Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sallar Liman ya dade yana addua akan abubuwan dake faruwa a masarautar Liman yayi zafafan adduoi akan Allah ya tuni asirin masu aikata mugun 'kulli a masaraura, Ciroma da galadima jikinsu ne yayi sanyi ganin yanda Liman ya dage yana addua jama'a na amsawa da ameeen ya Allah! duk sai suka tsargi kansu da kansu suna ganin kamar asirinsu na daf da tonowa.......Muddibo kuwa dama ana idarwa ba tare da kowa ya ankara ba ya silale daga massalacin, can sashen Uwargida ya nufa ya sheda mata abinda ke faruwa, Uwargida Huwaila ranta yayi mugun b'aci! jin cewa ai Yarima ya dawo gida su duk a tunaninsu hukuma zata ri'keshi akan abinda ya faru sai kuma suka ga sa'banin haka, jiki a sanyaye ta koma ta zauna kan kujera tana tunanin mafita.


Tare suka fito da Shatima daga massalaci, kai tsaye sashen fulani suka nufa suna tafiya suna tattauna al'amarin, karo suka ci da Muddibo ya fito daga sashen uwargida ganinsu a tare yasa gabansa faduwa amma da yake 'kwaro ne nan da nan ya dake! ya karasa inda suke a nutse ya basu hannu suka gaisa, yace."Yanzu nan nake tunanin zuwa sashen ka ashe ka dawo gida."? Yarima yace."Eh Allah ya takaita na dawo jiya misalin sha biyu na dare." Cikin alhini yace."To Ubangiji Allah ya kiyaye a gaba amma yana da kyau kasa ido sosai a sashen ka abubuwan dake faruwa da kai sunyi yawa." Yace."Insha Allah yau din nan zan zauna dasu saboda jiya bayan dawowata na samu abun hannun wani daga cikinsu hakan ya sake tabbatar min da cewa akwai sa hannunsu a cikin al'amarin."
Muddibo cikin faduwar gaba yace."Ka samu sheda kenan."? Yace."Kwarai kuwa." Muddibo girgiza kansa yayi yace."To babu damuwa Muje mu gaisa da Mamma sai mu zauna dasu din." tare suka shiga falon, tana zaune kan dadduma da carbi a hannunta, ganin gudan jininta lafiya lau yasa taji wani sanyi ya sauka a zuciyarta, lallai addua bata faduwa kasa banza, a nutse suka zauna gabanta suna gaisheta, ta dinga amasawa tana shafa kansu, tace''Ina rokon Allah yayi muku albarka ya kareku daga dukkanin sharrin abinqi dukkanin mai nufin ku da sharri ina rokon Allah ya mayar dashi kansa, babana hakika naji dadin ganinka cikin nutsuwa ina rokon Allah ya kiyaye gaba su kuma wad'annan bayin Allah da suka rigamu gidan gaskiya ina rokon Allah ya jikansu ya gafarta musu."
Suka amsa da ameeen suma ameeen."

Koda suka fito daga sashen mamma kai tsaye Sashen Waziri suka nufa, iyalin Waziri ganinsa lafiya lau yasa su farin ciki suka dinga yi masa adduar kariya daga dukkanin abinqi! lafiya lau suka fito daga sashen suka nufi na Galadima, babu yabo babu fallasa suka gaisa da juna har suka fito babu wanda yayi masa jajen abinda ya faru ballantana ya samu kyakkyawar addua, sosai al'amarin ya bashi mamaki! Shatima ma yaji takaicin abinda iyayensa sukayi 'karara suke nuna hassadarsu abin da iyayensa da sauran 'yan uwansa keyi sam bayayi masa dadi, hakuri ya shiga bashi, Magajin sarki ya dakatar dashi da fad'in "Kada ya sake bashi hakuri akan abinda akayi masa shi bai dauki abin da zafi ba yana ganin duk abinda sukayi a kansa daidai ne! Shatima ganin ransa ya baci yasa ya bar maganar, Suna daf da shiga sashin Ciroma Mudibbo yace." Su shiga kawai zai dauko wayoyinsa a gurinsa, ba tare da sunce wani abuba sukayi gaba, shi kuma kamar gaske ya nufi gurinsa, tsayawa yayi na minti biyar, ya leko kansa ganin sun 'bace daga gurin yasa da sauri ya fito, kai tsaye 'bangaran bayi ya nufa.


Babu yabo babu fallasa suka gaisa da iyalin Ciroma dukkaninsu suka cika falon kowa na fadin albarkacin bakinsa akan abunda ke faruwa, shi dai jinsu kawai yake dan ya kasa cewa komai saboda hayaniyar da tayi yawa a falon sai zagin Sumayya suke suna cewa ita za'a daure tunda itace ta girka abincin dole a tsaurara binkice akanta ta fadi wanda ya bata gubar.....Gimbiya Lawisa ta zage sai cin mutuncin Sumayya takeyi, 'yan uwanta suna taya ta, ga mahaifiyarta a zaune ta kasa tsawatar musu, takaici yasa ya mike Shatima ya mike sukayi musu sallama suka fito, rai a 'bace ya kalli Shatima yace." Gabad'aya naji na tsani Lawisa wallahi bata da tarbiya ko kadan." Yace."Kasan hausawa nacewa Tarbiya daga gida take farawa Hajiya Karima sam bata da tsawatarwa shiyasa 'ya'yanta suka lalace." Yace."Allah ya kyauta hakikanin gaskiya ina fargabar auran Lawisa ta haifi min lalatattun 'ya'ya." Yace."Haba ai ba 'anan take ba kaifa tsayayyan namiji ne kai zaka tsaya akan iyalinka sosai na tabbata zaka iya sanja mata hali idan kukayi aure." Girgiza kansa yayi yace."Hakika idan ta sake tazo min da mummunar d'abia to zata sha wuya a gurina dan na tsani mace mara nutsuwa wallahi." Shatima yace."Gaskiya mace mara kintsi bata da dad'in sha'ani kamar yanda na fad'a maka da farko hakane idan kukayi aure zaka iya canzata mutukar tana kaunar zama dakai dole tabi dokokinka." shuru yayi be sake magana ba har suka isa sashen nasa,


kafin su shiga ciki ya kira Mika'il yace dashi gabad'ayansu suzo yana san ganinsu.......Suna zama Muddibo ya shigo hannunsa rike da wayoyinsa kusa da Shatima ya zauna yana duba 'karamar wayarsa Shatima kallonsa kawai yake sam be yarda dashi ba, tuntuni yake zarginsa kawai dai yayi shuru ne yana kallonsa kuma yana rokon Allah ya tona masa asiri.......Su shida suka shigo suka samu guri guda suka jeru gabad'aya sunkunyar da kansu sukayi kasa suna jiran suji kiran da ake musu.




*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika futa da book din keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300...account... 0542382124....Binta umar gtbabk....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(kainuwa dashan Allah✊?)
81
"Idan ba shine yayi sanadiyar mutuwar Haruna ba to waye? ni daina nasan lafiya lau na gama abinci na shirya komai akan tire kafin na fito daga kicin din na sameshi yana kokarin fita! gabana ne ya fad'i! lokacin dana tuna kafin ya fita ya bani umarnin akan na gyara masa daki, tabbas a wannan lokacin wani zai iya shigowa ya aiwatar da kudirinsa" Anya kuwa ni nafi zarginsa akan shine keda hannu akan faruwar al'amarin watakila bayan haruna ya kai masa abincin ya zuba guba a ciki ya bashi." To in banda abinki Sumayya idan Yarima ya kashe Haruna akan wata manufa shi kuma direba mai yayi masa da zai had'a dashi ya kashe."? jikina ne yayi sanyi jin irin k'alabulanta ta da zuciyata takeyi akan zargin da nakeyi akan Yariman.

Gabad'aya jikina ne yayi sanyi na dinga tunanin waye yake da hannu a cikin wannan abu, ance zargi zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne to amma irin munanan kalaman da ya dinga yi akan haruna yasa nake zarginsa da kashe shi domin bukatarsa ta biya a kaina.

Na jima ina sa'kawa da kawancewa kafin naji motsin saukowarsa, kauda kaina nayi da barin kallonsa har ya karaso kusa dani ya zauna yana sanye da farar jallabiya mai karamin hannu da alama wanka yayi kafin ya sauko.

Ganin yanda ya naniqa dani yasa na janye jikina gami da sunkuyar da kaina kasa.

"Sumayya." Naji ya kira sunana! shuru nayi ban amsa ba.

Ya sake kiran sunana da fadin"Ina so ki kalle ni sosai zamuyi magana."

Kallonsa nayi, naga babu wasa a fuskarsa yace." Ni Ban kashe Haruna ba sai dai ajalinsa ya sauka ta dalilin cin abincin da ya kasance nawa, Allah yayi nufin Haruna da Atiku ne zasu mutu ta wannan hanyar saboda haka kada na sake jin kinyi furuci akan cewa ni na kashe su.

Bude baki nayi zanyi magana yasa hannu ya rufe min baki yana girgiza kai yace."Nasan abinda zaki ce! kina so ki kalubalance ni akan maganata ko."? shuru nayi ina kallonsa, ya cigaba da cewa." saboda kawai nayi wad'annan furucin nawa na baya kike so ki gazgata zargin ki a kaina wallahi Allah kenan ban kashe wad'annan bayin Allah ba."


Jin yanda yake rantsuwa da Allah! yasa jikina ya mutu, a sanyaye nace"To idan ba kai bane wanene ? ni dai nasan tsaf na kammala komai kafin naje na gyara maka dakinka kamar yanda ka umarce ni.


Girgiza kansa yayi yace." Wata'kila lokacin da kika tafi gyara min daki aka samu wani ya shigo yayi abinda zaiyi ya fita ba tare da kin sani ba, kin dai san yanda ni dake muke fama da masu farautata a kullum dama suke nema akaina su cutar dani , ki tsaya kiyi tunani sosai akan maganata, Sumayya duk 'kiyayyar da nakewa Haruna ba zan kashe shi a kan son duniya ba, naji ciwo sosai da abinda kikayi a station har kina fitar da hannu kina mari na! sannan har kina kiran mu azzalimai shin kin san irin masifar da zaki jefa kanki a sakamakon wannan haukan da kikeyi to bari kiji na tausayi miki ne saboda nasan kina cikin rud'ani inda naso a station d'in zan sa ayi miki rashin mutumci! bayan nan kuma na ku kulle ki har karshen rayuwarki!! ina da dama a hannuna wacce zan iya yi miki dukkanin abinda nake so amma na kyale ki kike cin kashi a kaina! ki sani idan ni na kashe Haruna wallahi ba zan 'boye ba, zan fada kuma na kwana lafiya babu wanda ya isa yace don me! ina da wannan ikon saboda dukkaninsu a k'arkashina suke, sai dai duk ikon da nake dashi na duniya ne idan naje Lahira nan zan ga sakamakona! Sumayya ki sani Haruna da Isa da Atiku sunyi mutuwar shahada wanda yayi sanadin mutuwarsu duk sun rataya a wuyansa Ubangiji ya wankesu tas saboda haka inaso ki nutsu sosai ki daina zargina akan wannan abu, idan Allah ya kaimu gobe Acp yazo ki nutsu kiyi masa cikakken baya ni amma kika sake wani mummunan furuci a kaina to zai cigaba da daukar ki a matsayin mahaukaciya."


Tun kafin ya gama maganarsa nake zubar da hawaye, ya kama dukkanin hannayena ya rike yana rarrashina, cikin sanyin murya nace"Yanzu to ta yaya za'a iya gane wanda yake aikata wannan mugun abu, idan ya kasance d'an sarauta ne shikkenan jininsu Haruna ya tafi a banza tunda kace shi mai mulki yana iya yin komai ba tare da an d'auki mataki a kansa ba."


Girgiza kansa yayi yace."Baki fahimce ba sumayya ina yi miki misali ne a kaina nace miki idan ni na kashe su Haruna ba zan 'boye ba zan fad'a nine saboda nasan da wuya a d'auki mataki a kaina saboda wani dalili misali bana fatan hakan ya faru dani ace na taka wani da mota ya mutu to zan aikata abinda musulunci ya tanada zan biya diyyar rai kana kuma nayi azimi sittin kamar yanda Allah yace. idan kuma ina sane na kashe rai to zan mi'ka kaina ga hukuma nima a yanke min hukunci daidai dani idan anyi min haka to anyi min gata tunda nasan idan naje lahira dole Allah ya tuhume ni.......Sannan idan ya kasance cewa binkice ya nuna wa'inda suke dasa hannu suna da alaqa da masarauta to dole duk yanda zanyi naga nayi kokarin ganin hukuma ta dauki tsautsauran mataki a kansu tunda dai al'amarin yi sukeyi ba d'aya ba biyu ba suna ta kashe rai duk a kokarinsu nasan suga bayana gashi har yanzu Allah bai basu iko ba suna ta daukar zunubi suna dorawa kansu saboda son duniya! ba zasu daina ba har sai sun ga bana numfashi kinga kuwa dole a dauki mataki akansu idan ba hakaba to zasuyi ta kashe wanda beji ba bai gani ba."

Tunda yake maganar nayi shuru ina sauraransa gabadaya jikina ya mutu da kalamansa ban ta'ba tsammanin yana da kaifin tunani da hange nesa ba sai yanzu, ni da kallon sakarai nake masa wanda ya mayar da duniya gidan jin dadi ashe yana da tunani mai kyau kuma ko yaya yana tsoron Ubangijinsa ko ga yanayin kalamansa sai dai dama ance dan adam tara yake bai cika goma ba, dole duk tsoron Allahn mutum ka same shi da wani abu na rashin kyautawa

Shuru nayi ina sake risinar da kaina kasa gabadaya kunyarsa ce ta lullub'eni gaskiya nima naga tsaurin idona dana falla masa mari gaban mutane! wani lokacin har mamaki nake idan nayi masa abu ya kyaleni bai d'auki matakin komai ba, matsayin sa ya wuce ace na hada hanya dashi, amma sabida rashin girman kansa yana zama kafad'a da kafad'a dani........"Sumayya kin manta furucinsa a kanki Yarima Ali dole ya kaskantar miki da kai saboda yana so ya mori albarkatun jikinki har kike kiransa mara girman kai akwai manufa a zuciyarsa." Zuciya tace take tunasar dani abinda na manta.....Jikina na janye daga kusa dashi gabana na faduwa nace"Ka bud'e min kofa na tafi."


Girgiza kansa yayi yana kallona kasa kasa yace."Kin san karfe nawa yanzu."? kaina na daga da sauri ina duba agogo, saboda rashin wadataccan haske a falon yasa banga lokacin ba
Yace." 'Daya na dare ta wuce yanzu ba zan barki ki futa ba kawai ki bari sai gobe." kallonsa nayi ya d'age min girar shi! na mayar da kaina kasa ina wasa da hannuwana gaskiya nima ba zan iya fita a daran nan ba ina jin tsoron kada wani yaga fitowa ta sai dai da asuba. shawarar dana yanke kenan da zuciyata.

"Tashi muje mu kwanta." Yafad'i maganar yana kokarin kamo hannuna. Da sauri na janye ina masa wani irin kallo nace"Kaje ka kwanta ni ka kyaleni anan." Girgiza kansa yayi yace."Babu amfani na tafi na barki a falo ke kadai ki tashi mu hau sama."

Na dinga kallonsa ina mamakin furucinsa sai kace matarsa ta aure kai tsaye yake fad'ar maganar, tsoronsa ne ya kama ni, murya ta na rawa nace"Ni dai bana san doguwar magana dan Allah kaje ka kwanciyarka ka barni anan." Mikewa yayi ba tare da yace min komai ba ya nufi kicin, kallo na bishi dashi, minti biyar ya fito daga kicin din yana kallona yace."dana na shiga kicin ne wai ko zan iya wani abu na kasa ko zaki dafa min coffee ne kema akwai bukatar kici abinci dan na lura da yunwa a tattare dake, girgiza kaina nayi ina kokarin mikewa nace"Ni bana bukatar komai amma dai bari na kawo maka coffee din." Zama yayi kan kujera tare da fadin" Nagode." Kicin din na nufa, cikin minti goma na had'a masa abinda ya bukata ina kokarin fitowa ya shigo, kallonsa nayi ya tsaya a bakin kofa yace."Kin gama."? kaina na daga, ya karasa shigowa yasa hannu ya kar'bi tire din hannuna, bayansa nabi naji k'afata ta hard'e da wani abu, da sauri na tsaguna domin na cire abinda ya hard'e ni! wata 'yar igiyace na dago ina dubawa! "Menene wannan."? yafada yana kallon hannuna, a sanyaye nace." Igiyar hannu ce wacce su Haruna suke d'aurawa duk wanda yake a matsayin bawa a masarautar nan yana da ita d'aure a hannunsa." kar'ba yayi yana dubawa, ya kalleni a nutse yace."Muje falo." a sanyaye nabi bayansa ina mamakin abinda ya kawo igiyar kicin din.


Ajiye igiyar yayi saman centar table din gabansa a nutse ya dauki cup din dake dauke da coffee din yasa a bakinsa, da sauri ya cire jin zafi na nema ya kona masa baki, ajiye cup din yayi ya dauki igiyar yana dubawa, a nutse nasa spoon a cikin coffe din ina d'an motsa masa saboda na lura zafinsa ne ya hana shi sha......"Sumayya me ya kawo wannan igiyar kicin."? naji ya jefo min tambayar, a sanyaye nace."Nima tun dazu tunanin da nake kenan."? Yace."Kodai akwai sanya hannun wasu daga cikin hadimai na idan ba haka ba me zai kawo abun hannunsu kicin me ya kaisu? me suka shiga suyi?
Nace"Gaskiya kam ga alama nan ni wallahi yanzu gabad'aya al'amarin tsoro yake bani." Girgiza kansa yayi yace."Dole ya baki tsoro sumayya mutum mugun ice ne babu shakka wasu daga cikin hadimai na dake waje suna da masaniya akan abinda ke faruwa akwai bukatar na zauna dasu domin wannan igiyar ita zata tona asirin wanda ya shigo tunda kince kowa yana daure da ita a hannunsa."


"Eh gaskiya ne duk wanda yake a matsayin bawa to in dai namiji ne yana daure da ita mahaifina ma yana da ita a daure a hannunsa na dama, saboda haka nima na bada goyon bayan akan ka tarasu kowanne ya nuna maka hannunsa sai ka tabbatar da yana daure da igiyar sai ka sallameshi."

Igiyar ya ajiye tare da daukar coffee d'in yace.''Kada ki damu in Allah ya yarda ba za'a ja dogon lokaci ba Allah zai bayyana mana komai." A sanyaye nace"To Allah ya yarda."

Falon ya dauki shuru na tsayin mintina tsakanina dashi babu wanda ya sake magana, shi yana k'urbar coffee dinsa ni kuma ina can tunanin wanda ya shigo bayan na bar falon.....Tas ya shanye ya ajiye cup din a nutse ya kalle ni yace."My lov." Gabana ne ya fad'i na kalleshi yana kallona, yace."Kin bani tea nasha ke zaki kwana da yunwa anya kuwa nayi wa kaina adalci." shuru nayi ina mamakin shu'umancin sa wai my lov muna cikin wannan tashin hankalin yake wani shirme, hannuna ya rike cikin wata kwantacciyar murya yace."Dan Allah tashi muje sama wallahi ba zan miki komai ba, ina so na kwanta na huta ne kuma bana so na barki a falo ke kadai."

Cikin faduwar gaba nace"Nifa ko na kwanta ba zan iya bacci ba saboda abinda ya dame ni shi ya dame ni, bana tsammanin zan iya yafewa wanda ya kashe min masoyi."

'Bata rai yayi yace."Na gama kiran ki masoyiyata kina kiran wanda ya mutu masoyinki ashe na zama shashasha kenan kin maida soyayyata karkashin kafarki kina takawa tare dayi min abinda kike so kada ki manta fa ina sane da marin da kikayi min a station idan kinyi wasa yanzu zan fanshe abina."


Kuka nasa ina masifar tsoron fitinar sa na riga nasan halinsa da naci! nace"Dan Allah kayi hakuri ka rabu dani naji da abinda ya dame ni, ka dame ni da surutai ni ban san ma sanda na mareka ba idan kuma baka bari ba ka rama marin ka shikkenan ka rabu dani da wani love."


Girgiza kansa yayi yana dan murmushi yace."Waye ni! ai da zan rama da tun a can na rama na kyale ki saboda soyayyar da nake miki."

Harararsa nayi ina share hawaye nace"Sau nawa kana marina a station d'in ai ka rama kawai dai yanzu kana neman wata fitinar ne ni dai na baka hakuri ka rabu dani dan Allah na samu nutsuwar zuciya nayi tunanin rayuwar da zan fuskanta bayan babu Haruna." Ina sane nayi wannan maganar domin na bashi haushi.

Aikuwa yaji haushi dan wani irin kallon banza yake min kafin yace."Kada ki sake maganar matacce idan kika sake zan miki abinda bakya so kin gane ko." ? Nace"To nima kada ka sake kira na da wannan suna saboda sunan bai cancanta ya fito daga bakin ka ba tunda kasan nasan ba soyayyar gaskiya kake min ba, Haruna shi yaf........Saukar hannunsa naji a kirjina! a zabure! na buge hannunsa gabana na faduwa na matsa daga kusa dashi, matsowa ya sake yi jikina, na fashe da kuka da fad'in.................!




*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi idan baki biya ba, keda kika futar da book din keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*0708465326*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
83
Cikin nutsuwa ya d'aga kansa yana kallonsu, "Ina Hamza yake."? yafad'a yana binsu da wani irin kallo. da sauri Mika'il yace." Yana can b'angaransu Haruna."
"Me yake yi a can."? Mika'il yace.''Yana taimakawa ne gurun had'a gawar." shuru yayi yana kallon k'asan kafet. Muddibo yace."Kai Mika'il maza jeka ce yazo yanzu yanzu." A nutse yace."Barshi kawai tunda akwai abinda yake yi, idan ya gama Mika'il kace ina nemansa." Mika'il yace."Insha Allahu zan sheda masa." Falon ya sake daukar shuru, Shatima ne ya mike fuska a daure ya karasa inda suke, daya bayan daya yake kallonsu kafin yace."Nasan kun san abunda yake faruwa ko."? gabadaya suka ce "Eh ranka ya dade mun sani muna rokon Allah ya kawo karshen Al'amarin." Ya amsa da ameeen kafin ya cigaba da cewa"Jiya misalin karfe bakwai zuwa takwas na safe waye ya shigo gurin nan wanda har ya samu nasarar zuba gubar data kashe wad'annan bayin Allah."?
Dukkaninsu suka shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali suka shiga tunanin waye ya shigo a daidai wannan lokacin." Shatima yace."Kunyi shuru idan fa baku fadi gaskiya ba dukkaninku d'aureku za'ayi muddun rai gwara ku fada mana gaskiya idan da akwai hadin bakin ku a cikin abinda yake faruwa."

Mika'il yace."Wallahi ranka ya dade ni dai banga wanda ya shigo gurin nan ba, iyakan mu ne kawai a gurin sai Sumayya da take shige da fice a gurin."

Magajin sarki mikewa yayi ya iso gurin, igiyar hannunsa ya fito da ita da fadin""Wannan ta wacece jiya na tsince ta a kicin." dukkaninsu suka tsirawa igiyar ido, kafin su fara duba hannuwansu! Shatima yace."Dukkaninku ku nuna min hannuwanku." suka fito da hannunsu kamar yanda aka bukata, abin mamaki kowanne da tasa a daure! al'amarin ya dauresu musu kai mutuka, Muddibo ya karaso gurin yasa hannu a kafadar Yarima da fadin"ammafa abun ya bani mamaki mutuka kodai Hamza nada hannu acikin al'amarin nan shiyasa ya tsaya a wani gurin."? Ya kalli Mika'il da fadin "Maza jeka idan sun gama kace ina nemansa, Mika'il ya kama hanya ya fita da sauri
Kujera ya samu ya zauna zufa na keto masa, Shatima ya zauna kusa dashi yana tausarsa, Muddibo kuwa kujararsa ya koma ya zauna yana cigaba da latsa wayarsa, Mika'il da Hamza suka shigo, da sauri ya mike tsaye, Hamza a tsorace yake kallonsa yace." Ranka ya dade a gafarce ni na tsaya ne gurin had'a gawar su

Please Login or Register in order to submit comment