Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'auye zamana a can yafi alkairi."

Yace." Me nayi miki wanda ya janyo wannan maganar."

Tace." Akan abunda kake Umaru shin ko ka samu ta'bin hankali ne."?

Yace." Lafiyata lau na san dai duk kina wannan maganganun akan Zinatu, gabadaya ni yanzu bana ra'ayin zama da ita.

Tace." Shine dalilin da yasa ka koreta dada gidanka.?

Babu wata damuwa a tare dashi yace." Aa ni ban kore ta ba, ita ta kori kanta."

Tace." To shikkenan tunda kace haka mutukar kana bukatar zama tare dani kaje kayi bikon matarka."

Yace." Uwale ni yanzu muhimiyyar tafiya ce a gabana gobe insha Allah, sai dai idan na dawo."

Shuru tayi kafin tace." Umaru baka kyauta ba wallahi jiya abokinka yazo gidan nan hankalinsa a tashe, a bakinsa na samu labari cewa yarinyar bata gidan.

Yace." Kina nufin Asp yazo gidan nan bayan na fita."?

Tace." Eh yazo kuma yayi min cikakken bayani akan abunda yake faruwa tsakaninka da matarka, gabadaya kaine baka da gaskiya Umaru me yasa ba zaka tausaya mata ba duba da juna biyun da take tare dashi."


Yayi shuru zuciyarsa nayi masa wani irin zafi! Asp ya samu damar da har yake shigo masa gida ba tare da izininsa ba, har ya samu damar da zai dinga bibiyar abunda ya shafi iyalinsa, shi ai ba yayi masa wannan katsalandan din, ya kamata a wannan karan ya nuna masa kuskuransa.


Hamra'u ta had'a masa ruwan wanka yayi ya samu sassauci amma kadan domin shi kadai ya san irin bakin cikin dake cin zuciyarsa.


Ya sanya jallabiya da gajeran wando ya fito falo fuskar nan a murtuke!

Ita kuwa Amarya ta rangad'a ado sai kamshin turare take mai dad'i da tayar da sha'awa.

Yana zama gurin cin abinci ta isa gurin cikin kwarkwasa da karairaya ta hada masa abincin ta zauna kujerar dake fuskantarsa tana murmushi take bashi labarai irin na jan hankali.


Shi dai uffan bece ba abincinsa kawai yake ci, abinda ya dame shi ne a gabansa.


A gabanta ya kira wayar Zinatu. koda ta duba taga shine sai ta ajiye wayar........Lokacin mahaifiyarta ta shiga dakin ta samu kiran ya sake shigowa a karo na biyu.

Ta kalleta cikin tausayi da jin kai irin na uwa, tace." Ki daga wayar mana."

Murya a dashe! tace." Shine fa."

Tace." To sai me? ki daga kiji abinda yake tafe dashi."

Kamar ba taso ta daga wayar tasa a kunne can kasan makoshi tayi sallama!

Gyaran murya yayi kafin yace." Na dawo na samu labarin kin tafi gidanku shin me kike nufi da aikata hakan."?


Shuru tayi ta gaza furta komai.

Yace." Ke nake sauraro ko kin gaji kamar yanda nima na gaji."?

Hanci taja kafin tace." Bani da lokacin tsayawa na saurarin wannan mayaudariyar muryartaka duk hukuncin daka yanke dai-dai ne a guri na."
Kawai ta katse wayar ta ajiye. wasu zafafan! hawaye suka kwace mata! ya cuceta ya dirka mata ciki yana mata iskancin da ransa yake so.

Uwar ma kamar ta fashe da kuka saboda da takaici. kaf rayuwar yarinyar kwatankwacin rayuwarta ne! tausayinta duk ya isheta, ta sassauta murya da fadin." Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki insha Allah zamu tattauna maganar da mahaifinki idan auran ba zai yuwu ba a rabu shi yafi alkairi."

Da sauri tace."Mammah ni kaina nafi bukatar rabuwar, babban takaici na wannan cikin da nake dauke dashi."

Tace." Wannan kuma sai ki barwa Allah, domin shi ya barwa kansa sanin abinda yake boye, kawai kiyi fatan rabuwa dashi lafiya."

Kasa magana tayi kawai ta sunkuyar da kanta sai so take ta tsayar da hawayen dake zuba amma ya gagara! zubar hawayen shine samun zaman lafiyarta.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta girgiza kai ta kama hanyar fita zuciyarta cike da tunanin neman mafita.

Kishingide ta sameshi a dakin hutawarsa.
A nutse ta zauna kusa dashi kafin tace." Barka da hutu ranka ya dade."

Ya amsa da "Barka kadai Gimbiyar mata ya gida ina 'yar uwar taki.''? ya tambayeta Safara'u saboda ya san abinda ya kawo ta gurinsa bayan ba girkinta bane tabbas itama Safara'un tana tafe.
Tana kokarin magana Safah din tayi sallama, jikinta nannade da lifaya kwantankwancin ta jikin Aysha.

Suka gaisa cikin girma da mutunta juna.

Zamansa ya gyara yana kallonsu daya bayan daya kafin yace." Labarin gizo a tambayi koki tun kafin kuyi min bayanin abinda yake tafe daku na karanci hakan a fuskokinku. to ina jiran shigowar Magajin sarki ne domin shi nakeso ya kira mijin yarinyar muji daga bakinsa."

Gimbiyar tasha kunu da fadin." Ranka ya dad'e wannan al'amarin fa bana wasa bane ya za'ayi a matsayinka na mahaifin yarinyar nan ka wakilta wani ai sai ya kara rainawa mutane hankali saboda haka kai ya cancanta kayi magana dashi."

Yace."Aysha ko bayan raina Abdullahi shine Magaji na, wannan dalilin ya sanya nasa shi a cikin maganar domin yayi wa 'yar uwarsa wakilci, ita tazo da magana to amma yana da kyau shima mijin nata aji daga bakinsa.

Tace." Wannan yaro fa bashi da kirki! ranka ya dade in banda wulakanci da ciki zai kori yarinya me tayi masa haka da zafi."?

Yace." Ashe har kin manta halinta kenan? Aysha idan ke kin manta wacece Zinatu ni ban mance ba, kada ki manta irin d'auki ba dadin da muka dinga yi da ita kafin ta amince da auran, ko shakka ba nayi matsalar daga gurinta take.

Safah ta katse shi ta hanyar fadin." Kada kayi gaggawar yanke hukunci ranka ya dad'e! yanda yarinyar nan ta zabge lokaci guda shine zai nuna mana cewa akwai matsalar da take faruwa a tsakaninsu kuma taura d'aya bata taunuwa, bahaushe yace idan anbi ta b'arawo to abi ta mabi sawu, dole shima nasa laifin saboda haka yana da kyau yazo gabanka ku tattauna domin magana ta waya ba zata gamsar ba."

Yace." Wannan shawarar taki tayi Safara'u abinda za'ayi kenan. Insha Allah komai zai warware.

Magajin Sarki ne ya shigo da sallama a bakinsa.

Gabad'aya suka amsa. ya samu guri ya zauna kafin ya fara gaishe su......Maimartaba yace." Ka kira Umaru mijin Zinatu kace masa ina san ganinsa idan ya samu dama."

Ya fito da waya domin bin umarni.

Daf da zata katse ya daga wayar............bai ma duba suna ba, sai da yayi masa bayanin kansa sannan yace." Magaji afuwa don Allah ya mutan gida ina fatan kuna lafiya."

Yace." Kowa Lafiya lau dama Maimartaba ne ya bukaci ganinka idan ka samu dama."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Magaji ayi min afuwa ina da uzuri aiki zai kani Zamfara sai dai idan na dawo.''


Ransa ya baci da jin abinda yake fada.......Yace." Okey to idan babu damuwa inaso na san dalilin da ya sanya Zinatu zuwa gida."

Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu wani 'kwakw'kwaran dalili nima kawai na dawo gida na samu bata nan."


Yace." No! akwai dalili Goje sai dai idan ba zaka fada ba."

Murmushi yayi kafin yace."Ka tambaye mana ni dai na san lafiya lau muke zaune amma ina tunanin kishi ne dalilin da ya sanya ta yanke wannan hukuncin."

Yace."Kishi kuma."?

Yace." Eh 'kwarai kuwa na 'kara aure kwana uku da suka wuce wannan shine abinda nake tunani."


Yayi murmushi da fadin." Ni a ganina wannan kadai ba zai janyo har tazo gida ba ko ka manta da lalurar da take tare da ita."? A dan kausashe! yayi maganar.

Shima ya fusata! yace." Magaji yarinyar nan fa bani na koreta ba, ita ta kori kanta, kuma saboda ita ba zan fasa abinda nayi niyya ba, nasan kasan mata hudu Allah ya halasta min to akan wata ba zan tauye rayuwata ba."


Ya girgiza kansa da fadin." Okey to babu damuwa Allah ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya.

Ya amsa da "Ameen ya Allah."

Cikin rashin dadi sukayi sallama da juna.

Da yake hands free yasa wayar duk suna jin abunda suka tattauna.

Yana kishingide bai ce komai ba.....Gimbiya Aysha kuwa sai fad'a take da fadin." Wannan auran warwareshi shi yafi alkairi dama can ita al'amarin be kwanta mata ba, auran jahili wanda yayi rayuwa a daji! bashi da fa'idah mutumin kauye akwai karancin ilimi ta tare dashi babu abunda ba zai aikata ba."


Duk yana jin sababin da take bai ce komai ba har sai da ta gama tukkuna ya gyara zamanshi kafin ya fara magana kamar haka.





*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/22/22, 21:16 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*117&118*
"Aysha duk wannan maganganun da kike basu da tushe ballantana makama, wannan dalilin kad'ai ba zai sanya mu kashewa yarinya aure ba, ba hujja bace, dole mu jirayi zuwansa kamar yanda ya fada yana da uzuri to zamu saurare shi zuwa lokacin da zai kawo kansa."

'Bacin rai ya hana ta magana, kawai taja bakinta tayi shuru takaici tare da tausayin 'yar ta kadai ke damun zuciyarta. Ganin yanda hankalinta ya tashi yasa Shafara'u kwantar mata da hankali da tausasan kalamai masu sanyaya zuciya gami da sa tawakkali da dangana.

Yana kallonsu yayin da suke tattauna maganar so kaunar Safah na cigaba da bin kowane 'bargo na jikinsa, har yanzu tana nan da kyawun zuciya da kuma fahimta, a duk sanda Gimbiyar tasa ta rikice ta tafka wani shirman yana alfahari da ita gurin ganin ta shawo kan matsalar da duk ta shafe su baki d'aya.

****
A daran Asp ya kira wayarsa don da shima har yayi zuciya da abubuwan da yake masa na rashin kyautawa, sai kuma yaga da cewar kiran wayarsa domin su tattauna akan maganar yarinyar da aka bashi amanarta.

Dai-dai lokacin da ya fito daga wanka kiran ya shigo wayarsa.

Sai da ya mula tukkuna kafin ya daga wayar yayi salama babu cikakkiyar walwala a tare dashi.

Ya amsa shima babu sakewa kafin yace." I dan babu damuwa ina so mu tattauna muhimiyyar magana."

Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Ba damuwa ina sauraranka."

Yace."Maganar dai akan Zinatu take duk da baka san na shiga cikin al'amarin amma ya zama dole na shiga tunda amana ce a hannuna."


Ya danne 'bacin ransa kafin yace." Okey ina sauraranka."

Ya cigaba da cewa." Yanzu Umaru dai-dai kenan abinda kayi ka kyauta! har ka rufe idonka kaci mutunci yarinya da juna biyu a tare da ita, 'bacin ran abinda kake har ya kai ta tattara kayanta ta tafi gidansu, Umaru kai a ganinka hakan dacewa ne."?

Yace." Kaga Asp ni da hankali da tunani nake al'amurana, wannan m  atsalar data shafe ni ce babu ruwanka da ita, maganar Zinatu ta tafi gidansu wannan matsalarta ce, idan tayi ra'ayi ta dawo idan tana ganin zama a can yafi mata bani da damuwa."


Asp din ya fusata! da fadin." Kana da hankali kuwa Umaru shin ko ka manta waye mahaifin yarinyar ne."?

Murmushin takaici yayi kafin yaja karamin tsaki da fadin." Shiyasa ai farkon magana ta da kai nace ni da hankali da tunani nake tafiyar da al'amura na, mahaifin Zinatu shine Sarkin *KANO* to sai me? bari kaji Asp Allah kadai shine abin tsoro ba wani mahaluki ba, kuma idan ka manta bari na tuna maka dama can ban furta ina sonta ba, bani akayi to akan me zan damu kaina, sai magana ta karshe da za muyi da kai dan naga ka damu da yarinyar nan da yawa baka kaunar damuwarta yanzu ma zan sake maimaita maka cewa zan iya rabuwa da ita ka aura sai kuma me."?

Asp jikinsa ya mutu murus! bakinsa ya mutu ya gaza furta kalma daya hakika ya bashi mamakin da bai taba tunani ba. kawai sai ya kashe wayar ya ajiye a gefe ya shiga tunani akan al'amarin......Tabbas akwai alamun tambaya wannan abun da abokin nasa yake bana masu hankali da tunani bane.


***
Kamar wanda aka daukewa sha'awa haka ya zama surkududu! duk da yana ganin amaryarsa a kusa dashi hakan bai sanya yayi sha'awarta ba, gashi nan dai zuciyarsa a kusa abu kadan yake fusata shi .


Ta shigo dakin ta sameshi a kwance ya tsirawa rufin dakin ido......A sanyaye ta zauna a kusa dashi da fadin." Yaya na."

Ya kalleta tare da kokarin tashi zaune.

Tace."Kayi hakuri kayi bikon matarka domin Uwale da gaske take akan kudirin data dauka. dan naga tana yi min wani irin kallo, yanzu bata sakewa dani.


Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu ruwanki a cikin wannan al'amarin kin gane ko." Shuru tayi tana kallonsa, ya cigaba da cewa." Aiki zai kai ni Zamfara da yardar Allah gobe da asubah zamu d'auki hanya, ki kula sosai gida kuma duk rintsi kada ki bari Uwale tasa kafa ta fita daga gidan nan."

Ta marairaice fuska da fadin." Yaya na tafiya kuma nifa amarya ce zaka tafi ka barni."

Ya tsira mata ido yana kallo, sam abunda take bai burge shi sai ma mugun haushi da ta bashi. tsaki! yaja dogo kafin yace " Tashi kije ki kwanta."
Ganin yanda ya murtuke fuskarsa! babu shiri ta tashi salo-salo ta fita daga dakin. ya koma ya kwanta yana cigaba da tunanin rayuwa.


***
A 'bangaran Zinatu kuwa tunda taji yanda akayi da mijin nata, ta 'kara tsanarsa a cikin ranta, cikinsa ma da take dauke dashi ta dora masa karan tsana tun kafin yazo duniya, dan dai yayi kwari ne amma da duk wuya sai ta zubar dashi ta yar da kwallon mangwaro ta huta da 'kuda.


****
Tafiyarsu Umar din da sati biyu, Asp ya shirya zuwa *KANO* domin tattauna maganar da ta shafi auran abokin nasa, ya kud'urce a ransa cewa kafin abokin nasa ya dawo daga bakin aiki yayi masa kokari gurin ganin matarsa ta dawo dakinta.


Bahaushe yace." Kiwon mutum ake ba dabbah ba, wannan damar Commissioner ya samu ya dinga bibibiyar al'amarin har dai ya fahimci abinda yake da akwai. dama yana bala'in jin haushin kusancin dake tsakaninsu.


A ranar da Asp din ya tafi shi kuma ya samu damar kiran Umar din su gaisa kana sukayi maganganun da ya shafi aikinsu, kafin ya shigo masa da maganar dake bakinsa Asp baya gari yaje Kano ziyara.


Sai ya shiga tunanin abinda ya kai Asp garin Kano bayan bashi da wasu 'yan uwa a can, wani sashe na zuciyarsa yace masa yaje gurin matarka ne.''

Wani irin bakin ciki ya turnukeshi tabbas ko shakka ba yayi abinda ya kai shi garin Kano kanan. wato dai mutumin nan ba zai daina bibibiyar matarsa ba, lallai wannan karon dole ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro!


Saboda haka yana sallama da Commissioner din bai jirayi komai ba ya nemi number Asp din, sai kuma aka samu akasi domin shi Asp din yana ganin kiran yaki dauka saboda jikinsa ya bashi ba alkairi bane.

Ya kirashi ya kai sau biyar bai daga ba.

Ya fusata! ya kira number ta, itama tayi shakulatun 'bangaro dashi yayi-yayi ya gaji tana kallo bata daga ba. takaici yasa ya jefar da wayar ya turmutsa yatsun hannuwansa cikin sumar dake kansa yana hargitsawa, jikinsa in banda karkarwa babu abinda yake.

Sai da yaci abinci tukkuna ya huta sannan Maimartaban ya zauna dashi domin tattauna maganar da ta kawoshi garin.

Da yake dattijo ne mai halin girma bai nuna 'bacin ran akan abinda ya faru ba, sai ma dinga kokarin dora laifin a kan 'yar tasa halin mutanan da kenan ma'ana (kaso naka duniya ta k'i shi) ka qi naka duniya taso shi) Asp din ya bada hakuri sosai ya bukaci a bashi Zinatu din domin tafiya da ita.

Ya jima yana nazarin maganar kafin ya kalleshi da fadin." Da izinin abokinka kake tafe ko kuma dai kaine kake kokarin gyara al'amarin."?

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kwarai kuwa ranka ya dade kafin nazo nan sai da muka tattauna maganar dashi, yace shi bai ce mata tazo gida ba sa'bani kawai suka samu ya dawo gidan ya samu bata nan. dalilin da yasa kuma ba muzo tare ba, yaje *Ran gadi!* garin Zamfara na san kana da labarin irin tashin hankali da yake faruwa a garin."


Yace." Tabbas muna da labarin irin rikicin da yake faruwa a garin, muna kuma rokon Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya.

Ya amsa da "Ameen ya Allah insha Allahu komai zai-dai ta za'a samu tsaro da kwanciyar hankali mutukar an hadu da shuwagabbani nagari."

Yace." Wannan haka yake, samun shuwagabbani nagari a wannan zamanin yana wahala dole muma mu dage da addua mu kuma gujewa abinda Allah baya so sai mu zauna lafiya.''

Asp ya risina cikin girmamawa yace ." Allah ya taimake ka kayi magana mai ma'ana yawancin zagin shuwagabbanin da muke shine babbar matsala a gare mu, addua ya kamata muyi musu domin Allah ya basu ikon aikata abinda ya dace to kaga dole mu kiyaye harshen mu mutukar muna so mu zauna lafiya a k'asa."

To tsakanin Asp da Sarki Umaru sun tattauna maganganu masu muhimmanci wanda sai mai hankali da tsinkaye ne zai fahimci inda suka dosa.


Da farko bijirewa tayi da taji maganar ita kam duk abinda za'ayi ba zata koma ba ta gama auran har abadah.

Babu wanda bai shiga dakin ya rarrasheta ba amma fafur! taki karshe ma sai kawai ta kwanta tana kuka ita ta gaji da wannan al'amari wane irin aure ne wannan mara 'yanci.


Da yake akwai kauna mai tsanani a tsakaninta da mahaifinta, koda ya shiga dakin rungumeshi tayi tana kuka tace." Ni ba zan koma ba nafi bukatar rabuwa da auran saboda babu kwanciyar hankali a cikinsa, tun farko sai da nayi tunanin hakan zata faru amma babu wanda ya fahimce ni sai yanzu gashi abubuwa marasa dadi suna biyo baya ina ganin ko na koma babu abunda zai sauya.

Jikinsa ne ya mutu a hankali ya zauna tare da zaunar da ita a kusa dashi, cikin laluma ya fara kwantar mata da hankali, shi kansa baya san ta koma a yanzu yafi bukatarta a gabansa saboda yana tausayawa halin da take ciki, hakika yaron ya bashi mamaki mutuka!


Ya rarrasheta sosai tare da sake bata umarni a karo na biyu, ya kuma tabbatar mata da cewa shine na karshe wata matsalar ta sake faruwa a tsakaninta da mijinta to ba zai mata dole ba amma dai a yanzu tayi masa alfarma ta koma dakinta.


Mahaifinta yafi karfin alfarma a gurinta, tabbas idan ta bijirewa bukatarsa ba zata ga da kyau ba, dole ta sanya hakuri da dangana a zuciyarta, amma a can kasan zuciyarta ita kadai tasan abinda damunta.



Albarka da addua da fatan alkari iyayenta sukayi mata insha Allahu kuma adduarsu ba zata fad'i a kasa ba.


****
Koda suka isa gidan Uwale kasa 'boye farin cikinta tayi ita kuwa Hamra'u kamar wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa! tayi kicin-kicin! idonta jawur kamar me shirin fashewa da kuka!


Uwale ta kalli Asp da fadin." Hakika samun irinka a wannan zamanin sai an tsananta binkice! kai ba za'a kira ka da aboki ba domin ka wuce haka! kana tsaye akan Umaru da al'amuransa Allah ya saka maka da alkairi ya biya ka da aljanna madawwamiya.

Ya amsa da "Ameen ya rabbi ai ba wani abu bane Uwale ban dauki Umar a matsayin aboki ba kamar yanda ki ka fada dan uwana ne! wannan dalilin yasa hankalina ya tashi ganin yanda abubuwa marasa kyau suke faruwa dashi. tabbas akwai abinda yake lullu'be kuma muna rokon Allah yayi mana maganin ko menene.

Tace." Insha Allahu kuwa Ai babu abunda yafi karfin Ubangiji kai dai Allah ya saka maka da alkairi."

Ya amsa da "Ameen kafin yayi musu sallama ya tafi muhallinsa.


Hamra'u tayi zaune a daki tana sakawa da kwancewa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dauki wayarta number sa ta kira.


Sai da ta kira sau uku ana hud'un ya daga! kafin ma tayi magana ya buga mata tsawa! dama zuciyar a kusa take ana fagen daga!!

Jikinta ya shiga rawa! sai ta manta ma abinda za ta fad'a

Yace." Wai shin ke ban ha naki kira na bane? da kaina nace ki bari idan na samu isheshshen lokaci zan kira ki me yake damunki ne."?

Hawaye masu zafi suka cika kwarmin idonta! kamar ta kashe wayar sai dai ta daure murya na rawa tace ." Dama zan fada maka cewa Zinatu t.........! jin ta ambaci sunan wacce ya tsana! yasa da gaggawa ya kashe wayarsa ba zai saurari karshen maganar ba ballantana ransa ya 'baci!






*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/23/22, 21:09 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




*119&120*
Kasa daurewa tayi ba'kin cikin abinda yayi mata yasa ta kasa fita falon, nan ta kwanta kan gado kuka mai cin rai ya k'wace mata, ita kam har yanzu ta kasa fahimtar inda ya dosa kullum babu kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu, ba dama tayi masa magana sai ya kyareta! ko ya hantareta! gabad'aya ta kasa shawo kansa a lokacin da ba suyi aure ba ma yafi kulawa da ita, yanzu kuwa da ya cancanta ace ya kula da ita hakan bai samu ba, wannan al'amarin yana bala'in damunta.

Haka ta zama mujiya a cikinsu, dan gabad'aya sai ta tsargi kanta ta dinga ja da baya tana wani abu irin abu na marasa gaskiya, Uwale kam tunda ta fahimci cewa ita da uwarta basu da gaskiya sai kawai itama ta shata mata layi, ta daina sakar mata fuska a yanzu babu kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu.
Tafi mayar da hankalinta kan Zinatu saboda tana tausayawa halin da take ciki, tunda ta dawo take fama yau da lafiya gobe babu sai ya kasance kusan kullum Uwalen tana can sashen nata domin debe mata kewa duk da cewa tana tare dasu Baraka amma kasancewar Uwalen a tare da ita ya faranta mata rai mutuka. sha'kuwa mai kyau ta shiga tsakaninsu.

'Bangaran Hamra'u kuwa abin duniya ya isheta, kullum sai ta zubar da hawayen takaici gidan kaf sun hade mata kai sun mayar da ita saniyar ware babu wanda yake yi da ita, sai ta fara rama a tsaitsaye saboda damuwar da ta sanya a ranta dole itama tabi ayari mutukar tana so tayi rayuwar farin ciki a gidan.

Sai ta dingi shiga sashen Gimbiyar, al'amarin da ya basu mamaki mutuka! amma basu nuna mata komai ba, tun bata sakewa dasu

Please Login or Register in order to submit comment