Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa kuma zai aureki da ikon Allah."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sassauci a cikin zuciyarta, idan ta fahimci maganganun Uwale suna nuna mata cewar zai yarinyar ne saboda mahaifinta, ba wai dan yana sonta ba, wannan dalilin shi kad'ai sanya zuciyarta yin sanyi, amma dai duk da hakan ba zata hakura ba sai ta sake jin matsayinta a gurinsa.

******
Tsakanin Madam da Aunty Zeey amaryarta basa shiri sosai fad'a suke da juna, dalilin da yasa ma kenan basa iya haduwa guri daya domin mutukar suka hadu to sai sa'ba ni ya gifta a tsakaninsu, kuma ba kowa ke janyo rikicin ba sai Aunt Zeey maca ce mai bala'in kishi da ganin ido, ta tsani Madam da 'ya'yanta don dai ita ma Madam din a tsaye take shiyasa take shakkarta amma dai duk da haka idan sa'bani ya gifta a tsakaninsu sai sun buga, duk da ita Madam din tana kokarin ganin ta kama girma da mutuncinta.

To wannan dalilin yasa Asp din be gayyaci ita Aunty Zeey gurin zuwa kai kayan lefen ba, sai kawai ya bukaci mutane biyu daga b'angaran Uwale da wasu daga cikin 'yan uwansa da ita Madam din da Nabila yace suje su kad'ai ya isa.

Hakan yayi wa Aunt Zeey din ciwo, domin ita babban burinta ta 'kulla abota da amaryar tunda taji an ce 'yar sarauta ce take san k'awance da ita dama kuma tana kishi akan cewa duk matan abokan mijin nasu kawayen madam ne, wannan dalilin yasa takeso tayi kwace Zinat din domin samun abokiyar shawara.

Kasa hakuri tayi da abunda yayi mata ta kira shi a waya tana masa 'korafi akan me yasa zai mata haka, ai itama matarsa ce me yasa komai zai faru Madam ce a kan gaba ita gaskiya ta gaji da wannan abu, da yake yasan halinta sai ya rarrasheta da fadin shi beyi hakan da wata manufa ba, amma tunda ya fahimci tana so tayi abota da amaryar to idan ya dawo zai bata number ta sai su dinga gaisawa, hakan yayi mata dadi sosai tayi masa fatan dawowa lafiya.


Babu wanda be yaba da kayan lefen ba, domin 'karshen isa da kasaitar mace kenan, kaya ne da aka kashe iyayen kudi gurin had'awa tun daga kan kayan shafe-shafe har kan under wears babu na Najeria takalma da jakkunansu sunfi kala ashirin, bayan manya manya atamfofi da lesuka da iyayen shaddudi da goyayen riguna na waje da mayafai masu asalin kyau da tsada, fashion na sarkoki kam ba zasu lissafu ba bayan gold din dake cikin akwatinsu set uku, kaya tamkar za'a bude sabon kanti..................Kowa ya yaba da kayan amma ban da ita, bata fito ta nuna hakan a zahiri ba, sai dai har hazar yau da kayan sukayi kwana uku a gidan ba ta duba taga meye a ciki ba, tana kallon dai 'yan uwanta suka d'ibar mata wasu daga ciki zasu bayar a dinka mata, shuru kawai tayi saboda bata so tayi wata magana su samu sa'ba ni da juna, suna ta murna da farin ciki gefe guda kuma suna shirye-shiryen yanda za'a gudanar da shagalin biki, ita dai ido ne nata duk abunda sukayi daidai ne, ta danne komai a ranta taki ta nuna musu zahirin abinda yake cikin zuciyarta.

Aunty Zeey sarkin shishshigi da iya waje sai da ta san yanda tayi ta samu shiga a gurinta, ta waya suka k'ulla abota, kullum sai sun gaisa da juna, wani sa'in har ita aunty Zeey din take dan bata labarin wasu abubuwan da suka shafeta da mijinta da kuma kishiyarta.......Tayi ta mamakin al'amarin, wani lokacin idan taji tana zagin Madam da 'ya'yanta ta kanyi mamaki! Tace." Ni kam kinga na zauna da matar amma ban ta'ba ganin mugun halinta ba.

'Kwafa take da fadin." Don ba kishiyarki bace shiyasa amma ki san irin zaman da za kiyi da ita kuma kada ki dinga sakin jiki kina fad'a mata sirinki."

Dariya ta kanyi a duk lokacin da sukayi irin wannan maganar ta kanyi mamakin yanda mata suke kishi akan namiji ita kam duk irin so da kaunar da takewa namiji ba zata lalace guri kishi a kansa ba, a ganinta kishin da ake a kansu shine yake sawa suna iskanci yanda ransu yake so, shiyasa ita da namiji babu mutunci.

Aunty Zeey ita ta maye gurbin aminiyarta Sakina wacce ta tafi yawan siyasa sai dai duk abunda yake faruwa tana samun labari daga bakin k'awar tata, tana sa ran dawowarta kafin d'aurin auran.





*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
1/31/22, 07:31 - Buhainat: Ī]
*45&46*
Hamra'u duk irin bayanin da Uwale tayi mata besa ta hakura ba ta kwantar da hankalinta ba, mugun kishin Zinatu take, gabadaya ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, gani take mutukar ya auri 'yar sarauta to maganar auranta dashi zai sha ruwa, da ta gaji da wasiwahsi da zuciyarta sai kawa ta yanke shawarar kiran wayarsa domin taji a matsayinta a gurinsa duk da cewa tunda ya tafi tsayin sati biyu da kwanaki goma be nema ta ba ballantana ya kira wayarta yaji ya take. Sai dai sa'i da lokaci ya kan kira Uwale su gaisa itama ba kullum ba, ita Uwalen ke bata sak'on gaisuwarsa gare ta, gashi kullum kara sonsa take da kishinsa, sam ta tsani wata mace ta kusance shi, gashi daj shine da bakinsa ya furta cewa yana sonta zai aureta amma duk wasu hanyoyi na nuna kauna da so da kulawa baya nuna mata, yanda ta lura kamar yafi bawa aikinsa muhimmanci a kanta.

Ta kira wayar tasa gabanta na dan fad'uwa! dalili bata san irin kar'bar da zai yi mata ba.

Koda yaga kiran nata beyi mamaki ba, sai da ya fita daga cikin jama'a sannan ya samu sararin amsawa.

Murya a sanyaye ta gaisheshi tana langwab'ewa! ya amsa cikin kulawa da fadin." Ina fatan duk kuna nan lafiya aiki ya hana ni samun sukunin kiran wayar ku mu gaisa, ina fata dai kina samun sakon gaisuwata a gurin Uwale."?

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke murya na rawa tace." Eh tana fada min a duk sanda ku kayi waya, amma yaya na me yasa ni ba za ka kira waya ta domin mu gaisa ba sai dai ka bada sa'ko."

Rashin abun fad'a yasa yace." Bana samun lokaci ne kullum cikin aiki nake wannan shine dalili amma kada ki damu har yanzu kina nan a cikin zuciyata."

Girgiza kanta tayi da fadin." Ina kokwanto akan maganar ka domin na samu labarin duk abunda yake faruwa wanda ka boye min zaka auri 'yar sarauta wannan ne dalilin da yasa kake kokarin ka juya min baya."

K'aramin tsaki yaja ya dan girgiza kai da fadin." Idan wannan ne tunaninki to ki daina domin ni ba a haka nake ba, aurena da Zinatu Allah ne ya kaddara! ban ta'ba tunanin had'uwa da ita ba, ballanatana har naji sha'awar auranta a raina, mahaifinta ne ya bani ita dalilin taimakon da nayi mata, babban mutum ne mai mutunci da dattako wannan dalilin yasa na kar'bi auranta domin yafi karfin alfarma a gurina."

Cikin jin sassauci sakamakon maganganunsa tace." To shikkenan ni yanzu na kira kane domin naji matsayina a gurinka."


Kansa ya dafe cikin rashin san damuwa yace." Wai shin Hamra'u sau nawa ki ke so kin san yaya matsayinki yake a guri na? na fada miki cewa ina sonki kuma ina da bukatar auranki saboda na yaba sa kyawawan halayenki wannan shine babban dalilin daya ja ra'ayi a kan ki, duk wasu kyale-kyale basa burgeni nagarta nake nema, amma duk da wannan bayanin da nayi miki na fahimceki kina kokwanto aikana shin me kike nufi ne."?

Dan murmushi tayi kafin ta kwantar da murya da fadin." Kayi hakuri Yayana bana nufin komai sai alkairi, na fahimce ka kuma na amince da maganarka amma don Allah ka dinga nuna min kulawa sannan kuma tun kafin amaryar taka ta shigo gidanka ka sheda mata maganata domin ta san da zamana a zuciyarka."

Maganarta ta bashi haushi da mamaki! Yace." Okey kina so ki tsara min yanda zanyi kenan."? Yanda yayi maganar cikin shan mur yasa tayi saurin fadin." Aa ba nufina kenan ba."

Yace." Idan ba haka kike nufi ba menene na damun kanki? alamu sun nuna akwai wani abu da yake zuciyarki game da ita Amaryar tawa, kin gane ko bana so ki fito da kishinki tun yanzu yin hakan zai janyo mana samun sa'bani dake, bana son tashin hankali a gidana kiyi kokarin ganin kin kiyaye faruwar wata matsala.''

A sanyaye ta bashi hakuri da fadin'' Zata kiyaye insha Allah, zuciyarsa babu dadi yayi mata sallama ya kashe wayarsa ya koma cikin mutane domin cigaba da abunda yake gabansa.

*****
A can masarautar kuwa komai yana tafiya kan tsari wata hatsaniya bata 'kara tashi ba, sosai Ta samu daidaito da zaman lafiya da 'yan uwanta, kowa yana kokarin faranta mata rai, kuma Komai na bukatar rayuwa an tanadar mata har da bayi wanda za taje dasu gidan mijin nata domin su bauta mata maza biyu mata biyu.

'Bangaran gyaran jiki kuwa har gajiya tayi domin kullum da kalar maganin da zata sha, al'amarin da ya janyo mata mugun ciwon mara wanda take kwana dashi ta tashi dashi ga wani ruwa da take zubarwa wanda ta riga ta fahimci ko na menene, haka nan take hakuri domin samun farin cikin mahaifiyarta tasan idan ta bijire to za'a ji kansu abunda bata fata kenan babban burinta ta samu ta rabu da ita lafiya.


Ya kasance yau saura sati daya daurin auran Sakina tazo gidan suka rufe kofa suna tattauna maganar, tace." Kawata ni kuwa zan so ganin wannan mutumin da ya samu wannan gara'basa shiyasa fa mutum in yana da dama a hannunsa ya dama tun kafin wankin hula ya kaishi ga dare, don Allah dube ki sankaceciya son kowa kin wanda ya rasa baki da kirar Allah wadai kin tara duk wani abu da ake bukata wanda ya kamata a ce kin kasance matar daya daga cikin shuwagabbanin kasa amma zaki kare a auran wani dan kauye bagidaje mafarauci wanda yake ci a karkashin gwamnati wallahi wannan al'amarin sam beyi min dadi ba."


Ido cike da 'kwallah tace." Ya zanyi Sakina dole nayi hakuri nayi biyyaya na zauna da mutumin nan domin hakan shine kwanciyar hankalina wallahi nasan idan na bijire wa wannan al'amarin iyayena suna iya tsine min albarka, Sakina baki ga yanda suke 'kaunarsa ba, haka mutumin yake da masifar kwarjini da shiga zuciyar duk wanda mu'amula ta had'asu........Kai tsaye ni ba zan kushe hallitarsa ba domin kyakykwa ne sosai gashi da kirar maza bashi da makusa fa, domin duk wani abu da mace take nema a gurin namiji ya mallaka hausawa suka juma'ar da za tayi kyau tun daga labara ake ganeta, kin ga dai ban san zahirin sa ba amma jarumtarsa ke nuna min cewa shi din ba rago bane zai iya daukewa mace dukkanin bukatarta, amma hakan besa naji ina sonshi ba, dalili shi ba abokin burmi na bane, naso an kyaleni na za'bi daidai dani na aura amma shi kaf family nasa mutanan k'auye ne matalauta, shima din akwai gidadanci da 'kauyanci a tare dashi wannan dalilin da yasa na tsaneshi! nake jin kunya a danganta shi dani a matsayin mijina, bayan haka bashi da wata makusa a suffar sa."



Tsaki taja da fadin." Wallahi kin bani haushi sai maganar suffa kike suffarsa ta banza da wofi, me za kiyi da suffarsa ai yanzu ba'a duba wannan, gabadaya mata sun gane sunyi wayo yanzu basa yarda su kai kansu gidan wahala, ni nan da ki gan ni ba zan ta'ba yarda na auri talaka ba wallahi mai kudin gaske zan aura koda kuwa ya kasance tsoho tukuf babu ruwana da tsufansa kudinsa nake bukata ya fadi ya mutu na samu rabona, idan kuma bukatar namiji ta kamani na fita na samu wanda zai biya min bukata, abunda duk gasu nan mazan da kudi ko babu zasu gamsar dake amma duk kin damu mutane da maganar suffa da kyau, nan gaba kadan ina kyautata zaton kyawunsa ne zai rinjayeki ."

Girgiza kai tayi da fadin." Baki fahimci magana ta bane shiyasa kike ganin kamar nan gaba zai iya jan ra'ayi na, kawai dai ina fada miki abinda yake zuciyata ne."

Tabe baki tayi da fadin" Ke nifa ban yarda ma dake ba wallahi anya kuwa babu soyayya ba'kauyen nan a cikin zuciyarki, ni dai nasan mutumin da kake qi ba zaka zauna kana kwarzanta shi ba."

Cikin takaici da jin haushin maganarta tace." Sakina mu bar maganar nan haka kada ki 'bata min rai, tunda dai kin kasa fahimtata shikkenan bana so mu rabu da bacin ran juna."

'Yar dariya tayi da fadin.'' Kada kiyi fushi k'awata tsokanarki nake yi amma don Allah bari nai miki wata tambaya."


Ba tare da tace komai ba ta zuba mata ido tana sauraranta.

Tace." Shin wanda za'a aura miki din mutumin wane gari ne."?

Jim tayi tana tunani kafin tace."Mutumin Katsina ne cikin wani karamin kauye dake karamar hukumar malunfashi, duk wani binkice daya cancanta Maimartaba yayi akansa da iyayenshi basu da wani aibu kaf family nasu mutanan kirki ne, sai talauci da yayi musu katutu! kaf d'insu matalauta ne asalin sana'ar mahaifin shi korar jakai, yanda Maimartaba yake fada mana shi kansa Umar din be taso da mahaifiyarsa ba sai kakarsa wannan shine abinda na sani.


Tace."Okay yanzu dai idan na fahimta can k'auyen zai kai ki ya ajiye."?

Girgiza kai tayi da fadin." Aa na fada miki yanzu yana aiki a karkashin gomnati a matsayin jami'in tsaro, ya samu daukaka sosai dalilin jarumtarsa wannan dalilin yasa gomnatin mallaka masa gida tare da abubuwan more rayuwa yana nan tare da kakarsa a gidan.

Murmushi tayi da fadin." Akwai hanyoyi masu sauki da za kiyi amfani dasu ki cuzgunawa rayuwarsa, ki hana shi jin dadi, sannan ki hana shi zaman lafiya, ni zan zan baki shawarwari masu kyau yanda za kiyi ki ha nashi kwanciyar hankali dashi da kakar tasa."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin sasauci tace." Nagode sosai k'awata.



A daran ranar ta sake kiran wayarsa tun bayan kiran da tayi masa ya d'ankara mata magana mai zafi, to wannan karon a shirye take dashi tayi alkawari kan cewa duk cin mutuncin da yayi mata sai ta rama.


Koda yaga kiran nata beyi kasa a gwiwa ba ya amsa cikin muryarsa mai cike da amo!!

Ji tayi ta daburce sakamakon jin sautin maganarsa a kunnuwanta, da sauri ta aro jarumta kafin ta fara magana cikin Izzah! da isa! tace." Kana jina dai ko."?


Ya maimaita maganar a fili da mamakin yanda take masa maganar gatsar kamar uwarsa.

Be tanka mata ba kuma be kashe wayar ba.

Ta sauke zazzafar ajiyar zuciya wacce taso ta jefe shi cikin wani yanayi yayi saurin janye wayar daga kunnashi, sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya mayar da wayar kunnanshi da fadin." Ke nake sauraro."


'Karamin tsaki taja za ta cigaba da magana ya katseta da fadin." Na tsani wannan da'bi'ar taki ke kuma na fahimci abinda kika sa a gaba kenan rashin d'a'a da tarbiya, ayi miki magana kiyi tsaki! to kada ki kuskura kizo gidana da wannan da'biar zaki sha wahala a hannuna."

Wani kuttun takaici yazo ya tsaya mata a wuya! wai gargadinta yake kamar wanda aka gaya masa cewa tana san zama dashi al'amarin ya bata mamaki mutu'ka ta daure ta had'iye bacin ran kafin tace." Magana nake so nayi da kai ni bakar magana nace ka gaya min ba saboda haka ina so ka tsaya ka saurareni."

Ya kalli agogon dake kafe a dakin goma saura na dare dawowarsa kenan ya kwa'be kaya zai shiga wanka ta kira shi, yace." Ni nafi ki Uzuri wanka zanyi yanzu naci abinci na kwanta domin yau gabadaya a tsaye na yini ina bukatar hutu a halin yanzu saboda haka minti uku na baki kiyi sauri ki fadi abinda ke tafe dake ina sauraranki.

Wata 'kwalla mai zafi ta ciko idonta, wai shin za tayi da wannan mutumin ne, wato bama shi da cikkken lokacin da zai saurareta.

Hanci taja kamar ta fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki da takaici tace." Matsalar kace wannan, abinda nakeso na fada maka shine ni ba zan zauna gida d'aya da kowa ba, idan wannan ne tunaninka sai ka sauya wani."


Ya jima yana jajanta maganar a cikin zuciyarsa kafin yace." A yanzu dai baki isa ki tsara min yanda zanyi ba, ballanatana kuma kina k'arkashi iko na, kafin na san kowa a duniya Uwale na sani, saboda haka akan ki dai ba zan rabu da ita ba Ina tare da ita, duk inda nasa 'kafa zata ajiye tata, Idan kuma kina ganin zaki zo da gurin zama daga gidanku to ni zan baki fili ki dasa ki zauna ke kad'ai, amma ni ina tare da Uwale muddun rai insha Allah."

Tace." Kana maganar nazo da gurin zama ai kasan nafi 'karfin wannan, kai ne matalauci ba'kon arziki da har kake wani tutiya! da arzikin gomnati, to shikkenan tunda kana ganin ba za kayi abinda nace ba, to kuwa kullum kana tare da bacin rai a cikin gidanka."
Bata jira jin ta bakinsa ba tayi saurin kashe wayar tana wani irin numfarfashi irin na b'acin rai!




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
1/31/22, 17:50 - Buhainat: *GJSR*
*47&48*
Cikin tsantsar 'bacin rai da damuwa ya samu gefen gado ya zauna yana auna maganganunta, "Kai ne mataulaci ba'kon arziki wanda yake tutiya da arzikin gomnati to tunda ba zaka yi abunda nace ba kullum zaka kasance cikin bacin rai." Wa'innan maganganun sune kawai suke masa amsa kuwwa a kunne! babu shakkah auran wannan yarinyar bashi da fa'idah a gurinsa, Dole abunda yake gudu babu makawa sai ya faru, tun kafin ta shigo gidansa ga irin furucin da take a kansa da famliy nasa, Annabi SAW yace ku auri salihan mata masu hankali da tarbiya duk wanda yake so ya gina zamantakewar auransa dole ya cire son zuciya gami da rudin duniya ya nemi nagarta ya aura, yarinyar ta tara komai na hallita wanda zata iya ja ra'ayinsa amma ta samu nakusu gurin mugun hali da rashin tarbiya, tana ta'kama da kudi da mulki da suffar jiki, wannan dalilin yasa take ganin tafi karfin kowa babu wanda ya isa ya tursasata! dama haka rayuwa take, ya jima yana addua akan Allah ya arzurta shi da mace tagari dalilin tsoro da gujewa hallayarsu, hakan yasa be tsawwalawa rayuwarsa akansu ba duk da cewa yana da bukatarsu amma bai bari hakan yayi tasiri a zuciyarsa da gangar jikinsa ba, ya cigaba dai da addua da neman zabin Allah, sai gashi kuma Allah ya jarabceshi da auran yarinyar da kwata-kwata tunaninsa be kai kanta ba, hakika kowane bawa yana tare da jarrabawarsa...................babu shakka shigowar yarinyar rayuwarsa babban kalubane a rayuwarsa tunda ya fahimci cewa shaid'aniya ce bata k'aunar zaman lafiya da kwanciyarsa hankali, dole ya zage damtse a kanta ya nuna mata bambancin mace da namiji, babu ruwansa da mulki da sarautarta domin basu ne a gabansa ba, mutukar an d'aura auran nan to dole ta zauna karkashin ikonsa ko tana so ko bata so kuma ba zai yarda da shirme da shashanci ba, kullum maganarta bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane to shine zai tabbatar mata da hakan daga zarar ta shigo gidansa zai nuna mata cewa ita ba komai bace a gurinsa.

Da wannan tunanin ya shiga wankan yana sake jin tsanarta a cikin zuciyarsa duk wasu iskanci da take masa bai ta'ba jin haushinta irin yau ba, in banda hauka da jahilci waye yayi mai kudi da talaka idan ba Allah ba, maganar yana ci da gomnati ai halak yake ci ba sata yayi ba, to duk wannan ma bai dameshi ba sosai akan yanda take kokarin kafa masa dokoki wannan shine yafi 'bata masa rai! yana samun nutsuwa zai auri wacce zata kwantar masa da hankali yayi rayuwar jin dadi da ita wannan shine shawarar da ya yanke.


*****
A cikin 'yan kwanakin da suka rage a daura auran gabadaya ta sauya tayi wani bal'in kayau na mussaman fatar ta tamkar kasa harshe ka lashe domin kyau da taushi sai sheki take saboda gyara na mussaman da Mamanta tasa ake mata, in ta zauna a guri kuwa har ta tashi kamshinta yana gurin, tasha gyara ciki da waje, wanda yake janyo mata feelings sa'i da lokaci shiyasa wani lokacin take fakar ido ta zubar da rabin maganin a toilet domin ita kadai ta san halin da take shiga idan sha'awarta tashi,

Sosai ta jinjinawa mamanta ta kuma yaba da kokarinta a kanta, sai dai kash duk wannan gyaran da ake har yanxu zuciyarta ta nan a kangare bata jin za taje gidan mijin nata da sigar san zaman lafiya.


Asp ya kira wayarta suka gaisa a mutunce da yake yanzu ta saki jiki dashi dalilin matarsa aunty Zeey kenan, suka dan ta'ba hira kafin ya shiga tsokanarta da fadin" Yau saura kwana biyu ki zama amaryarmu ina fatan dai yanzu kun sansanta da mutumin naki."?


'Bata fuska tayi tace." Asp ka daina yi min maganar wannan mara kirkin abokin naka saboda ya same ni a arha shine har ya samu damar kira na da *Matar ladan noma* to ka fada masa cewa koda na shigo gidansa yayi kokarin samun zaman lafiya dani, idan ba haka ba wallahi sai na hana shi kwanciyar hankali domin auranshi kaddara ne a tare dani, domin ni nafi karfinsa ni ba matar k'ananun yara bace."

Maganganunta sun bashi haushi da dariya amma bai yarda yayi dariyar ba ya danne cikin taushin murya yace." ZINATU wai me yasa ki ke haka ne? me kika dauki duniya? ita fa mace duk isa da kasaitarta gidan mijinta shine mutuncinta, duk da bakya san abokina amma bai cancanci haka daga gurinki ba, na tabbata cewa kece kika tunzurashi har ya kira ki da wannan kalmar *Matar ladan noma* wanda ni kaina nasan ya fad'a ne domin ya 'bata miki rai amma matan da za'a kira da irin wannan sunan kwata-kwata bakya cikinsu, ina mai tabbatar miki da cewa abokina yana sonki, abunda yasa ki ka kasa gane kansa wannan dabi'un naki marasa kyau! shi mutum ne wanda baya son raini ko kadan, yana da zafi! shiyasa bana so kije gidansa da wannan dabi'un naki, don Allah kiyi hakuri ki dauka cewa auransa alkairi ne ki zauna lafiya dashi da 'yan uwansa."


Baki ta ta'be da fadin.'' Asp ni ba zan yarda da wannan maganganun naka ba, kawai kana so ka tsara ni ne idan ba haka ba yaushe zaka zo kana fada min cewa yana sona ai da yana sona ba zai so bacin rai na ba, sannan duk abunda nace ina so sai yayi min amma tsakanina dashi kullum ba'kar magana kafada masa cewa a shirye nake idan ya bukaci ya zauna lafiya dani kansa, idan kuma tashin hankali yake bukata ashirye nake."

Da sauri ya tare ta da fadin." Mugun ji da mugun gani Allah ya tsare mu,

Please Login or Register in order to submit comment