Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fita ranta a mugun 'bace! addua ce kawai zata shiryar musu da ita.

Hawaye masu zafi suka dina sauka a saman fuskarta, wannan tozarci dame yay kama? kamar ita 'yar gata gaba da baya amma a kaita gidan aure babu kaya sai kayan miji wanda ta raina bata daukashi a bakin komai ba, kwata-kwata ba'ayi mata adalci ba.


Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, da sauri ta dauki wayar tasa a kunne sai ajiyar zuciya ta saukewa cikin kuka tace." Bana bukatar komai naka a gurin da zan zauna, ka kwashe komatsanka zanzo da nawa baka isa na dogara da kai da abunka ba."


Tun wayewar gari ya tsinci kansa cikin walwala da farin ciki, wanda shi kansa ya kasa gane dalilin.............Wannan shine dalilin yasa maganganunta ba suyi masa zafi ba, yay murmushi irin wanda ya saba kafin yace." To ke meye na damuwa bayan baki da niyyar zaman auran, ai zuwa da kayan daki zai miki wahala shiyasa na hutashsheki, bayan haka kuma nima haka na samu gidan cike da kayan more rayuwa gwamnati ta zuba min, kada ki damu sashenki daban sai kin so zaki ga wani kuma baki da matsalar komai, wannan dalilin yasa na shedawa Maimartaba cewa ke kadai nake da bukata."

hanci taja kamar za tayi magana sai kuma taja bakinta ta tsuke kokarin kashe wayar take yayi saurin fadin." 'Karfe nawa ma za'a daura auran."?

A kufule! tace."Ban sani ba."!! Kashe wayar tayi tana tsaki sai numfarfashi take na takaici da 'bacin rai!

Dariya yay mai yawa kafin ya ajiye wayar ya nufi toilet cikin wani irin farin ciki wanda ya jima be tsinci kansa a ciki ba.


*'DAURIN AURAN* Ya samu halartar manyan mutane sarakai 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa daga kowace jaha, daurin auran yayi albarka da yawa daga cikin mutanan da suka halarci daurin auran sunyi mamakin rashin halartar angon, sai dai Asp beyi kasa a gwiwa ba gurin sheda musu halin da ake ciki, hakan yasa wa'inda ba su sheda da UMAR din ba suka sheda dashi da jamurtarsa amma mafi akasari jama'a sun san shi a hoto da kuma gidajen television................ Asp bai samu kansa ba sai da ya tabbatar da cewa yasa jama'ar da suka samu damar hallatar daurin a auran a mota, da yawa daga cikinsu 'yan uwan UMAR din ne da suka dinga turereniya gurin zuwa daurin auran. wanda aka daura a garin KANO a fadar maimartaba Sarkin gari..




*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/2/22, 18:21 - Buhainat: _Ina muku tallan group dina mai suna_
*MAR'ATUSSALIHA*
*Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin 0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta wannan number... 07084653262*



*51&52*
Fitowarsa daga wanka yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa, koda ya dauki wayar ya duba sai yay murmushi domin ganin sunan wanda yake tsammani a fuskar wayar

Yasa wayar a kunnanshi tare da sallama a bakinsa.

Daga daya bangaran Asp ya sauke ajiyar zuciya da fadin."Alhamdulillhi komai ya kammala an daura aure cikin farin ciki da mutunta juna kowa ya kasance cikin walwala da farin ciki, bayan haka daurin auran ya samu halartar manya mutane daga kowane sassah na kasar nan, anyi taro an tashi lafiya duk jama'ar da suka samu damar halartar daurin auran daga b'angaran ka kama daga 'yan uwa da abokan arziki da kuma yaran ka yanzu haka suna kan hanyarsu ta komawa gidajensu da ikon Allah, muna rokon Allah ya bada zaman lafiya a cikin wannan auran sannan ya mayar da kowa gidansa lafiya."

Numfashi ya sauke bayan k'are maganar Asp din yace." Na rasa da wane baki zan mika godiya ta a gare ka, hakika ka cika mutum wanda ya tara duk wasu abubuwan da ake da bukatar mutumin 'kwarai ya kasance, wallahi wayewar yau haka kawai na tsinci kaina wani irin farin ciki wanda na kasa tantance ko na menene? bana gari ina wata uwa duniya ka tsaya min akan muhimmin al'amarin da cancanta ace ni nake tsaye a kansa, Asp da izinin Allah ba zan baka kunya ba, yanda ka tsaya kai da fata kaga tabbatuwar al'amarin nan, to nima nayi maka alkawari zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin na zauna lafiya da yarinyar nan, kafi karfin komai a gurina, duk irin kin al'amarin nan da nake tunda ka shiga cikinsa dole nayi mubaya da kai da abunda kake so nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkairi ya bar mana zumunci."

Murmushi yay da fadin." Haba babu komai wannan ba wani abun damuwa bane, dama ni fatana ka yarda ka amince dari bisa dari da wannan auran, domin haka kawai nake maka sha'awar auran yarinyar duk da a zahiri kai ka nuna cewa ba irinta kake da bukata ba, wannan dalilin ba zai ha naka nan gaba ka auri wacce zuciyarka take so ba tunda kana da damar hakan, nagode sosai da yanda kake mutuntani kana kar'bar shawarwarina daga karshe nake sake yi maka fatan alkairi da samun zuria dayyiba."

Cikin jin dadi ya amsa da ameeen ya rabbi Allah ya saka da alkairi mutumina."

Cikin zolaya yace."Yanzu zan shiga cikin gidan domin samun dauko maka hoton amaryar taka ko baka da bukatar hakan."?

Hannu yasa ya dan sosa sumar kanshi kafin yayi dan murmushi irin wanda ya saba, yace." Ina da bukata mana, ba kaji bahaushe yace."Amarya ko tabuzuzu ce tana rike da kambutan sarauta ba to ballantana ita wannan *GIMBIYA* ce mai lasisi wallahi haka kawai naji ina so nayi tozali da ita."

Asp ya kyalkyala da dariya da fadin." Allah mutumina ai dama ni na san duk wannan abun da kake iya fatar baki ne kana son yarinyar nan kawai ba zaka fito fili ka nuna ba."

Shima yana dariyar yace."Haka dai kake hasashe amma ni yar hanzu bana jin sonta a cikin zuciyata."


Yace."Okey to shikkenan mu bar wannan maganar amma ni na san akwai ranar da tarihi zai maimaita kansa."

Shuru yay bece komai ba har yanzu da kyakykyawan murmushi a fuskarsa sai wani sosa sumar kanshi yake kamar wani mara gaskiya.

Asp din yace."Zan kashe waya zuwa an jima zaka ji ni."

Yace."Okey to shikkenan babu damuwa sai na jika din." Sallama sukayi da juna kafin kowa ya kashe wayarsa.


To a can gidan Uwale kuwa hayaniya ce kawai take tashi tun bayan dawowar mazan daga gurin daurin aure suka taru a gidan tare da sauran 'yan uwansu mata kowa na fadin albarkacin bakinsa.

Da yawa daga cikinsu sun ji dadin kasancewar al'amarin, amma kuma akwai wa'inda suke ganin kamar hakan cin fuska ne da kuma rashin adalci idan akayi duba da irin halarcin da Hamra'u tayi masa bai cancanta ace saboda yayi arziki ya samu duniya ya juya mata baya ba, ita ya kamata ace ya fara aure kafin wata mace.

Uwale da yake tana da hankali da tsinkaye ta dinga nusar dasu domin su fahimci cewa shi UMAR din bashi da laifi domin yarinyar bashi akayi ba wai don yayi arziki zai guji auran ita Hamra'un ba, kuma ya tabbatar mata da cewar zai auri ita Hamraun a matsayin matarsa ta biyu...........Duk da wannan bayanin da tayi musu hakan besa hankalinsu ya kwanta ba domin ita mahaifiyar Hamra'un ma kasa zama tayi a gidan rai a bace ta tattara 'ya'yanta suka tafi........'Bangaran Ita Hamra'un, abun babu dadi domin tun waye war garin ranar take kuka duk ta tsangwami kanta da kanta gani take kamar bukatarta ba zata biya ba , haka kawai take tsoron hada kishi da 'yar sarautar tun ganin farko da tayi mata jikinta yay sanyi! 'Kawarta Zabbah da tazo ta sake rikirkita ta da cewar had'a kishi da 'ya'yan sarauta bala'i ne domin basa barin kishiyarsu ta zauna lafiya babu wanda be san gidan sarauta da asire-asire ba, saboda haka dole itama sai ta tashi a tsaye mutukar tana so bukatarta ta biya.

'Bangaran uwar Hamra'un ma maganar da suke tattaunawa kenan da yar uwanta, inda suke zuga ta kan cewa lallai dole ta tashi a tsaye domin ganin 'yarta ta auri UMARU idan ya kama tabi malamai a kansa ba damuwa bace tunda duk wani abu da akayi masa shi ya janyo dalilin rashin adalcin da yayi musu, idan ba haka ba mai zai sanya yaje ya auri wata bayan kowa ya san abinda yake tsakaninsa da Hamra'u, ta bauta masa sosai ta kori duk masu neman auranta akansa, ta zauna zaman jiransa, rana tsaka saboda yayi arziki zai je ya auri 'yar sarauta, ya wulakanta yarinyar da tayi masa halarci, wannan dalilin yasa suke zugata kan cewa lallai ta nemi taimako a gurin malamai domin janyo hankalinsa, idan kuma ta zauna to tana ganin daula da jin dadi zasu wuce 'yarta wacce akayi gwagwarmar tare da ita.

Sosai Dayyiba mahaifiyar Hamra'u ta dauki hudubar 'yan uwanta tasa a zuciyarta cewa gobe zakara ne zai bata sa'a yo ita da take a cikin garin Katsina to me zai gagareta, akwai malamai iri-iri wa'inda zasu taimaka mata, duk asirin da ake fadi cewa gidan sarauta suna dashi, to ita ta dauki alwashin bugawa dasu.

Tofah!!!9


*****

Yayi ta tsumayin Asp din shuru be turo masa hotonan ba, agogon dake daure a hannunsa ya duba awa biyu kenan da wayarsu, ko wane irin hoto ne yaci ace an dauka ya turo masa haka kawai ya 'kagauta ya kalli kwalliyar amaryar tasa.

Number sa ya nemo ya kira cike daso ya daga wayar, sai duk 'kagautarsa bai samu abunda yake so ba, domin wayar haka ta k'araci 'burari Asp din be daga ba.

'Karamin tsaki yaja tare da dan ya mutse fuskarsa, ya ga alama fa zuciyarsa ta nema ta takura masa.

Ajiya wayar yayi, ya dauki d'ayar dake saman drowar yana kunnawa ya shiga WhatsApp number tace kawai data Asp a layin.

Ya duba status Asp ya dora hotonan daurin auran........Jama'a birjik babu masaka tsinke harabar gidan sarautar cike da jama'a, murmushi kawai yake yana cigaba da duba status din.......... Kowa ya halarci daurin auran a cikin abokan aikinsa da 'yan uwansa da kuma yaransa su Alba da sauransu. hoton karshe shine Maimartaba Omar tare da maigirma Governor katsina wato Nasiru Alkanawi dashi Asp din da kuma mutuminshi abokin fad'ansa wato Commissioner of police wato Murtala Kabiru, serving din hoton yay a ajiye a gallery hoton yayi masa kyau sosai.

Yana k'okarin sauka sak'on ta ya shigo, da sauri ya shiga yana dubawa hotonta ne kusan goma ta turo masa.

Ya dinga duba hotonan d'aya bayan d'aya yana jin wani bala'in kishi na sukan zuciyarsa.

A zahiri dai shi ta turowa hotonan, amma a cikin rashin sanin ta, sai kawai ya tsinci kansa da jin haushin kansa da kuma kishin kansa da kansa.

A zahiri shi ya kamata ace ta turowa hotonan a matsayinsa na miji a gareta. amma ta turawa wani wanda bata da tabbas a kansa, wannan ya nuna masa cewa zata iya aikata komai bayan da auransa a kanta.


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dauki daya daga cikin hoton nan data turo masa yay magana a kansa.

"Wannan hoton yayi kyau sosai my love kallonki a yanzu ya jefe ni cikin wani hali mai wuyar fassaruwa, gabadaya kin gama kashe min jikina ina jin sha'awar kasancewa dake a halin yanzu, my lov ina kishin wannan mijin naki kada ki bari ya kusanceki ballantana wata mu'amula ta shiga tsakaninku, ki rike min amanar kanki."

Koda ya tura mata sakon be sauka ba har sai data ta duba, ba tace masa komai ba sai emoji data tura masa mai dauke da alamar kuka da ban hakuri.....Daga haka sai kawai ta sauka,

Cikin jin haushin abinda tayi ya kashe wayar ya ajiye yana nazari da tunani akan al'amarinta.


Kiran sallar la'asar ne ya katse tunaninshi, da sauri ya tashi ya nufi toliet domin daura alwala. koda ya fito daga bandakin kai tsaye masjid ya nufa wanda yake cikin barrack din da suke zaune........Da yawa daga cikinsu arna ne musulman cikinsu kadan ne, amma duk da hakan akwai kyakykyawar alaka a tsakaninsu domin tsayin kwanakin da yayi tare dasu bai ta'ba samun matsala da kowa ba.

Bayan fitowarsu daga masjid din Adewale abokin aikinsa wanda ta su tazo daya ya tsare shi da hira, hakan ya zauna ya biye masa yana ta bashi labarin ban dariya cikin harshan turanci yake magana domin hausar tashi bata fita sosai.

Kwanakin da yayi a cikinsu gami fa cud'anyarsa dasu yasa kwakwalwarsa ta kara bud'ewa dama can sama-sama yana jin turacin amma ba kamar yanzu ba, ya na ji sosai kuma idan ta kama yana sauya harshe yayi magana tamkar wanda ya jima a cikinsa.

Adewale mutum ne mai barkwanci shiyasa tasu tazo d'aya duk sanda basu da aiki sukan zauna guri daya yay ta sauraran shiremansa yay ta kyalkyala dariya kamar bashi ba.

Kiran Asp ne ya shigo wayarsa yasa a kunne tare da sallama Asp din yace. 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~"Ka duba tuntuni na tura maka sakon."

Yace."Okey to ina godiya sosai naje sallah shine dalili." Yace."Ba damuwa yanzu Ina shirye-shiryen d'auko hanya amma ina tsammanin jirgi zamu bi."

Yace." Saboda me? zaku bi jirgi ina Kano ina Katsina ? da har sai kun shiga jirgi."

Yace." Wannan amaryar tamu ai daban take da sauran mata, idan da akwai abunda yafi jirgi to a ciki zan kawo maka ita har Katsina."

Yayi yar dariya da fadin." Kana d'aurewa karya gindi wallahi, amarya babu ango a kusa ina tausaya mata kwanan kad'aici."

Asp din yay dariya sosai kafin yace."Ka fara tausayawa kanka kafin ka tausaya mata dukkaninku ababan tausayi ne."

'Yar dariya yay irin wacce ya saba da fadin'' Na yarda da maganarka amma ka mi'ka min sak'on gaisuwata a gurinta ka sheda mata cewa daga yau ta fara lissafin dawowata."

Yace."Wannan kuma aikin ka ne, domin saura kadan na kammala nawa, sauran kuma ya rage naka."

Kokarin magana yake Asp din ya kashe wayar

Ya cire wayar daga kunnansa yana murmushin da har yanzu ya rasa na menene.

Yana duba hoton nan Adewale ya leko da kansa.

Da sauri ya janye wayar don haka kawai yake jin kishin wani ya ga kwalliyarta.........duk da hakan sai da ya hangota, ya kyakyala da dariya yana sake le'ka kansa da fadin."Oga wannan yarinyar fa tana da kyau sosai ina san 'bakar mace domin tana da wani sirri na daban."

Wani irin kallo yay masa mai kama da harara kafin yaja karamin tsaki yasa wayar gaban aljihun rigarsa ya mike da fadin." Kai matsala ta dakai shiririta haka kawai daga ganin matar mutane kace kana so Adewale kana da son mata wallahi."

Yace."Ai sune jin dadin duniyar Oga hahahaha." Ya k'arashe maganar cikin dariya.

Girgixa kai kawai yay yana kallonsa da tarin takaicin shirmen da yake yace." Ni zan shiga ciki na huta kafin magriba domin naga alamar yau shirmen naka yafi na kullum."
Shima tashi yay da fadin." Nima ina da uzuri yanzu zanje na gabatar sai mun hadu da daddare." Hannu ya daga masa kawai, yana kallonsa yayin da yake kokarin barin gurin.

Kansa kawai ya girgiza kafin shima ya bar gurin cike da so ya samu zama a nutse domin samun damar kallon hotonan amaryar tashi a tsanake.



*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
2/3/22, 15:49 - Buhainat: _Ina muku tallan group dina mai suna_
*MAR'ATUSSALIHA*
*Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin 0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta wannan number... 07084653262*


*53&54*
Pictures din data tura masa a rashin sanin shi ta turawa, sun bambamta da wanda Asp din ya turo masa a yanzu, wanda ta tura masa a yanzu tayi ado sosai sa'banin wanda ta tura masa adon da tayi bai kai na yanzu ba, les din ne dai a jikinta amma kamar yafi na dazu kyau da kudi, riga da siket ne dinkin ya karbi jikinta sosai tai kyau tai ado da gold wuya da hannu sai tai amfani da set din jaka da takalmi da mayafi iri daya, mayafin a gefen kafada ta ajiyeshi, duk jikinta a waje breast dinta sun matse a cikin rigar don har sun dan fito daga sama, kishin hakan ya dinga sukan zuciyarsa ya cigaba da kallon hotonan wanda duk rabinsu ita da 'yan uwanta ne maza da mata sai kuma wanda Asp din ya shiga akayi musu ita dashi, shi kansa Asp din haushi ya bashi ya dinga jin kishinsa a ranshi, ganin yanda ya tsaya daf da ita bayan duk ga tsaraicinta nan a waje a maimakon yay mata magana ta yafa mayafinta tunda dai su 'yan uwan nata basu san abunda ya dace ba, shima sai yabi sahun su suna abunda bai dace ba........'Karamin tsaki yaja ya cigaba da duba hotonan yana kokarin danne abunda ke cin zuciyarsa.


hoton ta ida Sakina shine ya dauki hankalinsa, kallon fuskar Sakinar da shigar dake jikinta shi kadai ya nuna masa zahirin ta, duk rashin arzikin dinkin dake jikin Zinat din yafi na ita Sakinar mutunci, domin gabadaya wuyar rigar dake jikin Sakinar net ne nonowanta duk sun fito gashi rigar ta matseta sosai ba mayafin arziki a jikinta sai wani uban gashin doki da tayi ado dashi, gabadaya kamar ba 'yar musulmai ba..........Murmushin dake kan fuskokinsu shine ya nuna masa cewa da akwai kusanci mai kyau a tsakaninisu domin hannuwasu ma a rike yake dana juna.........Gabadaya yarinyar bata kwanta masa a rai ba, ba tare da ya gama kallon hotonan ba, ya kashe wayar ya ajiye saman drowar haushi duk ishe shi.



Koda Asp din ya kira shi domin ya shada masa cewa suna jirgi shi da amaryar tasa, sharrin zuciya sai kawai ya tsinci kansa da jin wani iri a ranshi, sai da yayi namijin kokari kafin ya iya yi masa godiya, Asp din yaji muryarsa a dakile, yace."Mutumina ya akayi ne naji ka wani iri."?

Ya dan yi gyaran murya da kokarin kawar da abunda yake ransa yace." Normal ba matsala idan kun sauka ka kira ni yanzu ina dan uzuri ne."

Yace."Okey to shikkenan ko na baka amaryar ne.''?

Girgixa kai yay da fadin." Aa bar ta kawai zan kira ta an jima idan ta huta." Yanda yake jin haushinta ya san ba zasu wanye lafiya ba, shiyasa ya fadi haka.

Wayar ya kashe ya ajiye saman drowr ya tsirawa kasan kafet ido.

Alamu sun nuna yana son yarinyar nan, domin da baya sonta ba zai damu kansa har ya dinga kishi a kanta ba.

Asp yafi karfin komai a gurinsa, kuma ya sheda cewa ba zai ci amanarsa ba, amma yana mamakin yanda zuciyarsa take raya masa wasu munanan abubuwa akan Asp din wanda yayi imani da cewa hakan ba zata faru ba, auziyya yayi a fili tare da korar shaidan din da yake so lallai sai ya nuna masa aibun abokin nasa.


Hadiman ta wato masu yi mata hidima tare da motocin kayan garar da akai mata sune suka fara sauka, duk girman store din sai da yay kadan gurin daukar kayan garar, babu abunda babu na dangin ci da sha, da store din ya cika sai kawai aka jibge ragowar kayan abincin a harabar gidan.

Asp sai da ya tabbatar da cewa komai ya kammala amarya na dakinta sannan hankalinsa ya kwanta ya godewa Allah kafin ya kira wayarsa ya sheda masa duk abunda yake faruwa.

Yace."Asp nifa ban bukaci komai a gurinsu ba, me zai sanya akawo min abinci ina dashi ai ba wai ina bukata bane."

Yace."Al'ada ce kawai kada ka damu ba wai dan ka gaza ko don baka dashi sukayi maka haka ba alkairi ne kawai."


Yace."Idan za suyi ai sai ayi dai-dai gwargwado amma ace har mota goma ta kayan abinci me zanyi dasu mybe ma kafin azo kan wani ya lalace kawai ka diba iya wanda kake bukata, sauran kuma zanyi magana da Uwale domin ta bawa wanda ya dace."

Yace."Hakan da kayi yayi dai-dai, amma ni kam babu abunda zan dauka acikin wannan kayan, akwai mabukatan da suke nema su ya kamata a rabawa.

Yace."Shikkenan tunda kace haka idan akwai masu bukata a bangaran ka sai ka basu duk abunda ya dace."

Yace."Okey babu damuwa zan duba insha Allahu.

Godiya yayi masa sosai tare da ban gajiya kafin suyi sallama da junansu.


Tun bayan fitar Asp din daga gidan, take bin dakin da kallo, duk iya hangenta bata hango abunda zata kushe a dakin ba, daga bedroom din har falon komai na kasar waje ne, kuma tsarin yayi mata babu abunda zata nema komai a kwai wanda zata bukata, toilet biyu d'aya a uwar daki d'aya kuma a falon, sai kicin dake can gefe a dai cikin falon, koda ta duba kicin din shima a shirye yake da komai na bukatar yau da gobe, hakan yayi mata dadi dama bata bukatar wani ya shiga sabgarta a gidan idan ba hadimanta ba.

Ta gama duba ko'ina ta koma bedroom din ta zauna gefen gado tare da zabga tagumi, to yanzu fa wata sabuwar rayuwa za tayi tare da wasu sabbanin mutanan da bata san ya hallinsu yake ba, koda yake a shirye take da kowa duk wanda ya bukaci zaman lafiya da ita bata da matsala amma ba zata yarda da raini daga gurin kowa ba ciki kuwa harda wanda yayi dalilin zuwanta gidan.


Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin akan irin zaman da za tayi da bagidajen mijin nata. Tsaki taja mai tsayi ta girgiza kai a fili tace." Idan yaso mu zauna lafia zamu zauna idan kuma yazo da tsiya to gidan ya tarar domin ba zan yarda da rainin hankali ba." Kamar dashi take maganar sai girgiza k'afafu take.

Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, data duba taga shine sai taki d'aga wayar har sai da ta katse.

Uzuri yay mata dan be kawo cewa iskanci ne ya ha nata daga masa waya ba.

A karo na biyu sai da ta kusa katsewa ta daga, ciki ciki tai sallama.

Be damu da abunda take ba ya amsa mata da fadin." Ya kike? ya kuma hidima da jama'a."?

Shuru tai ba tace masa komai ba.

Yace."Kin yi shuru ko baki da magana dani."?

Ta dan ya mutse fuska da fadin." Umm! yanzu bacci na keji okay sai da safe." Kokarin kashe wayar take yay saurin fadin." Kada ki kashe waya ina da magana dake."

Ta fasa kashe wayar da fadin "Ina jin ka."

Jim yay kafin yace."

Please Login or Register in order to submit comment