Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawa akwai masu gaskiya ma'ana masu kwatantawa mulki irin na Annabi Muhammad SAW da sahabansa, amma mafi akasari dai marasa tsoron Allah a ciki sunfi yawa, sannan kuma bahaushe yace." Idan anbi ta barawo to abi ta mabi sawu! ina nufin ba shuwagabbani kadai suke da laifi ba, har da jama'ar gari! rashin yiwa shugaba addua bai dace ba, kana kuma zagin shugaba da cin mutuncinsa bai kyautu ba, Umaru wata masifar da kanmu muke janyota idan Allah ya jarrabemu da masifa sai kuma mu dauki laifi mu dorawa shuwagabbani. akwai masu aikata manyan laifukan da Allah ya haramta, Zina tayi yawa a duniya uwa uba lud'u da madigo da suka zama gama gari wannan babban masifa ce zata iya janyo mana fushin ubangiji. duk abinda muke aikatawa na rashin gaskiya Allah ya na kallonmu kuma muna cin albarkacin Annabi Muhammad SAW ne da babu albarkasa da tuni Allah ya kifar damu, saboda haka kayi hakuri dole ranka ya baci kuma duk sharhin da kayi mana babu wanda ya bata mana rai, maganarka gaskiya ce, kasan da cewa muna alfahari dakai a Najeria da zamu samu jarumai irinka to babu shakka Najeria zata gyaru za'a samu sauyin rayuwa fiye da yanda muke tunani, kayi hakuri ka cigaba da bada gudumawarka mu bamu isa mu biyaka ba, amma ka ajiye a ranka cewa zakaje lahira ka tarar da aikin alkairin da kayi, Allah ya Ubangiji ya baka lafiya ya kuma kare ka a duk inda zaka shiga, muna rokon Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki d'aya."

Gabadaya suka amsa da Ameeen ya Allah."

To a takaice dai yini guda abinda ya kasance kenan.

Manya k'asa 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa masu sarauta suna sauka a garin domin dubashi. Sarki Umaru mahaifin matarsa tare da 'yan uwanshi a washe garin ranar suka sauka a garin. kai tsaye babban asibitin suka nufa domin dubashi.

Lokacin da suka isa asibitin yana bacci bayan an gamai masa aikin k'unar jikinsa Asp na kusa dashi a zaune.

Maimartaba tare da mukarrabansa suka samu guri suka zauna cikin alhini da damuwa.

Ganin Takawaran nasa a kwance magashiyan jiki duk a 'kone ya tayar masa da hankali mutu'ka! ya tausaya masa sosai kana yayi masa addua tare da fatan samun sauki da ramgwame.

Har suka shirya tafiya bai tashi ba, Sarkin yace a kyaleshi kada a tashe shi tunda sun dubashi a haka babu matsala.


Har bakin mota Asp ya rakasu yana godiya cikin girma da mutunta juna suka rabu.


Sarkin da kansa ya sanya Magaji ya kira masa Zinat a waya.

Koda suka gaisa sai ya shiga shaida mata abinda yake da akwai.

Kasa hakuri tayi hawayen da take dannewa suka subce tace." Ranka ya dade ya jikin nasa ina fatan ya tashi kun gaisa da juna."?

Yace." Alhamdullhi yaji sauki ki kwantar da hankali ki kuma kiyi masa addua domin adduarki tana da muhimmanci a tare dashi.

Tasa hannu ta share hawayen dake zuba tace." Bana iya bacci kullum addua nake masa Allah ya tashi kafadarsa nace ina san zuwa domin na dubashi Asp ya hana."


Yace." Zinatu kada ki janyowa kanki wata matsalar, kinga kema ba cikakkiyar lafiya gareki ba. ki barwa Allah al'amarin sannan kuma zuwanki bashi zai bashi lafiya ba, watakila akwai abinda yake nufi da hakan dan haka ki samu nutsuwa ki kuma tsananta da yiwa mijinki addua."

A sanyaye tace." To insha Allahu Na gode a gaishe min dasu Mommy. " Yace." Za suji da kyau." wayar ya kashe zuciyarsa cike da tausayin yarinyar.


Koda ya tashi daga baccin Asp yake sheda masa zuwa surukin nasa sai duk yaji rashin dadi.

Yace." Me yasa baka tasheni ba naso mu gaisa na nemi afuwar abubuwan da suka faru.

Yace." Shi da kansa ya hana a tasheka sosai ya dubaka ya kuma jajanta al'amarin, dattijon yayi adduo'i masu muhimmanci a garemu baki daya."


Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ranka ya dade wallahi har kunyar na hada ido nake dakai saboda irin abubuwa marasa kyau da suka faru tsakanina da kai wallahi duk abunda ya faru bana hayyacina don Allah kayi hakuri ka gafarceni."


Murmushi yayi da fadin." Umaru abubuwan da suka faru tsakanina da kai ban daukesu wata tsiya ba, domin dana k'ullace ka da ba zanzo inda kake har na kula da kai ba, ni kaina sai da na zargin hakan saboda nafi kowa sanin halinka, wasu abubuwan da aikata akwai alamun tambaya a ciki to amma Alhamdullhi tunda ka gane gaskiya kuma dawo nutsuwarka wannan shine farin cikinmu."


Yace." Na gode abokina Allah ya bar abota domin Allah, amma ina zargin wani abu dangane da al'amarin sai dai na kasa yarda da hakan."

Yace." Me kake tunani."?

Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Idan ban manta ba kwanakin da suka wuce da kaina na sheda maka cewa wata shida na tsayar domin daurin aurena da Hamra'u."


Yace." Eh kwarai kuwa hakane amma nayi mamakin yanda akayi ka sauya shawara akayi abun cikin gaggawa."


Murmushin takaici yayi kafin yace."Iyayen yarinyar basu da kirki sun jefe ni sun juyar min da hankali domin biyan bukatarsu na rasa abinda suke nufi da hakan, ko da ba suyi surkulle a kaina ba ni na amince cewar zan auri 'yarsu to wane irin rashin Imani ne zasu juyar min da tunanina su mayar dani kamar zautacce."


Yace ." Gaskiya basu kyauta ba wallahi ban san me yasa wasu mutanan suka yarda da asiri ba, to meye amfanin hakan da sukayi tunda gashi tun ba'aje ko'ina ba aikin da sukayi ya lalace."


Ya girgiza kai da fadin." Cikin mafarki da taimakon wani bawan Allah naje na lalata aikin.

Ya dinga kallonsa yana mamakin maganarsa......Murmushi yayi ya bagarar da maganar ta hanyar fadin .'' Tunda na warware sosai sai ka kira min matata mu gaisa ko hankalinta ya kwanta."


Yace." Kasan kuwa ta dameni kullum sai ta kira waya yafi sau biyar har kuka takeyi.

Tsigar jikinsa ta tashi, ido ya lumshe da fadin." Nima kukan zucci nake tsayin wata da wasu kwanakin ban sata a idona ba mun rabu babu jituwa wallahi hankalina gabadaya yana kanta.

Asp din yana laluben number yace." Kamar ita kadai ka ajiye a gidan ko ka manta su biyu ne ga Uwale ma babbar uwar gida."

Murmushi yayi bai iya cewa komai ba, hannu ya mika masa domin ya bashi wayar.


Yasa wayar a kunnanshi yayi dai-dai da maganarta......"Assalamu alaikum."

Idonsa ya lumshe wani irin yanayi na ziyartashi.

Gyaran murya yayi a nutse yace." Wa'alaikissalam Sirrina marufar asiri na."

Jin muryarsa a kunnanta ya sanya ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya a hankali tace." Alhamdullihi jin muryarka a yanzu ya tabbatar min da cewa sauki ya samu a gareka ina rokon Allah ya baka lafiya tare da sauran wa'inda suke kwance."

Ya amsa da "Ameen ya rabbi ya kike ya babyna dake tare dake."?

Hannu ta dora saman cikin da yayi wani irin girma tace.'' Babynka yana kewarka shima kullum sai yayi kukan rashinka a kusa dashi."


Yace." Ki bashi hakuri kinji ko insha Allah ina nan zuwa gare ku baki d'aya sannan ina neman afuwarki akan abubuwan da suka faru a baya.

Tayi dan murmushi da fadin." Na yafe maka nima ka yafe min."

Yace." Baki min komai ba my love ni ne mai laifi a gurinki amma naji dadi da ki kayi min afuwa zan dawo mu cigaba da rayuwa mai kyau."

Tace." Allah ya yafe mana baki daya.

Ya amsa da Ameen kafin yace." Ina Uwale ki bata wayar mu gaisa."

Tace." Gata a kusa dani tare da Hamra'u."

Shuru yayi bece komai ba .

Ta mikawa Uwale wayar suka gaisa sosai tana jajanta masa.

Yace." Uwale ku kwantar da hankalinku na samu lafiya insha Allan zan dawo da kafafuna.

Tace." To Alhamdulillhi Allah ne abin godiya mutanan *Kafur!* ma duk sun ce ayi maka sannu da jiki sai ka dawo gida zasu zo dubaka."


Yace." Na gode sosai Allah ya saka da alkairi."

Wayar ta mikawa Zinat din fuskarta yawalce da fara'a da jin dadin samuwar lafiyar jikinta nata.


Ta mikawa Hamra'u wayar dake zaune tayi jugum!

A sanyaye tace." Yaya na sannu ya jikin."?

Babu yabo babu fallasa ya amsa, iyayen yarinyar sun janyo mata tsana a gurinsa.


Daga haka babu wata kalma mai dadi kawai ya kashe wayarsa.

Idonta ya ciko da ruwan hawaye! tana so itama ya dinga gwada mata soyayya koda bata kai irin wacce yake gwadawa Zinat din ba.


A sanyaye ta mika mata wayar jikinta babu kwari ta tashi ta shige daki ta kwanta abin duniya ya isheta.

Zinat da Uwale kuwa yinin walwala da farin ciki sukayi sakamakon amsa adduarsu da Ubangiji yayi babu shakka Allah maji rokon bawansa ne.


To bahaushe yace ." Rana dubu ta 'barawo rana guda ta me kaya.

*UBAN DABA!* ya samu nasarar shiga asibitin cikin shigar Dr Shu'aib likitan dake tsaye a kan Umar din!

Yayi basaja sosai da yake Dr Shu'aib din gajere ne mai 'kiba shiyasa babu wanda yayi tunanin cewa bashi bane, abinka da dare duk da akwai fitilu a asibitin hakan bai sa an ganeshi ba,kai tsaye ya nufi d'akin da Umar din yake kwance!


A hankali ya mayar da kofar ya rufe.....Asp dake kwance a can saman kujera ya bude idonsa sakamon jin motsin a dakin
Dama can bashi da nauyin bacci.

Ganinshi yasa ya koma ya kwanta dan beyi tunanin cewa wani ne daban ba. baccin ya sake fizgarsa.

Da har ya tsorata amma ganin ya koma ya kwanta yasa ya sauke ajiyar zuciya.

Kai tsaye gadon da yake kwance ya nufa.


Isarsa ke da wuya ya b'ude idonsa!!

'Kwayar idonsa kawai ya kalla ya sheda waye a gabansa.


A zabure! yayi nufin tashi.......shi kuma da gaggawa ya rike masa wuya da kyau!!

Wata shegiyar igiya mai wasu k'ananun kososhi masu tsini! ya ciro daga can kasan aljihun wandon dake jikinsa.

Kokarin d'aure masa wuya yake da igiyar abun ya gagara! domin dambe! suke sosai! duk da ya sha'ke masa wuya! amma bai samu nasara a kansa ba.

Naushi! ya kaiwa hancinsa a take ya fashe ya fara zubar da jini. ya sake kawai fuskarka wawan naushi! yayi tagaga! zai fadi! amma saboda taurin zuciya bai sakar masa wuya ba.


Gurnani! ya dinga yi yana buge-buge! da kyar yake janyo numfashi! ya galabaita sosai! saboda dama can jikin babu 'kwari!


Kamar a mafarki ya dinga jin wani irin abu.

Ya bude ido da saurin gaske.

Abinda ya gani ya tayar masa da hankali shin mai yake faruwa a tsakaninsu.


Da sauri ya nufi gurin da fadin." Dr me yake faruwa ne."n

Juyowar da zai yi suka had'a ido! nan ya sheda ko waye! jikinsa ya shiga tsuma! ya zabura! zai fita. kawai ya d'aga igiyar dake hannunsa ya kai masa duka da ita a fuska! aikam duk ta yanke masa fuskarsa har kan idonsa ya rufe! idon jini ya 'bata fuska........Da kyau! yayi ihu!! da fadin." Babu lafiya a daki mai lamba 21."

Kafin kice me hankalin kowa ya tashi duk likitocin dake aikin kwana suka fito tare da masu gadi.

Kai tsaye d'akin suka nufa.....Lokacin ana buga damben Maza! tsakanin mutum biyu. Asp na kasa a kwance yana matagugu! rai a hannun Allah.

Sosai suke dambe!! irin na k'wanji da 'kwanji *UBAN DABA!* hannu guda gareshi amma ya san makwantan mugunta!


Shi kuma da yake da rauni a jikinsa hakan bai sanya yayi rauni ba, ganin Asp a kwance! ya tayar masa da hankali babu shakka yau sai yaga karshen mutumin nan mutu'kar yayi sanadin abokinsa.


Ganin abinda yake faruwa ya tayar musu da hankali.

Duk yawansu aka rasa wanda ya iya zuwa gurin domin bada taimakonsa.

Su kansu sucurity din abun yafi 'karfinsu!


Gabadaya ya manta da wanda yake gogayya! shine fa mutumin nan da wu'ka! bata aiki a kansa! amma ya dage yana wahalar da kansa sai kai masa sara da kaifaffar wukar dake hannunsa burinsa kawai ya illatashi.

Ganin haka yasa yayi kwankwance ya murd'e! masa hannu ya kwace wu'kar!

Bai kuma jirayi komai ba ya soka masa ita wuyansa!!

A take ya fadi a gurin yana wani irin gurnani! jini ya dinga tsartuwa!

Zubewa a kusa dashi da wu'kar a hannunsa da karfi yace *." Ashahadu Allah ila ha'illalahu -wa ashshahadu Anna Muhammadur-rasulullah.* fad'ar hakan keda wuya ya mi'ke cikin zafin nama yaje ya fizgo k'aramar bindigar dake jikin rigar Asp dake rataye bai jira komai ba ya sai ta a wuyansa.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/28/22, 21:25 - Binta: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





*123*
Asp ya hangi abinda yake shirin faruwa! cikin 'karaji! yace." Umaru kada ka harbi kan domin hakan ba hujjah bane."

'Dakin yayi tsit! tsananin tashin hankali ya hana su aikata komai!

Asp yaja jiki da rarrafe ya iske gurin da yake tsaye har yanzu bindigar na wuyansa.

Ya rike kafafunsa jikinsa na wani irin karkawa yace." Na fada maka kada ka harbi kanka Umaru zaka mutu kafuri domin abunda ka aikata a yanzu ba haram bane jahadi kayi kuma kayi dai-dai domin karshensa kenan a kashe shi kamar yanda ka kasheshi saboda haka ka cire bindigar nan daga wuyanka."

Dr Salihu dake tsaye jiki a sanyaye yace." Wannan magana haka take ranka ya dade kada ka aikata aikin daka sani kayi hakuri mu jin dadin abinda kayi a yanzu kuma muna alfahari da hakan."

Gabad'aya hayaniyarsu ta cika dakin kowa yana fadin albarkacin bakinsa.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya juya yana kallon gawar a kwance tayi muni! fuskar ta kara 'baki babu alamun rahama a tare da gawar!

Dr Salihu ya iso gurin a hankali ya cire bindigar daga hannunsa, ajiyar zuciya ya sauke da sauri ya matsa daga gurin, fita yayi yaje adana bindigar ya dawo dakin.

Lokocin likitocin sun rufu kan Asp suna bashi taimakon gaggawa!

Umar din ya tsugune gaban Gawar! yana dubata.

Dr Salihu ya tsuguna da kayan aiki a tare dashi.

Binkicen gawar yayi sosai nan ya tabbatar da cewa ya mutu mintina ashirin da suka wuce.

Ya kalleshi da fadin." Abin mamaki da al'ajabi ko ya akayi wannan takadirin ya samu nasarar shigowa asibitin nan."?

Murmushin takaici yayi kafin yace." Idan nace Najeria babu tsaro sai a musanta! handama! babakere! cin hanci! zamba! cikin aminci cin amanar 'kasa! zalinci! duk ya tattara a wannan 'kasa shuwagabbani kuma suna kallo. Dr Salihu ko shakka ba nayi wannan d'an ta'addan dake gabanmu yana da d,caurin gindin shuwagabbani."


Dr ya sauke zazzafar ajiyar zuciya da fadin." Yau dai karya ta kare wai bori ya kar boka gashinan a kwance ka alkadarinsa wannan babbar nasara ce a gareka amma a ina zamu samu cikakken bayani.

Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Akwai sanya hannun Dr Shu'aib ina zarginsa."

Dr Salihu ya jima yana kallonsa kafin a sanyaye yace." Amma ban ta'ba tunanin cewa Dr Sha'aib zai ci amanar aikinsa ba tsayin shekaru goma yana aiki ba'a ta'ba kamashi da wani laifi mai muni ba sai a wannan lokacin yana da kyau dai ayi binkice sosai.


Yaja dogon tsaki da fadin." Idan babu sanya hannunsa babu yanda za'ayi wannan dan iskan ya san in da nake, bari na sheda maka cewa kai tsaye da nufin kisa ya shigo dakin sai kuma yayi rashin sa'a! ni na kasheshi babban burina kenan naga gawarsa a kwance a gabana."
Cikin karsashi da kwarin gwiwa yayi maganar!

Dr Salihu dai gabadaya jikinsa yayi la'asar tausayin Abokinsa ya cika masa zuciya, wannan shi ake kira da mugun ji! ko mugun gani! ba shakka azal! ce ta ritsa da abokinsa amma kaf tarihin rayuwarsa bashi da wani tabo Dr Shu'aib mutumin kirki ne kowa ya sheda hakan.


Washe garin ranar da al'amarin ya faru gari ya d'auka Asibitin ya cika da mutune da kuma 'yan jarida babban burinsu a bar su su shiga domin su dauki hoton gawar sannan kuma su samu zantawa da Jarumin da ya kawo karshen d'an fashin daya Addabi kasa.

Labari har fadar shugaban k'asa cewa a daran jiya *GOJE! ya samu nasarar kashe UBAN DABA!* wanda ya addabi 'kasa da ta'addanci sai dai kafin ya samu nasara a kansa sai da sukayi dauki ba dad'i! anan ya samu nasarar galabaitar da kakakin rundunar 'yan sanda Jahar katsina wato Asp Musa Baharu yanzu haka dai yana kwance ana bashi taimakon gaggawa."


Mai girma shugaban kasa yayi farin cikin faruwan hakan, ba kuma tare da bata lokaci ba ya tura wakilansa domin zuwa su tabbatar da al'amarin kana kuma suyi jinjina tare da mik'a gaisuwa da godiya da yawunsa.


Comissinoner ya kasa zaune ya kasa tsaye! jikinsa sai rawa yake bakinsa ya bushe tsabar fargaba da tashin hankali sun ha nashi sakat! sa'i da lokaci gabansa sai ya yanke ya fad'i! watakila ya tattara kayansa ya gudu shine kawai kwanciyar hankalinsa.


Umaru shi da kansa ya bada Umarnin d'aure Dr Sha'aib a cewarsa a gurinsa za'a samu duk wasu bayanan da ake bukata.


Da farko dai gardama ya fara, sai suka cire imani da tausayi suka fara laftarsa! babban mutum da girma da iyali sukayi masa tik! suna masa tujara! duka ko ta inaa!.......Yana kuka da hawaye da majina ya daga hannuwasa da fadin" Ku saurara zanyi bayani."
Suka saurara da dukan da suke masa. wasu zafafan hawaye masu zafi suka fara tsare a saman fuskarsa.


A daddaure! aka shiga dashi dakin.

Sun kai su ashirin a tsaye a kansa!

Asp dake kwance a hankali ya tashi yana kallonsa sosai yake mamakinsa! fuskar salihai gareshi ba za kayi tsammanin zai aikata wani mugun aiki ba.


Umaru kuwa yana tsaye ya goya hannuwansa a baya. shima mamakin Dr Shu'aib din yake, wai dashi aka hada baki domin ganin bayansa.


'Yan jarida biyu maza da mace daya suka shigo dakin da kayan aiki a tare dasu.


Ganin shigowarsu yasa kai tsaye ya nufi gurin da Dr Shu'aib din yake gurfane! gumi yayi masa dabaibaiyi.
*(Allah mugun ji da mugun gani Allah ka karemu)*


Ya tsuguna gabansa a nutse ya kira sunanshi.

Cikin tararrabi da damuwa ya kalleshi bakinsa ya bushe tsabar wahala!

Zuciyar musulci gabadaya sai tausayinsa ya rufeshi, amma bai nuna a zahiri ba, ya sha kunu da fadin." Dr kayi mana cikakken bayani gamu gabad:aya ga kuma manema labarai shin ya akayi *Uban daba!* ya samu damar shigowa asibitin nan da mummunan kudiri, ya shigo dakin da nake kwance jikinsa sanye da kayan aikinka yanayin hallita ya sanya da yawa mutane basu sheda waye ba saboda basaja! shin ya akayi hakan ya faru."?


Ya jima kansa ya sunkuye yana dawurwura! kafin da kyar yace." Umaru kaddara ce ba halina bane wallahi azal ce ta afka min."


Yace." Duk na yarda da maganarka amma kasan cewa idan da kaddara tabbas akwai son zuciya a ciki akwai sanya hannun shugabbani a tunani sunyi maka alkawarin makudan kudi shin ko ba haka bane."?


Maganar a kan hanya take, wannan ne dalilin da ya sanya ya kasa furta kalma guda. tabbas hakane.


Yace." Shurun ka na nufin maganata a kan hanya take."

Ya kalleshi idonshi jawur! ya tara 'kwallah! yace." Umaru babu ruwan shuwagabbani a cikin wannan al'amarin. abunda na sani shine mai girma Commissioner naku shi yayi tattaki ya sameni har cikin gidana da mummunan kudirinsa.

Cin amana ba halina bane. ba a shedar kai amma tunda nake ban ta'ba yunkurin cin amanar aikina ba sai a wannan lokacin. nayi mamaki mutuka lokaci guda na amince da manufarsa. a take yayi min alkawarin miliyan goma bayanshi wani babban dan kasuwa Alhaji Mutari mai zinare yayi min alkawarin miliyan ashirin mutukar na amince da manufarsu.

Nan na tambayesu dalilin da yasa suke bukatar ganin bayanka.

Dukkaninsu suka tabbatar min da manufarsu....Commissioner yana adawa da yanda Allah yayi maka d'aukaka! yayi maka baiwa! ya daga darajarka! duniya ta sanka manyan mutane suke alfahari da kai! a cewarsa yana ji a jikinsa watarana zaka iya gadar kujerarsa ko kuma ka iya mulkar kasar baki daya. to wannan dalilin yasa yake jin haushinka yake bukatar ganin bayanka a doron duniya.

Alhaji Muktari mai zinare ya tabbatar min da cewa. kai ne kayi sanadiyar tattalin arzikinsa, wannan dalilin yasa ya sanya ido akanka har ya samu nasarar samun labarin asibitin da kake kwance.
A take suka had'u shi da Commissioner suka sauya min ra'ayi! suka rinjaye ni na amincewa bukatarsu.
Wannan shine abunda ya faru." Cikin rauni da rashin confidence ya 'karasa maganar.

Asp ya kalleshi da fadin." Dr Shu'aib kaci amanar aikinka! bayan haka kuma kaci amanar k'asa! kwanakin da suka wuce na dauka tare da kai muke jajanta yanda al'amura suke faruwa. rashin tsaro ha'inci da cin hanci! ashe ta ciki na ciki zuciyarka babu alkairi! akan miliyan talatin ka yarda kaci amanar Allah har ka bada goyon baya kashe rai! shin ka dauka kai cewa zaka zauna a duniya ba zaka mutu ba? haba Malam yanzu kana maganar kaddara! akwai ta amma kuma son zuciya yafi yawa a ciki saboda haka dole ka fuskanci hukunci daga hukuma!

A raunane! yace." Asp na amince da kowane irin hukuncin da za'a yanke a kaina! kamar yanda na sheda muku da farko wallahi ba halina bane tsautsayi da kadd.........Umaru ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa. "Ya isa haka."! shuru yayi yana kallonsa.
Ya kalli jami'an tsaron dake tsaye a kansa umarni ya basu cewa a fita dashi.
Suka mikar dashi tsaye. damar da 'yan jaridar suka samu kenan suka dinga daukar hotonsa suna masa vedio sai sunkuyar da kansa yake abin duniya ya dameshi! basu fasa d'aukar hotonsa ba har sai dai aka shige dashi mota tukkuna.

Kaf ya tattara bayanai da hujjoji da suka cancanta! da kansa ya kira kakakin rundunar 'yan sandan jahar! domin su sake tattaunawa, dama kuma shine ya bashi wu'ka da nama domin yin binkice akan al'amarin. bai jirayi komai ba ya had'a komai kai tsaye kotu aka shiga dashi.

Mummunan labarin da ya faru a garin Katsina shine Commissioner yayi mummunan accident a hanyarsa ta tserewa! yanzu haka dai yana kwance a asibiti rai a hannun Allah. amma kuma cikin ikon Allah an samu nasarar kama Alhaji Mutari mai zinare yana hannu ana gudanar da binkice a kansa.

*Allah kayi mana tsari kasa mufi karfin zuciyarmu!*


To sai da 'kura ta lafa tukkuna! iyalinsu suka samu damar zuwa dubasu.

Lokacin Asp ya warware sai abinda ba za'a rasa ba, amma fuskarsa duk ta fitar da tabo in da Allah ya taimaka ma idonsa bai nakasa ba!


Kowa ya ke'be da iyalinsa domin jajantawa juna. babban farin cikinsu ganin mazajen nasu sun samu sauki tare da samun nasara akan aikinsu. hakan ya faranta musu rai mutuka.


Ita da Hamra'u suka zauna a gefe da gefensa ma'ana suka sanya shi a tsakiyarsu.
Ita kam Uwale tana gefe zaune kan wata kujera.

Hankalinsa kaf yana kanta tausayinta duk ya dameshi gabadaya kammaninta sun sauya sakamakon tsufan da cikin jikinta yayi.

Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi. a tausashe! yace." Kiyi hakuri kinji ko."

Murmushi tayi kafin tace." Me akayi."?

Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya da fadin." A halin da kike ciki a yanzu ya kamata ace ina kusa dake amma hakan bai samu ba, sai rashin kwanciyar hankalin da ya faru! amma insha Allah komai zai wuce da ikon Allah."

Murmushin dai tayi don

Please Login or Register in order to submit comment