Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu, ke daya ce cikin katon gidan nan?" Ta girgixa kai tana murmushi tace "A'a bani kadai bace, mu shiga ciki Barrister" Yace "Do I have to Amira?" Tace "Why not?" Daga haka ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, yana shiga cikin gidan ganin fararen kujeru da table a bangaren flat dinta karkashin wani shade yace "That's all, I will prefer staying outside" daga haka ya nufi wajen ya xauna ta tsaya tana kallonsa, bata fuska tayi tace "Barrister mu shiga ciki mana kaga fa akwai sanyi wajen..." Yace "Ke dai kike jin sanyin, just get me my tea sai ki yi wucewar ki ciki tunda kina jin sanyi" murmushi tayi ta wuce ciki sai ga ta ta fito da tray mai dauke da karamin flask da plate din cake" ajiye masa tayi ta ja kujera ta xauna tana dubansa tace "But me yasa baka son shiga ciki Barrister?" Ya bude plate din ya dau cake daya yace "What did you mean?" Ta xaro ido tace "But is there anything wrong with going inside?" Shiru yyi yana kallonta, can ta wara ido da sauri tace "Ohh yes you are right Barrister" sai kuma tayi murmushi, murmushin yayi shima ya kai cake din baki, a hankali tace "But.... Seven years back...." Sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi kafin yace "Don't forget you where sick and pregnant then, I have no choice...." shiru tayi a sanyaye tana kallonsa, ya buda ido sosai yace "Wait... Ina Shureim din?" Ta sauke idonta daga kallonsa, cikin sanyin murya tace "Sun tafi Nigeria da Aliyu" da mamaki yace "Wani Aliyun?" Bata ce komai ba na few seconds kafin daga karshe tace "Aliyu dai" Sudais ya ajiye sauran cake din hannunsa yace "is he also in Uk?" Kai ta gyada masa, Bai iya ya sake cewa komai ba, bayan wani lkci a hankali yace "Kuna haduwa da shi kenan?" Ta sauke idonta daga kallonsa tace "Sometimes in school" Sudais bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, tana ta kallonsa har ya gama wayar sanann ta sunkuyar da kanta, ya ajiye wayarsa in a very low tone yace "Amira?" A hankali ita ma tace "Na'am" yace "I don't want to deprive you of anything you wish for ur self, be frank plss Amira ki fada min gaskiya, did you want to go back to the father of ur kid?" Kallonsa ta dinga yi da wani expression, cike da karfin hali tace "Ban gane ba Barrister" Dago kai yyi yana kallon eye balls dinta yace "I mean, kina da ra'ayin komawa gun Aliyu ku yi aure ne?" Ta fashe masa da kuka tace "Anybody can say this but not you barrister, kai me tuna min irin wahalar rayuwar da na sha ta dalilin Aliyu ne, you witnessed everything, ko kuma ince tare muka sha wahalar barrister coz all those time you where by my side, Aliyu raped me without mercy har yau memory din na kai na very fresh, scene din na ido na, bayan faruwar hakan ya canxa min a gidan ya daina ma amsa gaisuwata ya daina xama duk inda nake, daga karshe he sent me away without thinking twice, with huge sum of money bayan yasan bani da kowa, Bai yi tunanin ko xan gane gida ko baxan gane ba" kuka take sosai, Sudais ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido ya kasa cewa komai, Tana ci gaba da kuka tace "Har yau ni ban ga wani prove that will convince me that ba da gangan Aliyu yayi min abinda ya min ba, ban ga prove da xan yarda cewar ba da gangan yayi raping dina ba, fine... Mahaifiyarsa cewa tayi it's a set up, did she have any choice? Dole ta kare d'an ta, an taba set up da rape dama?? Wllh dalilin marigayin yaro na nake raga ma Aliyu har nake kulasa naji kuma xan iya xumunci da shi albarkacin yaran dake tsakaninmu, of recent I dreamt of my little boy telling me to forgive his dad, so why will I not forgive him, nasan ya cuce ni ya bata min rayuwa but he gave me happiness at the same time... My boys" hade kanta tayi da table tana kuka sosai, Sudais ya bude idanuwansa yana kallonta cike da tausayin ta, cikin sanyin murya yace "Am sorry Amira, you misunderstood me, I know ur pain but..." Ta dago hawaye na sakko mata tace "But what?" Yyi kasa da murya pleadingly yace "I am sorry plss" kin cewa komai tayi, yace "Kin hakura?" A hankali ta gyada masa kai, ya lumshe ido ya bude yace "Nagode dear, do you have any plans for our wedding?" Ring dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace "Kin yi shiru" wani mugun haushin kanta taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d'an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Ke da wa kuma??" Da sauri ta kallesa ta xaro ido tace "Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san...." Katse ta yayi yace "Nasan ba da ni kike ba Amira, I can see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of" ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace "Uhn ba komai fa" murmushi yayi yana shafa kansa yace "Toh shkkn" flask din ya bude ta mike da sauri tace "Bari in xuba maka" daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace "In sa maka Madara?" Ya girgixa kai yace "Noo, I prefer it black" Komawa tayi ta xauna tana murmushi tace "Toh, what will you take for dinner?" Ya d'an bude ido bayan ya dau Lipton din yace "Da daddare sometimes ina shan tea with irish and egg" ta langwabar da kai tace "Toh da safe fa?" Yayi murmushi yace "Tea and bread" da mamaki ta kallesa tace "Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai any other food?" Yace "Ina ci idan na samu" shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane Matarasa ce bata girki kenan, d'an murmushi tayi tace "Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba" ya xaro ido yace "A'a ku mata da bakwa son girki mai wahala don't stress ur self dear I will take tea na riga na saba" tace "No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake so xan girka maka anjima" murmushi yayi sosai yace "Toh nagode Amira" Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la'asar bane..." Ta rakasa har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace "Barrister baka dawo ka karba ba kuma" yayi kasa da murya yace "I really don't want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala..." Katse sa tayi tace " Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun ragwayen mata dai" dariya yayi yace "Ohh really?" Tace "Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss" a hankali yace "Toh gani xuwa Amira, I am proud of you" murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa a hankali tace "Bacci kake barrister?" Yace "Uhn am now awake" tace "Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka breakfast" ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace "Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito" tace "Toh, kayi hakuri" ya wara idanuwansa yace "Hakuri kuma dear" murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d'an tsaki tayi a ranta tace do I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna.

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace "How are you Iman" tace "Fyn, how about my son" yace "Naga kin ma mance da shi gaba daya" ta hade rai tace "Taya xan mance shi?" Murmushi yayi yace "Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl" tace "Kun dawo ne?" Yace "Yea daxu da yamma" shiru ta d'an yi kafin tace "Bring him in the afternoon" yace "Alryt then" daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa "Sannu" Khadijah tace "Ina yini?" Yarinyar tace " Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo" Khadijah ta d'an yi murmushi tace "Ehh yanxu na dawo" yarinyar tace "Ayya, to Sannu da xuwa" Khadijah tace "Idan na gama xan shigo yanxu" yarinyar tace "Toh sai kin shigo" daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace "Ina yini" yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace "Lafiya lau" shigowa parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Ina yinin ku" amsa mata suka yi da fara'a, wata a cikinsu tace "Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon" Yarinyar da ta bude kofar tace "Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai" Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace "Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya" warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace "Lah Khadijah ashe kin dawo" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Ehh ban dade da dawowa ba" Maryam tace "Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna" Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace "Khadijah har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa" Khadijah tace "Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita ce" A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara'a tace "Mun taho rakiyar amarya" Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace "Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya" sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace "Ameen" Deejah sai kallon jawahir take alamar bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace "Lahh ashe har kin shigo" Khadijah tayi murmushi tace "Eh na shigo" ta karaso ta xauna ita ma tace "Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?" Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace "Ikon Allah kenan" Safeenah tace "Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki" Khadijah tayi murmushi tace "Na amsa sosai" hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace "Xan dan shiga ciki ina aiki ne" Safeenah tace "Amma xa ki dawo ai?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ehh xan dawo anjima" Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya gida" fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la'asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren yace "Amira" tace "Na'am good day" yace "Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba" Yar dariya tayi tace "Barrister amma ai kai ma kasan sun yi kyau" yace "My question is wanne kika fi so" tayi murmushi tace "Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister" yace "Ask ur frnds then" tace "Toh xan tambaya" yace "Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai" a hankali tace "Toh barrister" daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace "Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya" kallonta kawai yake, can a hankali yace "Khadijah" kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, "Ki fito muna waje" abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace "Jira ki karbi sakon Mumy" Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace "Mun gode Allah saka da alkhairi" Har ta juya xata tafi sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace "Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya" karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika mata, ta amsa tace "Thanks" yace "Don't forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata" tace "Har yanxu bata samu sauki ba?" Yace "She is still at the hospital" Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace "Toh Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen" Cike da karfin hali tace "Ya jikin iklima fa?" Ya shafa kansa yace "Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty Khadijah" Khadijah tace "Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma" Yace "Alryt" shiru ta kara yi, sai kuma ta kallesa tace "Ina son tambayar ka pls" yana kallonta ya rungume hannunsa yace "Ina jin ki"

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

Khadijah tace "Ya dangartakar ku da su Deejah?" Ya d'an yi shiru yana tunani kafin yace "Wacece Deejah kuma?" Ta kallesa tace "Deejah ce baka sani ba?" Buda ido yyi yace "Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam" Khadijah tace "Ehh" yace "I think, noo they are just family frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that's just it" Khadijah tace "Toh Maryam fa?" Ya shafa kansa yace "Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin" Khadijah tace "Ohk" yana kallonta yace "But why did you ask?" Wani kallo tayi masa tace "Is there anything wrong with me asking?" Murmushi yayi yace "Not at all, yaushe xa ku fara exams?" Tace "Nan da 3wks" yace "Ohk Allah ya kai mu" tace "Ameen" daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace "Waye?" Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace "Khadijah I want to spend the nigh here if it's ok by you" Khadijah tace "Oh you are welcm" daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa "Su Anty Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi" Khadijah tayi murmushi tace "To mu shiga ciki" bin bayanta Safeenah tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan" Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma tace "Ki hau saman gadon" Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace "Hope baxan takura ku ba" Khadijah ta xauna gefen gadon tace "Haba dai ba wani takura" Safeenah tace "Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki" Khadijah tayi dariya tace "Haba dai" Safeenah tace "Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having same parent" Khadijah tace "Ayya that's nyc" Safeenah tace "Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan" Khadijah ta gyada kai tace "Na ma kusa gama wa" Safeenah tace "Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?" Khadijah tace "Kaduna" Safeenah ta gyada kai tace "Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja muke" Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace "Let me answer my call Khadijah" daga haka tayi picking call din, murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she's just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa... Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim

Please Login or Register in order to submit comment