Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa ka tsaya a kaina kana kalubalanta ai na dauka sai mutum yay laifi za'a tuhumeshi."?


Yaga kamar ta raina masa hankali da jan ido yace." Zaki 'karyata maganarsu ne? wanda ya tabbatar min da abinda ki ka 'aikata ba zai miki 'kaharu ba idan yayi miki k'arya yayi wa? ki kiyaye nifa."? jikinsa na tsuma! ya ke maganar.

Man shafawa ta dan lakato tana mutsikawa a hannuwanta kafin tace." Sai kaje ka tambayi shi wanda ya fada maka cewa naci mutuncinsu idan sharri nai musu, mai zai sanya su shigo in da nake suna wari! da tsamin hammata."!!

Hankalinta kwance take maganar domin bata tsammanin cewa hukuncin mai tsauri zai bi ta kanta ba.........Wani bahagon mari yayi mata da bayan hannunsa, wanda ya sanya ji da ganinta daukewa na wucin gadi.


Kai ta sunkuyar kasa tana mamakin al'amarin! ita ya Mara akan wasu gigidadawa!! wani katon bakin ciki yazo ya tsaya mata a wuya.

Yana tsaya a kanta yana surfa mata bala'i tare da jajjada mata muhimmacin mutanan da take rainawa har tana fadin duk maganar da ta ga dama a kansu.

Ta danne kukan da yake kokarin kufce mata tace." Ko zaka ce 'karya nake sai na fadi gaskiya domin kai kanka wari kake ballanatana su, na fad'a din."


Hannu yasa ya gwa'be bakin! zafi ya hanata karasa maganar dake bakinta............Ido ta zuba masa ganin yanda fatar goshinsa duk ta tattare sai wani irin gumi yake kamar ba sanyi safiya ba.

Yanda yake rawar jiki yana kai kawo a kanta yasa ta tsorata, babu yanda ta iya haka ta shirya jikinta, ya nuna mata hanyar fita da hannunsa, ba tace komai ba tayi gaba zuciyarta na wani irin zafi! tsaki mai tsayi yaja kafin yabi bayanta.


ZINATU ba tayi musu 'karya ba da gaske take tsami da wari suke shima ya san haka ya kuma ji warin a hancinsa amma saboda rashin gaskiya ya take.

Rashin gurin zama yasa taja ta tsaya a bakin kofa, ta daure zuciyarta da fadin." Ina kwananku."?

Wasu daga ciki sun amsa wasu kuma sukayi mata kallon uku saura kwata *Yo a fad'awa mutumin k'auye iyashegeƒ™Äi*


Bata damu da hakan domin ba sune a gabanta ba burinta taje ta amayar da aman da yake taso mata.

Jinsa kawai take yana mata bayaninsu da nuna mata muhimmanci su a tare dashi, yawu ya cika mata baki, duk ta rasa yanda za tayi, itama a karan kanta bata san abinda take sai dai don ba yanda za tayi ne.


Duk irin dauke kan da take yana lure da ita, ransa idan yay dubu ya baci! ya daure ya cigaba da cewa.


" Kada kiyi tunanin don kin fito daga gidan sarauta kinfi wasu kima da daraja! to ina so ki san cewa babu wanda yafi wani a wannan duniyar face wanda yafi bautawa Allah, duk daya muke a gurinsa, kuma shi yayi na burni yayi na kauye, kana kuma shi yayi mai kudi yayi talaka, yayi sarki yayi bafade, mulki talauci arziki duk shi yake bayarwa ga wanda yaso, saboda haka ni 'yan uwana sun fi min komai a duniyar nan don haka ba zan lamunci kici zarafinsu ba, ina so ki rike wannan, ki zauna a matsayinki na matata, suma su zauna a matsayinsu na jinina wannan shine abinda nake so ki rike kuma kiyi aiki dashi."


Uffan bata iya cewa ba to yaushe ma ta samu sararin maganar bakinta cike da yawu.

Tana kallonsu suka tashi daya bayan daya suka dinga fita, falon ya rage su biyu, harararsa tayi kafin ta bude daki ta shige kai tsaye toilet ta nufa ta zubar da yawun bakinta, tsugunawa tayi zuciyarta na cigaba da hantsilawa......Dole dai sai da tayi aman sannan ta samu sassauci.


Tana fitowa ta samu Baraka tana gyara dakin

Kan Sofa ta kwanta tana mayar da numfashi tace." Baraka don Allah kiyi kokari a falon nan wannan wari duk ya fice kinji ko."

Tace." To ranki ya dade insha Allah bari na gama gyara miki dakin."

Kai ta girgiza kafin ta rufe idonta tana kukan zucci! wai dangin mijin da take aure sune kucakai masu warin daud'a daddawa da tsamin hammata! wannan al'amari yana daure mata kai, a mafarki ba ta'ba tsammanin cewa za ta auri d'an 'kauye ba.


Hamra'u a ranar da al'amarin ya faru kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki taji dadin yanda ya nuna mata muhimmancinsu bayan haka kuma tayi farin ciki sosai da maganarsu ta karshe da Kawu Ado, domin kafin su tafi sai da ya jaddada mata cewa ta kwantar da hankalinta UMARU zai aureta da ikon Ubangiji, wannan shine abinda sanya farin cikinta kara nununkuwa.


Sosai ta dauki fushi dashi saboda abunda yay mata yayi masifar 'bata mata rai, da farko tayi tunanin zama dashi saboda salon soyayyarsa amma yanda yake kambaba darajar 'yan uwansa yasa duk taji ya fice daga zuciyarta, tunaninta ya za'ayi ta samu namiji wanda yay daidai da rayuwata wanda kuma ya iya love irin nashi.


'Bangaranshi bai damu da shan k'amshin da take masa ba, domun shi a ganinshi bai ga abun 'bacin rai da daukar gaba ba, kuskure tayi wanda ya cancanta da ayi mata gyara akai shiyasa ya tsaya kai da fata ya nuna mata kuskuranta saboda a cikin zuciyarsa ya kudirci zaman lafiya da ita, saboda baya so famliy nasa su tsaneta saboda mugun halinta, shi zai iya jure duk abunda za tayi masa amma ba zai yarda taci zarafin wani nasa ba.


Haka suka cigaba da zama tsayin kwanaki uku wata mu'amular arziki bata sake hadasu ba kowa yana gurinshi, sai dai shi da safe yana shiga ya dubata, ta shuka masa tsiya idan bata so ba, wani sa'in kuma a lalace zata amsa masa magana, kyaleta kawai yake ya nufi gurin Uwale a can yake zama yaci abinci suyi hira, wanda hakan yay bala'in farantawa Hamra'u rai, cikin zuciyarta ta dinga jin dadin yanda masoyin nata yake mu'amula da ita, a cikin kwanaki wata irin shakuwa sukayi, gabadaya ta siye zuciyarsa da kyawawan halayenta wanda suke mutukar burgeshi, a cikin ransa yake jin ina ma ace Gimbiyarsa ce take da wannan kyawawan halayen.


Asp ya kira shi a waya da muryar bacin rai yace." Umaru me yake faruwa ne? yanzu mu kayi waya da mutuniyar a maimakon ta sheda min abunda ya had'a ku kawai sai ta fashe da kuka."


Ranshi ya d'an 'baci, a zuciyarsa baya son yawan kiran da Asp din yake mata, ya danne 'bacin ransa da fadin." Ita ce ta kira ka ko kaina ka kira ta."?

Yace." Itace ta kira ni, da kyar muka gaisa kafin ta fashe min da kuka."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Asp kuskure tayi na gyara mata shine take fushi dani tsayin kwana uku bata saurarata to akan me zan damu kaina a kanta."


Yace." Idan ba damuwa ina so na san kuskuran ko akwai shawarar da zan iya bayarwa."



*Ina jin dadin comments dinkuƒ™°0ƒ™°0*

*Sai dai ayi hakuri a kar'bi labarin a yanda yake, kada kuce lallai sai anyi muku yanda kuke so, labarin yana dauke da darrusa daban-daban, ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun isar da sakon dana d'aukoƒ™Éi*



*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/17/22, 14:16 - Binta: *71&72*
Ajiyar zuciya ya d'an sauke kafin yace." Laifi tayi min wanda ya cancanta da ko wane irin hukunci, to amma tunda ka bukaci sanin abinda ta aikata ba zan boye maka ba domin kai ma ka taya ni nuna mata kuskuranta."
Cikin nutsuwa duk ya sheda masa abinda ta aikata bayan zuwan 'yan uwansa gidan.

Girgiza kai kawai yake yana sauraranshi har ya gama yi masa bayani ya sauke ajiyar zuciya yana jimanta al'amarin, ko da yake ba abun mamaki bane yarinyar zata iya aikata abinda yafi haka amma shi bai ji dadin yanda abokin nasa ya fifita 'yan uwansa akanta ba, ita ta sheda masa cewa ya tozartata ya wulakantata a gabansu harda duka da mari wannan dalilin ne yasa hankalinsa ya tashi mutuka! bayan mijinta to shine mutum na biyu wanda aka bawa amanar ta, dole idan wani abu makamancin wannan ya faru yayi kokarin ganin an samu maslaha.

Ya dan ja numfashi kafin." Yace." Gaskiya abinda ta aikata bata kyauta ba, domin ita gaskiya duk inda take dole a fada, abokina iyaye sun wuce wasa! dalili kenan da yasa kowane d'a nagari yake kokarin kare mutuncinsu, babu yanda za'ayi kana kallo wani ya ci zarafin iyayenka ka 'kyaleshi, ban ga laifinka ba, amma kuma kamar hukuncin da dauka bai kyautu ba Umaru kada ka manta cewa yarinyar nan amana ce a hannunmu bata da kowa a garin nan face kai da kuma 'yan uwanka, sai kuma ni da iyalina, Umaru duka babu shi a cikin sharadin aure don Allah ka kiyaye ka daina saurin hannu, domin hukuncin duka baya shirya mutum nasiha gami da nunawa mutum kuskuransa shine ke sanya mutum ya shiryu ya kuma gane hanya mai kyau."


Murmushin takaici yayi kafin yay kokarin danne b'acin ran dake taso masa yace." Duk naji bayaninka Asp amma me yasa da farko ka nuna kamar ba kasan abinda yake faruwa ba."?

Yace." Saboda kawai ina so naji bayani daga bakinka, tabbas abinda ta sheda min gaskiya ne tunda gashi baka 'karya ta ba, ka doke ta a gaban 'yan uwanka wannan ba dai-dai bane."


Asp yana da 'kima da mutunci a idonsa, dalili kenan da ya sanya ya kasa d'aukar mataki akansa, amma da babu wannan darajar da tuni sunyi uwaka! ubanka! domin ganin kamar rainin hankalin yayi yawa.

Yace." Asp ban doki yarinyar nan ba, ban kuma tozarta a gaban 'yan uwana ba, duk maganganun da ta fada maka akaina ta fadi ne domin ta kare kanta, kuma babu yanda za'ayi ta sheda maka laifinta, ni ne dai mugu! kullum kalmar da take kira na dashi kenan, to bani da damuwa da hakan, amma ina so ka san wani abu, kamar yanda yanzu ka gama magana cewa yarinyar amana ce a hannun mu to babu shakka ba zan zauna na zuba ido ina kallonta tana aikata kuskure na kyaleta ba, dole na nuna mata kuskuran abinda ta aikata kuma ba zan yarda da sakarci da rashin kunya ba."

Cikin tsare gira yake maganar har ya gama Asp din na auna maganganunsa kafin yace." Gaskiya ne abokina amma kamar yanda na sheda maka cewa babu duka a sharadin aure to don Allah ka kiy...........Cikin fusata! ya katse shi ta hanyar fadin." Wai shin waye ya fad'a maka dukanta nayi ne? Asp ashe har yanzu ba kasan sharrin mace ba, ni Umaru na san abinda nake kuma ina da ilimin addini dai-dai gwargwado ban doke ta ba kamar yanda kake tsammani face na musulunci, amma kada ka sake yi min maganar duka domin na san abinda ya cancanta."


Asp din yay murmushi ganin yanda abokin nasa ya fusata! sai numfarfashi yake masa a kunne! yace." Allah ya huci zuciyar *MAI DAWA."!* Ayi hakuri na fahimci maganarka naga ranka ya 'baci da wannan al'amari amma bari na bari ka sauka tukkuna sai mu karasa maganar."


Yana fesar da wani irin huci! na tsantsar bacin rai da damuwa yace." Ranka ya dade wannan yarinyar bata isa ta shiga tsakanin abotarmu ba domin naga abinda yake shirin faruwa kenan to ba zan yarda da hakan ba tun kafin tafiya tayi nisa zan dauki mataki."


Yace." A'a wannan gugar zana kawai kake min kace dai kawai na daina magana a cikin al'amarinka kuma zan kiyaye hakan da ikon Allah." Kashe wayarsa yayi ba tare da ya saurari da amsarsa ba.

Wani 'baci rai mai tsanani ya sake rufeshi, wai yau shi Asp ya kashewa waya ta dalilin abinda bai taka kara ya karya ba, tunda suka hadu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba, sai ta dalilin yarinyar, dama sai da ya tsammaci faruwar hakan, ya rasa mai yasa Asp din baya ganin laifinta, duk abunda zata aikata dai-dai ne a gurinsa, kullum shine mai laifi, ya kasa fahimtar abinda yake kudundune a cikin zuciyarsaýÿÿÿ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ abokin nasa, yana zargin kamar sonta yake to idan ba haka ba mai zai sanya ya damu da damuwarta haka?

Ya jima da wannan tunanin a cikin ransa kawai yana kokarin kawar dashi ne saboda baya so zuciyarsa ta gazgata zargin da yake can cikin ransa.


Kai tsaye sashensa ya nufa yaje ya samu hayakin Shisha ya banka, ya samu relief a zuciyarsa kafin yayi wanka ya fito har yanzu zuciyarsa babu dadi, saboda yanayin garin ana zafi yasa ya shirya cikin 3qutar da t-shirt mai gajeran hannu, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa, yanayin yanda yake taka 'kasa da karfi shi kadai ya isa ya sheda maka cewa shi din jarumi ne a gida da waje.

Koda ya shiga sashen nata hadimta ya samu suna kai kawo Baraka na gyare-gyare yayin da Marakisiyya ke kokarin shiga kicin.


Sallama yayi suka amsa kafin su tsuguna har kasa su gaishe shi, amsawa yayi bayan ya sassauta fuskarsa, sai da wuce tukkuna kowacce ta tashi domin cigaba da aikinta.

Tana zaune a bakin gado da kayan bacci a jikinta, da alamu ba ta jima da tashi a bacci ba tun ba bayan sallar asubah da ta gabatar.

Kallo d'aya tai masa gabanta ya fad'i! tai saurin dauketa kanta tana auziyya a cikin zuciyarta........Kayan dake sanye a jikinsa sunyi masa bala'in kyau! kwana biyu gani take yana wani irin kyau! shiyasa ba ta fiye kallonshi ba saboda kada tayi abun kunya.


Shima nasa 'bangaran namijin kokari yayi gurin danne zulamarsa domin duk sanda zai tozali da wani bangare na jikinta muguwar sha'awa kan taso masa yanzu ma abunda yake shirin faruwa kenan, ya shiga dakin da karsashi da power! amma ganin ta a haka yana nema yasa ya rasa kuzarinsa.

Ya iske inda take kawai yaja tunga ya tsaya a gabanta.

K'amshin turaran dake jikinsa ya dinga fizgarta haka kawai taji kamshin ya kwanta mata a rai.

Sun jima a haka babu wanda yayi magana, ita hankalinta yana kan wayarta tana tunane-tunane shi kuma ya zuba mata na mujiya yana mata wani irin kallon kurrula.

Gabad'aya gabu'bin jikinta suka saki idanuwansa na da wani irin dafi, ko shima ya san da haka wannan shine ba ta sani ba.

Shawarwari take da zuciyarta shin ta gaisheshi ko kuma ta tashi ta bashi guri.

Tana so ta dauki nasihohin da Asp yake mata a koda yaushe amma tana wani tunani gani take kamar idan ta rusina masa ajin ta zai zube wannan shine abinda take gudu.

Da k'yar ta iya bud'e baki tace." Ina kwana."?

Bai tsammaci haka daga gare ta ba, dalilin da ya jefa shi mamaki kenan, a cikin kaso d'ari na damuwarsa kashi hamsin ya zube dalilin wannan gaisuwar.


Bai amsa ba amma ya sassauta fuskarsa still idonsa na kanta kafin yace." Yanzu ki ka tashi kenan."?

Shuru kawai tai masa domin a ganinta wannan ba hurumin sa bane.

Ya duba agogon dake daure a hannunsa, 10:30 na safe ya kalleta da fadin." Goma da rabi a halin yanzu ina fatan kinyi sallah."

Ba tace masa uffan ba, ta mike tsaye, ya bita da wani mayataccen kallo kayan baccin sunyi mata masifar kyau, lebansa ya dan ciza ya fesar da wani numfashi kafin yayi saurin tare mata hanya don ganin tana kokarin barin gurin.

Karo na farko kenan da ta kalleshi.

Yanayin kallon da yake mata da yanda k'wayoyin idanuwansa suka rusuna yasa jikinta mutuwa, ta dinga jin wata irin kasala na kokarin rufeta.

Hanya take kokarin sanjawa ya sake tare ta, gabadaya ya zuba hannuwansa cikin aljihun 3qutar din dake jikinsa.



Cikin bacin rai tace." Wai meye haka ka bani hanya na wuce."

Ya girgiza kanshi ido a lumshe yace." Ba zan baki hanya ba sai kin bani amsar tambayata."


Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Babu ruwanka da rashin ibada ta ko kuma kai ne kake bada aljanna."


Ya girgiza kai da fadin.'' Ba ni bane amma hakkin kulawa dake yana hannuna mutukar kinyi wasarere da addini da ibadarki to babu shakka nima ina da kamasho
"(zunubi)

Da gefan ido ta kalleshi har yanzu da sauran jin haushinsa a zuciyarta............Kawai saboda tana so ya kyaleta yasa ta bashi amsa da fadin." Tun asubah nai sallah sai na kwanta okey abinda kake so kaji kenan."

Yace." Eh abinda nake so na tabbatar kenan saboda haka kiyi duk wani uzurinki ina jiranki za muyi magana." Hanya ya nuna mata da hannu alamun ta wuce.

Ba tace komai ba ta ratse shi ta wuce tana tunanin abinda yake tafe dashi.


Wanka tayi ta fito ta shirya tayi komai a kan idonsa, hakika ya shiga tashin hankali sosai amma da yake yana iya sarrafa kansa beyi yunkurin yi mata wani abu saboda ba abunda ya shigo dashi kenan ba.


Tana gyara daurin dankwalinta, ya cimma inda take, ta mirror ta ganshi a tsaye a bayanta...........Gyara daurin dankwalin da ba tayi ba kenan ta fara kokarin barin gurin.

'Kungunta ya riko ya dan janyota jikinsa, ta kalleshi da mamakin abinda yake a fuskarta.


Dankwalin ya fara kokarin daura mata kawai ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah.

Sai da ya daura mata tsaf! sannan ya kai ta gaban mirror domin taga ni.

Sosai tayi mamakin yanda ya iya daura dankwali kamar mace, daurin yay mata kyau sosai, ta dan saki fuskarta amma bata iya yi masa godiya ba, juyowa tayi kawai taji ta a jikinsa, da yake yana daf da ita.

Ya dan rungumeta na second kafin ya cire ta daga jikinsa hannunta ya rike suka samu gurin zama.


Yanda yake kula da ita yasa jikinta ya mutu, abinda take bukata kenan dama, wasa take da yatsun hannuwanta tana sauraran maganarsa.


"Me yasa baki da sirri? me yasa zaki kira Asp a waya ki kai masa 'korafi akan abunda bai taka kara ya karya ba, Zinatu mai yasa kullum kike daukata a matsayin macuci azzalimi, ko kina tunanin Asp din ya fi ni sonki shiyasa kika fi yarda dashi a kaina, tsayin kwanakin ki a gidan nan mai nayi miki na cutarwa, ko don na gyara miki kuskuranki shine kike ganin kamar ina cutarki."


Fashewa tayi da kuka ta daga masa hannu da fadin." Kaga baka da bakin da za kayi min wata magana a yanzu, ka dauko ni daga gaban iyayena kazo kana kuntatawa rayuwata, me yasa kai baka da uzuri a rayuwa, duk abunda na fada ai ba 'karya bane kuma kai ma ka san gaskiya amma kake takewa, Asp kuma da kake magana a kansa dole na kira shi domin na sheda masa abunda ke faruwa, saboda a gurinsa kadai nake samun sassauci."

Zuciyarsa ta cunkushe da tsananin bacin rai da takaicin kalamanta, hakan ya nuna masa cewa Asp din ya fishi matsayi a zuciyarta.


Yayi namijin kokarin danne masifaffan kishin dake taso masa kafin yace.''Kina nufin Asp din ya fini iya kalamai kenan."?


Ba ta iya munafurci da kumbiya-kumbiya ba, wannan dalilin yasa take zaune lafiya, ta kalleshi da fadin." Eh shi baya zagi na duk abunda zanyi yana kokarin nusar dani cikin saukin kai, amma kai kullum cikin aibata ni kake har ka iya fitar da hannu ka tsinka min mari! shin kai kad'ai ne kake da 'yan uwa? nima ba daga sama na fad'o ba."


Yace." Wannan ne dalilin da yasa kika kira shi a waya kenan."?

"Eh shine dalili."

Ya girgiza kai da fadin.'' Okey bari nai miki magana ta 'karshe cewa duk sanda wani sa'bani ya gifta a tsakaninmu ki ka sake kiran sa a waya wallahi tallahi kinji na rantse da Allah sai na kwace wayar hannunki wannan shine hukuncinki."

Kallonsa tayi da mamakin furucinsa a tare da ita.

Ganin yanda fuskarsa take a murtuke yasa ta gazgata cewa zai aikata abinda ya fada, kawai sai ta dauke kanta daga kansa tana zumbura baki.

Ya cigaba da cewa." Tun da muke abotarmu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakanin mu ba sai ta dalilinki, to ina so na sheda miki cewa ke baki isa ki shiga tsakaninmu ba dole na dauki mataki a kanki idan yaso sai kiji dadin kirana da macuci da hujjah."!

Ita dai ba tace masa komai ba, har ya 'karaci fad'ansa ya tashi ya fita bata tanka masa ba.

Fitarsa daga dakin da kamar minti biyar Marakisiyya ta shigo, suka gaisa kafin ta sheda mata cewa ta shirya mata abun kari.

A ya mutse ta kalleta da fadin." Marakisiyya yanzu bana sha'awar komai sai funkaso saboda haka kije can sashen masu gidan ki basu uzuri na."

Tace." Shikkenan an gama ranki shi dade.'' Da sauri ta tashi ta fita domin isar da sa'kon uwar dakin nata.


Hamra'u ce ta shirya masa abin kari mai kyau! ta kuma yi ado da kwalliya tamkar wata amarya, bayan ta hada masa komai sai ta zauna a gabansa tana bashi labarai irin na ban dariya, yana break fast din yana sauraranta sosai yake jin dadin abincinta da labaran da take bashi fuskarsa sake sai murmushi yake.........Ita kuwa farin ciki mara misaltuwa ya cika zuciyarta dama babban burinta kenan tasa farin ciki a zuciyarsa ta kuma janye hankalinsa, don dai kada ta wuce gona da iri ne amma da tuni ta bashi abincin a baki.


Cikin wannan halin Marakisiyya ta shiga ta samesu.

Ita kanta sai da taji wani iri a zuciyarta, haushin Hamra'un ya rufe ta a ganinta hakan kamar bai dace ba.

Gabadaya hankalinsu ya koma kanta, daga can gefe ta tsuguna kafin ta fadi abunda yake tafe da ita.

Yayi jim! na minti biyu kafin yace." Okey babu damuwa je ki sheda mata cewa za'ayi mata abunda take bukata."

Hamra'u ta kalleshi da mamakin furucinsa, idan bata manta ba, a kwanakin baya da bakinsa yake cewa zai dauki mataki akan matar tasa amma shine yanzu ya kar'bi Uzurin ta, to ita dai gaskiya ba za tayi mata bauta ba idan ma tunaninsa kenan.

Bayan fitar Marakisiyyar ya kalleta da fadin." Kin ji Uzurin 'yar uwarki ko."?

Ta d'anyi murmushi da fadin." Eh naji yaya na."

Yace."Kiyi hakuri ki shiga kicin ki mata abunda take bukata kafin komai ya daidaita."

Ta d'an sauke munafukar ajiyar zuciya kafin tace." Yaya na ban iya funkaso ba domin wancan lokacin ma Uwale ce tayi mata ni idan nayi lalacewa yake."

Yace."Ayya! kinga yanzu kuma Uwale bata jin dadin amma bari na kammala na sheda mata ko zata iya shiga kicin din."

Ranta ya 'baci jin maganarsa, wato uzurin matarsa har yafi rashin lafiyar kakarsa......Tai shuru bata sake wata magana ba, da kansa ya dan fahimci wani abu amma bai kawo cewa kishi ne ya ha nata bin umarninsa ba.


A kwance ya samu Uwalen tana bacci, baya tsammanin zai tashe ta, don haka sai kawai ya fito daga dakin, ya kama hanyar fita, hankalinsa gabadaya yana kan gimbiyar ganin har sha daya ta gota bata ci abinci ba.


Ganin yana kokarin fita yasa da sauri tace."Yaya na akwai fa maganar da nake so mu yi." hannu kawai ya daga mata da fadin." Idan na shigo da daddare zamu tattauna." bai jira amsarta ba ya kama hanya ya fice.

Ta ciji yatsa cike da bak'in kishi a zuciyarta ta kwashe kayan karin kicin ta nufa ta wasu irin tunane-tunane a zuciyarta.


Shigarsa dakin besa ta dago kai ta kalleshi ba, hankalinta gabadaya yana kan wayarta hira suke da Sakina tana bata labarin irin rayuwar bakin ciki da take a gidan auran nata.

Maganarsa ce ta dauki hankalinta ta daga kai ta kalleshi........"Kin tura baiwar ki kina bukatar funkaso ko."?

Ta gyada kai alamun E......Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale ba ta jin dadi ita kuma Hamra'u tace bata iya ba me yasa ba zaki sanya hadiman ki suyi miki ba."

Ta dan ja numfashi kafin tace." Kawai nafi bukatar na gurin Uwalen yayi min dadi a wancan lokaci amma ko da wasa kada kasa wata

Please Login or Register in order to submit comment