Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wancan kayan dake cikin baggo na tsaraba ne ya kamata tunda zaki shiga cikin jama'a ki tafi dasu."

Tace." Kina nufin akwai wasu kayan da ki kazo dasu."?

Tace." Eh suna can dakin." tafada tana nuna dakin Umar din da yake dake rufe.

Uwale kasa magana tayi saboda mamakin mutunci da karamcin yarinyar, tana da kyawun zuciya tana kuma da kyauta da alkairi hakan kamar a jinin jikinta yake.....Ta kalleta da fadin." Sannu da kokari, Allah ya saka da alkairi amma yana da kyau muje tare dake sai ki basu da hannunki.

Tayi jim tana nazarin maganar kafin ta girgiza kai da fadin." Babu komai Uwale ni dake duk daya ne kawai ki basu a matsayin kece ki ka kawo musu babu komai."

Tace." Aa ba za'ayi haka ba, idan ma ba za kije ba babu damuwa amma tabbas da sunanki zan bada kayan."

Tayi murmushi da fadin." To hakan ma yayi ni zan shiga na kwanta Allah ya sanya alkairi." Ta amsa da ameen tana kokarin bude dakin Umar din domin fito da kayan.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/18/22, 20:29 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*109&110*
Gidan ya rage saura ita kadai, sai ta shiga tunanin abubuwan da suke faruwa, jiya da daddare kafin su kwanta Uwale tayi mata cikakken bayanin abunda yake tsakanin mijinta da yarinyar da tuntuni ta d'ora zargi a kanta, tabbas koda Uwale ba tayi mata bayanin komai ba dama tuntuni ta fahimci wani abu, duk da dai shi bai fad'a mata cewa akwai al'kawarin aure a tsakaninsa da yarinyar ba, to ita yarinyar ta nuna mata alamu tun farkon fara had'uwarsu...Ba zata ha nashi aure ba, domin a yanda Uwalen ke sheda mata yanda yarinyar tayi wahala a kansa hakan ya sanya taji tausayinta, bayan haka kuma ta san duk daran dadewa bai zama lallai ta zauna ita kadai ba, wannan ne dalilin da yasa ta tausayawa yarinar. wai akace son maso wani koshin wagala! amma babu shakka ba zata lamunci munafurci da kumbiya-kumbiya ba. domin tafiso duk abinda za'ayi a fada mata kada a munafurce ta, abu na karshe kuwa dole ya jawa yarinyar kunne ta kiyayi shiga gonarta ko kuma yi mata rashin kunya anan ne za'a samu matsala! domin mutukar yarinyar tace zata raina mata hankali to abu ne mai sauki a gurinta ta cire blet ta zane mata jiki dashi, sai dai duk abunda zai faru ya faru.


To can gidan biki kuwa ya kacame! da hayaniya mata sun fi ashirin akan Uwale dake rabon turaman atamfofi da mayafai da sabulai na wanka da wanki.

Da yawa wasu basu samu zanin ba, saboda yawansu, wasu kuma mayafai suka samu da sabulai, duk wanda ta mik'awa sai tayi masa bayani cewa daga matar Umaru ne.

A cikin wa'inda suka samu kayan har da mutanan Dayyiba......sai suka silale suka nufi gidanta domin kai mata rahoto.

Wasu kuwa gidan Uwalen suka nufa domin mika godiyarsu da kuma jin dadin alkairin da akayi musu.

Hayaniyar shigowarsu gidan ya katse tunanin da take.

Ta fito tsakar gidan ta gan su da yawa a tsaye....ikon Allah har da masu durkusa mata, ta jingina jikin bango (garu) tana amsa gaisuwarsu da fadin." Ku daina godiya haka babu komai an zama daya.


D'aya daga cikinsu tace." Dole muyi godiya yarinyar kirki! domin bamu tsammaci haka daga gurinki ba, dalili mun samu labari a bakin wasu daga cikin 'yan uwanmu cewa baki da kirki mutuniyar banza ce ke da dai sauransu, sai gashi kinyi mana bazata mun gode sosai."

Murmushi kawai tayi kafin tace." Ba komai kun san mutum tara yake bai cika cif ba, kowa yana kuskure a rayuwa, wa'inda na 'batawa rai a cikinku su yafe min tunda har Allah yasa na shiga cikinku ai mun zama daya dama rashin sabo da juna ne."

Matar tace." Kwarai kuwa Gimbiya to mu dai muna bayanki insha Allah domin dai Dayyiba bata da alkibula mai kyau! mu mutanan *KAFUR* muna sonki da kaunarki dan haka ki cire kokwanto a ranki."


Tace." To na gode sosai Allah ya saka da alkairi."

Gabadaya suka amsa da ameen. kafin suyi mata sallama su fita....Itama cike da farin ciki da jin dadi ta koma dakin ta kwanta, cikin zuciyarta take adduar Allah ya bata hakurin zama dasu, tunda tana son mijinta babu abinda ba za tayi ba.


Dayyiba da labari ya iske ta kamar ta kurma ihu saboda bakin ciki, idonta ya ciko da ruwan hawayen bakin ciki ta kalli Taburni da fadin." Amma dai kinji kunya wallahi Ashe amincin da yake tsakaninmu na 'karya ne."?


Taburni tace." Kamar yaya ban gane ba."?

Ta zabga mata harara da fadin.'' Meye amfanin zuwa ki kar'bi turmin atamafa kamar baki ta'ba daura zani ba."


Ta daga mata hannu da fadin." Kinga Dayyiba saurara! kawai saboda gudun bacin ranki ina kallon alkairi sai na bar shi, kema kin san ba zai yuwu ba, zani da sabulai na samu ke ko dake ko babu ke dole ina da rabo saboda matar Kawunsa ce to meye abin damuwa."

Dayyiba ta sanya gefan zani ta share guntun hawayen daya fara fitowa tace." Taburni ban san ya zanyi ba akan wannan al'amari, wallahi idan Hamra'u ta samu shiga gidan Umaru buri na bai wuce ace ta zama mowa ba, amma na san hakan ba zai yuwu ba sai na taka muhimiyyar rawa. gashi bani da kudi a hannuna ballanatana naje a taimaka min."


Tace." Yanzu dai abu na farko da za fara shine janyo hankalinsa kan 'yarki, ma'ana ya daina ganin kowa a gabansa sai ita, kafin ace ta shiga gidansa, sai kuma ayi musu farraku da Uwargidansa.

Tace." Taburni bani da kudi wallahi, kuma kin san wannan harkar sai an ajiye kudi dole a zubar da jini."


Taja tsaki da fadin." Ashe wasa ki ka dauki al'amarin, ai idan zakiyi yawo tsirara ba abun damuwa bane mutu'kar bukatarki zata biya, ki sayar da gado da katifarki ai ba'a kanki aka fara ba.

Tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas hakan shine mafita domin idan ta tsaya kallon ruwa to kwado ne zai yi mata 'kafa gwara ta tashi a tsaye.

Uwale ta kawo mata gurasa *(band'asho)ƒ™Âi* Kanawa mune gurasa Allah yasa akwai wa'inda suka san meye ma'anar *(Band'asho)* Taji k'uli da man gyada mai kamshi gefe da kabeji da sauran kayan had'i, sosai taji dadi gurasar taci ta k'oshi kafin tayi wanka ta shirya jikinta cikin wani milk din les mai taushi da stones a jikinsa, sai ta dora alkyabba mai tafe da hula a jikinta, ta sanya takalmi rufaffan takalmi irin nasarauta, sosai tayi kyau, kamshi turaranta duk ya cika gidan.


Waje ta fito da wayar ta a hannunta.......ido yayi caaa! a kanta, itama kallonsu takeyi sunyi rukuni-rukuni a gindin bishiya suna ta cin abinci babu kimtsi balle kamun kai.

Can gefe kuma amaryar ce da k'awayenta da ango da abokansa sun sanya katuwar redio a tsakiyarsu kalangu sai tashi yake amarya da ango suna rawa ana lika musu 'yan biyar-biyar.

Abin ya burgeta ya bata dariya kai tsaye gurun ta nufa cikin yanayin tafiyarta.


Hamra'u tare da Zabbah dake can nesa suka hangeta tawagar 'yan matan garin sun rufeta a lokacin da take tsakiyar amarya da ango tana manna musu 'yan dari biyar-biyar.......Ihu!!! da kaya-kaya ya cika gurun!


Takaici ya hana Hamr'au karasawa gurin, ta juya a sukwane ta koma gida.....Ita kuwa Zabbah! sai da ta k'arasa gurin, ta kutsa ta samu rabonta dan sai da ta tsira da dubu biyu.


Da wayarta ta dinga yi musu vedio sai hauka suke suna he da he kowa so yake tayi hoto dashi, amarya da ango kuwa kamar su zuba ruwa a kasa su sha a tarihi ba a ta'ba biki irin nasu ba.


Hamra'u ta 'karaso gurin tana wani dauke kai! ita gata wacce ta fita zakkah a cikinsu, da ba a san asalin balbela ba sai ace daga masar tazo .......Ta zuge jakar hannunta ta fito da kudi 'yan dari -dari ta fara watsawa a gurin.........Wani abokin ango yayi saurin sanya wakar *Komai na Babah yafi na yaro!* Zinat kuwa ganin haukan da yarinyar take ya sanya tayi gaggawar fita daga gurin.

Ita kuwa Hamra'u sai wani jin kai take tana wani ya mutse fuska! Zabbah taja ta gefe da fadin." Wannan wa'kar fa da Salmanu yasa dake yake, kinzo kina lika dari-dari ita kishiyar taki dari biyar biyar ta dinga watsawa kuma ta watsa yafi dubu ashirin kinga nima na samu dubu biyu. amma ke kina lika 'yan dari -dari sai wani jin kai kike."

Jikinta yayi sanyi ta kalleta da fadin." Kina nufin dama saboda naji haushi Salmanu yasa wannan wa'kar!

Ta fashe da dariya da fadin." E mana ma'ana kiji haushi kema ki watsa musu kudi."


Ta girgiza kai da fadin.' Lallai Salmanu bashi da mutunci."

Tace." Hamra'u ni dai shawarar da zan baki shine kiyi hakuri ki kwantar da kanki ku zauna lafiya, dan na fahimci matar nan kamar tana da saukin kai kuma ba zaki samu matsala da ita ba, sannan kuma a zahiri ta fiki ta ko'ina kada kice zakiyi gasa da ita."

Tace." Idan na fahimce ki kina so kice na zauna nayi mata bauta ko."?

Ta girgiza kai da fadin " Aa ba haka nake nufi ba, ina nufin ki dai daina kishi a kanta dan naga kin zafafa da yawa, baki da gashin wance dole ki zauna a matsayinki."


Ta girgiza kai da fadin." Ba zai yuwu ba Zabbah shekara sama da goma ina dauki ba dadi akan biyan bu'kata na amma lokaci guda wata ta shiga rayuwata, wallahi ba zan iya daina kishi a kanta ba, domin bana kaunarta na tsaneta! kuma zan iya komai akan ganin bayanta."

Zabbah ta dinga yi mata kallon mara hankali da tunani! itafa gabadaya rayuwar yanzu ta zama wayo da dubara da kuma siyasa mutukar ka iya wannan zaka zauna lafiya, amma shikkenan tunda tayi iya bakin kokari gurin ganin ta nusar da ita ta kasa fahimta zata kyaleta kawai taje duk abinda za tayi rayuwarta ce.


Shida shaura ya sauka a garin.......Tun kafin ya fito a mota gurin ya hautsine! hayaniya da ifece-iface! tare da haushin karnuka!

Saboda ba ta san ganin bacin rai yasa tayi gaggawar shiga gida, ta san mybe sai ya tsaya yayi abinda ya saba.


Sai dai kuma bata jima da shiga gidan ba ya shigo cikin inform da alama daga gurin aiki yake.


Koda ya shiga gidan hankalinsa gabadaya yana kanta....ya rungumeta yana ta sumbutar fuskarta. A lokacin su Uwale suka shigo gidan.

Uwale Hamra'u da Zabbah dake bayansu......Gabadaya jikin su ne yayi sanyi ganin irin soyayyar da ake zabgawa a gurin, kamar zai cinyeta ya rike fuskarta sai so yake ya kama bakinta tana kaucewa.

Gilmawar Uwale a gurin ita ta hankaltar dashi, ya sakar mata fuska yana sauke wani irin numfashi.....Juyawar da zai yi yayi ido hudu da Hamra'u dake tsaye kamar wacce aka dasa, gwiwarta tayi bala'in sanyi!

Ya d'an ji kunyarta amma da yake namijin duniya ne sai ya basar yace." Kanwata ina fata dai kin shirya kin kuma yi sallama don yau zamu tafi."


Murya na rawa tace." Ni ba zan koma ba."

Ya kalleta da mamakin furucinta a tare dashi yace." Saboda me."?


Ba tace komai ba, kawai ta juya ta fita kawarta ta rufa mata baya.


Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin al'amarin.

Ya dan juya in da take, wayam babu ita a gurin......bai kawo komai a ransa ba, ya cire takalman dake kafarsa ya shiga dakin da sallama a bakinsa.


Gabadaya suna uwar dakin ita da Uwalen.

Kusa da ita ya zauna yana d'an satar kallonta a idonsa ya hango rama a tare da ita kwana uku kacal ta sauya masa tayi haske sannan duk ta rame.

Uwale dake had'a kaya tace." Naji kuna magana da Hamra'u ko."

Yace." Eh wai me yake faruwa ne?

Murmushi takaici tayi kafin tace." Alkairi ne, amma tunda tace ba zata koma ba, sai ka kyaleta a ranar da aka daura muku aure ai dole ta zauna a dakinta."

Gabansa ya fadi da jin maganar da Uwalen tayi zata tona masa asiri! be shirya sanar mata da maganar yanzu ba, ya saci kallon fuskarta yaga babu abunda ya sauya a yanayin ta wayarta ma take dubawa.

Ajiyar zuciya ya sauke cikin zuciyarsa yake addua Allah yasa ba taji maganar ba, duk da ya san da kamar wuya hakan dan kyau Uwale ta fadi maganar.


Ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi har an fara kiran sallar magriba, yace." Zan je nayi sallah mu gaisa da wanda ya dace kafin na dawo sai ku shirya."

Tace." Ai mu a shirye muke Umaru sallah kawai za muyi.

Yace." Uwale anya ba wani abu ne ya faru ba kuwa."?

Tace." Me ka gani kake wannan maganar.''?


Yace." Naga kamar kina Allah-Allah mu bar garin bayan kinyi alkawari cewa sai kinyi sati uku ko hudu."


Shuru kawai tayi ba tace masa komai ba. Ya girgiza kai tare da mikewa tsaye. bahaushe yace shuru ma magana ce, lallai akwai abinda ya faru bayan barin sa garin.


Uwale na idar da sallah ta kalleta da fadin.'' Kafin Umaru ya shigo zan dan shiga muyi sallama mutane."

Tace."To shikkean ba komai idan ya shigo zan sheda masa.

Fitar ta keda wuya ya shigo gidan, yana haska dakin da wayar hannnsa, kan dadduma ya sameta, ta idar da sallah amma bata tashi ba.


Ya zauna saman gadon karfen dake dakin yana kallonta.


Babu yabo babu fallasa ta juyo suka had'a ido taga yana mata wani irin kallo kafin yace." Zo nan ki fada min abinda ya faru bayan tafiya ta."


Ta iske in da yake ya rike hannunta tare da zaunar da ita kusa dashi, gabadaya hankalinsa yana kanta, yana jiran abinda za tace.


Tace." Kai me kake tunanin zai faru."? Shuru yayi be san me zai ce ba kawai yana ji a jikinsa ne."


Tace." Kamar yanda Uwale ta fada maka alheri ne hakane, Allah ya sanya alkairi a tsakaninku.''


Ya rasa gane abinda take nufi......Ganin yana kallonta yasa tace." Ya aiki ina mutuminka Asp ina fatan kuna lafiya.''?


Hannunta ya rike da fadin.'' Asp yana nan lafiya har ya bani sakon gaisuwarki amma da ba kiyi maganarsa ba na manta, sai kuma ni da nake cikin matsala."


Tace." Matsala kuma.''?

Kai ya daga mata kamar karamin yaro.

Ta zuba masa ido tana kallonsa.

Hannunta dake cikin nasa ya fara kokarin cusawa k'asan mararshi.......Tsigar jikinta ta tashi da sauri ta fizge hannun tana harararsa.


Ido jawur! yake kallonta, kafin yace." Kin gane matsalar ko."?

Tace." Kai kam baka da matsala sai wannan."?

Yace." Ina dasu amma wannan itace a kan gaba."

Ta'be bakinta kawai tayi ta d'auke kanta.

Duk ya rasa yanda zai yi baya so tana sha masa k'amshi! tabbas ya san da akwai wani abu a kasa.

Ganin abinda take yasa ya kama kansa, yayi kokarin danne kwad'ayinsa, saisaita muryarsa yayi kafin yace." Ina Uwale take ne."?

Ba tare da ta kalleshi ba tace." Ta fita domin yin sallama da mutane."

Ya mike ba tare da yace mata komai ba ya kama hanyar fita, kallo ta bishi dashi tana girgiza kanta.


Bata yarda ta zauna kusa dashi ba, a kusa da Uwale tayi zamanta suna hira, shi kuwa kamar maraya suka mayar dashi direba haushin hakan ya sanya bai sa musu baki a maganarsu ba, sai dai sa'i da lokaci yana amsa waya jefi-jefi! a haka suka isa gidan kowa da abunda ya dameshi.

A maimakon ya nufi side dinshi kawai sai ya bita nata, ta riga ta san bin diddigin da yake mata, haka kawai ta tsinci kanta da jin haushinsa.


A nan yayi wanka ya kimtsa ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya kaiwa Uwale nata sannan yayi mata bankwana, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa babu wani kuzarin kirki a tare dashi.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/18/22, 20:30 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganinĪ(\Ī(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



*111&112*
A kwance ya sameta bacci na shirin d'aukarta, ya zauna kusa da ita da fadin." Ki tashi ga abinci na san akwai yunwa a tare dake."

Ta d'an muskuta da niyyar gyara kwanciyarta a ta'kaice tace." Bana jin yunwa."

Yayi kasa'ke yana kallonta kafin yace." Ban yarda ba kwayar idonki ta tabbatar min da cewa akwai abinda ke damunki ko bayan haka ma ai ba ke kadai ce kike rayuwa ba, akwai wanda yake bukatar kici abinci shima ya samu rabonsa.

Shuru kawai tayi masa ba ta da niyyar tashi ballanatana taci abincin.

Ya 'bata ransa da fadin." Na lura kina so mu sanya kafar wando guda, me yasa ki ke min haka ne? ko dan kin ga na damu dake."

Uffan ba tace masa ba, asali ma idonta yana rufe sama-sama take jin sa.


Cikin zafin zuciya ya janye bargon dake rufe a jikinta murya a sama ya kira sunanta "Zinatu."

Ta bude ido tana kallonsa fuskarta babu fara'a ko kadan.

Yace." Na gaji da wasa da hankalin da kike min ki fito fili kiyi min bayanin dalilin da yasa kike wannan abun ai ba haka muka rabu ba da juna ba.


Zaune ta mike tana kallonsa duk ya wani firgice! har gumi yake kamar babu Ac a dakin.

Zum'bura baki tayi ba tace komai ba ta fara kokarin komawa ta kwanta, da sauri ya rike kafadarta ya hana ta kwanciyar in ban da rawa babu abunda jikinsa keyi, da alama baya son b'acin ranta.


"Kina so ki jefa ni cikin damuwa ko? shin ko dai wani abu 'yan uwana sukayi miki wanda kike hukuntani dashi."

Ta kalleshi tare da girgiza kanta kafin tace." Ko daya ni 'yan uwanka ba suyi min komai ba sai alkairi saboda haka ba wannan ce matsala ta ba."

Da sauri yace." Menene matsalarki ki fada min zanyi miki magani."

Cikin ranta ta ayyana wani abu, ta kalleshi ba tare da ta auna maganar ba tace." Ka janye maganar auran Hamra'u."


Ya tsira mata idanuwansa da suke a rikice! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dashi, yace." Wacece Hamra'u."?

Kallon mamaki take masa "Wacece Hamra'u."? wai tambayarta yake saboda ya raina mata hankali.

Ganin tana masa kallon zargi yasa ya daburce kafin yace." Waye ya fad'a miki zan aure ta da har kike wannan maganar."?


Tsaki taja kafin tace." Ba ka da gaskiya wallahi kuma ban san cewa kai munafiki bane sai yau wato har ni kake tambaya wacece Hamra'u? yarinyar da kowa ya sanka da ita a gari shine zaka raina min hankali.

Maganganunta sun 'bata masa rai mutuka! ya fusata! tare da nuna ta da hannu "Kin ga saurara kada kiyi min rashin kunya ni kike kira da munafiki."?


Tace." Kana nad'e tabarmar kunya da hauka meye dan ka fada min dalilin zuwanka garin cewa maganar auranka zaku tattauna har ka bada sadaki kun tsayar da magana to sai me don kayi aure ko ka d'auka zan damu kaina a kan hakan namijin da ake so shi ake kishi a kansa."


Yaji wani mugun bakin ciki da jin kausasan kalamanta! ya dinga fesar da wani irin huci! yana kallonta idonsa yayi jajawur! magana daya da tayi itace take sa hankakinsa ya tashi, (Namijin da ake so shi ake kishi a kansa) wato wannan yana nuna masa cewar duk abinda zai yi yaje yayi bata sonsa.


Ya tashi ya fita ya bar mata dakin domin zamansa zai iya haifar da kowace irin matsala mara kyau.


Ba ta wani damu da yanayin da ya shiga ba, bacci tayi sosai babu wata damuwa a tare da ita, ta riga ta san duk abinda yake raragefe ne da kame-kame.

Washe gari bai saurareta ba ya shirya ya fita da tarin bacin rai a tare dashi. Wanda har sai da abokinsa ya fahimci cewa yana da damuwa domin kallo daya yayi masa ya sheda hakan, abota ce ta gaskiya wannan dalilin yasa dukkaninsu suka fahimci junansu.

Ya kalleshi da fadin." UMARU kana da damuwa domin na ganta a cikin idanuwanka."


Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Zinatu ce damuwa ta Asp yarinyar nan idan ta burkice na kan rasa gane kanta."

Asp din yace." Wani abu ne ya faru."?


Yace." Ta samu labarin tabbatuwar aurena da Hamra'u shikkenan take fushi jiya da k'yar na rintsa wallahi."


Yace." Sai hakuri, amma dole ka fuskanci wannan matsalar, kai dai kawai kabi hanyoyi masu kyau da zaka rarrasheta mussaman yanzu da take da juna biyu dole sai an bi komai sannu a hankali."

Yace." Kana nufin nayi ta bin kanta ta nayi min yanda takeso, bana tsammanin yin hakan."

Yace." Aa ba haka nake nufi ba abinda nakeso ka fahinta shine kada ta dauki zafi kaima ka dauka, ka kai zuciyarka nesa ka rarrasheta kada ka biye mata idan ka kwantar da kai ina mai tabbatar maka da cewa fushin ba zai yi nisa ba."

Shuru kawai yayi yana nazarin maganar.......Wani sa'in shi kansa mamakin kansa yake idan yana wani abu akan yarinyar ya rasa dalilin da ya sanya yake gudun bacin ranta, amma baya so ya sakankance ta gane lagonshi ta raina shi. shi yasa wasu lokutan yake mata jan ido.


Da tarin yunwa da damuwa ya isa gidan. jiri da ciwon kai sun addaba masa! kai tsaye gurin Uwale ya nufa ya samu abinci yaci ya kwanta yana hutawa.

Uwalen da kanta ta fuskanci bashi da lafiya....Tace." Ai ba kwanciya ya dace kayi ba asibiti za kaje a dubaka shine abinda ya dace."


Idonsa a rufe yace." Kada ki damu ina so na huta tukkuna muna da likitoci na mussaman zan kira daya daga ciki ya dubani."


Tace." To hakan shine dai-dai ai matar taka ma ai ta jima anan muna hira sai bayan la'asar ta shiga gurinta.


Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale me yasa kika shedawa yarinyar nan abunda yake faruwa."?


Tace." Me yasa ba zan sheda mata ba Umaru ko kafiso mu tafi a haka ta samu labari

Please Login or Register in order to submit comment