Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mummunan fahinta, domin ni dake da Zinatu duk daya na dauke ku a zuciyata, bayan na shiga gurinta take sheda min cewa tafi bukatar ni nayi mata abinda za taci saboda taji dadin wanda nayi mata jiya, don haka kada ki sanya a ranki cewa domin ta tozartaki ta 'kyamaci abincinki."

Kasa magana tayi tsabar bacin rai da yanda zuciyarta take tururin zafi, zuwan gimbiyar gidan yana barazana da rayuwarta domin abubuwan da Uwale take mata zasu iya sanyawa zuciyarta ta buga......Tana can tana tunani Uwalen ta fita motsin kofa ne ya dawo da ita nutsuwarta.

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta mike ta nufi dakinta.

Tana shiga ta zauna gefan gado tare da daukar wayarta, kai tsaye number wayarsa nemo, a wannan ga'bar dole itama tayi wani k'okorin domin samun cikar muradin ta, bata iya k'arya ba amma tana ganin yau zata fara saboda abubuwan da Uwale da ita Gimbiyar suke mata a gidan sun isheta.


Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka duk ta sheda masa abunda yake faruwa bata tsaya a haka ba, sai da ta kara gishiri kamar yanda ta tsara hakan a ranta.


Yace." Hamra'u banyi mamakin jin wannan al'amarin ba, domin duk abinda akace min yarinyar ta aikata ba zan karyata ba, saboda dama can bata da tarbiya, to amma duk abinda za tayi ya tsaya iyakacin kaina domin ni na ajiye ta a gidan, ba zan lamunci taci zarafin wata daga cikinku ba, Mussaman Uwale da bani da kamarta a duniya , saboda haka kiyi hakuri idan na dawo zanyi wa tufkar hanci, na roki alfarma a gurinki cewa duk irin rashin arzikin da za tayi miki kada ki biye mata, ai kin fita nutsuwa da hankali da kuma ilimin addini, banda jahili babu wanda yake da ta'kidin cin zarafin dan adam wanda Ubangiji ya karrama shi a cikin hallita, mulki! izzah! iko! sune suke damunta da sannu ni zan sauke mata duk wani abu dake kanta."

Sassauta murya tayi cikin kissa gami da kokarin kar yaga laifinta tace." Insha Allahu zan kiyaye duk abunda za tayi min koda zata zagi iyayena ne to ba zan tanka mata ba, zan bari ne har ka dawo."

Yace." Yawwa nagode sosai my lov dina, maganar hidimar da Uwale take mata kada ki kara magana akai ki kyaleta tunda tana ganin zata iya idan na dawo dole ta ajiye aikin ta zauna ta huta."

Tace." To shikkenan Yaya na Allah ya dawo da kai lafiya."

Ya amsa da ameen ya Allah, kafin suyi sallama da juna.


******
Bayan kwana biyar da faruwar al'amarin, Asp ya kira ta a waya suka gaisa da juna ya tambayata ko tana da matsala tace babu, sai yace." To masha Allah haka ake so, ai mutumin naki yana kan hanya gobe mybe iwar haka ya sauka, ko da yake ma ai nasan ya fada miki dawowar tasa.

Gabanta yana d'an faduwa Tace." Aa ni bai fada min ba." Kawai ta tsinci kanta da fadin." Yaushe rabon ma da ya kira ni a waya."

Asp din ya shiga mamaki mutuka, kafin yace." Kinga kullum kuwa muna waya dashi kuma idan na tambayashi cewa kuna waya sai yace min Eh amma kiyi hakuri kada ki damu mybe aiki ne yay masa yawa.

Ta danne bacin ran dake taso mata tace." Ranka ya dade abokinka mak'aryaci ne, kuma bashi da kirki wallahi, ai ya san abinda ya aikata dole ya kare kansa a gurinka.

Yace." ZINATU ki daina jifan sa da irin wannan kalaman mijinki ne fa a koda yaushe ya zama magana mai kyau ce zata fito daga bakinki.

"Humm kawai ta iya cewa ranta idan yayi dubu ya baci Tace." Ba ka tambayi dalilin komai ba ka nema ka dora min laifi idan nace maka kana tsoronsa sai kace ba haka bane."


Yar dariya yayi yace." Ai na san labarin gizo ba zai wuce na koki ba, shiyasa ban tambayi dalili ba, amma dai ki fada min laifin da yay miki ina sauraranki."


Tace."Gabad'aya ya sanya an fita da kayan masarufin da masarautar mahaifina ta bashi, a cewarsa yafi karfin komai baya bukatar taimakon wani, shine ni kuma nai mamakin hakan nace har yaushe yayi arzikin da zai dinga yiwa mutane tutiya shin wai nawa ne ma albashinsa a wata."?


Asp din ya dinga jinjina maganar a ransa, ba tun yau ba yasan da cewar yarinyar ga'buwa ce zata iya farfada masa wannan maganganun.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Aa kece dai ki ka fahimceshi a bai-bai amma ba nufinsa kenan ba, domin mun jima da yin wannan maganar in da yake sheda min cewa akwashe kayan a rabawa mabukata, ba wai don baya bukata ba, tunda akwai wa'inda suka fishi bukata a raba musu sai a bar masa kadan, ni kaina yayi min kyautar wasu, nace A'a saboda nima Allah ya rufa min asiri, wannan shine dalilinsa, amma ina fatan bakiyi masa rashin kunya ba."

Shuru tayi masa domin shi kansa a yanzu haushinsa takeji ganin har yanzu yaki hango laifin abokin nasa .

Jin tayi shuru yasa ya gazgata zarginsa, yace." shikkenan shurunki ya bani amsa ba, kinga kuwa duk wani abu da yay miki a yanzu ke kika janyo amma bari zan kira shi yanzu domin naji komai daga bakinsa."

Still ba tace masa komai ba har ya gaji ya kashe wayarsa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tare da cire wayar daga kunnata. ta a jiye saman drowar, kwanciya tayi ta lumshe idonta kawai ta shiga tunanin abinda zai faru a tsakaninsu idan ya dawo gidan.


Koda Asp din ya kira shi cikin mutumci da dattako suka gaisa kamar koda yashe, Asp din ya tambayeshi yanayin aikin da kuma maganar dawowarshi gobe, yace." Na kammala komai cikin nasara da sahalewar ubangiji kuma insha Allah gobe iwar haka na sauka da ikon Ubangiji.

Yace." Alhamdullhi masha Allah, mutumina na taya ka murna da samun cigaba a rayuwa Allah kuma ya sauke ka lafiya."

Cikin farin ciki ya amsa da ameen ya Allah mutumin kirki nagode kwarai."

Yace." A babu komai fa abokina idan nai maka addua da fatan alkairi ai kamar kaina nayi wa sai dai kuma hanzari ba gudu ba, yanzu-yanzu na gama waya da mutuniyarka."

Jin abinda yace yasa ya d'ora idonsa kan agogon dake kafe a dakin, goma da rabi na dare, sai ya shiga mamakin dalilin da yasa ya kira ta acikin wannan daran, be yarda da abinda zuciyarsa take raya masa ba, yace." ta kawo maka 'kara ta kenan."?

Murmushi yay da fadin." Kwarai kuwa UMARU a gaskiya idan baka sauya halinka ba zamu 'bata domin ni yanzu gabadaya na daina ganin laifin yarinyar nan laifinka nake gani."

Cike da mamaki yace." Wannan ya nuna min cewar kana goyon bayan duk iskancin da take."

Yace." Ba nufi na kenan ba, na san abinda take bata kyautawa, to amma ni nafi yarda da cewa kaine kake janyo duk abunda yake faruwa me yasa ba zaka rarrasheta ba; me yasa ba zaka dinga tausasa harshenka gurin yi mata kalami ba? nasha fada maka cewa mata wasu irin hallita ne masu wuyar sha'ani amma daga ranar daka gane hallinsu to za kaji dadin zama dasu, domin suna da dadin sha'ani da kuma saukin hali, me yasa kai baka daukar shawara ne."?


Asp yana da 'kima da daraja a idonsa, wannan shine dalilin da yasa ya dinga tausar zuciyarsa kada ta tunzurashi aikata abinda zai janyo musu samun sa'bani da juna, bayan haka kuma wannan gantafalfalar yarinyar bata isa ta shiga tsakaninsa da amininsa ba, hakuri ya bawa zuciyarsa dake turari! gami da jin kishi-kishin Asp din domin haka kawai yake jin haushin kyakykyawar fahintar dake tsakaninsa da yarinyar wanda hakan ya janyo yazo yana gaya masa magana a kanta..........Ajiyar zuciya ya sauke da fadin."To Naji na dauki laifina domin a yanzu yanda kake a tunzure ko nayi maka bayani ba zaka fahinta ba, okey komai zai yi dai-dai kamar yanda kake so, zan kuma yi kokarin ganin na gyara kuskura na."


Asp din yace." Yawwa to ko kai fa mutumina, ni wallahi banga abin gudu a tattare da yarinyar nan ba, a ganina kai da kanka zaka sauya mata hallaya kada ka manta kuma bata da kowa a garin nan sai kai da family naka sai kuma mu da muke abokanan arziki."

A d'an tunzure yace." Asp maganar nan abar ta haka don Allah, nace naji na kar'bi laifi na zan gyara kuma shikkenan ko."?

Yace." Shine abinda nake bukata a tare da kai, ka dawo gida naga sauyi daga gareka."

Shuru yay masa yana jin wani irin abu na sukan zuciyarsa, a duk sanda Asp din yake nuna kulawarsa akan yarinyar yakan ji abun ya dame shi a ransa, sai yayi auziyya ya kori shaidan din dake kusa dashi tukkuna yake samun sassauci, shi kansa be san me yasa yake tsananin kishin yarinyar ba.





*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/9/22, 10:22 - Binta: _*GOJE!!ƒ™†_ƒ™¤`%’]bqýÿ*_
_*Ya dawo!! ga Akuya ga kura!! tofah! 'ka'ka-'kara-'ka'ka-tsara!! A yanzu ne labarin zai fara....! Na jima ina rubuce-rubuce amma ban ta'ba rubuta littafin daya dauki hankalina irin wannan ba, dalili littafin yazo da sabon salon da ba'a ta'ba yin irinshi ba, bahaushe yace yabon kai jahilci ƒ™Âi a wannan ga'bar dole na jinjinawa kaina gurin rubuta littafin farauta ba tare dana shirya hakan ba, Tirk'ashi idan ana dara fidda uwa ake, shin wai ina labarin uban daba ne? ina nufin (mashekin daji) wanda Ubana UMARU ya samu nasarar sare masa hannu gudaƒ™´j akwai badakala anan gaba.......GOJEƒ™¤`%’]bq
*61&62*
*GJSR*
Wayewar garin ranar da zai dawo tun safe gidan ya fara cika da mutane yan uwa da abokan arziki daga can garinsu, yaran shi ma kaf sun hallara, jiran saukar sa kawai suke, hayaniyarsu har part d'inta, ta dinga mamakin al'amarin, Baraka ce take shaida mata cewa ai ba'ki akayi a gidan, kuma da alamar su mutanan k'auye ne, jim tayi tana nazarin meye dalilin zuwansa, wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita cewa sun zo tarar d'an uwansu ne, kasancewar a cikinsu shike da kumbar susa shine dalilin da yasa suke tururubin zuwa gidanshi.

Tsaki taja a fili tace." Duk inda d'an kauye yake sai ya nuna halin dabbanci." Ta kalli Barakan dake zaune a gefanta tace." Ki sheda musu cewar hayaniyarsu tayi yawa su rage."
Ta amsa kafin ta yun'kura ta mike kai tsaye hanyar fita ta nufa.

Da yake a 'bangaran da suke zaune ba'kin suka sauka, kai tsaye can ta nufa. aikuwa ta samesu sunyi kaca-kaca da guri sunci abinci duk sun zubar sai dirkar lemon roba suke da sun shanye sai su ajiye su dauki wani, lemo da ruwan kusan kwali biyar aka a je musu amma sun shanye saura kadan.
Sosai ta cika da mamakin yanda ta gansu mazan da mata sai hira suke suna shewa kowanne rike da robar lemo a hannu.

Tayi musu sallama suka amsa tace." Dama sa'ko ne daga matar gidan wato Gimbiya Zinatu tace na sheda muku cewa hayaniyarku tayi yawa ku tak'aita."

Sai suka hada baki gurin fadin." To shikkenan amma dai mutum da bakinsa ai ba za'a ha nashi magana ba ko."?

Tace." Eh itama ba tace kuyi shuru ba cewa tayi ku rage hayaniya."

Wasu daga ciki suka amsa sauran kuwa shewa sukayi irin ta shakiyanci suka fara kuskus da yawa daga cikinsu mutanan 'Dayyiba ne wato mahaifyar Hamra'u, domin ita bata samu damar zuwa ba, sai ta tura wakilai domin dauko mata rahoto.

Tun kafin ya sauka ya samu labarin tarin jama'ar dake jiransa, sosai yay farin cikin hakan ya kuma dinga Allah-Allah ya sauka domin haduwa da 'yan uwansa wanda bashi da kamarsu.


Uwale da kanta ta jagorance su duk yawan su maza da mata suka nufi sashen Gimbiyar.


Suka cika falon duk girmansa ko wanne sai zare ido yake da kalle-kalle falon ya dumame da wani irin wari da tsami mara dadin ji!!

Marakissiya ce ta shiga ta shiga ta sheda mata cewa tana da baki.


Koda ta fito ta riske su jigum-jigum! a zaune ga tsami da hamami! ya cika mata falo, ranta yay masifar b'aci, toshe hanci tai ba tare da tace musu komai ba ta juya da sauri ta koma daki.................A gaggauce ta nufi toilet ta dinga kwara amai! wanda ta kasa tantance na meye, ta dai fi zargin warin data sha'ka ne.

A galabaice ta fito ta zauna kan Sofa tana mayar da numfashi, ita kanta ba ta ji dadin faruwar hakan ba, sai dai ba yanda za tayi ta iya zama a falon yana wannan uban warin!


Uwale kuwa kunyar duniya ce ta isheta ta kalle su suna zaune har yanzu sai dai akwai alamun 'bacin rai a tare da wasu mussaman Kawun sa wanda suke 'yan maza zir da mahaifinsa.

Ya kalleta da fadin." Uwaýÿÿÿ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~le wannan yarinyar i ta ce matar UMARU."!

Tace." Eh ita ce kuyi hakuri da abunda ya faru.

Kawu Ado ya girgiza kansa rai a bace yace." Babu shakka albasa ba tayi halin ruwa, yanda muke jin labarin mahaifinta a duniya mutum mai nagarta da dattako, bashi da nuna bambanci ko 'kyama ga al'ummah! yana da kyauta da sakin fuska, kowa nasa ne, tabbas da yarinyar nan ta gaji halin mahaifinta to da ba zata tozarta dan adam ba, amma babu komai. saboda nagartar Mahaifinta za'a zauna da ita amma dole sai UMARU ya auri za'bin mu matar da zata girmama ta kuma mutunta mu."

Gabad'aya suka amsa da fadin." 'Kwarai wannan hukuncin shine dai-dai Kawu."

Ya mi'ke tare da basu Umarnin tashi su fita, gabadaya har ita Uwalen suka fita duk jikinsu a sa'bule.

Kai tsaye sashen Uwalan suka nufa kowanne da b'acin rai a fuskarsa, ganinsu a sa'bule babu karsashi! ya sanya Hamra'u murmushi dama ai ta san za'a yi haka, da kamar ta hana Uwale jagorantarsu saboda ta san hali, to amma hakan ma babu laifi sun ga halinta a zahiri a gaba sai su kiyaye.

To Asp da kanshi ya d'auko daga airport kai tsaye Headquarter 'yan sandan suka nufa, nan ya tarar da yanda abokan aikinshi da wakilan manyan manyan 'yan siyasan da sukayi dafifi gurin taron shi, yaji dadin hakan sosai, ya saki fuska yana gaisawa da kowa, sai fatan alkairin suke masa yana amsawa da farin ciki a tare dashi, a zahiri yana ganin 'kauna tun daga kan abokan aiki da kuma jama'ar gari.

A takaice suka tattauna da Commissioner kafin ya bashi hutu na sati daya, Asp yace." Ranka shi dade ango ne fa, ya kamata a bashi hutun wata guda ya huta sosai ya kuma ci angoncin sa a tsanake." Cike da barkwanci yake maganar.

Yana 'yar dariya ya kalleshi da fadin." *GOJE* kaji abinda abokinka yake cewa."

Murmushi yayi yana kallon Asp din yace." Hutun wata daya yay min yawa sai kace mace na dingi zama a gida, ranka ya dade sati daya ya ishe ni."

Asp din yace." Okey shikkenan tunda kace haka amma nasan nan gaba da kanka zaka nemi hutun."

Dariya kawai yayi sam bai bawa maganar muhimanci ba, a ganinsa babu yanda za'ayi ya dauki hutu na wata saboda wata mace.

Cike da wasa da dariya sukayi sallama da commissioner din wanda yayi kokarin danne bacin ransa, domin ya tsani wannan kusancin dake tsakaninsu.


Tun a mota Asp din ya kira ta ya sheda mata cewa ta shirya kar'bar angonta gashin suna tare yanzu iso gidan."

Gabanta ne ya shiga fad'uwa, ta tashi zaune tana sa'ke-sa'ke, ba wai tsoron haduwa take dashi ba, kawai a jikinta takejin kamar akwai abinda zai faruwa a tsakaninta dashi.

Wanka tayi ta cancand'a ado turaruka masu dadin kamshi ta fesa a jikinta.

Sai dai tana fitowa falon tayi saurin toshe hancin ta, har yanzu akwai sauran wari da hamamin mutanan 'kauyen.


Baraka ta 'kwalawa kira da suke kicin suna aiki.......ta fito da sauri tare da risinawa, har yanzu hannunta na toshe da hancinta tace" Ki san duk dubarar da za kiyi wannan warin ya fitar min a falo." Tana gama maganarta ta koma cikin dakin.

Baraka ta dinga bunka turaran wuta sako da loko na falon tana hadawa da air freshener da turaran tsinke, amma ina warin daban kamshin turaran ma daban.

Motar tana parking yaran shi, da suke dakon! isowarsa suka mike tare da karnukansu! kafin kice kwabo gurin ya kacame! da bushe-bushe! gami da gangi mai taken sunansa!

Fitowarsa daga motar ta sanya karnukan wani irin haushi!! gabad'aya suka cika gurin kafin su zagaye shi sai koke-koke suke suna shanshana rigar jikinsa, da alama sun jima kewarsa...........

Gabad'aya jikinsa ne ya rikice! kafin kice kwabo gumi ya fara yanko masa daga kowace kusurwa ta jikinsa! ganin haka ya sanya yaran nashi cigaba da bushe-bushen suna masa kirari irin wanda suke masa.


Rigar jikinsa ya fara kokarin cirewa, Asp ya zuba masa ido yana mamakin abinda yake shirin faruwa...........Har singlet din dake ciki be bari ba duk ya cire ya mi'ka masa tare da rigar.

Ya kar'ba kawai yana kallon ikon Allah...................Ya kalli gabas! yamma! kudu! a rewa! kafin ya kurma wani irin ihu!!! wanda ya jima beyi irinshi ba, aikuwa gurin gabadaya sai da ya amsa!!! Ihun! sai da ya ziyarci cikin gidajen mutanan dake Barack din, Uwale ta zabura! ta mike tsaye da fadin.'' UMARU ya sauka domin ga alama nan.........Mazan ne suka fara turareniyar fita, su kuma matan suka cigaba da tsumayin shigowarsa.


Gabad'aya jikinsa ya bud'e Damtsan hannuwansa suka wani kumbura! jijiyoyi rad'od'o!! Sai wani irin motsi suke. tsigar jikinsa duk ta mike! gumi sai karyo masa yake daga kowace ga'ba ta jikinsa. ihun!! yake kafin ya fara yi wa kanshi kirari kamar haka.............!
*" Namiji uban maza!! UMARU! Uban UMARU! d'aga Tanimu, Kandagarki kurmar dutse mugun makaganri sai kure! Naci dubu sai ceto! nayi tawa kuma nayi ta wasu! Ni ne K'adangaran bakin tulu mai maganin wani Takadiri! guguwa! maganin barazana! Namiji a cikin maza! UMARU mai masoya gabas! yamma! kudu! a rewa!!" Yana wani irin nishi yake kirarin tare da dadura! wuka! a kowane sassah na jikinsa.*

Tun sa'ilin da ya fara ifece-ifecen! Asp din ya fito da wayarsa ya fara masa vedio sosai abun ya bashi sha'awa, ya dinga masa vedio da hotona a lokacin da yake kai kawo a gurin yana ciccije! baki tare da gurzar jikinsa da kaifaffar wu'kar! da ya fizga a jikin yaron shi Alba.

Kawu Ado ne ya k'araso gurin da 'kyar ya samu nasarar rike hannunsa, sai ya fara kwantar masa da hankali yana shafa kirjinsa dake cike da gargasa...........Ya dinga sauka a hankali a hankali amma har yanzu numfashinsa bai dai-dai ta ba.

Asp yayi serving din duk abunda ya d'auka ya mayar da wayar ajihunsa, in da suke ya nufa, a hankali yasa hannu ya kar'bi kaifaffar wukar dake hannunsa, ya mik'awa Alban tare da bashi umarnin mayar da ita gidanta.

Numfashi da huci kawai yake fesarwa gabad'aya hancinsa duk ya bude gumi shar'ban a saman karan hancin, Asp din ya fara kokarin mayar masa da rigarsa, ya daga masa hannu alamun ya bari.

Kawu Ado yace." Kyaleshi ya sarara tukkuna ai duk ranar da tsumin ya tashi mu kan rasa gane kanshi

Yace." Okey to idan hakane kuwa yana bukatar hutu bari kawai mu shiga dashi cikin gidan."

Kawu Adon yace." Hakan shine maslaha.

Duk yana jin su tsabar rashin nutsuwa ya ha nashi magana, babu abunda yake bukata a yanzu sai haya'ki walau na Shisha ko na Sigari.


Jiki a masifar sanyaye ta saki labulan ta samu gefen gado ta zauna tana jin wani fad'uwar gaba! duk badakalar da take faruwa faru a kan idonta, domin itama tana jin azababben ihun! ta zabura! ta mike tsaye da farko gigicewa tayi ta shiga neman ma'boya domin ba ta manta irin kicimilin wahalar da tasha a daji ba, jin ihun!! yana kara karfi had'e da sambatu yasa ta gazgata cewa shine ya sauka a gidan.
Gabanta na wani irin bugawa taje ta zuge window da kyar ta d'age lalube, duk da akwai tazara mai tsayi hakan be ha nata hango cibad'idi'n da yake faruwa a gurin ba.

Mamaki take sosai akan al'amarin sa, wane irin mutum ne mai taurin kai wanda wuk'a duk kaifin ta bata yanka shi, haka fa ya dinga yi a daji, ta dinga kuka domin ita a ganinta wannan kaikkafar wukar a take za tayi kisa amma ko gezau! idan yana dadurawa jikinsa har wani tsalle yake, gabadaya yanzu al'amarinsa tsoro yake bata.


Asp ne ya shiga dashi dakinsa ko'ina tsaf tsaf kamshi sai tashi yake wannan duk aikin Hamra'u ne, domin tun bayan tafiyarsa ba ta bar aikinta ba, duk bayan kwana uku take shigowa ta gyara ko'ina tasa turare.


Ya kalleshi da jajayen idanuwansa da suka rine sakamakon tashin tsumin jikinsa........"Bani Sigari." Ya fada tare da mika masa hannu.......Da yake Asp din ma ya dan busawa sa'i da lokaci shiyasa baya rabo da ita a jikinsa ko a motarsa sai ya shiga laluban jikinsa, babu ko kara d'aya, da sauri ya fita domin duba masa a cikin mota.

Kasa hakuri yay ya mike ya fara binkice dakin, *Shisha* ya dauka ya zauna kasan kafet ya fara tada hayaki, Asp ya shigo ya samu dakin ya turnuke bece masa komai ba ya zauna gefansa yana kallonsa.


Sai da ya tabbatar da cewar ya sha'ki hayakin ya ishe shi sannan ya ajiye, yana fesar da wanda yay saura a bakinsa.

Asp din ya kalleshi da fadin." Yanzu dai na tabbatar da cewar ka samu relief kamar yanda kake bukata."

Shuru yay na minti biyu kafin yace." Alhamdulillhi wanka zanyi na huta domin bana tsammamin zama da kowa a yanzu sai Allah ya kaimu gobe."

Yace." Hakan yana da kyau, yanda kayi wannan gumurzun nima zan so ka huta ka samu nutsuwa kafin wani abu ya biyo ba......Ya mike tsaye da fadin." Bari na shedawa Gimbiya cewa tazo ta had'a maka ruwan wanka ko."? Yana yar dariya ya kare maganar.

Kallonshi kawai yay yana mamakin furucinsa, shima Asp din be sake wata magana ba, ya kama hanyar fita yana amsa kiran da akayi masa a waya.

Duk da ya damu yin wankan amma sai ya kasa tashi domin yaje yayi, kawai ya zauna jiran zuwan yarinyar kamar yanda Asp din yace, amma shi a jikinshi yana ganin kamar hakan ba zai yiwu ba, kawai dai ya biyewa san zuciyarsa ne.




*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/11/22, 06:44 - Binta: *GSUR*
*63&64*



*ROMANTICƒ™²j*
Da 'kyar da jibin goshi Asp din ta shawo kanta har ta yarda da zuwa sashen angon nata.........Asp din ya cigaba da kwantar da murya yana rarrashinta tare da bata tabbacin cewa shi angon nata ne yake bukatarta a kusa dashi yana kuma da kyau taje ta kula dashi kamar yanda sauran mata suke yi.

Ta kalleshi cikin rashin walwala tace." Ai shi ya kamata yazo guri na bani zan kai kaina ba, kamar yanda ka fada idan ya damu dani to ya

Please Login or Register in order to submit comment