Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to duk matakin da hukuma zata dauka a kansa daidai ne saboda haka yanzu zan sa aje fada a sanar da mahaifinka cewa yazo shida 'yan uwan nasa a zauna ayi magana." girgiza kansa yayi yace."Hakan yayi yana da kyau kowa ya sheda cewa Muddibo shine wake d'aya a cikinmu ke Sumayya ki nutsu sosai duk wani abu da kika san ya faru to kiyi bayani yanda kowa zai fahimta, kaina na daga gabana na wani irin faduwa.

Fulani wayarta ta dauka ta kira jakadiyarta tace maza taje fada ta sanar da Maimartaba tana da magana dashi da 'yan uwansa su Waziri.'' Jakadiya da sauri ta amsa ta mike ta fita.


Ya kalli mahaifiyar tasa a nutse yace."Mamma inaso Yarinyar nan ta zauna a gurinki bana bukatar ta sake koma sashen su har abada ta bar gurin sai dai taje da niyyar gaishe da iyayenta.

Murmushi tayi tace"Babana babu damuwa Sumayya zata zauna a gurina har zuwa lokacin da za'a daura muku aure.''' Yace."To nagode kwarai da gaske Mammana." Falon ne yayi shuru kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa, ni dai gabad'aya hankalina a tashe yake ina tsoron abinda zai faru idan jama'a suka sheda cewa Muddibo shine yake farautar d'an uwansa shin idan kowa ya yarda da maganata iyayensa zasu yarda kuwa? wace irin fahinta zasuyi min......shigowarsu falon yasa hankalina ya dawo daidai lokaci guda na shiga nutsuwata kaina a kasa, na gaishesu, Maimartaba ya dinga kallona yana girgiza kansa, a nutse ya kalli yaron nasa da fadin"Ina fatan yarinyar nan bata hadu da wata matsala ba."?


Yace."Ranka ya dade Allah ya kiyaye bata samu rauni mai muni ba amma hakika wanda ya aikata mata wannan mugun abu ranta yaso ya d'auka.'' Waziri yace."Subahannallahi! wai shin ke Sumayya ya akayi al'amarin nan ya faru dake muna so kiyi mana bayanin komai."

Mamma tace"Eh shine ai yasa na tura nace kuzo dukkaninku dan mu tuntuni tayi mana bayani kuma mun gamsu mun yarda da cewar yarinyar nan ba zata 'kir'kiri karya domin ta d'orawa wani sharri ba, a gaskiya idan kukaji wanda ya aikata mata wannan mugun abu sai kunyi mamaki amma inaso kafin ta fara bayani maimartaba ya bada umarnin kiran iyalan 'yan uwansa."

Maimartaba yace."Fulani maganarki tayi ma'ana yana da kyau Huwaila na gurin nan yana da kyau Hajiya Karima na gurin nan yana kuma da kyau ace Hajia Kubra da Falmata na gurin nan domin kowa yaji bayanin da wannan yarinya za tayi."


Gabad'ayansu suka amince da maganarta, da sauri ta kira Jakadiyarta tace maza taje ko wane sashe tace maimartaba nada bukatar ganinsu domin tattauna muhimiyyar magana." Jakadiya da sauri ta tafi cika umarni.

Shuru falon yayi bayan kowa ya hallara, Maimartaba ya kalleni a nutse yace."Sumayya dukkaninmu ke muke saurare muna bukatar muji komai daga gurinki."

Ajiyar zuciya na sauke a hankali na dago kaina sai naga dukkaninsu sun zuba min ido yanayinsu ya nuna min cewa ni suke saurare.


Kaina na sunkuyar cikin nutsuwa na fara magana.......................'Karya kike munafuka."!! Hajiya Karima ce ta katseni tana wani irin huci! ta mike tsaye tana nuna ni da hannu 'Karya kike algumguma! kice Muddibo shine wake d'aya 'bata gari! a masarauta me Magajin sarki yayi wa Muddibo da zai kasheshi."!?? Maimartaba ya buga mata tsawa! Mijinta Ciroma shine ya zaunar da ita gumi! sai karyo masa yake, Hajiya Karima ta koma ta zauna tana muzurai idanunta sunyi jajawur saboda tsananin tashin hankali.


Sai da kowa ya samu nutsuwa tukkuna maimartaba ya umarceni dana cigaba da maganata, Na cigaba da cewa"Ranka ya dad'e na rantse da wanda raina yake a hannunsa wannan maganar dana fad'a ba karya bace Muddibo shine ya tareni cikin dare bayan fitowa ta daga sashen Yarima, ya umarceni dana kar'bi magani lallai yana so na zubawa Yarima a lemo ya kuma tabbatar min da cewa mutukar na sake lalata musu aikinsu akan Yarima to sai ya kasheni, koda na kar'bi maganin a hannunsa sai na kwance na watsa masa shi a fuskarsa, na tabbatar masa da cewa ni ba za'a hada baki dani akashe mai rai ba! kafin nayi wani yunkuri ya dauki wani dutsen wuta dake gurin ya tad'e kafafuna na fadi a gurin kawai ya dinga buga min a kaina ina karewa , sawun mutane yasa ya jefar da dutsen ya bar gurin......to tun daga sannan ban san inda kaina yake ba."


Maimartaba yayi shuru yana girgiza kansa gabadaya yanayin fuskarsa ta sauya da zallan 'bacin rai! Ya kalleni a nutse yace."Sumayya koda ba kiyi rantsuwa da Allah da mazon sa ba, na tabbatar da cewa ba zaki zauna ki shirya wannan maganar ba, Tabbas ni na amince da maganarki Muddibo zai iya aikata wannan abu saboda wata manufa tashi." Ya kalli su Waziri da duk fuskokinsu suka nuna alamun alhini da tashin hankali mussaman Ciroma da duk ya muzanta a gurin sai gumi yake idanunsa sun kada sunyi jajawur saboda tashin hankali!

Maimartaba yace."Inaso gabad'ayan ku ku amince da maganar yarinyar kada wanda ya saka kokwanto a cikinta yarinyar nan Sumayya ni na amince da cewa ba za tayi wa muddibo k'arya ba sannan kuma inaso dukkaninnku ku kauda kanku akan irin hukuncin da zan yanke a kansa mutukar hukuma ta tabbatar mana da gaskiyar magana a kansa."


Hajiya Karima ta fashe da kuka mai tsanani! tace"Ranka ya dad'e ka tsaya ka nisa tukkuna kayi binkice akan wannan al'amari wallahi na tabbatar Muddibo ba zai aikata wannan mummunan akin ba a duniya me magajin sarki yayi masa da zai kashe shi, ranka ya dad'e ka duba maganata."

Maimartaba yace."Karima ki kwantar da hankalinki kamar yanda Magajin sarki ya sheda mana cewa yanzu haka Muddibo na hannun hukuma to ba zamu yanke hukunci ba sai mun tabbatar da gaskiya kan maganar saboda haka ki daina kuka kina tashin hankalinki dole Masarauta ta nuna fushinta akan abinda ya aikata.


Da bakin zaninta ta fyace hanci ta kalli Magajin sarki murya na rawa tace"Ali dan Allah kayi hakuri da wannan al'amari kada fa ka manta Muddibo dan uwanka ne tare kuka taso kuna kaunar junanku idan binkice ya tabbatar da gaskiya a kansa to ka yafe masa abinda ya aikata maka.


Yace."Hajiya kiyi hakuri wallahi idan ni Muddobo ya bugawa dutse ya fitar min da jini zan k'yaleshi saboda dangatakar dake tsakanina dashi, amma ki sani ba zan iya hakurin ganin ya zubarwa da wannan baiwar Allah jini na kyaleshi ba haki'kanin gaskiya sai nabi kadin jininta."


Falon yayi shuru kowa yana mamakin maganarsa, ya kalli mahaifinsa a nutse yace."Ranka ya dade wannan yarinya sumayya nayi alkawarin aureta a cikin satin nan nake so a daura min aure da ita inaso gabadayan ku kusa min albarka a cikin aurena da ita." Maimartaba da Waziri fuskarsu ta fad'ad'a da farin ciki suka dinga fatan alkairi a ciki, Ciroma da Galadima kadarah kadahan sukayi magana akai, ita kuwa Hajiya Karima tashin hankali biyu ne ya had'e mata Yarima zai auri baiwa kafin ya auri 'yarta sannan yasa an d'aure mata gudan jininta Muddibo! rai a mugun 'bace! ta mike ta fita, dukkaninsu suka bita da kallo suna girgiza kai......Hajiya Huwaila da yake tana da wayo da siyasa kwata kwata bata nuna wani alamun da zai nuna cewa bakinsu daya da Muddibo ba, cikin nuna farin ciki takeyin fatan alkairi kafin ta tafi........Ciroma kuwa ya jima yana jajanta al'amarin kafin ya mayar da komai ba komai ba a zahiri kenan a bad'ini kuwa shi kad'ai yasan abinda ya kudirta, ya kalli Magajin sarki da fad'in "Inayi maka fatan alkairi a rayuwarka ina kuma baka hakuri a bisa wannan abu da ya faru da kai da dan uwanka sannan kuma inaso na jaddada muku cewa duk wani mataki da hukuma zata dauka akan Muddibo bana bakin ciki da hakan mutukar binkice ya tabbatar mana da gaskiya to ina mutukar farin ciki da umarnin da maimartaba zai yanke a kansa." Maimartaba ya dafa kad'arsa cikin taushin murya yace."Inaso ka kwantar da hankalinka akan wannan abu insha Allahu hukuncin da zamu d'auka akan Muddibo zai zama izina ga masu mugun hali irin nashi.



Muddibo na ofis d'insa sakatarensa ya shiga ya sheda masa cewa yana da baki, kai tsaye yace ya shigo dasu, koda yayi tozali da Acp da sauran jami'ai sai yaji tsoro amma da yake 'kwaro ne sai ya dake! ya nuna musu gurin zama da fadin"Bisimillahi ku zauna." Acp ya girgiza kansa da fadin"Ba zama ne ya kawo mu ba, munzo domin mu tafi dakai." Cike da mamaki yake kallonsa kafin yayi murmushin gadara yace."Akan wane dalili zaku tafi dani Acp me na aikata.''
Acp ya murtuke fuskarsa yace."Muddibo ka aikata mummunan ayyuka ciki kuwa har da yun'kuri kisa."

Muddibo gabansa na bugawa yace."Acp wannan wace irin banzar magana ce? mikewa yayi tsaye cikin hayaniya ce "ku fitar min daga ofis."

Acp ya gyara tsayuwarsa da murmushi a fuskarsa yace."Wannan hargagin da kake da yanayin yanda fuskarka ta nuna ya tabbatar mana da cewa kaine ka aikata abinda muke zarginka dashi."

Muddibo zufa! na keto masa yace."Wai shin Acp wane irin sharri kuke so ku laqaba min ne? wa na kashe da kuke zargina da aikata ta'addanci irin wannan."?


Acp ya kalleshi sosai yace."Kayi yunkurin kashe baiwar gidanku wato sumayya saboda ta'ki kar'bar umarninka."!


Muddubo zabura! yayi yana nunashi da yatsa baki na rawa yace."Acp ka kiyaye harshenka ka daina jifana da wannan munanan kalaman."

Acp ya kalli na kusa dashi cikin bada umarni yace."Ka daure masa hannu muje station idan yaji mazga! zaiyi mana bayani."


Da sauri suka nufeshi, muddibo ya dinga zare ido jikinsa na kyarma gumi! na keto masa, yau shi za'a daurewa hannu!!! yana dan mulki dan sarauta kafin ya ankara yaga sun kamo hannunsa duk biyun ya dinga fizgewa suka rike da kyau suka daura masa ankwa.


Acp yazo ya cire hular dake saman kansa ya ajiye, botiran rigarsa ya cire yace."Ku fita dashi." Muddobo turjewa ya shiga yi bakinsa na rawa yace."Acp ni zaka ciwa mutunci a gurin aikina.''? Acp yace."Kaga Muddibo bani da wata magana da kai muje station kawai dukkanin bayanai suna can.

Muddibo yace."Babu inda zanje wallahi." yafada yana turjewa, Acp wani bahagon mari! ya kwada masa! hancinsa ya fashe ya fara d'igar jini! a harzuke! yace."Muddobo bana san gardama muje station kawai." Muddibo idanunsa sukayi jajawur ya dinga kallon acp din yana mamakin marin daya kwada masa! Acp cikin wata irin tsawa! yace."ba za ka tafi ashe sai na kwance blet kenan."? cikin tsantsar takaici da tashin hankali ya soma tafiya, jami'an suka rirrike kafad'unsa, a haka suka fito daga ofis d'in, cikin tashin hankali jama'ar dake zaune a reception din suka mike tsaye suna kallonsu har suka fita, wasu daga cikinsu har bakin mota suka rakosu, sai da suka ga motar police din ta fita daga ma'aikatar sannan suka koma ciki suna mamakin abinda yake faruwa..........




*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya kudi...keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...binta umar gtbank...idan kati zaki turo..#400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
87
Acp suna isa station yasa aka rufe Muddibo a cell ofis d'insa ya shiga ya zauna a kan kujera yana godewa Allah. Hakika samun nasarar dam'ke Muddibo babbar nasara ce a tare dasu, wayarsa ya dauka cikin nutsuwa ya nemi number Magajin sarki ya kirashi ya sheda masa cewa Muddibo na hannu a halin da ake ciki, a nasa 'bangaran ajiyar zuciya ya sauke yace."Alhmdullhi Acp gani nan zuwa insha Allah." Sallama sukayi ya kashe wayar yana kallon mahaifiyarsa, yace."Mamma ni zanje station domin ina bukatar naji komai a daga bakinsa, Tace."To babu damuwa babana Allah ya tsare.'' yunkurin mikewa yay ya kalleni da fadin"Idan kinci abincin rana kisha magani kinji ko." kaina na daga, cikin sauri ya fice daga falon, ajiyar zuciya na sauke ina kallon 'kasan gurin, gabadaya hankalina yana kan iyayena su kawai nake da bukatar gani...."Sumayya kina bukatar hutu saboda haka bari na kira jakadiya tayi miki jagora daki ki kwanta ki samu nutsuwa." Jin abinda tace yasa naji kamar na fad'a mata abinda ke damuna, shuru nayi ina jin nauyin fad'a mata, wayarta ta dauka ta kira Jakadiya, ta shigo da sauri tare da gurfana a gabanta, tace"Jakadiya kuje da Sumayya wancan dakin dake kusa da gurin cin abinci ki gyara dakin sosai idan da akwai abinda ake bukata sai kiyi min magana." Jakadiya tace"To ranki ya dade.'' Ta kalleni cikin kauna tace"Sumayya tashi kuje kinji ko kiyi wanka ki gasa jikin ki kafin ki kwanta ki huta." Yun'kurawa nayi domin tashi nace"Ranki ya dade godiya nake Allah ya kara girma." mirmushi kawai tayi min ta cigaba da kallona har muka shiga dakin.

Komai Jakadiya ta nuna min yanda zanyi amfani dashi a toilet din, ta fito ta barni ina wanka cikin sanyin jiki, har yanzu fargabar abinda zai faru a gaba nakeyi yanda naga mahaifiyar Muddibo na kuka yasa gabadaya jikina ya mutu.

Koda na fito daga toilet din samun kan gadon nayi da kayan sawa sabbi a d'inke cikin wata leda, atampopi da lesuka masu kyau da tsada sabbi kar dan kallo daya nayi musu na tabbatar da cewa ba wanda ya ta'ba amfani dasu, hannuna ne ya sauka kan wata leda, nayi saurin zazzageta sai naga wanduna dasu breziya na dudduba kayan sosai ina mamakin al'amarin! Jikina na shirya tsaf, na sauke ledojin kayan kasa, juyawa nayi ina kallon makeken gadon da yaji shimfid'u na alfarma, ko a mafarki banta'ba tunanin zan kwanta a irinsa ba, nasa hannu ina shafa lallausan zanin gadon da yake yad'e da bargo da wasu irin pillows masu ban sha'awa! lumshe idona nayi a hankali na kwanta rigingine a gadon ina tunanin halin rayuwa.



'Bangaran Magajin sarki kuwa yana fita mota ya shiga direba yaja kai tsaye station suka nufa amma kafin su isa sai da ya kira Shatima a waya yace."Idan bashi da aiki ya sameshi a bomfai wato headquarter 'yan sanda gabad'aya, Shatima cikin mamaki yace."Ina fata dai lafiya." ajiyar zuciya ya sauke yace."Kai dai kawai kazo idan baka da aiki za kayi mamakin abinda ke faruwa." Shatima yace."Okey to shikkenan bani da aiki da yawa a ofis insha Allah nan da minti ashirin zaka ganni." Yace."Okey to babu damuwa." Sallama sukayi da juna ya kashe wayarsa ya cigaba da kallon hanya.



Acp da magajin sarki suna ofis suna tattauna maganar Shatima ya iso kai tsaye Acp yace a bude masa kofa ya shigo, cikin nutsuwa ya shiga ya samesu a zaune kafin ya zauna sai da ya basu hannu suka gaisa tukkuna ya nemi kujera ya zauna yana kallonsu.

Acp waya ya dauka domin bada umarnin shigowa da Muddibo......Magajin sarki ya kalli Shatima cikin yanayin alhini da damuwa yace."Shatima ka jima kana kawo min 'korafi akan Muddibo ina gwasale ka, ashe kana da gaskiya kawai kana bari ne saboda a zauna lafiya, Shatima a yau Allah buwayi ya tonawa Muddibo asiri kowa ya gane cewa shine ke aikata 'barna mai muni a cikin masarautar mu.''


Shatima hularsa ya cire yasa hankici saman goshinsa ya goge gumi, girgiza kansa yayi yace."Dama ni nasan dole watarana asirinsa ya tonu Wallahi dukkanin wani abu da zanzo na fada maka akan Muddibo gaskiya ne ba wai dan na had'aka dashi bane, aa inaso ka kiyaye dashi, to sai dai kuma a duk sanda zanzo nace maka Kada ka yarda da Muddibo ta kowace siga kai kuma baka daukar maganar da muhimanci dan a wasu lokotan idan nayi maka maganarsa ka gwasale ni raina yakan 'baci ina daurewa ne kawai, amma yanzu alhamdullahi nagode Allah daya ganar da kai gaskiya, shi kuma Muddibo naji dadi sosai da Allah ya toni asirinsa, Acp kuyi binkice sosai a kansa na tabbatar da cewa yasan komai akan mace-macen da aka dingayi a masarauta."

Acp yace."Kada ka damu Shatima zamuyi binkice sosai akan wannan al'amari."

Dukkaninsu kofa suka tsirawa ido, jami'ai biyu suka shigo dashi ofis din, ganinsu a zaune yasa yaji wani iri a tare dashi 'boye razanarsa yayi ya tsaya hannu daure da ankwa......Acp ya zagayo hannunsa rike da key ya kwance masa hannun, kana ya nuna masa gurin zama, jami'an dake tsaye gaisuwa suka mika a gaggauce suka fita daga ofis d'in."

Magajin sarki da Shatima kallonsa kawai sukeyi suna mamakin sauyawarsa lokaci guda ya zabge yayi rama tsabar fargaba da rashin gaskiya, gashi dan tijara Acp yasa an cire masa tufafi daga shi sai Singlet da gajeran wando.

Acp ya koma gurin zamansa tare da tsira masa ido yace."Muddibo dani da 'yan uwanka guda biyu muna so ka gaya mana gaskiyar abunda yake faruwa, kada kayi mana gardama da jayayya zakasha wuya hukuma na bukatar kayi mata cikakken bayani akan yunkurin kashe Sumayya da kayi sannan kuma hukuma naso kayi mata cikakken bayani akan wane nau'in magani ne kace Sumayya ta zubawa Yarima a lemo kuma ka tabbatar mata da cewa idan ta sa'ba umarninka sai ka kasheta."!!!!!!!

Muddibo kallon acp yake bakinsa sai rawa yake yi yace."Wato Acp ba zaka daina yi min qazafi ba ko? yanzu ku dan Allah kun yarda da cewa zan iya kisa."!!! dukkaninsu suka kalleshi suna girgiza kai.

Ya cigaba da cewa"Shatima Yarima ni dan uwanku na jini amma kun bada goyon bayan aci zarafi na ashe ba zuwa kukayi ku tafi dani ba yanayin fuskokin ku ya nuna min da cewa kun yarda da wannan 'kazafin da akayi min."!

Magajin sarki ya girgiza kansa ko ka dan bai tausaya masa ba sai ma mugun haushinsa da ya tokare masa a kirji, yace."Muddibo ni dan uwanka ne amma kuma kullum cikin bibiyar rayuwata kake, a zahiri kana nuna min kauna a bad'ini kuma kai kadai kasan irin 'kiyayyar da kake min, wai shin dan Allah mai nayi maka ne."?


Cikin rawar mirya yace." Ya za'ayi na'ki ka Ali ka tuna fa tare muka taso in banda ka tafi america karatu babu abinda ke rabamu komai tare muke gabatarwa shak'uwar dake tsakanina da kai har tafi wacce ke tsakaninka da Shatima to kan wane dalili zan kashe ka me kayi min da zan dinga bibiyar ka."


Shatima yace."Dalilai suna dayawa Muddibo ni nasan waye kai tinda Ali tafiya yay ya barni tare da kai tsayin shekaru masu yawa, na sanka nasan kuma kan abinda yasa kake kokarin halakar da d'an uwanka, Muddibo ba zan za'bi Ali na barka ba dukkaninku d'aya kuke a gurina duk kuma wanda yayi kuskure sai nayi masa magana, a tun lokacin da naga kana da damun kanka akan sarauta da yanda kake zagin mai girma Maimartaba yasa gabadaya al'amarin ka ya fita daga raina saboda nasan mutukar akan mulki ne to babu abinda ba zaka aikataba kamar yanda ka fad'a cewa insha Allahu daka kan Maimartaba mulki sai ya dawo hannun zuriar ku, yasa na shiga kokwanto akanka saboda irin mugwaye kalaman da kakeyi akan zuriar sarki Abdul-aziz a wancan lokacin kayi furucin kisa ba d'aya ba biyu ba duk akan mulki Muddibo me yayi zafi? mecece duniyar kuma menene mulki da zaka d'aga hankalinka akai! har ka dinga d'aukar nauyin daya fi karfinka na tabbata kana da hannu a cikin wannan mace-macen da akeyi a masarauta! shiyasa gabadaya banyi mamaki ba dana ganka anan na tabbatar da cewa hakkin mutunan daka dauka ne yasa asirinka ya tonu."

Muddibo cikin wani irin yanayi na nadama yace."Shatima kaine da kanka kake fadar wannan maganganun akaina? hakan ya nuna min cewa kana da bukatar hukuma ta cigaba da binkice na akan abinda ban aikata ba! ashe zumunci yace haka? Magajin sarki kada ka yarda da wannan tatsuniyar Shatima dama tuntuni yake adawa da sha'kuwar da take tsakanina dai kai 'karya yake min ni ban kasance azzalimi ba ballantana na zalince ka, Ali kayi wa maganar kyak.............Acp ya buga tevur! din gabansa cikin tsawa! yace."Ka rufe mana baki a gurin nan bama bukatar wannan soki burotson naka sahihiyar magana muke bukatar kayi mana idan kuma ka tsaya gardama da 'karyata masu gaskiya yanzu zansa aje ya zane maka jikinka idan kaji a jikinka za kayi bayani."!!!


Muddobo bakinsa ne ya mutu murus! dan har yanzu bai manta da marin da yasha ba.....Acp ya mike daga gurin zamansa zagayowa yayi yaja kujera ya zauna yana fuskantarsa, fuska a murtuke yace."Kai nake saurare.''

Cikin inda-inda yace."Acp na fad'a maka wannan al'amarin 'kazaf........Kafin ya 'karasa ya bashi wani wawan mari! da bayan hannu! Muddibo jinsa da ganinsa ne suka dauke na hucin gadi! ya bude idanunsa da sukayi jajawur! dishi-dishi yake ganinsu, murya na rawa Yace."Ali Shatima kuna kallon cin zarafin da ake min kuna kallo ko.''? ko gezau babu wanda yayi..........Da 'karfi! Acp yayi magana, sai aka bud'e kofar ofis ne, jami'an d'azu ne suka shigo da sauri suka qame alamu gaisuwa, Yace."Soloman kuje dashi ku bashi kashi! idan yaji ajikinsa zai mana bayani." Da sauri suka nufeshi, Muddibo ya dinga daga hannunsa da fad'in "Kada ku ta'ba ni na fad'a muku ni nafi karfinku kuma wannan abinda kuke zargina dashi qazafi ne."!!!!!! Soloman ne ya buga masa kan bindiga a kansa cikin tsawa! yace." Mi'ke tsaye! Muddibo ya mike da sauri yana kallon 'yan uwansa dake zaune suna kallonsa, hannu yasa ya sharce gumin goshinsa, Soloman da dan uwansa suka tasa 'keyarsa......Bayan fitarsa da minti biyu Acp ya kallesu tare da fad'in" Nasan dukkanin ku ranku zaiyi rashin dadi a bisa abinda yake faruwa da d'an uwanku, wallahi kuyi hakuri banso mukayi haka dashi ba naso muyi komai cikin mutunci! amma taurin kansa ya janyo masa kask'anci na tabbata yanzu idan su Soloman suka dan bubbugeshi yaji wuya zaiyi mana bayani."


Magajin sarki ya sauke ajiyar zuciya mai zafi yace."Acp ko kusa ko alama bana tausayawa Muddibo wallahi duk irin hukuncin daya kamata a dauka a kansa bai dame ni ba.'' Shatima yace."Nima sam be bani tausayi ba wallahi saboda nasan dashi ne ya samu dama akanmu abinda zaiyi sai yafi haka


Acp ya bude baki kenan zaiyi magana, sukaji wani irin ihu!! Muddibo yaji bugu!! sai zunduma ihu! yake! Acp mikewa yayi ya fita ya barsu suna tattauna maganar.......kafin Acp ya isa gurin Middobo har ya suma! yace maza maza a yayyafa masa ruwa ya farfado, da sauri suka yayyafa masa ruwan sanyi a fuska.

A firgice ya bude ido ya gansu a tsaye a kansa kowanne da k'atuwar gora! hannunsa fuskokinsu tamkar towon dawar daya kwana biyu!

Had'a ido sukayi da Acp a take fitsari ya kufce masa bakinsa cike da jini yake kokarin magana, Acp ya tsuguna a gabansa yana kallonsa, yace."Yanzu zaka iya yi mana bayani ko a

Please Login or Register in order to submit comment