Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai cikin walwala da farin ciki.



Yau dai shiri na mussaman yayi kafin ya tunkari inda take sai da yayi wanka da turaruka bakinsa sai kamshi yake fitarwa shigar da yayi ma ta mussaman ce, domin wasu kayan bacci yasa masu kyau da daukar hankali.


Tana kwance kan gado abun duniya ya isheta kwana biyu ta kasa gane kanta, komai na duniya yayi mata zafi ta rasa yanda za tayi da rayuwarta.............Yawan tashin zuciyar da take yana damunta.


Shigowarsa dakin yasa da sauri ta juyar da kanta, sam bata san Kallon fuskarsa.


Cikin bargon da take ciki ya shiga yana lumshe mata ido, kokarin janyota yake tayi sauri tashi tana yamutse fuskarta........Yawu ne ya taru a bakinta ta sauka daga gadon toilet ta nufa ta zubar da yawun ta dawo.


Abun ya bashi haushi mutuka! ya rufeta da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.


Hannu ta daga masa da fadin." Don Allah ka kyaleni haka, ni wallahi gabadaya yanzu bana san damuwa, kai kuma na lura duk sanda ka shigo dakin nan sai ka 'bata min rai! kawai ka daina shigo min daki."


Ya mike zaune yana mata wani irin kallo kafin yace." Iskancin banza da wofi! meye abun k'yama a jikina da har kike tara yawu! na dauka yau kwana takwas rabon da ki bani hakkina na aure ina ruwanki da tsarin rayuwata maciji ni naci abina mai zai dameki kuma."


Tace." Ni fa ba maganar maciji nake maka ba, kai din ne kawai bana son gani." da gaskiyarta take maganar.


Takaici da bacin rai sukayi masa katutu! ya daina jin tausayinta kuma duk abunda za tayi sai ya biya bukatarsa.


A daran bai saurara mata ba ya turmusheta ya zage dukkakin karfinsa a kanta, ya galabaitar da ita sosai domin dama yakan dade kafin ya kawo haka hallitarsa take da nisa.

Aikuwa da ciwo ta tashi dan rasa gane kanta yayi.....babu shiri ya kira likiti domin ya duba masa ita.

Kallon farko likitan ya gane abunda ke da akwai amma bai tabbatar ba sai da ya auna fitsarinta.....nan ya tabbatar da zarginsa, ciki ne sati bakwai da kwanaki.

Sai ya rasa ina zai sanya ransa yaji dadi, kawai ya shiga godewa likitan kamar shi yayi masa kyautar cikin, kudi ya fito dasu daga aljihu ya bawa likitan yana godiya.


A ranar sai bayan azuhur yaje gurin aiki, yana tare da ita yana rarrashinta da kalamai na so da k'auna, ita dai jinsa kawai take tana mamakin al'amarin, dama jikinta sai da ya b'ata cewa hakan na iya faruwa aikuwa gashi hakan ta kasance.....ita kam bata shirya haihuwa yanzu ba, tunda beyi k'wari ba tasan yanda za tayi ta zubar dashi.


Koda ya dawo daga gurin aiki sashenta ya nufa domin dubata, ya same ta fes da ita domin duk jin jikin da take bata fasa ado da kwalliya ba hakan kamar ya zame mata jiki.


Ya zauna kusa da ita yana nanikar jikinta, shi yana bala'in san kamshin ta ita kuma tana gudunsa, ba komai ne ya janyo hakan ba, sai d'an tayin cikin dake kwance a kasan mararta.

Be damu da yanda take kauce-kauce ba, ya dinga sumbatar fuskarta yana ta so ya hada bakinsa da nata tana kaucewa.......da kyar ya samu nasara! tunda ya kama harshen be saki ba sai da ya gamsu tukkuna.

Idonta ya ciko da ruwan hawaye harara kawai take zabga masa ta rasa wane irin mara zuciya ne shi.


Ido jawur! yace." Ya jikin ina fatan kin wuni lafiya tare da babyna."

Shuru tai masa tana dauke kanta.

Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da kallon agogon dake daure a hannunsa, magariba ta gabato, tsaye ya mike ya dan kalleta tana ta yamutse - yamutse! huci ya fesar! kafin ya kama hanyar fita, tabi shi da kallo tana zum'bura bakinta.


Kasa daurewa yayi ya bar maganar a ransa a daran ya shedawa Uwale, farin ciki kamar ya kasheta, tace." Lallai kace da kwarin gwiwarmu za mu shiga k'auyen *K'afur!* ai wannan abun alkairi ne da ya kamata ace yan uwa sun sani.

Murmushi kawai yayi da fadin." Saura kwana nawa bikin ne."?

Tace." Ashe baka lissafi ai yau saura kwana uku mu tafi dan duk wasu shirye-shirye mun kammala."

Yace." To Allah ya kaimu amma ni ina tsammanin a ranar zan dawo bayan an daura aure.''

Tace." To babu damuwa amma ita matar taka sai ka bar ta tare damu domin 'yan uwa su kara sanin ta."

Yace." Shikkenan haka za'ayi insha Allah."

Sallama sukayi da juna kai tsaye da ya fito sashen Gimbiyar ya nufa cike da farin cikin kasantuwa da ita.





*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/8/22, 18:59 - Binta: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




*97&98*
Wani irin bacci sukayi mara dad'i sakamakon damuwar da suke ciki. da yake namiji ne shi yakan iya danne damuwarsa ita kam ta kasa dannewa domin gabadaya jin kanta take a takure! ita akan kin kanta tasan yun'kurin da tayi ba mai kyau ba ne, shiyasa take bala'in jin kunyar hada id'o dashi!

Kwance ya sameta saman gado tun bayan sallar asubahi ta kwanta tana k'okarin gayyatar bacci yaki zuwa babu shi ma gabad'aya a idonta tunani yafi yawa a tare da ita.

Ido ta tsira masa har ya k'araso bakin gadon, ya shirya tsaf da niyyar fita gurin aiki.

Babu yabo babu fallasa ya kalleta da fadin." kin tashi lafiya."?

A hankali ta amsa tana dan lumshe idonta.

Kallonta yake yana ayyana abubuwa da yawa a kanta, yanayin ta ya nuna kamar mara lafiya.

Ya daure zuciyarsa yace." Ko kina da damuwa ne."?

Zuciyarta ta karye hawaye naso ya zubo tana mayar dashi bata bukatar tayi masa kuka tunda yana kiranta da shagwababbiya.


Shuru tayi ba tace masa komai ba. sai da ya sake maimata maganar sannan tace." Lafiya na kalau."

Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin" Okey haka nake so ni zan fita amma idan kinji wani guri nai miki ciwo ki kira ni a waya."


Ta kalleshi k'auna da sonsa na kara nunkuwa a zuciyarta, a jiyar zuciya ta sauke a hankali tace " To."

Ya kama hanyar fita jikinsa duk babu dadi, yarinyar ta tsaye masa a rai.

"Haka zaka fita ba kayi breakfast ba."?

Maganarta ta katse masa hanzari. juyowa yayi yana kallonta.

Ta sunkuyar da kanta domin bata jurewa kallon kwayar idonsa.

" Kada ki damu zan samu abunda zan ci buri na ki tashi ki nemi abinci kici ko dan abunda ke cikin ki idan kinyi min haka kin gama min komai."

Ta yun'kura ta tashi tana d'an ya mutse fuskarta.

Saurin kawar da kansa yayi sakamakon ganin zahirinta kayan bacci ne a jikinta wanda suka fitar da wasu sassan na jikinta.

Yay gaggawar bude kofar dakin ya fita yana jin yanda jarumarsa ke motsi har ta fara yun'kuri! al'amarin ya bashi mamaki mutuka! koda yake ba'a abun mamaki bane idan anyi la'akari da kwanakin da ya dauka rabon da ya hada shinfida da ita.


Yana zama a ofis kiran wayar Maimartabar ya same shi.

Suka gaisa cikin mutunci da dattako.

Maimartaban yake sheda masa cewa suna da baki da misali sha biyu jirginsu zai sauka anan filin jirgi na Katsinan.

Farin ciki yayi sosai ya dinga godiya tare da adduar Allah ya saukesu lafiya.

Sukayi sallama cikin girmama juna.


Cike da farin ciki ya kira wayar ta.

Fitowarta daga wanka kenan tayi saurin dauka tare da zama gefan gado.

Ya sheda mata abunda yake faruwa.

Jikinta a sanyaye tace." Me yasa ka sheda musu abunda yake tsakanimu.''? murya na rawa take maganar


Yayi shuru yana nazarin maganarta.

Tace." Shikkenan na shiga uku ka janyo min bacin ran iyaye na."

Ya kwantar da murya da fadin." Ni fa ban fada musu maganar da wata manufa ba, na fada musu ne domin su ta ya ni neman mafita, amma bana fatan ranar da zan shiga tsakaninki da iyayenki."


Ta share hawayen saman fuskarta kawai ta kashe wayar saboda kukan da yake kokarin kufce mata.


Sake kiran wayar yayi tana kallo tana ringing taki dauka, ita yanzu tashin hankalinta zuwan Mahaifiyarta tasan bacin rai ne zai biyo ba.


Babu kuzari a tare da ita ta kimtsa jikinta, ta nemi kujera ta zauna tana duba agogo sha biyu ta gota tasan yanzu mybe sun sauka .


Wayarta ta d'auka cike da fargaba ta kira mahaifiyarta.

Murya na rawa tace."Mommy ina wuni."?.

A dakile ta amsa gaisuwar.

Ta daure tace." Kun sauka ne."?

Gimbiyar tace." Eh sun sauka dan yanzu suka kira waya, babu ni 'Yar uwata ce sai yayyunki."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta tasan SAFAH tana da sanyi rai ba kamar mahaifiyarta ba.


Ta katse tunaninta da fadin.'' Kin kyauta abunda ki kayi ZINA kin janyo min zagi da cin mutunci na gode." Ba ta jira amsarta ba, kawai ta kashe wayarta.

Ita kam shuru tayi da waya a hannunta gabadaya ta rasa ya za tayi da rayuwarta.



SAFAH tare da Hassana da Hussaina da Magajin sarki suka sauka a gidan......Farin cikin ganinsu yasa ta fashe da kuka! ta dinga rungumesu duk ta rasa yanda za tayi saboda jin dadin ganinsu.

Magajin Sarki yace." Ki samu nutsuwa haka zuwan mu gidanki baya nufin farin cikin ki. akwai babban dalili ne ya kawo mu gidanki."

Ta nemi kan kujera ta zauna jikinta duk a sa'bule.


Ya fara yi mata fad'a tare da kawo mata ayoyin al'kur'ani da hadisai duk dai akan abunda ta aikata mara kyau!

Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, dukkaninsu kowa ya tofa albarkacin bakinsa mussaman SAFAH da ta dinga yi mata nasiha mai ratsa jiki anan ne ta zubar da hawaye, tana kukan tace." Mammah dan Allah ku gafarce ni wallahi tsautsayi ne da son zuciya insha Allah ba zan sake maimaita abu mai muni irin wannan ba.


Hassana tace." To Alhamdulillhi haka muke so muna rokon Allah ya sauke ki lafiya ya kuma inganta duk abunda zaki haifa."


Gabadaya suka amsa da "Ameen." Kafin su fara yun'kurin tafiya.

Tace." Mammah har zaku tafi ni wallahi na dauka kwana za kuyi."


Magajin Sarki ya harareta da fadin." Sai kace mahaukata ko."?

Ta 'bata rai da fadin." Aunty Hassana don Allah ku zauna ku kwana mana."


Hussaina tace." Baki da hankali ZINA daga zuwa sai mu kwana ke a ganinki hakan yayi dai-dai"?

Tace." To meye wallahi babu matsala kuna gani dai kowa da gurinsa to me zai dame ku."


SAFAH ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta da murmushi a fuskarta tace." Zinatu rigima kin ga tashi kiyi mana Jagora cikin gidan mu gaisa dasu. ke kanki kin san abinda kike bukata ba mai yuwu wa bane.

Cike da rashin dadi ta tashi ta shiga daki domin dauko mayafi, nan Aunty Hussana ta bita dakin ta bata wata leda dake cike da turarukan wuta da humra masu kamshin gaske, sai kuma kaninfari da yawa cikin wata leda a d'aure, tace mata ta jika cikin wani abu tana shan ruwan.

Godiya sosai tayi mata kafin su fito daga dakin a tare.

Uwale tsohuwa mai dattako! ta kar'be su hannu biyu tana ina a saka ina a sauke dasu.......Da yake basa rabo da abinci ta sanya Hamra'u ta had'a musu abinci wanda zai gamsar dasu.

Haka nan suka saki jikinsu suka ci abinci wanda Hamra'u ta sarrafa sosai Allah yai mata baiwar iya sarrafa abinci ko wane iri ne a zahiri suma sun yaba sosai kuma ci sun gamsu.


Itama ZINAT din taji dadin yanda aka karramasu ta saki jikinta tamkar akwai sabo a tsakaninsu, har tana jan Hamra'un da hira, wanda hakan ya basu mamaki mutuka, to itama dai Hamra'un saki tayi kamar wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba.



Tafiyarsu keda wuya ya kira wayarta yana tambayarta.

Tace." Ai har sun tafi."

Cike da mamaki yace." Sun tafi."?

Tace."Eh nima wallahi babu yanda banyi dasu ba su kwana amma sun tafi kamar ana korarsu."


Ya girgiza kai da rashin jin dadin hakan, yace." Me yasa da zasu tafi baki kira ni kin sheda min ba, sai na bar duk abunda nake nazo mu gaisa."

Tayi shuru domin ba tasan me za tace ba.


Yace." Laifin duk naki ne Zina kwata-kwata banji dadin tafiyarsu ba naso mun gaisa da juna sosai."


Tace." Kayi hakuri amma ai sun gaisa da Uwale har suka ci abinci a gurinta.

Yace." Hakan ma yayi amma Uwale daban ni daban."

Tace." Hakane kuma." Shuru ya ratsa tsakaninsu kafin tace." Daddare me kake bukatar ci."?

Kai tsaye yace." Towon dawa da miyar kuka."
Iya gaskiyar sa ya fadi maganar.

Amma sai ta kyalkyale da dariya da fadin." Towon dawa! gaskiya ni ban iya ba."

Yace." Aikuwa ki koya domin shine favorite d'ina mussaman dumame towo ko wane iri ne ina sonsa.

Tace." To shikkenan kada ka damu yau ma da kaina zan maka abincin insha Allah."

Yace."Okey da can bake kike ba kenan."?

Da sauri ta gyara maganarta tace." Ni ce mana ina nufin yau na mussaman zanyi maka towon da kake so.

Yace." Idan da akwai matsala ki zauna ki huta kin san baki da koshin lafiya."

Murmushi tayi da fadin." Naji sauki ai ina bukatar samun ladan aure."


Murmushi jin dadi yayi yana juyi kan kujerarsa yace." Shikkenan yau da daddare za muyi hira kenan."

Tana 'yar dariya tace." Sosai irin wacce ba mu ta'ba yin irinta ba."


Yace." Alhamdulillhi na gode Allah da ya bani ke a matsayin matata."


Tace." Nima haka amma dai ka yafe min laifi na ko."?

Ya gyara zamansa da fadin.'' Na yafe miki kuma da ikon Allah zan d'aga miki ki shiga aljanna Bakya laifi a guri na GIMBIYATA."

Tace." Na gode *Mazan Fama!* Allah ya barmu tare." ya amsa da "Ameen wani irin farin ciki na ziyartarsa.


Aikuwa kamar yanda tayi masa alkawari, da kanta ta shiga kicin din, ta sanya Marakisiyya ta harhad'a mata komai wanda zata bukata, yau abunda bata ta'ba yi ba zata kwatanta.

Ita kad'ai a kicin din tana gwagwarmaya! duk ta jigata, sai gumi take abunka da wanda bai saba ba.

Akayi rud'e kalau! aka rufe ruf! sannan aka shiga had'a miya, tayi dubarar silala naman da albasa da kayan 'kamshi amma bai wani dahu sosai ba, ta zuba su daddawa da kayan miyan data murza a gireta, ta zuba uban farin mai tamkar me shirin yin jar miya.........Can rud'en dake rufe ya fara za'bal'bala kafin kice me murfin tukunyar yayo sama talgen ya fara kumfa yana zuba saman gas din, da sauri take k'okarin cire murfin aikuwa ta 'kone a hannu!! baya ta matsa tana ihu!! taje ta kwance famfo tana wanke talgen daya kona ta. kuka ne kawai ba tayi ba fatar hannunta tayi jajawur! ido jawur! ta fita daga kicin.

Ta zauna kan kujera tana mayar da numfashi..........A'a abu kamar wasa hannu ya fara tashi! ga wani irin zafi da yake mata......kira ta kwalawa Marakisiyya tace mata maza taje ta k'arasa ita tayi abunda zata iya.

Tashi tayi ta shiga d'aki ta kwanta, tana jinyar hannunta.



Daf da zai shigo gidan ya kira wayarta, ta daga su gaisa yana tambayarta jikinta, tace." Lafiya amma garin yi maka towo na k'ona hannu.


Yace." Subahanallahi garin ya hakan ya faru."?


A shagwabe tace." Talgen ne ya dinga zuba naje bude tukunya ya zubo min a hannu."


Yaji duk wani iri a jikinsa yace." Sannu my love amma ba sosai bane ko."?


Tace."Eh ba sosai ba amma har ya tashi sai ciwo yake min."


Yace." Yi hakuri kinji bari yanzu zanzo nai miki addua insha zaki ji sauki."

A sanyaye tace." Okey my darling na gode sai ka shigo." kashe wayar yayi yana Allah-Allah ya isa gidan.


Wanka tayi ta kimtsa domin bata so ya shigo ya sameta babu ado, tunda tasan yana san haka shiyasa ta mayar da hankali gurin yi masa ado da kwalliya na kece raini.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/9/22, 22:27 - Binta: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




*99&100*
Wani sanyi ne ya ziyarceshi yayin da yayi tozali da ita a hakimce tayi ado irin wanda yake bala'in burgeshi, in ban da kamshi babu abunda take........Gabadaya wata irin kasala ta rufeshi tsananin sha'awarta ya sake kamashi, shi dai yana bala'in son kamshin jikinta.

Kusa da ita ya zauna ya jifanta da wani irin kallo, ta marairace fuska tana kallonsa kafin tayi masa barka da zuwa.

Ya dubi hannun da ya kone! tsigar jikinsa ta tashi, a hankali ya rike hannun ya fara tofa mata addua ya gama ya kalleta cike da kulawa yace." Ke zanyi wa sannu duba da irin tsautsayin da kika samu ta dalili na, tunda kika sheda min hankalina ya tashi ina Allah-Allah na iso gida naga halin da kike ciki, amma abun mamaki sai na sameki cikin koshin lafiya kinyi ado da kwalliya irin wanda nakeso ina mai tabbatar miki da cewar ina alfaharin kasancerki a matsayin matata."

Murmushi tayi tare da jin dadin kalamansa, dama kuma babban burinta bai wuce ace ta siye zuciyarsa kaf ya daina ganin ko wace mace a gabansa ba sai ita, ta lura yana da sau'kin kai! kuma ta fahimci ya kamu da tsananin sonta wannan abin alfahari ne a gurinta.

*****
Da safe kafin ya fita gurin aiki yake sheda mata tafiyar da za suyi, sam ba tayi tunanin cewa har da ita za'ayi tafiyar ba, sai da taji yana fadin." Za ku kwana biyu a k'auyen domin kisan 'yan uwana suma su sheda ki sosa.''

Sai ta kasa 'boye bacin ranta! ta dan 'bata fuska tana kallonsa.

Ya fuskanci ba tayi na'am da tafiyar ba, ransa bai masa dadi ba.

Ganin taki yin magana ya sanya ya tashi da niyyar fita.

Ta kalleshi a lokacin da yake gyara f-cap din kansa. da kyar tace." Sai ka dawo."

A dakile ya amsa ya kama hanyar fita zuciyarsa duk babu dadi, sam bai ji dadin abinda tai masa ba, ya lura har yanzu ba ta k'aunar a halinsa, a ganinsa duk soyayyar da take nuna masa a banza take, mutukar ba zata kaunaci yan uwansa ba.


Ya saba kiran wayarta idan ya samu saukin aiki amma a ranar sai ya share ta yana so ya nuna mata kuskuranta


B'angaranta kuwa ba wai zuwa 'kauyen ne ba taso ba,cewar da yayi zata zauna tare dasu har na tsayin wasu kwanaki shine abinda ya 'bata mata rai! gaskiya bata tunanin kwana a kauyen 'kafarta-'kafarsa.


Da taji shuru bai kira ta ba, sai ta kira shi, ya daga yana shan k'amshi.

Murmushi tayi kafin tace." Fushi kake ko darling."

Gyaran murya kafin yace." Fushi akan me? a halinki ai ba sabo bane a gurina."


A shagwabe tace." Au! mugun hali ne dani."?

Yayi shuru bai ce mata komai ba.

Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye tace." Kayi hakuri ba wai bana so naje bane naji kayi maganar kwanaki shine bana so."


Ya fusata! yace." Kin ga idan ma ba zakije ba kiyi zamanki okey." Kawai ya kashe wayarsa.

Ta dinga bin wayar da kallon mamaki! ita fa yanzu kwata-kwata bata bukatar abunda zai shiga tsakaninsu, amma ta fahimci akan 'yan uwansa zai iya cin mutuncin kowa.


A'a! abu kamar wasa 'karamar magana na nema ta zama babba! fushi yake da ita sosai! dan koda ya dawo daga gurin aikin bai shiga gurinta ba, ya gama duk abunda yake ya nufi sashensu Uwale, zuciyarsa duk babu dadi.



Koda taji shuru bai shigo ba, sai ta yanke shawarar zuwa gurinsa, tunda zuwa yanzu ta san ya dawo, ita sam ba taga abun fushi da 'bacin rai ba, bata gudin 'yan uwansa. halinsu ne kawai abun gudu.


Koda ta shiga gurin nasa, Babu shi babu dalilinsa. amma akwai alamun ya dawo yayi wanka sannan ga 'karamar wayarsa nan a saman drowar.


Kai tsaye gurinsu Uwale ta nufa domin tana da tabbacin yana can.

Abunda taci karo dashi ya kusa tarwatsa mata zuciya, amma sai ta jajurce! tayi kokarin danne mugun kishin da yake taso mata.. tayi musu sallama.

Su biyu ne a falon, Uwale na daki domin gabatar da sallar magariba, shima dawowarsa kenan daga massalancin, ya samu Hamra'un ta shirya masa lafiyayyan towon farar shinkafa da miyar kubewa d'anya wacce taji bushashshen kifi da man shanu!


Ya dinga shi mata albarka domin yini cur bai ci abinci ba, tun breakfast din safe, b'acin ran da ya fita dashi ya ha nashi cin wani abu.

Tana zaune durshan a gabansa bayan ta zuba masa abincin yana ci tana bashi labarai sai dariya yake sai kace mata da miji.


A zabure! ta kalli bakin kofar! suka had'a ido, bahaushe yace (Mara gaskiya ko a ruwa gumi yake) duk sai ta daburce! tayi gaggawar matsawa daga kusa dashi, shi kam ko gezau! abincinsa kawai yake ci amma ya amsa sallamar bai dai kalleta ba.


Ta zauna kujarar dake kallonsa da fadin.'' Ranka ya dade ashe ka dawo."?


Ya dago kansa yana kallonta da mamakin sunansa da ta kira shi, sam bai mayi tunanin za tayi masa magana ba, saboda ya san azabar kishinta.


Da yake Namijin duniya ne babu kunya yace." Eh na dawo kina raina yanzu nake maganarki a zuciyata."


Taji kamar ta fada masa bakar magana! amma sai tayi shuru kawai tana masa wani irin kallo na tuhuma!


Saurin sunkuyar da kansa yayi! duk dadin towon a bakinsa yaji ya fice masa daga rai!

Hamra'u kam! simi-simi ta kama hanyar d'akinta! tana ta wani kumbura fuska shigowar Gimbiyar ya 'bata mata rai mutu'ka! domin ta katse mata jin dad'inta.


Ya kalleta da fadin." Ya zaki tafi baku gaisa ba.


Ya'ke tayi ta juya da fadin." Aunty Gimbiya ina wuni."?


Tace." Lafiya lou ina Uwale."? Kafin ma ta bata amsa Uwalen ta fito da carbi a hannunta, ganin Gimbiyar yasa ta washe bakinta, sosai tayi farin cikin ganinta a zaune babban burin ta ace Gimbiyar ta saki jikinta dasu.

Hamra'u kasa tsayuwa tayi a gurin da sauri ta shige dakinta, ranta idan yayi dubu ya ba'ci, ita dai tana kishin yanda Uwale ke nuna kauna da kulawa akan Gimbiyar.


Cikin mutuncin da girmamawa suka gaisa da juna.

Ta kalleta da fadin." Ya jikin naki jiya Ai yake fada min kin 'kone a hannu har nake cewa zan shiga na dubaki Allah

Please Login or Register in order to submit comment