Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana...." khadijah tace "Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne" Umma tace "Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace "Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun" Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace "Sun gode Ummu" Ummu tace "Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce" ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Ina ji Ummu" sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace "Abuu kasan fa saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi" Khaleel ya shafa kansa yace "Ina sane Ummu" tace "Toh Alhmdllh tun da kana sane, amma ba wani shiri da xa ku yi ne?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace "Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron nan na aura....ina da interest a kanta" Ummu ta dinga masa wani kallo tace "Kana da hankali ma kuwa khaleel???" hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa Arabiya... toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d'an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi" Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace "Khadijah jiran ki fa suke" a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace "I missed you Anty" ta shafa kansa tace "I missed you same" Umma tace "Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota" Khadijah tace "Yanxu Shureim din ya shigo?" Umma tace "Yanxu ya shigo" Khadijah ta karasa gun umma ta rungume ta tace "Ummata sai mun dawo" Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace "Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss" murya can kasa Khadijah tace "Nagode Umma" Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar, Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace "Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim" Umma tace "Lah kin ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport" Khadijah ta gyada mata kai ta fita parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara'a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace "Good morning" yace "Morning how was ur nyt?" Ta sauke idonta tace "Alhmdlh" Wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace "Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan suka yi waya tana yawan tambayar ta shi...." Khaleel yace "Ohk then" daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace "Ku shiga toh" tace "Kai baxa ka shiga ba" da sauri yace "A'a, am waiting for you two a nan" a hankali khadijah tace "Ohk," daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace "Come down" daga mata hannu yyi yace "Anty ki dauke ni" ta hade rai tace "Sakko my friend" khaleel yace "Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?" murmushi kawai tayi ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga, babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi Shureim yake yana kallonsa yace "Uncle good morning" Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace "Morning how are you sweetheart" yace "Am fine" Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace "Good morning Iman" kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa "Ina kwana, wajen mumy muka xo" yace "Ohk tana Bedroom" taki yarda ta sake kallonsa tace "Toh kayi mata magana muna sauri ne" yace "mu je up stairs" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace "Mama good morning" lkci daya bakin cikin dake tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace "Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka" Yace "Ni da Anty na" Aliyu ya juya yana kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace "Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah" kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace "Ina kwana mumy" da fara'a mumy tace "Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?" A hankali khadijah tace "Suna lafiya Mumy" gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace "Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in kawo sa yayi ma ki sallama" Mumy tace "Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema" kallonta Kawai Aliyu yake jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace "Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan" daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta tace "Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai" Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace "In sha Allah Mum na gode" Bayan kusan minti goma Mumy ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace "Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh" khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara'a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci daya mood din mumy ya canxa a hankali tace "Mu shiga ki gaida iklima" Khadijah tace "Toh" daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace "Sannu iklima Allah ya sauwake" kallonta kawai Iklima take ita ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace "Mu je" Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace "Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping" murmushi kawai khadijah tayi tace "Ba komai mumy na gode" Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace "Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah" Khadijah tace "Ameen mumy" daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace "Baxa mu yi sallama ba?" Still ba tare da ta kallesa ba tace "Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba" yayi murmushi yace "Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow" Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace "Me ya samu iklima haka?" Da kamar Aliyu baxai ce komai ba sai kuma yace "She is suffering from Hiv" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace "Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da ita..." Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace "Toh Anty khadijah fa?" Yace "Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?" Khadijah ta girgixa kai tana kallonsa, yace "She had accident 2 weeks back" da damuwa tace "Toh ya jikin nata?" Yace "Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don't knw" Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa tace "Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci" ya d'an yi murmushi yace "No problem" tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace "Barka da asuba" sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace "Good morning" Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace "Allah ya tsare" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ameen" ya rufe masu motar, driver ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace "Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a aljihuna, I told him no but he didn't even listen to me" Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace "Uncle ma ya bani wannan" Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce.

Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi, khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai taxin yace "Bridge street" har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude idanuwanta yace "Ae da mai cab din ya wuce da ke" ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace "Hope baki mance makulli ba" karamar jakar hanunta ta bude ta dubo makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace "Hey, ai ba gudu xan yi da shi ba hajiya" Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace "Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci" mikewa xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace "Have you eaten?" Yace "Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor" Shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace "Kayi wanka?" Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace "Bari in yi alwala" Ko da ta fito daga bayin bata ga Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace "Kun sauka lafiya?" Tace "Alhmdllh Umma" Umma tace "Ina Shureim din?" A hankali Khadija tace "Yana can wajen khaleel" Umma tace "Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?" Khadija ta gyada mata kai tace "In Sha Allah Umma" Umma tace "Toh Allah maku Albarka" Khadija ta amsa da "Ameen" daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace "Ina kika shiga Amira?" Ta langwabar da kai tace "Bacci nayi" yace "Ohk, ya hanya?" Tace "Alhmdllh ya takwarata?" Yace "She's good, where is my son?" D'an murmushi tayi tace "Yana waje" yace "Waje kuma, babu sanyi ne?" Tace "Akwai amma it's not much" yace "Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won't be funny from next week I guess" tace "Haka ne" yace "Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one's, kema ki siya" murmushi tayi bata ce komai ba, yace "Alryt then, sleep tight dear" tace "Toh nagode ka gaida min Amira" yace "Xata ji" daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d'an tabe baki ta rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace "Xa ki fara koh?" Ta hararesa tace "Xan fara me?" Yace "Kin fi ni sani ai" Bata tanka sa ba ta bar wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace "Yes?" Muryar khaleel taji yace "Hmm koh?" Bude kofar tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace "Alryt good nyt" tace "Allah ya tashe mu lafiya" juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace "Me yasa baka yi bacci can ba" yace "I said I want to come to you" bata ce komai ba ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace "Good morning" ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace "Ina kwana?" Yace "Hamdan, Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?" Ta d'an bude ido tace "Gadi na kake yi kuma?" D'an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun windown yana kallonta yace "Ina kika je?" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace "Market" yace "What did you get?" Ta hade rai tace "Ina ruwanka" yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace "Ohk then" daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida masa darduma tace "Idan ka gama sllhn meet me at the parlor" daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace "Anty na gama, good morning" tace "Morning dear" kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace "Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan" yace "Toh" ta bude masa kofa ya fita, ta danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace "Good morning handsome" Shureim yace "Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka" karba yyi yana kallon flask din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace "Uncle tace it's remaining one" rufe kofar yayi yace "Kyaleta xata kawo da kanta" Khadija tayi ta jiran dawowan Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace "Uncle Anty is calling me" xaunar da shi yyi yace "Don't worry she will come in now" Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace "Good morning" dauke kai Khadija tayi kamar ana tilastata tace "Morning" xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace "Good morning Dr Ayman...." Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace "Morning Lydia, hw did u knw I am back?" Tace "I just met with Dr Ahmad, he told me you are back" shafa kai khaleel yayi a hankali yace "Ohk, we will meet later in the day, I am about going out now" tace "Ohk do you mind dropped me?" Ya girgixa kai yace "You get a taxi" daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.

Not edited.🤷🏻‍♀

Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai ba, Babu yabo babu fallasa tace "How may I help you?" Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce "Where is.... the food?" Tace "Wani abincin? I didn't cook with you ai" ya d'an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo yana dubanta yace "This" daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna wanda hakan sai da ya d'an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn, mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn't her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah ta mike ta wuce kitchen don kawo

Please Login or Register in order to submit comment