Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inaga kuma na aure ta."?


Yace." Kai dai zaka zage damtse ka tsaya a matsayinka na namiji ka nuna mata bambanci sosai amma naga duk ka wani susuce! wai shin ko tsoronta kakeji ne."?

Murmushin takaici yayi kafin yace." Asp mu rufe maganar nan dan Allah! muyi abunda zai yuwu domin ina so na tafi gida na kwanta na huta."


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ai shikkenan tunda ka fadi haka amma ni kam dole na tauna tsakuwa domin aya taji tsoro."

Shuru kawai yayi masa yana jin wani irin takaici a ransa.........Wai yana tsoron yarinyar, wannan maganar ta sosa masa rai mutu'ka! shin akwai wata mace da zai ji tsoro a fadin duniya, Uwarsa ce kuma bata raye.


Takardun dake hannunsa yake bud'ewa, wata doguwar takarda ya fito da ita da hoto kati daya, mika masa yayi kafin yace." Ka duba hoton sosai ka kuma duba rahoton dake jikin takardar.

Saman takardar kawai ya duba yaga an sanya *AMINIYA GIDAN JARIDA KANO STATE*

Ya kalleshi da fadin." Wani abu ne yake faruwa a jahar *KANO."?*

Yace." Duba dai amma ka fara nazarin hoton mutumin dake hannunka."

Ya 'kurawa hoton ido yana ta so ya hasaso kowaye.....ya girgiza kansa da fadin." Bangane waye ba wallahi."

Asp din ya kar'bi hoton da fadin........
*UBAN DABA NE."!* A zabure! ya kar'bi hoton yana sake dubawa, kafin kice kwabo gumi ya fara tsatstsafowa a saman goshinsa.

Tabbas idan ba wanda yayi masa farin sani ba ba zai ganeshi ba domin duk kammaninsa sun sauya......duk babu wannan 'kasumbar! yana sanye da kayan hausawa riga da wando harda hula sai dai jikinsa lullube yake da wani farin mayafi irin na maza wannan shi ya hana bayyanar nakasar dake tare dashi .........Tabbas shine domin k'wayar idonsa basu sanja ba suna nan yanda suke gwala-gwala masu tsananin ja! kamar garwashin wuta!

Ya kalli Asp din da fadin." Ya akayi yanzu meye abin yi."?


Asp din yace." Nafiso ka karanta rahotannin kafin mu tsaya a matsaya ana bincike ne a kansa da yaransa da suka sauka a garin.


Ya mayar da hankalinsa kan takardar yana karantawa.

Rahoto ne daga gidan jaridar *AMINIYA* cewa wasu 'yan gudun hijira da suka samu masauki a k'auye *KUYAN TA INNAH* ana zarginsu da ta'addanci tare da yiwa k'ananun yara fyad'e........Ana dai binkice a kansu domin tabbatar da gaskiya magana.


Ya share zufar saman goshinsa, ya kalli Asp din da fadin." Ko shakka ba nayi zasu aikata abunda yafi haka, babu wani maganar binkice! wai shin me yasa jami'an tsaron *KANO!* suke da sakaci ne? to ni da kaina zan shiga Kanon domin a gudanar da binkicen dani idan ba haka ba zasu iya kyaleshi ya cigaba da ta'addanci tare da kashe rayukan da basu ji basu gani ba."
Murmushi Asp din yayi kafin yace." Kai ka fiye gaggawa! yanzu idan akayi wani yun'kuri zasu ankara su samu damar tserewa.....wannan rahoton babu wanda ya san dashi sai ni da kai sai kuma Commissioner.......Domin Abokina *Wali Nasiru* dake *KANO* tare da sauran abokan aikinsa ne suka shiga 'kauyen suna binkice akan matsaltsalun dake faruwa.....nan suka samu cikakkaken bayani daga bakin wani dattijo cewa tsayin shekara dari da wani abu wata gagarimar matsala bata ta'ba faruwa ba a 'kauyen sai dalilin zuwan 'yan gudun hijirar.......Dalilin da yasa kenan suka tsananta binkice akansu domin gano gaskiyar lamari.......Kasan abokina ne sosai tare mu kayi karatu to yana bani labarin abunda ke faruwa sai na bukaci da ya turo min rahoton domin ni kaina sai da na zargin wani abu, saboda haka muyi hakuri kada muyi gaggawa domin hakan zai zaburar dasu, su gudu! a nutse zamu kamasu. ina kuma kara tabbatar maka da cewar babu wanda ya san wannan rahoton daga ni sai kai sai kuma mai gayya mai aiki don bana tsammanin ma gwamnati tasan da abunda ke faruwa domin yanzu muka gama tattaunawa commissioner din akan hakan."

Dogon tsaki! yaja ransa duk a dagule! wane irin aikin gaggawa ai a ganinsa jinkiri shi zai cutar dasu, ya ga dama sun samu amma za suyi wasa da ita! ya dinga jan tsaki! kansa ya cigaba da sarawa! tabbas da ba dan a karkashin gwamnati yake aiki ba to da babu shakka yau zai yiwa garin *KANO* dirar mikiya duk inda *UBAN DABA!* Da yaransa suke sai ya lalubo su domin gwabzawa!

Asp din yace." Ya kamata kaje gida ka huta idan zai yuwu ma gobe ka zauna ka sake jin 'kwarin jikin ka Allah ya sawwake."

Ya amsa da "Ameen yana duba agogon dake daure a hannunsa, uku da rabi na yamma....Asp din ya mike da niyyar fita shima mikewar yayi, ya dauki gilas dinsa ya sakaye idonshi kafin yabi bayan Asp din da niyyar zuwa gida ya sha magani ya kwanta ya huta.



'Bangaranta kuwa tunda ya fita ta kasa samun nutsuwa, tana ji kamar ta kira shi a waya tana kuma tunanin kada ta zubar da ajinta.....Haka ta dinga juye-juye a saman gado sa'i da lokaci tana share hawayen takaici! ita kanta ba'a son ranta ta aikata masa hakan ba, kawai ya b'ata mata rai ne.


Kafin ya shiga gidan sai da ya gabatar da sallar la'asar tukkuna.........Ya duba gurin su Uwale domin ya tabbatar da cewa sun fito daga asibitin saboda a d'azu da safen Likitan yake tabbatar masa da cewa zai sallamesu zai kuma sanya direba ya kai su gida.

Sosai yayi farin cikin ganinsu A falo suna hira har ita Hamra'u domin ta wartsake kamar ba ita ba, hakan duk ya faru ne dalilin kwantar mata da hankali da Uwale keyi ta tabbatar mata da cewa suna zuwa k'auye manya zasu tsayar da maganar daurin auransu, wannan ne dalilin da yasa ta samu nutsuwa ta kuma kwantar da hankalinta.


Gabadaya suka dinga bin sa da kallo har ya samu guri ya zauna.......Uwale ce ta magantu, cikin damuwa tace." UMARU mai ya samu 'kafar ka."?

Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Na d'an taka k'usa ne kin san tana da dafi! shine dalilin da yasa kafar ta kumbura!

Sosai tayi mamaki kafin tace." Cikin wannan uban takalmin da kake sanyawa har kusa ta iya huda maka 'kafa UMARU anya kuwa."?

Murmushi yayi da fadin." Uwale ki bar tsautsayi kawai! Allah ne kawai ya takaita min wahala 'kusar bata shiga sosai ba ku cigaba da yi min addua."

Tace."To Allah ya kiyaye ya tsare gabanka da bayanka."

Ya amsa da "Ameen ya rabbi kafin ya kalli Hamra'u da tunda suka fara maganar ba tace komai ba.

Ya dan saki fuskarsa da fadin." Ya jikin naki."?

Tace." Da sauki Yaya na, kai ma ya jikin naka? Allah kiyaye gaba."

Ya amsa da "Ameen ya rabbi nagode sosai amma kin dai ji abunda likita yace miki ko? ki rage tunani dasa damuwa a ranki."


Tace." To Yaya na insha Allah zan kiyaye nagode Allah ya saka da alkairi."


Bece komai ba ya kalli Uwale da fadin." Uwale a dan bani abinci zanci kafin nasha magani."


Ko kafin Uwalen ma tace komai zumbur ta mike ta kama hanyar kicin......Gabadaya suka bita da kallo suna girgiza kai, tausayi take basu.


Yaci abincin sosai yayi godiya ga Allah kafin ya wuce sashensa dan beyi niyyar shiga gurinta ba gudun b'acin rai! abunda baya bukata kenan.


Marakisiyya dake shanya kayan data wanke a harabar gurin ita taga wuce war sa, ta dur'kusa har kasa tana gaisheshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya wuce ya bar ta a gurin.


Ita din ke shedawa uwar dakin nata dawowar mijin nata.........Tace mata ta ganshi ya fito daga sashen masu gidan ko za'a kai masa abinci."


Ranta ya 'baci! ta kalli Marakisiyyar ta watsar kafin ta buga mata tsawa! had'e da nuna mata hanyar fita.

Da sauri ta mike ta kama hanyar fita gabanta na faduwa! sam ba tayi tsammanin cewar maganarta zata fusata! Uwar dakin nata ba, a ganinta kamar gwaninta tayi.


Ita kuwa har Marakisiyyar ta fita ba daina hararar hanyar data bi ba.......Wani irin kishi ne yake damunta. wannan ai abun kunya ne mijinta ya dawo amma ace mai'aikinta ce ke sheda mata, bayan haka kuma tana jin haushin abunda ya kai shi sashen masu gidan, hakan baya rasa nasaba da mutsiyaciyar yarinyar data tsana a rayuwarta.


Sabon wanka tayi....... sosai tai gayu tayi cikin kananun 'kaya masu daukar hankali, masifaffun turarukan da take d'aukar hankalinsa dasu tasa a kowane sassah na jikinta, kai tsaye sashen ta nufa zuciyarta cike da wasiwahsi!


Idar da sallarsa kenan domin tun daga magaribar har isha'in a gida ya gabatar bai samu shiga massalaci ba dalilin matsanta masa da kafarsa tayi, koda yake yasha magani da sauki akan da.


Kamar bata so tayi masa sallama, shima babu yabo babu fallasa ya amsa, yana bin ta da kallo har ta samu saman kujera ta zauna.


Shuru tayi tana dan wasa da yatsun hannunta!.....shi kuma bai fasa kallonta ba, da carbi a hannunsa yana ja yana nazarinta.


Ta d'ago kai suka had'a ido! bai janye idonsa ba bai kuma ce mata komai ba......Itace dai ta janye idonta sakamakon dafin idanuwansa dake kokarin kassara ta!


Da 'kyar ta iya bude baki tace." Ashe ka dawo."?

Uffan bece mata ba kawai dai ya zuba mata idonsa dasu yake hukuntata!

Ta kalleshi a karo na biyu idonsu ya sake had'uwa.......Wani abu mai yuwar fassaruwa take hange a cikin kwayoyin idanuwansa, gabadaya jikinta ya mutu sai kawai hawaye ya kwace mata! suna zuba tana sa hannu tana sharewa tare da shak'ar hanci! tabbas da tana da iko da sai ta dawo da ciwon jikinta a ganinta ma kamar ta fishi damuwa!


Gyaran murya yayi kafin yace." Me kuma nayi miki? zaki sanya ni a gaba kina kuka! ai ni zanyi kuka duba da ta'addancin da ki kayi min."


Ta kalleshi hawaye share-share! "Nice 'yar ta'addah."? tafada tana nuna kirjinta.


Kansa ya daga da fadin." Eh mana baki da imani! idan ba haka ba mai zai sanya ki farfasa min kwalabe a daki ai kinso ki cutar dani ne."

Taja hanci tana goge ragowar hawayen daya rage tace." Okey kai yanzu a ganinka abunda ka aikata shine dai-dai."?


Ya ajiye carbin dake hannunsa sosai ya mayar da hankalinsa kanta yace." Me nayi ? ina so kiyi min cikakken bayanin abinda nai miki ko'ina akaje baki da hujja!


"Shikkenan tunda haka kace ni bazan yi wata magana da kai ba a yanzu amma ina mai tabbatar maka da cewa wallahi idan baka daina ba nima ba zan fasa ba."!


Yace." Idan kuma ta hanyar halak nayi fa? shin ko zaki hana ni aikata sunnah da matata."?


Shuru tayi tana kallonsa gabanta in banda faduwa babu abunda yake.


Yace." Ki kiyaye domin kishin hauka babu inda zai kai ki, sai halaka hakan kuma da kike bashi zai ha nani abunda nayi niyya ba."

Jikinta duk ya mutu da maganarsa, a sanyaye tace." Kayi hakuri."

Wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa.......Lallai ya yarda da maganar Uwale da Asp in da suke cewa cikin laluma ake nusar da mutum idan yana aikata kuskure......gashi kuwa yayi amfani da damar bukatarsa ta biya bai ta'ba tsammanin zata bashi hakuri ba, koda yake yabi hanyar da hakan zata kasance!


Yace."Na yafe miki Allah yayi miki albarka."

Ta amsa da "Ameen Nagode."

D'akin yayi shuru na 'yan mintina kafin tace." Kaci abinci."?

Yace." Eh naci gurinsu Uwale yanzu kwanciya kawai nake bukata."


A hankali ta mike ta iske inda yake zaune.........Hijab din jikinta ta cire kafin ta zauna kusa dashi..........Kallonta kawai yake yana sha'kar kamshin jikinta da yake masifar so!! idonta kuri kan k'afarsa kafin ta kai hannu gurin ciwon!

Da sauri ya janye yana ya mutse fuskarsa!

Tace."Da zafi ko."?

K'amar karamin yaro ya daga kansa!

Sai kawai ta taya 'bera 'bari ta janyoshi jikinta kansa ta rungume a kirjinsa tana jijjigashi tare da shafa sumar kanshi kamar k'aramin yaro!

Tabbb! =4s
{ ai neman ciwo yayi ya rasa irin wannan soyayya! haka mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki! mutumin da ake rarrashi! domin yayi bacci sai kawai ya 'buge da kusurkusur yana motsi tamkar yaron dake tsananin bukatar nono! haka ya dinga cusa fuskarsa a kirjinta da wayo da dubara ya 'balle bireziyar ya sa'bule! 'karamar rigar dake jikinta........Daga nan labari ya sauya.M0



*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
3/4/22, 21:42 - Binta: *Assalamu alaikum warahmatullahi masoya yan uwa na musulmai...*
`````
````
```
``
`
*Tabbas wani kaya sai amali ,busa sai sarewa jiniya sai a gidan gomna ,ina kuke mata ma'abota tambayar ina wannan shahararriyar y'ar mutan nijer wato mali ,wacce akafi ma lak'abi da...*````BUZHUWA EMPIRE````
*Ina kuke matan Aure n mu masu fuskantar tangard'a tare da k'alubale a gidan mazajen Auren mu??bb.*
*Ina kuma y'ammata masu buk'atar farin jini ta hanyar samun mijin Aure?? Don raya sunnar manzon mu SAW...Nasan duk kunce gamuuu!!!aaa.* *Gafa BUZHUWA EMPIRE ta* *taho maku duk don share hawayen dake kwaranya akan fuskokin ku ta hanyar kawo maku sirrin mallaka tare da* *magani ,haka ma y'ammata ga sirrika nan da maganin shi ,wanda anyi mutane babu adadi kuma anzo anyi* *godiya....ki tambaya wacece Buzhuwa empire ga dukkan wanda* *yasanta ,zakuji karin bayani daganan. Muna bada mallaka ta hanyayoyi dabam* *dabam ,wanda da alfarman annabin rahma xamu sha mmki.* *Mallakar tamu akwai na 3k akwai na 5k ,akwai na 10k da sama ma da haka. Mudai fatan mu shine babu cuta babu cutarwa , kamun mu biya* *maki bukatanki sai kin mana rantsuwa akan bazaki cutar dakowa* *ba ,mallaka matan aure muke ba zallah. Na farin jini kuma na y'ammata ne ,shi munayin shi akan 5k ne da kuma na 10k.* *Zakuna iya tuntu6an wannan numbern domun karin bayani...09061466409/08081202932.*
*Ga kad'an daga cikin mallakar da muke amfani wajen yinsua.*
*Mallaka ta hanyar K'wai.*
*Mallaka ta hanyar nono*
*Mallaka ta hanyar zobe*
*Mallaka ta hanyar guru*
*Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su.... Sai kin taho domun share hawayenki daga kunci zuwa farin ciki....* ```BUZHUWA EMPIRE taku ce!!!```
~08081202932 ko 09061466409~




*93&94*
A daran rigima ce ta kaure tsakanin Asp da Zeey sosai yayi mata jan ido ya kuma tabbatar mata da cewar kwa'bar ta tayi ruwa, amma ta kwana da shirin cewa mutukar da sanya hannunta auran yar mutane ya mutu to itama ta kwana da shirin nata auran sunansa matacce.

Al'amarin ya bata mamaki sosai, domin ba tayi tsammanin matakin da zata dauka ba kenan, tasan dai sunyi zantuka da yarinyar, ta kuma bata shawarwari! amma kuma koda wasa ba tayi tunanin cewa za ta cutar da mijin nata ba.

Jikinta duk ya mutu dan tunda take da mijinta bai ta'ba ci mata mutunci irin yau ba, lallai babu shakka dole tayi takatsantsan gudun faruwar wata matsalar domin ta fahimci mijin nata a fusace yake, hakuri ta bashi da fadin.'' hakan ba zata sake faruwa ba, ko sauraranta beyi ba ya kama hanya yayi tafiyarsa gidan Madam tunda dama a can yake.


Karfe uku da rabi na dare.....Gidan jaridar *AMINIYA* ya tashi da wuta! wacce ba'a san abunda ya haddasa ta ba, tashin hankali kenan! wutar sai da taci mutum hudu masu aikin kwana 'kurmus! suka mutu dan da 'kyar aka samu gawarsu........Wannan ibtila'in da ya faru ya tashi hankali jama'ar gari gabadaya gari ya dauka da maganar...... mahukunta kuwa sun tsananta binkice domin gano abunda ya haddasa tashin wutar.


Wayewar gari a cikin k'auyen sukayi 'batan dabo! shi da jama'arsa sama ko kasa aka neme su aka rasa.....sun gudu bayan sun tafka ta'addanci dan gabadaya sai da suka yashe jama'ar garin, da yake k'auye ne basu waye da kai kudi banki ba, a gida suke ajiyewa, wannan dalilin yasa suka bi dare suka haura gidajen mutane suka tafka musu sata, kudi cikin jakar baggo suka fita daga cikin garin.

Wannan ne ya tabbatar da zargin da ake musu.....Mane ma labarai suka fara d'aukar rahotanni daga bakunan jama'ar kauyen suna watsawa a duniya.....Jami'an tsaro kam basu zauna ba sun bazama domin binkicen inda suke.


Wannan labarin yayi masifar 'batawa UMARU rai dan koda Asp din yake sheda masa abunda yake faruwa, tsaki kawai yaja ya kashe wayarsa, shi kansa Asp din haushinsa yake ji domin da yabi shawararsa a ganinsa da duk haka bata faru ba.



Ta fito daga toilet ta sameshi ya dafe kai sai sakin tsaki yake.....Cike da damuwa ta dafa kafadarsa nan taji yanda jikinsa yake mazari da tsuma!

A sanyaye tace." 'Kafar ce take damunka."?

Kallonta yayi...sai ta kasa hada ido dashi ganin yanda gabadaya kwayoyin idonsa suka sauya jijiyoyin kansa sunyi rad'a-rad'a! lallai da akwai abunda yake faruwa!


Tana kokarin magana ya mike tsaye.... ya kai ya kawo a dakin! fatar goshinsa duk ta tattare ta tara zufa!

Hankalinta ya tashi domin duk sanda ya shiga irin wannan yanayin abunda zai faru ba zai kyau ba.


Cikin dauriya ta 'karasa inda yake kokari take ta rungumeshi amma hakan ya gagara! domin gabadaya ya kasa tsayuwa a guri guda.


Sai kawai ta fashe da kuka da fadin." Wai meye haka ? ni bana san ganinka a irin wannan yanayin idan nai maka laifi kayi hakuri."

Bece mata komai ba gefe ya matsa yana kokarin cire rigar jikinsa.. 
....Ta tsira masa ido dake cike fargaba da tashin hankali!


Gabadaya jikinsa ya bude mussaman kirjinsa da damtsan hannuwansa sai rawa jikin yake ruwan gumi na diga.


Da sauri taje ta dauki wayarta, Asp zata kira ta sheda masa abunda yake shirin faruwa domin ta tsorata da ganin ya cire riga.

Kafin ma ta kai ga kiran Asp din ya kwarma ihun!!! da ya sanya wayar hannunta fad'uwa, ta juya da sauri! kawai sai ta ga har ya cire zabgegiyar wukar dake rataye a dakin.......Ya fara da dadurawa! a jikinsa, mussaman wuyansa.......

Ita kam tana ganin tashin hankali a rayuwarta! a kid'ime ta nemo number Asp din sai dai a kashe take...........Ta juya ta sake kallonsa, bai fasa dadurawa jikinsa wuka ba yanayi yana taune bakinsa.

Auran d'an tauri akwai tashin hankali! wallahi ita ta d'auka tuntuni ya bar harkar ganin ya kwana biyu beyi ba.

Tsabar fargaba k'afafunta kasa daukar ta sukayi kawai ta zube kasan kafet ta takure jikinta guri daya ta fashe da wani irin kuka! babban tashin hankalinta taga yana gurzawa jikinsa wuka gani take idan rana ta 'baci wukar zata samu nasara!


Can ta hango wayarsa saman kujera, da sauri taje ta dauka, number Asp din dai ta nemo ta kira shi, aka ci sa'a wayar ta shiga, tana kuka take sheda masa abunda yake faruwa......da yake weakened ne yana gida ko minti goma ba'ayi ba ya shigo gidan.......ita ta shiga dashi Dakin tana nuna masa shi yana nan yana Aikin abu daya ko gezau! domin wani irin karfi da kwarin jiki yake ji a duk lokacin da wukar ta sauka a jikinsa.


Asp din ya durfafeshi da fadin.'' Ya isa haka! ni da nasan abinda zai faru kenan, da ban fada maka ba, nasan dole ranka ya 'baci amma ai basu tsira ba da ikon Allah sai bukatarmu ta biya a kansu.


Kasa hakuri tayi ta karasa gurin tana tambayar Asp din abunda yake faruwa.........kasa bata amsa yayi domin a lokacin burinsa kawai yaga ya samu kan abokin nasa.

Da 'kyar ya iya zaunar dashi gefan gado ya mayar da wukar gidanta rataye ta yayi a gurinta, ya dawo ya zauna a kusa dashi.

Sai suka sanyashi a tsakiya, dukkaninsu babu wanda baya jin sautin fitar numfashinsa huci kawai yake yana hura hanci!

Ita kam jikinsa kawai take kallo domin ganin koda akwai rauni babu wata matsala fatar jikinsa tana nan a inda take.


Asp hannu yasa cikin aljihunsa kwalin Sigari ya fito dashi da leta ya kunna masa, aikuwa zuka uku yayi mata ta kare, ya sake kunna masa wata, a kalla sai da yasha kara biyar sannan ya dawo hayyacinsa...............Asp ya kalleta da fadin." Ta had'a masa ruwan wanka.

Da sauri ta kama hanyar band'akin duk jikinta a sanyaye!

Ya kalleshi da rinannun idanuwansa a kausashe yace." Jiya nayi magana kace ina da gaggawa! yanzu me jinkirin ya haifar."?


Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kai dai da kawai akwai lauje cikin nad'i! domin Wali Nasiru ya sheda min duk abunda ke faruwa akwai sanya Hannun manyanmu dangane da faruwar al'amarin.


Yace." Kai wa kake zargi."?

Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Commissioner domin har yanzu bai kira ni yace min komai ba, kuma ina da tabbacin cewa yasan abunda yake faruwa.


Yace." Shikkenan yanzu mutanan sun dinga samun nasara da sa'a kenan! me yasa ba zamu sadaukar da rayuwarmu akan ganin mun kawo karshen su ba......Akan wannan dalilin fa wallahi zan iya ajiye wannan aikin."


Yace." Haba kada kayi haka abokina kabi komai a sannu a hankali, insha Allah komai zai daidaita za kuma mu samu nasarar kama wa'innan mutane, saboda haka mu cigaba da addua da kuma bincike akansu."


Shuru kawai yayi masa domin har yanzu akwai sauran takaici a tare dashi...............Ta fito daga toilet din tana sheda masa cewa ta hada ruwan.

Ba tare da yace komai ba ya tashi ya kama hanyar toilet din, sai ta rufa masa baya, ganin haka yasa Asp din tafiya gida gabadaya shima ranshi a bace yake da faruwar al'amarin.


Taimaka masa tayi yayi wankan suka fito a tare.


A sanyaye take goge masa jiki da towel sai kallonsa take tana wasu tunane tunane a ranta mutum sai kace mai aljanu ita yanzu tsoro ma yake bata.


Kallon da take masa ne ya dameshi ya juyo suka hada ido.


Sunkuyar da kanta tayi ta shafo mai a hannunta ta fara shafa masa a gadon bayansa.


A hankali tace." Wai me ya faru ne hankalina yana tashi a duk sanda ka shiga irin wannan yanayin bana so ko kadan."


Hannunta ya riko yana kallonta idonta ya tara kwalla, da gaske bata so domin ya ga hakan a cikin kwayar idonta.


Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga warware mata abunda yake faruwa.


A tsorace take kallonsa kafin tace." Kayi wa Allah da Annabi kada kasa kanka a cikin wannan al'amari domin muna sonka kada ka mayar damu marayu." Murya na rawa take maganar.


Ya dunga kallonta yana jin wani irin sonta na ratsa jikinsa!

Fad'uwar gaba asarar namiji! dashi da *UBAN DABA!* Yanzu aka fara! har sai yaga abunda ya turewa buzu nadi........a zuciyarsa yake wannan maganar, a zahiri kuwa ganin yanda duk hankalinta ya tashi yasa ya sassauta muryarsa yana rarrashinta, sai ya kasance suna rarrashin juna ita dai burinta yay mata alkawari cewa ya bar harkar *TAURI!* Kuma bai zai tunkari *UBAN DABA!* ba.


Alkawarin gaibu yayi mata domin ta samu nutsuwa! amma baya tsammanin zai janye kudirinsa! harkar *Tauri* kuwa wannan a jinin jikinsa take.


Yayi mata alkawarin ya bari, amma abun mamaki taji yana waya da babban yaronsa *ALBA* yace lallai - lallai gobe ya kawo masa maciji yana bukatarsa.

Cikin faduwar gaba take kallonsa har ya 'kare wayar ya ajiye a gefansa.......Ta 'bata rai da fadin." A'a ina za'a kawo maciji kuma me za kayi dashi."?


Yace." Ina bukatarsa ne babu ruwanki dashi."

A raunane! tace." Yanzu fa kayi alkawari ka daina wannan harkar, me yasa duk ga dabbobi ne wanda Allah ya hallata ba zaka ci ba sai maciji me kukeji a jikinsa."?


Ya d'aga mata hannu da fadin." Kinga *ZINA* kada ki dameni dan Allah ba fa zaki ha nani aikata abunda na taso dashi tsayin shekaru da yawa ba, saboda haka ki cire kanki daga wannan sabgar."


Rai a b'ace! ta kama hanya ta fice daga d'akin, tana Allah wadai da al'amarin.


Tsayin sati suna 'yar tsama a tsakaninsu domin tun ranar da ta fita daga dakinsa bata sake shiga ba, kowa a dakinsa yake rayuwa, shima bai nemata ba sai da ya tabbatar da cewar ya cinye miyar macijinsa sannan ya nemi in da take da bukatarsa domin dauriya kawai yake a tsayin kwanakin.


Tace bata san wannan ba, domin data kalleshi zata dinga hasaso shi yana cin maciji sai zuciyarta ta tashi, takai ta kawo ma duk sanda yayi yunkurin sumbatar bakinta sai ta kwara amai na bam mamaki!


Al'amarin ya dinga dugunzuma masa zuciya yana bala'in jin haushi yaje da bukatarsa ta dinga gudunsa gashi sam baya son ya dinga gwada mata k'arfi! yafiso suyi

Please Login or Register in order to submit comment