Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafe insha Allah."

Da sauri tace." Laa da wasa fa nake maka."?

Ya 'bata rai da fadin." ZINAT an ta'ba wasa da lafiya ashe.'?

Jin yanda yayi maganar babu wasa yasa ta zama serious tace." Allah tsokanarka nake yanzu haka ma motsi yake yaji muryarka."

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Saboda kin ga na damu shiyasa zaki mayar dani shashasha ko.''?


Kunshe baki tayi tana danne dariyar dake kokarin subce mata, tace." Kayi hakuri Darling."


"Um-um! naki hakurin." Cikin shagawaba yayi maganar.........Tace." Dan Allah fa."

Yace." Nayi amma kada ki sake min wannan wasa hankali na ya tashi wallahi."

Tace." To ba zan sake ba insha Allah.''

Yace." Uwale ta tashi."? tace." Eh tana kicin tana aiki."

Yace." Idan babu damuwa ki kai mata wayar mu gaisa."

Tace." To insha Allah bari na kai mata."

Cikin jin dadi yace." Allah yayi miki albarka."

Ta amsa da "Ameen tana kokarin tashi tsaye.


****
Hamra'u da kanta ta shirya abincin ta zuba cikin kwanuka masu kyau ta jera kan tire kafin ta nufi bandaki a gurguje ta shiga wanka.

A lokacin ne mahaifiyarta Dayyiba ta samu damar aikata mugun nufin ta.

Ko kafin ma Hamra'un ta fito daga bandaki har ta sanya k'aramin d'anta ya dauki tiran dake dauke da abincin sun fita a tare.


D'aya da rabi na rana Uwale na aiki a kicin Dayyiba tayi sallama a gidan.

Uwale ta amsa ta fito daga kicin din tana mata barka da zuwa, kai tsaye daki suka nufa.


Suka fara gaisawa tare da tambayar bayan rabuwa.....Dayyiba tace." Ai da wuri yau na gama abinci nace bari nazo mu gaisa na kuma ga matar Umaru kin san dama ni ban ta'ba ganinta ba."

Uwale tace." Allah sarki sannu da kokari Dayyiba har da wahala haka to mun gode sosai."

Tana murmushi tace." Babu komai Dambu ne na turara mata na san masu ciki da kwad'ayi watakila yayi mata dadi."


Tace." Eh 'kwarai kuwa, bacci takeyi yanzu amma bari na leka na gani ko ta tashi."


Lokacin da ta shiga dakin zaune ta sameta a bakin gado tun bayan shigowar Dayyibar ta tashi duk tana jin maganganunsu.


Tace." Ashe kin tashi dama mahaifiyar Hamra'u ce tazo ku gaisa ta kuma kawo miki abinci."


Tace."Allah sarki amma na gode sosai bari na fito mu gaisa."

Ta juya da fadin." To bari na sheda mata."

Shuru tayi tana nazarin al'amarin, mahaifiyar Hamra'u? ita sunan yarinyar ma bata kauna ballantana wanda ya danganceta.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi da k'yar! yunwa sai sasakar cikinta take, abun goge baki ta dauko cikin kayanta.

Koda ta fito bata zauna ba tukkuna sai da ta wanko bakinta ta dauro alwala sannan ta dawo dakin.

A nutse ta zauna kusa da Uwale ta kalli Dayyibar dake mata wani munafikin kallo tace." Ina wuni fatan mun sameku lafiya."?


A firgice ta amsa da fadin." Lafiya lou muke ya mutan gida da can gurin manyan."

Tace." Duk suna nan lafiya lou."
Daga haka sai ta kawar da kanta tana nazari akan matar kamar mara gaskiya.

Uwale ta bud'e kwanunkan abincin da fadin." Dambu ne ko kina sha'awa."

Kamshi ya bugi hancinta Dambun ya hadu yaji gyada da zogale ga k'amshin man gyada ziryan yana tashi...........Tunda take sau biyu kacal ta ta'ba cin irin wannan abincin, shima kuma irin na shinkafa bana masara ba , wannan dalilin yasa gabadaya ta rikice yaron dake cikinta ya nuna kwadayinsa akan abincin .

Ta kalli Dayyibar da fadin" Na gode sosai."

Tana washe baki ta amsa da babu komai dan nayi miki hidima kamar 'yar cikina kike."

Murmushi kawai tayi ta kalli Uwale da fadin." Nayi sha'awarsa.".

Uwale tasa dariya da fadin.'' Ai dole ni kaina ya bani sha'awa ballanatana ke da kike da lalura."


Dayyiba ta dinga dariyar farin ciki tace." Ai kin san Hamra'u ta gwane gurin iya abinci gargajiya dama na turawan kowacce mace tana da baiwa, amma tabbas duk macan da ta iya girki zata samu soyayyar mijinta.

Ba ita Zinat din ba har Uwale sai da taji babu dadi da maganar Dayyibar dan kamar maganar tayi kama da habaici.

Babu dai wanda yayi magana a cikinsu, ta zuba mata a ma daidaicin plate. tayi bisimillah ta fara ci a nutse ba ta tunanin komai a ranta.

Sosai dambun yayi mata dad'i, tas ta cinye wanda yake gabanta. a cikinta tana jin k'oshi amma a bakinta ba ta gaji ba, haka dai tayi kawaici tasha ruwa.Uwale ke tambayarta, tace." A yanzu dai ta koshi sai zuwa an jima tukkuna."

Dayyiba mahaifiyar Hamra'u zuciyarta fes! ta fita gidan, babban burinta cikin ya zube ko kuma Gimbiyar ta galabaita.

Aikuwa dai jikinta ne ya mutu kasala ta dame ta, sai kawai taje ta kwanta tana ya mutse fuskarta cikinta ne yake hautsinawa zuciyarta na tashi.

Minti ashirin da kwanciyarta ta tashi a gigice! sakamakon jin wani irin mahaukacin amai da yake taso mata.


Bakin rariya ta gurfana ta dinga sheka aman tana rike kirji!


Uwale hankalinta ya tashi ganin mawuyacin halin da Gimbiyar ke ciki.

Ta rike ta tana mata sannu a lokacin kanta ya dinga juyawa tayi kwance a gurin tana mayar da numfashi.

Uwale tace." Sannu ki daure ki tashi ki koma daki ki kwanta a can kinga nan akwai rana gaki a bakin kwata a kwance."



Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, gabadaya ma bata cikin hayyacinta, tana jin yanda cikinta yake kartawa! wannan karan ba amai takeji ba zawo! ne mai karfi yake kokarin kwace mata.

Kokarin tashi take domin shiga bandaki abun ya gagara domin gabadaya jikinta ya shika babu kwari! duk yanda taso da ta daure ta kasa ba ta ma san lokacin da zawon ya kwace mata ba, kawai sai tsuuuuuu! ta dinga jin fitarsa kamar an kwance famfo.


Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! shine abinda Uwale take nanatawa.

(Cutar a mai da gudawa!) ya kama 'yar mutane! cutar dake saurin halaka mutum, hankali a tashe ta nufi gidan Tasallah.


Suka shigo tare lokacin gudawar sai bin rariya take ita kuma tana kwance a gurin sai matagugu take domin wani masifaffan ciwo cikinta yake mata.


Tasallah tayi salati tana sanar da Ubangiji kafin tayi azamar fita, gidanta ta koma da yake akwai magungunan gargajiya da take aje dasu, ta daga karkashin gadon karfenta ta dauko ledar maganar duk tayi kura da dauda! da yanar gizagizo ajikin ledar ta dauka ta fita.


Aje ledar tayi a gefe ta taimakawa Uwalen suka fara gyarata, idonta a lumshe yake amma duk tana jin taretaran da suke da ita, ta riga ta mika wuya yanda take jin jiki bata tsammanin zata rayu.

Jikinta suka wanke mata lokacin anyi sa'a Gudawar ta tsaigata da zuba.

Uwale tayi saurin dauko mata wasu kayan da wando da rigar nono suka sanya mata jikinta mikar da ita sukayi kafafunta suka dinga kyarma! a daddafe suka shiga da ita daki.


Uwale ce ta shiga gyara gurin, ita kuma Tasallah sai da ta tsaftace hannuwanta, sannan ta kwance ledar maganin data dauko ta fito dasu a daddaure! daka gani sun jima a ajiye, wuta ta hura kafin ta wanke maganin tas ta zuba a tukunya tasa jar kanwa sannan ta d'ora a wuta.

Sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke domin yasha iska.


To cikin ikon Allah da hukuncinsa tana shan wannan magani ta samu sassauci ciwon cikin da yake damunta yayi sauki baccin wahala ya d'auketa.

Uwale ta kalli Tasallah da fadin." Sai yanzu hankalina ya kwanta Tasallah al'amarin nan ya tsorata ni mutuka."

Tace." Dole ne, ni kaina ganin yarinyar a galabaice sai da na firgita kasancewar na san cewa wannan cutar na saurin halaka mutum! Allah yasa akwai ajiyayyun magunguna kinga cikin ikon Allah sunyi amfani "


Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Tasallah nifa ina zargin Dayyiba."

Shuru tayi tana kallonta da mamakin maganarta.

Tace." Tun bayan da yarinyar nan taci Dambun da Dayyibar ta kawo mata shikkenan ta rikice shiyasa nake zargin ko da abunda tayi.


Tace." Uwale zato zunubi aka ce koda ya kasance gaskiya ne, ni kuma nafi tunanin ko sauyin cima ne da ruwan sha, kin san hakan na iya janyo faruwar mummunar matsala.


Tace." Idan hakane me yasa jiya da taci abincina ta kwana lafiya? ruwa kuma ba irin wannan muke sha yarinyar take sha ba, kafin mijinta ya tafi sai da ya siya mata ruwan roba gashi can a daki kwali guda. gaskiya ina zargin Dayyiba.


Tasallah tayi murmushi da fadin." Hakan na iya faruwa amma kada kiyi gaggawar yanke hukunci tukkuna.

Shigowar Hamra'u ne ya katse maganar, babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska, ta zauna suka gaisa, kafin ta kalli Uwale da fadin." Ummana ta kawo miki Dambu ko."?

Tace." Eh ta kawowa dai Gimbiya."

Ta dan 'bata rai da fadin." Ai naki ne kasancewar na san kina son Dambun masara yasa na tashi da wuri nayi miki, ko kafin na fito daga wanka na samu Ummana bata gidan wai ashe anan tazo."

Tace." To Na gode sosai Allah yayi miki albarka."

Tasallah na 'yar dariya tace." Hamra'u kenan to menene dan kishiyarki taci ai abun burgewa ne "

Zumbura bakinta tayi tana ya mutse fuska.......Dukkaninsu babu wanda yaji dadin abinda tayi, kiri-kiri take nuna kishinta a fili.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/15/22, 22:22 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*107&108*
Sai gefin magariba ta tashi daga baccin daya d'auketa, jiki babu kuzari ta tashi zaune da sunan Allah a bakinta, shiru tayi tana tunanin irin wuyar da tasha a d'azu, tabbas da kwananta ya 'kare babu wanda ya isa ya hana Allah zartar da Allah ikonsa, sam ba tayi tsammanin cewar zata sake wata rayuwar ba, duba da irin siradin data tsallake, a mai da gudawa ba karamin cuta bane, yanzu ma gabad'aya bata jin dadin jikinta, duk yayi laushi akwai bukatar karin ruwa a tare da ita.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta fara kokarin sauka daga gadon, kira ya shigo wayarta dake saman gadon, ta dauka tana dubawa, a kalla ya kira yafi sau ashirin tana bacci, tausayinsa ya rufe ta, tasan yana can a dame kamar yanda take a takure! ko kuma jikinsa ne yake fada masa cewa akwai matsala.

Ta daga wayar cike da so taji muryarsa, network yayi tsiya dan sai magana take masa amma shi ba yaji.....Ta kashe wayar ta sake kira anan ma ba babu biyan bukata, kamar zata fashe da kuka ta ajiye wayar takaici duk ya isheta.

Uwale ta shigo dakin, ganinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tace." Kin tashi ko ya jikin naki."?

Tayi kokarin danne damuwarta ta amsa da fadin." Naji sauki sosai na gode."

Tace." Haba ai babu godiya a tsakaninmu Gimbiya Allah dai ya kiyaye gaba."

Ta amsa da "Ameen ya Allah."

A sanyaye tace." Amma don Allah ina neman alfarma a gurin ki."

Cike da mamaki take kallon matar wace irin alfarma ce."?

Tace."Don Allah kada ki fad'awa mijinki abunda ya faru kinji ko."?


Murmushi kawai tayi kafin tace." Insha Allah kada ki damu ba zan fad'a masa ba."

Tace." To na gode sosai.''


Har ta juya zata fita daga dakin ta dakatar da ita....."Ina bukatar nayi wanka jikina bana jin dadinsa."

Tace." Ai dole! amma kiyi hakuri ayi sallah tukkuna bari na dora miki ruwan zafi sai ki gasa jikinki."


Tace." To shikkenan hakan yayi." Uwale ta fita daga dakin tana godiya ga Allah ganin yanda ya gajarta musu wahala.


Cikin ikon Allah ta na yin wanka jikinta ya warware ta zauna taci abinci zuciyarta fes domin ba tayi tunanin cewa wai abincin da taci dazu ne ya janyo mata matsala ba, itama tafi tunanin cewa ko sauyin yanayin gari da sauransu.

Ta kalli Uwale da fadin." Ina so nayi waya amma gidan nan bashi da network yana bada matsala."


Tace." To yanzu ya za'ayi kin ga yanayin gidajen namu ginin da ne babu tsayin katanga a daki ga zurfi.

Tace." Zan fita waje ko Allah zai sa a dace."

Tace." To shikkenan babu damuwa.


Can wani fili ta nufa, duk da dare ne hakan bai hana gane ta ba, ido yayi caaa! a kanta, yara da manya masu wuce wa.

Ita dai bata damu ba bukatar ta, ta samu wayar masoyinta.

Bugu daya ta shiga ya daga, abun mamaki tar taji muryarsa babu gargada.

Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke kafin tace " Darling ya kake? ina fatan kana cikin koshin lafiya."


Yace." Kin san hakan ba zata samu ba, ZINAT me yasa baki d'aga wayata akan lokaci ba."


Tace." Ba laifi na bane network ne babu a garin, nima na damu da kai sosai wannan dalilin yasa na fito waje wani fili duk dan naji muryarka."


Yace." Yanzu kina nufin ba'a cikin gida kike ba."?

Tace." Eh ai cikin gidan na fad'a maka babu network mai kyau.

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ki koma gida bana san tsayuwar ki a gurin nan."

Tace." Haba babu fa abunda zai faru duk ga jama'a nan suna kai kawo a gurin."


Ajiyar zuciya ya ýÿÿÿ‚
ƒ




ˆ

Š

Œ

Ž









˜

š

œ

ž
Ÿ
 
¡
¢
£
¤
¥
¦
§
¨
©
ª
«
¬
­
®
¯
°
±
²
³
´
µ

·
¸
¹
º
»
¼
½
¾
¿
À
Á
Â
Ã
Ä
Å
Æ
Ç
È
É
Ê
Ë
Ì
Í
Î
Ï
Ð
Ñ
Ò
Ó
Ô
Õ
Ö
×
Ø
Ù
Ú
Û
Ü
Ý
Þ
ß
à
á
â
ã
ä
å
æ
ç
è
é
ê
ë
ì
í
î
ï
ð
ñ
ò
ó
ô
õ
ö
÷
ø
ù
ú
û
ü
ý
þ
ÿ
 sauke yana tunanin wani abu a ransa, jiya kwana yayi yana munanan mafarkai a kanta, amma yasan babu wani mahalukin da ya isa ya cutar da ita face Allah ya mayar masa da sharrin kansa.


Hamra'u da k'awarta Zabbah suka hangota a tsaye da waya a kunne.

Hamra'u tace." Zabbah ga mutsiyaciyar can."

Zabbah ta kalli gurin da fadin." To me ya fito da ita a wannan daran ita ba 'yar gari ba."


Tace." Waya ta take na san kuma da masoyina take, yau sai naci mutuncinta in yaso duk abinda zai faru ya faru."


Zabbah ta rike hannunta da fadin." Hamra'u kada fa ki aikata abunda zai janyo miki matsala ki bi komai a sannu a hankali."


Ta fizge hannunta da fadin." Zabbah ni kad'ai na san irin b'akin cikin da wannan matar ta k'unsa min, ai magana ta 'kare tunda manya sun shiga maganar har an tsayar da ranar daurin aure."


Hannunta ta fizge ta durfafi gurin da Gimbiyar take tsaye....Zabbah ta rufa mata baya.


Tace." Darling zan shiga na kwanta sai da safe." Daga d'aya b'angaran yace." Okey Allah ya tashe mu lafiya amma ki mika min gaisuwa gurin babyna kafin mu had'u."


Tana murmushi tace." Zai ji da kyau! amma shima yayi kewarka sosai.

Yace." Haka nake so ai duk sanda muka had'u zamu gaisa sosai ki bashi hakuri."

Cikin shagwaba tace." 'Daya babyn naka ma yana bukatarka fa."

Ya lumshe ido tsigar jikinsa na tashi! ya gane abinda take nufi shiyasa gabadaya kasala ta rufeshi yana bala'in son yanayin shagwabarta.

Yace." Wannan babyn yayi min laifi ki sheda masa cewa idan muka had'u zan hukuntashi da kyau."!

Ta fashe da dariya da fadin." Ba ruwana amma na yarda duk sanda kuka ka had'u kayi masa hukuncin da ya dace."


Yana sake release a kujera yace." Zan kuwa cire masa kai shine hukuncin da zanyi."

Maganar ta bata kunya sosai tana 'yar dariya tace." Ni dai sai da safe."

Yace." Dole ki gudu mana kin san halin da ki ka jefa ni ciki kuwa."?


A sanyaye tace." Kayi hakuri gobe ka dauki azimi."

Yace." Azimin dole kada kiyi tsammanin gani na gobe kuma idan nazo komai rigimarki tare zamu tafi."

Tace." Ai gobe ne bikin idan kazo sai mu tafi shikkenan."

Yace."Okey Allah ya kaimu amma mybe shigowar dare zanyi.

Tace." To idan hakane kawai ka bari sai jibi da wuri sai ka shig.......maganar ta katse sakamakon zuwansu Hamra'u gurun.

Ta kashe wayar tana kallonsu.

A wulakance tace." Munafukar Allah ta ala to duk asirin da kuke Allah ya karya alkadarinki, ina so ki san cewa baki isa ki hana abinda Allah ya hukunta ba."

Cike da mamakin maganarta tace." Ke wannan wace irin magana ce."?


Da yatsa ta nuna ta kamar zata tsone mata ido tace." Hamra'u ta UMARU ce shekara da shekaru ina nufin ke baki isa ki shiga tsakanin masoya ba."

Sai abun ya bata dariya amma ba tayi ba ta dake ta sha kunu da fadin." Kin san ni nafi karfin kiyi min rashin kunya ko."?


Aikuwa sai ta fusata! ta sake nuna ta da hannu da fadin." Ke asuwa kuma? ko kin dauka kina da mutunci a garin nan, to bari kiji dake da kare! baku da maraba domin bama 'kaunarki, kuma ki kwana da shirin wata shida kacal ya rage a daura min aure da mijinki sai kiyi duk abinda za kiyi."

Ranta ya 'baci sosai da irin fitsarar da yarinyar take mata, kawai sai ta girgiza kai ta kama hanya domin barin gurun.......Tace." Matar cushe bata daraja."!!

A fusace! ta juyo ta wanke fuskarta da mari wanda sanya ta ganin gilmawar taurari! ta dafe gurin cikin kad'uwa da mamaki take kallonta.

Ta nuna ta da hannu tana so tayi magana, amma tsabar b'acin rai ya ha nata furta komai, kawai ta girgiza kai a gaggauce ta bar gurin, zuciyarta kamar ta fashe saboda tsananin bacin rai!


Zabbah ta kalleta da fadin." Ko babu komai kin sha mari! wallahi Hamra'u baki da wayo har yanzu."


Ido jawur! take kallonta kafin tace." Kin san Allah Zabbah! sai na rama mari na don kutumar ubanta tazo cikin garinmu ta mare ni, wallahi ba zan yarda ba." Fizge hannunta tayi ta nufi cikin gidan.

Zabbah ta bita da kallon takaici tana girgiza kai kwata-kwata Hamra'u bata da wayo wallahi, kishi hauka take, ai idan itace ba zata fito da kishinta a fili kowa ya fahimta ba, amma ita duk inda ta zauna maganar kenan, tayi ta zagin Gimbiyar

Kai tsaye da ta shiga gidan kanta ta nufa gadan-gadan! mari ta kai mata, tayi saurin kaucewa ta mari iska!! ta tsaya tana numfarfashi idonta cike da ruwan hawaye take fadin." Wallahi baki isa ki mare ni na kyale ki ba, sai na rama." Ta sake mika hannu da niyyar marin ta, kafin tayi aune! taji saukar wani lafiyayyan marin a fuskarta!

Uwale hankali a tashe! ta shiga tsakaninsu tana tambayar ba'asi.

Gimbiyar ranta a 'bace tayi mata bayanin duk abinda yake faruwa.

Uwale ta kalli Hamra'u da fuskar bacin rai tace." Amma wallahi kinji kunya Hamra'u kin 'bata wayonki ban ta'ba tunanin haka zuciyarki take ba sai yau."

Sai kawai ta fashe da kuka takaici biyu ya dameta, na farko tasha marika masu zafi daga gurin Gimbiyar, gashi bata samu sararin ramawa ba ana fada mata bakar magana, dama ba tun yau ba ta gane cewa Uwalen tafi kaunar Gimbiyar a kanta.

Bakin ciki da takaici ya ha nata magana kawai ta kada kanta ta kama hanyar fita tana share hawaye.

Zabbah dake tsaye a tsakar gida tabi bayanta tana rarrashinta.....''Yanzu idan Umar din yaji abinda ki kayi wa matarsa kina tsammanin zai kalleki da mutunci? Hamra'u shifa yaki dan zamba ne me yasa zaki 'bata rawar ki da tsalle."

Ta daga mata hannu da fadin." Kin ga Zabbah na gaji da jin wannan maganar taki, domin ta kunan hagu take fita, kin san Allah sai na saubata matar nan! sai ta gwammace kida da karatu."

Zabbah tace." Yawwa to dama tuntuni ta wannan hanyar ki ka biyo yafi sauki idan kin bi ta karkashin kasa babu wanda zai fahimce ki, amma kin zauna kina hauka haba Hamra'u!

Mugun tsaki taja mai tsayi fuuuuuuu! ta shiga gidansu ba tare da tayi mata sallama ba, girgiza kanta tayi itama ta kama hanyar gidansu cike da mamakin al'amarin.


Malam Shafi'i yana dawowa Dayyiba ta shirya masa karya da gaskiya cewa yana da kyau yaje har gidan Uwalen ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro domin ba zai yuwu ace 'yar uwar tasa tana fifita wata a kan jininsa ba.

Aikuwa ya dauki zugar matarsa domin ransa ya baci da jin abinda 'yar uwarshi ciki daya tayi wato tana fifita wata a kan 'yarsa


Har gida yaje ya sameta ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sai kumfar baki yake yana sakin kausasan maganganu wanda duk wani mai hankali ya auna maganar ya san habaici ne.

Tana daga cikin daki duk ta na jin abinda yake faruwa....Uwalen na share hawaye tace." Shafi'i na gode da cin mutunci matarka ta zuga ka kazo har gida kaci mutuncina cikinmu daya da kai, baka duba furfurata ba, ka tsaya a kaina kana fada min magana babu komai na gode."

Yace." Ai gaskiya na fada miki Uwale ki gyara kuskuranki, kafin ki k'aunaci kowa Hamra'u ya kamata ki nunawa kauna da kulawa, amma a karon banza kin watsar da zumunci saboda kwadayi kin kama wata mara tarbiya kina mata ladabi a gabanki ta fitar da hannu ta tsinkawa yarinya mari ki kasa daukar mataki, karshe ma ki ka mayar da laifin kanta, wannan ba adalci bane."


Ta sanya gefan zani ta goge ragowar hawayen da ya rage tace." Tabbas da na san wannan bacin ran zan samu da nayi zamana banzo ba, Shafi'i ban ta'ba tunanin akwai ranar da za tazo ka tsaya a gabana ka nayi min rashin kunya ba."

Yace." Duk abinda nayi miki ke kika janyo idan kina son zumuncinmu ya cigaba da gudana to kiyi gaggawar sanya albarka a cikin auran Umaru da Hamra'u! domin da kin so da tuni Umaru ya auri yarinyar nan idan da rabo a kusa ma da tuni ta haihu."

Tayi shuru ta kasa magana tsabar bacin rai!

Shi kuwa rigarsa ya buge ya fita daga gidan ransa a bace.



Tana daga cikin dakin take jin sautin kukanta, tausayinta ya rufeta,duk akan ta nuna kulawa da ita ne yasa aka zo har gida aka sanya ta zubar da hawaye......ita kuwa zata bawa mara da kunya. taji wani kwarin gwiwa a tare da ita.


A nutse ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafad'arta.

Ta kalleta a sanyaye da fadin." Kiyi hakuri abinda akayi miki kinji ko."

Girgiza kanta tayi da guntun murmushi a fuskarta tace." Uwale ke zan bawa hakuri nasan dalilina dan uwanki yazo har gida yaci miki mutunci iya son ransa, kuma cikin maganganunsa na fahimci abunda yake nufi. Ban hana Umar Auran Hamra'u ba, nima kaddara ce ta had'a ni dashi ashe shine uban 'ya'yana ban sani ba, Amma wallahi kaf tunanina bai ta'ba kawowa cewa zan aureshi ba ballantana har na fuskanci matsala irin wannan, wallahi na amince ya auri yarinyar nan mutukar shine kwanciyar hankalinku gabadaya.

Uwalan ta dinga kallonta tana mamakin furucinta, sam ba tayi tsammanin cewa tana da sauki kai irin haka ba, yarinyar nada nagarta sai mu'amula ta had'aku sannan zaka fahimta.

****
Washe gari da sassafe ta fita wajen gidan domin samun network......Lokacin jama'a basu fara kai kawo ba, ta kira shi yana shirin fita.

Cike da farin ciki ya daga wayar ''Farin ciki na kin tashi lafiya."?

Ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta d'ora da fadin." Za kazo yau din."?

Yace." Eh insha Allah, ina fatan lafiya.''? ba tace masa komai ba, kawai ta kashe wayarta ta koma gidan.

Ta samu Uwale ta fito da shirin shiga gidan Tasallah........Tace." Na fita ne nayi waya da maigidanki yace yana kan hanya insha Allah."

Tace."Allah ya kawoshi lafiya da dai nayi niyyar mu zauna mu kwana biyu amma saboda abubuwan da suke faruwa na rashin dadi gwara mu tafi shi yafi alkairi."

Murmushi tayi wanda ya tsaya iyakacin fatar bakinta, tace."

Please Login or Register in order to submit comment