Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kina ina yanzu."? tambayar da yay mata kenan

Tace."Wace irin tambaya ce wannan."?

Dan murmushi yay kafin yace." Ke dai ki bani amsar tambayata."

Tsaki tayi niyyar ja, sai kuma ta fasa tace."Abokinka ya kamata ka tambaya ai."

Yace." Tun dazu nake kiran wayarsa bata shiga shine dalili.

Tace." Okey to gani yanzu a cikin gidanka zaune daki."

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Alhamdulillhi dama abunda nake so naji kenan daga bakinki."

Numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Da bakin ki yanzu kike sheda min cewa kina cikin gidana zaune a daki a matsayin matata ta sunnah, bana gari anyi komai an gama duk ta dalilin jajurcewar abokina wanda ya tsaya min a cikin al'amara na, Asp hankalinsa bai kwanta ba sai da ya tabbatar da cewa kin zama mallakina bayan haka kuma be samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar da cewa ya kawo ki har cikin dakinki ya ajiyeki kamar yanda ki ka sheda min a yanzu.


Ina so ki san cewa ni mutum ne mai tsananin kishi akan abuna, duk da ga yanda akayi wannan auran namu cewa bana so bakya so hakan ba zai sa na zuba miki ido kiyi abunda ki ke so ba.........Katse shi tayi ta hanyar fadin." Me kake nufi ne."? Yace ." Alkairi nake nufi dake."? Shuru tai ba tace masa komai ba amma ya fara kai ta karshe........Ya cigaba da cewa." Yanzu sabuwar rayuwa zakiyi domin aure ba wasan yara bane. Ki kiyaye mu'amula da wanda bai dace ba, kada kiyi mamakin cewa ina can wani gari amma labarin halin da kike ciki zai sameni har lokacin dawowata gida, ki goge number duk wanda kika san cewa ba muharramin ki bane kafin na dawo, sannan ban yarda kije ko'ina ba, akwai securities da zasu sheda min shigarki da kuma fitarki. idan kina da wata Matsala kina iya shedawa Asp domin dashi kadai na yarda bayan shi ban yarda wata magana ta shiga tsakaninki da ma'aikatan gidan nan ba, wannan shine abunda nake so ki rike a ranki kuma kiyi aiki da umarni na."


Wani bacin rai ne ya tsaya mata a wuya jin yanda yake mata magana cikin isa da gadara kamar wani ubanta, koda yake tunda aka daura auran iyaye da kakanni ke mata nasiha cewa tabi mijinta sau da kafa domin tunda ta riga ta bar hannun iyayenta to basu da hakki mai karfi a kanta kamar yanda mijinta yake da hakki a kanta, dole ne ta bishi ta kuma bi umarninsa, yi nayi bari na bari wannan sune irin nasihohin da aka dinga yi mata kafin kawo ta dakin mijin nata shi kansa Maimartaba fada yay mata sosai akan biyayyar aure...............Ita kuma sai take ganin kamar wannan shine dalilin da yasa su mazan suke nuna izzah! da gadara! akan matayensu saboda wannan damar da Allah ya basu, gashi dai ita ko kwana daya ba tayi ba a gidan ya fara kafa mata sharud'ai bayan ma baya garin amma yana nuna mata isa da mulki saboda kawai yana wasu tunane- tunane marasa kyau a kanta, Ajiyar zuciya ta sauke tare da kokarin danne bacin ranta tace." To i dan ka gama maganar ka zan kashe wayata.''

Ashe maganar banza take domin tuntuni ya kashe wayarsa ya bar ta da tata a kunne sai kace shashasha.

Cire wayar daga kunnanta yayi dai-dai da zubar hawaye da take kokarin dannewa.

Ta jefar da wayar saman gado ta dafe kanta da duk hannuwa biyun kukan takaici ne ya kufce mata!

Hakika an kassara mata rayuwa tunda har aka had'ata aure da bagidajen namiji wanda bai iya lallashi da lallami mace ba, kullum bakar magana ce take shiga tsakaninsu, ya za'ayi ta iya zaman aure dashi a haka, burin ta a rayuwa ta auri namijin da ya iya soyayya da kula da mace sai gashi ta b'ige da auran bahagon mutum wanda ya rako maza duniya.

Ta jima tana share hawayen takaici kafin ta cire kayan jikinta ta nufi bandaki domin watsa ruwa a jikinta.

Lokacin da ta fito yayi dai-dai da shigowar Uwale dakin, suna hada ido sai tayi saurin kawar da kanta tana ya mutse fuskarta, kai tsaye dressing mirror ta nufa.

Uwale jikinta yay sanyi domin ta lura da irin kallon banzan da tayi mata.

Ta nuna kamar ba ta gani ba da 'yar fara'a tace."Sannu yarinyar arziki dama na shigo ne na dubaki sannan na tambayeki ko da akwai abunda ki ke bukata, ga dai abinci can a falo ajiye miki."

Uwale tafi minti biyar da gama maganar amma ko kallonta ba tayi ba ballantana ta samu damar bata amsa, sai kawai ta juya jikinta a sanyaye ta bude dakin ta fita tana mamakin rashin tarbiyar yarinyar.

Tana fita taja tsaki ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta daga shi har kakar tasa haushinsu takeji.

A sanyaye ta zauna kan kujera jikinta duk babu karsashi.

Hamra'u ta kalleta da fadin." Uwale ya naga kin dawo da jiki a sa'bule."?

'Yar dariya tayi da fadin." Aa ba wani abu ne ai Gimbiyar tayi bacci lokacin dana shiga gurin nata."
Cikin rashin so ta bayyana mata abunda ya faru ta k'arasa maganar.

Tai 'yar dariya da fadin." Uwale kenan, jikina na bani akwai wani abu da ya faru amma tunda kina boye min shikkenan."

Da sauri tace." Ke 'yar nan me zai faru kuma idan ba alkairi ba? ni babu wani abu da yarinyar nan tayi min koda na shiga na sameta tana bacci sai kawai na fito nace idan Allah ya kaimu da safe sai mu gaisa da juna kawai kuma sai ki zargi wani abu."

Yanda take magana da son kare Gimbiyar sai ranta ya baci kishi yasa ta ta'be baki tare da mikewa da fadin." Ni zan shiga na kwanta sai da safe."
Ta bita da kallon nazari kafin tace."Allah ya tashemu lafiya." Da sauri ta bar gurin ranta a masifar b'ace, Ta rasa gane mai yake damun Uwale, tunda Gimbiyar ta sauka a gidan ta rasa nutsuwarta sai kai kawo take tsakanin kicin da falo da kanta ta shirya mata abinci mai dadi irin na tsofaffin hannu, duk tana zaune tana kallonta tana rawar jiki ta dauki abincin domin ta kai mata, sai gashi kuma ta dawo da jiki a sab'ule, tabbas wani abun ne ya faru amma wai sai take 'boyewa mata kome menene dalilin hakan oho! ita kam tayi alkawari cewa ba 'yar sarauta ba ko wacece ita wallahi tayi rantsuwa cewar ba zata bauta mata ba, tunda dai ba zaman ta take a gidan ba, itama Uwalen itace ta d'orawa kanta wahala amma ita kam duk rintsi ba zata yarda ayi haka da ita ba.




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/4/22, 19:16 - Buhainat: *55&56*
Kayan bacci masu taushi ta sanya a jikinta, babu wani kuzarin kirki a tattare da ita, ta kwanta kan gado tare da jan bargo ta rufe jikinta. Ido ta rintse bacci kawai ta keso tayi ko ta samu saukin 'bacin ran da ya addabeta a zuciyarta, amma duk yanda taso ta gayyaci baccin yaki zuwa, idonta tar mazai! har yanzu tana tunanin kausasan kalamansa a kanta, a mafarki bata ta'ba tunanin cewa za tayi irin wannan auran ba, duba da yanda ta dinga katantanwa da tarin maza masu mulki da mukamai daban-daban wanda suka mace a soyayyarta. Tabbas maganar Sakina gaskiya ne in da take cewa a lokacin da kake dama ya kamata ka dama, idan ba haka ba, to wanki hula zai kai ka ga dare, yanzu wa gari ya waya gashinan ta 'bige da auran namijin da bata ra'ayinsa...........Idonta a lumshe take wannan tunanin tana kuma hasaso fuskar b'oyayyan masoyinta wanda take jin bala'in sonsa a cikin zuciyarta saboda soyyarsa da kuma iya kalamansa, shi kad'ai ne a yanxu zai kawar mata da b'acin ran dake damunta, amma kuma haka kawai a zuciyarta take jin tsoron kiran wayarsa. zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta dan gyara kwanciya tana takure jikinta guri guda kamar me jin sanyi koda yake hakan nan ta tsinci kanta cikin wannan halin duk sanda za ta kwanta bacci ta dinga juye-juye kenan kafin baccin ya dauketa sai an ja dogon lokaci tukkuna, daga nan kuma sai ta dingi mafarkai barkatai! masu kyau da marasa kyau har sai garin Allah ya waye tukkuna, za ta tashi cikin tsananin sha'awa domin duk yawanci mafarkan akan sex ta keyi alhalin sam bata kwanciya da abun a ranta, wannan dalilin yasa tayi alkawarin cewa duk magungunan matan da Aunty's dinta sukayi mata guzurinsa ba zata sha ko daya ba domin ta riga ta d'ora zarginta kan cewa duk magungunan data dubga dalili, saboda da can ba haka take ba, duk yawan shekarunta bata ta'ba mafarkin wani da namiji ba sai gashi kullum idan ta kwanta sai tayi mafarki gata dumu-dumu da namiji suna sex yana biya mata bukata.


Bargon dake rufe a jikinta ta sake gyarawa kafin k'ira ya shigo wayarta dake saman bedside, cike da mamaki ta dauki wayar tana dubawa ashe bata kashe ba ta kwanta.


Sunan 'boyayyan masoyi ne yake yawo kan fuskar wayar.

Gabanta ya dinga faduwa ta shiga nazari da tunani akan ta daga wayarsa ko kada ta daga..........*"Ki goge duk number wanda ki kasan ba muharramin ki bane kafin na dawo, kada kiyi mamakin cewa duk halin da kike ciki zan samu labari saboda haka ki kiyaye kuma kibi umarnina."* Manganganunsa suka fad'o mata a rai, ta tsirawa fuskar wayar do tana kallo har ta katse.


Ya sake kira still dai bata daga ba, sai bin dakin take da kallo tana tunanin ko da akwai wata na'ura da ya daura a dakin domin ganin duk motsinta..............haka kawai take jin tsoron ya kamata da wani laifi mussaman irin wannan ba wai don tana tsoronsa ba, yanda ta lura dashi kamar shima yana zargin ta irin yanda wasu daga cikin jama'ar gari suke mata abunda ta tsana kenan a zarge ta akan fasikanci, wannan shine dalilin da yasa take jin tsoron daga wayar boyayyan masoyin nata.......Sai kawai ta yanke shawarar shiga whasp ta duba ko ya ajiye mata sako.


WhatsApp ya shiga domin har yanzu ya kasa yarda da abinda zuciyarsa take raya masa a kan yarinyar zai cigaba da gwadata har sai ya fahimci in da ta dosa.


Yaji dadin ganinta a online sai ya tura mata sako kamar haka.

_My love me yasa baki daga waya ta ba."_?

Ta bashi amsa kamar haka"

_Ai ba muyi da kai cewa zaka dinga kiran waya ta ba, idan hakan ma ta kama cewa nayi ka bari ni zan kira ka, to mai zai sanya ka kira ni a irin wannan lokacin."_


Yace."
_My love menene a ciki don na kira ki na debe miki kewa, na san da cewa angon naki baya gari shiyasa nake so na debe miki kewarsa._

Emoji ta tura masa na mamakin maganarsa.

Yace." _Kin san irin son da nake miki ne yasa nake bin diddigin duk abinda ya shafe ki mijin baya gari yana gurin training ko ba haka bane."?_

Murmushi takaici tayi kafin ta tura masa da amsa.

_"Eh hakane maganar ka amma nayi mamakin yanda akayi ka san haka."_

Yace." _Kada kiyi mamaki da sanina halin da kike ciki, ko kin manta nima d'an cikin garin katsina ne, ai shiyasa ban cire tsammanin had'uwa dake a kurkusa ba tunda muna cikin gari daya._

Amsa ta bashi kamar haka..
_"Faruk ina sonka sosai irin wanda ban ta'ba yiwa wani namiji ba, hakika zan so na ganka a zahiri sai dai wannan mijin nawa yana da zafi! kuma ma'aikacin tsaro ne ina jin tsoron ka shiga hannunsa ba za kaji dadi ba._


Murmushi yay lokacin da ya karanta sa'kon ya gyara kwaciyarsa kafin ya bata amsa kamar haka.


_"Na san da haka my love bana tsoron had'uwa dashi ballanatana naji tsoron gwabzawa dashi ina mai tabbatar miki da cewa a kanki babu abunda ba zanyi ba, zan iya fansar da raina akan soyayyarki ina so ki cire tsoro a cikin zuciyarki, ki cigaba da kokarin ganin kin rabu dashi kizo gare ni muyi aure, ni nayi alkawarin baki dukkanin kulawar da kike bukata."_


_Cikin jin dadin maganarsa tace."Nagode sosai wannan manganun naka sun kashe min jiki wallahi na rasa abinda zance maka nagode sosai da kulawarka kuma nayi maka alkawari cewa zanyi kokarin ganin mun hadu da juna, kada ka damu bukatarmu ta zata biya da izinin Allah."_


_Yace." Nagode my love yanzu me kike bukata nayi miki wanda zai faranta ranki."?_

Shuru tayi bata iya ce masa komai ba, gabadaya ya gama kashe mata jiki da salon soyayyarsa.

Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba kuma yana ganinta a online bata sauka kawai ba tare damuwar komai ba ya tura mata sticks masu tayar da hankali gami da tayar da sha'awa mussaman yasa Adewale ya tura masa su, a cewarsa shima zai turawa matarsa domin taga irin style din da yake so tayi dinga yi masa idan ya dawo gari.

Adewale abun nema ya samu a take ya tura masa kala-kala wanda har sai ya rintse ido gurin kallon wasu daga ciki, don dai ma yana da kok'arin danne sha'awarsa amma da anyi katari da mara hakuri ganin sticks din zai sanya shi aikata aiki mara kyau.

Yana tura mata ya sauka daga layin ya dauki daya wayar tasa kai tsaye what'sApp din ya shiga tana online har yanzu.

Sai kawai yay mata magana.

_"Me kike a online? karfe goma sha biyu da rabi."_

Ganin shigowar sakonshi yasa gabanta mugun faduwa!.

Koda ta duba sai ta kasa magana, baki da jikinta gabadaya sun mutu in banda faduwa babu abunda gabanta keyi a dabarbace ta kashe wayar ta kwanta lamo kan gado ganin sticks din ya sanya ruwan ni'imar da ya saba zuba a jikinta yin 'karfi, gabadaya pant din ya jike ta dinga takure jikinta guri guda yanayin yana sake shiga jikinta sakamakon tashi da tsigar jikinta keyi nipples dinta basu ta bayi mata 'kai'kaiyi irin na ranar ba.

Haka ta kasance cikin mawuyacin hali har asubah bata rintsa ba sakamakon ciwo da cikinta ke mata.

Da 'kyar tayi sallah ta koma ta kwanta lamo kan daddumar ..........dole taja masa kunne kan cewa kada ya sake turo mata da hotonan iskanci.


Misalin bakawai da rabi na safe, Baraka wato daya daga cikin hadimanta tayi knocking din kofar dakin.

Ta mike zaune da kyar da fadin." Waye."?

Cikin girmamawa tace." Baraka ce ranki shi dade."

Sai da ta dauki kusan minti biyar sannan ta tashi taje ta bude mata kofar.

Tana shigowa ta zube gwiwa biyu tana gaisheta.

Da kyar ta amsa ta nemi saman sofa ta zauna yanayinta kadai shi zai nuna maka cewa akawai abinda ke damunta.

Ta kalleta da kulawa tace."Ranki ya dade ko bakya jin dadi ne? domin naga alamun haka."


Girgixa mata kai tayi da fadin."Lafiya ta lau ina Marakissiya."? tana nufin 'yar uwarta da suka zo tare.

Da sauri tace."Tana kicin domin had'a miki abin kari."

Tace."Okey ki hada min ruwan wanka, sannan ki shirya min kayana cikin wardrobe ki ajiye komai a muhallinsa."

Cike da bin umarni ta amsa da "an gama Gimbiya." Mikewa tayi da sauri ta kama hanyar toilet din sai ta dakatar da ita da fadin." Ruwan da d'umi sosai zaki had'a min kinji ko."

Ta amsa da "To ranki ya dade." Toilet din ta nufa cikin bin umarni.

Bayan ta hada ruwan ta fito sheda mata sannan ta fara sauke akwatinan kayan domin gabatar da aikinta na gaba.

Ta dauki kusan minti goma a zaune kafin ta yunkura ta tashi domin shirin wankan, kira ya shigo wayarta dake can kan daddumar da tayi sallah.

Kafin ma ta bata umarni taje ta dauko mata wayar, ta karba a yatsine tana dubawa.

*BA 'KYAUE* sunan dake yawo kan fuskar wayar kenan.

Tsaki taja da fadin.'' Da sassafe ya kira waya kamar wanda yake bin bashi.....Daf da zata tsinke ta daga tasa a kunne.

A maimakon tai masa sallama sai kawai ta sauke masa ajiyar zuciya a kunne, tai shuru da bakinta.


Shi yay mata sallamar ta amsa kamar bata so, yace."Kin tashi lafiya ya kwanan ba'kunta."?

A takaice tace."Alhamdulillh." Ya dan ja fasali kafin yace."Jiya na gan ki a online misalin daya na dare ke da waye."? Cikin sigar zargi da tuhuma yake mata tambayar.

Gabadaya duk sai ta daburce! tana so ta tonawa kanta asiri........."Wac....Wace irin tambaya ce wannan.''?

Yace."Alamu sun nuna baki da gaskiya ga yanayin yanda kike magana a daburce! okey duk wani abu da za kiyi ina ji a jikina domin bani kadai bane akwai masu sheda min halin da kike ciki saboda haka ki shirya dawowata sati biyu masu zuwa."

Da kyar ta iya saisaita muryarta amma inaa! sautin muryarta rawa yake yaki saisaituwa duk ta tsure jin yace bashi kadai bane dama tun haduwarsu a daji ya ta'ba fada mata cewa yana da aljanu tana jin tsoron kada su sheda masa halin da take ciki, Ta daure da 'kyar tace." Bana neman tashin hankali ko wata 'bakar magana zargin da kake min ba zan ha naka ba ka cigaba sannan duk sharrin da aljanunka za suyi min sun jima ba suyi ba, dai kai dasu duk baku dame ni ba." Tana gama maganarta ta kashe wayarta ba ta jira amsarsa ba.

Shi kam dariya ma ta bashi ya tsaya ya dara yana jin dadin yanda game din yake tafiya a tsakaninsu, Hamra'u ya kira suka gaisa ganin zata jashi da hira alhalin fita zai yi yasa a tausashe yace." Kanwata yi hakuri yanzu ba lokacin hira bane lokacin aiki ne idan na dawo na samu nutsuwa zan kira ki muyi hirar soyayya, yanzu ki bani Uwale idan tana kusa mu gaisa domin na kira wayarta bata shiga ba."

Taji ciwon hakan a cikin ranta amma sai ta danne a sanyaye tace" Bari na kai mata wayar tana kicin.?

Cikin mamaki yace."Kicin kuma me takeyi? Hamra'u keyi menene amfaninki."?

Da sauri tace."Aa nima ba laifina bane domin babu yanda banyi da ita ba akan ta zauna ta huta ni zanyi mana komai kamar yanda na saba tace ita lallai sai ta shiga kicin da kanta tayi wa amaryarka girki."

Ya dinga girgiza kai yana mamakin rigima irinta kakar tasa, yace." Yanzu je ki kai mata wayar za muyi magana."

Ta amsa da "to" kafin ta je ta kai mata wayar.

Tana kicin taa dage sai soya funkaso take gefe guda kuma had'addiyar miyar taushe ce wacce taji nama da gyada da alayyahu sai turiri take tana tayar da kamshi mai dadi.

Tace."Uwale yayana yana son magana dake."

Da farin ciki ta karbi wayar tasa a kunnuwanta da fadin." UMARU ina kwana.''?

Ya amsa da "Lafiya lou Uwale kun tashi lafiya ya kuma hidima da jama'a."?

Tana 'yar dariya tace." Alhamdulillhi an yi taro lafiya jama'a kowa ya koma gidansa lafiya "

Yace."To alhamdulillhi haka akeso nima insha Allahu sati biyu masu zuwa na kammala komai na dawo gida."

Tace."Alhamdullhi, Allah abin godiya UMARU Allah ya dawo da kai lafiya ya kuma cigaba da baka nasara akan duk abunda kasa a gaba."

Ya amsa da "Ameen ya Allah." Ya dora da fadin." Yanzu Hamra'u take sheda min cewa kina kicin kina aiki Uwale me yasa ba zaki zauna ki huta ba sai kin wahalar da kanki Hamra'un za tayi duk abinda ya dace."

Tace."Hakane maganarka UMARU bahaushe yace YABA KYAUTA TUKWICI yarinyar nan 'yar babban gida ce wannan shine dalilin da yasa nake dawainiya da ita ba wai don naga gazawar ita Hamra'un ba."

Yace."Duk da haka dai ki samawa kanki lafiya domin ba na so kina aikin wahala saboda shekaru sun ja miki, idan ya kama na dauko masu hidima a gidana ina da ikon yin hakan, domin itama Hamra'un ba ita take da alhakin haka ba tunda dai ba auranta nake ba."

Tace." To yanzu dai nayi laifi kenan don na nuna kulawa a kan matarka."? Ya girgiza kai da fadin." Ba kiyi laifi ba Uwale cewa nayi ki zauna ki huta ita Hamra'u ta cigaba da aikinta kafin na dawo gari."

Tace."Ai shikkenan tunda kai baka san gwaninta ba sai anjima." Sallama tayi masa ta mikawa Hamra'u wayar tana mita akan abunda yay mata.

Yace." Hamra'u bata wayar da sauran magana dani da ita.

K'in kar'ba tayi yana jinta tana fadin." Oho!oho! ai ka gama magana UMARU har da zan nuna kulawa kan matarka ka gwasale ni."

'Yar dariya yay ya daga murya yanda za taji sosai yace."
Yanzu dai mu bar wannan maganar haka Uwale kina ji na ko."?

Shuru tai masa ta cigaba da soya funkasonta.....Ya cigaba da cewa." Wannan kayan abincin da aka jibge a store ba na bukatar na dawo na samesu, ki tara 'yan uwa da abokanan arziki da kuma yara na ina nufin su Alba kenan duk ki raba musu, ni a bar min kadan sun isa."

Tace."Kana da hurumin hakan amma sai an shedawa ita GIMBIYAR domin itama tana da hakki."

Ya jima yana mamakin maganar kafin yace." To shikkenan ki sheda mata cewa Umarni na ne nace rabawa mabukata kayan masarufin da tazo dasu sannan kuma nagode da hidima."

Tace." UMARU ba haka sharad'in kayan gara suke ba, kana da hakki tana da hakki, saboda haka ni sai naji hukuncin da ta yanke idan bakinku yazo daya shikkenan sai ayi yanda kace."

Takaici ya ishe shi, kawai ya kashe wayarsa ba tare da yayi mata sallama. aljihu yasa wayar, ya janyo takalmansa ya fara kokarin sanya wa a kafafuwansa dake cikin safa, yana ganin idan an jima kadan, ya samu sukuni zai kira yarinyar ya sheda mata hukuncin da ya yanke, bawai don baya bukatar kayan masarufin ba, kawai dai yana so ya tsira da mutuncinsa domin ganin tsarin yarinyar watarana zata iya yi masa gori akan wani abu daya dangance ta.




*SAI RANAR MONDAY ZA MU CIGABA DA IKON ALLAHƒ™čjƒ™Ž_ NA 'DAUKI HUTUN KWANA BIYU A CIKIN SATI DAYA, INA GODIYA A GARE KUƒ™čjƒ™Ž_*




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/7/22, 09:01 - Binta: *G-J-S-U-R*
*57&58*
'Daure da towel mai dan girma wanda ya sauko mata har kasan gwiwa ta fito daga toilet din har yanzu akwai sauran damuwar a tattare da ita sai kace wacce ta jima tana kuka idonta yayi wani ja bayan 'kan'kancewar da sukayi wannan shine dalilin da ya sanya Baraka baiwar ta dake aikin jera mata tufafinta a wardrobe ta fara lallaminta saboda duk wani abunda yake faruwa suna da labarinsa.

Rarrashinta take sosai tana kara 'kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari masu kyau wanda idan ta dauk'esu to tabbas za taci riba anan a gaba.

A 'kalla Baraka za ta iya shekaru talatin da biyu a duniya, ta girmeta da wasu shekarun shiyasa take da sinkaye da hangen nesa, kuma dai itama haka kawai take sha'awar uwar dakin nata tayi zaman aure kamar yanda sauran 'yan uwanta suke zaune a dakinsu lafiya, sau daya ta ta'ba ganin mijin nata a zahiri amma duk iya bin k'wa'kwkwafin ta bata hango wani nakasu a tattare dashi ba, namiji ne na nunawa sa'a irin mazan da suke da wahalar samu, 'yan mata da yawa ire-iren ta gasu nan birjik duk a zaune babu mijin aure, wannan dalilin ne yasa take mamakin wasu 'yan matan idan dadi yayi musu yawa suke tsula tsiya iri-iri, ita dai

Please Login or Register in order to submit comment