Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a duniya tayi mana kallon mutanan banza."


Yace." Ba nufina kenan ba, nafiso duk abinda zai faru a bari ta haihu tukkuna kinga tun bayan dawowarmu babu kwanciyar hankali, na san kuma dalilin jin wannan maganar ne."


Tace." Umaru dole ne fa kayi hakuri da duk abunda zai biyo baya domin lusarin namiji baya ta'ba iya zama da mace biyu uku ko hudu, ka zama jarumi jajurtacce! akan duk abinda zai faru, bayan haka kuma ya zama dole ka jawa Hamra'u kunne ta kiyaye ta kuma sauya munanan d'abi'un da take yi kishi ai ba hauka bane."


Ya kalleta da fadin." Me tayi Hamr'un."? Girgiza kanta tayi da fadin." Aa ni ba zan fada maka komai ba, amma lallai ka ja mata kunne akan abubuwan da take aikatawa."


Ransa ya 'baci! idan ya fahimci maganar wato Hamra'u ta samu hanyar cin mutuncin matarsa saboda tana da tabbacin cewa ta kusa zama dai-dai da ita, wannan shine tunanin da yake, Hamra'u taki dawowa saboda akwai wani abu da tasan ta aikata       

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  na rashin kyautawa.
sosai yayi mamakin al'amarin beyi tsammanin cewa zai samu matsala da yarinyar ba, saboda yana da tabbacin nutsuwa da hankalinta.


Sai wajejan goma da wani abu ya shiga gurinta, lokacin ma ita har taci abinci tayi shirin kwanciya ba ta dai kwanta ba wayarta take dubawa.

Yayi sallama ya shiga dakin kamar mara laka a jikinsa.


Babu yabo babu fallasa ta amsa tana kallonsa har ya zauna kusa da ita.......Tace." Sannu ka dawo lafiya."?

Wani sanyi ya sauka a zuciyarsa, sam bai tsammaci haka da gurinta ba.

Da kwarin gwiwa yace." Lafiya ya kika wuni ya babyna."?

Tayi shuru ba tace komai ba.

Ya sake matsawa jikinta yana nanik'arta. ba tace komai ba, amma gabadaya tsigar jikinta ta tashi jinsa a kusa da ita yana nema ya haifar mata da matsala.


Ya sassauta murya da fadin." My love ki kalleni za muyi magana ta fahimta."

Ta jim na minti biyu kafin ta kalleshi. ya dinga sarrafa kwayoyin idonsa a kanta, gabadaya jikinta ya mutu, dama abinda ya keso kenan.

Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya kafin ya lalubi hannunta ya rike cikin nashi, a hankali yace." Hamra'u bake taci mutunci ba, ni taciwa mutunci kuma dole na nuna mata muhimmancinki kiyi hakuri kinji ko."

Murmushin takaici tayi kafin tace." Waye yace maka Hamra'u taci mutunci na."?

Yace." Uwale ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku kuma raina ya 'baci sosai wannan dalilin yasa na yanke shawarar kiran wayarta a gabana ta baki hakuri."


Ta kalleshi tana so ta gazgata maganarsa, kamar gaske dai gashi nan yana mata dadin baki.

Ya fito da wayarsa ya nemi number Hamra'un.....cikin ikon Allah wayar ta shiga ba'a samu matsalar network ba.

Bai wani saki fuska ba ya amsa gaisuwarta kafin ya dora da fadin." Hamra'u abinda ki kayi ban ji dadi ba, kuma ba Gimbiya ki ka tozarta ba ni Umaru ki ka wulakanta sanin kanki ne cewa mutanan garin *Kafur!* muna da karrama bako da mutuntashi me zai sanya ki wulakanta min mata saboda kin ganta a mahaifarki."


Murya na rawa ta fara rantse-rantse da fadin." Ya saurara tayi masa bayani.....'Kin sauraranta yayi yace." Mutukar kina so mu shirya da juna dole ki bata hakuri akan abinda ki kai mata wannan ne kadai zai sanya na saurareki.

Sai kawai ta fashe da kuka da fadin." Wallahi ni ba zan bata hakuri ba, kuma duk wanda ya fada maka cewa na tozarta ta Allah ya isa tsakanina dashi, ka tambayi Uwale itama idan zata fad'i gaskiya ai a gabanta komai ya faru! sau biyu tana gaura min mari! a fuskata amma saboda son zuciya za'a ce na bata hakuri! ni kam duk abunda za'ayi sai dai ayi ba zan bata hakuri ba."


Yace." Ashe baki da mutunci dama."? Shuru gabanta sai bugawa yake! yace." Okey shikkenan tunda haka ki ka za'ba zan baki mamaki." sai kawai ya kashe wayarsa yana jan tsaki!


Ta kalleshi da fadin." Nifa idan saboda ka faranta min rai kake wannan abun to ka daina, domin hakan ba burge ni kayi ba...........koda yarinyar nan tayi min laifi na hukuntata tuntuni ka dai ja mata kunne ta kiyaye! idan kuma taki za fuskanci b'acin rai."

Yace." Akan hakan zan iya janye auranta sai me."?

Tace." Duniya za tayi Alla wadai dakai! wane irin hallaci ne yarinyar ba tayi maka ba, ai samun nutsuwarka ka aureta, ni bani da matsala domin ban san abinda Allah ya rufe a tsakaninku ba."

Yace." A da can baya ina sha'awar auranta saboda kyawawan halayenta amma yanzu duk ta fice min rai saboda d'abi'un data sauya, bayan haka kuma mutukar ba zata zauna lafiya dake ba, to kamar yanda na fada a farko zan iya janye auranta."

'Yar dariya tayi tare da girgiza kanta tace." To Allah ya rufa asiri ya tabbatar da alkairi ni dai duk wanda ya nufe ni da sharri kansa zai koma."
daga wannan maganar ba ta sake cewa uffan ba, ta shige cikin bargo tana gyara lulluba, tashi yayi ya fita, minti goma ya dawo dakin, ya kashe fitila kai tsaye gadon ya nufa ya kwanta kusa da ita, kamar zai daure ya danne abinda ke cinsa, sai ya kasa ya matsa jikinta sosai yana shanshana sassan jikinta, gabadaya ya rikice jikinsa sai rawa yake ya birkito ta rungumeta yayi tsam a jikinsa yana kesses din fuskarta da wuyanta.



*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/19/22, 15:08 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._


*113&114*
Da asubar fari 'Dayyiba ta fice daga gidanta da mummunan kudiri a zuciyarta. wani k'aramin kauye ta yiwa tsinke anan take sanya ran biyan bukatar ta, to duk da sammakon da ta buga sai da ta samu kusan mutum biyar suna zaune tsumayin fitowar wacce ta shiga zauran malamin. Dayyiba ta kama layi ta zauna a kusa da wata mata hankalinta kaf yana kan hirar da suke da abokiyar tafiyarta.

Magana suke tattaunawa akan abinda ya kawosu gurinsu bokan wacce tayi kamanceceniya da wacce ta kawo ta, ta kalli matar da fadin." Nima abinda yake tafe dani kenan, ni abinda nakeso ma a rabasu gabadaya ko kuma a haukatata ta shiga duniya."

Matar tace." Wannan duk mai sauki ne mutukar kin cika sharud'ai to bukatarki za ta biya."

Tace." A shirye nake bani da matsala duk abinda akace zanyi mutukar bukatata za ta biya."

Wannan shine 'karshen magana.......Fitowar matar dake ciki ya katse maganarsu, wacce take kan layi tayi saurin shiga ita kuma wacce ta fito daga zauran ta tsaya tana musu sallama da wani irin murmushi a fuskarta da alama akwai nasara a kan abunda tazo dashi gurin.

To d'aya bayan daya suke shiga har layi yazo kan Dayyiba ta shiga ta gurfana gabansa kafin ma ta fara yi masa bayanin abinda yake tafe da ita yace." Kina tafe da aikin babban aljani wanda yake da bukatar kafa hud'u ina fatan kin fahimta."

Gabanta yana faduwa tace." Malam har aikin nawa ya kai haka."?

Ya buga mata tsawa da fadin." Tashi ki fita ashe da sauran imani ta tare dake tunda kike jayayya damu."

Tace." Ayi hakuri ranka ya dad'e ina neman alfarma na bada kafa biyu amma samuwar kafa hud'u a gurina zai yi wuya."

Ya shiru yana kallon wani jan koko mai kurji-kurji cike da jini a ciki.

Ya kalleta da fadin." To dai gaki gashi nan yana kallonki sai kiyi masa bayani idan ya amince.

Gabanta na bugawa tace." Ubana idan zai yuwu zan bada rago mai koshin lafiya a taimaka min."

Shuru gurin yayi bayan k'are maganarta, can kuma bokan ya kama wata girgiza farar kumfa na fitowa daga bakinsa, ya kai minti goma haka kafin ya dawo hayyacinsa duk yayi wuri-wuri sai uban gumi yake.

Ya kalleta da fadin.'' Kin ci sa'a yau yana cikin walwala ya kuma amince da maganarki, sauran aikin kuma ya rage naki idan kika kuskure wani to aikin zai dawo kanki.

Cike da farin ciki tace." Na gode ranka ya dade zan kuma kiyaye da izinin ku."

Yace." Da daddare karfe biyu ki samu bakin kwatami (kazamar kwata) ki yanka ragon da hannun hagu ki nayi kina zagin uwarki da ubanki."

Tace." To an gama ranka ya dade.......Ya siffan ta mata kalar ragon da ake bukata sannan ya bata wata laya yace a gurin da ta zubda jinin zata binne.

Cike da farin ta dawo gida, kuma hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar ta samu kalar ragon da aka bukata.

Karfe biyu na dare ta fito babu tsoro babu imani ta fara aiwatar da mummunan kudirinta tana yanka ragon tana zagin uwarta da ubanta.........Ta gama ta haka rami da wukar hannunta ta binne layar....kamar saukar aradu taji wata tsawa! "Tashi ki gusa daga gurin."! a gigice! ta shige gida kafafunta na karkarwa.

Koda ta duba gurin da safe wayam! babu alamun anyi wani abu! hankalin ya kwanta ta koma gida da tunanin abinda zai biyo baya.


A daran kwanan soyayya sukayi sai dai kuma gari yana waye wa suka tashi da bala'i da masifa! kamar karnuka! ya nayi ta nayi a fusace! ta jefa masa kwalbar turare a goshinsa a take gurin ya kumbura! shima ya fusata ya zazzabga mata maruka ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa na wani tafasa! gabadaya hankalinsa yayi kan Hamra'u

Koda ya isa ofis din kasa samun nutsuwa yayi ya kasa aikata komai, kawai sai ya nufi ofis din Asp yana sheda masa cewa zai tafi *'Kafur* 'Kauyensu.

Asp din yace." Allah yasa dai lafiya domin naga kamar baka hayyacinka.

Budar bakinsa yace." Daf yake da ya rabu da Zinatu saboda wasu dalilai.

Asp ya tsirawa goshinsa ido da fadin." Kun samu matsala kenan Umaru wai me yasa kake biye mata kuna abu sai kace kananun yara."

A fusace! ya daga masa hannu da fadin." Kaga saurara Asp na lura da kai dama tuntuni kai baka san laifin yarinyar nan komai tayi dai-dai ne a gurinka, okey shikkenan ni zan iya rabuwa da ita bani da damuwa kai ka aureta."

Asp ya dinga jin maganar nayi masa kuwwa! a kunne hankalinsa yayi masifar tashi! kokarin magana yake amma ya rasa abinda zai ce, yana kallonsa ya fita daga ofis din ya kasa aiwatar da komai.

Ya dauki wayarsa ya kira Zinatu, lokacin tana zaune bayan taci kuka ta koshi abin duniya isheta jin ta take kamar a cikin kurkuku bata so ta bude ido ta ganta a cikin gidan, domin hotonansa na da suke kafe a dakin duk tabi ta farfasasu.


Fashewa tayi da kuka bayan ta daga wayar.

Yace.'' Ki daina kuka Zinat na kira ki ne domin kiyi min bayanin abinda yake tsakaninku.

Cikin shashshekar kuka take fadin." Na tsaneshi bana k'aunarsa bashi da adalci.

Yace." Me yayi miki na rashin adalci ko dan zai kara aure ki ka tsaneshi."?

Shuru tayi ta gaza furta komai in banda ciwon kai babu abunda ke damunta.

Ya dinga magana tayi masa shuru, kawai sai ya kashe wayar, ya kira Madam tare da bata umarnin shiga gidan domin ta rarrasheta.

'Bangaransa kuwa hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ganshi ya sauka a cikin garin *'Kafur!* tukkuna.

Kai tsaye gidan Kawu Ado ya nufa, lokacin dawowarsa kenan daga kasuwa, ganinsa a birkice ya tayar masa da hankali, sai dai kuma da yaji abinda yake tafe dashi hankalinsa ya kwanta, da farin ciki a tare dashi yace." Ai wannan mai sauki ne Umaru, za'a daura auran a yau babu matsala yanzu zamuje tare da kai domin mu tattauna maganar da mahaifin yarinyar domin yaji abinda kake tafe dashi.

Yace." Ba damuwa Kawu tashi muje domin a yau din nake san na koma gida."

Kusan a tare suka tashi, kai tsaye kuma can gidansu Hamra'un suka nufa.

Abu kamar al'mara gari ya dau'ka! jama'a sukayi dafifi! a kofar gidan malam Shafi'i Kawu Ado ya bada kudi aka siyo goro da alawa....Shi kuma angon ya ajiye dubu hamsin kudin sadaki....Limami ya daura aure bayan gabatar da sallar magariba.


Cikin gidan kuwa Dayyiba cike da 'yan uwanta da k'awaye da makota kowa da abinda yake fad'a.....Da yawa sunfi gazgata cewa ta shiga ta fita a cikin al'amarin, domin dai kowa ya san wata shida aka sa amma ko wata daya ba a cika ba an daura aure sai kace wasan yara.


Hamra'u kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki, hakika babu abunda za tace da mahaifiyarta domin ta taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarta.


A daran ya dauketa suka kama hanyar gida. gabadaya tunaninsa ya tsaya cak! saboda duniyar ma gabadaya ta rikice masa ya rasa wane irin tunani zai yi, gani yake kamar duk abinda yake mafarki ne.


Cikin dakinsa ta kwana, kuma babu wani abu da ya shiga tsakaninsu, to ina kwanciyar hankalin da wata mu'amula zata wanzu babu ma sha'awa a tare dashi.


Da sassafe ta fita daga d'akin, lokacin yana toilet yana wanka. fitowar ta akan idon Marakisiyya, al'amarin da ya bata mamaki mutuka! ba tayi kasa a gwiwa ba taje ta sanar da Uwar dakinta abinda idonta ya gane mata.


Tace ta tashi ta taje....bayan fitar Marakisiyyar minti goma ta nufi sashen nasa...........Koda ta shiga basu kwashe lafiya ba, dan da abun yayi tsamari ma turo ta yayi ta fadi bakin kofa ya mayar da kofarsa ya rufe, ya cigaba da abinda yake.

Ta zauna taci kukanta ta k'oshi, ido jawur! ta fito daga sashen, sai sukayi kicubus da Hamra'un tayi wanka tayi ado sosai sai kamshin turare take.....kallon banza tayi mata kafin taja tsaki ta shige ta bar ta a gurin.

Girgiza kanta kawai tayi ta nufi gurin Uwale domin jin k:arshen labarin.


Ta sameta a zaune fuskarta akwai alamun damuwa.

Suka gaisa sama-sama kowa da abinda ya dameshi a zuciya.

Uwalen ce ta fara magana kamar haka......"Zinatu kiyi hakuri kinji ko, na san wannan abun shiryayye ne amma babu komai duk auran da ba'a gina shi ta hanyar Allah da Annabi ba, baya zuwa ko'ina kiyi hakuri da duk abinda za ki gani."


Tace."Uwale me yake faruwa ne? naga yarinyar nan Hamra'u sai shige da fice take a gidan, shin yaushe ma ta dawo? kuma naji kina maganar aure, ban san me yasa ba tun jiya muke rigima da mijina na rasa abinda nayi masa."


Murmushi takaici tayi kafin ta shiga warware mata abinda yake da akwai, tace." Ni kaina ban sani ba, sai yanzu da ita Hamra'un take sheda min cewa jiya da magariba aka daura auran shi Umar din da kansa yaje garin akayi komai a ka gama to kinji abinda yake faruwa.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." To saboda kawai zaiyi aure sai ya zama tamkar mahaukaci! gabadaya fa tsakanin jiya da yau ya fice daga hayyacinsa.

Tace." Ni kaina yau kwana biyu kenan rabon daya shigo mu gaisa da duk rintsi yakan shigo idan zai fita, sannan kuma idan ya dawo ma zai shigo ya dubani. wannan dalilin yasa nake zargin wani abu akan al'amarin.


Tace." Uwale idan da matsala ni zan tattara kayana na tafi gida hankalina sai yafi kwanciya bana san tashin hankali."

Ta kwantar da kai da fadin." Kada ki yanke wannan hukuncin Zinatu ki cigaba da hakuri duk abinda mijinki yake baya hayyacinsa. Asiri akayi masa."

Ido ta tsira mata tana mamakin maganar ASIRI to waye zai yi musu ASIRI irin wannan.


A tare suka shigo falon, duk suka zuba musu ido suna kallo....Ita Hamra'un kicin ta nufa, shi kuma ya zauna kusa da Uwale suna gaisawa.

Babu yabo babu fallasa ta amsa sai kallonsa take tana mamakinsa.........Ya dan duba agogon hannunsa da fadin." Uwale sai ki kaji sabon al'amari ko."?

Tace." Eh abun ya bani mamaki Umaru ya akayi ka sauya shawara."?


Kai tsaye yace." Hakan ne samun kwanciyar hankalina domin bana samun nutsuwa a tare da wacce nake rayuwa da ita.


Tace." Wannan maganar sam bata dace ba Umaru me yasa zaka sanja hali zaka kawo rashi zaman lafiya a gidanka."


Yace." Uwale ki bar wannan maganar don Allah nifa dama can dole akayi min yanzu ne na auri zabin raina."


Ta fusata! zuciyarta na tafasa! tace." Yanzu ma ba'ayi maka dole ba ka *SAKE NI MANA."!*

Innalillahi wa'inna ilahi raji'un! abinda Uwale take nanatawa kenan, lallai Dayyiba bata da Imani tana so ta raba sunnar ma'aiki.


Ta sake maimaita maganar kamar sabuwar mahaukaciya.....*"KA SAKE!* ni idan ka cika dan halak ne kai." Jikinta har karkarwa yake ta mike tsaye tana so taje gurin da yake zaune.


Ya mike a zabure! da fadin" Kada ki kuskura kizo nan sai kakkarya miki 'kafafu." yana gwada yanda zaiyi da hannunsa.......Ba ta tsorata ba ta 'karasa da fadin." Gani dama tun jiya kake duka na ka karya ni kaga abinda zai faru."

Ya daga hannu da niyyar zabga mata mari Uwale ta rike hannun tana kuka take fadin." Wannan wane irin tashin hankali ne Umaru anya ba za kayi wa kanka fad'a ba."

Hawaye masu zafi suna gudana a saman fuskarta tace." Uwale ki kyaleshi ya aikata abinda yayi niyya dama ai ba yau bane farko.

Tace." Aa ba za'ayi haka ba Zinatu kiyi hakuri ki koma gurinki insha Allah komai zai daidaita."

Hanci ta shaka kafin ta girgiza kanta ta juya da sassarfa ta fita daga falon.

Ya koma yana zauna yana wani irin nishi, sai gumi yake kamar wanda yayi 'yar tsere......Hamra'u dake tsaye da fulas din shayi a hannunta ranta ya 'baci ganin abinda takeso bai faru ba, jikinta a sanyaye taje ta ajiye fulas din kan daining ta koma kicin domin fito da sauran kayan breakfast din.


Ta shiga sashenta ta sanya Baraka ta hada mata kayanta gida zasu tafi .

Ta zaune gefan gado jikinta sai rawa yake ta nemi number Asp murya a dashe suka gaisa, tace." Zan tafi gidanmu ranka ya dade bahaushe yace." Ta inda aka hau ta nan ake sauka."

Da sauri yace." Zinatu idan na isa dake kada ki kuskura kije ko'ina kinji abinda nace miki ko."?

Kashe wayarta tayi bata tsammanin zata tsaya jiran wani abu.

Wanka tayi a gurguje! ta shirya, ta umarci hadimanta suka shirya.......Direban dake dawainiya da gidan ya daukesu a mota suka dauki hanyar *KANO*

Minti ashirin da tafiyarsu Asp ya shiga gidan, kai tsaye sashenta ya nufa........ya tarar ko'ina a rufe! hankalinsa a tashe ya nemi number wayarta a kashe.

Hannu na rawa ya kira abokin nasa yana ganin kiran yaki d'auka idan akwai wanda ya tsana a duniya yake jin haushinsa Asp din ne.

Yayi ta kiran wayarsa yaki dagawa, sai ya hakura ya shiga har gurin Uwale suka gaisa, anan ne ta san da cewar Zinat din bata gidan.

Tafi Asp din shiga tashin hankali, lallai babu shakka a wannan karan dole ta tauna tsakuwa dan aya taji tsoro.




*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/22/22, 07:32 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





*115&116*
Suna shirin tashi daga aiki mai girma Commissioner ya same shi a ofis, cikin girmamawa ya mika masa hannu suka gaisa kafin." Yace." Tunda naga mai girma da kansa to na san babban al'amari ne."

Murmushi yayi kafin yace." K'warai kuwa Umaru wani aiki ne ya taso sai naga da cewar kaja tawaga ma'ana ka zama jagora a tafiyar."

Yace." Insha Allah zan bayar da gudummawata.

Wata takarda ya fito da ita yana masa bayani cewa za suje *ran gadi* Zamfara saboda rashin kwanciyar hankalin da suke fama dashi.....za su hadu da jami'an tsaron garin domin kawo karshen ta'addancin da yake faruwa. gwamnatin garin tare da jami'an tsaron can suka bukaci wannan taimakon daga gurinsu domin suna sa ran idan ya shiga cikin al'amarin za'a samu maslaha."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.'' Ranka ya dade babu matsala yaushe ne tafiyar."?

Yace." Idan Allah ya kaimu gobe amma da Asubah zaku dauki hanya."

Yace." To Allah ya kaimu lafiya, amma me yasa ba'a za'ayi tafiyar da Asp ba."?

Girgiza kansa yayi da fadin." Akwai dalili shi akwai muhimman ayyukan da zamu gabatar tare dashi."

Ya mika masa hannu da fadin." Allah yasa mu dace." Ya amsa da ameen ya rabbi.

Sallama sukayi cikin mutunci da girmama juna. tun lokacin da Commissioner ya fahimci cewa Umar din ba irin mutanan da ake nuna su da yatsa bane ya kiyaye abinda zai kawo musu samun matsala domin ya fahimci cewar Umar din yana da babban matsayi a government house bayan haka kuma manya 'kasa suna ji dashi, domin shi kansa shugaban k'asa yana alfahari dashi saboda yana taka muhimmiyar rawa gurin dakile harkokin ta'addanci a kasa baki daya.


A maimakon ya kira Asp ya sheda masa abinda yake faruwa sai kawai yaja bakinsa yayi shuru haka kawai yake jin wani irin haushinsa da kiyayyarsa a zuciyarsa duk wanda ya danganci yarinyar haushinsa yake ji.


Asp ya samu labari a bakin Commissioner dole sai da sa hannunsa komai zai tafi dai-dai, koda yaga abokin nasa ne zai jagoranci tafiyar sai yayi mamaki mutuka amma bai nuna a fuskarsa ba saboda baya so wani ya fahimci cewa akwai sa'bani a tsakaninsu.



Ya isa gida cikin tarin gajiya da damuwa da rashin walwala duniyar gabadaya tayi masa zafi ya rasa wane irin tunani zai yi.

Ya samu Uwale ta had'a kayanta tsaf tana jiran shigowarsa, ganinsa sai kawai ta fashe da kuka! kariris!

Hankalinsa ya tashi ainun! domin ko kadan baya kaunar damuwarta.

Ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, amma fafur! taki tayi shuru! ya kalli Hamra'u da tayi tsuru-tsuru! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, yace." Me yake faruwa ne shin me kukayi mata."?


Tace." Wallahi nima ban sani ba tun dazu nake tambayarta tayi shuru sai share hawaye take wai *'Kafur!* za ta tafi."

Ya kalleta da fadin." Wane irin *'Kafur* kuma? ai na dau'ka ko sati uku baki da zuwa ba, ko wani ne ya mutu a can."?


Tace." Umaru zama a tare da kai bashi da amfani tunda ban isa na saka ba kuma ban isa na ha naka ba, to zanyi tafiya ta

Please Login or Register in order to submit comment