Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har dai ta saba ta daina dari-dari domin ganin ta sauya hali ya sanya Uwalen sassauta mata, wannan ya sanya hankalinta ya kwanta a gidan, ita ta cigaba da yi wa Zinat din d'awainiya har wankin undis wani sa'in ita take wanke mata ta tsafe mata kitson kanta kana ta kitsa mata sabo, idan kafafunta sun dameta da ciwo itake matsa mata.

Abun dai har ya soma damun Zinat din saboda bata so wasu daga waje suga abunda yake faruwa su d'ora ayar tambaya a kanta shiyasa tayi wani tunani akan al'amarin.


Da fara'a ta shiga ta sameta kan doguwar kujera a kwance tace." Aunty Gimbiya jikin ne ko garin ina fata dai babu abunda ke damunki."?

Ta ya mutse fuska da fadin." Kinga wallahi tun safe na tashi da ciwon mara asibiti nake so muje yanzu."

Tace." Eh lallai zuwa asibitin yana da muhimmanci bari na shedawa Uwale."

Tana kokarin tashi tace." Okey bari na shirya kafin ki dawo." Daki ta nufa tana cire kafa da kyar! ciki wata biyar kacal yayi girma sai suddubaru iri-iri!


Uwale tace." To ko na shirya muje tare."? kai ta girgiza da fadin." Ki zauna kawai yanzu zamu dawo." Tace." Shikkenan amma yana da kyau kafin ku tafi ki shedawa mijinku koda ta waya ne."


Tace." Uwale bana so na kira shi yayi min fad'a ki bari kawai mu tafi."

Tace." Aa dole ki fada masa hakkinsa ne."

A sanyaye tace." Shikkenan.

Cikin tararrabi da jin tsoro ta kira shi, akaci sa'a ya dauka bai kuma yi mata fada ba, su gaisa a mutunce ya tambayeta gida tace." Kowa lafiya lau."

Shuru tayi tana nazarin maganar dake bakinta. tuntuni tasan baya kaunar tayi masa maganar matarsa amma ya zama dole ta sheda masa abinda yake faruwa.

Yace." Hamrau ko da matsala ne."?

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Dama za muje asibiti ne da Aunty Gimbiya bata jin dadin jikinta."


Yaja wani dogon tsaki da fadin." Ba da yawu na ba, kada ki kuskura kije ko'ina."

Ta bude baki kenan za tayi magana ya kashe wayarsa! ta tsirawa wayar hannunta ido tana mamakin irin k'iyayyar da yake nunawa matarsa kamar wacce ta kashe masa uwa da uba.

A sanyaye ta fito daga dakin ta shedawa Uwale yanda sukayi......Cikin bacin rai! tace." Kamo min wayar tasa muyi magana."

Koda ta kira shi yana kallo har ta katse bai dauka ba, ta dinga kira tana katsewa, kwata-kwata yaki dauka.

Tace." Wallahi yaki daga wayar na kira ya kai sau bakwai.

Murmushin takaici tayi tana girgiza kai! hakika Dayyiba bata kyauta ba ta shiga tsakanin ma'aurata ta sanya musu kiyayyar junansu.

Sosai fa take jin jiki dan koda ta shiga dakin da niyyar sauya kaya kasa komai tayi ta sake kwanciya tana kiran sunan Allah, cikinta ne yake mata wani irin ciwo ga wani uban gumi da take shar'bawa!

Cikin wannan halin ta shiga ta sameta, bahaushe yace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne! Hamra'u hankalinta ya tashi ganin yanda take murkususu! duk kiyayyar da take mata sai ta nemeta ta rasa hankalinta ya tashi ta rasa wane irin taimako za tayi mata.

A hankali tace." Na shigo dan na sauya kaya amma na kasa saboda yanda ciwon cikin nan ya dameni."

A sanyaye tace." Sannu yanzu ya za'ayi? Uwale tace." Lallai sai na kira maigidan na sheda masa abinda yake faruwa, to koda na kira shin sai yace kada muje ko'ina."

Ta kalleta tana jin wani irin 'bacin a can cikin ranta, rintse idonta tayi tana tunanin yanda za tayi, ta bud'e idon tare da kallonta tace." Kyaleshi kawai miko min wayata gata can saman mirror."

Da sauri ta mika mata wayar. ta lalubi number Asp da kyar ta iya sheda masa halin da take ciki.


Hankali a tashe yace." Insha Allahu zan turo Likita zai zo ya dubaki yanzu ya baki magani ba sai kunje ko'ina ba tunda muna tare da kwararrun likitoci a cikin gidan.

Tace." To shikkenan nagode Allah ya saka da alkairi."

Ya amsa da" Ameen ya Allah." kafin ya kashe wayar ya fara laluben number Likitan da yake da tabbaci a kansa.


To cikin ikon Allah tana shan magungunan da likitan ya d'ora ta akai ta samu sassauci a take wahalallan bacci ya dauketa, duk ta rame na lokaci guda.

Asp yana tashi daga aiki bai nufi ko'ina ba sai gidan abokin nasa hankalinsa gabad'aya yana kan yarinyar, sai da yaje ya dubata sannan hankalinsa ya kwanta mussaman da ya sameta a zaune ta warware tana cin abinci.

Ya dubata sosai ya kuma bata shawarwari masu amfani kafin yayi mata sallama ya nufi muhallinsa.



A daran ranar ya samu labarin duk abunda yake faruwa.

Koda yake ba labari ya samu ba, hotonan Likitan da ya dubata da hoton Asp da shigarsa da fitarsa duk aka tura masa ta WhatsApp bashi da tabbaci akan wanda ya turo masa sa'kon asali ma bashi da number.


Hankalinsa ya tashi ainun! Asp ya zame masa kadangaran bakin tulu, baya gari amma yana shigar masa gida ba tare da izininsa ba, garadan maza suna karakaina a cikin gidansa har cikin dakin matarsa.

Kansa ya dinga yi masa wani irin ciwo! tunaninsa gabadaya ta tafi gurin ganin ya samu hanyar da warware matsalarsa, yanzu zargin cikin da yake jikin yarinyar yake, Asp ya wuce gona da iri babu abunda ba zai aikata ba.

Cikin rashin tunani da gushewar hankali da tsinkaye ya kira Asp din yana wani irin huci! ya fara surfa masa rashin mutunci! Asp din ya fusata! da karfi ya buga tevur din dake gabansa ya mike tsaye da wayar a kunnansa yana fadin." Umaru ni kake kira fasiki! anya kana da hankali kuwa ko dai ka fara shaye-shaye ne."?

Shima a fusace! yace." Bana shan komai! hankali kuma bani dashi mutuk'ar akan na zuba maka ido kana abunda kaga kake so, nifa ba bagidaje bane da zaka dinga raina min hankali. kullum kana bibiyar matata a gindi-agindi dole nayi zarginka, kaje ka dawo da ita ba tare da izinina ba, bana gari kana zurga-zurga a cikin gidana, akan me ba zanyi zarginka ba."

"Ya isa haka."!! Da karfi yayi maganar jikinsa na wani irin karkawa.

Ya cigaba da cewa." Wallahi ban ta'ba tunanin da'kiki! bane kai sai yau! dole kayi wannan tunanin saboda jahilcin da yake damunka, ka jima kana mummunan furuci a kaina har kana danganta ni da matarka ta sunnah. to bari kaji kwata-kwata kai baka dace da wannan yarinyar ba, wallahi dana san haka halinka yake da ba zan shige maka gaba har ka samu nasarar auranta ba, babu damuwa kayi kuskuran sakinta ni kuma zan baka mamaki."! Bai jirayi amsarsa ba kawai ya kashe wayarsa.


Wayar ya tsirawa ido yana kallo hankalinsa a tashe! wannan shine a dake ka a kuma hana ka kuka, Asp ya shiga huriminsa amma saboda tsabar rashin tsoron Allah yana nad'e tabarmar kunya da hauka.

A daran kasa rintsawa yayi koda yake dama can ba wani baccin arziki suke ba, kullum suna tsakanin border suna kai kawo amma dai wani lokacin idan baccin yazo yi suke ba tare da saninsu ba, domin shi bacci daban yake a cikin abinda Allah ya hallata mara sa rai.

Yana kallon wasu daga cikin abokan tafiyarsa suna bingirewa bacci na kwasar su, bai hanasu ba kwai ya kyalesu su sarara shima ya samu damar nazari da tunanin hanyar warware matsalarsa......Sai dai a gurin tunanin baccin dai da yake gudu yazo ya sace shi ba tare da yayi tsammani ba.

Cikin baccin yayi mafarki da wani dattijon mutum da fararan kaya a jikinsa kansa nade da farin rawani farin gemunsa ya kusa ta'ba kasa akwai wani zabgegen carbi a hannunsa. suffar mutumin dai gashinan ba mutum ba ba kuma aljan ba.

Sunansa ya kira." UMARU."

Ya amsa da "Na'am."

Yace." Ni ne abokinka ina tare da kai tun kana cikin uwarka nima sunana UMARU ni musulmi ne ina kuma taimakon bil'adam mussaman musulmai. ban ta'ba bayyana a gare ka ba sai yau duba da ganin yanda al'amuranka suka lalace! me yasa kake sakaci da addua? a can baya baka da wasa amma yanzu ka bari har ma'kiya sunyi tasiri a kanka."

Shuru kawai yayi yana kallon Dattijon.

Yace." Rufe idonka.

Kallonsa yayi nan ya hango k'wayoyin idon dattijon sunyi kama dana *ZAKI!* Ya zabura! da sauri ya rufe idonsa.

Kamar al'amara ya ganshi gurfane bakin kwatami (kwata mara kyau) yana hake kasar gurin. yana fito da layar! a zabure! ya bude idonsa yana duba hannunsa yaga layar sai ya fara dube-dube a gurin, babu dattijon babu dalilinsa.

Ya dinga kiran sunan Allah yana tu'ajibun Al'amarin shin waye wannan dattijon daya ziyarceshi.?

Ya sake duba layar dake rintse a hannunsa tunanin a inda ya ciro ta yake.....Kofar gidan Malam Shafi'i." Zuciyarsa take tuna masa.

Tabbas hakane shin me hakan yake nufi? surkulle akayi maka aka shiga tsakaninka da iyalinka. wannan karon ma zuciyarsa ta sake tunasar masa.

Sai kawai abubuwan da suka wuce suka dinga dawo masa daki-daki! jikinsa ya jike sharkaf da gumi tsabar fargaba da tashin hankali.

Haka ya wayi gari cikin rashin karsashi da kwarin jiki, duk abunda yake daurewa kawai yake ya rasa ma tunanin da zai yi.

Ya kira wayar Asp din sau curin masaki amma yaki dauka domin ya dauki fushi! dashi mai tsanani.

Ya kira Hamra'u da fadin.'' Lallai ta kai wa Zinatu wayar yana so yayi magana da ita, dalili ya kira wayarta itama taki dauka.

Rasa abinda yake damunta tayi ba dan ranta yaso ba ta kai wa Zinat din wayar ta sheda mata abunda yake da akwai.

Tace." Kinga Hamra'u fita dan Allah bana san b'acin rai! kinzo da rawar jikinki watakila ba alkairi bane a kiran nasa, saboda haka kije kawai bana bukata.

Jikinta babu kwari ta fita da wayar a hannunta tana tunanin irin masifar da zai mata.

Aikuwa dai rufeta yayi da bala'i yana nema ya d'ora mata laifi! takaici yasa kawai ta fashe da kuka ta kashe wayar ba tare da ta cigaba da sauraransa ba kwanciya tayi ta dinga kuka tana tunanin ya rayuwarta zata kasance a gidan, dan taga kamar hankalinsa ya dawo kan matarsa watakila ita za ta zame musu 'yar aiki, gashinan sai walagigi suke da rayuwarta shi ya kyareta! ya hantare! ta ita kuma ta aike ta shin wannan wane irin aurene mara 'yanci.





*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/24/22, 19:24 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._


*121*
Ya kira wayar Asp yafi a 'kirga amma bai saurareshi ba, kawai sai ya yanke shawarar rabuwa dashi ya mayar da hankalinsa guri daya amma can kasan zuciyarsa akwai tarin fargaba da tashin hankali a dan'kare! domin duk abubuwan da suka faru a baya yana tunaninsu yana kuma nazarin ya akayi hakan ta kasance. babu shakka yanzu ya fara hangen gaskiya akan mafarkin da yayi cewa da akwai sanya hannun iyayen Hamra'u gurin 'bacewar tunaninsa, idan ba haka ba ya akayi al'amura suka sauya, da hankalinsa da tunaninsa ba zai manta lokacin da yanke hukuncin wata shida kafin a daura musu aure ba, amma ya akayi al'amura suka sauya, babban abinda yafi damunsa yanda suka samu matsala da amininsa ya rasa dalilin da ya janyo hakan, burinsa ace Asp din ya d'aga wayarsa sun tattauna maganar, amma ga dukkan alamu yayi fushi dashi irin wanda bai ta faruwa a tsakaninsu ba.

Damuwar da yake ciki ta sanya masa rashin karsashi! da 'kwarin jiki duk abinda yake 'kok'ari kawai yake amma gabadaya hankalinsa yana gida gurin iyalinsa mussaman ita Zinat din da take tare da lalura.


Wani irin tashin hankali ne ya faru a daran ranar da suka gama shirye-shiryen tafiya gida.

Abinda ya faru shine, tun bayan zuwansu garin. 'yan ta'addan da suka damu garin ta'addanci suka sauya dubara! domin tuntuni suna da labarinsa da irin jazaba da baiwar da Allah yayi masa, sai duk suka watse suka sauya ma'boya, amma suna da labarin duk abinda yake faruwa a garin.

Iya bakin kokari da binkice sunyi a garin basu kama wani mai laifi ba. wannan dalilin yasa suka shirya tafiya domin hakan ma nasara ce, ace zuwansu garin ya tsorata masu laifin sun gudu saboda rashin yarda da kai.

Ashe lamfo sukayi. a daran ranar suka saka musu bom! gurin da suke ya kama da wuta!.........Mutum shida suka kone kurmus! wasu suka jikkata! tashin hankali kenan! wannan al'amarin ya dunguzuma shi! shima bom din wurgi yayi dashi can wata nahiya.
Cikin mawuyacin hali yake lalube da hannunsa so yake ya tashi zaune amma inaa! jikinsa yayi nauyi wasu guraran duk sun 'kone! ya kira sunanan Allah da k'arfin gaske! kafin yayi kalmar shahada! ya zabura! ya mike tsaye! yana wani irin ihu!!! da gurnani!!

Abinda ya tsorata su kenan dama sunyi lamfo a ma'boyarsu! duk sai suka gigice! suka fara fitowa wasu na gudu wasu kuma na harbinsa da bindiga.

Basu samu nasarar samunsa ba, saboda yafiso da dabaru!!

Shi din dai Allah ya bawa nasara ya harbe kafafun mutum biyar sukayi kwance a gurin suna jan jiki da ihu!!

Sauran suka ranta a na kare! duk da haka bai fasa sakar musu bullet ba, sai da ya sake samun mutum biyu suka zube a gurin.


Hayaki! da zafin wuta ne kawai yake tashi a gurin.

Jini da sassan jikin dan Adam dole ya firgita wanda bai saba gani ba.


Ya dinga bin 'yan uwansa yana dubawa wasu da rai wasu babu wasu sunyi daga-daga! naman jikinsu ya tarwatse!


Kuka ya dinga yi da hawaye yana kiran sunan Allah! a fili. wannan wane irin tashin hankali ne!


Wannan al'amarin da ya faru ya tashi hankali kowa ba mazauna garin ba kawai duk wani mai kishin musulunci da kishin 'kasa dole ya jajantawa kansa zubar jini a Najeria ya zama kamar zubar ruwan famfo.

A galabaice aka nufi asibiti dashi da sauran wa'inda suke raye.

'Yan jarida mane ma labarai basu samu cikakken bayanin da suke bukata ba, dalili shi wanda zai musu bayanin baya hayyacinsa, sai dai sun d'auki rahoton gurin da abin ya faru, kuma sun samu nasarar daukar hotonsa a lokacin da ake kokarin sanyashi a cikin motar asibiti, sannan suka kutsa suka dauki hotonan masu laifin da aka samu nasara a kansu.

To kafin kice kwabo labari ya cika 'kasa baki d'aya
*GOJE!* wannan mafaraucin mutumin da ya kasance Jami'in tsaron dake garin katsina ya samu nasara akan 'yan ta'addan da suka addabi garin Zamfara! sai dai yana da muhimmanci mutanan Zamfara da 'kasa gabadaya su dage da addua akan Allah ya tashi kad'arsa! saboda yana cikin tsaka mai wuya dashi da abokanan tafiyarsa dalilin tashin bom da 'yan ta'addan sukayi ya k'ona wasu daga cikinsu kuma sun rigamu gidan gaskiya, yanzu haka dai *UMARU wanda kuka fi Sani GOJE!* Yana kwance a babban asibitin garin Zamfara domin ceto rayuwarsa."
wannan rahotanin da ke yawo gidajen television redio tare da wayoyin mutane .


Tashin hankalin da Asp ya shiga yafi gaban a kwantatashi! kaf headquarter 'yan sandan suna cikin tsananin tashin hankali da damuwa sakamakon abinda ya faru da ma'aikatansu mussaman shi Umar din da suke alfahari dashi........mutum daya ne zuciyarsa babu alkairi domin shi bai so al'amarin ya tsaya a haka ba, amma a zahiri ya jajanta kuma shine ya jagorancesu tafiyar zuwa can garin domin duba marasa lafiyan.


Idan kuka ga yanda hankalin iyalinsa ya tashi sai kun tausaya musu. Zinatu tsayuwa ta gagareta! kafafunta sai karkarwa suke! tun lokacin da taga mijin nata a tv an nuna shi kan wani gado irin na asibiti kamar matacce hankalinta ya tashi, kuka ta fashe dashi tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!! shikkenan mun zama marayu!

Kuka gabadaya gidan aka rasa mai rarrashin wani dan Uwale ma kasa daurewa tayi abunka da mutan k'auye sai sambatu takeyi tana share hawaye.


Zinat kasa zaman gidan tayi tasa hijab ta fice. kai tsaye gidan Asp ta nufa.

Lokacin bai jima da dawowa ba wanka ya shiga domin shiryawa tafiya.

Kukan da yaji a falon ne yasa cikin gaggawa ya fito.

Ya sameta sai rusa kuka take Madam ta rungumeta tana rarrashi itama Nabila dake zaune a gefe hawaye take sharewa.

Ya sassauta murya da fadin." Kuyi hakuri addua za kuyi musu Allah ya basu lafiya.

Jage-jage da hawaye a fuskarta take kallonsa da k'yar ta iya cewa." Ranka ya dade kuna 'boye mana wani abu amma a jikina nake ji mijina ya mutu."


Ya girgiza kai da fadin" Zinat da mijinki ya mutu da yanzu gawarsa ta iso gida yana nan a raye amma ba zan boye miki ba yana bukatar adduarki."


Tana shashshekar kuka tace." Don Allah kayi hakuri ka tafi dani gurinsa inaso na ganshi mu yafewa junanmu."


Tausayinta ya rufeshi yace." Insha Allah zai dawo gida da rai da lafiya ku cigaba da rayuwa. kiyi hakuri tafiya dake ba zai yuwu ba tunda bani kadai bane amma insha Allahu idan mun isa zan kira ki a waya ki dubashi.

A sanyaye tace." Rayuwata ta kare idan na rasa mijina ina sonshi bana so ya mutu barni amma mutuwa dole ce."!!


Wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskar Madam dauriyarta ta k'are sakamakon tausayin yarinyar.


Shima zuciyarsa ce ta karye kawai sai yayi gaggawar shigewa daki yana kiran sunan Allah a zuciyarsa, a gurguje ya shirya ya fita ta can kofar waje domin baya so yazo fita tausayin yarinyar ya sashi zubar da hawaye.


Isar su keda wuya Allah ya kar'bi rayuwar mutum biyu daga cikin wa'inda suke kwance! Asp dai kasa hakuri yayi ya fara share hawaye ganin tashin hankali da masifa mutuwa dole ce amma irin wannan akwai tausayi da tayar da hankali.
Gawarwakin aka had'a guri guda kafin asa a motar da zata kaisu gida.

A daran suka juya amma banda Asp domin cewa yayi ba zai tafi ba tukkuna sai yaga abinda hali yayi, gabadaya ya cire tsammani da samuwar abokin nasa.


Commissioner bai ce masa komai ba kawai ya rabu dashi amma akwai abinda ya kud'ire a ransa!


Da asubah bayan ya idar da sallah yaje ya zauna kusa dashi yana kallonshi cikin zuciyarsa yake masa adduar samun sassauci.

Likita ya shigo dakin, suka gaisa kafin ya k'arasa bakin gadon yana dubashi.

Ya kalli Asp din da fadin ." Insha Allah yau din za'ayi masa aikin wannan 'kunar dake kafafuwansa za'a cire fatar gabad'aya a wanke gurin. kana a sanya magani."


Yace." Dr amma bayan wannan babu wata matsala ko ina nufin babu wani abu daya nakasa a tare dashi.

Yace." Bana tsammanin hakan gaskiya tension ne yayi masa yawa da kuma fargaba amma insha Allah zai tashi da tunaninsa wannan shine iyakar binkicen da mukayi a kansa.

Yace." To Alhamdullhi Allah ya bashi lafiya, su kuma wanda suka rasu Allah ya yafe musu ya kuma kar'bi shahadarsu."

Likitan ya amsa da Ameen ya rabbi kafin ya gama duddubashi ya fita daga dakin.


Misalin tara da rabi Governor garin katsina tare da mu'karrabansa suka sauka a gidan gomnatin garin.

Tare da governor Zamfara suka isa asibitin domin duba marasa lafiyan.

Lokacin ya tashi kuma cikin hayaccinsa kamar yanda Likitan ya fad'a! sai dai ya gaza furta kalma daya sakamakon nazari da tunanin abunda ya faru.

Shi kansa Asp din gajiya yayi da magana yayi shuru da bakinsa farin cikinsa dai ya tashi cikin nutsuwa babu buge-buge!


Shigar su keda wuya ya bisu da wani irin kallo yana girgiza kansa gabad'aya haushinsu yake ji Malam me za'ayi da mulki bala'i ne ga wanda ya san hakan!


Asp ya mi'ke tsaye yana musu barka da zuwa.

Suka samu kujeru suka zauna hankalinsu gabadaya yana kansa alhini da damuwa ya bayyana a fuskokinsu da alama dai ko a cikin shuwagabbanin suna da imani.

Kafin ma wani yayi magana a cikinsu shi ya mangantu....Asp yayi mamakin hakan mutu'ka!


"Rashin tsaro da rashin tsoron Allah da son duniya da mulki shine babbar asara! ga duk wani shugaba."

Duk suba zuba masa ido jin maganar da yake.

Ya cigaba da cewa."
Lokacin da kake ya'kin neman za'be! idonka ya rufe ka tara talakawa kayi musu al'kawaririka kan cewa idan sun mara maka baya zaka tallefesu zaka basu aikinyi za kuma ka taimaki k'asa baki daya."


"Mulki ya zama abun rububi da kokawa! saboda samun jin dadin duniya, kayi rantsuwa da Allah da al'kur'ani kan cewa zakayi adalci daga bisani idan bukatarka ta biya sai ka mance da komai ka fara gina rayuwarka ka auri kyawawan mata ka ajiye a gida kaci mai kyau! kasha mai kyau! ka kwanta a mai kyau! ka sanya suttura mai kyau! kayi facaka da kudi! ka nemi duk macen da kake bukata ka tura yaranka kasashen waje suyi karatu, ka tara kudi a banki ka sayi gidaje gonaki ka gina gidajen mai kayi duk wata bukatar rayuwarka ka manta da talakawa da nauyinsu yake wuyanka wannan shine al'kawarin daka kayi wa Allah."?


D'akin yayi tsit! babu wanda yace uffan.

Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa........."Talauci yayi yawa a duniya      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  saboda zalincin shuwagabbani mai yasa matasa ba zasu shiga wani mummunan hali ba."?

"Sace-sace fyad'e harkokin Daba gami da sara suka sun zama ruwan dare shin menene ya jawo hakan? idan akwai son zuciya irin na mutum to akwai sanya hannun gwamnati.

Akwai matasan da suke da degree takardunsu sunyi kyau amma ba'a daukesu aiki ba, an dauki wanda yake takardar secondary aiki a halin yanzu sai kana da hanya zaka samu, mahukunta da shuwagabbi basa bin doka kowa kansa ya sani yaya rayuwarsa za tayi kyau ya ingata iyalinsa......Idan haka ake mulki Allah yayi mana tsakani dashi."






*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/26/22, 06:13 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin(\(\ gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





*122*
Governor Nuhu Bamalli ya sauke zazzafar ajiyar zuciya bayan kare maganganun Umar din yace." Umaru ba zamu musanta maganarka ba, domin duk abinda ka fada gaskiya ne, mulki a yanzu ya zama Innalillahi wa'ina wa'ina ilaihi raji'un! amma inaso ka sani cewa ba duka aka taru a ka zama daya ba, da

Please Login or Register in order to submit comment