Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana gida yana hutawa wani sa'in har na gama abinda nake na fita yana sama yana bacci abunsa abin mamaki yau dana shiga samun sa nayi a falo a zaune yana kallon kwallon kafa. gaishe shi nayi babu yabo babu fallasa ya amsa, kicin na nufa ya kira sunana

Tsayawa nayi ina kallonsa, kusa dashi ya nuna min. "Zo ki zauna yau ranar taki ce zamu tattauna maganar dana jima ina fada miki."


Gabana ne ya fadi ni sam na manta da wata magana, cike da rashin tsoro nace"Yallabai wace irin magana zamu tattauna wacce har sai nazo na zauna kusa da kai."


remot din hannunsa ya ajiye yace."Magana ce ta mussaman wacce take bukatar sirri."

Ajiyar zuciya na sauke nace"Ni da kaine kadai a dakin nan ina ganin ba sai na zauna kusa da kai ba babu wanda zaiji ko ya gani kawai ka fadi maganarka ."


'Kure ni yayi da ido yana kallona, nima nawa idon nasa masa dan gabadaya yanzu na daina jin tsoransa, "Kinga ni ba wani abu zanyi miki ba naga kina min kallon rashin yarda maganar da zanyi miki nafi bukatar na ganki a kusa dani shine dalilin daya sa nace kizo ki zauna?"

Shuru nayi ina naxarin maganarsa a sanyaye yace."Ki yarda dani da maganata ba zanyi miki komai ba." kallonsa nayi naga yana marairaicewa, ajiyar zuciya na sauke naje na zauna kusa dashi.

Ya kai minti biyar yana kallon k'asan gurin kafin ya dago kansa ya kalleni, kauda kaina nayi gefe, hannuwana ya ri'ke nayi saurin kallonsa! a sanyaye yace."Sorry.'' ajiyar zuciya na sauke nace"Ka sakar min hannuwa ka kuma fadi maganar dake bakinka."

Murmushi yayi yace."Yarinyar nan watarana idan kina bani umarni har mamaki kike bani gaskiya kina da karfin hali kina kuma burgeni wani lokacin kuma kina 'kuntata min"

Zum'bura bakina nayi na kauda kaina gefe hannuwana na cire daga nasa.
Hannu yasa ya juyo da fuskata naga yana min wani irin kallo wanda ya sani faduwar gaba, da sauri nace"Wai baka zaka fadi maganarka ba." Ba zato naji saukar hannunsa a le'bena yana shafawa.'' doke hannun nayi ido jawur nace"Ai dama nasan sai ka gwada halin ka." mikewa nayi da sauri yay gaggawar mayar dani na zauna
Fuska a hade yace."Ni kike dokewa hannu.'' hanci na hura ina ji tamkar na doki bakinsa dan haushi fitinannan mutum ne shi mai 'ketare iyakokin ubangiji.

Ajiyar zuciyarsa naji na kalleshi naga ya shiga hankalinsa sosai, kasa nayi da kaina ina jiran naji ta bakinsa


"Kin san abinda yasa nace kizo kusa dani muttauna." ? girgiza kaina nayi nace"Sai ka fada." Yace."Na dauki d'amarar auranki kamar yanda kika kwad'aita min zan aureki insha Allahu ina bukatar amincerki."


Kai tsaye nace"Yallabai ai ka makara me yasa tun lokacin da nayi maka maganar baka amsa ba a yanzu iyaye sun riga sun shiga cikin lamarina da Haruna an tsayar da maganar auranmu wata hudu masu zuwa maganar auranmu ma maimartaba ya san da ita


Wani irin shan kunu yayi yana kallona yace."Karya kikeyi kizo min da wannan maganar baku isa ba keda Harunan naki aure ni zan aureki shi yaje can ya nemi daidai dashi.'"

Cike da mamaki nake kallonsa nace"Haruna nice daidai dashi kamar yanda yake daidai dani kaine zakaje ka nemi daidai da kai tunda ka fada cewa ni ba tsaran auranka bace.''


Shuru yayi gumi na yanko masa. nace"Idan ka gama maganarka ni zanje nayi aikina." Ido jajawur ya dago yana kallona yace."Na fada miki fa baku isa ba wallahi sai an warware maganar auranki da Haruna ko kuma naga bayansa."

Gabana ya fad'i jin abinda yace nace."Ranka ya dad'e kana musulmi kake fad'ar wannan maganar zaka ga bayan Haruna me zakayi masa to."?
Ido yasa yana kallona nace"Ashe kaima zuciyarka irin ta 'yan uwanka ce gashinan kana mummunan lafazi akan wanda be maka komai ba."

Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannuwana duk biyun ya rike a raunane yace."Kada kiyi min wata fassara ta daban raina ne ya 'baci na fad'i wannan maganar Please Sumayya muyi maganar da zata amfane mu ni dake a yanda nake jin ki a zuciyata bana tsammanin zan iya bari Haruna ya aure ki."

Nace"Ranka ya dad'e Haruna shike sona tsakani da Allah kai kuma sha'awata kake zaka aureni domin ka kawar da sha'awarka shikkenan idan bukatarka ta biya sai ka sake ni, Haruna kuma zai aureni saboda yana sona tsakani da Allah badan wani abu na jikina ba kai kanka ka zauna kayi nazari da tunani akan al'amarin nan Yallabai kasowa kanka abinda zakasowa d'an uwanka yanzu babu wata sauran magana a tsakanina da kai tunda maganar aurena da Haruna ta shiga tsakani."

"Kin san dai Haruna bai isa ya had'a neman aure dani ba ko."? kallonsa nayi inaso nayi magana ya katseni a harzuqe yace.''Kije ki kira min Harunan naji ta bakinsa."

Cikin fad'uwar gaba nace"Bangane kaji ta bakinsa ba." Hannu ya d'aga min fuska a had'e yace."Kada ki sake harzuqani kije ki kira min shi nace."

Jikina ne yayi sanyi nace"Dan Allah ka bar wannan maganar ka fuskancin abinda ke gabanka ka auri daidai da kai nima na auri daidai dani."

"Sumayya." ya kira sunana kallonsa nayi, yace."Ba zan hakura dake ba ki rubuta wannan ki ajiye idan kin auri Haruna kin barni sai na hana ku jin dadin rayuwa gwara ku magance matsalarku keda shi Nafi karfin na nemi abu wanda yake kark'ashina ya had'a takara dani dole Haruna ya janye maganar auranki."


Nace"Ranka ya dad'e lafazan ka na nuna min cewar babu kyakkyawan nufi a cikin zuciyarka kada ka cutar da Haruna dan beyi maka laifin komai ba kuma ka daina gwada iko da mulki a kaina Allah ba'a nuna masa gadara idan Allah ya kaddara ni d'in ba matarka bace ya zakayi."?


Jajayen idanunsa ya zuba min yace."Bakya shakka kallon tsabar idona ki fada min magana ko." ? sunkuyar da kaina kasa nayi nace"Gaskiya d'aci gareta shiyasa kake gani kamar naci maka fuska."


Kwafa yayi yace."Dallah tashi ki bani guri kafin na da'uke fuskarki da mari."!! ganin yanda yake zabura yana huci! yasa nayi gaggawar tashi ina mamakin al'amarin.......kicin na nufa ba tare da naje aiken da yayi min ba.


Mikewa yay ya bude kofa ya fita, suna ganinsa suka taso daga inda suke zubewa sukayi a gabansa suna tambayarsa, babu walwala a tare dashi ya kalli Haruna da fadin"Ka shigo ina neman ka." Haruna yace."To ranka ya dade." Juyawa yayi ya koma ciki Haruna yabi bayansa.


Yana tsaye a tsakankanin kujeru Haruna ya same shi, Cike da ladabi yace."Ranka ya dade ina fata banyi laifi ba. wani irin kallo yayi masa kai kana ganin kallon kasan na kishi ne......Yace."Meye tsakaninka da yarinyar nan Sumayya."? Haruna yasha jinin jikinsa a sanyaye yace."Ranka ya dade itace matar da zan aura.'''

''Yaushe aka tsayar da ranar auran naku bani da labari."? Haruna ya sake kaskantar da kansa yace."Ranka ya dade ayi min afuwa wallahi na sha'afa shiyasa ban fada maka halin da ake ciki ba."


Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kan kujera yana kallonsa da wata iriyar murya yace."Inaso ka janye maganar auranka da Sumayya."!


Haruna gabansa ya buga da sauri ya dago kanshi yana kallonsa bakinsa sai rawa yake ''Ranka ya dade ban.......! Hannu ya daga masa ya hanashi karasa maganarsa, Haruna 'kasa yayi da kansa Gumi na tsiyayo masa.


"Kasan a 'karkashina kake ba zai yuwu ina neman abu kana nema ba dole ka janye maganar auranka da yarinyar nan." Wannan maganar da yayi yasa Haruna ya gane inda ya dosa.

Shuru yayi ya kasa magana yayin da gumi ya jikashi jagab ta yaya zai janye maganar auransa da Sumayya bayan ansa rana iyaye da abokanan arziki duk sun san halin da ake ciki, ta yaya zai iya cire tsananin so da kaunar da yake wa Sumayya a cikin ransa? babu shakka wannan babban al'amari ne a gare shi.


"Haruna kana jina ko."? da sauri yace." Eh Yallabai naji maganar ka nasan kai ba sa'ana bane ta kowane fanni! insha Allahu zanbi umarninka."

"Okey nagode sosai inaso ka shedawa iyayenka umarnina." Jiki a mace yace."Idan Allah ya yarda zan sheda musu." "okey kana iya tafiya." Yafada yana nuna masa hanya da hannu.

Yana juyowa muka had'a ido dashi, sai naga yayi wani irin murmushi kai kana ganinsa kasan na saduda ne tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace ( bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane) ina shi ina had'a neman aure da Magajin sarki mai jiran gado tilas yanaji yana gani ya hakura da Sumayya ya bar masa, girgiza kansa yayi yana kallona nan na hango yanda idanunsa ya tara ruwan hawaye da sauri ya bude kofa ya fita.

Nima hawayen dake kokarin zubo min na mayar ina danne wani k'aton abu a mak'ogwarona, kallonsa nayi yana hard'e a kan kujera nace."Wallahi idan ka raba wannan soyayyar da k'arfin mulkin ka idan ka raba wannan k'aunar da karfin ikon ka to na tabbata Allah ba zai barka ba, kuma mutukar ka samu nasarar raba tsakanina da masoyina na gaskiya ka rubuta ka ajiye ko ka aureni ba zaka samu biyan bukatarka ba, saboda haka ka zauna kayi tunani da kyau akan maganata." Hanya na kama zan fita, da sauri na ganshi ya tari gabana zuba masa ido nayi ina kallonsa, Yace." Ni kuma nayi al'kawarin auranki ko kina so ko bakya so auranki bani na nema ba ke kika nema bayan kin kwad'aita min kuma daga baya kizo min da wata maganar banza! to na d'aura d'amarar auranki domin na kawar da sha'awata a kanki."

Cikin 'kunar zuciya na kalleshi magana nake so nayi tsabar bacin rai da takaici ya hana ni cewa komai ratse shi nayi zan wuce ya sake tare min hanya yana min wani irin kallo. girgiza kaina nayi nace "Bani hanya na wuce." Sake babbake hanyar yayi ya dogare hannusa a jikin bango....karfi nasa na doke hannun na ture shi! taga-taga yayi zai fadi baki ya bude yana kallona! tsaki mai karfi naja na bude kofa na fita. Murmushi yay yana mamakin k'arfin yarinyar har ta iya tureshi yana tsaye bai dauki mataki ba, kan kujera ya zauna yana tunanin ta yanda al'amarin zai yuwu.....





*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya ke kuma da kika futar da littafin keda Allah, idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account.... 0542382124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊?)
71&72
Cikin kasala da mutuwar jiki yake tafiya tsirarun mutanan da suka rage a gurin suka dinga mika gaisuwarsu zuwa gareshi baya iya amsawa hannu kawai yake daga musu ya wuce.....Ya kusa isa kofar shi ya tuna da maganarsu da Maimartaba idan yake cewa idan ya fita ya bada umarnin fito da yaran, kai tsaye can ya nufa ya tarar da masu tsaron kofar suna shawagi a gurin, suna ganinsa suka zube gwiwa a kasa suke gaishe shi tare da sunkuyar da kansu kasa, a kasalance yace."Ku bude yaran nan su fito." Yana kare maganar ya juya da niyar barin gurin........."Yallabai babu lafiya." Da sauri ya juyo yana kallon mai maganar cikin rawar murya yace." 'Daya daga cikin yaran ce ta suma."
Gabansa ne ya fadi jin abinda bawan ya fada, da sauri ya dawo da baya, bawan ya matsa masa hanya ya shiga dakin, wayarsa ya kunna yana haskawa, ganinta a shema tamkar matacciya gabansa ya tsananta fad'uwa! da sauri ya tsuguna kusa da ita tare da umartar daya daga cikinsu ya kawo masa ruwa.
Ido ya tsirawa fuskarta yana mamakin tsayin lokacin data dauka a sume, hannunsa ya d'ora a kirjinta shuru babu alamun numfashi, ya sauke ajiyar zuciya tare dayin zaman durshan a gurin, kanta ya tallafo ya dora a cinyarsa, yana danna kirjinta a hankali a hankali, Bawan ne ya shigo da ruwa a hannunsa, ya kar'ba tare da umartarsa ya futa, bayan futar bawan sai ya shiga shafa mata ruwan a fuskarta da wuyanta yanayi yana kallon fuskarta, ya kai minti goma sha biyar yana aikin shafa mata ruwa a fuska bata motsa ba, jikinsa ya dinga kyarma yana addua Allah yasa itama ba mutuwa tayi ba.......Ruwan ya ajiye a hankali ya gyarata a jikinsa rigarta ya cire yayi saurin kauda kansa yana sauke wani irin numfashi, ya kai minti biyar yana kallo gefe guda kafin ya dan juyo a hankali yasa hannunsa a ruwan ya d'ebo ya yayyafa mata a jikinta ya cigaba da shafawa a kirjinta, hannunsa na mutsika nonowanta yana ya'ki da zuciyarsa kada ta rinjayeshi, yafi bukatar ta farfad'o tayi rayuwa a duniya.
Ido jawur ya cigaba da shafa mata ruwa a sassan jikinta yana sakin wani irin nishi mai wahalar gaske.

Ganin gashin idanunta na motsi yasa ya sauke ajiyar zuciya, alhmdullhi ya fad'a sai ya saurin de'bo ruwan da yawa ya yayyafa a fuskarta, a firgice ta bude idonta tana kalle-kalle a dakin, wayarsa ya dauka yana haskata, ta dinga kallonsa shima yana kallonta, jikinta tabi da kallo taga babu riga ballanatana breziya duk ya cire mata ga sanyin ruwa tana ji da tashin tsigar jiki, hannuwanta tasa ta rufe kirjinta zafafan hawaye suka shiga zubowa a fuskarta bakinta na rawa take so tayi magana amma ta kasa fargaba da tashin hankali sun dabaibayeta

A kasalance yace."Kina iya saka kayan ki ko na sanya miki.'' Kallon banza na watsa masa ina masa kallon macuci azzalami wato duk guje-guje na sai da yasan yanda yayi yazo ya cutar dani

Hannu nasa na goge hawayen fuskarta, Yace."Kisa kayanki mu fita daga cikin duhu da sauro." Banzar harara na watsa matsa tare da dauke kaina

"Kada ki 'kara hararata ballantana kiyi min tsaki sai ranki ya 'baci.''' A zafafe nace" Sai me idan raina ya 'baci! ashe da sauran 'bacin rai bayan wannan da nake ciki, wato ka samu labarin a inda nake shine ka biyo dare kazo ka biya bukatarka a kaina ko."!?

Kallona yay da yanayi na 'bacin rai a tare dashi yace."Idan ina so nayi wani abu dake ba sai na biyo dare na fakaici idanun mutane ba, ko can baya ni ne banga dama ba banyi ra'ayin yin abinda nake so dake ba dan haka ki daina wannan maganar sam ba wannan dalilin ne ya shigo dani ba''

A fusace! nace"To ai sai ka fada min dalilin daya shigo da kai! gashi nan ka tu'be min riga kaima ka cire botiran rigarka wane irin iskanci ne yasa zaka tu'be min rigata bayan bana cikin hayyacina."


"Sumayya bana neman wata magana mai tsayi na fada miki ba wannan dalilin ne ya shigo dani dakin nan ba ki yarda ko kada ki yarda be dame ni ba ki tashi kisa kayanki mu fita daga cikin duhu."

Tsaki! mai karfi naja nace"Babu abinda zan......Bakina ya murd'e min ya tsira min jajayen idanunsa, nan na hango tsantsar damuwa da tashin hankali a cikinsu.

Mutsika min le'buna yake cike da muguna hawaye suka dinga karakaina a kuncina, sai da ya gaji dan kansa ya sakar min baki.
Kaina na sunkuyar kasa hawayen azaba na zubo min .

Rigata ya dauko zai saka min da sauri na daga hannu zan mareshi! ri'ke min hannu yayi ya murd'e da kyau! yace." Marina zakiyi irin na kwanakin baya." Shuru nayi ina kallonsa, yace."Ki kiyaye aikata hakan idan kuma kin'ki watarana kina ji kina gani zan 'balla miki hannu babu abinda ya dameni." Yana gama maganarsa ya jefa min rigata a jiki da fadin "Dallah dauka kisa ki tashi."
Babu yanda na iya haka na dauki rigar nasa hannuna daya murde sai zafi yake min.

Mikewa tsaye yayi yana mayar da botiran rigarsa, yace."Ina d'aya yarinyar take?" Shuru nayi masa, ya buga min wata irin tsawa da fadin"Ba magana nake ba." Nace"Muddubo yazo ya fita da ita."
Shuru yay yana kallona na dauke kaina tare da nufar kofar fita, sawun tafiyarsa naji a bayana da sauri na 'kara gabana ina addua a cikin zuciyata


Jugum-jugum! na samu iyayenta Tambaya taci kuka ta koshi kanta sai ciwo yake mata, ina shigowa suka mike tsaye suna godewa Allah! Tambaya rungumeni tayi tana kuka hade da dudduba jikina, nace"Tambaya dan Allah ki daina kuka wuya bata kisa kuma Allah zai bayyana gaskiya dukkaninku ku kwantar da hankalinku


Babana ya rike hannuna a sanyaye yace.''Sumayya dole hankalinmu ya tashi ana tuhumarki da aikata mummunan abu ba zamu ta'ba samun nutsuwa ba sai gaskiya ta bayyana babu shakka duk wanda ya aikata wannan abu bashi da imani tunda gashi yayi nasarar kashe mai rai."


Cikin faduwar gaba nace"Waye ya mutu a cikinsu.'' A sanyaye yace."Isa ya rigamu gidan gaskiya yanzu haka gawarsa na ajiye sai da safe za'ayi jana'izarsa." Zubewa nayi a gurin ina fadin "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!! Tambaya tasa hannu ta rungumo ni ina kuka muka shiga daki tana rarrashina.

Yanda naga dare haka naga rana, tsabar fargaba da tashin hankali ya hanani rintsawa, 'bangaran Magajin Sarki ma hakan take a zaune ya kwana yana tunanin yanda zai 'bullowa al'amarin babu shakka akwai saka hannun Muddibo a cikin faruwar wannan al'amarin ya rufewa iyayensa maganar ne saboda gudun tashin hankali dan mutukar Maimartaba ya tabbatar da cewa Muddibo ne ya aikata wannan mugun abun to zai dauki mataki akansa kamar yanda yake yankewa duk mai laifi hukunci, 'Bangaran Ciroma da iyalansa kuwa zasu sake 'kullatarsa dashi da iyalansa gaba gami da 'kiyayyar juna zata sake nunkuwa akan tada shiyasa kawai yace matsalar ta faru ne daga man da'akayi suyar doyar dashi, amma dole ya zauna da yarinyar da tayi aikin ya tsorarta da ita domin ya tabbatar da zarginsa.


Kasa tsayawa nayi na karya kummalo na nufi sashensa, nan na samu Haruna da Hamza a harabar gurin sunyi jugum-jugum! ganinsu ya sanya hawaye suka 'kwace min koda na karasa inda suke kasa magana nayi kallonsu kawai nake ina share hawaye.

Haruna yace." Ba kuka zakiyi ba Sumayya addua ya kamata kiyi." Nasa hannu na goge fuskata "Haruna ya mukaji da hakurin rashin Isa."! Sunkuyar da kansa yayi murya na rawa yace." Hakuri da godiya Isa ya rasu yayi shahada muna rokon Allah ya gafarta masa." A sanyaye na amsa da "ameeen ya rabbi dan Allah kuyi hakuri da faruwar wannan al'amari Haruna kunsan ba zan ta'ba cutar daku ba, wallahi dana san akwai guba acikin doyar nan ba zan kawo ku muku ba kai kanka kasan yanda mutanan gidan nan ke dauki ba dadi akan Yarima burinsu suga bayansa Allah bai nufeshi da cin doyar ba sai ku gashi sunyi nasara sun kashe wanda beji ba be gani ba amma babu komai zasuje su tarar da Ubangijinsu."
Hamza yace.Hakane maganarki Sumayya mu bamu ga laifinki ba wallahi saboda tuntuni mun riga mun san halinki ba zaki cutar damu ba sabida haka ki kwantar da hankalinki duk wanda kikaga ya mutu to dama can kwanansa ya kare Allah yasa ta wannan sanadin Isa zai rasa rayuwarsa muna rokon Allah ya kar'bi shahadarsa.''
Jiki a sanyaye na amsa da ameen ya rabbi ni zan shiga gurin Yarima." Suka ce to sai kin fito."

Yana tsaka da saukowa daga benan shi na shiga, sai na tsaya har ya karasa saukowa, kauda 'bacin raina nayi na gaishe shi. a dakile ya amsa min. nace"Me zakace dangane da abinda ya faru jiya."? Harara ya watsa mun yace." 'Yar jarida ce ke da zaki titsiye ni da tambaya."?

A dake nace"Dole na titsiye ka da tambaya saboda duk abinda 'yan uwanka keyi maka baka ta'ba yarda gashi sanadiyar cin doyar da aka zuba maka guba a ciki wani yaci ya mutu ina fatan yanzu ka gazgata maganata."


"Kinga Sumayya ba wannan ne a gabana ba wanda ya mutu dama can kwanansa ya 'kare mai yasa su sauran da suka ci doyar basu mutu ba, bana son zargi akan abinda mutum baida tabbas a kai nayi binkice na gane ba guba ce ta janyo faruwar al'amarin ba man da yarinyar tayi suyar doyar dashi shine ya gur'bata saboda haka kada na sake jin kinyi wata magana akan wannan al'amarin idan na sake jin kin sako wani nawa a ciki sai ranki ya 'baci!

Kallon shashasha nayi masa nace"Ai dama ba zaka ta'ba yarda ba sai ranar da suka kai ka 'kasa sannan zaka yarda da abinda ake fada maka! kai me 'yan uwa kullum baka so ace ga abunda sukayi maka su kuma kullum cikin shirya maka mugun abu suke ka'ki ka gane ka dauki son duniya ka d'ora musu idan sun kashe ka iyayenka su sukayi asara su kuwa ranar zasuyi kwanan farin ciki bukatarsu ta biya a kanka."


Har na 'kare maganata idanunsa na tsaye a kaina, yace.''Idan sun kashe ni ina ruwanki."? shuru nayi ina kallonsa ya cigaba da cewa 'yan uwana ne ba naki ba ko Wu'ka suka dauko suna yankar namar jikina idone naki kullum ina fad'a miki cewa ki fitar da kanki akan abinda be shafeki ba kin'ki kije kiyi tayi yanda suke farautata kema ba zasu barki ba." Yana gama maganarsa yazo ya wuce ta gabana fita yayi daga falon, da sauri nabi bayansa na sameshi tsaye shida hadimansa suna magana nan na gane gurin jana'izar Isa zasu tafi! a sanyaye na nufi gurinmu ina share hawaye shikkenan Isa ya mutu mutumin kirki sarkin fara'a da barkwanci Isa bashi da abokin fada kullum zaka sameshi da carbi a hannunsa, duk wanda yasan Isa dole ne ya fad'i halinsa nagari.

Koda na koma gurinmu shuru na same shi Tambaya bata nan shima babana baya nan jikina ya bani dukkaninsu sun nufi gurin jana'izar Isa, juyawa nayi nima da niyyar naje can inda ake jana'izar sai kuma nayi wani tunani gurin nasan akwai dandazon mutane ina iya zuwa wata hatsaniyar ta tashi, can kuryar daki na shiga na kwanta a shimfidata rufin dakin na tsirawa ido ina tunanin rayuwa hakika da ina da inda yafi nan da tuni na gudu dan masifar ta isa haka! tunani nake akan maganarmu dashi ta dazu na yarda da maganarsa da yake cewa nima ba zasu barni ba saboda yanda nake saka ido sosai akansa da dukkanin abinda suke aikatawa, ni kaina na rasa me yasa nake damuwa dashi da lafiyarsa sam! bana kaunar abinda zai cutar dashi ko ya ta'ba lafiyarsa inda shi kuma kullum yake nuna min na tsaya a matsayina babu ruwana da 'yan uwansa babu shakka da zan iya dauke idona daga kansa da abinda suke masa to dana zauna lafiya, amma ba zan iya ba saboda ina tsananin tausayawa mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka qallafa ransu a kansa, hawaye masu dumi ne suka zubo a kumatuna nasa hannu na goge wasu na sake zubowa hakika ina cikin tsaka mai wuya ina rokon Allah ya kawo mana mafita dani dashi da dukkanin wanda yake da damuwa a cikin zuciyarsa.............Haka na yini a kwance lokacin sallah ne kawai yake tayar dani, Tambaya bata shigo gidan ba sai dab da magariba ta shigo kai tsaye kicin ta nufa ta ajiye kayan abincin hannunta, tsakar gidan na fito muka hadu tace"Ashe kina ciki dama."? kaina na daga nace "Tun dazu dana shigo na tarar bakwa nan bacci ya dauke ni." Tace."Ayya ai bayan futar ki can gurun Iyayen Isa naje akayi jana'iza dani la'asar nayi kuma na nufi gurin aikin abinci shiyasa ban shigo da wuri ba." Nace"Sannu da aiki nima nayi niyyar zuwa sai na fasa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.''

Tace."Ai gwara da baki je ba dan ni kaina zaman hakuri nayi a gurin Lami da sauran mutane sun had'u sai gulma sukeyi

Please Login or Register in order to submit comment