Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fadin." Sakina ni yanzu sulhu nake nema da iyayena farin cikinsu nake bukata dole nabi komai sannu a hankali amma ni kaina bana tsammanin zan amince da auran wanda bana ra'ayi."

Tace."Wannan shine tunani mai kyau, ki zauna kiyi nazari da kyau domin ki taimaki rayuwarki."

Haka suka wanzu a daki suna k'ulle-k'ullen yanda za'ayi su rusa hukuncin da yake da niyyar tabbata a ranar.

Sai yamma likis tayi mata sallama ta tafi bayan ta bata shawarwarin da take ganin sune kwanciyar hankalinta.

Lokacin da sakon maimartaba ya sameta sai da cikinta ya murd'a tsabar fargaba da tashin hankali, ta kai minti goma a zaune tana sa'kawa da kwancewa kafin tayi namijin kokarin amsa kiran.


Tun kafin ma ya fara magana ta fara kuka, kawai sai ya zuba mata ido yana kallo, ta rarrafa har inda yake ta rirrike k'afafunsa tana wani kuka da fadin." Ranka ya dade kaji tausayina don Allah kada ka tarwatsa min farin cikin rayuwata bana so ka aura min wanda bana ra'ayi yanzu an dena auran dole idan kace za kayi min hakan zai janyo matsala babba.

Numfashi ya sauke kafin ya tallafo fuskarta, ya sanya hannu yana share mata hawaye rarrashinta yayi da fadin tayi shuru suyi magana ta fahinta.

Da 'kyar ta iya dakatar da hawayen dake zuba, ta zuba masa idanunta dake cike da fargaba burinta kawai taji abinda ke bakinsa.

Babu alamun wasa a tattare dashi yace." Wannan shi ya nuna min da cewa baki da matsaya kin dauki maganata a banza ace duk a cikin mane ma auranki baki da gwani wanda kike ganin zai zama abokin rayuwarki, wannan karon ba zan tausaya miki ba, domin ni na haifeki amma na gaji da ganinki a haka babu aure, tunda har na baki dama kika watsar to ni ina da wanda nake ganin ya dace dake wanda kuma nake da tabbacin cewa idan na bashi auranki zai rike min ke da gaskiya da Amana, wannan hukuncin nawa babu wanda ya isa ya janye shi ZINATU mutukar ni na haifeki to baki da mijin aure wanda ya wuce takwarana UMARU ina nufin yaron nan daya cece rayuwarki a daji a kwanakin da suka wuce shine wanda na za'ba miki a matsayin mijin aure, kuma na sheda masa kyautar da nayi masa a ranar suka dawo dake gida, shi din ya kuma tabbatar min da cewa ya kar'ba kyautar da nayi masa saboda haka kada ki bani kunya ko kiyi jayayya da umarnina, insha Allahu nan da wata biyu auranku zai tabbata da ikon Allah."!

Wani irin bugawa! gabanta yake kanta yana juyawa! tunda ya fara maganar ta nemi yawu ta rasa a bakinta! wani rikitaccen yanayi ta shiga wanda ta kasa fassarashi! kuka take ta gayyatowa amma fafur! yaki amsa gayyatarta idanuwan ma soyewa sukayi sai wani dan banzan zafi suke! jijiyar idon data kanta sun had'u sun d'aure guri daya wanda hakan ya janyo mata mugun ciwon kai irin na 'bari guda, sama-sama takejin maganarsa a lokacin da yake bata umarnin tafiya.

Jiki a masifar sanyaye ta iya kai kanta dakinta, kawai ta zube kasan kafet tana janyo numfashi da kyar! ke kace ita din mai jinyya ce wacce ke fama da cutukan dake da ala'ka da numfashi.

Wai ace kamar ita jinin saurata gaba da baya, sannan kuma bata rasa komai ba na matantaka ba, Matar manya manyan mutane masu kudi da mu'kamai! aka dauketa kacokan aka bawa wani ma'kaskanci kyauta! mutumin data riga ta raina masa hankali, bashi da komai na rayuwa! bak'auye dashi, wanda ko direbanta be kai matsayi ba amma wai yau shi mahafinta ke ikirarin bawa auranta, koda wasa ba tayi tsammanin hakan na iya faruwa ba! har yanzu ta kasa gano dalilin da yasa mutane suke k'aunarsa! a'iya nazari da tunaninta, ta fahimci cewa jarumtarsa ce take kawai ke burge mutane.......Wannan shine babban dalilin da sanya mahaifinta yin sha'awar bashi ita a matsayin matar aurensa, tabbas kuwa idan ya sake akayi auran nan to zai gane shayi ruwa ne a hannunta, domin sai ta nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, sam-sam! ba zata yarda wannan karan ya samu nasara a kanta ba, babu ruwanta da jarumtarsa! tunda a zahiri ta fishi komai, to dole shi zai rusana mata!!!!
*TURKASHI!!*


*Tofah! yanzu za'a fara wasanƒ™Âi ko ya zaman auran nasu zai kasance oho? ni ban san ma me zance muku ba, amma dai muje zuwa..............!*



*Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, don darajar Allah da Annabi idan kin san ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min maganaƒ™čjƒ™Ž_*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*
1/31/22, 07:31 - Buhainat: Ī.c
*41&42*
Shigowar mahaifyarta d'akin ne ya katse tunaninta, cikin mutuwar jiki ta tashi zaune ta tana kallonta har ta k'araso ta zaune gefen gado babu walwala a fuskarta.

A d'an raunane tace."Mamnah barka dare." Tana nazarinta ta amsa da fadin." Barka dai me yake damunki ne baki fito kin ci abinci ba."? Kamar me jiran kiris sai kawai ta fara share hawaye murya a sarke tace."Mammah ya za'ayi na iya cin abinci a irin wannan halin, gabadaya kun kasa fahintata kuna nema ku jefa rayuwata a cikin masifa, yanzu tsakani da Allah a gidan nan wa aka ta'ba yiwa auran dole acikin 'yan uwana, kowacce fa wanda takeso aka aura mata amma ni an d'auke ni kyauta an bawa wani wanda bashi da cikakken asali wallahi ba'ayi min adalci ba."

Ta dinga kallonta tana tunano wani lamari daya shud'e shekaru masu yawa, Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Yanzu Ke a ganinki hakan da akayi miki rashin adalci ne." ? shuru tayi ba tace komai ba, ta cigaba da cewa." Ke ba kiji kunyar fadin wannan maganar ba? shin wai to ya kike so ayi miki da har kike fadin ba'ayi miki adalci ba, ai na dauka sai da aka baki lokaci domin fita hakkinki me yasa baki fitar da mijin aure ba, ko kuma kin fiso kiyi ta zama a haka babu aure mutane na zarginki."?

Girgiza kai tayi da fadin" Mammah sati biyu yayi kadan, har yaushe na dawo na samu nutsuwa komai fa yana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali, amma sai kawai a yanke min hukuncin da bai cancanta ba, gaskiya ni ba'ayi min adalci ba don banga abunda zanyi da wannan ba'kauyen mutumin ba."


Murmushi mai ciwo tayi kafin tace." Wannan ba'kauyen da ki ka raina shine marufar asirinki domin a halin yanzu idan bashi din ba babu wanda zai aureki ki samu zaman lafiya saboda haka ki kiyaye ni wallahi, kada na kara jin kin furta wata mummunar kalma akan wannan al'amari, idan ban da butulci ma irin naki wannan yaron ai bai cancanci haka daga gurinki ba."

Hawaye ta goge da fadin." Ni dai kawai bana son shi ne ko kadan a raina domin ba tsaran aura ne bane, amma shikkenan tunda kun gaji da zama dani zan aure shi kamar yanda kuke so sai duk abunda ya biyo baya kada kuyi kuka dani."

Cike da mamaki! take kallonta kafin tace." Zaki caka masa wuka ya mutu kenan."?

Girgixa kai tayi tana share hawayen dake zuba a saman fuskarta.

Taja dogon tsaki da fadin "Karshen k'iyayye dai ki caka masa wuka a mak'oshi! ko kuma ki zuba masa guba a abinci ya mutu! to idan baki fasa aikata daya daga cikin wannan ba bakya kaunar Allah da Annabi, wallahi ki ka kashe shi kema sai an kashe ki! kina ta'kamar gata ko? ubanki yana da kudi da mulki idan kin kashe rai yana da abunda zai fanshe ki, to bari kiji wallahi nayi miki rantsuwa da Allah ki ka kashe rai! sai na tsaya kai da fata kema kin fuskanci hukunci dai-dai da abunda ki ka aikata! idan wannan ne kud'irinki akan UMARU to kada ki fasa."
Tana gama k'are maganar ta tashi ta fita daga dakin ranta a b'ace! al'amarin yarinyar yanzu tsoro yake bata, dole ta tsananta da addua akan al'amarin.

Bayan fitar ta daga dakin komawa tayi ta kwanta hawaye na bin gefen fuskarta, ita ba nufin ta kenan ba, kawai ta fadi abinda yake cikin zuciyarta ne, bata fatan kashe kiyashi ballantana wani dan adam.

Bacci rabi da rabi tayi saboda tsabar damuwa.

Da asubar fari ta kira wayar Asp dama duk tana da numbers su. A lokacin data kira wayar dawowarsa kenan daga massallaci, ganin sabuwar number besa shi mamaki ba, wayar yasa a kunnansa da sallama a bakinsa.

Murya a dashe ta amsa kafin ta gaisheshi.

Sai ya shiga tunanin inda ya san muryar don dashewar ta sanya ya kasa tantance muryarta.

"Wacece ne bangane mai magana ba."?

Hanci taja ta dan sake bude muryar da fadin." ZINAT ce."

Gabansa ya fadi kadan, yace." Zinatu kece ashe ina fatan dai lafiya."?

"Numfashi ta sauke kafin tace."Ai kai ma tunda kaga wannan kiran kasan ba lafiya ba."
Tafad'a cikin dusashewar murya.

Lokaci guda ya harbo jirgin, gefen gado ya zaune da wayar a makale a kunnansa yace." To menene kiyi min bayani Ina jinki."

"Asp me yasa za'a hada baki da kai a cuci rayuwata."? cikin sigar tuhuma take tambayarsa

Yace." Bangane maganarki ba." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Ba zaka gane ba tunda bakinku daya amma ina so ka sheda masa cewa ni ba tsaran auransa bace idan yana farin ciki da dariya to ya dena domin aure na zai zame masa tashin hankali."

Da sauri yace."Subahanallahi! Zinatu duk me ya janyo wannan maganar."?

Tayi saurin tare shi da fadin."Ni dai sako na baka, ka fada masa cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane."

Maganar sai ta bashi dariya, ya d'an dara kafin yace." Aa ni wannan maganar bana cikinta amma bari na baki number sa sai ki fada masa baki da baki."

Tace."Ai ba tsoronsa nake ba turo min number. " Yace."Yanzu kuwa.'' Kashe wayar yayi yana mamakin al'amarin, gaskiya akwai matsala babba.


Kafin ya tura mata number sai da ya kira shi ya sheda masa abunda ke faruwa yace." Don Allah kada ki biye mata ku lalace gabadaya na fahimci rarrashi take bukata, ka rarrasheta kada ka kara mata wani takaicin."

Dariya kawai yayi kafin ya amsa masa da "to shikkenan zanyi yanda kace din." Yaji dadin hakan sosai domin shi haka kawai yake so yaga tabbatuwar auran.


Yana tsaka da shiryawa ta kira wayar, da yake Asp ya bashi numberta koda ya duba yaga itace sai ya share yaki dagawa.

Sai da ta kira sau uku sannan ya daga babu wargi yayi sallama.

Ba tare da ta amsa ba cikin gadara da fitsara! tace. Kana jina ko."?

Shuru bece komai ba, taja dogon tsaki! da fadin." Nasan a halin yanzu kana nan cikin murna da farin ciki da samun abunda ba kayi tsammani ba, to bari kaji wani abu farin cikin ka zai zama bakin ciki! haka zalika dariyarka zata zama kuka domin daga ranar da akace an d'aura mana aure zaka gane cewa kayi tsaurin ido! na bawa abokinka sako yace sai da ya bani number ka, nace ya bani domin bana tsoron sheda maka abunda yake zuciyata."
Ta'kare maganar tana numfarfashi!

A nutse yace." Kin san macen da ake kira da (Matar ladan noma."?) shuru tayi tana nazarin sunan.

Yace."Tunda baki gane ba bari na ganar dake, mahaifinki ya bani kyautarki sadaki kawai zan bayar, ban ta'ba jin sonki a raina ba, domin baki ma da abinda zaki ja ra'ayi na, ina da wacce nakeso yarinya mai kyau mai hankali nutsuwa da tarbiya ke kam (Matar ladan noma ce) banyi noma ba, amma taimakon da nayi miki yasa mahaifinki ya bani ke ni kuma na kar'ba saboda kada na watsa masa k'asa a ido, zan zauna zaman aure dake ba don ina sonki ba."ya kare maganar hankalinsa kwance.

Bakinta ne ya mutu murus! bata tsammaci ya iya cin mutunci haka ba, ta kasa ce masa komai sai wata irin zazzafar ajiyar zuciya da take sauke masa a kunne.

Cikin rashin damuwa Yace."Zan kashe waya idan baki da magana."

Da 'kayar ta iya danne kukan bakin cikin da yake kokarin kufce mata tace." K'azami bagidaje ba'kauye kawai."!
Tayi saurin kashe wayar ta jefar saman gado, zaman 'yan bori tayi kasan kafet taci kukanta ta koshi. kalmar ce kawai take mata amsa kuwwa a kunne *Matar ladan noma!* lallai in baki ya san abinda zai fada to be san abunda za'a mayar masa ba.

Sam maganganunta basu bata masa rai ba, hankalinsa a kwance ya cigaba da shirye-shiryensa, besa damuwarta a ransa ba tunda ya riga ya san dole hakan zata faru, yasan cewa akwai jan aiki a gabansa, amma hakan be daga masa hankali ba ya riga ya shirya ya kuma tanadi hanyoyin da zai bi cikin ruwan sanyi yayi maganinta.

***
Tafi sati biyu tana jinyar kanta, tare da bakin cikin ba'kaken maganganunsa! duk sanda zata tuna sunan daya kira ta dashi sai tayi kukan takaici (Matar ladan noma) wannan sunan yakan sanya duk wani alkadari nata ya karye duk shirin da tayi a kansa daga zarar ta tuna cin mutuncinsa sai jikinta ya mutu! gabadaya ta rasa yanda za tayi da rayuwarta gashi ta kasa gane kan mahaifiyarta fushi take da ita sosai! hakan ya k'ara daga mata hankali mutuka, dole haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta aro walwala da farin cikin tasa a cikin ranta ta nuna sadudarta a zahiri. sannan har dakinta taje ta nemi afuwarta akan furucin da tayi a kwanakin da suka wuce.

Ganin yanda ta saki ranta tana walwala da farin ciki sai itama ta sakar mata fuska ta fara janta a jiki tana yi mata nasiha tare da nuna mata yanda rayuwa take gefe guda kuma tana gyara mata jiki da magungunan mata masu kyau da inganci.

Hakuri kawai tayi ta daure zuciyarta take amfani da kayan matan, duk dan ta nuna mata cewa ta hakuraęÿÿÿ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ da auran kuma babu wani mummunan kudiri a cikin zuciyarta. .........Hakan da tayi sai tasa 'Yan uwanta farin ciki dama kullum adduarsu Allah ya shiryi ta ta gane hanya me kyau.


Tun ranar data kira shi a waya yaci mutuncinta bata sake kuskuran 'kara kiran sa ba saboda tana gudun ya kuma dan'kara mata wata mummunar maganar.

A nasa bangaran shima be tsammanci kiran nata ba harkokin gabansa kawai yake, ya manta da ita da lamarinta, shirye-shiryen tafiyarsa training yake, sai dai be manta da adadin kwanakin da suka rage a d'aura auran ba.


A daran ranar da zai tafi suke tattauna maganar da Asp yace." UMARU tafiyarka training ba zata hana faruwar komai ba, meye amfanin abotarmu ni zan tsaya maka akan komai kuma zan wakilce ka, sannan kuma ni ne zan bada sadaki domin a gabatar da komai anyi hakan ba daya ba kuma sau biyu rashin hallatarka d'aurin auran ba zai hana ace aure be d'auru ba, saboda haka ka kwantar da hankalinsa insha Allah sai dai kawai ka dawo ka samu amaryarka na jiranka." Cikin zolaya ya 'kare maganar.

Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya Yace." Nagode sosai mutumina Allah ya saka da alkairi ya kuma bar abota da amana."

Ya amsa da ''Ameen ya Allah amma yana da kyau kafin ka tafi ka shedawa mahaifin yarinyar halin da ake ciki koda ta waya ne."

Yace."Eh dama ina da tunanin hakan, a daran nan zan kira shi mu tattauna maganar."

Ya bashi hannu da fadin."Hakan yayi Allah yasa ayi sa'a." Ya amsa da ameen ya Allah abokina.

To koda ya shedawa Maimartaba Omar halin da ake ciki sai shima ya nuna masa cewa hakan ba wani abu bane, kamar yanda Asp din ya tabbatar masa da cewa ana yin hakan ba matsala bace mutukar akwai wakilinsa shikkenan magana takare, ya kuma karfafa masa gwiwa tare dayi masa kyawawan adduo'i.
Cikin mutunci da karamci sukayi sallama da juna...........Mutunci da dattakon dattijon yana mutukar burgeshi wannan dalilin ne kadai yasa har ya amince da auran yarinyar, tabbas da babu wannan bega dalilin da zai sashi auran mace mara nutsuwa da tarbiya irinta ba.





*Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!*

*#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE*
1/31/22, 07:31 - Buhainat: *43&44*
*GSR*
A daran ranar dai zai yi tafin ya samu Uwale da maganar domin su tattauna, ya sheda mata duk abunda yake faruwa ya kuma tabbatar mata da cewa halin da ake ciki a yanzu saura sati biyu kacal a daura auran, saboda haka ta shedawa duk wanda ya dace acikin 'yan uwa da abokan arziki.........Sosai tayi farin ciki da al'amarin dama shi aure lokaci ne gashi lokacin da ba suyi tsammani ba Allah ya nufa , sai dai kuma bata bar shi ya tashi ba sai da tayi masa maganar Hamra'u da yanda za'ayi da al'amarinta.

Yace."Uwale Hamra'u itace za'bi na kuma har yanzu ina sonta, aure na da wannan yarinyar ba zai hana na aureta ba, wannan auran yazo min bagatatan cikin rashin shiri, insha Allahu itama zan aure ta idan na samu nutsuwar da nake bukata.

Ta kalleshi da fadin." UMARU idan fa baka auri yarinyar nan ba ka yaudareta sai Allah yayi mata sakayya domin dai kai kanka kasan tuntuni kai take jira kuma da bakinka kayi mata alkawarin aure kasan dole idan ta samu wannan labarin ta shiga damuwa tare da iyayenta don Allah kada ka bani kunya UMARU kada ka raba zumuncin da yake tsakanina da mahaifin yarinyar nan."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Uwale kin san fa komai nufi ne na Allah, mutum kan iya tsara rayuwarsa amma Allah sai ya sauya masa, mahaifin yarinyar nan yafi karfin komai a gurina dalilin kenan da yasa na karbi kyautar da yayi min, na kuma fada miki cewa hakan ba yana nufin na janye auran Hamra'u ba, zan aure ta da yardar Allah saboda haka ki kwantar da hankalinki itama yarinyar ki taushi zuciyarta."

Tace."To shikkenan UMARU Allah ya tabbatar da alkairi amma kafin ka tafi ka samu yarinyar ka sheda mata abunda yake faruwa kamar yanda kayi min bayani."

Agogon dake hannunsa ya duba, sha d'aya shaura na dare, yace." Ban 'ki maganarki ba, zan sameta mu tattauna maganar ko ba yanzu ba tunda yanzu dai dare yayi watakila tayi bacci." Tace." To shikkenan Allah ya kai ka lafiya ya kuma dawo da kai lafiya." Ya amsa da "Ameen ya Allah." Sallama yayi mata ya nufi wajensa.

Da Asubah bayan sun fito daga massalaci suka tsaya suna sake tattauna maganar, Asp din yace."Naga tunda aka fara maganar auran nan ba kayi maganar lefe da sauran abubuwan bukata ba, kasan yarinyar nan fa 'yar rigima ce yana da kyau a rarrasheta ta wannan hanyoyin.

Yace."Asp ban san me yasa kake jin tsoro da shakkar yarinyar nan ba, mahaifinta fa kyauta ya bani ita sadaki kawai zan bayar to akan me zan takurawa kaina saboda ina gudan rashin kunyarta."


'Yar dariya yay da fadin." UMARU har yanzu ba'ayi macan da zata tsorata ni ba, kawai dai ina nuna maka yanda za'ayi ka zauna da ita lafiya ne idan kana mata butsu to ba zaku ta'ba samun zaman lafiya da juna ba, maganar lefe kuma abunda ya dace ne koda kyauta aka baka kai kuma sai ka duba cancanta da abunda ya dace."

Yace." A yanzu dai bani da kudin had'a mata lefe sai dai idan tazo daga baya nayi mata."

Asp din ya dinga kallonsa yana mamakin furuncinsa, wai bashi da kudi bayan irin tarin miliyoyin da yake dasu account ko sati biyu ba'ayi ba daga can abuja mai girma shugaban kasa yayi masa kyautar manyan kudi da dan'kareriyar mota harda gida a garin abujan amma shine yake maganar rashin kudi.

Girgiza kansa kawai yayi da fadin." UMARU wato abunda dai kayi ra'ayi shi kake ba'a baka shawara ka d'auka to ai shikkenan."

Yanda Asp din yayi maganar da b'acin rai a tare dashi yasa jikinsa sanyi ya bashi hakuri da fadin." Afuwa abokina ba wai naki daukar shawararka bane akwai dalilina na yin hakan, amma na janye domin farin cikin ka, yanzu nawa zan bayar ayi lefen tunda kaga ni yau zan bar gari sannan kuma ban ma san yanda ake hada lefen ba.

Yace."Ai magana ta wuce ko sisin ka bazan kar'ba ba, lefe kuma ba za'a fasa ba, zan bawa madam kudi ta shiga kasuwa ta had'a duk abunda ake bukata." Yana gama maganar yayi tafiyarsa.

Murmushi kawai yake yana binshi da kallo har ya k'urewa ganinsa, tunda Allah ya had'asu yake nuna masa 'kauna da sadaukarwa Asp ya zame masa dan uwa na jini, yanda yake sonsa da kaunarsa shima haka yake kaunarsa saboda duk wasu alkairai yayi masa kuma duk wani mataki da yake kai yanzu dalilinsa ne da jajurewarsa, hakika bashi da wani abu da zai saka masa dashi face addua.


*****
To kamar yanda Asp din yayi wa kansa alk'awari sai da cika, don kudi masu yawa ya fitar aka had'a lefe dasu akwatina goma sha biyu cike da kaya set din gold har uku kuma duk masu nauyi, da yake da akwai fahimta a tsakaninsa da matansa babu wacce ta daga hankalinta, sai dai kuma sa'bani ya kusa giftawa a tsakaninsa da yarinyar da zai aura a matsayin ta uku , al'amarin ya dinga bashi mamaki yana tunanin a inda ta samu labarin Zinatu da har take kishi a kanta, ganin yanda ta tashi hankalinta ne yasa ya zauna yayi mata bayani cewa yarinyar da abokinsa zai aura ce, dalilin da yasa ya tsaya akan al'amarin shi abokin nasa baya gari yayi tafiya shiyasa ya tsaya masa akan al'amarin auransa." Wannan bayanin da yayi mata yasa ta kwantar da hankali amma da tayi tunanin ko yaudararta zaiyi.

Tun ranar da aka kai wa Uwale kayan lefen domin tasa albarka, Hamra'u ta shiga tashin hankali mai tsananin gaske, domin kasa zaman falon tayi ta shiga daki ta rufe kofa ta dinga rafsa ihu! bakin ciki da bakin kishi kamar ya kasheta.

Uwale ta shiga dakin ta sameta cikin mummunan yanayi, ta zauna tana rarrashinta gabadaya itama zuciyarta ta karye da al'amarin anya kuwa UMARU ba yaudararsu yake ba? a tunaninsu duk shine ya fitar da kudi masu nauyi aka had'a lefan, al'amarin dai duka bai musu dadi ba, ace ayi ta abu d'aya sai kace cin k'wan makauniya.

Tana kuka tace."Ashe Uwale har dake za'a had'a baki a tozarta ni! me nayi miki kika tsanani har ki ka bada goyon bayan auro wata bayan gani, kin san kuma tsayin shekarun dana dauka ina jiransa, me yasa zaku ci amanata."

Hawayen tausayinta ta share kafin tace." Hamra'u ashe duk abunda yake faruwa UMARU be fada miki ba.?

Ta girgiza kai da fadin." Ni be fada min komai ba kuma kema ai be kamata ki 'boye min ba, yana da kyau duk abunda yake faruwa ki sanar dani nasan matsayina."

Tace."Hamra'u kada ki zarge ni ko kuma kiga laifina akan wannan al'amari, wallahi ni kaina ban san da maganar ba sai ana i gobe zai yi tafiyar nan yake sheda min halin da ake ciki, kuma ya tabbatar min da cewa wannan auran da zaiyi ba zai hana ya aureki ba, al'amarin ne yazo a k'urace shiyasa kuma kinga mahaifin yarinyar nan babban mutum ne wannan shine dalilin da yasa beyi jayayya dashi ba, a yanda na fahimtashi shima Auran zeyi shine saboda ganin mutuncin mahaifin yarinyar saboda haka ki kwantar da hankali UMARU ya tabbatar min da cewa kece za'bin

Please Login or Register in order to submit comment