Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallon khadijah da ke bakin kofar fita tana jiransu, ganin kallon da yake mata ta dauke kai da sauri dai dai lkcn da idonta ya sauka kan barrister sudais dake tahowa rike da kyakkyawar daughtern sa, matarsa na biye da shi tana rike da ledan siyayyar da suka yi, still Khadijah tayi a gun da take tsaye taji komai nata ya tsaya cak, yanda take kallonsa shi ma haka yake kallonta ko kiftawa babu har ya iso dab da ita ya sauke idonsa kasa ya mika ma security dake bakin kofar receipt din kayan da ya biya aka mayar masa sannan ya fita mall din, matarsa na biye da shi.

Khadijah ta bi sudais da kallo cikin shock sosai, fita tayi da sauri tana ci gaba da kallon sa xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya juya bai san ta fito ba suka kara hada ido yayi saurin dauke kansa, motarsa ya nufa ya bude, matar ta bude back seat ta ajiye ledan hannunta sannan ta bude seat din gaba xata shiga ta dakata da sauri tana kallonsa tace "Lahh Barrister na bar masu wayata a counter..." Bata jira cewarsa ba ta juya da sauri ta koma mall din, Sudais ya kara daga kai ya kalli khadijah, bata san lkcn da ta nufesa ba tana kallonsa ta fashe da kuka sosai cikin raunin murya tace "Why are you pretending you don't knw me? Did I deserve that Sudais.... Me yasa kake yin kamar baka taba sanina ba" sosai hawaye ke xuba idonta, Ya kasa kallonta ya kuma kasa cewa komai ba, ganin Jiddah na fitowa mall din ya sa ya shiga motarsa ya rufe, gwiwa a sake Khadijah ta koma baya tana kallonsa ko kiftawa babu kai kana ganinta kasan she is over shock, Tun daga nesa jiddah ke kallon khadijah da tayi saurin share idonta, har ta iso tana mata wani kallo daga sama har kasa tace "Baiwar Allah, do you have any problem? Tsayuwar me kike a nan" Khadijah bata kalleta ba ta juya da sauri ta bar wajen ta koma can jikin wani mota xuciyarta na mata xafi, ta fashe da wani matsanancin kuka, me yasa ko da yaushe a cikin mall take haduwa da abinda ke mugun daga mata hankali, yau ga ta ga sudais yyi kamar bai taba sanin ta ba, me tayi masa xai mata haka, ta sulale wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, bata yi deserving yyi mata haka ba da ya bari ko godiyar abinda yyi mata a rayuwa ta kara masa don tasan baxa ta iya biyansa ba kuma ba lallai su sake haduwa ba. Jiddah na shiga motar ta kalli sudais fuska a murtuke tace "Wacece ita Aliyu?" Buda hannu yyi alamar bai sani ba, ganin kallon da take masa yace "Kawai ce min fa tayi in ara mata waya xata yi making call, ni kuma nace bani da airtime, that's all madam" tsaki jiddah tayi cikin bacin rai tace "Da ta fada a gabana in koya mata hankali yau wllh, irin yan iskan matan nan ne masu bin maxajen mutane a titi, banda haka ta baka ajiyar kati ne xata ce ka ara mata waya?? dear idan baka son matsala da ni wllh ka bar ko da responding wa ennan mutanen, idan xa su shekara suna ma magana kar ka ko da kalli inda suke balle ka bude baki ka basu amsa ka xama kamar deaf and dumb, domin kuwa yawancinsu da asiri suke xuwa, ni dai na gaya maka kada a fara jin kan mu kuma" "Toh" kawai Sudais yace ya tada motarsa ya bar harabar mall din tana ci gaba da mita, Khadijah taji xuciyarta ya mata nauyi ta dinga kuka ko xata samu relieve amma kamar ana kara mata ciwon da take ji, babu irin neman da khaleel bai mata cikin mall din ba amma bai ganta ba, jawahir ma sai dube dube take tana neman ta, atm dinsa ya mika ma jawahir yace "Dear gashi you pay the bill" tace "But the pin?" Fada mata yyi ya fita mall din ta bi sa da kallo a sanyaye, little Sudais na kallon jawahir yace "Anty ba mu ga Antynmu ba" jawahir ta duka tana masu murmushi tace "Yanxu Dr xai nemo mana ita cuties" daga haka ta mike ganin an xo kanta a gun biyan kudin. Tafiyar few minutes sudais yyi ya tsayar da motar, Jiddah dake kallonsa ganin yanda ya ja tsaki tace "Ya aka yi Abban Amira?" Ya d'an dafa kansa yace "Wannan matsalar dai da nace maki motar ta bani last week, I don't knw what's wrong with this car" tace "Yanxu baxai tashi ba kenan?" Yace "Sai wani ikon Allah, gashi ban san ko Ahmad na garage ba da na kirasa ya taho yanxu... Am just bored of this car" ta hade rai tace "Toh ni ya xa muyi yanxu ga ranan yamma" ya kalli cute angel dinsa me suna Khadijah yana kiranta da Amira ya ja hancinta ganin yanda take kallonsa da kwala kwalan idonta yace "Kar Amirata ta sha wahala bari kawai in tsayar maku da adai daita ku wuce gida ni xan taho daga baya" Jiddah tace "Wai to ka kara gwada tada motar mana, ba girman ka bane barrister a gan ka bakin titi mota ta lalace" Murmushi yyi ya bude motar ya fita ya tsayar da adai daita ya gaya masa sunan anguwar su sannan ya xaga ya bude motar yana kallon jiddah yace "Ki fito ku wuce yanxu xan taho nima in sha Allah" ta hade rai tace "Aa mu je gaba daya kawai, ai babu me satar motar idan ya so sai Ahmad yaje gida ya karbi makulli ya lallaba ya kai motar gareji" kallonta ya tsaya yi kafin yace "Plss be a good wife and humbly come down kinga na tsayar maku da d'an sahu, you don't worry about me I will be okay sai kace ba namiji ba" da kyar ya lallaba ta ta sauka ta shiga napep din ya mika mata Amira da kayan da suka siya a supermarket, yana tsaye har napep din ya sha kwana sannan ya shiga motarsa da sauri ya tada yyi reverse ya koma mall din at high speed kamar xai tashi sama. Babu irin duban da khaleel bai ma khadijah ba a haraban Shopping complex din, har yyi give up a xaton sa gida ta wuce sai dai kuma haka kawai ya ji ransa ya baci, ya juya kenan xai koma ciki ya hangota durkushe bayan mota, da mamaki ya dinga kallonta lkci daya ya isa gabanta ya durkusa yace "Me ya faru Khadijah me kike yi a nan?" Ta kasa cewa komai sai shessheka take hawaye na sakko mata, a rikice yace "Ki min magana don Allah khadijah, me ya faru" ganin ba shiru xata yi ba ya daga ta ya nufi gun motarsa bai damu da mutanen dake kallonsu a gun ba ciki har da jawahir da ta fito da su shureim ya bude back seat ta shiga ya rufe, Sudais ya taho gun khaleel da sauri hankalinsa tashe yace "Uncle what's wrong with my Anty" Daukan sa Khaleel yayi yana murmushi yace "She is having a headache" kokarin sauka ya shiga yi a jikinsa kamar xai yi kuka yace "Uncle ina son in xauna kusa da ita I don't like d front" bude masa bayan motar khaleel yyi ya shiga sannan ya rufe, shi dai shureim na tsaye can kawai ya fashe da kuka, jawahir ta duka tana kallonsa da mamaki tace "Me ya faru handsome" Khaleel na ganin haka ya karasa ya daukesa shi ma ya bude back seat din ya xaunar da shi sannan ya rufe, jawahir dai na tsaye tana kallonsu ya bude mata front seat ta karaso ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver, Khadijah ta hadiye kukan da take da kyar ganin yanda yan biyunta suka rikice su ma suna kukan tana yin shiru su ma suka yi shiru, khaleel sai kallonta yake ta madubi duk ya ji ba shi da nutsuwa kamar ya jawo ta jikinsa ya lallasheta, Jawahir ma sai kallon khadijah da yaranta take, Khaleel na fita mall din da motarsa sudais ya shigo shi kuma da tasa motar, ko parking din kirki bai yi ba duk da maganar da securities din gun ke masa ya wani rikice ya dinga duba nook and cranny din wajajen yana nemanta har ciki sai da ya shiga amma babu khadijah, ya fito jikinsa a sanyaye ya hade kansa da motar sa.

Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace "Toh ku fito" da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace "Uncle Anty bata sakko ba" khaleel ya shafa kansa yace "Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku" yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace "Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?" Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace "No plss I don't want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?" Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace "Khadijah" a hankali tace "Uhn" yace "Kukan me kike yi?" Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace "Sudais" still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace "What about him?" Har lkcn idonta a lumshe tace "I saw him" dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace "Where?" Ta ki kallon kwayar idonsa tace "A inda muka je shopping" da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace "He shunned me, he pretend he don't knw me...." Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace "Khadijah..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" dai dai kunnenta yace "forget about sudais plss, forget him...." Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace "Toh, nagode" ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace "I... I know I love you from day 3 of our encounter....." Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba.

Khaleel ya dago kanta yana kallonta, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi murya can kasa yace "Kin tuna ko in tuna maki" dauke kanta tayi xata bude motar yace "Wait" still tayi a wajen bata yi motsi ba, yace "promise me baxa ki sake kuka a kan hanya ba, sannan you wil forget your past and face the future" shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Khadijah" ta gyada masa kai kawai, yace "Noo, say it out" bata san lkcn da tayi murmushi ba a hankali tace "Ohk" yace "Ohk kadai" kamar bata son ya ji ta tace "I promise" yyi murmushi yace "Yauwa baby" ta turo baki tace "Tana can kayi dropping dinta a gida" wara idanuwansa yyi yace "Wai jawahir?" Khadijah ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Ita daban ke daban..." Daga haka ya bude side dinsa ya fita ita ma ta fito yana kallonta, a hankali tana fidgeting fingers dinta tace "Thanks" bata jira cewar sa ba ta wuce cikin gida da sauri, ya bi ta da ido. Aliyu na jin alamar Farouq xai shigo parlorn ya jefar da wayarsa dake hannunsa kan kujera kusa da wanda yake, yyi concentrating kan nasa wayar dake hannunsa, Farouq yace "Toh baka taba abincin ba har ynxu Dr" Aliyu yace "I told you I am not hungry fa, ni xuwa ma xan yi in tafi yanxu" Farouq yace "So soon" mikewa Aliyu yayi yace "Sure, tun da baka da kirki" Farouq yyi murmushi yace "Ko da kai da khaleel baku fada min komai ba na dai san akwai yar tsama tsakaninku, domin kuwa kamar yanda ka min xancensa haka shi ma yyi min naka, amma bai yi requesting karban digit dinka ba ko sanin inda kake, shi yasa kai ma baxan baka na sa ba" ko Kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa Farouq ya bi bayansa yana murmushi, Aliyu na isa gida direct sama ya tafi, har xai shiga dakinsa ya dawo ya bude kofar dakin baby, tana linke kaya ya same ta, ganinsa ta hade rai ya karasa cikin dakin, da farko rasa abun cewa yyi can kuma yyi karfin halin cewa "Ina yan gidan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Suna asibiti" yana kallonta yace "Who is sick?" Tace "Iklima" sai a lkcn ya tuna yana kokarin fita mumy ta kira saleem yayi driving dinsu xuwa asibiti, yace "Anyi hospitalizing dinta ne?" Baby ta gyada masa kai, yace "Su waye a asibitin?" Tace "Su mumy, mun dawo daukan abu ne da Anty Khadijah" yace "Tana ina?" Tace "Tana dakinta ina ji" fitowa yyi daga dakin har xai wuce nasa sai kuma ya bude na anty Khadijah, babu kowa a dakin ya gani, ya dinga kallon jakarta dake kan gado an xaxxage komai na ciki, karasawa yyi ya ga duk tarkacen takardu da kayan kwalliya ne sai wani kulli a fallen zani, dauka yyi yana jujjuyawa yana kallo, murya ya ji kasa kasa a bathroom, yyi still ya kasa kunne don saurare, "Wllh ban sani ba, sai bayan da aka daura auren alamomin cikin ya fara bayyana...." Aliyu yyi tiptoeing xuwa bakin kofar bayin ya jingina da bango yana jin muryar Anty Khadijah radau amma fa a hankali take maganar "Ko kafin bikin sai da na fita tsakar dare na duba ajiyar yana nan yanda yake na kan dutse" shiru ta d'an yi sai kuma tace "Aa gaskiya ta gun angon kadai ne da matsala, shi ma da bai gano cikin ba nasan da idan ya sha wannan garin da ka bada a ruwan shayi shkkn sai kuma yanda muka yi da shi to bai sha ba, to bai sha ba" da damuwa tace "Haba na kan dutse tuni fa aka cire cikin ban san meye matsalar ba tana dai can a kwance har yanxu cikinta ciwo kamar baxa tayi ba, kilan rashin sabo ne, kasan da karafuna ake cire cikin, ni dai yanxu abinda nake so shine ka taimaka ka karkato mana da hankalin shi yaron, wllh shi ke ba mu matsala" tace "Ehh Aliyu sunansa, wlh taurin kansa ya fi karfinsa, ka ladabta min shi... ka tuna wani hadi da ka taba min da dadewa shekaru masu d'an yawa na xuba masa a ruwan tea....?" Da sauri tace "Yauwa to ka kara min irinsa ta haka ne kadai xa mu samu abinda muke so, sai ya tattara ta ya tafi da ita, ita kuma 'ya ta ka tada min kafadunta" runtse ido Aliyu yyi jin furucinta na karshe ya dinga nanata innalillahi wa inna ilai hi raji'un a xuciyarsa, Anty Khadijah tayi wani ihu tace "Dubu Dari da hamsin kuma na kan dutse??? Haba haba a dube ni domin Allah mana, yanxu kudaden wuya suke wllh, ina xan samo har dubu dari da hamsin ni ba Sana'a ba, sai fa yayata ta bani.... Da ma atm dinta na guna ne ban ki in sa ta ba, Duk fa yan kudadena sun kare ta dalilin xuwa gun ka da nake na kan dutse" ta kwantar da murya bayan wani lkci tace "Amma ka fa san nace ni baxan sake wannan harkar da kai ba kake ambatosa yanxu, sai in ce ma yayata xan je ina? Kawai duk ka bi ka wahal da mutum haba na kan dutse, wajen fa da nisa" da sauri tace "To to na ji, ko xuwa jibi xan taho, sai kuma batun yan gidan don Allah ka kara gume min bakinsu wannan karan har da wata kakarsu ta gun uba ana ce mata yaya naga xata bani ciwon kai ita ma, da yake ta fi shekara 10 a gun yar ta dake aure kasar waje to dai yanxu ta dawo duk da ba gida daya muke ba amma dai ance prevention is better den cure, ita ma a kulle min bakinta plss, sannan abu na karshe, ina yarinyar nan da na sa kayi ma Aliyu hadin nan saboda ita, wata warce nace yayata ta dauketa shekarun baya......" Da sauri tace "Yauwaaaa na kan dutse, to ina son yau dai a bincika min ita, a wani garin take yanxu, kuma ya rayuwa ta kaya da ita, ta haife cikin ne ko ta xubar? A bincika min na kan dutse" cike da confusion Aliyu ke kallon kofar bayin don bai gane komai ba a xancen ta na karshe ba, wani hadin take nufi aka yi masa, wani cikin? kuma wacece?? daga haka tayi sallama tace "Toh sai ka ji ni na wajena" Aliyu dake ta xufa yyi saurin barin bakin kofar sai dai tun bai bude kofar dakin ya fita ba ta shigo dakin, wayancewa yyi kamar shigowarsa kenan, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace "Ina yini" kasa amsawa tayi, just to make her comfortable yace "Yanxu na shigo baby ke ce min an kwantar da iklima ban sani ba" ta hadiye abu da kyar tace "Toh ya aka yi?" Ya isa gefen gado ya xauna a hankali yace "Anty ina son mu yi magana dake plss" tana kifta ido tace "Ina ji" yyi kasa da murya yace "Anty ki taimaka ki taya ni ba mumy hakuri, nasan tana fushi da ni, Anty abinda yasa ku ka ga na damu hada ni aure da aka yi da iklima naga ba jituwa muke ba, kuma fa kuna ganin bata jin maganar kowa gidan nan, idan ta fita sai lkcn da ta ga dama take dawowa to ta ina xan fara bata umarni ta bi a matsayina na mijinta yanxu?" Tuni hankalin Anty Khadijah ya kwanta ta kara tabbatar da shigowar sa dakin kenan bai ji wayarta ba, tace "Toh Aliyu hannunka na rubewa ka cire ka yar ne! Sannan ikliman da ka sani da ba ita ba ce yanxu, wllh wllh ta canxa fitan nan xuwa gidan kawaye da take duk ta bari, wllh ta nutsu saboda rokon Allahn da ake mata" a hankali Aliyu yace "Toh shi kenan Allah sa hakan ne mafi alkhairi" Anty Khadijah tayi mugun jin dadi ta na murmushi tace "Toh Amin, amma ka dade baka sanya ni farin ciki irin yau ba my son, Allah ya maka albarka, kuma duk abinda ya faru a da can mu yafi juna Sharrin shaidan ne" yace "Haka ne Anty, yanxu asibitin xa ku koma?" Ta girgixa kai tace "Yanxu daga nan ma kasuwa xa mu da baby kayan ciki xan siyo in farfesa mata shi ke ran ta...." Aliyu yace "Toh mu je sai in ajiye ku a kasuwan daga can in karasa asibitin dubata" Anty Khadijah ta dade bata shiga farin ciki irin na ranan ba, ta kasa yarda Aliyu ne ke mata wannan jawabin, ta dau jakarta ta bi bayan sa tana shi masa albarka. Tare da baby suka tafi kasuwar, Aliyu ya tsaya cikin mota ya jira su gama siyayyarsu ya ajiye su gida sai ya wuce asibiti kamar yanda ya ce, har lkcn he was very shock, ya kasa gaskata abubuwan da ya ji, duk jikinsa ya yi mugun sanyi, Anty Khadijah ta dinga sa ana yanka kayan ciki har na dubu shidda duk na Iklima kadai, Baby dai na tsaye kusa da ita tana kallon ikon Allah, kamar ance baby ta juya ta wara ido tana kallon wasu twins dake tafiya tare da wata dattijuwa duk tana rike da hannunsu, da sauri tace "Innalillahi Anty kalli yaran can" da sauri Anty Khadijah ta juya ita ma idonta ya sauka kan yaran ko kiftawa bata yi, Baby tace "Anty don Allah da wa suka maki kama?" Anty Khadijah ta share wani xufa tana ci gaba da kallon yaran tunani kala kala a ranta, kamar daga sama suka ji ance baxawara??? Duk suka juya da sauri, kyauta suka gani tsaye cikin shiga ta alfarma gun mai kayan miya tana rike da haba baki bude tana kallon Anty Khadijah, Baby tayi wani kara xata tafi ta rungumeta da gudu Anty Khadijah ta fixgota, kyauta na rike da haba har sannan tace "Ikon Allah su baxawara ashe rai kan ga rai? Ana nan ana xawarcin gidan mutane ko anyi aure?" Anty Khadijah da kamannin ta suka canxa tayi kan kyauta kamar xaki kan kace me ta cakumota tana kunduma mata xagi tace "Ni kike kira baxawara don kaza kazan ki, a ina kika taba sani na" dambe ta fara yi da Kyauta da ta xage ita ma lkci daya sai gashi ta na na Anty Khadijah ta da kasa ta dinga duka tana tula mata kasa a fuska mutane suka taru kansu amma kyauta taki saketa dukarta take kamar an aikota tana tula mata kasa a fuska da baki, Baby da ta rude ta tafi da gudu ta kira Aliyu dake mota, Cikin masu kallon fadan har da Nanny da ta ja yan biyun hannunta suka tafi wani rumfa suka tsaya kallon ikon Allah, da kyar aka janye kyauta kan Anty Khadijah da jini ke ta dalala a hancinta da baki, Kyauta ta kunduma mata wani mugun xagi tace "In kin cika yar halak cikin uwar ki da uban ki mu hadu a ba wani shege gobe mu da sa daga inda aka rabamu, axxaluma yar uwar shaidan kawai" daga haka kyauta ta bar wajen tana cewa "Alhmdllh na san inda na dosa a rayuwa yanxu, ke kam a cin arxiki xa ki kare kina rabe gidan mutane" Aliyu ya bi ta da kallo baki bude, Da kyar aka daga Anty Khadijah dake kunduma ma kyauta xagi bayan ta ga ta tafi, Baby ta kama hannunta suka nufi gun mota da sauri ganin yanda ake kallonsu, naman da basu amsa ba kenan duk da ta bada kudi, Aliyu dai ya kasa motsi inda yake, a hankali ya juya xai bar wajen ya ji ance "Uncleee" ya juya da sauri idonsa ya sauka kan twins dake wani gefe a tsaye Nanny kuma na siyan abu a shago bayan taga karshen damben, ya wara ido ya buda hannunsa shureim ya taho da gudu ya daga sa sama ya rungumesa yace "What are you doing here sweetheart?" Shureim ya washe fararen kananun hakoransa yace "We came with nanny and Anty to get something, Ga Nanny a cikin shop Anty kuma tana cikin mota tana jiran mu" kallon sudais Aliyu yyi ya ga yana tsaye ne yana kallonsu, a hankali ya ajiye shureim yana rike da hannunsa ya isa gun sudais haka nan yaji gabansa na faduwa ya duka dai dai height dinsa yace "How are you angel?" Sudais ya sauke idonsa yace "Am good" daga haka ya shiga shagon da Nanny take ciki, Aliyu ya bi sa da kallo, shureim yace "Uncle what are you doing here?"

Please Login or Register in order to submit comment