Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damunsa kullum idan zaici abinci sai yayi takaici da bacin rai dan Suwaiba sam bata iya girki ba wani sa'in inda ta ajiye abincin haka take zuwa ta tarar da abunta beci ba, wani lokacin kuma idan yaci loma daya yaji babu dadi kiranta yake yayi tai mata masifa irin wacce yake min akanta yake huce fushinsa, Suwaiba ta dinga data sanin zuwanta sashen dan komai tayi masa bata gwaninta.


Umartar Gimbiya Lawisa yayi data dinga kawo masa abinci dan baya tsammanin zai iya tunkarar mahaifiyarsa da maganar daina zuwa yarinyar yasan dole ta binciki dalili shiyasa ya kasa tunkararta sai ya Umarci gimbiya Lawisa da ta dinga kawo masa daga sashen su, Lawisa abin nema ya samu kullum xata zauna ta tsara masa girke girke safe da rana da dare ta barbade da maganin mallaka ta kawo masa sashensa, ta zauna yana ci suna hira babban burinta maganinta yayi tasiri a kansa, aikuwa ha'kan ta ya cimma ruwa dan yanzu sun daina fad'a yana nuna mata kulawa farin ciki tamkar ya kasheta......

Bayan wata biyu al'amura suna ta tafiya cikin nutsuwa yanzu na manta na daina fargabar abinda zai biyo baya tunda naga har an dauki tsayin wannan lokaci fulani bata kirani da wata magana ba sai hankalina ya kwanta sosai na cigaba da karatuna maganar auranmu da Haruna kuwa an tsayar da lokaci wata shida mai zuwa Mahaifina da Mahaifin Haruna har gaban Sarki sukaje suka sheda masa abinda ke faruwa, Sarki ya nuna farin cikinsa kana kuma yasa mana albarka.......Tsakanina da Haruna soyayya mai karfi ta sake 'kulluwa Bangaran Lahira kuwa abun nata sai a hankali dan daukar gaba tayi dani ta daina yi min magana, na tambayeta dalili taki fada min sai nima kawai na tattarata na watsar da ita na cigaba da sabgogina hankalina a kwance..


Bangaran Magajin Sarki kuwa sai godiyar Allah Cikin nasara da yardar Ubangiji ya fara aiki a asibitinsa yayin da jama'ar gari ke zirga zirga cikin asibitin domin nemawa kansu da 'ya'yansu lafiya kamar yanda ya fada a ranar Walima haka Asibitin na dauke da 'kwarrarun ma'aikata wa'inda suka san aikinsu wannan dalilin ya sanya hatta da manyan mutane masu kudi suke zuwa a dubasu a asibitin, alhamdulillhi bukatarsa ta biya ta kowane b'angare sai abu guda dake damunsa shine yanda zai tunkari Hadimarsa ya fada mata cewar ya yanke hukuncin auranta kamar yanda ta bukata ya amince zai aureta ita da Lawisa a rana daya, kullum da tunanin yanda zai tunkare ta da maganar yake kwana yake tashi gabadaya kunyar hada ido yake da ita sabida abin da yayi mata, amma yana ganin tilas yaje ya samu mahaifiyarsa ya shirya mata wata maganar akan rashin zuwan yarinyar gurinsa.


Karfe takwas da rabi na dare ya samu mahaifiyar tasa a kishingide akan dadduma ta idar da sallah tana jan carbi, a nutse ya zauna a gabanta tare da mika gaisuwarsa, ta amsa da fuska a sake tace"Babana aiki ya 'boye ka bana ganin ka a kan lokaci."
Murmushi yayi yace."Wallahi kuwa Mamma wannan dalilin yasa ma na yanke shawara cewa kullum kafin na fita zan dinga shigowa mu gaisa sabida wani lokacin bana shigowa gida da wuri sai can dare.

Tace"Aikuwa dai hakan shine daidai ina fatan komai yana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." Yace."Alhmdullhi mamma komai na tafiya daidai jama'a da yawa najin dadin alkairin da kukayi musu kullum cikin yi muku addua sukeyi." Murmushin jin dadi tayi tace"Alhamdullhi dama babban burinmu shine mu faranta ran mabukata kaima Allah ya saka maka da alkairi ya baka ladan abinda kake yi.".

"Ameeen Mamma na." Dakin ne yayi shuru na minti biyu kafin ya dago kansa a nutse yace."Mamma wannan yarinyar dake yi min hidima kwana biyu ta dauke kafarta ta daina zuwa ni ban san dalili ba rashin samun zama yasa ban shigo na sheda miki ba sai yanzu dana shigo gidan da wuri nace bari nazo na sheda miki halin da ake ciki ko zaki aika a kira ta gani gata gaki sai ta fad'i abinda akai mata ta daina zuwa tayi aikinta ."

Fulani mikewa tayi zaune tana kallonsa da mamaki a fuskarta tace"Babana har tsayin wane lokaci sumayya ta dauka bata tare da kai."?




*Na kudi ne*
Idan kika karanta baki biya ba Allah ya isa! idan kina so ki biya ga yanda abin yake...VIP gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
63&64
'Bangaran Yarima Ali kuwa al'amarin ne ya dinga bashi mamaki! kamarshi yarinyar nan ta fitar da hannu ta tsinka masa mari! wannan al'amari ya girgiza mutuka kaf a tarihin rayuwarsa ba'a ta'ba cin mutuncinsa kamar na yau ba amma babu komai yasan duk abinda ya faru shine ya janyowa kansa kamar yanda yarinyar ta fada kafin ta fita, yana ganin dole ya hakura da ita komai k'ulafucinsa kuwa tunda raini da wulakanci ya soma shiga tsakaninsu, lallai dole ya kafa tarihi da yarinyar dan tunda yake babu 'ya macan da ta ta'ba yi masa abinda ta aikata masa, mari!! abin ya bashi mugun mamaki ta yanda har ya rasa wane irin hukunci zai yanke akanta
........Yana ganin ko kawai yabi shawarar ta ta farko wato ya aureta tunda taki bashi hadin kai idan ya biya bukatarsa sai ya saketa dan shi abin kunya ne a gurinsa ace itace matarsa sam bata kai matsayin da zaiyi zaman aure da ita ba, amma dole zai zauna yayi nazari da tunani akan al'amarin yanzu babban burinsa ya wulakantata kamar yanda ta wulakanta shi ta mare shi ba tare da taji tsoron abinda zai biyo baya ba, da kyar ya iya barin falon duk jikinsa yayi sanyi nadama da kunyar hada ido da yarinyar duk ya dameshi.

Washe gari da zazzabi na tashi na dinga daurewa domin bana so iyayena su fahimci abinda ke damuna.

Muna gama karyawa na nemi guri na kwanta ina lumshe idona babu abinda ke damuna sai al'amarin daya faru jiya har yanzu na kasa yanke hukunci.

"Sumayya ya kika koma kika kwanta kuma ki tashi kiyi wanka ki shirya jikin ki yau ai kaya zamu sa masu kyau tunda Walima za'a gudanar.

Tambaya ce take wannan maganar a lokacin da take tsaye a kaina.

bude idona nayi ina kallonta, tace" Ki tashi ga ruwa can na dora nasan yanzu yayi zafi sai kiyi wankan'' nace"Sai fa sha daya na rana za'a zauna zaman Walimar." Tace''To idan kinyi wankan ai kin huta."
Mikewa zaune nayi ina gyara daurin dankwalina.

Tace"Kuma naga baki je sashen Yarima ba Allah yasa dai lafiya."Nace."Lafiya lau sai an dan jima zanje." Fita tayi daga dakin tana fadin"To ai sai kiyi maza kizo kiyi wankan kafin lokacin Walimar yayi kinje kin gama abinda zakiyi.

Mi'kewa nayi ina kokarin cire rigata gefe guda kuma ina mamakin yanda tambaya ta damu da dole sai nayi wanka na shirya nida zan samu yanda nake so wallahi ba zan fita ba balantana na ganshi gabad'aya ya fice min daga raina tausayinsa ma na daina ji sabida irin rashin kyautawar da yayi min jiya.


Daya daga cikin tamfofin da Fulani keyi min kyautarsu na dauko wata super mai ruwan ganye nasa a jikina, nayi mamaki sosai da dinkin ya zauna a jikina tamkar an auna ni.
Murmushi nayi a sanda na kalli mudubi naga yanda nayi kyau Atamfar ta haska ni

Zama nayi domin na gyara fuskata babana ne ya shigo fuskarsa cike da walwala da farin ciki yace."Yawwa Sumayya ki shirya sosai ga 'yan uwanki can kowacce tayi ado inaso ki zama tauraruwa a cikinsu.' cikin tsokana yake maganar

Dariya nasa nace"Baba kenan ashe kana so nayi kyau nafi kowa ko."? da mirmushi a fuskarsa yace."Eh mana ai kowa nasa ya sani." murmushi nayi nace"To kaima sai ka shirya mu fita tare." Yace."Ke dai ki fara fita nida mahaifiyarki zamu biyo bayanki."
Nace"To shikkenan baba yanda kace haka za'ayi......Kwalli na zirara a idona na shafa hoda sama-sama! sai nasa man le'be kadan a fuskata kana na hada kayan kwalliyar naje na ajiye.

Ina kokarin nade lifaya a jikina Tambaya ta shigo dakin....gani nayi ta tsaya tana murmushi, na saki fuskata ina dariya nace nayi kyau ne."? Kanta ta daga tace"Sosai kuwa idan zaki futa kiyi addua saboda bakin mutane." Dariyar maganar ta bani nace"To shikkenan zanyi insha Allah.

Tsakar gida na fito da mudubi a hannuna ina dubawa, gaskiya nayi kyau ni kaina nasan hakan, ajiye mudubin nayi kan taga nace"To Tambaya ni na fita sai kun fito." Tana daga daki tace"to shikkenan."

Koda na fito ban zarce gurin Walimar ba sai dana na biyawa Lahira na sameta a tsaye da mudubi a hannunta tana gyara daurin dankwalinta, wani irin kallo naga tabi ni dashi a take yanayin fuskarta ya sauya naso na fahimci wani abu...."Lallai Sumayya kece kikayi kyau haka."? abinda tafada kenan tana kallon sutturar jikina.

Yar dariya nayi ina duba jikina nace"Haba Lahira wane irin kyau banda zagi dai." Ta'be baki tayi ta cigaba da gyara daurin dankwalinta sosai abinda tayi ya bani mamaki na hango hassada da ganin kyashi a idonta.

Lami mahaifiyarta ce ta fito daga daki sai naga itama ta saki baki tana kallona, cikin sanyin jiki na tsuguna har kasa na gaisheta, bata amsa ba sai kumbura fuska takeyi tace"Ke Sumayya waye ya baki wannan kayan ni dai in banda ke banta'ba ganin wata baiwa tasa irin wannan sutturar ba.''

Wasa na shiga yi da hannuwana nace"Wallahi Mamma Fulani ce tayi min kyautarsu kin san ni nake kula da Yarima ta fanni abincinsa jin dadin yanda nake bashi kulawa yasa tayi min kyautar sutturu harda zoben gold."

Lahira da mahaifiyarta suka saki baki suna kallona kafin su mayar da hankalinsu kan zoben dake hannuna! Lami tsaki taja tayi gaba ba tare da tace komai ba, kallo na bita dashi ina mamakin abinda ya janyo haka.

Lahira kuwa gani nayi idonta yayi jawur kamar wacce tayi kuka duk sai naji banji dadin hakan ba, daurewa nayi nace."Lahira idan kin gama kizo muje mu samu gurun zama kada guri ya cika da jamaa mu tsaya a tsaye kinsan ni bana jurar tsayuwa.

Fitowa tayi daga dakinsu tana yafa mayafi ba tare data kalleni ba tace"Muje.'' bayanta nabi ina dana sanin biyo mata dan dana san zata nuna min hassada to da sai dai ta same ni a can..........."Sumayya da gaske ne auranku da Haruna."? Katsaham naji ta jefo min wannan tambayar....ajiyar zuciya na sauke nace"Eh mana ko haruna nada wata illar ne."
Ta'be baki tayi tace"Babu." dauke kaina nayi ina jin haushin abunda take yanzu na gano Lahira da zuciya biyu take zaune dani tunda gashi nan tana nuna min bakin ciki.

Koda muka isa gurin taron samunsa mukayi a ciki da kyar muka samu gurin zama muka zazzauna muka cigaba da jiran fitowar Sarki da tawagarsa shi kansa wanda ake gabatar da Walimar dominsa bai fito ba. amma kuma manya bakin sun fara zuwa an tanadar musu gurin zamansu na mussaman.

Mun kai kusan mintina arbain da zama kafin Maimartaba ya fito da tawagarsa, gurin ne ya hautsine da bushe bushe gami da hayaniyar jama'a kullum idan Sarki zai fito jama'a nunawa suke kamar basu ta'ba ganinshi ba, da kyar aka samu gurin yayi lafiya, Sarki ya zauna a mazauninsa 'yan uwansa suka zauna kusa dashi, can gefe guda kuma Yarima Ali ne dashi dasu Shatima sun sashi a tsakiya sunsha kwalliya da kayan sarauta amma nashi na mussaman ne dan ba karamin kyau yayi ba yana sanye da farar shadda sai ya dora bakar alkyabba a jikinsa, gaskiya wanda ya nad'a masa nad'in dake kanshi gwani ne dan ya fito dashi sosai kuma nad'in yayi masa kyau mutuka! kamar koda yaushe fuskarsa a had'e babu fara'a jefi jefi yake kallon jama'a gabadaya ya kasa sakewa a gurin sabida rashin san mutane

Malam Ahamad Sulaiman shine ya gabatar da karatun al'akurani mai girma gurin yayi tsit har malam ya gama karatun kana ya bude taron da addua. Maimartaba yayi jawabin godiya ga jama'ar da suka samu damar hallartar taron sannan yayi addua tare da fatan kowa ya koma gidansa lafiya.
Bayan ya koma gurin zamansa, Waziri ya fito yayi nasa jawabi Bayanshi Galadima Yayi Ciroma yazo yayi nasa dukkaninsu sun danne bakin cikin dake cikinsu suna ta fara'a gami da nuna farin cikinsu.

Koda Yarima Ali ya taso domin yin nasa jawabin gurin ne ya hargitse da hayaniya, sai da masu kula suka tsawatar tukkuna aka samu lafiya, dago kansa yay an samu ya dan saki fuskarsa ya daga hannuwansa sama alamun gaisuwa ga tarin jama'ar dake gurin, gurin ya sake rikicewa kowa na fadar albarkacin bakinsa, zuciyoyin Ma'kiya kamar su buga saboda ganin yanda Jama'a ke nuna kaunarsu akan Ma'kiyinsu.......Shima nasa 'bangaran yaji dadi sosai da yanda jama'a ke nuna masa kauna dalilin da yasa kenan ya sassauta fuskarsa ya dinga d'aga hannuwansa sama yana sakin murmushin farin ciki...Dauke kaina nayi daga kallon fuskarsa dan ni duk mubayar da jama'a ke masa ba burgeni suke ba, da sun san waye shi da duk basu yi masa ihu gami da fadin sai yayi ba, gabadaya ma ni ji nayi zaman gurin ya isheni kallonsa ko jin muryarsa na tayar min da bacin rai.
Tsaki naja lokacin dana ji miryarsa yana fadin"Alhamdullhi Allah kaine abin godiya daka nuna min wannan rana mai albarka wannan rana r ba zan ta'ba mancewa da itaba a cikin kundin tarihin rayuwata saboda rana ce mai muhimanci a gareni daku baki daya nagodewa Allah na kuma godewa mahaifina wanda ya zama silar samuwa ta a wannan duniya, mahaifina ya taka muhimiyyar rawa a tare dani ya tsaya min akan dukkanin al'amurana na yau da gobe tun ina yaro yake dawainiya dani har na kai wannan matakin dana ke kai a yanzu.....Naje america nayi karatu mai zurfi dan na taimaki kaina da al'ummar musulmi alhamdullhi yau wata na hudu da dawowa gida duk wani hutu dana ke bukatar nayi na samu insha Allahu ranar monday litinin kenan zan fara aiki a sabon asibitina mai musa *Zinariya Hospital* asibitina ya kasance kyauta ga duk masu wa'innan lalurorin da zan lissafo.".. ...........Jin wannan magana tasa yasa jama'a da yawa suka mayar da hankalinsu kansa suna sauraransa.
Yarima Ali ya cigaba da cewa." Idan akwai masu fama da matsalar hawan jini Sugar ciwon qoda ciwon hanta cancer duk suna iya zuwa asibitina a sati mai zuwa domin su fara kar'bar magani, sannan akwai 'bangaran mata masu cika da masu haihuwa akwai bangaran yara masu fama cutar sikila asma nimonia da sauran cutukan dake dake addabar yara a kananu idan d'anka ko 'yarka na fama da daya daga cikin wa'innan cutukan dana lissafo to sai ka maxa ka garzaya dashi asibiti a sati mai zuwa insha Allahu za'a dora shi kan maganin daya dace, akwai likitoci na mussaman da muka tanada domin duba marasa lafiya amma duk da haka muna bukatar karin wasu kananun ma'akaita saboda haka dik wanda ke bukatar mu daukeshi aiki sai yazo mana da takardunsa a cikin satin da zamu shiga insha Allahu idan mun duba cancanta da nagartarsa zamu daukeshi aiki domin ya taimaki kansa kuma ya taimaki al'umma da ilimin da Allah yayi masa, wannan shine takaitaccan jawabin da zanyi!.'" Yarima Ali na gama jawabinsa guri ya hautsine jamaa suka dinga murna da farin ciki jin abin alkairin da suka samu. da kyar aka samu gurin yayi shuru, Maimartaba tsabar farin ciki kasa cewa komai yayi sai mirmushi yake yi, Waziri na taya shi, Bangaran su Ciroma kuwa tamkar zuciyarsu zata fito waje saboda haushi da takaici...Muddibo kuwa tashi yayi ya bar gurin can bangaran Uwargida Huwaila ya nufa, nan ya samesu sunyi jugum! abin duniya ya ishe su Aunt Safiyya da Aunty Bushira sai kuka sukeyi suna fad'in su basu yarda da wannan kyautar da Sarki yayi wa Yarima Ali ba kyautar Asibiti gari guda su suna zaune ko tsinke bai basu ba dan haka wallahi ba zasu tafi ba sai ya shigo gidan suma yayi musu kyautar filaye ko gidaje.,....


*Na kudi ne..!*
Kika karanta baki biya ba Allah ya isa! idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake...Vip group #600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
69&70
Gabad'aya tsarguwa nayi da yanayin kallon da mutane suke min bina suke da kallon zargi da tuhuma sun had'a rukuni rukuni suna surutai a kaina kowa dai da abinda yake fad'a dangane da faruwar al'amarin, can gefe na hango iyayena cikin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali Tambaya sai hawaye take sharewa babana ne mai karfin halin danne abinda ke zuciyarsa amma kallo guda za kayi masa ka gane cewar yana cikin tashin hankali......Zuciyata ce ta sake karyewa zafafan hawaye suka zubo min da sauri nasa hannu na goge nayi kasa da kaina gami da cigaba da bin bayan jakada zuciyata cike da wasiwahsin abinda zanje na tarar a fadar sarki, duk nasan ina da gaskiya amma zuciyata ta kasa tsayawa guri d'aya sai sa'ke-sa'ke takeyi min dangane da abinda ya faru.

Ganin Maimartaba a tsaye yana kai komo yasa naji gwiwata ta sage, a sanyaye na zube a kasan gurin murya na rawa nace"Ranka ya dad'e barka da wannan lokaci ina rokon Allah ya ja zamanin ka ya kara maka lafiya da nisan kwana." Zama yayi kan kujerarsa ya tsira min ido, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da yatsun hannuna. Maimartaba kallon yarinyar yake yi yana mamakin abinda ta aikata masa a masarauta dole ne ya binkiceta domin sanin wanda ya sata zubawa d'ansa guba mai karfi a cikin abinci."

A nutse yace."Yarinya ya sunanki."? Kaina a kasa nace"Sunana Sumayya Lawi. kallona yake yana girgiza kansa, Yace."Yanzu na samu labarin abinda ya faru a bangaranku ina so ki fada min gaskiyar magana."

Hawaye ne suka zubo min da sauri nasa hannuna na goge wasu suka sake zubowa. gyaran mirya yayi yace."Ba kuka nace kiyi ba kiyi min bayani akan irin gubar da kika zubawa d'an uwanki musulmi."

Muryata na rawa nace"Ranka ya dade na rantse da wanda raina yake a hannunsa ban sawa kowa guba ba." Shuru yayi na minti biyu kafin yace."To kinyi rantsuwa da Allah Sumayya kin san Allah ba abun wasa bane idan baki sa musu guba a abinci ba ya akayi bayan sunci abincin da kika basu suka fita daga hayyacinsu."

A sanyaye nace"Naje sashen Yarima domin nayi ayyukan dana saba sai na tarar da Suwaiba tana soya doya da 'kwai Yarima ya shigo kicin din ya sallameta yace ba zai zauna ya ci komai ba saboda ya makara a gurin aiki, ganin kada ayi asarar doyar yasa na juye a cikin kula na kawowa su Haruna daga nan na wuce gurin karatu ina zaune a cikin 'yan uwana malam ya shigo ya fito dani yana tuhumata akan wannan dalilin daya faru Ranka ya dade wannan shine iyakacin abinda na sani."

Shuru fadar tayi Maimartaba yana nazari akan maganar da nayi, yace."Me ya hanaki cin doyar bayan kema kina bukata." Jin abinda yace ya sanya gabana faduwa, cikin mika lamura na ga Allah nace"Lokacin ina sauri na shiga karatu shiya banyi tunanin tsayawa naci ba." Girgiza kansa yayi kafin ya kalli Jakada dake tsaye a bakin kofa yace."Kaje da yarinyar can cikin gida ka rufeta a dakin duhu gabad'aya hujjojin da ta kawo basu gamsar dani ba ina ganin idan taji matsa zata fada min yanda al'amarun suka faru."

Kuka na fashe dashi nace"Ranka ya dade wallahi tallahi iya gaskiyata na fada maka ban san komai ba akan faruwar wannan al'amari ranka ya dade ka yarda da rantsuwata."


Babu yabo babu fallasa yace."Kwantar da hankali binkice zanyi akan al'amarin idan na gano gaskiya zansa a fito dake." Gwiwa a sanyaye nace"Godiya nake ranka ya dade ina rokon Allah ya bayyana mai gaskiya akan faruwar wannan al'amari." Ameeen yace ya bawa Jakada umarnin tafiya dani dakin duhu.


"Ya sunanki."? Suwaiba dake gurfane tana shar" ba gumi tace"Sunana Suwaiba Munzali." Maimartaba yace."Ke kika soya doya a bangaran Yarima ko."? da sauri tace"Eh nice ranka ya dade." Yace."Waye ya baki guba kisawa Yarima a cikin abincinsa." Suwaiba hannu tasa ta sharce gumin goshinta cikin inda inda tace "Ranka ya dade babu kowa." Yace."Sumayya ta tabbatar min da cewa kece kika soya doyar ta shigo ta sameki kina aiki kafin Yarima ya sallame ki bana son kiyi min gardama akan abinda na tambayeki inaso ki fada min gaskiyar abinda ya faru.''

Suwaiba kuka ne ya 'kwace mata jiki na kyarma tace"Wallahi babu kowa ranka ya dade ni dai nasan na soya doya da kwai amma bansan abinda ya biyo baya ba."

Shuru yayi yana kallonta babu shakka yaran naso suyi masa wasa da hankali a cikinsu dole a samu mai gaskiya da mara gaskiya dan haka itama Suwaibar tunda ta'ki fada masa gaskiyar magana sai kawai ya umarci Jakada da ya kaita dakin duhu inda yasa aka kai Sumayya.


Mun jima muna kallon junanmu cikin yanayi na tashin hankali da damuwa nace"Suwaiba ashe baki ji maganata ba sai da kika janyo mana shiga masifa yanzu meye ribarki a duniya idan aka hada baki dake aka kashe rai me zaki ce da Ubangiji a ranar lahira."

"Ke kinga Sumayya kada ki d'ora min sharri dan sabida kinga ta kwa'be dake a ciki shine zaki ce naji tsoron Allah to idan banji tsoransa ba tsoranki zanji mtssw! dan Allah kada ki sakeyi min wannan maganar dan ni ban zubawa kowa guba a abinci ba kije ki tuhumi kanki."

Tsabar haushi da takaici kasa cewa komai nayi ina kallonta sai surutai take tana fuffukar karya nace"Shikkenan tunda kin k'aryata kanki akan abinda kika aikata insha Allahu a yau sai Allah ya tona muku a siri keda wa'inda suka saki."

"Sai dai Allah ya tona miki asiri banza kawai! kece baki da tabbas amma ni na tabbata ba zan kwana a gurin nan ba za'a fito dani banza kawai."
Shuru nayi mata ina jinta tana zagina gami da fadin na zuba ido na gani sai an fita da ita daga gurin an bar ni a ciki.

Gefe guda na samu na karkade kurar dake gurin na zauna ina bin dakin da kallo, tabbas ya amsa sunansa dakin duhu babban daki ne wanda yake da taga d'aya itama yar mitsitsiya kuma acan sama take, ta wannan tagar haske yake dan shigowa, idan mutun na dakin baya gane yanayin gari safiya ko dare sai dai kawai kaji kiran sallah yanzu ma hakane ya kasance ina zaune a gefe Suwaiba na zurga zurga a dakin mukaji kiran sallar magariba na mike tsaye na isa bakin kofar fita, kofar na dinga jijjigawa rufe take gam ko motsi takiyi, juyowa nayi cikin rauni da sarewa da al'amarin muka had'a ido da Ita gani nayi tana share hawaye nace"A'a ya kike kuka keda kikace baki da damuwa."
Tsaki taja ta koma jikin bango ta jingina, girgiza kaina nayi naje na zauna a inda na tashi, addua na cigaba dayi a cikin zuciyata

Motsin bude kofar mukaji da sauri na mike tsaye Suwaiba kuwa har ta kai bakin kofar tana zazzare ido.

Wani babban bawa ne ya bude kofar duk muka zuba masa ido muna kallonsa, gefe ya matsa yana me yin kasa da kansa, Muddibo ne ya shigo dakin, gabana ya yanke ya fadi ganin yana watsa min wani irin kallo, sunkuyar da kaina nayi, ya kalli Suwaiba da fadin"Biyo bayana." Da sauri na dago kaina naga Suwaiba da sauri tabi bayansa nima sai na rufa mata baya, tana fita nayi yunkurin bin bayanta mari ya kwada min ya tankad'ani ciki faduwa nayi kaina ya bugu da wani babban dutse dake girke a gurin, dishi dishi na dinga gani kafin na fadi a gurin, Muddibo umartar bawan yayi da yayi maza ya kulle dakin..........


Magajin sarki ya shiga tsananin rudani a lokacin da aka kai masa manya hadiman sa a sume a take ya shiga basu taimakon gaggawa da irin baiwar

Please Login or Register in order to submit comment