam sai can dare na samu da kyar bacci ya dauke ni.

Kasancewar na jima banyi bacci ba yasa yau ma na makara, lokacin dana tashi har ya gama shirinsa yana zaune gefan gado yana gyara igiyar takalminsa kallonsa nai ina mamakin dalilin daya sa bai tasheni nayi sallah akan lokaci ba, yanayin fuskarsa yasa na gane akwai matsala.
Ba tare da nace masa komai na na mike a sanyaye na shiga band'aki......koda na fito samun dakin nai babu shi ya fita ba tare da ya tsaya mun gaisa ba dama baya wani damuwa dayin break haka yake ficewarsa sai yaje ofis din yake kiran mahaifiyarsa ta tura masa da abinci.....a rabar yini nayi cikin tsananin damuwa da tashin hankali na dinga tunanin hanyar da zanbi na warware wannan gagarimar matsalar da nake fuskanta.............Har dare ya shigo gari yay shuru idona biyu ina tsammanin sa bai shigo bai kuma kira waya ba, da dai na gaji shirin kwanciya nai na rufe kofa na kwanta da wayata a hannuna, karfe goma da rabi na dare na nemo number sa.....Lokacin yana kokarin shiga gurin Lawisa yaga kiran wayarta, dauka yayi babu yabo babu fallasa ya amsa gaisuwarta.


Ajiyar zuciya na sauke nace"Baka dawo bane.''? kai tsaye yace."Yanzu na shigo yau aiki ya ri'ke ni ina fatan kin wuni lafiya." nace"Lafiya lau.'' yace."To masha Allah sai da safe." kafin nace wani abu ya kashe wayarsa.

A sanyaye na kashe wayar tare da ajiyeta a kan bedside naja bargo na rufe jikina ina addua a cikin zuciyata.


Gajiya da wahala basa hanashi fitina koda yaci abinci ya gama komai na rayuwarsa zuwa yayi ya zauna kusa da ita....Lawisa ta mike zaune tana kallonsa, babu fara'a a fuskarsa ya mi'ka mata magani da goran ruwa. a sanyaye ta kar'ba ta watsa a bakinta ta kora da ruwa.


Goran ruwan ya kar'ba ya ajiye ya hau gadon sosai janyota yayi jikinsa yana sa hannunsa a cikin rigarta Lawisa ajiyar zuciya ta sauke ta sakar masa jikinta sosai suka shiga biyawa junansu bukata.


Washe gari da safe ita dashi cikin walwala suka rabu yana jin dadin mu'amula da ita saboda tabi ra'ayinsa da dokokinsa shiyasa yake jimawa akanta yana dogon zango kuma baya fargabar zubar da sperm dinsa a jikinta domin yana da tabbacin ba zata dauki ciki ba, sa'banin Sumayya da idan yana sex da ita yake fargaba sam baya sakin jikinsa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo yana jin zai kawo yake gaggawar cire jikinsa.....Ya fahimci cewa hakan na 'bata mata rai! ita da kanta ta nemi hakan tunda babu yanda baiyi da ita ba akan tabi ra'ayinsa taqi dama sai da ya gargadeta kacewar duk abinda ya biyo baya kada tayi kuka dashi tai kuka da kanta.


Cikin rashin walwala ya shiga gurinta, ko zama bai ba yana tsaye suka gaisa ya juya ya fita ba tare da ya nuna mata wata cikakkiyar kulawa ba.

Kuka sosai tayi a ranar kafin ta yanke shawarar tunkararsa da maganar gwara suyi wacce zasuyi ta gaji da irin wannan zaman da suke mara dadi da ma'ana.


Koda ya dawo guri nata kunya da nauyi yasa ta kasa tunkararsa da maganar duk dare haka zai danneta ya biya bukatarsa ba tare da ya damu da tata bukatar ba.



*******
*BAYAN WATA BIYAR*
Rayuwar dai da suke sai kara tsanani take Sumayya ta shiga cikin wani irin hali na damuwa da bukatuwa yayinda ta 'bangaransa yake gudanar da harkokinsa na yau da gobe ba tare da ya bawa damuwarta mahimanci ba, duk da yasan abinda ke damunta yana saka ta kuka a koda yaushe hakan bai sa ya sauka daga kan ra'ayinsa ba koda yaushe idan bukatarsa tazo zaije gurinta ya biya bukatarsa ya barta cikin matsananciyar sha'awa, lokaci guda ta shiga rama yayinda Lawisa ke 'kara cika tana bunkasa da wata irin 'kiba mara kyau! hakan bai dameshi ba saboda yasan magungunan da take shane suka hura ta yanzu zaman lafiya suke sosai a tsakaninsu ya daina yi mata wulakanci kamar lokotan baya.



Cikin shirin fita ya shiga ya sameni a kwance a gado kwana biyu duk na rasa gane abinda ke damuna kullum da zazzabi nake kwana ga yawan fitsari da nake, shigowarsa tasa na mike zaune.

Nace"Ka zauna mana mu gaisa." girgiza kansa yayi yana duba agogon hannunsa yace."Babu lokacin zama ina fata kin tashi lafiya.''?


'Dan ya mutsa fuska nayi nace"Lafiya lau zazzabi ne dai yake damuna kwana biyu kullum dashi nake kwana."


Tsira mata ido yayi na tsayin minti uku! da sauri yace."Dago ki kalleni." da sauri na kalleshi jin yanda ya fadi maganar! 'Kwayoyin idona ya tsirawa ido kafin ya wani murtuke fuska yace"Bude min tafin hannuwanki." Bud'e masa nayi ya shiga dubawa......."Sumayya watan ki nawa rabonki da al'ada."? gabana ne ya fad'i nace"Wata biyu da kwanaki."

Cikin tsawa! yace."Kin san da haka me yasa baki min magana tun wuri ba." nace"Wai duk me ya jawo wannan hayaniyar ne ciki ne dani ai kai baka isa ka hana Allah ikonsa ba duk dubarar ka kuwa."

Mari ya kwad'a min a zafafe! yace." Ni kike fad'awa wannan maganar." mikewa nai hannuna dafe da kuncina nace" Gaskiya d'aci gareta kai kuma baka so a fada maka dan ka mareni ba zan damu ba kuma insha Allahu komai abinka sai na haife cikin nan."


Zuciyarsa ta dinga tafarfasa yana ji kamar ya zare blet yayi mata dukan tsiya ashe dai yarinyar nan da gaske so take ta rugaza masa tsari! 'kwafa yayi ya kwashi wayoyinsa a fusace! yace."Mutukar kina bukatar zaman lafiya dani sai kin yarda da umarnina idan ba hakaba sai na wulakantaki."

Cikin dauriya nace"Duk abinda za kayi min a shirye nake dama ai na saba da wulakancinka ni ba zaka had'a kai dani gurin sa'bon Allah ba."

Kansa ya girgiza ba tare da ya sake magana ba ya fita daga dakin kamar zai tashi sama.

Tunda daga ranar ya dauke min wuta ya daina shiga sabgata koda a gurina yake baya ta'ba yarda muyi mu'amular arziki fuskarsa kullum a daure idan na gaishe ya amsa a dakile abincina kuwa inda na ajiye anan zan dauki abuna, gabad'aya ma ya daina kusantata yayi tsayin sati hud'u muna cikin wannan hali gashi kullum cikin ciwo nake babu ruwansa dani da lafiyata, ina kuka na sameshi yana shirin fita nace"Wai kai dan Allah baka da imani ne? me nayi maka kake azabtar dani haka? cikin nan fa bani na bawa kaina ba Allah ne ya bani me yasa kake gudun rahamar Allah? dubbanin mutane nacan na nema kai Allah ya za'be ka a cikinsu ya baka kana nema ka butulce masa kaji tsoron Ubangiji ka kar'bi kyautar daya baka watakilama shi kadai zaka haifa a duniya."

Hannu ya daga min ya juyo cikin shan toka yace."Sumayya ke kika zalinci kanki ciki kuma na bar miki kije ki haihu amma babu ruwana dashi."

Nace"Bangane babu ruwanka dashi kayi cikin kace ka bar min wannan wace irin magana ce." !?

Cikin wani irin yanayi yace."Sanin kanki ne bana zubar da k'wayoyin haihuwata a mahaifarki wannan dalilin yasa nace miki kije duk inda zaki da cikin ki."

Cikin fitar hayyaci nace"Aikuwa zani duk inda zani dashi zanje na shedawa Mammah duk halin da ake ciki nasan ita din cikakkiyar musulma ce ba zata yarda da wannan yahudancin ba."

Cikin tsantsar 'bacin rai yace."Sumayya kada ki fasa zuwa gurin Mamma da maganar nan wallahi kikaje kika tayar mata da hankali duk abinda ya biyo baya kada kiyi kuka dani." Yana 'kare maganarsa ya fice daga dakin a mugun fusace!! kwanciya nayi akan kujera na dinga kuka ina nadamar rayuwa ashe dai auran nan na tattare da babban kalubale maigirma mutum sai kace kafuri ya dinga gudun haihuwa kamar wanda bata wannan hanyar aka sameshi ba.....


*Na kudi ne..*!
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300....account... 0542382124.....Binta umar gtbank.....idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
99
Cikin nutsuwa na amsa sallamarta zama tayi kasan kujera ta ajiye kwandon dake a hannunta a kusa da ita Tace "Ranki ya dade barka da safiya." a nutse na amsa da fadin"Jakadiya kin tashi lafiya." ? da dan murmushi a fuskarta tace"Lafiya lau ranki ya dad'e dama Fulani ce tace na kawo miki wannan." kwandon data shigo dashi ta turo min gabana.
Nace"Nagode sosai." mikewa tayi da fadin"Ranki ya dade zan koma." nace"To jakadiya kice nagode Allah ya saka da alkairi." ta amsa "Insha Allah zan isar da sa'kon ki." bayan fitar ta na umarci Mariya data bude min kwanukan dake cikin kwandon, kwano daya farfesu ne sai tururi yake da alama ba'a jima da gamawa ba, kwano na biyu gurasa ce manya manya taji kantu! sai kamshi takeyi, a take naji ina sha'awar cinta da farfesun nace"Mariya kawo min ruwan tea na fara d'umama cikina kafin naci wani abun." da sauri tace"To ranki ya dade. " Dainng din ta nufa da sauri! ni kuma na cigaba da tunanin abubuwan da suka faru tsakanina dashi jiya daddare duk da bana cikin hayyacina na d'an fuskanci wani abu da yayi a lokacin da yake kokarin biyan bukatarsa, amma ba zan d'ora zargina akansa ba sai ya sake aikatawa tanan zan fahimci abinda yake nufi.


Tea din nasha sosai cikina ya warware, nasa tasa min gurasa biyu tasa min farfesun akai.........Nace"Mariya ku dauka kuje kuci." tace"Ranki ya dade mu mun karya wannan abincin naki ne na mussaman bai kamata muci ba.

Nace"Ai ni na baku ku dauka wannan ya ishe ni." Hannu tasa ta dauki kwandon da fadin"Ranki ya dad'e mungode kwarai hakika muna jin dadin yanda kike mu'amula damu munji dadin kasancewarki a matsayin uwargiyarmu." Murmushi nayi nace"Mariya kenan nima ina alfahari daku kuna kulawa dani yanda ya kamata kada ku damu da dukkanin abinda zanyi muku." Cike da jin dadi sukayi min sallama suka fita, girgiza kaina nai ina mamakin al'amarin wai yau nice a wani matsayi mai girma wanda banta'ba tsammanin kasancewa cikinsa ba, koda yake Ubangiji Allah babu yanda baya tsara lamarinsa........Bayan na kammala cin abincin da kaina na gyara gurin, na dauki wayata daki na shiga na kwanta a gado, number shi na kamo na tura masa text kamar haka.

_Yallabai ina fatan kaje asibiti lafiya? sannan ina rokon Allah ya kula da kai kamar yanda kake kulawa da masu bukata."_

Ina tura masa text din na ajiye wayar kusa dani, lumshe idona nayi ina janyo bacci da kyar naji ana buga kofar dakin, da sauri na mike zaune ina mamakin irin bugun da ake! anya kuwa! saukowa nayi da sauri ina fadin "Waye ne."'" ?


"Ke d'iyar bayi wato har tambaya kike waye ki bude kofar mana sai kiga ko su waye."!! da sauri na bude kofar! Hajiya Karima ce tare da wata mata mai qiba da alama kanwarta ce dan naga suna kama da juna.

Cikin fargaba nace" Hajiya barkanku da zuwa ku zauna mana." Tsaki taja ta matsa gefe guda tana watsa min harara!!

Lauratu itace ta 'karaso inda nake ta kalleni sama da k'asa yawun bakinta ta tofa min a fuska! kafin nai wani yunkuri ta tsinke sar'kar gold din dake wuyana!! hannu nasa na dafe kirjina ina mamakin abinda tayi! karfi tasa ta bugi! kirjina nayi taga-taga zan fad'i! da sauri na rike 'kofa( 'kyaure) ina kallonta....... hajiya Karima tace"Aa Laure banda duka kici mutuncinta nace kada ki doketa."

Laure tace"Hajiya ki kyaleni nayi 'kuli-'kulin kubura da yarinyar nan jiya da takaicinta na kwanta bacci wallahi tunda Lawisa ta kira waya ta tana kuka take sheda min cin mutuncin da Ali ke mata akan wannan 'yar iskar yarinyar nake Allah- Allah gari ya waye nazo naci ubanta! kina 'Yar bayi sama da 'kasa har kina da wata power kwace miji wato ke ga gwana kin cancad'a ado da gold kina zaune lafiya kin dasawa wata ciwon zuciyata to yau sai kin gaya min waye ubanki."!!! tana dukan kirjina take wannan maganar.....Hajia Karima tazo taja hannunta suka matsa gefe tace"Lauratu kada ki doketa bata isa ki had'a jiki da ita ba kawai ki nuna mata matsayinta."


Nace"Hajiya wai duk me ya kawo wannan abun me nayi muku ko kuma akwai wacce nake aure a cikin k.......Gwa'be min baki tayi da fad'in "Rufe mana baki fanko bud'add'an gwangwani! har kina da bakin magana wacce ta rako mata duniya." !!! Hawaye suka wanke min fuska, Hannu tasa zata fizge yarin kunnena na rike hannun tare da yarfar dashi!! cike da mamaki suke kallona!

Sunkuyawa nayi domin daukar tsarkata dake tsinke a k'asan gurin, da sauri tasa kafarta mai dauki da takalmi mai tsayi ta danne min hannu! rintse idona nayi ina jin wani irin zugi!! ciki zafin nama! na tureta tai taga-taga zata fad'i! kafin tayi wani yun'kuri! na kwad'a mata mari a kunci! a gigice! suke kallona! sabida gudun abinda zai faru yasa da azama na banke kofar dakin, key na murza na barshi a jiki kan gado na zube na dinga rizgar kuka ina jiyyar yatsun hannuna data mutsike min da takalminta.

'Karar waya ta dake daf da kaina yasa nayi gaggawar mikewa zaune wayar na laluba na dauka ina dubawa, gabana ne ya buga ganin miss call dinsa hud'u! da sauri na daga wayar tare da daidata nutsuwata a sanyaye nace"Hello." Yanayin muryarta yasa ya dan ji wani iri........."Sumayya lafiya dai ko.''? da sauri nace"Eh.''' Yace."Okey to me ya hanaki daukar wayata na kira sau uku kin duba ko kuwa kina sane."?

"Kayi hakuri wallahi bana kusa da wayar na barta a daki shiyasa yanzu ma na shigo daukar abu sai naga kiran ka."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Nifa yanayin muryarki yasa jikina mutuwa ina fata dai ba jikin bane." ? nace"Babu abinda ke damuna sai kasala ina fata kaga text d'ina."?

Murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunnena yace."Naga text dinki kuma naji dadi sosai dalilin daya sa ma kenan dana samu sukuni na kira wayarki na ji lafiyarki."


Murmushi nai ina kokarin kawar da damuwata nace"Nagode sosai amma dai kasha tea din kamar yanda kace."

Girgiza kanshi yayi yace."Har yanzu ban samu nutsuwa ba tukkuna zan nemi coffee nasha d'azu nace miki zan dawo kiyi hakuri bana jin zan dawo gida da wuri inada marasa lafiya sosai."

A sanyaye nace"Allah sarki mijina gaskiya bama kyautawa da muke barinka kana fita da yunwa dan Allah ka bari a kawo maka abinci."

'Yar dariyar jin dadi yayi yace."My love bana son wahalar dake shiyasa nace kisha magani ki kwanta ki huta! kada ki damu zan kira Mamma a waya insha Allah zata sa a kai min abinci."


Ajiyar zuciya na sauke nace"Har naji dadi a raina wallahi sam bana son zama da yunwar da kake bashi da amfani." Murmushi yay yace."Naga sai wani lalla'bani kike me zan samu idan na dawo."?


'Yar dariya nayi nace"Zan baka duk abinda kake so.' " cikin wani irin voice yace."Kinyi alkawari dik abinda na bukata daga gurinki zaki bani."?


Nace"Eh nai al'kawari." ajiyar zuciya ya sauke yace."To nagode kwarai sai na dawo." Ina kokarin magana ya kashe wayar, ajiyar zuciya na sauke na ji sanyi a cikin zuciyata waya ta dashi yasa na samu sassaucin bakin cikin da nake ciki bazan damu da duk wani cin fuska da wulakancin da zan fuskanta tunda mijina yana sona iyayensa suna kaunata to komai mai sauki ne kuma bana jin zan fad'a masa abinda ya faru yanzu zan bari idan sun 'kara sai na samu Mamma na fad'a mata nasan dole za tayiwa tufkar hanci.


Sai bayan isha'i ya shigo gidan kai tsaye gurin Lawisa ya nufa dan tun jiya rabon daya taka inda take......Tana zaune tayi ado sosai amma kallo daya za kayi mata ka tabbatar da cewa tana cikin fargaba da tashin hankali, abinda Lauratu kanwar mahaifiyarta taje ta aikatawa Sumayya shike damunta bata ta'ba tsammanin mahaifiyarta zata bada goyon bayan a rugaza mata zaman auranta ba......Tunda ya shigo take kallon fuskarsa bata hango 'bacin ran daya tsallake tunaninta ba, sakin ranta tayi tai masa barka da zuwa ya amsa yana bin falon da kallo, kanta ta sunkuyar da fadin"Kayi hakuri akan abinda ya faru jiya."

Shuru yayi bai tanka mata ba! tace"Dan Allah kayi hakuri." Yace."Magana ta wuce ina fata ki gyara halinki sai ki zauna lafiya dani! ajiyar zuciya ta sauke tace"Insha Allah zan kiyaye.....Mikewa yayi yace."Ni zan tafi sai da safe kenan." ta mike tare da rakashi bakin kofa har da cewa ya gaishe mata da Sumayya." yace "Zataji insha Allahu." Yana fita kai tsaye sashen mahaifiyarsa ya nufa domin su gaisa, ya jima a tare da ita kafin suyi sallama da juna.


Ado da kwalliyar da sameta dashi ya 'kyatar dashi mutuka ya dinga murmushi yana satar kallonta wai lallai shi ba zata kamashi yana kallonta ba, sai kauda kai yake amma daga ya samu faraga zai ta kallonta daga yaga sun had'a ido zai kauda kansa.....Sumayya dariya kawai take masa tana mamakin halinsa, tun bai gane ba har ya fahimci dariya take masa ya 'bata rai tare da ajiye cokalin hannunsa" Yace." Wato Kin samu mahaukaci kinsa a gaba kina dariya ko."? da sauri na had'a hannuwa cikin sigar bada hakuri nace"Dan Allah kayi hakuri kaci abincin nan ni bakai nakewa dariya ba." Harararta yayi yana sake release akan kujera yace."Sai dai kici kayanki na koshi."

Kamar zata fashe da kuka tace"Haba rabin rayuwata dan Allah kada kayi min haka ka daure kaci abincin nan dan Allah kaji."!!! a marairaice ta karasa maganar......Yana dariya yace."Sai kin maimaita sunan da kika saka min.

Da sauri nace"Rabin rayuwar Sumayya." wani irin kallon kauna yayi mata yace."Da gaske kike."? kaina na daga nace"Eh wallahi idan babu kai babu Sumayya." ji yayi kanshi na kumbura! ya dinga jefa mata kallon so yace."Ashe kin iya irin wannan kalaman shine baki ta'ba yi min ba."

Mirmushi nayi nace"Akwai wasu ma na mussaman kai dai kaci abinci zan fada maka su." Kamar wani shashasha ya dauki spoon din ya ciko da abinci yasa a bakinsa yana taunawa yana kallonta, dariya ta kusa sub'ce mata daka gani abincin yay yawa a bakinsa, tissue ta dauka tana goge masa inda ya 'bata

Ya sake ciko spoon har yana zubewa ya tusa a bakinsa yana taunawa yana kallonta! dariya tasa tana gumtse bakinta da hannunta....'Kwarewa yayi da sauri ta mi'ka masa ruwa ya kar'ba yasha ya ajiye cup din spoon din ya dauka zai sake d'ebo

Please Login or Register in order to submit comment