Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bama neman tashin hankali kullum alkairi muke nema ZINAT Abokina zuma ne (ga zaki ga harbi) duk da ban dade tare dashi ba amma na karanci halayyansa tsaf, yana da saukin kai ga wanda ya fahimceshi baya san tashin hankali zaku jima wani sa'bani bai shiga tsakaninku ba, mutukar ka kiyaye abunda zai kawo muku samun sab'anin, ina so ki rike wannan don Allah na ro'ke ki, ki zauna lafiya dashi kada ki bari shaid'an ya samu nasara a kanki.

Murmushin takaici tayi kafin tace." Ranka ya dad'e na rasa me yasa kake tsoron wannan abokin naka kullum kai kenan gurin yi masa campaign kana kare shi to ni duk abunda zaka fada a kansa ba zai sanya naji tsoronsa ba, ka fada masa cewa nafi karfin wannan b'akin kwallin da yake rambad'awa a idanuwansa, kuma be isa ya firgitani ba."

Dariya yayi kafin ya girgiza kai da fadin." Kinga mu bar wannan maganar tunda kin kasa fahintata, yanzu wane shirye-shirye kike yi game da hidimar biki."?


Baki ta ta'be ta yatsine fuska da fadin." Wane irin shirye-shirye sai kace wacce za tayi auran so, ni babu wani shiri da nake kuma bana bukatar komai daga gurinku.

Yace." A haba dai gimbiya koda ba auran so bane yana da kyau ki d'an yi gyare-gyare domin ki fita daban a cikin mutane kasancewarki amarya, wannan hakkinki ne, ki fadi ko nawa kike bukata sai na tura miki yanzu."

Dariyar takaici tayi kafin tace." Ranka ya dade na fada maka fa duk campaign din da za kayi masa wallahi baku isa ku sayi soyyayata ba, ka fada masa cewa har yanzu bai kai wannan matsayin ba,har yaushe yayi arzikin da zai zo yayi wa mutane tutiya dashi."

Asp ransa ya b'aci da jin maganarta, Yace." Wai ke mai yasa kike hakane? ina yi miki kallon mai ilimi amma kina aikata aiki irin na jahilai, Zinatu girman kai da izzah duk ba dabi'u ne marasa kyau! don Allah ki daina sannan ki daina daukar kanki daban da mutane dukkaninmu Allah ne ya hallice mu, shine kuma yayi mai kudi da talaka kuma shi yake bada mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, kada kiyi mamaki Allah zai iya musayan miki rayuwa, ki zama mak'askanciya wannan kadan kenan daga irin hukuncinsa, ki gane duniya dan Allah."

Shuru tayi da alama nasiharsa ta shige ta.

Ya sauke numfashi da fadin." Kin san Allah duk wannan kai da kawon da na keyi akan wannan al'amari UMARU be sani ba, amma magana kadan sai kice ina masa campaign ai ba sai munyi campaign ba tunda an riga an bamu kyauta wane campaign za muyi." Cikin zolaya ya 'karashe maganar.

Ta kuwa fusata! da fadin." Ina ganin mutuncinka fa kada ka 'kara yi min irin wannan wasan."

Ya tsagaita dariyar da yake da fadin." Na daina ranki ya dade yanzu ake hukuma ce sai da rarrashi duk da an bamu kyauta muna godiya domin mun san ba karan mu ne ya kai tsaiko ba, dami a kala muka tsinta."


Ya mutse fuska tayi da fadin." Shikkenan ni zan kashe wayar sai an jima."

Yace." Ai bamu gama ba.

A k'agauce tace." Saura me kuma Asp idan kun kwantar da hankalinku saura 'yan kwana ki aka kawo muku ni." Yace." Ni da kaina ma zanzo na dauke ki tunda kin san mutumin naki baya gari yana gurin training ni ya bar wa wuka da nama."

Shuru tayi ba tace uffan ba.

Yace."Yanzu nawa kike bukata."? babu wasa yayi maganar.

Itama cikin rashin wasa tace." Bana bukatar ko kwabon ku."

Murmushi yay da fadin."Shikkenan tunda kin ce haka mu dai mun fita hakki dan kada watarana ayi mana gori."

Cikin takaicinsa tace." Sai an jima kace ina gaishe da da k'awata."

Ba ta jira jin abinda zai ce ba ta kashe wayarta tana jan tsaki, gabadayansu haushinsu takeji, magana d'aya da yayi itace ta tsaya mata a rai..........Inda yake cewa duk wannan abubuwan da yake abokin nasa bai sani ba, ita ai ta dauka shine ya wakiltashi kafin yayi tafiyar yazo ya kafa masa gwamnati a gurinta, tsaki mai tsayi taja kafin ta nufi toilet da bacin ran hakan a cikin ranta.


Cikin baccin da ya fara daukarsa yaji alamun kira ya shigo wayarsa.

Hannu yasa yana laluban drowar da wayar ke kai.

Murmushi yay ganin mutumin shi ke kira.

Yasa wayar a kunnashi tare da sallama a bakinshi.

Daga daya bangaran Asp din ya amsa da fadin." Jarumi ya na jika wani iri ne ina fata dai lafiya."?

Ya bude murya sosai da fadin." Lafiya lou wallahi bacci ne ya fara daukana kiran wayarka ya tashe ni."

Yace."Okey yau kun dan samu hutu kenan."

Hamma! yayi kafin yace." Eh amma hutun duka na two hours shine dalilin da yasa na kwanta domin na rage baccin dake idona.

Yace."Hakan yana da kyau mutumina, shin kana waya mutuniyar kuwa."?

Murmushi yay wanda ya tsaya iyakar fatar bakinsa ya fahimci wacce yake nufi shiyasa yayi murmushin takaici.


Asp yace." Tunda naji wannan murmshin naka na san baka d'auki shawarata ba, UMARU na fada maka fa dole a wannan ga'bar kai ka sauka kabi yarinyar a sannu a hankali kafin ta shigo gidanka, idan ta shigo shine zaka nuna mata kai ne a sama da ita, har yanzu ka kasa gane hallayar 'ya'ya mata, wallahi da ka dauki shawarata da tuntuni yarinyar nan ta bada kai bori ya hau, na fada maka tana bukatar rarrashi da nuna kulawa mybe *Ilove you* wannan ka kasa fad'a mata wanda ni nayi imanin da cewa abinda take bukata kenan."


Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Asp wannan yarinyar fa bahaguwace! kai ne har yanzu baka fahimta ba kake ganin nuna kulawa ko kuma *I love you* zasu sanya ta daina rashin mutunc! a haka take, haka Allah ya halliceta zan iya karyar mata da kaina domin samun soyayyarta ta dizgani girmana ya zube a banza a wofi, ni bana wahalar da kaina a in da na san ba zan samu biyan bukata ba.

Yace." Kai ne dai kake ganin haka, amma ni nayi imanin cewa kabi wannan matakin wallahi sai ka sameta a hannu kuma ka gwada ka gani."


'Yar dariya yay da fadin." To shikkenan zanyi kokarin ganin nayi abinda kace duk yanda mukayi da ita za kaji."

Yace."Yawwa haka nake so na ji yanzu nima muka gama waya da ita na kira ta domin jin abunda take bukata na hidimar biki, tace bata bukatar komai daga gurinku kuma tace lallai na sheda maka cewa duk irin campaign din daka turo ni gurinta to ba zaka samu abunda kake so ba.

Dariya ya fashe da ita, ya dinga yi yana girgiza kai ya ma kasa magana saboda yanda dariyar taci karfinsa.

Asp shima yana dariyar yace." Ai ban ta'ba ganin rigimmiyar yarinya irin wannan ba, amma na fahimci nasiha tana ratsa ta wannan ma makami ne wanda ya cancanta ka rike hannu bibbiyu.


Dakatar da dariyar yayi da fadin." Asp maganar nan ta bani dariya da haushi wallahi amma dai dariyar tafi yawa, lokacin da tace maka kana yi min campaign sai kace mata kai din ubangidana ne kafi karfin kayi min fadanci ko wani aiki, amma na san da wuya ka iya mayar mata da martani.

Yace."Ni da nake kokarin ganin an raya sunnah ma'aiki SAW yaushe zan dagula al'amarin ai duk abunda tace dai-dai ne, amma ina kokarin ganin na nusar da ita idan tayi wani shirman."

Yace." Nagode sosai abokina, yanzu a wace matsaya kuka tsaya."?

Yace." Tunda tace bata bukatar komai namu shikkenan, amma na fada mata cewa kada daga baya tazo da wata magana.

Yace." Kwarai kuwa tunda an fita hakkinta wannan shine sharadi."

Yace." To kaji yanda mu kayi da ita insha Allahu kuma za'a gabatar da komai cikin tsari amma ya kake gani? shin a ranar da aka daura auran za'a daukota ko kuma sai washe garin ranar."?


'Dan 'bata fuska yayi da fadin.'' Aa ana d'aurawa ka d'auko ta, bana tsammanin ma mahaifinta zai bari ta sake kwana a gidan mutukar an d'aura auran."

Yace." Okey to shikkenan hakan dama shine tsari mai kyau, insha Allah zanyi kokarin hakan ya tabbata."

Yace." Godiya nake abokina Allah ya kara zumunci ya kuma bar abotar mu." Ya amsa da "Amen ya rabb mutumina ka wuce aboki a gurina a matsayin dan uwa kake a gurina."
Cikin wani irin farin ciki yace." Haka kake a gurina wallahi jinka nake tamkar wanda muka fito ciki d'aya Allah ya kawar da idon makiya a tsakanimu." Ya amsa da "Ameen ya Allah, kafin suyi sallama da juna.


*****
To a daran ranar da sukayi wannan tattaunawar da Asp din ya yanke wata shawara wacce yake ganin zata taimaka masa gurin tantance nagarta da kamun kan yarinyar........ da yake yana amfani da layin waya biyu sai yayi amfani da d'aya layin da ba kowa ya san shi dashi ba, wata irin rikitacciyar wasika ya tura mata mai dauke da zafafan kalaman soyayya da tsuma zuciya, sosai yayi amfani da hikima gurin shirya kalaman wanda yake da tabbacin cewa dole su rikirkita mata lissafi, bai fayyace mata kansa ba asali ma babu suna a wasikar yana tura mata ta in box ya cire sim card din ajiyeshi cikin cover shi sai an kwana biyu zai mayar.

Kamar yanda yayi tsammani hakan ne ya faru, domin tunda ta karanta wannan text din gabadaya ta rikice ta rasa abinda yake mata dad'i a duniya, macace mai bala'in son soyayya da kulawa shiyasa kullum cikin kallon indian film take amma irin na soyayya, tana bala'in san wanda kullum zai dinga kasheta da kalamai yana rarrashinta ita kuma tana masa shagwaba da sangarta irin yanda take so, kasa hakuri tayi tabi layin da kira, sai dai ta kisa sau goma ana ce mata layin baya aiki a halin yanzu, hawaye masu zafi ta share tana tunanin daga wace duniya sakon wasikar yazo gareta? wanene wannan wanda yake da kalamai irin haka? shin a ina ma ya samu number ta, hakika zata so ganin sa ido duk talaucinsa zata iya zama dashi mutukar zai dinga lallabata yana bata abincin zuciya irin wanda take bukata.

Hanci taja tasa hannu ta goge hawayen dake karakaina a saman fuskarta, me za tayi da wancan ba 'kauyen mutumin da be iya komai ba sai 'bakar maganar magana, tunda take dashi bai ta'ba yi mata kalami mai dadi ba, ko a lokacin zaman su a daji ta lura kan dole yake rarrashinta idan wata masiba ta sameta, a halin yanzu ya kamata ace ya kwantar mata da hankali domin samun soyayyarta amma saboda girman kai ya kasa duk sanda zaiyi mata magana cikin gadara! da isa! shi ba kowa ba sai iko yake nuna mata ita kam ba zata yarda da wannan ba, tunda dai a zahiri tana ganin ta fishi da komai ba zata yarda ya mulke ta ba har yanzu tana nan akan bakanta ko auran sukayi.


Kullum sai ta gwada kiran layin sai ace mata baya aiki, duk ta susuce! tunaninta ya kammanin mutumin yake? ba abunda take so taji sai muryarsa.

A na gobe daurin auran da daddare kowa yai bacci ta gwada kiran layin, jin yana shiga yasa ta tashi zaune da saurin gaske farin ciki gabadaya ya cika mata zuciya burinta kawai ya daga wayar taji sautin muryarsa.....





*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/2/22, 18:21 - Buhainat: *49&50*
Cikin wata murya mai sanyi da ita kanta bata san tana da ita ba tayi sallama kafin ta dan lumshe idonta tare da sauke ajiyar zuciya tace." ina so na san da wanda nake magana a halin yanzu."

Shuru yayi bece uffan ba, gabad'aya mamaki ya gama kashe shi jin irin salon da take masa magana ashe ta iya tausa murya haka.

Shuru be ce mata komai sai saukar numfashinsa da takeji a kunnawanta.

sai gabadaya jikinta ya sake rikicewa, haka kawai Allah ya jarabce da son wanda bata ta'ba gani ba.

Cikin 'yar shagwaba tace." Please don Allah waye ne? kwana biyu da suka wuce naga text dinka shine dalilin da yasa ma na kira ka domin san kowaye kai ."

Idonsa a lumshe yayi d'an gyaran murya kamar zai yi magana sai kuma yaja bakinsa yay shuru, gabadaya ta gama kashe masa jiki da salon da take masa magana yana masifar son shagwabbiyar mace.

Jin yayi shuru ta sake narkar da murya dan a zahiri saura kadan ta fashe da kuka tace." Ba za kayi min magana ba ko? ka san kuwa halin da ka jefa zuciyata."?

Zaune ya tashi yana sake rike wayar a kunnunsa, kafin ya aro wata murya da duk bin diddigin mutum ba zai gane muryarsa bace yace." Wani bawan Allah ne yazo da kokan baran shi a k'urataccan lokaci."

Jikinta ya 'kara saki jin sanyayyiyar muryarsa ya jefa ta cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa, tace." Kayi min bayanin kanka daga ina kake kuma ina ka samu number ta."?


Dan murmushi yay kafin yace." Sunana FARUK ni dan asalin hajar katsina ne." Gabanta yay fadi jin ya ambaci garinsu ma'kiyinta.

Jin tayi shuru ba tace komai ba ya cigaba da cewa." Na tsinci hotonki a social media gurin wani biki sai kawai Allah ya jarabceni da tsananin sonki da kaunarki, talaka ne ni amma ina da zuciyar nema, duk da na san cewa ke ba tsaran aure na bace, hakan bai sa na saduda ba sai da nayi fafutukar samun number ki, amma wanda ya bani number ya sheda min cewa aure za kiyi hakan be firgitani ba, tunda dai ba'a daura auran ba zan fito na nuna miki tawa soyayyar da take gudana a cikin jikina."

Tun sanda ya fara maganar take share hawaye, tayi duk yanda za tayi ta tsayar da kukan abun ya fassakara, tana kukan tace." Kazo a 'kurataccen lokaci bawan Allah, sosai nake son mai sona kuma ina alfahari da soyayyarka, hakika da kazo a kan ga'bar da iyayena suka yanke min hukunci to babu shakka kai zan nuna musu a matsayin mijin aure, babu ruwana da talaucinka mutukar zaka bani abincin zuciyata bani da damuwa, yanzu maganar da nake maka gobe za'a daura min aure da wani wanda bana ra'ayinsa." Cikin wani irin kuka mara sauti takarashe maganar.

Jikinsa ne ya mutu jin kukanta yake har tsakiyar kansa, Cikin taushin murya da sigar rarrashi yace." Yi shuru ki daina kuka kinji ko wannan kukan da ki ke yana ta'ba min zuciyata ina jin kamar nazo inda kike na rarrasheki bana son zubar hawayenki.


Hannu tasa ta goge hawayen amma ba tace komai ba.


Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Yanzu ya za kiyi dani da soyayyata Gimbiyata bana jin zan iya rabuwa dake fa.''

A sanyaye tace." Nima bana tunanin hakan a zuciyata, ka bari a kwana biyu zan yanke shawara akan soyayyarmu."

Murmushin takaici yay kafin yace." Okey na fahimta yanzu zamu cigaba da gaisawa ne ta waya babu matsala hakan."?

Shuru tai na minti biyu kafin tace." Babu matsala amma ka bari ni zan dinga kiran ka"

'Yar dariya yay da fadin." Shikkenan my love yanda ki ke so hakan za'ayi amma inaso muna gaisawa koda ta charting ne."

Ba tare da damuwar komai tace."Wannan babu damuwa zanyi serving number naka yanzu."

Yace."To ina godiya my princess bari na barki ki kwanta ki huta ko, amma ina tabbatar miki da cewa yau ba zan iya rintsawa ba."

Da sauri tace."Saboda me."? Cikin tausayawa kansaYace. " Saboda gobe za'a daura miki aure da wani."

'Karamin tsaki taja kafin tace." Ka kwanta kayi barcin ka, kada kasa damuwar komai a ranka domin wanda za'a daura min aure dashi, bashi da wani muhimmanci a zuciyata, bana sonsa bana ra'ayinsa, da auransa da babu duk daya suke a gurina, ka kwantar da hankalinka nayi maka alkawari kai zaka mallake ni, domin da kai zuciyata ta aminta duk da ban ta'ba ganinka ba ina hasaso fuskarka a idona, ina sonka a duk yanda kake, zanyi mana duk wani kokari da zai tabbatar mana da biyan bukatarmu."

Yaji haushi da takaicin maganarta amma sai ya danne a zahiri ya nuna mata farin cikinsa, sallama yay mata da jin zafin maganganunta a zuciyarsa ya kashe wayar yana tsaki da fadin." Sakarai mara wayo kawai."

Kwanciya yay yana tunaninta, gabadaya ma ya raina wayonta da dubararta, koda yake macace mai rauni zata iya yin abinda yafi haka.


Agogon ya d'an duba, yanzu minti talatin kenan da wayarsu, ya kama sha daya dai-dai na dare, yanzu da Asalin number shi ya kira ta.


Sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka tana cin magani, wayar tasa a kunne amma ba tace komai ba.

Yay mata sallama cikin asalin muryarsa mai cike da amo!!

Ciki-ciki ta amsa tana ya mutse fuska.

Yace." Tun dazu nake kiran wayarki sai ace dani busy shin dawa kike waya a cikin wannan daran."?

Cikin tsiwa da gadara irin yanda take masa magana tace." Ina ruwanka da wanda nake waye? ko kana da damuwa da hakan ne."?

Daurewa yay yace." Ni nake da damuwa da hakan kuwa, dalilina kuwa nasan baki nutsuwa da kamun kai zaki iya raba dare da wani namijin a waya saboda rashin kintsi."

Zuciyarta ta dinga wani irin zafi da tukukin bakin ciki!

Abinda yake had'ata dashi kenan bakar magana, kwata-kwata be iya rarrashin mace ba, haka kawai zai tayar mata da hankali tana zaman zaman ta.

Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka tace." Bagidaje kawai kana da matsala wallahi, haka kawai zaka shiga rayuwata cikin daran nan to ta Allah bata ka ba"

Yay dariyar cusa takaici yace." Naji bagidajen ne dole kuma a zauna dani a haka na kuma bada umarni ayi ko ana so ko ba'a so."!

Tsaki mai tsayi taja irin wanda ta san baya so tace." Wahalalle kawai bani da lokacinka." Da sauri ta kashe wayarta domin bata so ta sake jin sautin muryarsa!

Bacci k'auracewa idonta yay ta dinga zubar da hawaye tana tunanin boyayyan masoyinta daya bayyana mata kansa a yau..........Shin wai ya za tayi da wannan takad'irin mutumin da ake kokarin aura mata bayan be tara duk abunda take da bukata ba.


Haka ta kasance cikin tsananin damuwa gami da juye-juye sai gefin asubah bacci mai nauyi ya d'aukata.

Shigar aunty Hassana dakin yayi daidai da bude idonta gari ya waye tarwai.

Zaune ta mike tana dan ya mutse fuska! wani irin ciwo kanta yake ba komai ya janyo mata hakan ba illah kwanan kuka da tunanin da tayi.

A nutse ta 'karasa kusa da ita ta tsira mata ido na minti biyu kafin tace." Sai yanzu ki ka tashi kenan."?

Kai ta daga a raunane tace." Aunty an d'aura auran ne."?

Girgiza kai tayi da fadin." Sai goma da rabi tukkuna, na shigo ne domin naga ko kin gyara jikinki ashe ke kina ma kwance."

Kai ta dafe da fadin." Jiya ban samu bacci ba sai gefin asubah, shiyasa ban tashi da wuri ba ko sallah fa banyi ba."

Tace." Zinat ba zaki sanyayawa ranki ba ko? me yasa kike so ki jefe kanki cikin wani hali, iyayenki fa ba zasu ta'ba cutarki ba."

Tace."Aunt Hassana don Allah mu bar wannan maganar domin ni ba wannan ne dalilin ya hana ni bacci ba, ai na hakura na barwa Allah."

Tace."Okey to idan hakane ki tashi ki gyara jikinki kiyi kwalliya sosai tunda kinqi yarda da ayi miki kitso da kunshi (lalle) irin na amare kada dai ki yarda mu da muke 'yan gayya mu fiki kyau zakiji kunya.

Murmushin takaici tayi tana kokarin saukowa daga gadon tace." Bana ra'ayi ne kawai, amma ban ha naku kuyi kwalliyarki ku ba, ban damu ba idan kun fini kyau."

Hanyar toilet ta nufa jikinta duk a sanyaye........Aunty Hassanar ta bita da kallo tana girgiza kanta, ta rasa wane irin hali ne da ita gabadaya a baud'e take.

Wani dan'kareran les ta fito mata dashi kudinsa ya kai dubu dari da wani abu rigar bubu ne anyi ado da wani irin net bayan stones din dake jikin les din an kuma baza wani stones din masu walwali a jiki, c-green ne, color shi tayi kyau sosai.

Duk wani abu da ta san za tayi amfani dashi sai da ta fito mata dashi ta ajiye mata.

Tana kokarin fita daga dakin, kira waya ya katse mata hanzari.

Ta dawo ta dauki wayar tana dubawa, sunan ba'kauye ne yake yawo kan fuskar wayar.

Cike da mamaki take duba wayar, waye wannan kuma? toilet din ta kalla, ta san halinta tun tana yarinya take da nawa bata da zafin nama haka take idan ta shiga wanka sai an manta da ita.

Yanke shawarar daga wayar tayi a nutse tai sallama.

Jin sabuwar murya cikin nutsuwa yasa shima ya amsa a nutse da fadin." UMARU ne."

Da sauri tace." Angon ne ashe kayi hakuri tana bandaki sai dai idan ta fito ko."

Yace."Babu damuwa idan ba matsala ina so na san da wa nake magana."

Murmushi tai kafin tace."Hassana ce yayar amaryar taka.

Yai murmushi da fadin." Ai kinga tambayar tayi amfani Auntynmu ya hidima da jama'a."?

Tace."Alhamdulillhi wallahi, Allah dai ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya UMARU kayi hakuri da yarinyar nan daban take a cikinmu tana da wani irin hali, amma kuma idan ka'iya zama da ita tana da sauki kai da iya mu'amula."

Yace." Kada ki damu aunty insha Allah zan rike amanarku zan iyakar bakin kokarina."

Tace." To mungode sosai Allah ya baku zaman lafiya."

Ya amsa da ameen ya Allah ya dora da fadin "bari na bari zuwa an jima zan sake kira."

Tace."To shikkenan babu damuwa." Sallama sukayi ta zauna zaman jiran fitowarta.


Ido suka hada lokacin data fito daga toliet din tace."Wai dama kina zaune har yanzu."

Tace."Nazo fita ba k'auye ya kira wayarki."

Saurin kallonta tayi suka hada ido ta girgiza kanta rai a bace tace." Kin ji kunya ko."?

Girgiza kai tayi tana dan tabe baki tace."Wane irin kunya kuma." Gaban dressing mirror ta wuce tana ya mutse fuskarta.


Aunty Hassanar tace."Kullum kina nuna mana cewa kin saduda ashe ba haka bane, a zuciyarki don iskanci ki rasa da wane suna za kiyi serving number sa sai da ba k'auye wai shin ma dame ki ka fishi kin san dai baki fishi kyau ba."

Tana 'yar dariya tace."Aunty Hassana ai sunan da ya dace dashi kenan, d'an k'auye ne dashi da family sa, kinga kuwa babu laifi don an kira shi da wannan sunan ba kauye bagidaje."

Ta girgiza kai cikin takaici tace." ki cire wannan sunan bai dace ba, gwara kisa masa sunansa na Asali hakan shi yafi mutunci."

Saboda bata san suyi ta ja'in ja yasa tace."To shikkenan aunty zanyi yanda ki kace din, amma da ya kira me yace miki."?

Tana kokarin mikewa tace." Be ce komai ba zai dai sake kiran ki abinda fada kenan.

Ta'be baki tai ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta.

Aunty Hassanar tana kokarin fita daga dakin ta dakatar da ita da fadin." Aunty Hassana ya maganar mutanan da aka tura su shirya min daki."


Tace."Ai babu wannan maganar domin mijin naki ya shedawa Maimartaba cewa ke kadai yake bukata akwai komai na bukata a gurin da zaki zauna wannan dalilin yasa aka rushe wacan maganar.

Ta girgiza kai da fadin." Wannan ai zubar da kima da mutunci ne, Aunty Hassana cikinku wa aka ta'ba yiwa haka? ai na dauka kowacce sai da aka cika mata daki uku da kaya amma ni saboda ba'a sona za bar ni haka, to wallahi babu wanda ya isa na dogara dashi da kayansa.

Hannu ta daga mata da fadin." Wannan maganar Maimartaba zaki samu ki fada masa bani da kika raina ba, Zinatu kije ki samu mahaifinki ki nuna masa cewa baki yarda da hukuncinsa ba, wannan shine zai tabbatar mana da cewa kin fita zakkah a cikinmu."

Tana gama maganar ta bude dakin

Please Login or Register in order to submit comment