Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi yace "Ina yini kawu?" Kawu ya kallesa yana maxurai yace "Lafiya lau daga ina, wa ku ke nema" Aliyu yayi kasa da murya yace "Ni ne mijin khadijah, mun xo gaishe ku ne kawai kawu" da sauri yace "Toh madalla... Gaisuwa ce kawai koh" Aliyu ya gyada masa kai yace "Eh kawu" khadijah ta karaso har gabansa ta durkusa kanta a kasa tace "Ina yini kawu?" Yace "Lafiya lau" Kai kana ganin yanda yake maxurai kasan duk a tsorace yake, Aliyu yayi murmushi yace "Ka kwantar da hankalin ka kawu, xumunci kawai ta sa ni in kawo ta tayi" Yana gyada Kai kamar kadangare yace "Madallah" Khadijah dai ta kasa cewa komai, bata taba xaton ganin Kawunta da iyalensa a halin da ta samesu ba, ganin gaba daya mutumin is uncomfortable Aliyu yace "Kawu xa mu koma yanxu, don gobe da safe xa mu wuce uk shine tace in kawo ta..." Kawu ya kasa kallon khadijah sai gyada kai yake yana cewa Madallah Kamar xararre, Dubu hamsin Aliyu ya ajiye gabansa, Kawu ya dauka yana kallonsa, lkci daya idanuwansa suka kada yace "Maa sha Allah, nagode nagode nagode Allah yayi albarka" Aliyu yace "Ameen" a sanyaye Khadijah tace "Allah ya baka lafiya kawu" hawaye ta gani idonsa amma yana ta boyewa bai son su gani yace "Toh Amin, sai a yayyafe...." murmushin karfin hali tayi tace "Nima ku yafe min kawu, Allah ya yafe mana baki daya" hatta Maimuna sai da tace da khadijah a yayyafe da xasu wuce, ganin bata ga kishiyarta ba tace "Mama Ina mamansu Usman?" Maimuna tace "Ta amshi takardar ta ta wuce kusan shekara kenan" khadijah bata ce komai ba duk jikinta yayi sanyi har suka bar gidan xuwa inda xa su samu mota xuwa kano. Sai bayan la'asar suka shigo kano, Khadijah sai bata fuska take irin ita ta gaji din nan, ya langwabar da kai yace "Toh ai we still have 3 more hours journey kike bata fuska madam" ta xaro ido tana kallonsa tace "Ni dai na gaji wllh" murmushi yayi yace "Just reserve this comment, xa su maki amfani anjima idan mun isa gida da daddare" Kallonsa kawai take kamar mai son gane ma'anar abinda yace, can tace "Kamar ya?" instructing din mai adai daitan da ya tsayar masu yyi yace "Airport xa ka kai mu" Khadijah ta turo baki ta shiga shima ya shiga yana matsa cinyarta a hankali, tayi kara tana kallonsa, dauke kai yayi da sauri yana murmushi, har suka isa airport idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, ya siyar masu tickets na kaduna, hudu da rabi jirgin ya tashi, cikin few minutes suka sauka kaduna. A gajiye ta shiga parlor ta wuce dakinta direct ta fada kan gado, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Sallahn fa?" Kallonsa tayi a hankali tace "Xan yi" yace "Toh tashi kiyi" Sai da ya idar da sllhn shi ma sannan ya fita eatry siyo masu abinci, yana dawowa ya shigo dakinta, xaune ya sameta kan darduma yace "Come down mu ci abinci" Tace "Sai na fara wanka" yace "Toh jira ni in xo muyi" mikewa tayi da sauri ta shige bathroom din ta sa makulli, yana dariya ya juya ya fita dakin. Karfe goma na dare tana kwance parlor kan 3 seater har bacci ya dauketa taji an dauketa kamar baby, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya manna mata kiss a lips dinta ya shiga bedroom dinsa ya kwantar da ita saman gado, ya kwanta shi ma ya shige jikinta... Kamar xata yi kuka tace "Bacci fa nake ji" yayi kasa da murya yace "Wai baki son mu tafi da tsaraban baby mai kama da ke UK ne?" Hararansa tayi ta juya masa baya tana turo baki, ya marairaice mata yace "Plsss Ummu Shureim" kukan shagwaba ta fara masa as usual, nan ta kara rikitar da shi, ita ma dai kamar jira take ta bada kai bori ya hau, they couldn't just get enough of each other, ta kankamesa kamar xata koma jikinsa su xama daya, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace "I love you Iman..." Shiru tayi idonta a lumshe, bayan wani lokaci ta kwanta kan kirjinsa a hankali tace "I love you more Abu Shureim" kissing dinta ya shiga yi, and that really turn her on. Da asuba tare suka yi wanka ya ja su sallah a dakin, a hankali ta dawo kusa da shi ta durkusa murya can kasa tace "Good morning Abu Shureim" ya jawota jikinsa yace "Morning Ummu Shureim...." Murmushi tayi tace "I am missing him" yace "You better don't, shi din me iyaye ne da yawa, so kar ma ki wani sa shi a rai" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki hada abubuwan da kika san xa ki bukata, anjima xa mu wuce airport" tace "But I have everything back there, a can gidana..." Kallonta ya dinga yi kafin yyi murmushi yace "Kina tunanin xan je gidan ki in xauna wife?" Shiru tayi tana kallonsa, yyi yar dariya yace "Lallai, I rather rent a new flat, balle ma muna da apartment can din, kawai I prefer staying a gun aunt dina ne saboda kadaici" murmushi tayi bata dai ce komai ba, sai dai ita ma hakan ya mata, coz she don't think xata iya xama gida daya da su Khaleel, it's just not possible, lakutan hancinta yyi yace "Kin fi son can ne saboda yar uwar ki" da sauri tace "Not at all, ur wish is my command sir...." Rungume ta yayi yace "That's sweet of you baby"

A year and a half later....

Tun da khadijah ta tashi yau take ta girke girke iri iri duk da xaxxabin da ta dinga yi kwana biyu da suka wuce, kana ganinta ka ga mai karamin ciki, yanxun ma daurewa take girkin da take yi, don aroma din na hawa mata kai but she have no option, Aliyu ne ya shigo kitchen din yana rungume da little Fatima, yarinya da baxata wuce shekara daya da few months ba, she is just a duplicate of her mother, babu inda ta bar khadijah, kyakkyawa ce ta karshe yarinyar, Khadijah ta kallesu tace "Dear kasan yanxu xata ce sai na dauketa kuma ni ba taya ni aiki xaka yi ba" Yar dariya yayi yace "Tsoro nake kar in fita da ita tayi ta min ihu a mota, xan je airport dauko Umma, same flight kuma suka bi da su Baby" Khadijah tace "Lahh da gaske?" Yace "Sure, Aryan ma ba yarda xai yi ya bi ni ba da sai mu tafi tare da su..." Tace "Ae tun daxu na gane gida yake son wucewa ya gaji da mu" dariya Aliyu yyi yace "Aa miskilanci ne kawai, ya ki yarda in dauke sa ma" Ta dauraye hannunta ta amshi Noor ta mana masa kiss a lips dinsa tace "Toh Allah ya tsare babyna...." Yace "Uhn you are looking for trouble koh" yar dariya tayi ta kashe masa ido tace "Don ma ban maka french one ba" Ya wara ido yace "Toh mu je daki ki min" ta hararesa tace "Naki wayon" juyawa yayi ya fita yana murmushi, yau ranan farin ciki ne gareta don a ranan xata sama qualified pharmacist, a ranan xa ayi convocating din su, kafin Aliyu su shigo gidan ta gama komai tana jiran Ummarta da yanxu take auren yayan mahaifiyarta wato dad din su Maimoon, tare da Baby uwar gida ga Barrister Sudais, fitowa parlor tayi jin shirun Aryan yayi yawa, xaune ta ga little balaraben kan kujera kiris yake jira ya fara kuka, ta karasa gun sa tana murmushi ta ajiye Noor, ta daukesa ta rungumesa tace "Haba sweetheart, in dafa maka indomie xaka ci?" Kitchen ta koma tana rike da shi ta daura ruwan indomie sanin abinda yake ci kenan, tana tsaye har ya dahu ta juye a plate ta dawo parlor ta xaunar da shi ita ma ta xauna ta shiga basa, Babu inda ya bar ubansa tun daga kyau har gashin kansa, hatta idonsa irin na babansa ne, murmushi tayi tana ci gaba da ba sa indomien yana ci, tana gama basa ta wuce daki da shi ta sauya masa kayan jikinsa duk da ba su yi komai ba ta dauko masa favourite toy dinsa ta basa ya amsa ta kunna masa cartoon ta xaunar da shi kusa da Noor da ta kwanta kan kujera, sannan ta shiga daki don yin wanka, tana shiryawa bayan ta fito ta ji shigowar mota, ta gama saka kayan da sauri ta fito, Aryan na ganin xata fita ya sauka saman kujera xai fara kuka, ganin haka ta dawo ta daukesa, Noor ta fashe da kuka ita ma, dariya tayi ta dauketa ita ma, tana rike da su ta fita compound, tsaye tayi tana murmushi ganin motar Khaleel ne, jawahir ta fito daga motar, Aryan na ganinta ya fara murna, khadijah ta saukesa yaje da gudu ya rungume uwarsa ta daga sa tana dariya tace "Kai lallai khadijah, dubi yanda kika maida min yaro kato, wani irin abinci kike basa haka" dariya khadijah tayi tace "Bayan ma ya rame, duk kwanan nan a dole yake xaune gidan, naga alamar kewar ki yake" Khaleel ya fito daga mota yana murmushi ya nufo ta yace "Oum shureim good morning" tana murmushi ita ma tace "Morning doctor...." ya amshi Noor yana shafa dogon gashinta idonsa a kan khadijah yace "Congrat once more, Allah ya sanya alkhairi, our pharmacist..." Tace "Ameen Thumma Ameen, thanks much Abu Aryan" Bata rufe baki ba motar Aliyu ya shigo gidan, Baby ce ta fara fitowa daga motar tare da little Amira, khadijah ta wara ido tana kallonsu ta nufe su da sauri, Barrister Sudais ya fito daga gaban motar with Shureim, sannan Umma da ta fito ita ma rike da little Farouq yaron da baxai wuce wata bakwai ba da baby take goyo, khadijah ta rungume baby cike da murnan ganinta suka dinga babbaka dariya, lkci daya ta tafi gun Ummarta ta rungume ta ita ma, tsabar murna ta kasa cewa komai, ta rasa me xata ce, tana sake Umma ta daga handsome yaronta sama ta rungume sa ya dinga kissing fuskarta very happy seeing her..... Aliyu ya fito ya jingina da mota ya rungume hannunsa yana kallonsu, Kamar yanda Barrister Aliyu da Dr Ayman ke kallonsu suna murmushi su ma....



*ALHAMDULILLAH*


A nan na sauke littafina mai taken *Noor-Al-Hayat* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min....👏🏻 Darussukan dake ciki Allah yasa mu amfana da su Amin. Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah... She is my first love, my role model, my momma, my world, my everything... Allah bar min ke Hajjaju Yaya❤ My sweet Anty Didi ur daughter Jiddo is greeting with respect, tnx for being there for me during this book, Allah ya raya su Aneesah... And my second role model Anty Rukaiyya...😍 am so grateful for the encouragement from the beginning of this novel till the end, I always gat ur back small mum ur daughter Khaleesat Haiydar is saying a big thank you, Allah bar mu tare ya raya Little Khaleesat Haiydar, Baby and Jaheed...
Na sadaukar da littafin *Noor-Al-Hayat* xuwa ga lovely sister na, my Blood... Khadijah M Bello (Amira/Baby) nd my sweet cousin like no other Khadijah Sadi Yusuf (Baby) Allah ya albarkace rayuwar ku ya raya mani ku bisa imani, ya baku ilimi mai albarka da amfani. Sakon gaisuwa ta na musamman xuwa ga wa enda for sure ba siyan littafin Noorul Hayat suka yi ba, ihisani kawai suka min, duk ina sane da ku kuma na so contacting din ku but I lost my contacts, ban san ya xan yi in same ku ba, Amma ku sani I will for ever be grateful, Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi duniya da lahira, nagode nagode.... And finally my fans, ban taba xaton yea da gaske I have fans ba sai a littafin nan, you guys really patronized me fiye da tunani na, you all made me feel loved😥 words alone can't express how happy I am, ku sani... Billah Khaleesat na ji da ku har ranta, Ina son ku, Ina alfahari da ku, Ina maku fatan alkahiri, Ina maku fatan rabuwa da iyayen ku lafiya, Ina maku fatan daukaka, Ina maku fatan gamawa da duniya lafiya, ina maku fatan samun aljanna, I wish you all the very very very best in life, nagode nagode nagode... Allah ya sa mu cika da imani ya yafe mana kura kuran mu...👏🏻

Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) 📚✍🏻

Thanks once more for patronizing my book fans... For those still wanting to buy the complete document it's just 300 Via transfer 👉🏻 3276052019 Hauwa Jiddah Bello, fcmb.

07087865788.
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment