Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwanta, suka dinga hira, har ta gaza boye mata abinda ke damunta ta sheda mata, ita kanta aunty Zeey din sai da jikinta yayi sanyi kuma ta tausayawa Hamra'un.

Suna tsaka da hira Madam da Nabila sukayi sallama.


Cikin sakin fuska ta amsa ta mike domin girmamawa. gurun zama take nuna mata, ita kuwa aunty Zeey din kamar wacce aka aikowa da mutuwar iyayenta, muraran ta fito da bacin ranta da kishinta.


Madam wayayyar macace mai ilimi da sanin ya kamata, ta kalleta da fadin." Zainab kina nan kenan."?

Ta dauke kai da fadin." Aikuwa."

Murmushi tayi kafin ta juya tana amsa gaisuwar da Zinat ke mata, a mutunce suka gaisa Madam tayi mata gaisuwa daman abinda ya kawota gidan kenan.


Aunty baki a tabe ta kalli Nabila da fadin." Ke kuma kin isa kenan babu wanda yake da mutuncin samun gaisuwarki a cikinmu.

Tace." Haba dai Aunty Wallahi ina ta gaisheki ba kiji ba sai nace bari ku gama gaishe-gaishe sai mu gaisa a nutse.

K'aramin tsaki taja ta kawar da kanta.

Itama Nabilan taji takaicin abinda tayi mata amma sai ta daure ta sake gaisheta, ta amsa kamar bata so.

Ta juya ta gaishe da Zinat din tare dayi mata gaisuwa. ta amsa a sake da nunawa kulawa.


Ba su wani zauna ba suka suka tashi da niyyar tafiya, har bakin kofa ta rakasu tana godiya.

Tana juyowa suka hada ido da Zeey sai harararta take, taja tsaki mai karfi kafin tace." Wannan matar kike wa ladabi matsiyaciya sumu-sumu macijin sari ka noke.

Ta zauna kujerar dake fuskantarta tace." Aunty zeey me yasa kike zagin Madam ne? wallahi ni duk laifinta da kike fadi ba tayi min komai ba.


Tace." Dama yaushe za tayi miki tunda baku hada miji ba, matsiyaciya ai gashinan tana zaune da god'amemiyar 'yarta taki auruwa, babu mashinshini."


Cike da mamaki tace." Aa kamar an sa ranar auranta.

Tsaki taja da fadin." A bakin wa ki kaji babu wani mai so bakin jinine da ita.

Yar dariya tayi kafin tace." A bakin maigidana naji cewar dashi aka karbi kudin auranta an sanya shekara guda.

Aunty Zeey jikinta yayi sanyi ta zuba mata ido da mamaki a tare da ita.

Tace." Wallahi kuwa kin san abinda yayi Asp shi yayi mijina shiyasa na samu labari.

Tace." Aikin banza to meye abin rufa-rufa dan ya fito ya fada min wani abune mtwwws! ni na rasa me yake damun Asp wallahi matar nan gabad'aya ta shanye shi sai abinda tace masa.....


*Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
5/10/22, 13:59 - Binta: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





_*(Uwace ita a gurina kuma 'Yar uwa ce, ina jin ita din kamar 'yar uwa ta ta jini, ta damu da damuwataƒ™öi ta kasance kullum mai min addua da fatan alkairi, na rasa a wane matsayi zan ajiyata a zuciyata, tana kira na da Mamana, ni kuma ina kiranta da Daughter, dalilin rubutuna muka hadu, tsayin shekaru hudu muna tare abin farin cikin kuma muna gari d'aya, Daughter ZAINAB KHABIR ISHAK koda nisan in da kike ya kai birnin sin sai nayi fatan Ubangiji Allah ya sadamu da juna, to ballanatana muna cikin gari daya, wannan zumuncin zai cigaba da wanzuwa da ikon ALLAH. na jinjina miki k'warai Allah ya saka da alkairiƒ™¹jƒ™Ž_)*_



*129*
Cikin nazari take kallonta tana auna maganganunta, ba tun yau ba ta lura da cewar tana da masifar kishi irin wanda ba a so, to idan ba hakaba meye laifin Madam mace mai mutunci da sanin ya kamata, a ganinta idan haka duk kishiyoyi suke to babu shakka za'a samu maslaha a zamantakewa, amma Zeey ta tsawwala da yawa, tunda suke da Madam bata ta'ba zagin Zeey ko ta fadi wata mummunar kalma a kanta ba, amma ita a koda yaushe cikin zagin matar take.

Ajiyar zuciya ta sauke tace." Zeey ki sanyawa zuciyarki salama don Allah kiyi tsaftataccen kishi, ba wai ina goyan bayan Madam bane amma a ganina kamar bata da matsala da zakiyi hakuri to babu shakka zaku zauna lafiya."

Tsaki taja da fadin." Na lura dai tsakaninmu babu amana fuska biyu gareki Zinat idan ba haka ba mai zai sanya a gabana kina goyan bayan mutsiyaciyar matar nan da kowa ya san da cewa mutuniyar banza ce wacce babu abinda tasa a gaba sai bin bokaye da zinace-zinace duk domin biyan bukatarta." cikin masifa da kumfar baki take maganar.

Ita dai tsabar mamaki kasa cewa komai tayi, kawai ta dinga kallonta tana jimanta al'amarin.

Tana cigaba da zagin Madam din ta lalubi mayafinta ta yafa, ta mike da fadin." Ni nayi nan ai yau na fahimci inda kika nufa kuma."

Ta mike da fadin." wallahi Zeey baki da fahimta itafa rayuwa gabadaya hakuri ake da ita, amma duk kin bi kin tayar da hankalinki sai zage-zage kike akan kishiya wacce bata damu dake ba, ta mayar dake shashasha wallahi kiyi gaggawar gyarawa."

Ta watsa mata kallo mai muni kafin taja wani dogon tsaki fuuuuu! ta kama hanyar fita tana surutai marasa ma'ana.

Baki a bud'e ta bita da kallo har ta fita daga falon, girgiza kai tayi tana mamakin al'amarin, tabbas an san kishi halak ne amma a ganinta irin nasu aunty Zeey din ya sa'bawa sharia domin kuwa zuciya za ta sanya su aikata abinda ba shikkenan ba.
Ita dai zata cigaba da hakurin zama da Hamra'u tunda dai Allah yasa yarinyar ta gane gaskiya to sai suyi hakurin zama da juna.

*BAYAN WATA UKU*

Zaman lafiya da daidaito yake wanzuwa a gidan tun bayan dawowar Hamra'u babu wata matsala data sake faruwa, kowacce na kokarin kyautatawa 'yar uwarta hakan yayi wa Uwale dadi, sai dai kuma shi daga b'angaran uban gayyar babu wanda ya san abinda yake cikin zuciyarsa sai Allah sai kuma shi, amma yana bala'in jin haushin had'e masa kai da sukayi, idan Zinatu tayi magana a gidan to ta zauna, duk yanda yaso ya ruguza alakarsu ya kasa, a yanzu Hamra'u tafi jin maganar Zinatu a kan tashi maganar, babban takaicinsa kenan, zai bada umarni ayi abu amma idan ya dawo gidan sai ya tarar ba'ayi ba.


Hamra'u cikinta wata bakwai ta gaza komai ta lanjare abinka da mara jiki, cikin har rinjayarta yake saboda girmansa, anyi scanning an tabbatar da cewa twins 'yan biyu ne duk mata, wannan dalilin yasa likita ya kafa mata dokoki, wannan bai dameta ba tunda akwai kyakykyawar fahimta a tsakaninsu, gabadaya ta tattara mijin ta barshi a gurin Zinatu......Hakan yayi masa dadi mutuka, amma bai nuna ba, sai ma ya fara wasu irin zantuka domin neman magana da tada zaune tsaye.

Cike da mamaki ta kalleshi bayan ya gama maganganunsa.

"Ta nan ka bullo kuma."?
Ta fada tana masa kallo na rashin fahimta.

Yace." Eh kwarai kuwa ai gaskiya ce, gabadaya kin tattara komai kina zalintar 'yar mutane duk abinda ki kace shi za'ayi idan kina tursasa Hamra'u to ni baki isa ba."!
Cike da karsashi da kwarin gwiwa yake maganar.

Ta danne bacin ranta dalili ba taso suyi hayaniya hakan babu amfani, amma ta lura kwana biyu neman masifa yake da ita.

"Kai yanzu dan Allah ba kaji kunyar fadin wannan maganar ba."?

Shuru yay mata yana duba wayarsa.

Ta girgiza kai cikin 'kunar zuciya tace." Ka tashi ka tafi dakin nata ai ba rike maka kafafu nayi ba, domin bani na gayyatoka ba."

"Ba za'a tashi ba." ya fada yana watsa mata harara!

Ta daga masa hannu da fadin." To tunda abun ya kasance haka kaje can ku yanke shawara da matarka, amma kada ka kara shigo min daki ranar girkinta."

"Kin riga kin lalata min ita yaushe zanyi magana taji ta saurara."

Ta dinga kallonsa da mamakin furucinsa ta rasa wane irin hali ne dashi kwana biyu ya d'ora mata karan tsana masifar yau daban ta gobe daban.

Tashi tayi ta fita daga dakin ta barshi, shi kad'ai ya gama duk wasu uzurinsa ya fito cikin milk din jallabiya, tana zaune a falo tare da Marakisiyya suna kallo yazo ya fita yana baza 'kamshin turare, bayanshi tabi da kallo tana ayyana wasu abubuwa a kanshi gabadaya ya sauya halaye sai tsiro musu da abubuwa yake marasa dadi.


Babu kunya a daran ya lallabo da bukatarsa, aikuwa ta furje tace." Tunda yana zarginta da zalinci to yaje can gurin matar tasa ya biya bukatarsa itama ta daina yarda tunda abun arziki yana zama sharri

Yayi-yayi da ita ta'ki, sai ya shiga kwantar da kai yana yi mata dadin baki tai masa banza ta cigaba da gyarawa yaronta shimfida.

Kallonta yake yana lumshe idonsa lokacin tana sanye da karamar riga iya gwiwa mai santsi duk ta kwanta a jikinta komai yana gani a idonshi, hallitarsa ta sanja wata irin jaraba ce take cinsa. ya dinga wani micincina ido yana shafa gemunsa.

Ta gama komai ta nemi guri ta kwanta duk yana kallonta.

Kallonsa tayi da fadin." Idan zaka fita ka kashe min fitila.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ." Kina tunanin kinfi karfina ko."?

Da sauri tace." Me za kayi min to ko ka danne ni kayi ta karfi babu abunda zaka samu."

"Haka ki kace."?

Shareshi tayi, ta gyara kwanciyarta tare da rufe jikinta da bargo.

Ya tashi yaje ya kashe fitila ya dawo gaba gadi gadon ya nufa.

Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi yana kokarin cire rigar jikinsa.

Kamar ya san abinda take shirin aikatawa yayi gaggawar rike hannunta rikon tsauri yayi mata ya fara gudanar da abinda yake ganin shine mafita a rayuwarsa.

To da yake sun riga sun zama daya ya gama gane lagonta duk turjiyar da take masa abu daya yayi mata ta bada kai bori ya hau, dan har sai da ta fishi ficewa daga hayyaci! ita dashi a wannan fagen ba'a cewa komaiĪM0


*****
To har yanzu dai Commissioner yana kwance a asibiti tare da kyakykywar kulawa daga manya likitoci hakan ba yana nufin komai ya wuce ba, Aa ana so ya warware ma'ana ya samu sauki a yanke masa hukuncin da ya dace da abinda ya aikata a matsayinsa na wanda yayi rantsuwa da Allah cewa ya dauki amanar kula da k'asa da kuma al'ummar dake cikinta, iyalinsa na cikin tsantsar tashin hankali duk da cewa basu rasa komai ba na rayuwa amma tabbas suna da tabbacin cewa hukuncin da za'a yanke masa mai tsauri ne, dalilin gagarimin laifin da ya aikata na cin amanar k'asa.


******
Haihuwar Hamra'u tazo da tangard'a, wannan dalilin yasa babu shiri aka shiga da ita dakin fid'a domin ceto ranta da abinda ke kwance a cikin nata.

Anyi cikin nasara an ciro tagwayen mata kyawawa farare tas masu kama da ita lafiyarsu lau, itama kuma alhamdulillhi, ta tashi da hankalinta an kuma kira sunanta ta amsa.
Wannan ya sanya hankalinsu duk ya kwanta ganin yanda Allah ya takaita wahala komai anyi cikin nasara da amincewar ubangiji.

Allah kenan kana taka yana tasa, a daran Hassanar ta mutu ta bar Husainar, likita ya tsananta binkice gurin gano dalilin mutuwar yarinyar bai ga komai ba dan Ubangiji bai so ya gani ba, kawai dai ya kar'bi abarsa ne bayan ta nuna kamanni.

Ban ta'ba ganin kukan Umaru ba sai a ranar ya dinga share hawaye yana kallon Usainar yaso Allah ya hada duka ya bar masa domin da haihuwar yaran Allah ya jarabceshi da masifar son su.

Hakanan sukayi hakuri suka barwa Allah ikonsa.


Kwananta goma sha hudu sati biyu kenan aka sallamesu suka koma gida lokacin ta warware sosai tana iya komai da kanta sai dai wasu abubuwan Zinat din ke mata ko kuma ta sanya daya daga cikin hadimanta suyi mata.

Kwana arba'in da biyu da haihuwar jini ya 'balle mata, hankali a masifar tashe suka nufi asibiti aka fara bata taimakon gaggawa!

Sai da kwana ta biyar a kwance a asibiti sannan ta samu sassauci, likita ya kafa sharudai da dokoki kafin ya sallameta suka koma gida.


Ba batun bin ba'asi ya shigo dakinta ya rufe ta da masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, a ganinsa Ita take cutar yarinyar har hawan jini yake so ya kamata.

Wannan al'amarin yayi bala'in 'bata mata rai! da yake shad'ain yana kusa! abinda yake so kenan! sai ya kara rura wutar rikicin suka dinga masifa yana fada tana fada karshe dai 'bacin rai yasa yace ta fitar masa daga gida, ita kuma tayi rantsuwa ita din 'yar halak ce sai ta fitar masa daga gida kamar yanda ya bukata. amma kafin hakan dole ta in da aka hau ta nan ake sauka.
Wayar Asp ta kira domin sheda masa halin da ake ciki...
5/12/22, 07:44 - Binta: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




_*Sanin hali ya fi sanin kama, AYSHA BAGUDO wanda bai san ki ba shi zai miki mummunan zato d'an adam tara yake bai cika goma ba, alkairinki yafi sharrinki yawa, Aysha tarayya ta dake alkairi ne, ina jin dadin amincin dake wanzuwa a tsakaninmu, ALLAH ya hada fuskokinmu da alkairi*_



*130*
Lokacin yana gidan Madam bama ya jin dadi zazzabi na damunsa, sai kawai yace tazo gidan ta sameshi su tattauna amma ta janye kudirin tafiya gida hakan ba hukunci bane.

Koda taje gidan ta zube masa magana da duk abinda yake faruwa ransa ya 'baci sosai shi kansa ya kan rasa gane kan abokin nasa wataran.

Yace." Kiyi hakuri Zinat kin san kowane bawa akwai irin hali da d'abi'arsa, mafi akasari maza suna da wannan halin, idan sun ga iyalinsu na zaman lafiya da juna sai su dinga zargin wani abu amma ki bar ni dashi zan nuna masa kuskuransa."

Ta goge hawayen dake karakaina a saman fuskarta tace." Ranka ya dade ni kam nagaji wallahi a halin yanzu ina bukatar nutsuwa zuciyata ta samu sauki tunda yace na fitar masa a gida to zaman me zanyi duk sanda ya bukaci cigaba da zama dani sai na dawo, idan kuma karshen auran ne yazo Allah yasa haka shi yafi alkairi."


Ya girgiza kai da fadin." Ba za'ayi haka ba, komai yayi tsanani maganinsa Allah, dazu mu kayi waya dashi yana gurin aiki nima abinda yasa ban fita ba zazzabi ke damuna, amma tabbas zai shigo idan ya dawo zamu tattaunar maganar kada ki damu ki tashi ki koma dakinki."

Ta girgiza kai da fadin." Babu fa inda zan koma ai tunda kace zai shigo ina nan sai ayi wacce za'ayi idan ya gaji sai ya sawwake min.

Ya dafe kansa yana girgisa kansa, al'amarin ma'auranta yana nema ya jefashi cikin matsala kullum cikin sulhu har yanzu sunqi girma suyi hakuri da juna, laifin kuma ba na kowa bane na abokin nasa ne, shine mara hakuri amma babu komai ya san abinda zai masa.



Tunda suka gama hayaniyar ya fita bai sake tuna da matsala a gidansa ba, domin koda wasa bai yi tsammanin cewa zata yanke hukuncin tafiya ba, kawai barazana yayi mata tunda sun saba irin wannan rikicin da wanda ya fishi ya kuma dawo gidan ya sameta.

To wannan ne dalilin da yasa da ya dawo ya ga bata gidan hankalinsa ya tashi ainun! koda ya tambayi Hamra'u tace itama wallahi bata sani ba domin tana bacci lokacin data fita.



Jiki a sanyaye ya gudanar da uzururrukansa kafin ya nufi gurin Uwale kamar wani mara laka a jikinsa, shi kansa ya san da cewa yarinyar itace jin dadin rayuwarsa.


Ta kalleshi cikin nazari tace." Umaru kana da damuwa ga dukkan alamu."

Ya dan mutsika fatar goshinsa da fadin." Uwale ba zan boye miki komai ba sa'bani muka samu da Zinat shine ta bar gidan.

Uwale ta dinga kallonsa da bacin rai a tare da ita tace." Ni ba zan saurareka ba Umaru domin ko shakka ba nayi laifin naka ne yarinyar tana iyakacin bakin kokarinta a gidan nan, amma kai baka gani da idona nake kallon wasu abubuwan na rashin kyautawa da kake mata, amma tunda nake da ita bata ta'ba zuwa gurina ta kawo karar kayi mata laifi ba, saboda haka ni babu ruwana a cikin wannan al'amari."


Da gama maganarta ta tashi ta shige daki ta bar shi a zaune yana sakawa da kwancewa.


Ganin zaman bashi da fa'idah yasa ya nufi gurin Hamra'u, nan yace ta kira wayar Zinat din ta tambayeta.

Tace." Ai yanzu muka gama waya da ita take sheda min cewa tana KANO."

Gabadaya yaji yawun bakinsa ya d'auke! tsabar fargaba da rashin sanin takameman abinda zai fadawa iyayenta.


Gabadaya ya rasa abinda ke masa dadi babu karsashi a jikinsa ya fita daga dakin.


****
Kwana uku da faruwar al'amarin ya galabaita yayi wani zuru-zuru! dole ya tunkari ASP domin warware matsalar dan baya tunanin tunkarar mahaifin yarinyar shi kadai tilas Asp din zai zame masa garkuwa.


Aikuwa yana zuwar masa da maganar yace." Sai dai ka nemi wani ya shege maka gaba, ni ina da Uzuri."

Ya zuba masa ido da mamakin maganarsa.

Asp ya murtuke fuska babu alamun wasa a tattare dashi.

Ya girgiza kai da fadin." Ka san dai da kunya na tunkari mutumin nan da wata magana Asp ni kaina na sheda abinda nayi ban kyauta ba, amma me yasa za kayi min haka bayan kasan cewa kaine wakilin yarinyar nan ai maganar babu ruwanka bata tashi ba."


Yace." Eh kwarai ni ne wakilinta, kuma ni na shige maka gaba har komai ya tabbata amma ka mayar dani mutumin banza wannan dalilin yasa nace na daina shiga cikin al'amarin kaje ka gyara kwa'barka."


Ya sharce gumin saman goshinsa! cikin damuwa yace." Zahirin gaskiya ban san ta inda zan fara ba wallahi, gabadaya ma kunyar hada ido nake da yarinyar gashi na kira wayarta ya kai sau ashirin taki d'auka da alama har yanzu bata huce ba.


Yace." Ga hanyoyi nan da yawa idan bata dauki wayarka ba, ai kana da kafa ka taka kaje can ka sameta ku warware matsalarku."

Yace." Shi yasa nace kayi min jagora tunda tana ganin mutuncinka."


Ya girgiza kai yana kara gyara fuskarsa, yace." Na fada maka fa wannan karan babu wani abu da zanyi maka kai da kanka zaka gyara kuskuranka."


Ya gaza furta komai domin gabadaya kansa ya kulle ga Asp din ya taurare masa ya kasa shanyo kansa.


Hannu na rawa ya dauko wayarsa number ta ya kira ya mika masa wayar da fadin." Taimakon daya za kayi min kace da ita ta daga waya ta."


Ya jim yana kallonsa kafin yace." Bari kawai na kira ta da waya ta."

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata irin damuwa a tare dashi.


Jin muryarta ya sanya jikinsa mutuwa wata irin kasala ta dabaibaye shi, ya tsirawa Asp ido a lokacin da suke wayar ji yake kamar ya kwace daga hannunsa.



Ya kalleshi da fadin." Tace babu damuwa amma dai kaji da kunnanka albarkaci na ne."

Bai damu ba yace." Eh ai kai din babban mutum ne shiyasa na kama kafa da kai."

Maganar ta bashi dariya sai da yayi kafin ya mike da fadin.'' Bari na shiga toilet na fito."

Be ce masa komai yana can tunanin irin kalaman da zai yi mata zuciyarta tayi rauni ta dawo gareshi.

Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke a lokacin da ta daga wayar.

Cikin nutsuwa ta gaishe shi, ya amsa yana mamakinta, ta dora da tambayarsa mutan gidan, yace." duk suna lafiya sai dai kewarki.'

Shuru tai masa ba tace komai ba.

Ya raunana muryarsa kamar mummuni yace." Ke yanzu abinda ki kayi a ganinki shine dai-dai.''?


Tace." Me nayi."?

Kaskantar da muryar ya sakeyi yace." Saboda kawai sa'bani ya gifta a tsakaninmu sai ki tafi gida kin san halin da kika jefa mu a ciki kuwa ."?


'Karamin tsaki taja kafin tace." Kaga Umaru bana san wasu maganganu yanzu ina jiran takarda ta."!
Ba ta jirayi amsa ba ta kashe wayarta.

Aikuwa gigicewa yayi hannunsa na wani irin rawa yake sake kiran wayar, tana kallo taki d'auka.

Ya mike tsaye yana kai kawo a falo!

Cikin wannan halin Asp ya fito ya sameshi.

Ya kalleshi kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu!!

Shi kansa Asp din bai ta'ba ganin ya shiga tashin hankali irin haka ba.

Hankalinsa a kwance ya zauna kan kujera da fadin." Ya kukayi da ita."?


Ya sharce gumin goshinsa da jan kafa ya samu kujera ya zauna kafin yace." Asp yarinyar nan bata da hankali wallahi! da kamar da arziki muka gaisa a mutumce har ina murna amma budar bakinta tana jiran takarda wannan maganar ta 'bata min rai wallahi."


Yace." Allah ya kyauta to kadai yi kokarin ganin kayi gaggawar gyarawa tun kafin al'amarin ya lalace''


Yace." Wai kai da gaske kake ba zakayi min jagoranci ba."

Ya kishingida da fadin." Zancen kake so ai na yanke magana babu ruwana a cikin al'amarin dan ina so na tsira da sauran mutuncina a idon mahaifiyar yarinyar shiyasa na cire kaina daga sabgar."


Da karfi ya buga! hannun kujarar da yake zaune! ya mike tsaye! jijiyar kansa ta tashi idonsa yayi jawur!! ita da take daki a kwance sai da taji hargowarsa yana saukewa Asp din ashafa kamar wani ubansa.


"Dole da kai a cikin sabgar tunda tun farko kai kayi ruwa kayi tsaki al'amarin ya tabbata, mahaukaci kuke so ku mayar dani! ita tana dankara min duk maganar da tayi ra'ayi kaima kana farfad'a min abinda ranka yake so, to baka isa ka kashe min aure ba, idan ma kaine kake zugata duk zanyi maganinku."
Tamkar mahaukaci sabon kamu haka ya tubure!!

Yana kishingide yana kallonsa har ya kare cin mutuncin bai ce masa uffan ba, ya kama hanyar futa yana wani irin huci!

Fitarsa keda wuya Madam ta fito ta zauna kusa da mijin nata suna sake tattauna maganar.

Wayarsa ya dauka ya kira Zinat din ta fito ta samesu a zaune.


Tace." Duk ina jin hargagin da yake ka rabu dashi kawai domin mai hali baya fasa halinsa wallahi ranka ya dade dan dai kawai ka hana ni tafiya gida ne amma da tuni na tafi dan zaman nawa bashi da amfani."


Yace." Akwai dalilina na aiwatar da hakan, shi kuma ki kyale ni dashi idan da sabo na saba da halinsa."


To a daran dai bai iya rintsawa ba, asubar fari ya dauki hanyar KANO zuciyarsa cike da tararrabi da Alhinin 'bacin ran da zai je ya tarar....




*Kada ki karanta min littafi idan baki

Please Login or Register in order to submit comment