Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon so da k'auna tare da ayyana abubuwa masu kyau a tare dashi......Yanda ta daukeshi ba haka yake ba yana da kyawun zuciya.


Sosai yayi mata adduar shiriya da fatan dorewar zaman lafiyarsu, yanda yake jin ta a cikin ransa yana ganin zai iya kare rayuwarsa tare da ita kad'ai mutukar zata cigaba da kyautata masa tare da bin iyakokin da Allah ya ajiye.


Sai da ya gabatar da isha'i tukkuna ya koma gidan.


Gurin su Uwale ya nufa domin baya tsammanin idan ya shiga sashensa zai sake fitowa yafi bukatar ya zauna tare da gimbiyar tasa yana kallon ado da kwalliyar ta.


Wai akace kowacce mace da irin kissa da kisisinar ta, duk yanda Hamra'u tayi domin ta janye hankalinsa abun ya gagara! domin dai gabadaya kaf hankalinsa da tunaninsa na kan matarsa magana yake amma tunaninsa na gurin ta.


Tayi- tayi! ta buga dashi kan yaci abinci fafur! ya'ki, jikinta yayi mugun sanyi dan ba tayi tsammanin faruwar hakan ba, domin tunaninta yana nuna mata cewar sulhu da Gimbiyar ta nema ya samo asali ne ta dalilin jajurcewarsa ashe hasashe kawai take ba haka abun yake ba......Kuka ne kawai ba tayi ba don ganin ha'kanta bai cimma ruwa ba.
Yayi musu sallama ya tafi babu wani 'kulli a zuciyarsa........Ita kam kasa daurewa tayi ta shiga dakinta taci kuka ta koshi! gaskiya ta gaji da wannan game din dole tasan matsayinta ta gaji da zama ba tare da ta san meye makomarta..........To itama dai Uwale tunanin da take kenan tana so idan Allah ya kai su 'Kauyen *Kafur!* su samu zama da iyayen yarinyar domin su tsayar da magana.


Duk da abincin bai masa yanda yake so ba, haka nan ya daure yaci domin ya 'karfafa mata gwiwa domin duk a tunaninsa itace tayi, tissue yake kokarin yaga, ta rigashi ba jira komai ba ta fara goge masa baki, fuskarsa a sake yace." Ashe amaryar tawa gwana ce a kowane bangare."

Murmushi kawai tayi ta gyara zamanta kan kujera kamar gaske tace." Na iya girki ko."?

Yace." Sosai kuwa! yayi dadi amma ko dan gaba ki kiyaye bana san yaji sosai a abinci."


Tace." To zan kiyaye insha Allah."

Shuru gurin ya dauka na 'yan mintina kafin ya kalleta da fadin." Kwana nawa abun yake kafin ya tafi."?


Ta kalleshi da nazarin maganarsa sam bata gane abinda yake nufi ba.


Yace." Ina nufin wannan abun da yayi min karan tsaye ya hana ni amsar hakkina a jiya."

A take ta gane hausar..........Sai kawai ta shagwa'be fuska tana jujjuyawa kwayar idonta a kansa tace." A 'kalla yana kwana goma ko sati biyu kafin ya d'auke."


Ya d'an harareta da fadin." Ban yarda ba 'karya ne! duk da ban san ya abun yake ba, amma a hasashen da nake kwana uku zuwa shida idan yayi nisa yayi sati, idan ya wuce haka to ya zama lalura."


Tayi shuru kawai tana kallonsa...........Yace." Kin san me."? kai ta girgiza.

Yace." Banyi tsammanin cewa zamu daidaita tsakaninmu da wuri ba, koda yake shi *SO!* Ya wuce wasa domin duk yanda kake tsammaninsa ya wuce nan."!


'Yar dariya tayi kafin tace." Hakane kam!!

Yace." Ban yarda da ba ina so yau da bakin ki kice dani Ilove you."!

Cikin wani irin yanayi take kallonsa kafin tace." A'a ni dai sai ka fara fadi tukkuna."

Yace." Jiya bana fad'a miki ba."
Yana nufin lokacin da suke romancing bai manta yanda ya dinga nanata Ilove you ba adadi ba.

Tace." Ai wannan da dalili, na yanzu kuwa kana hayyacin ka, sai nafi gamsuwa."


Rikitattun idanuwansa ya zuba mata gabadaya jikinta ya mutu, tabbas a cikin kwayar idonsa akwai wani sirri wanda yake saurin ladabar da mace.


Cikin wata murya ta mussaman yace." Ilove you *ZINA* i really love you *GIMBIYATA!* Na baki kaina duka habibty."!

Wani irin hali ta shiga mai wuyar fassaruwa, gabadaya ta rasa yanda za tayi da shau'ki! ta dago kanta tana kallonsa da gajiyayyun idanuwanta da so ya gamai musu illah tace." Nima ina *SONKA!* ina da burin kasancewa da kai har karshen numfashina, amma ina rokon abu daya a gurinka."

Ya d'an had'iye yawun bakinsa da fadin." Ki fada min komeye baki da matsala dani."

Kai tsaye tace." Bana so kai min kishiya."

Yaji maganar kamar saukar aradu a kansa.........Ido ya zuba mata da so ya gazgata maganarta, tabbas har cikin zuciyarta ta fadi maganar.
Baya tsammanin zai mata alkawari domin rayuwar ba a hannunsa take ba, kawai sai yace." Idan kin cika cif kuma kin cike duk wani gurbi da nake da muradi to ki sanya a ranki cewa ni naki ne ke kad'ai, dan haka kiyi kokarin ganin cika cif-cif kamar yanda nake bukata."


Ganin tayi shuru tana kallonsa yasa yayi saurin jan kujerar da yake zaune......Kai tsaye gurinta ya nufa ya mikar da ita tsaye, suka kurawa juna ido, fuskarta ya tallafo cikin tafin hannuwansa kafin ya sanya bakinsa saman goshinta, ta rintse ido ta na jin wani bakon yanayi na ziyartar gangar jikinta......Jiki a mace ta kwanta a jikinsa ya rungumeta tsam-tsam! a haka suka nufi dakin mak'ale da juna.


Romancing din da sukayi yau yafi na jiya domin sun raya daran da wata iriyar soyayya ta mussaman gabadaya ficewa sukayi daga hayaccinsu, mussaman shi da yake kasa sarrafa kansa mutukar yana tare da ita.


Wai akace kowa dai da irin zuciyarsa..............Da sassafe ta tashi cikin k'warewa da iyawa ta kammala komai, tayi wanka tayi ado sosai duk da zuciyarta a 'kuntace take amma ba tayi zuciya ba, ta shirya komai cikin kwando mai madaidaicin girma, kai tsaye sashen ta nufa da abincin.


Dai-dai lokacin da suka fito daga wanka a tare, Hamra'u ta fara knocking.

Ta kalleshi da fadin." Mybe Hamra'u ce ka bude mata kofar kawai."

Kallon mamaki yake mata......Tayi murmushi da fadin." Kada ka damu da hakan, ni na umarce ta kan cewa ta cigaba da aikinta, mussaman da safe tunda naga tana da himma! akan ka fita ba tare da kaci komai ba yasa na yanke wannan shawarar idan yaso da daddare ni nayi maka abincin.

Bai kawo komai a ran shi ba yace." Okey tunda kin zabi hakan, to ni a gurina babu matsala." Bugun kofar ya katse maganar ta, tace." Bari kawai na bude mata kofar."

Yana kokarin sanya uniform d'insa yace." Okey ba damuwa.........D'aure da 'karamin towel wanda bai gama ratsa jikinta ba ta bud'e kofar gashin kanta jike da ruwa tana gogewa da karamin towel din dake hannunta.


A razane! take kallonta gabad'aya sai jikinta ya fara rawa, wani masifaffan kishi ya tokare mata a wuya.


Murmushi tayi ta kalli tsakiyar idonta kafin tace.'' Shigo mana kin tsaya kina kallona."

Kamar da dutse take magana, sai da ta sake maimata maganar sannan ta razana! ta kalleta sai kace wata mara gaskiya."


Da hannu ta nuna mata hanya da fadin." Ki shigo Hamra'u."

Ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya gabanta na wani irin fad'uwa! taja matattun kafafunta ta shiga falon da kwandon abinci a a hannunta sai kace wata house girl.


Ta mayar da kofar ta rufe tana watsawa bayanta kallon banza cikin zuciyarta tace." 'Yar iskar 'karya daga yau idan an ce ki sake shigo min dakin miji kya 'kara.''


Hamra'u ta tsaya tsakiyar falon sai kace wacce aka dasa ta kasa zama ballanatana ta fara aikin daya kawo ta, gabadaya ma ta rasa nutsuwarta sakamakon ganin Gimbiyar daure da towel ga gashin kanta a jike da ruwa, kawai sai taji wasu zafafan hawaye na kokarin kufce mata!


Ta kalleta da fadin." Ogan yana ciki bari ya fito sai ki shiga kiyi ayyukanki.''


Ita dai kasa magana tayi sai aukin kallonta kawai take tana mamakin cika da kasaitar ta, gabadaya k'yashi da hassada suka rufe mata ido!

Koda ta shiga dakin samun shi tayi ya gama shiryawa yana kokarin daura agogo a hannunsa, ta kar'ba tana daura masa, yana ta sanya mata albarka........Ba ta fesa masa turare ba sai da suka fito falon, wanda shi gabadaya ma idonsa ya rufe baya ganin kowa sai ita dake gabansa, dan koda suka fito falon bai ga Hamra'u ba saboda yanda idonsa ya rufe, tana kokarin fesa masa turare! yana k'o'karin shan bakinta, dan sai tallafo fuskarta yake tana gocewa tare dayi masa dariya.........Kawai sai ya fara kokarin kwance towel din da yake daure a jikinta, al'amarin da ya sanya Hamra'u suman tsaye! ta rintse idanuwanta kanta yana juyawa a dakin............Dariyarsu kawai take ji a tsakiyar kanta, kafin taji muryarsa yana fadin." Ba zaki bani na sha ba ko."?

Da sauri ta bude idonta tana kallonsu, kokawa suke yana jan towel din tana ja tare da kukan shagwab'a!

Hankalinta a masifar tashe! ta dire kwandon abincin dake hannunta ta kama hanya ta fita da mugun sauri kafarta take takawa bata sanin a in da take ajiyewa.


Fitar ta ya sanya ta daidaita hankalinta ta kalleshi duk ya wani rikice tace." Ka bari don Alla jiya fa har gajiya kayi dasha yanzu haka nipples dina zafi suke miki ka bari su warke."


Yace." Ni ban ce miki na gaji ba, kece dai ki ka ha na ni saboda haka yanzu ba zan fita ba sai na tsotsa."

Dariya ya bata ganin yanda ya lalace! sai kace soko sai jan towel din yake idonsa yayi jawur!

Tace." Duba bayan ka 'kanwarka tana kallonka."

Yayi saurin juyawa, hakan ya bata damar rugawa daki da gudu ta murza key tana sauke ajiyar zuciya.


Shima ajiyar zuciyar ya sauke tare da kokarin danne sha'awarsa! ya kalli kwandon abincin dake ajiye, falon ya shiga bi da kallo wai Hamra'un yake nema.

Ganin babu ita a falon ya sanya shi godewa Allah tabbas da anyi abun kunya


A gurguje yayi break fast din kafin ya kama hanyar fita ba tare da ya tunkari inda take ba, domin hakan shine kwanciyar hankalinsa..........


*SAI MUN HADU MONDAY DA IKON ALLAH*


*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/28/22, 13:25 - Binta: _*Zahirin gaskiya jiya naga sahihin SO!! wallahi naji dadin yanda kuka dinga turareniyar kiran waya ta da masu turo min text messages na fatan alkairi, tabbas adduarku tana tasiri a tattare dani, ba zan gaji da sheda muku cewa nima da bazarku nake taka rawa ba, MANAZARTA abin alfahari na, mutunan kirki ina alfahari daku, ina rokon Allah ya bud'a 'kwakwalwarku ya baku hikima da basirar rubuta abunda za'a amfana dashi, nagode sosaic SAI DAKU!APZFq MARUBUTA Abokan aiki, baiwa ce ta Allah domin shi ya ajiye hikamarsa a gurin, hannuna yafi karfin rubuta alkairin ku sai dai addu'a da fatan alkairi............NA GAISHE KI (NA'IMA SULAIMAN) (Nimcy luv) matashiyar marubuciya, tabbas al'kalamin ki ba zai ta'ba rubuta shirma ba, saboda aiki da hankali da kuma neman shawarwari, ina miki fatan alkairi tare da cimma burin abinda ki ka sanya a gaba............MASHA ALLAHj_ Thousands greeting to my fans love you allc0*_



*85&86*
Wannan shine 'karshen matsalar domin ko da wasa Hamra'u bata sake bin hanyar sashen maigidan ba ballantana har ta kai ga shiga dakinsa da wata manufa...........To Sosai suka samu daidato a tsakaninsu suka d'inke kamar tif da taya ke kyace dama can auran so da k'auna sukayi, sun riga sun sabarwa da junansu kwanciya tare cikin bargo daya suyi romancing iyakacin yanda ransu yake so.....sai dai b'angaran sa daurewa kawai yake, domin bukatarsa bawai tana biya duka bane, kawai dai yana rage zafi da hakan, wannan dalilin ya sanya ranar da tayi wankan tsarki kamar ya zuba ruwa a kasa yasha ganin tana sallar asubahi yasa daya dawo daga masjid ya cire jallabiya yayi rashe-rashe a gado yana kallonta tana gyara tarin turarukan dake saman mirror, kallonta kawai yake yana lumshe idonsa tare da shafa kasan mararsa gabadaya a dame yake yanda yake jin jiki baya tsammanin ko yaje gurin aiki zai iya tsinana wani abun azo a gani.

Ta juyo tana kallonsa ganin condition din da yake ciki yasa jikinta ya mutu ita kanta tasan a cikin damuwa yake, kuma ba komai ne ya janyo masa damuwar ba sai tarin sha'awar dake damunsa duk da tana iya bakin kokarinta gurin ganin ta yi masa wasa amma ta fahimci kamar hakan baya gamsar dashi.

A sanyaye ta zauna kusa dashi, ya kama hannunta ya rike yana murzawa......cire hannunta tayi tare da fadin.'' Ina kwana."

A kasalance ya amsa yana kokarin janyota jikinsa......Ta matsa a tsorace tana kallon kwayar idonsa wacce ta jirkice tayi jajawur!

"Me kake bukata wanda za kayi break fast dashi."? wannan tambayar tayi masa babu walwala a tare da ita.

Ya sauke ajiyar zuciya idonshi gabadaya yana kanta yace." Dake nake so na karya kummalo."

Zum'bura bakinta tayi tana dan matsawa daga jikinsa.

Ya bita da wani mayataccan kallo kafin yace." Meye haka kike gudu na ko bakya so mu zama abu d'aya."?

Tsaye ta mi'ke har yanzu taki sakin fuskarta tace." Ni dai ka fada min abinda kake bukata zan shiga cikin gidan yanzu."


Ya mike zaune tare da kokarin janyota jikinsa, ta matsa gefe da sauri.........Yace." Na fada miki ke kad'ai nake buk'ata idan kuma zaki min rowa ne to."

Ba tace komai ba ta kama hanyar fita, haka kawai taji tana sha'awar taja masa rai! haka kawai kai tsaye ba zata bashi kanta ba sai ta wana shi!


Kasa katabus! yayi kawai ya saki baki yana kallonta har ta bude kofar dakin ta fita......Sai sanda yaji wani irin motsi da gabansa yayi ya dawo hankalinsa, ya kalli gurin yana girgiza kansa, gabad'aya girmansa ya bayyana bai ta'ba riskar kansa a irin wannan yanayin ba.


Lamo ya kwanta yana matse k'afafunsa, ai ko ana ha maza! ha mata! sai ya sake aure saboda irin wannan ranar, domin ya lura mata da yawa mugwaye ne basu da tausayi! amma yana tsammanin ba duka suka taru suka zama daya ba, yana da tabbacin idan Hamra'u ce ba zata bar shi cikin halin ni 'yasu ba.

Sosai cikinsa yake ciwo mussaman k'asan mararsa, ga wani irin girma da gabansa ke karawa sai hauhawa yake tamkar ya fasa wandon ya fito.


Kira ne ya shigo wayarsa dake can nesa dashi.......ya sanya hannu yana lalubanta har Allah ya bashi ikon ganinta.


Asp ne yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya.........Cikin sha'kewar murya yake magana.

Cike da kulawa Asp din yace." Subahanallahi baka da lafiya ne."?


Gyaran murya yayi yana janyo maganar da 'kyar yace." Da sauki dai za'a ace amma ina jin jiki bana tsammanin ma zan fito aiki a halin yanzu."


Yace." Nima abinda nayi tunani kenan, ganin takwas ta wuce baka shigo ba yasa nace lallai akwai matsala, shin me yake damunka."?


Shuru yayi yana nazarin maganar, Asp abokinsa ne kuma kamar dan uwa yake a gurinsa amma baya tsammanin zai iya fada masa sirrinsa.

Dawurwura! yake domin ya rasa ma abinda zai ce masa.

Yace." Ashe har mun fara haka da kai, ai na d'auka abunda ya shafeka ya shafeni me yasa zaka b'oye min damuwarka? ni fa na d'auke ka tamkar dan uwa na jini."


Gabadaya sai jikinsa yayi sanyi damuwarsa ta sake tsananta Asp din ya gama kashe masa jiki.


Yace." Bafa wani gagarimin abu bane kada ka tashi hankalinka''


Yace." 'Karamin abu ba zai sanya ka damu kanka haka ba, a sanin da nayi maka jarumin namije ne wanda k'aramin abu da babba basa firgita ka babu shakka akwai abunda yake faruwa da kai."


Jin yanda Asp din yake kambaba! shi ya sanya shi dariya, ya rintse idonsa tare da kokarin danne sha'awar dake damunsa.........Shi kansa mamakin kansa yake, kamar yanda Asp din ya fada k'aramin abu ko babbah basa ta'ba d'aga masa hankali, amma abun mamaki! abunda bai taka kara ya karya ba shine yake wahalar dashi, yarinyar ta zame masa matar jaraba ita kadai yake gani a gabansa koda ya hasaso wata macan ba kamar ita ba.


Jin shuru bai magana ba ga wayar na bin iska yasa yace." Kodai har yanzu ban kai matsayin da zanji matsalarka ba kayi shuru, bahaushe yace (shuru ma magana ce.")


Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya kafin yace." Matsalar mutuniyarka ce."

'Yar dariya yayi domin sai dama ya raya hakan a ransa, shi kansa matsalar da yake fama da ita kenan......Zeey bata barin sa ya sarara, k'orafin yau daban na gobe daban! yafi samun nutsuwa da Madam Uwargidansa, wannan dalilin ya sanya yaji gabadaya auran ya fice masa daga rai yana jin tsoron auro ta ukun tazo ta daga masa hankali domin tun kafin ta shigo gidan tana nuna zafin kishi akan matansa, yasan ba zai samu matsala da Madam ba, Zeey ce 'yar tujara! baya tsammamin kanwarsu zata jiku guri d'aya.

Yana 'yar dariya yace" Umar matsalarka da Zinatu taki 'karewa amma kada kayi mamakin watarana kai da ita zaku iya zama kamar *Laila Majnun!* saboda tsananin so da 'kauna." cikin wasa yake maganar.

Girgiza kansa yayi kafin yace." Bana tsammanin faruwar hakan domin ita wannan yarinyar babu macan da ta kai ta 'keta da mugunta! ban san da hakan ba sai yau."
Iyakar gaskiyarsa yake maganar.


Da sauran dariyar a tare dashi yace." Wai dan Allah me tayi maka ne? nifa kaina ya kulle wallahi."


Tsaki! yaja kafin yace." Rabu da ita kawai ai nima ina da rana."

Yace." Ai tambayar ka nayi amsa ya kamata ka bani naga kana waskewa.


Shuru yayi na second biyu kafin yace." Naga kamar tana jin maganarka kayi mata nasiha cewar abunda take haram! ne mala'iku suna tsine mata! tabbas da taje islamiyya ba za tayi haka ba, amma kai a matsayinka na waliyyin ta sai ka nuna mata hanyar gaskiya."



Shi kam Asp dariya kawai yake 'kya'kyatawa domin ya kamo bakin zaran! *Namiji!* har *Namiji!* mace ta mayar dashi sakarai! koda yake shima hakan take a gurinsa lallabawa kawai yake a gidansa, idan ya fito gurin aiki a fafata!


Yace." Waye ya fad'a maka mata wasa ne! duk isa da jin kai! idan ka shiga hannunsu sai ka raina kanka.......kawai ka iya zama dasu shine samun kwanciyar hankalinka, domin yawancinsu basu da imani idan wani sa'bani ya shiga Tsakaninku ta nan suke fanshewa babu ruwansu da dokar Allah! sun bi sun take saboda san zuciya, amma kuma muma mazan muna da namu laifin domin bama sanin muhimmamcin matan mu sai bukatar kan mu ta kawo mu, sannan suke da daraja a gurun mu, wannan ba dai-dai bane, yana da kyau mu gyara kuskuranmu suma matan su gyara nasu."

A sanyaye yace." Kwana biyu zaman lafiya muke sosai kuma na zauna nayi tunani domin gano dalilin da yasa take gudu na ban ga komai ba, kawai dai nafi tunanin mugunta ta shirya min shiyasa ta bari na saki jikina da ita."


Yace." Kasan suna da wani abu, idan kazo biyan bukatarka a gurinsu to burinsu su ja maka rai! yanda na fahimci hakan yana musu dadi."


Yace." Nima nayi tunanin haka mybe tana so naje na fashe mata da kuka ko."?


Asp din ya fashe da dariya yana girgiza kansa yace." E to hakan ma ba laifi bane zaka iya zuwa amma dai kasan irin kukan da za kayi."


Dogon tsaki yaja kafin yace." Allah ya kiyaye."! da karsashi! da karfin gwiwa! ya fadi maganar kamar gaske baya kukani


Yace." Ka daina cika baki fa."

Cikin jin takaicinsa yace." Ranka ya dade mu bar wannan maganar haka domin wallahi ni raina ne ma yake b'aci! kawai abunda za kayi anan shine ka kira wayarta kayi mata nasiha watakila taji tausayi na ta bani hakkina, amma ina mai tabbatar maka da cewar idan ta'ki to zan k'wata ta karfi da yaji."


Yace."Duk ba za'ayi haka ba, kayi hakuri insha Allah zan mata magana kuma komai zai wuce amma ina so dan Allah ka bata muhimmanci domin su mata babban burinsu suga ana kula dasu gami da nuna musu soyayya."


Murmushi kawai yayi yana girgiza kansa, a ganinsa duk wata kulawa da soyayya ya bawa yarinyar kawai dai ta shirya zalinci ne don ganin ya jarabtu da tsananin sonta.


To kamar yanda Asp din yayi alkawari zai kira wayarta domin yay mata nasiha hakane ya faru..........bai fito 'karara ya nuna mata abunda yake nufi ba, amma yayi mata hannunka mai sanda wanda yasa ta fahimci abunda yake nufi.......Ba ta iya cewa komai ba, har yayi mata sallama, ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.

Tabbas bata raba daya biyu shine ya shedawa Asp din abunda yake faruwa a tsakaninsu..............Ita fa akwai manufarta kai tsaye ba zata amince masa ba a yanzu sai nan da wasu kwanaki.

Na farko tana tsoron daukar ciki tunda tsarkinta kenan.........tana da tabbacin cewa idan rabo ya rantse a tsakaninsu za ta iya samun ciki dalilin k'ofofin jikinta da suke a bude.....Wannan shine babban dalilin da yasa take gudunsa, tafiso ko wani abu zai shiga tsakaninsu ba yanzu ba tukkuna.


Wanka tayi taci gayu tana kamshi turare kala-kala ta zauna a falo tana kallo tana tsikarar duniyarta da tsinke babu abunda ya dameta!


Ta manta dashi domin duk a tunaninta ya tafi gurin aiki..... ........Kawai sai ta tura Baraka ta nufi sashen domin gyarawa kamar koda yaushe.


Baraka tasa key tana muzara kofar taki bud'ewa, shi da yake kwance a uwar daki ya dinga jin motsi ya fito falon yana tambayar waye."


Gabanta na faduwa tayi saurin barin gurin.........tana kokarin shiga wani korido ya hango bayanta, nan ya fahimci cewa d'aya daga cikin masu aikinta ne, ya koma ciki da mamakin hakan a tare dashi.


Baraka ta sheda mata cewar yana nan bai fita ba, jikinta a sanyaye tace." Amma dai baku had'u ba ko."?

Da sauri tace." Eh ai jin yay magana yasa da sauri na matsa daga gurun.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da jin sanyi a cikin zuciyarta, tasan duk ranar da yasan abunda yake rufe akwai rikici.


Sai bayan la'asar ya samu kansa, a gida ya gabatarsa da sallah dan bai iya shiga massalaci ba gudun abunda ka iya zuwa ya dawo kawai ya hakura yayi sallar a gida...............Kai tsaye sashen Uwale ya nufa ya same su zaune a falo suna kallo.

Ya samu guri ya zauna yana kiran sunan Allah.....Uwale ta kalleshi da fadin." Ashe baka fita."?

Yace." Eh wallahi na yini bana jin dadi sai yanzu na samu sassauci."


Tace." Ayya ai ba labari me yake damunka."?

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Ciwon ciki ne amma yanzu da sauki tunda nasha magani."


Tace." To Allah ya sawwake." Ya amsa da "ameen yana kallon gefan da Hamra'u take zaune sai cika take tana batsewa!


Abun ya bashi mamaki sosai! yarinyar ba ta'ba share shi irin yau ba......Cikin kulawa yace." Kanwata lafiyarki kalau kuwa? bako gaisuwa."

Ta kalleshi tana sake hasaso abunda ya faru! kawai sai wasu zafafan hawaye suka ciko idonta.......Wani irin haushinsa take ji tare da masifar kishin matarsa.


Sunkuyar da kanta tayi tana kokarin boye hawayen kada ya zuba.


Uwale tace." Ai Hamra'u kwana biyu ta zama shuru-shuru! ko ni ma da kyar take min magana."


Da kulawa yace." Ko baki da lafiya ne."?


Kai ta girgiza kuka naso ya k'wace mata.


Yace." To ki daina damuwa komai yana da lokaci dan haka ki kwantar da hankalinki."


Wannan maganar da yayi ta sanyaya mata zuciya......Ta kalleshi tare da sake jin sabon sonsa na ratsa cikin jikinta......Murmushi yayi mata da fadin ." Ko zaki iya taimaka min da abinci."


Tai murmushi da fadin." Me zai hana bari na kawo maka.''


Ta ajiye romot din hannunta ta nufi kicin tana adduar samun nasara a zuciyarta.


Ido ya dauke daga kanta shima adduar yake a cikin zuciyarsa Allah ya bashi ikon yi mata adalci.

Uwale ta kalleshi da fadin." Ina matar taka ina fata dai lafiya lau kuke zaune."?


Yace." Lafiya lau ai tana zuwa ku gaisa ko."?

Girgiza kai tayi da fadin.'' Oho! o! ni ai na kwana biyu rabon dana sa ta a idona."


Da mamaki a tare dashi yace." Kina nufin bata zuwa ta gaishe ki "?


Yanda ya fadi maganar a harzuke! yasa jikinta yayi sanyi ta dinga nadamar

Please Login or Register in order to submit comment